kuma Aira ta sadda kai.
Washegari Aira na bangarensu ta na Wanki A washing machine Mamy ta lek'o ta ce "Aira idan kin gama ki shirya zaki rakani Gidan Safiya zanyi mata barka" To Mamy Ai na gama ma bari naje na shirya Cikin kankanin lokaci ta shirya a parking space ta tarar da Mamy "Mamy ta ce duk'ursa na goya maki shi " Cikin marairaicewa Aira ta ce "Goyo kuma Mamy ki bari na daukeshi wlh d'annan naki nauyi garai Yaro wata shidda ai Yama wuce goyo ni banma iya goyon ba" Hararta Mamy ta yi ta ce "To yau saiki koya idan dankine wazai goya miki " Dariya Aira tayi ya ce "Maid house mana Mamy yanzu Dan Allah taimaka ki bari na rikeshi a hannu" to Naji raguwa muje Motarta Mamy da dauko tayi mata key suka bar gidan Aira na gaba da Amer a hannunta.
Suna isa gidan Safiya Mamy tayi mata barka Hjy Safiya ce ta ce "Wai Rahama y'armuce ta zama Haka Allah mai iko kice kin kusa Taramu" Dariya Mamy tayi ta ce "Aikodai ku iyaye saiku fara shiri Fita Aira tayi ta basu waje Arman ta kira tayi mashi kwatancen Inda Take cikin k'ank'anin lokaci ya kira ya shaida mata yazo.
tsayuwar Hijab d'inta ta gyara tukwana ta fita A mota ta tarar dashi ciki ta shiga Arman ya ce " kindai maidani bita zaizai ko My cutie duk Inda kikayi ina binki"Dariya Aira tayi ta ce "Yaya kenan ni kuma a kirani da me da duk Inda naje ina kiranka" Sun tab'a Hira Kad'an cikin nishad'i Sun kwashi wajen minti Talatin Mamy koda suka gama fira da Hjy Safiya suka fito sosai tayi mamakin k'in ganin Aira da batayi ba Tana fitowa waje bata ganta ba Aira ko ta cikin mota ta Hango Mamy sosai gabanta ya fad'i ta ce "Na shiga ukku '"
'Kallon Inda take kallo ARMAN yayi ya ce " Daman tare kuke da Mamy"Eh wlh yaya wlh banzaci har zata fito yanzu ba"To yanzu yi Sauri ki fita danma Mamy ce Ai da sauki "Kamar wacce kwai ya fashewa haka Aira ta fito daga motar Sosai Mamy ta kafeta da idanu ganin Fitowarta daga mota Aira ko dukta tsure bin motar da Kallo Mamy tayi Bayan ya tafi Kallon Aira tayi da ta kasa motsi ta daka mata tsawa ta ce " Saikizo mu wuce gida ko"
"Cike da tsoro Aira ta shiga Mota Mamy ta zagaya ta tada Ranta na matuk'ar k'una tama rasa ita ina zata saka ranta game da Lamarin Aira daman basu rabu ba kenan Aira ko duk ta tsure jira take taji zagi ko saukar dukan Mamy amma bataji ba harsuka isa Mamy Saidai ta Kalleta ta girgiza kai ta ma rasa abunda zatace " Suna isa Aira ta ce "Mamy Dan Allah kiyi hakuri" girgiza kai kawai Mamy ta yi ta ce "Allah ya shiryeki Allah ya shiryeki ita kad'aice Addu'ar da zan dinga maki ta fad'a tare da shigewa ciki Aira ko kamar wacce kwai ya fashewa Haka ta shiga part d'in Inna idan ta tuno kuma da karfafa gwuiwar da Inna tayi musu saitaji sanyi A ranta.
Bayan Sati Biyu Da misalin k'arfe goma Na dare Aira na kwance wayarta tayi ringing d'auka tayi Dan tasan Arman ne kad'ai ke kiranta " ki shirya yanzu ina palourn inna zamuje wani wuri,Cike da mamaki Aira ta ce fita kuma Yaya ?ina zamuje a Daren nan "kede kiyi abunda nace kinsan dai bazanyi Abunda zai cutar dake ba Kuma kinfi kowa sanin bansan gardama " Badan Aira ta lamunta ba ta ce To yaya Doguwar Hijab Ta d'auko tare da sanya flat takalmi ta fesa turare d'an Kad'an ta fito a palour ta tarar dashi shida Inna tana fitowa Inna ta ce.
"To kumaza kuje Allah kiyaye" Kallon Mamaki Aira takebin Inna Dashi to ina zasu a Daren nan Arman ko har yayi gaba binshi baya Aira tayi Tana zuwa harya tada Mota da yake ciki ya shigo da ita Aira na shiga suka ja suka bar gidan daman get man ya bud'e musu kofa.
Aira dai zuciyarta cike take ta tunannika kala_Kala"A wani katoton shagon make up taga yayi parking Kallonshi tayi murmushi yayi mata ya ce "muje ko" Itama mayar mashi da murmushin tayi"Ta bishi suna shiga Shagon y'an mata biyu Aira ta tarar Duka sun girmeta Cikin girmamawa suka dinga gaishe da ARMAN ya amsa sama sama Mai kwalliyar ta ce .
"yallab'ai ko ita ce " Gyad'a mata kai yayi ya ce "ita ce so nake kiyi mata kwalliyar da Baki tab'a yiwa wata irinta ba ko nawane zan biyaki" Dariya Zey tayi ta ce "Angama yallab'ai kai kanka dak'yal zaka ganeta" Haka nakeso Rafar y'an dubu ya bata guda biyu Zey sai Godiya take dan yau ta warke Kallonshi Aira tayi Shima ita yake kallo murmushi ya sakar mata bata samu damar mayar mashi ba saboda a tsorace take saikuma ta tuna Ai Arman bazai tab'a abunda zai chutar da ita ba hakan yasa ta saki jikinta.
Fita Arman yayi ya ce zaije ya dawo itadai tana zaune mai make up ta sanyata tayi wanka a toilet d'in Shagon tana fitowa ta bata wata had'ad'd'iyar gown Fara ita kanta Aira saida ta tsorata da ganin rigar Dan bama zata iya kwatanta Misalin kud'inta ba irin rigunan Amaren nan ce Amaren ma sai d'an waye da wane Bayan Aira ta sanya rigar sosai tayi chif a jikinta kamar a jikinta aka d'inka rigar.
Ba b'ata lokaci aka shiga tsansarawa Aira kwalliya ta ban Mamaki saida suka shafe sama da Awa d'aya tukwana aka gama ya subhanalla Ai Ni kaina kasa gane Aira nayi ta sani sauya kamar ba ita ba tayi wata irin masifar kyau Wanda ko mace ta ganta saita yaba da kyan da tayi mai make up cewa take masha Allah a Gaskiya bantaba make up mai kyan wannan ba kodan nayi a jikin me kyau ne kanwata ki godewa Allah Gaskiya yayi miki kyau da baiwa kala kala"
"murmushi Aira tayi ta ce "Nagode hotuna Sosai Zey da abokiyar aikinta suka dinga wa Aira 11:30 Zey wayarta tayi ringing itadai Aira bataji me akace ba daga dayan bangaren Taji dai ita ta ce " Eh Angama Yallabai yanzu haka muna shirin Tahowa da ita ne bada jimawa ba "tana gama wayar itama ita da d'ayar suka shirya cikin wasu Riga da sicket pink rigar siket din bak'i
rigar Anyi rubutu a jiki an rubuta *A & A* k'asar rubutun kuma anrubuta HBD MRS..sauran rubutun taga An rufe da wani Abu ita dai bata tambayesuba har suka gama shiryawa suka fito a wata dalleliyar mota suka shiga Aka jasu suka tafi Basuyi wata diguwar tafiya ba motar ta tsaya Alamun sunzo wajen da zasu Kallon Aira sukayi tare da kama hannunta Zey ta d'auko wani Farin kyalle sai kamshi yake Duka zanan heart ne jikinshi zagayawa sukai suka rufewa Aira idanu dashi itadai kawai binsu take taga ikon Allah.
a haka suka dinga Jan hannunta idonta Rufe suna zuwa wani waje taga sun damk'a hannunta jikin na wani ko wata ita dai bata bambance ba tana nan tsaye anyi kusan 5 minutes tukwana taji Wanda yake rik'e da hannun nata ya fara since mata Kyallen da aka rufe mata Idanu Har ya isa sincewa yana gama sincewa Taji suka wajen ta d'auko satin wak'ar Love mai narkar da zuciya wara idanunta tayi Dan son ganin Da gaskene ko mafarki take Arman ta Kalla dake sakar mata murmushi sosai yayi kyau sanye yake cikin bak'ar coated Fuskarnan tashi Cike da annurin farinciki a cikinta.
Juyawa tayi ta kalli wajen Bata San Lokacin da ta furta Kalmar wow ba "Duka wajen Anyi mai decoration na ban mamaki ko biki Sai y'ar gata zata samu wannan daular Duka wajen kuma robobine ga wasu danjoji da suke Rubuta Happy Birthday Aira Wasu na fita wasu na fitowa ga kuma mutane Sunkai 20 Sanye da Riga An rubuta *A A HBD MRS ARMAN* Photographer ko sunfi biyar hada Camerar gidan wasu gidajen television ta gani bama ta Tantance gidan television d'inba Juyawa tayi ta kalli wata k'atotuwar Laptop dake nuna duk abunda suke Alamun Live Kenan Kallon Arman tayi da ya ke ta kallonta Yasan dole tayi mamakin duk wannan Abun da ya shirya .
Ai batasan lokacin da ta fad'a Jikinshi ba ta saki kuka " Tallabota yayi cikin rad'a ya ce "Kiyi shiru mana so kike ki b'ata make up d'inki ko so kike mutane suce Matar tawa saurin kuka gareta " Dagowa tayi ta Goge hawayenta saikuma ta zumb'uro mai baki Murmushi yayi ya kama hannunta .
A wani makeken High Table suka Je K'atoton cake shake wajen zan iya cewa tunda nake ban tab'a ga cake mai girma da Kyanshi ba Ga wata had'ad'd'iyar agogo dake Juyawa a Gaban wajen Rik'e hannunta yayi Tare da wuk'a a hannunsu.
Mutanen wajen ne suka hau lissaafi daidai lokacin da 12 ta kusa Bugawa 1,2,3,4,5,6,7,8,9,10 Arman ya kama hannunta suka Yanka cake Duka wajen tab'i ya d'auka tare da wakar Happy Birthday Aira sosai wak'ar tayi Bala'in dad'i Aira zata iya cewa cikin rayuwarta bata tab'a shiga farinciki irin wannan ba kwata kwata ta ma mance yau ne ranar birthday d'inta sai yanzu ta tuna .
Ita ta fara bashi cake d'in a baki tukwana Shima ya bata ya na Gama bata Ya amshi Abun magana tare da kallonta duka camera na kanshi
k'asa da kanta Aira Tayi Ya fara magana cikin zazzak'ar muryarshi kamar haka "Alhamdulilla Alhmdllh Alhamdulilla My Love sister she's +1 year God bless you for many more years Happy Birthday Lover for you is the real,real,real,a deal a really ,really really big deal You are my North Star and help me know my direction in life you make me happier and a better person Happy Birthday to you My cutie Aira I Love I Love I Love you so much My Cutie Please Love Me my Aira sannan ya durk'usar da gwuiwarshi har k'asar Inda take tare da kallonta ya had'e hannayenshi biyu Alamun rok'o ya ce " will you marry me?...........βπΏ
*Tofa ya kenan Arman ya k'ara ringimo wata rigimar ya kuke tunanin iyayensu zasuyi idan sukaga wannan birthday d'in a duniya*???
*Wani irin mataki kuke tunanin Abba Da Daddy zasu d'auka Kuna tunanin zasu bari wannan Abun ya tafi a banza kuwa*??
*Yau dai Arman ya fito ya bayyanawa Aira tare da duniya Kalar son yake mata tilon dβan governor guda ya dukursawa mace cikin bainar Jamaβa*
*Iyayensu zasu samu daman raba su kuwa*???
*ya makomar soyayyarsu zata kasance nan gaba Zasu mallaki juna ko akasin haka*
*Idan iyayensu suka samu damar rabasu ya kuke tunanin halin da wannan masoyan zasu shiga yanda suke jin bazasu iya cigaba da rayuwa ba ba tare da d'ayansu ba*
*Shin Abba da Daddy Zasu shirya kuwa*?????
*Duka wannan Amsoshin zaku samesu ne kai tsaye idan kin biya 200 kachal zaku karanta cikin kwanciyar hankali karku bari kice sai an sata a kawo maki ki karanta ba girmanki bane Hajiya ki biya ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali darajarshi tafi ta kudin na barshi hakane a saboda k'auna da soyayya Masoyan Asali*πππ
*wannan shine last page na free page na wannan littafin kamar yanda na fad'a daga yanzu sai Wanda suka biya ne suke da damar ci gaba da karanta wannan k'ayattacen littafin mai cike da salon burgewa sannan duk Wanda zata saya ta saya da zuciya d'aya Karki saya ki fitar mun da Littafi kud'in karantawa kika biya ba na mallaka ba Kunsan dai mahimmanci hak'k'i Sarai bazanyi Allah ya isa ba Ammafa ban yafe ba akwai hak'k'i ni da yaya Arman koda kudinka saida rabonka nasan babu wacce zataso ayi tafiyar nan babu ita ga masu bukatar saya ga tsarin yanda biyan yake*
*Normal group Transfer Ko hoton katin MTN #200 kachal*
*PC Wanda basa buk'atar sakasu group ta PC zandinga tura musu zasu biya #300*
*VTU 300*
*Zaku turo ta wannan number 07026166536*
_Saimun had'e a Paid group_
Taku har kullum
π
*_Miss Hajo ce_*π€πΏ
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels