An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪
𝘿𝘼 𝙎𝙐𝙉𝘼𝙉 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙈𝙀 𝙍𝘼𝙃𝘼𝙈𝘼 𝙈𝙀 𝙅𝙄𝙉 𝙆𝘼𝙄
Chapter 1-------------------
LEGOS NIGERIA
AJEGUNLE
Gidan Ale Idi, babban gida ne da ke ɗauke da mutane mabanbanta, tun daga kan mahaifiyar Ale Ido me suna Inna Tabawa, har kan matan Ale Idi da suka kasance su huɗu reras.
Inna Lantana ita ce mace ta farko da Ale Idi ya soma aura tun auren saurayi da budurwa, yaranta shidda reras biyar maza ɗaya mace ita ce ƴar auta.
Sai Inna Balaraba mace ta biyu da ya aura bayan Inna Lantana, ita ma ta zazzaga na ta yaran guda takwas reras maza da mata (Nan gaba zaku ji sunan kowa kudai ku biyo ni.)
Sai Inna Sabuwa itama ce mace ta uku daya auro bayan matansa biyu itama da tata turigar ƴaƴan su shida, Maza biyu ma ta huɗu.
Sai Mama Saudah mace ta huɗu wacce daga kanta Ale Idi ya rufe ƙofa, kusan za'a iya cewa kaf cikin matayensa ya fi sonta, kasancewarta ba ƙabilar hausa ba, cikakkiyar buzuwa ce gaba da baya, Allah ne ya haɗa zukatansu waje ɗaya, sannan ya dasawa ko wannensu tsananin soyayyar ɗan uwansa.
Gidan Ale idi wani irin birkitaccen gida ne me cike da tarin mutane mabanbanta.
Zazzaume duka ilahirin matan gidan tun daga kan iyaye har zuwa ƴaƴa suke akan tamfal na buhu da aka ɗinka, gurzazzun farantai ne waɗanda du sunyi lamba alamar tsufa ciccike da lafiyayyar jolourp ɗin shinkafa wacce tai jazur da manja, Inna Tabawa kaɗai ce kwanonta daban, amma su duka a haɗe suke cin abinci.
Fira ce ke tashi a bakunan su, su na yi su na buga loma kamar abin dole, sai tabga gardama suke kamar zasu tashi su dambata, amma hannuwansu na cikin kwanuka.
Hankaɗo ƙofar langa-langar da aka yi ne ya dakatar da gardamar, inda kowace ta maida dubanta zuwa ga farar yarinyar da ta shigo bakinta ɗauke da sallama, a madadin su amsa sai Inna Sabuwa tai karaf ta ce.
"Yau ni naga zakama da baƙin hali, ke Najma ba ɗazu-ɗazunan na ji Ale ya gama kashe ma ki gargaɗi akan dawowa gida da ranaba, amma hine ɗan ɗibar albarka zaki tsallake kalamin ubanki ki kwaso jiki raɓai-raɓai ki dawo gida, to ai hikenan gaki ga gidannan ki ci uwar da muke ci, kuma dai hinkawa ta ƙare sai ƙanzo idan za ki karkara ki kai bakin salati."
Tana aje maganar ta rarumo wawakekiyar loma ta wurga baki, sai faman zare idanuwa ta ke kamar shege a rabon gaɗo.
Mama Saudah ce ta zare hannunta daga tiren abinci farar fuskarta zagaye da annuri ta ce.
"Ɗiyar arziƙi irin albarka har kin dawo sannunki da isowa ta shi muje ɗaka in baki abincinki kinji ko ƙyale mahassada da ƴan baƙin ciki."
Ta yi maganar tana zuwa gaban matashiyar ta kamata, babu musu ta miƙe tsaye daga ɗosanon da ta yi a saman botiki ta bi bayan mahaifiyarta zuwa ɗaki.
"Ahayye nanaye, ayidai mu gani idan tusa zata hura gani, ma ji ma gani ai."
Cewar Inna Lantana da ta gama tsotse hannu tas, tare da sakin wa ta ƙatuwar gyatsa.
"Yo ai wallahi ko babu abin da zamu ji mu gani sai takaici, indai Sauda ce da wannan jemamiyar ƴar tata sauran cuta haka zasu dawwama babu cas ba huss."
Cewar Inna Laraba da ta ɗauki tire tana suɗewa.
Taɓe baki wa ta babbar buɗurwa ta yi tare da dire kofin hannunta wanda yai damal-damal da baƙin tukunya da manja, sannan ta ce.
"Yasin Inna kun ishemu da ɗumi, ko narkewa baku bari abincin yayi a cikunanmu zaku dasa da gulma waccw bata ƙarewa, matsalar mutun ya wuni gidanan kenan yasin, ɗuminku du ya gajiyar da mutum ina dalili."
A harzuƙe Inna Laraba ta yunƙuro har tana sakin zane ta ce.
"Kam burar ubanan kayyasa, Sahura ni kike yiwa rahin kunya ɗan abun kazan tsohonki, yau ga lalatattar yarinyar barbaɗaɗɗiya sauran mazan titi, dan ubanki mu sa'aninki ne da za ki raina mana wayo, wallahi tsaf zan ɗage hammata in lakaɗa ma ki hegen duka uwa sakwara."
Ta faɗi tana kumfar baki muryarta a sama kamar me yi da ƴan waje.
Muryar Inna Tabawa ce ta karaɗe wajen cikin kuka irin nasu na tsofafi.
"Yau ni Tabawa naga abin da ya ishi uwata, da mata da ƴaƴa duka ƴan banza, in banda ɗibar albarka ace da tsakar rana zaku gallabi al'umma kai Allah wadai da halinku ƴan bantan uba, ni da gidan ɗana an hana ni in wala, to wallahi gobe zan tattare tsumokaraina in koma ƙauye ina dalili."
Abin mamaki sai duka matan hankalinsu ya tashi, jikunansu suka hau rawa, nan take suka soma bata haƙuri gami da rarrashinta.
Inna Sabuwa ce ta ce.
"Haba Inna tayaya za ki fara maganar barin gidanan, ya kike so mu yi da rayuwarsa, sannin kanki ne Idi sam bamu ne a gabanshi ba, hatta abin da zamu jefa a bakin salati sai ya gagare mu muddin kika barmu, gaskiya ko tahiya za ki yi sai dai ki tahi tare da mu, mu koma can ƙauyen baki ɗaya."
Haka suka shiga rarrashinta gami da ban baki har suka samu ta haƙura, dama rayuwar da ake yi kenan a gidan, Idi yayi rantsewar muddin Inna tabar gidannan to ya gama cida ko wace mace, sun san halinshi kar shiyasa suke taka tsantsan da ɓatawa innar rai.
A ɗakin Mama Saudah, shimfiɗa ta yi wa Najma tabarma, da zallar fara'a a fuska da muryarta ta ce.
"Najma ƴar albarka ɗiyar Mamanta, zauna kici abinci ki more guminki, kina da ni babu ke babu kwamacalar gidanan bari in haɗa ma ki ruwan wanka kiyi ki koma kafin wancan jarababben Idin ya dawo ya hayyace ki da mita."
Lumshe lumsassun idanuwanta Najma ta yi, kafin cikin taushi gami da sanyin murya ta ce.
"Ina son ki Mamana, amma ki bari idan na gama cin abincin zan haɗa ruwan da kaina, nasan kin gaji da yawa."
"A'ah wallahi ban gaji ba sam, ina ni ina gajiya da ɗawainiyar yarinyar kirki yar albarka, ai ni indai hidimar ki ce to gaba na bata ba baya ba, ki huta abinki ƴata ina zuwa."
Cire mayafin kayanta Najma ta yi sannan ta tankwashe fararen ƙafafuwanta ta janyo kwanon abincinta ta soma ci tana lumshe idanuwa, dan Mama Saudah ba dai iya girki ba, sai da ta ci kusan rabi da kwata sannan ta ajiye cokalin hannunta ta ɗauki goran ruwan da Mama Saudah ta aje ma ta, sai da ta shanye ruwan tas sannan tai godiya ga Allah gami da janyo wayarta ta soma latsawa tana jiran Mama Sauda ta kammala haɗa ma ta ruwan wankan.
WANNAN KENAN.
VICTORIA ISLAND
Zazzaune suke a ƙayataccen falon wanda ya gama haɗuwa da tsadadun kaya na zamani ƙirar ƙasashen turawa, gaba ɗaya mutanen da ke zaune a parloun farare tas ƴan gayu na gaban kwatance, zagaye suke da wani baturen matashi su na ta faman maimaita ma shi kalmar "Sorry", yayinda ya ke ta faman jujjuya kanshi gefe da gefe farar fuskarshi ta yi jazur.
Wa ta farar mata ce tallabe da kansa a kan ciyarta tana ta share hawaye gami da ɗaura hannunta a saitin zuciyarshi inda ya riƙe gam da nashi hannun.
"Mommcy anya ba za'a kira Papie ba, kar ciwon yai ƙamari mu kasa control ɗin shi, kin riga da kin san matsalar Broth."
Wa ta farar ƴar gayun budurwa ta faɗa fuskarta a yamutse da damuwa.
"Ko da mun kaishi hospital babu abin da zasu yi ma shi sai allura, kuma yanzu a gabanki ya sake jadadda roƙon kar a kaishi hospital, please kuci gaba da yi mishi addu'a." matar wacce aka kira da Mommcy ta daɗa cikin sanyin murya.
Sake sanyaya jikunansu suka yi, nan suka zagaye shi kuma soma tofa ma shi addu'o'i idanuwansu na zubda kwallar tsananin tausayin matashin.
Tun yana juye-juye cike da azaba har ya fara kafawa a hankali ya soma sauke ajiyar zuciya, amma still hannunsa na damƙe da saitin zuciyarshi, a hankali wahalallen barci ya yi awon gaba da shi.
A tare suke sauke ajiyar zuciyoyi fuskokinsu na sauyawa daga damuwa zuwa farin ciki.
MUZAFFAR MAHMUD DOLLAR's FAMILY kenan, familyn da ke zagaye cikin farin ciki da walwala, basu da wa ta damuwa anan duniya kasancewarsu shahararun masu kuɗi da suka zo lamba ta ɗaya a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta da sauran ƙasashen turawa sun san da tarin dukiyar MUZAFFAR FAMILY, domin kuwa ana damawa da su sosai a harkokin business iri daban-daban, a fanni siyasama ba'a barsu a baya ba, dan sune siyasarma baki ɗaya, muddin suka ambaci sunanka, suka haɗa da ɗaga hannunka, shikenan cikin hukuncin ubangiji kai ka gama hayewa.
Sai de akwai wa ta gaba me ƙarfi tsakaninsu da talaka, a cewarsu talaka sam bashi da alƙawari, talaka butulu maci amana.
(Domin jin yanda zamu warware wannan asalin cakwakiyar ku biyo ni)
Su na taimaka talakawa sosai da gumi da kuma aljihunsu, amma su na bayar da tazara me yawa a tsakaninsu dan sam basu yarda da raɓar talaka ba, bawai dan wulaƙanci ba, A,ah a kwai babban dalilinsu na aikata hakan.
Mahwish Shine babban ɗa a cikin tarin ƴaƴan da ke akwai a MUZAFFAR FAMILY, ana matuƙar ji da shi sosai da sosai, shine hasken idanuwansu kasancewarshi gwarzon jarumi da ke da kyakkyawar alaƙa da kowa, kaf hali da ɗabi'unsa sak irinna Alhaji Muzaffar ne wato mahaifinsa.
Kamar yanda ya zamo ɗan lele a familyn haka kuma ya zamo rauninsu, musamman da Allah ya jabarce shi da matsalar zuciya, ba daga baya ciwon ya same shi ba da shi aka haifeshi, sai de ciwon ya sake tsananta ne bayan ya girma ya shiga shekarun samartaka, inda wani lamari daya girgiza duniyarsa ya faru da shi (Ku biyoni sannu a hankali a sannu zaku ji komi dalla-dalla.) lamarin da ya zaftare rabi da kwata na farin cikin rayuwarsa, sannan kuma ya ƙara tsananta ciwo a gareshi, har sai da takai baya cika sati ɗaya ƙwaƙwara ba tare da ya kwanta gadon asibiti jinya me tsanani ba......✍🏻
Anan zan dasa aya ku kasance tare da Alƙalamin MARYAM STAR dan jin wanda zamu warware zaren da ke dabaibaye da wannan labari.
MABANBANTAN ZUKATA littafin kuɗi ne, a halin yanzu muna free pages ne
KIYI JOINING SABON CHANNEL ƊINA DOMIN SAMUN DAMAR YIN KARATU CIKIN SAUƘI.
M.STAR⭐ WRITER...✍🏻
https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪
💗𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙏𝙀𝘼𝙈💗
𝙘𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 2
Mahwish matashi ne kyakkyawan gaske, ga kyau ga tsari, sannan iya yuwa ka maƙuɗen kudaɗe baibaye da shi gaba da baya, yana gudanar da rayuwarshi cikin tsari kasancewarshi me rauni, akullem yana ƙare lokacinsa ne wajen samarwa kanshi farin ciki, badan komi ba sai dan sanyaya raunananniyar zuciyar, ya sani shi me rauni me, amma baya bari raunin yayi yasiri a kanshi, yana haƙurewa kanshi abubuwa da dama dan gudun tashin ciwonshi, ko yaya yaga abin da zai ɗaga hankalinshi babu makawa sai ya kwanta jinya, jinyar da akullum yake bawa kanshi mutu a kurkusa saboda tsananin a zabar da yake sha.
Jiniyar lafiyayyun jibga-jibgan motoci ƙirar M.B.W ta karaɗe tun daga farkon main get na MUZAFFAR mansion, jere ajere suke tafiya cikin tsari da burgewa, basu tsaya a ko ina ba sai a gaban tangamemen diamond get wanda samanshi ke fitar da rubutu da mabanbantan kaloli an rubuta.
WELLCOME TO MUZAFFAR HOUSE 001, da kanshi get ɗin ya soma buɗewa bayan na'ura ta tabbatar da wanda suka iso, harba motocin kwararun drivers ɗin suka yi har zuwa wawakeken ƙeraren gidan wanda ya gaji da haɗewa, a gari guda ɗin ƙayataccen parking lot suka jere motocin, kafin daga bisani securitys suka shiga firfito kowa na ɗana ƙunamar bingidar hanunsa jiran ko ta kwana, sai da suka tabbatar da komi daidai sannan wani sangameme ya isa jikin motar da tafi kowace ɗaukar ido ya buɗe gidan baya tare da ƙamewa a gefe.
Haɗaɗen tsadadden coven takalmi ɗan zamani ne irin na manyan attajiran duniya ya zuro zuwa ƙasan da aka lailaye da tattausan grass carpet, anɗauki mintuna uku sannan gaggar jikin ta idasa bayyana gaba ɗaya.
Dakakken babban mutum ne me cike da haiba gami da kwarjini na musamman ya fito, cike da izza irinta gogagun attajiran masu kuɗi ya soma takawa ahankali kamar me tausayin ƙasa, du inda ya gifta sai ma'aikata sun ɗurƙusa tare da kwasar gaisuwa, ko kallo basu isheshi ba haka ya ke giftasu ya wuce a binshi.
A daidai sanda ya dira ƙafarsa cikin kyakkyawan parlon nan take gabanshi yai mummunar dokawa, da ɗan sauri ya idasa shigowa tare da yin siririyar sallama wacce babu wanda ya ji shi, bai tsaya a ko ina sai a gaban Mommcy da ke wurga ma shi wani irin kallo me cike da rauni gami da gazawa.
Lafiyayyun nahhayensa ya saka gami da tallafar Mahwish daga jikinta zuwa na shi, nan take ya saki ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya.
One by one mutanen parloun suka shiga darewa kowa na komawa muhalinsa.
A hankali Mommcy ta kwantar da kanta akan kafaɗar me girma MUZAFFAR a tausashe ta saki wani sassanyan kuwa me tsuma zuciya. (Kunsan ƴan gayu komi nasu dabanne🤩😁), Lumshe fararen idanuwanshi da suka soma sauya launi yayi sannan ya kwantar da Mahwish akan cinyoyinsa ita kuma ya janyota zuwa jikinshi tare da soma shafa bayanta sannu a hankali.
A ƙasan ranshi yana jin yanda kukanta ke nuƙurƙusar zaman lafiyarshi, sannan kuma ciwon Mahwish na tayar da hankalinshi fiye da kima.
Cikin muryar ƙuƙa Mommcy ta ce.
"Papie!!😭 bazan iya jurewa ba, nima zuciyata ta kusa daina aiki, ina tausayawa ɗana."
Ta yi maganar tana ƙanƙame hannun Alhaji Muzaffar kamar ance wani zai ƙwace ma ta shi.
"Shshshhhh, ki daina wannan maganar in sha Allah Mahwish zai samu lafiya kamar kowa, ki ɗauki lalurarsa a matsayin jarabawa daga Allah, kiyi ƙoƙari mu cinye jarabawarmu, sannan shi kuma ki ci gaba da tarairayarsa gami da nuna mashi ƙaunar, ki daina nuna damuwa akan abin da Allah ya riga da ya rubuta a lauhil mahfuz, bamu da tsumi bamu da dabara sai a wajen Allah."
Papie ya faɗa da muryarsa wacce da zurfi cike da izza.
Sun ɗauki tsawon lokaci a haka, zirawa kyakkyawar fuskar Mahwish idanuwa suka yi su na tazbihin yanda Ubanjigi buwayi gagara misali ya bawa Mahwish baiwar kyawu, du lokacin da zai motsa yana motsawa ne da nutsuwarsu, domin kuwa Mommcy na jin yanda gabanta ke kakkaryewa yana faɗuwa cike da tsoro, ba komi ta ke tsoro ba sai irin halin da Mahwish ɗin zai iya farkawa a ciki, addu'arta ɗaya ya farka cikin sabun sauƙi da salama, idan kuwa akasin hakan ta faru tana da tabbacin itama sai ta kwana a gadon asibiti.
Mahwish bai farka ba har lokacin sallah ya shiga, hakan ya saka Papie ya sureshi cike da taka tsantsan ya kama hannun Mommcy ya wuce da shi ɗakin barcinsu, ɗakin da ya kasance sirri a garesu kafin samuwar Mahwish babu mahaluƙin da ke shiga, amma a yanzu sun mayar da ɗakinsu su uku, idan dai ba tare da Mahwish zasu kwanta ba to ba shakka ba zasu runtsa ba a ranar.
A kan lafiyayyen gadon alfarma Papie ya aje Mahwish cike da kulawa da taka tsantsan, bayan ya kwantar da shi a hankali ya shafa fuskarahi tare da sumbatar goshinshi da saman dogon hancinshi da yai jazur.
Ita ma Mommcy sumbatar shi ta yi tare da fatan samun lafiya, sannan suka shiga bathroom suka ɗauro alwala a tare suka fito, a nan ɗakin Papie ya ja su sallah, bayan sun idar suka shiga nemawa ɗansu lafiya a wajen me bayarwa kuwa me hamawa Ubangijin dukanin hallita (Allah).
AJEGUNLE
"A ƙalla Najma ta kwashi mintuna arba'in da ɗoriya a cikin bayin tana ƙalƙale farar fatarta, tana jin yanda Yaya Saddi ke ɗuɗɗura ma ta guma-guman ashariya lokacin da ya shigo gidan a harziƙe zai shiga bayi yaga towel ɗinta a kan kyaure, biris ta yi da shi kamar bata san yana yi ba, idan da sabo ta saba da irin banzar rayuwar da ake gudanarwa a gidan na su, tana jin shi ya gama buyagin na shi ya fice, su Inna Labara na sake zugashi su na tayashi kwashe ma ta albarka.
Aiko dai bata yi asarar wanka ba, domin kuwa wani irin sheƙi da ɗaukar ido jar fatarta ta soma yi lokacinda ta fito ta tsugunna cikin hasken rana tana alwalar sallar la'asar data gabato.
"Ke ko wannan yarinya anyi ƴar kwal uba, jarabarki ta gallabi kowa a gidannan, ina ce ko shi kanshi Ale Idi me gidan idan ya shiga bayi ya daɗe yai mintuna goma, amma dan kan bura uba ke idan kika ahiga sai kin kwashe awanni kamar me sauya fata, a haka za ki dawwama ai."
Cewar Inna lantana da ke zaune akan kujera ƴar tsuguno tana tankaɗen garin tuwo, sam Najma bata kulata ba sai ma juyawa da ta yi cikin takunta me kawa da tafiyar hawainiya ta shige ɗakin Mama Saudah.
"Yo ke Lantana in banda iyayi irin na ki miyayi ruwanki da wannan ƙallemar yarinyar marar tarbiya, a kule dai kinsan ba kulaki zata yi ba saboda babu albarka a tare da it...."
Bata ƙarashe ba sai ganin Mama Saudah ta yi tsaye akanta ƙerere ta riƙe ƙugu fuskarnan a ɗaure ta ke faɗin.
"To munafukan Allah ta'ala, masu barci da ido ɗaya, kunbi kun takura rayuwar baiwar Allah ita da gidan ubanta kun hanata sakewa, ku ubanwa ya sakawa naku watsatsun yaran idon akan lamuransu, wato sai ita kuka me daɗin hawa ko, to wallahi tallahi zan rufe ido in zabgagawa ma ta rashin mutunci muddin ta sake shiga harkar ƴa ta."
Aifa dama kamae jira ake nan waje ya kacame aka ci gaba da hayaniya anata kace na ce, sai ɗuɗɗuran guma-guman manyan ashariya ake, daga ƙarshe dai harda taƙa dambe gida ya rikice, tuni aka hankaɗar da garin da Inna Lantana ke tanƙaɗewa ƙasa, aka tattake shi ya shige cikin jar ƙasar wajen wacce ta haɗu da danshin ruwa.
Guntun tsaki Najma ta saki gami da girgiza kai, a fili ta furta, "Allah kyauta halin gidanan". ta ci gaba da shirinta anutse, tsaf ta fito cikin ɗinkin riga da sket mix and match pich colour, yanayin ɗinkin ya bi jikinta ɗas gwanin kyau, duda ba kamata kayan suka yi ba, wadataccen mayafi wanda yai matching da kayan ta gyala irin na manyan ma ta, sosai ta yi kyau kamae ka sace ta ka gudu, fuskarta babu wa ta ƙwalliya face kwali data zizarawa manyan fararen idanuwanta, sai kuma lips glow data shafa shima ɗan kaɗan akan siraran lips ɗinta, amma karku so kuga bala'in kyan da ta yi, kamar me shirin zuwa bikin president.
Lokacin da ta fito hatsaniyar ta lafa dan baka jin muryar kowa sai ta Inna wacce ta raba faɗan tana ta mita gami da kwashe musu albarka tana zaginsu ta uwa ta uba tana kiran sam ɗanta baiyi dace da mata na kwarai ba.
Ina fitowa Ale Idi na shigowa gidan shima yana kwasa kala-kalar ashariya bakinsa har kumfa ya ke dan masifar faɗa.
Karaf idanuwansa suka hasko ma shi Najma take saka tarkacenta a cikin jaka, ashar ya kutuntumo tarw da nufar inda ta ke, da mugun ƙarfi Mama Saudah ta furta.
"Najma ruga da Abbankinan."
A zabure ta kwasa da gudu kamar zata kifa ta fice tana salati, duda haka sai da Ale Idi ya samu nasarar ɗirma ma ta dundu a baya, bayan ya rakata har ƙarshen layi.
A rumfar wani shago ta tsaya tare da maida numfashi, sai ta da saisaita kanta sannan ta tashi bayan ta ƙama sun glasiss a idanuwanta.....✍
KU KASANCE TARE DA ALƘALAMIN.
MARYAM
STAR ⭐⭐⭐
WRITER
Domin morewa karatun zafafan litattan hausa.
Karku manta wannan littafin na kuɗi ne iya book one ne kawai free amma book two paid ne.
https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪
THE SHIDORIA WRITERS TEAM.
Chapter 3
A nitse ta soma tafiya a hanya tana tsallake caɓali da kwatocin da suka baibaye unguwar tasu har ta isa bakin hanya, cikin sa'a ta samu abin hawa nan ta tsaida tare da sanar da shi inda zai kaita, suka yi ciniki ta hau suka ɗauki hanya.
A zahiri idanuwanta na kallon manyan gine-ginen kamfanonin da ke wajen, amma a baɗini ta yi nisa ne a duniyar tunanin irin rayuwar da ake gudanarwa a gidansu, wa ta rayuwa da sam babu tsari a cikinta, tana tsananin son ahalinta son da ya zarce gaban kwatance, amma tana tsananin jin haushin irin rayuwar da ake gudanarwa a cikin ahalinnata, daga ka karyo kwanar layin gidansu zaka fara jin ɗure-ɗuren ashariya iri da kala na tashi, ko kuma ka ji ƙarar doke-doken faɗa, ba daga yaranba ba daga iyayenba.
A daidai makeken babbar ma'aikatar aka sauke ta, inda ta zaro kuɗinshi ta bashi sannan ta soma yakawa cikin sassanyan taku me