Share this page
6 / 7
tallabe da kumatunka ta yi nisa sosai a duniyar tunani har batasan zuwan matar da ke tsaye a kanta ba tana ƙare ma ta kallo cike da takaici. Girgizar da ta yiwa kafaɗarta ce ta dawo da ita duniyar zahiri, a ɗan firgice ta ke kallonta tana murtsuke ido, a sanyaye ta ce. "Sorry Mamaah ban san da zuwanki ba wallahi." ta faɗa tana share guntuwar ƙwallar data silalo akan idonta. "Wai ke Najwa yaushe za ki daina tunani akan wancan matacen wanda ya jima da mutuwa, a kullum kina ƙara ƙona raina idan na ganki a irin wannan halin, ko ki so ko ki ƙi, wannan yaron ya mutu, ya jima da mutuwa Najwa." Kallon matar ta yi idanuwanta na sake cika taf da zazzafar kwalla murya a hasale ta ce. "Ya mutu, tabbas ya mutu a idanuwanki amma banda nawa idon, ni nasan bai mutu ba, Mahwish bai mutu ba Mamaah, na sani kin sani shi ɗin yana da rauni, munyi amfani da rauninsa muka cutar da shi amma tabbas ni nasan yana raye, cuta ba mutuwa bace bare kuma dama can ya jima da ɗanɗara zafin ciwo, kina tunanin dan na yaudaresa shikenan zai mutu, a'a zai rayu, ni nasan zai rayu da ace zai mutu da tuni ya mutu Mamaah, tun kafin in shiga rayuwarsa, kin san raɗaɗi da azabar da nike fuskanta kuwa, kin san iri ɗacin da zuciyata ke yi, ba Mahwish muka cuta ba Mamaah kaina muka cuta, bai aikata komi bai da zunubin kowa, amma mufa, ga dukiya nan mun tara amma ta gagara ciyuwa a garemu, indai kuɗi ne mun samu a wajensa amma tsoron cin su nike, nasani ni da shi muna da MABANBANTAN ZUKATA, ni tawa zuciyar baƙa ce ƙirin saɓanin tashi da take fara ƙal mai nufin kowa da alkairi, Allah sarki Mahwish bawan Allah, bawanda ya ke kwanciya yana tashi da ɗumbin gafarar Ubangiji akan jinyar da ya jarabeshi da ita." .......✍🏻 Taufa masu karatu kun ji mun buɗo wani shafin kuma, ku biyoni sannu a hankali dan jin yanda zata kaya. LAST BORN wannan shafin naki ne baki ɗayansa alkairin Allah ya kai miki sister💞 CIKIN IKON ALLAH MUN TAHO GANGARA, DAMA TUN A FARKO NA FAƊA MUKU BOOK ONE FREE NE AMMA BOOK TWO PAID NE, GA MASU BUƘATAR KARATUN LITTAFIN MABANBANTAN ZUKATA BOOK TWO DA ZARAR MUN GAMA BOOK ONE ZAKU IYA NEMAWA A WANNAN LAYIN. 0912636748 NAGODE MASOYA, ALLAH YA HAƊA MU DA ALKAIRI AMIN NI CE TAKU MARYAM STAR ƳAR BAIWA (RAYAM STAR⭐) https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 11. Zama Mamaah ta yi kusa da Najwa sannan ta dafa kafaɗarta tare da faɗin. "Daga yau kuma yanzu anan ina umartarki da ki cire Mahwish da tunaninsa akan ki kwata-kwata, ban yafe maki ba idan har kika sake bari tunaninsa yayi galaba akan ki, babu ke babu shi, sannan ki sake sabon shiri domin kuwa nayi maki wani sabon kamu, ina so ki nutsu da kyau dan mu fara shiri." Har zuciyarta tana tsananin danasanin irin baƙar rayuwar da suka zaɓawa kamsu ita da mahaifiyarta, amma bata da yanda zata yi, dolene ta ƙarasa abin da ta ɗauko, domin kuwa ita ta wayar wa Mamaah ido ta hanyar damfarar samari su samu manyan kuɗaɗe masu nauyi, sai kuma gashi mahaifiyar taata ta zarceta a yanzu, a yanzu da ita ta tsani harkar tsana me yawa, saboda manyan dalilai guda biyu. Ta shi ta yi daga wajen ta shige wani ɗaki tana ɗauke kwallar idonta, kai tsaye toilet ta shige bata jima ba ta fito jikinta na ɗigar ruwa da alama wanka ta yi, a ɗan gaggauce ta shirya cikin riga da wando waɗanda suka kame jikinta kam, sai wani yalolon vail data yane kanta da shi, babu laifi kyakkyawa ce, sai dai ba iya kyawunta ne yake haskata ba, harya irin wayewar da ta yi ya sake fitar da kyawun nata. "Mamaah ina so zan ce hospital dan a duba ni, har yanzu ƙirjina yana yi min nauyi sosai, har nakan kasa yin numfashi da kyau, idan na dawo zamu ƙarasa maganar." Tana gama faɗin hakan ta juya a gaggauce ta fice ba tare data jira cewar Mamaah ba, dan kuwa a ƙage ta ke ta bar gidan ko ta samu sauƙin abin da ta ke ji. (To ke Najwa ta ina zaki samu sauƙi alhalin kin cuci ɗan mutane, ai haƙƙi bazai barki ba kema.) LEGOS NIGERIA. A cikin ƙasa da wata ɗaya, ƙaƙƙarfar alaƙa me ƙarfi da gifta a tsakanin mitane biyu masu MABANBANTAN ZUCIYOYI. Mahwish ya kamu da soyayyar Najma me tsananin gaske, sai dai ya kasa bayyana ma ta, kamar yanda itama sannu a hankali tsananin ƙaunarshi ta dabaibaye zuciyarta, duda tana gayawa kanta shiɗin ba ajinta bane, musamman ranar da suka ji labarai ita da Inna aka dinga lissafo manyan kamfanoni guda biyu da Alhaji Muzaffar ya kyautar, kuma ba wani nashi yayiwa kyautar ba wani babban ɗan siyasa ne wanda ke tsimakon talaka bakin gaskiyarshi, lokacin da Inna ke bata labarin ai shine ya bayar da maƙuden kuɗaɗe lokacin da ta kwanta jinya sosai kanta ya ɗaure, da kuma Ale Idi ya shigo aka dasa firar da shi sai yake bawa Inna labari ai Mahwish ɗan Alhaji Muzaffar ne, daganan bata sake sauraren firarsu ba, ta nutsa a kogin tunanin ta yanda aka yi ta ke waya da babban mutum ɗan manyan masu arziƙin Nigeria wato Mahwish, kanta bai idasa kullewa ba sai da ta kwantar da haƙarƙarinta a kan gado tana jiran kiran wayarshi, magana ta farko da tayi bayan sallama ita ce. "Da gaske kai ɗa ne ga shahararen mai kuɗinan wanda sunanshi ke yawo a mujallu wato Alhaji Muzaffar?." Amsar da Mahwish ya bata kai tsaye ita ce ta tsiyaye man kanta tas. "Ih Najma, ni ɗanshi ne, ya aka yi ne." Ya amsata da iya gaskiyarshi da ta karanta a maganarshi. "Tayaya haka?." Bai gane abin da ta ke faɗi ba dan haka sai ya idasa daskarar da kwanyarta ta hanyar faɗin. "Ai baki saniba kullum gabanshi shi da Mommcy muke wayafa, yanzu haka wayar na hannun Papie bara ku gaisa." Bata jira ya isada faɗi ba tai wani irin tsalle ta diro daga kan kagon ƙarfe inna tana ƙoƙarin datse kiran, sai de kuma kafin ta yanke ɗin ta tsinkayi cikakkiyar muryarsa me cike da zallar izza na yi ma ta sallama, 'Yah Allahi yah Rahaman.' shine kalmar da ta faɗi a zuciyarta, a fili kuma ta amsa sallamar tare da soma gaisar da shi a mutunce, bayan gaisuwar kuma sai ya ta sake tsinkayo lallausar muryarsa na faɗin. "Ga Mommcy itama ku gaisa." Itama da girmamawa ta gaisar da ita, tsananin mamaki na kassara tunaninta. Daga wannan ranar ta zaɓi janye jikinta daga Mahwish, saboda nesa ba kusa ba shi ɗin ba ajinta ba ne, babu wani abu da zata tsinta idan taci gaba da alaƙa da shi, saima cutar da kanta da zata yi. Daga ranar da ta fara ƙauracewa kiran wayar Mahwish ta gagara samun sukuni da walwala, wunin ranar a ƙuntace ta yi shi, hakama da tazo kwanciya juye-juye tai ta yi sautin muryarshi da yanda ya ke magana na yi mata gizo, da kyar ta samu barci ya ɗauketa, daga ranar bata sake yarda ta kunna wayarta ba, sai ma sake ma ta wajen ajiya da tayi, ta kuma tattaro litattafan karatun addini ta samu Ale Idi da maganar tana son komawa makarantar islamiyya, ya so tambayarta batun komawa aiki amma sai ya share, da kanshi ya kaita wa ta sabuwa da aka buɗe, tun a wajen gwaji da aka yi mata malamin ya ce ai ita ta zarce a koyar da ita, sai de su ɗauketa ta koya kasancewar suna fuskantar ƙarancin malamai, aji uku aka kaita a matsayin malama, dan sosai malaman suka yabawa ƙoƙari da gazaƙarta, a cikin farin ciki ta koyar da su karatun Ƙur'ani, tana tunano faɗar Manzon Allah a wani hadisi inda ya ke cewa. "MAFI ALKAIRIN CIKINKU SHINE WANDA YASAN ALƘUR'ANI KUMA YA KOYAR DA SHI". Ko gida bayan ta dawo ana firar dare bata saka musu baki ba sai bitar karatukanta da ta ɗauke mata hankali taci gaba da yi, duda irin busy da take saka kanta, sam tunaninshi bai bar kwanyarta ta huta kona second ba, ko bayan da ta gama komi ta nufi wajen barcinta, hakanan ta kwanta tana ta juyi kewarshi na addabar zuciyarta, tana jin Inna na mitar yanda ta ke juyi har tana faɗin idan bata da lafiya ta tashi ta nemi magani amma tai biris da ita, da kyar da haka barci ya ɗauketa bayan ta raba darw tana juyi, a cikin barcin ma sam bata huta ba, dan mafarki tayi akan shi. Da kyar ta sabawa kanta rayuwa ita kaɗai kamar yanda ta ke yi a baya, tana zuwa makaranta ta koyar idan ta dawo ta tattara yaran gidansu suna ta koyar da su, duda ba ƙaramin ciwon kai suke bata ba amma ahaka take jurewa, dan bata so su taso babu ilimin addini a tare da su, to dama gashi ba wargi take ɗauka ba hakan ya saka suke jin shakarta, idan tayi ƙari kowa ƙoƙari ya ke ya iya, idan ko mutum bai iyaba sai ta dake shi ko a gaban babarshi ne. Haka rayuwa taita haurawa har aka kwashe satika uku kwarara ba tare da wa ta magana ta sake shiga tsakaninta da Mawish ba. A ɓangaren Mahwish kuwa kwana biyu sam baya jin daidai ga matsalar rashin samun Najma a waya da yake, haka zai tasa iyayenshi a gaba yana musu mitar yana son zuwa dubata amma sai Alhaji Muzaffar ya dinga kawar da tunaninshi akanta, ga ciwo da ke ta cinsa a tsaitsaye, a kwana na uku ne ciwo yaci ƙarfinsa, ko tashi baya iya ci numfashima a hankaki yake yinsa, babu shiri aka kaishi asibiti, kafin su isa tuni ya shiga mawuyacin hali, likitoci sun jima akanshi kafin suyi nasarar daidaita numfashinsa, bai farka ba sai da ya kwashe kwanaki biyu cur, kuma koda ya farka ɗin baya iya cewa komi, zai buɗe idonshi na ƴan mintoci sannan ya sakw kulle su, sai da ya kwashe sati guda babu wani ci gaba, ganin hakan ya saka Alhaji Muzaffar shirya musu tafiya, zuwa ƙasar turawa, kusan ƙasashe uku su na zuwa ganin manyan likitocin zuciya, amma sam babu wani ci gaba sai magana ɗaya da ake maimaita musu, maganar da ke sake hargitsa tunanin Alhaji Muzaffar, du inda suka je ganin likita za'ace da su. "Yaronku na da matsalar zuciya, ba lallaine ya rayu kamar kowa ba saboda raunin da yake da shi, zai rayu ne kawai idan ya samu wanda zai taya shi ɗaukar abin da zuciyarsa bata iya ɗauka ita kaɗai " Idan aka yi wannan maganar babu abin da ke zuwa kan Mommcy da Papie irin hoton fuskar Najma, musamman a ranar da aka kwantar da ita gadon asibiti da tarin raunika a jikinta, bama wannan ba, wani abu na musamman suke hangowa a tattare da ita, wanda a ganin su na farko da ita suka lura da hakan, tsanani jarumtaka da taurin zuciya suka gani a kwayar idanuwanta a lokacin, sannan yanayin da Mahwish ke waya da ita, da irin dakiyar da ke ciki tata siririyar murya ya sake haska wani abu game da ita a kawunansu, sai de akwai abu ɗaya daya gina babbar katanga a tsakaninsu da ita, ba komi bane wannan abun face kasancewarta talaka, ita ɗin ƴar talakawa. Ko bayan da Mahwish ya farfaɗo ya samu kanshi, tambayarshi ta farko ita ce ina Najma, yarinyar da ko a yanayin jinyar daya tsinci kanshi yana jin yanda raunananniyar zuciyarsa ke dokawa da tsananin ƙaunarta, ƙaunar da yake jin zata iya zama ajalinsa muddin ya rasa ta, ya rasa hope a karonshi na farko daya faɗa soyayya a wannan karon yana fatan mallakar abin da zuciyarshi ke so, ko zai samu rangwame daga azaba biyu, azabar raɗaɗɗin ciwo da kuma azabar azababbiyar ƙauna, wacce ta ƙulle da ruhinsa a zare ɗaya. Wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyar Alhaji Muzaffar, a tunaninsa hakan zai zama kaifin datse du wata alaƙa da zata sake haɗa ɗanshi Mahwish da talakawan mutane, sai de ba tare da saninshi ba tabka ƙaton kuskure, kuskuren da zai iya shafar sauran ƙanfin daya ragewa tilon ɗansa, da ace yasan abubuwan da zasu faru marasa daɗi idan ya aikata abin da zai aikata ɗin, da tun a matakin farko da zuciyarsa ta bashi shawarar yayi fatali da ita, bayan hakan ya kulle zuciyar yasa me ya hanata sake tunani na tsawon lokaci dan kar ta sake maimaita ma shi abin da ta maimaita, sai de kash alƙalamin kaddara ya riga da yayi rubutu akan faruwar lamarin.....✍🏻 KU KASANCE DA AKƘALAMIN RYAM STAR DOMIN SAMUN CIGABAN WANNAN DADDAƊAN LABARIN. SAURA ƘIRIS MU IDASA BOOK ONE MA'ANA FREE, ASALIN ZALLAR CAKWAKIYA NA NAN GABA. KU KASANCE TARE DA NI. 09112636748 Only whatsapp 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 12 Daga ƙasar da suke ya bayar da umarni ta waya akan cewa yana so a tayar da duka mutanen da ke unguwar AJEGUNLE gaba ɗayansu cikin kwana ɗaya jal, maƙuden kuɗaɗe ya ɓarnatar akan a bawa kowane gida, sannan au tashi cikin hanzari. A safiyar ranar Asabar ne saƙon tayar da unguwar ya riski iyalan Ale Idi, nan kowa ya shiga safa da marwa bayan gama jajanta lamarin, mama Saudah ce ya ce. "A ganina tunda ance kowa ya tashi cikin mutunci ya kamata ace mu soma haɗe kayanmu mu jirayi tsammani, ance su na biyan kuɗaɗe masu kauri, idan kuma aka saka musu taurin kai sai su bazar da gidan gara kawai mu haɗe kan kayanmu mu zama ready idan Allah yasa babu mu cikin waɗanda za'atayar falillahil hamdu." Cike da gamsuwa da zancen Mama Sauda aka shiga harhaɗe kan ilahirin shirgin gidan, sun jima su na aiki tuƙuru, basu suka gama ba sai wajajen azahar, lokacin jikunnansu du a sanyaye, su na zaman hutawa ne Ale Idi ya shigo gidan, bai ce da kowa komi ba ya dire jakar kuɗaɗe a gabanshi sai ya tallafe goshinshi yai shiru, Inna Lantana ce tai ƙarfin faɗin. "Lafiya dai ko?." A nan ma bai ce komi ba sai jakar da mayar gefen Mama Saudah sannan ya ce. "Sauda idan baki komi dan Allah ki ƙirga kuɗaɗenan, kuɗin gidannan ne aka bani yanzu dana dawo zan shiga gida, sun ce kar mu wuce gobe bamu tashi ba, wai rusau zasu yi." "Oh ni Laraba yau muna ganin jalala, ita kuma wannan gwamnatin haka zata yi da mu?." Ta yi maganar tana jinjina kai. "A,a Laraba wannan aikin bana gwamnati bane, a majiya me ƙarfi na ji wai wannan shahararen me kuɗin ne yake son unguwar zai gina babban kamfani, aikin ya taso cikin gaugawa shine aka bama kowa kwana ɗaya ya tashi, sauƙi-sauƙinma dai suna biya me kwari naji ance." Wani abu ne me kama da mashi ya soki zuciyar Najma da ke ɗakin Inna tana harhaɗa sauran kayanta, cak ta tsaya da komi jin yanda kanta ya shiga sarawa, zuciyarta ta soma tafarfasa tana hayaƙi, a hasale ta soma taka ƙafafuwanta da niyyar ta fito waje, ta yi nasarar fitowa amma bata idasa isa wajensu ba jiri ya kwashe ta, tai taga-taga ta faɗi ta baya. A kuje suka yo kanta amma sai da Inna Laraba ta ɗauki jakar kuɗin ta jefa ƙofar Mama Saudah. Ruwa Inna kw shafa ma ta a fuska amma shiru babu wa ta alamar da ke nuna tana numfashi, du wani abu da zasuyi ma ta, sun yi amma shiru babu wani ci gaba, shawarar zuwa asibiti Inna ta bada ganin an kwashe awa ɗaya babu wani ci gaba, haka suka rankaya aka tafi zuwa asibiti kowa da irin fargabar da ya ke, a canma likitoci suka duƙufa akan Najwa sun yi ƙoƙarin daidaita numfashin ta hanyar saka ma ta abin shaƙa, amma bata farko ba, har dare babu wani bayani, hakan ya saka Ale Idi komawa gida yayi shawara da Inna akan ko dai su haƙura da zaman Legos su koma gida hakanan sai a nema ma ta na gargajiya, dan abin ya soma bashi tsrono, Inna ma tayi na'am da hakan badan komi ba sai dan dama ita ta jima da gajiya da zaman Legos tana son zama cikin ƴan uwanta da sauran abokan arziƙi. Lokacin da aka zauna cin abincin dare ne ya sanar da sauran matanshi batun barinsu Legos gobe, dukansu jikunnan su sunyi sanyi dan basu son komawa ƙauye, sun saba da zaman birni, hakanan ba don san ransu ba suka amsa shi, ganin sun amsa ya saka inna ce. "Barin Legos ba shi ke nuna zako koma ƙauye da zamaba, Idi zai yi magana da abokinsa da ke dillacin gidaje a Katsina sai ya sama sa shi gida acan sai ku koma, amma nidai zan tafi ƙauye cikin dangina in zauna." Sosai suka yi farin ciki da hakan, suka zauna jiran tsammani. Bayan Ale Idi ya yiwa Mama Saudah bayani, sai ya nemi sallama a wajen likita, dama ƙaramar asibiti ce babu wani ƙarin bayani aka basu sallama suka rankaya gida da Najma wacce take kwance kamar gawa. MATAKI NA FARKO. Matakin farko daya fara gida bagon ƙadarrar da ya gifta atsakanin MABANBANTAN ZUKATA, waɗanda suka cure a waje ɗaya shine barin Ale Idi da iyalansa a washe gari suka kama hanyar barin Legos da sanyin safiya. Yayinda jirgin Alhaji Muzaffar da iyalansa yaiwa garin Legos tsinke a safiyar ranar, ranshi fes da tunanin ya raba alaƙar ɗansa da talakawa, rabuwa ta har abada, tun da gaba ɗaya unguwar ya siye ya saka a mayar da ita flate, mataki na biyu kuma dayabi wajen sake ruguza ƙaƙƙarfar alaƙar da ubangiji ya haɗa shine saka gidan layi lalata wata lamba wacce Mahwish ke waya da iya, ba tashi lambar aka lalata ba, wancan layi dai na ƴar talakawan ya saka aka lalata shi ta yanda baza'a sake kiran waya ya shiga ba. Yana cikin farin cikin dawowa da Mahwish gida cikin ƙoshin lafiya, shi kuma Mawish yana cike da ɗokin san yi tozali da wacce ta zama bugun zuciyarshi gaba ɗaya, yana ji ajikinsa yana da gwarin guiwar tunkarar gidansu, gidansu da hotonshi ke zane a kwanyarshi, bana iga gidanba, du wa ta hanya da ake bi wajen zuwa unguwar ta su tana zane ne a kwanyarshi, yana jin yanzu ne lokaci mafi dacewa da zai tunkareta ya bayyana ma ta kalmar da zata wanzar da ɗorarriyar alaƙa a tsakaninta da shi, sannan zai sanar da ita rauninsa, yana buƙatar ta bashi ƙwarin gwuiwa a yayinda ya gaza, zai buɗe ma ta sirrin zuciyarshi da kuma sirrin rayuwarshi gaba ɗaya, tun da suka sauka a jirgi aka zo ɗaukarsu ya ke ƙawata fuskarshi da murmushi me kyau, ya kuma zaɓi yin tafiya da ƙafafuwanshi tun daga sauka akan matattakalar bene har zuwa wajen mota, a maimakon shiga mota ɗaya da iyayensa sai ya zaɓi wa ta motar daban ya shiga yana ɗaga musu hannu da murmushi akan fuskarshi. A madadin murmushin fuskar Mahwish ya burge Alhaji Muzaffar sai tsintar kanshi ya yi cikin wani yanayi me kama da fargaba, amma sai ya dake shima ya ɗaga ma shi nashi hannu ya shiga mota shi da Mommcy suka jera akan layi su na barin airpot ɗin. Ko da suka isa gida cike da farin cikin ganinsu mutanen da ke rayuwa a gidan suka tarbesu, abin mamaki shine yansa Muhasin ke nan-nan da Mahwish, mutumin da kowa na gidan ya kwana da sanin rashin jituwar da ketsakaninsu, amma sai gashi ya taryesu da annuri akan fuskarshi yanayin da ya sosa ran Mahwish ganin yau ɗan uwansa ya yarbeshi da sakin fuska. Bayan ya tashi daga barcin huce gajiya, duda jikinshi babu kwari sosai hasalima ƙarfin hali kawai ya ke yi, sai ya hau shiryawa cikin shiga ta musamman, babbar shaddace yar ubansu blue kala, wacce ta ji lafiyayyen tsadadden ɗinki irina hausawa, ba ƙaramin kyau shaddar ta yi mashi ba, ya ɗauki tsadaddiyar hula ya kafa asaman lallausan ɗan kaɗan ɗin gashin kansa wanda bai da cika sai tsayi, agogo wacce sam bai damu da sakawa ba ya ɗauka ya saka a tsintsiyar hannunsa, ba ƙaramin kyau me daskarar da zuciya ya yi ba, ko da ya kalli wawakeken mirron da ke kafe a ɗakin sai da ya saki ƴar ƙaramar dariya, a zuciyarshi ya shiga hasaso yanda Najma zata kalle shi da waɗannan jaruman idanuwanta masu tafiya da nutsiwarshi. Sosai Iyayenshi suka shagala da kallonshi lokacin da ya fito, zaka rantse ba shi bane ya kwanta tsawon sakita jinya asibiti kamar bazai rayuba, bayan ya zauna a tsakiyarsu a taɓare ya kallesu su duka biyun sannan ya ce. "Ku yi min addu'a zan je in buɗewa wa ta zuciyata." Idan na ce faɗuwa na rage ƙarfin abin da gaban Alhaji Muzaffar ba ya yi, kwankwatsewa gaban shi ya yi da tsananin ƙarfi har bai san lokacin da ya ce da sauri. "Wcece wannan, miyasa kaza yi haka, ka manta bakada lafiya ne?." Babu tunani komi Mahwish ya ce. "Najma ce tauraruwar zuciyata, zan je in sameta in sanar da ita ina tsanani ƙaunarta dama jinyar ai ta kewarta ce." Wata irin zuface ta shiga tsatstsafowa Alhaji Muzaffar, kafin yasan abin cewa Mahwish ya bisu da sumbata, sannan a gaggauce ya fice. Zuciyarshi ta soma sauya bugu ne daga lokacin da bahaushe driver ɗinsa ke sanar da shi ai antashi unguwar da ya sanar zasu je, gardama ko musi sam ba halinsa bane, amma haka ya sake jadadda akaishi can cikin kaushin murya, tiryan-tiryan ya ke ƙarewa hanyar kallo, yana nazarin wasu abubuwa, zuciyarshi cike fal da farin ciki. A daidai lokacin da suka shiga kwar ne idanuwansa suka soma hasko ma shi filayen gidajen da aka barbaje, a kuma daidai lokacinne motar rusau ta tinkarin gidansu Najma, tare da bi takanshi nan take ya faɗi rugu-rugu a ƙasa, wa ta iriyar zaburarriyar ƙara Mahwish ya saki daga cikin motar, hakan yayi daidai da taka birki da sauran drivers waɗanda ke tuƙa security suka yi. Ta ɓalle mota da fitarshi akan ƙafafuwan da suke lankwashewa duka ya faru ne cikin abin da bai gaza second biyarba, kafin ƙafafuwansa su idasa kaiwa wajen da ya ke iya hangen ƙurar ƙasar gidan Ale Idi tuni motar ta gama tushe gidan tabi takan na kusa da shi. Wa ta razananniyar ƙarar ya sake saki, tare da durƙushewa akan sagaggun gwuiwoyinsa ya dafe kanshi dake barazanar ɓallewa saboda ciwon daya dirar ma shi nan take, a cikin kunnuwansa ya ke jin ƙarar bashewar glashin zuciyarshi, kamar yanda yake ganin yanda aka ruguje gidansu Najma, nan take a wajen ya yankewa kanshi hukuncin haƙura da rayuwa na har abada, domin kuwa idan har ya sake yai gangancin cigaba da rayuwa ba shakka sai ya gwammaci mutuwa, Najma ta zama rayuwarshi gaba ɗaya rasa ta tamkar rasa tashi rayuwarne, nan take bayan ya gama yankewa kanshi hukunci ya ɓingire a wajen. Hakan yayi daidai da isowar Alhaji Muzaffar harma da matarshi Mommcy wajen hankulansu a mugun tashe, domin kasa jurewa ya yi bayan fitowar Mahwish ya labarta ma ta abin da ya faru, ko kafin ya gama bata labari tuni tayi waje babu ko mayafi tana kiran sunan ɗanta, sai dai kuma lokacin har motocinsa sun gama ficewa, a yaune rana ta farko da bata tsaya sauraren jawabi daga bakinsa ba kai tsaye ta wuce shi da sauri ta bada umarnin a ɗauko motoci cikin gaugawa, koda aha jere motocin idanuwanta a rufe ta shiga ta zauna tana bada umarnin a tafi, sam bata san da shigowar Alhaji Muzaffar motar ba sai da aka tayar sannan ta tsinkayi muryarsa, karo na garko

Chapter 6 of 7