Share this page
5 / 7
Ale Idi da Najma a cikin unguwar VICTORIA ISLAND, kuma du inda aka tsare su sai an bincikesu, a hakama dan su na nuna katin asibitin LAGOON ne shiyasa ake kyalesu. A daidai get na biyar ne mai adaidaita ya sauke su ya ce shi bazai iya ƙarasawa ba ya gaji wallahi, dan haka tun da ba tafiya sosai su idasa da ƙafarsu, magiya Ale Idi ya soma yi akan ya daure zasu ƙara musu kuɗi amma ya ƙi, hakan ya saka Najma ta sauka ta nemi waje ta tsaya tana jiran fitowar Ale Idi, ganin ta sauka ya saka shima ya sauka bayan ya biyashi kuɗinshi kusan dubu biyar. Tafiya suke Najma na kalle-kallen yanayin wajen tana mamakin yanda akwai irin wannan shahararrun unguwar a nigeria, ita wallahi ta ɗauka sai a ƙasashen turawa da ake nunawa cikin film ke da irin haka, ashe a cikin garin da ta ke akwai irinsu sani me bata taɓa yi ba. Wasu arnan motocine lafiyayu sabuwar ƙira suka tsaya daidai saitinsu, sau ɗaya ta ɗaga ido ta kalli motocin tai saurin kawar da kai gabanta na faɗuwa ta ci gaba da tafiya ba tare data damu da tsayuwarsu gefensu ba, fatanta kawai su isa ciki suyi abin da zasu yi subar wannan unguwar.....✍🏻 MAZA-MAZA KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZA TA KAYA. INA ƳAN TEAM MAHWISH KU MATSO KUSA DA NI🗣️🗣️🤩🎊 PLEASE LIKE SHARE AND COMMENT. NI CE TAKU MARYAM STAR ⭐⭐ ƳAI BAIWAR JAJIRTATTU WEITER'S https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 9. Haka kawai ta samu kanta da tsayawa cak, dalili wani sauti da ta ke tunanin iska ne ya ɗauko ma ta shi zuwa cikin kunnuwanta, amma mi ba iya sautin kaɗai ba, harda muryar Ale Idi ta ji yana ambatar cikakken sunanta. "Fatima tsaya manah." Shine abin da ta ji, sai kuma ta sake jin wannan tattausar muryar na tambayar Ale Idi ina zasuje, ji tayi da ace tana da dama da tuni ta saka remote ta tariye amsar da Ale Idi sai bayar, ta saka play daidai inda zai sake yin magana, aiko sai da Ale Idi ya bashi tun daga farkon labarin fitowarsu gida yau har zuwa yanzu, ta saki wa ta ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ne a sa'ilin da ta jiyo muryar na faɗi. "To ku shigo mu ƙarasa nima zan je asibitinne zanga doctor." "Yah Allahu ya Rahaman ka kawo min ɗauki." Najma ta furta a daidai lokacin da ta ke ɗaura hannunta me lafiya sitin zuciyarta da take jin wani abu na narkewa kamar yanda ƙanƙara ke narkewa, ba iya abinne kaɗai ya narke ba, ya narke ne tare da wani ɗaurin data kwashe satika tanajin zuciyarta ta yi, bama iya wannan ba, jinta ta ke fresh batada damuwar komi a rayuwarta, komi ya goge daga zuciyarta sanyin salama da nutsuwa ta soma sauko ma ta. Ji tayi koda sau ɗaya ne, tana so, tana so kawai ta ganshi koda a fizgenw, badan komi ba sai dan wani abu, wani abu wanda itama batasan ko minene ba. Saukar manyan dara-daran idanuwanta kalar madara a kan innocent pace ɗinshi, ya saka zuciyoyi biyu mabanbanta motsawa tare da soma harba jini ciki sauri da karsashi. Ita da ta ke nesa ita ya kamata ace ta karaso, amma sai ya ji bazai iya jure tsayuwa a inda ya ke ba, zai je ya isketa ya sake kallon tsakiyar cikin idanuwanta masu fizgar gami da ɗaukar hankalinshi. Abu na ƙarshe da bai zo tunaninta ba bayan zuwanshi gareta shine, kama hannuwanta duka buyun masu ɗumi da taushi da yayi a cikin nashi masu laushi da sanyi, sanyin daya haɗu da ɗumin hannunta suka bada wani abu na musamman, na musamman wanda ya soma aiki a mabanbantan zukata masu buƙatar samun kusanci na sosai. Hannayensa na cikin na ta ya soma takawa da baya-baya, dan bai jin zai iya sakinta saboda yanda yake jin sauyi na musamman na baibayeshi. A karo na farko a rayuwar Najma data nemi inda taurin kanta da kafiya ya ke ta rasa, lokaci na farko data sallamawa wani namiji jikinta tana cikin hayyacinta, kuma lokaci ɗaya da ta ji zuciyarta ta buɗe, buɗewa irinta son shigar da wani abu me girma da muhimmanci a cikinta. Lokacin da suka isa gaban motar ne, ikon mallakar kai ya kwacewa Mahwish, yayinda kai tsaye yabi umarnin zuciyarshi, ba tare da jiran komi ba ya janyota da wani irin ƙarfi wanda a iya saninshi bai san yana da shi ba, yayinda ɗumin jikinta ya haɗu da nashi sai ya ji gamsashiyar nutsuwa irin wacce ya jima yana buƙata na baibaye shi. Lokacin da ta kwaci kanta gami da juya mashi baya tana sauke numfarfashi sai ya ji wani abu na matsewa tare da zuciyarshi. Ƙur ya ƙure bayanta da kallo, yana mamakin yanda rigar ta zauna ɗas a jikinta, duda bata kamata ba amma yana iya hango shape ɗin mazaunanta, haka kawai ya ji hannu sa na motsawa yana ƙoƙarin ɓallo mashi ruwa, sai de dawowar Ale Idi wanda ya amsa wayar Inna Sabuwa tun bayan tsayuwarsu wajen ya saka shi dawowa hayyacinsa. Cike da girmamawa irinta tsakanin talaka da mai kuɗi Ale Idi yaɗan rusuna yana neman afuwar ɓata mashi lokaci da yayi. A idon Mahwish kuwa babu komi sai tarin kunya data baibayeshi, kunya aba ce da bai cika jinta ba, hasalima zai iya ƙirga adadin sau nawa ya ji wata aba wai ita kunya a rayuwarsa, kuma koda zai ƙirga ɗin ba zata wuce cikin ƴan yatsun hannuwansa ba, amma ayau akuma yanzu sai ya ji wannan kunyar na baibayeshi, dan haka sai ya saka tausasan hannuwansa ya riƙi na Ale Idi tare da furta kalmar. "Papah, mu je ko." Ba tare da ya saki hannun Ale Idi ba ya bada umarnin ɓuɗe gidan gaba kusa da driver sai da ya tabbatar ya shiga da kyau sannan ya rufe ma shi motar da kanshi, sai kuma ya dafa kafaɗun Najma da ke tsaye ta juya baya har a lokacin, bai jira komi ba ya juyo da iya gabanshi sannan ya kama nata hannuwan cikin nashi ya soma janta sanu a hankali har zuwa jikin motar. Tirjiya da kafewa abune da suka zama ɗabi'arta amma a yau kuma ayanzu ta nemi kafiyar ta rasa, haka kawai ta ke jinshi kamar wani massarafinta. Koda ta zauna cikin motar kusa da shi a gidan baya, sai take jinta kamar a wa ta duniya ta daban, kuma kamar an sauya wani abu daga gareta, wanda bata taɓa tunani zai sauyu cikin sauƙi har haka ba, wato zuciyarta, zuciyarta data kasance mai taurin gaske, ta yanda take iya jin taurinta a cikin jikinta, amma a yanzu sai ta ji tayi laushi, laushi sosai irin wanda idan akace zata ti ita kanta zata ƙaryata hakan. Ale Idi na gidan gaba yana bawa Mama Saudah labarin wulaƙancin da ɗan sahu yai musu, yana kuma gama wayar sai suka hau fira da driver, do dama bakin drivern yayi tsami na rashin yin fira kullum zaman shiru, shima bahaushe ne amma irin samudawannan, dan haka sai suka ƙulle da Ale Idi suka ci gaba da fira. Mahwish ya so ya tsaida hannunshi daga ƙoƙarin kama nata hannun da take wasa da shi, amma ikon mallakar kanshi ya kwace ma shi, dan sosai zuciyarsa ta shiga ingizashi har sai da ya damƙi hannun nata. Ɗan buɗe baki tayi da sauri tare da watsa ma shi wani kallo da dara-daran idanuwanta, kafaɗu ya daga irin i dont care, sannan yakai hannun ya sumbata tare da ƙanƙameshi a ƙirjinshi. Sai kuma ya kalleta da idanuwansa wanda take iya hango raunin a cikinsu sannan ya ce cikin lallausar muryarsa. "Ina son hannunki yana mini taushi sosai ina so please za ki bani." Idan ta ce ta fahimci abin da yake nufi to tabbas ta shutala zuƙeƙiyar ƙarya me wasilla, dan gaba ɗaya komi nata ya tsaya ne cak. Ana cikin haka motocin suka ci burki a bakin ƙofar shiga cikin asibirin, kuma har lokacin bai saki hannuwanta ba, yana riƙe da su ahaka ya sauka tare da taimaka mata itama ta sauka. Kallon Ale Idi yayi tare da faɗin. "Papah zata iya tafiya ko in ɗauketa kawai." Baki washe Ale Idi ya ce. "Kai ɗannan wace ɗawainiya kuma ras ta ke iya tafita wallahi, Faɗima ce hwa, ai daga nan har birnin sin zata iya zuwa da ƙafafuwanta." Ware idanuwa da mamaki Mahwish yayi duda bai gama fahimtar maganganun Ale Idi ba amma sai ya ce. "Kai to tayaya take iya tafiya itada bata da lafiya sosai." Dariya Ale Idi ya kuma yi sanan ya ce. "Yo kai yaro indai gwagwarmaya ce ai babu wacce Faɗima taba saba da ita ba." "Papah, Mahwish, Mahwish sunana." Dariya Ale Idi yayi kawai dan yaso ya kira sunan amma sai ya kasa, gudun kar ya kwafsa sai ya share kawai. Najma bata ji ta gama shiga uku ba, sai da litita ya bata umarnin hawa gado, sannan ta buɗe raunikan. Ƙur ta ƙure Mahwish da ido tana jiran fitarsa amma sai taga ya sake gyara tsayuwa yana sakin murmushi. Ɗan taƙune fuska ta yi sannan tace da Doctor. "Kace mishi ya fita to." Da dariya Doctor ya faɗawa Mahwish wai tace ya fita amma sai ya ƙi fitar illa zama da yayi a kujerarda Ale Idi ke zaune yana bawa Doctor bayanai jikinnata. Ko da ta yaye rigar zuwa sama sai da ta rintse idanuwanta duda akwai wando 3 kwata a ciki, amma irin me kama jiki sosai ɗinan ne. Har doctor ya gama dube-dubensa da gwaje-gwaje Najma bata buɗe idanuwanta ba, har sai da aka gama komi, kuma kodata buɗe basu sauka a ko ina ba sai a kan innocent face ɗinsa, batasan yanda aka yi ba sai kawai ta samu kanta da gallara ma shi galelleyar harara gami da muguɗa baki gefe da gefe. Haƙuri ya bawa Ale Idi akan suɗan jirashi kaɗan zai amshi saƙo, saƙonda ya mance da saboda shi ya zo asibitin, sai da Doctor ɗin ya sake kiranshi akan koya fito ma shi da shi sai ya turo driver ya amsar ma shi, sai a lokacin ya tuna ya je ansa. Ko da ya je amsar a tsaitsaye suka gaisa a amsa tare da juyowa ya dawo, lokacin har an gama musu komi an sallamesu saboda babu wa ta damuwa. A wannan karon gidan gaba Najma ta kankane driver na buɗewa Ale Idi tau wuf ta shige ta zauna, yayinda Ale Idi ya zauna kusa da Mahwish yana jinjina irin kyawun halin yaro na rashin wulaƙanci da kuma karamcinsa. Tun Ale Idi na labari da Mahwish har Mawish ɗin ya gaji, suka koma yi da driver, sai da aka jima ahanya basu isa ba, ahakama dan motocin lafiyayyu ne shiyasa suka isa da wuri. Kallon farko da Mahwish yayiwa gidan da yake mallakin Ale Idi sai da wani abu ya tsarga a zuciyarsa, ko a labari ba taɓa jin irin akwai ire-iren waɗanan gidajen ba, kuɗaɗen da shi kanshi bai san adadinsu ba ya bawa Ale Idi tare da faɗin. "Papa ga wannan please a nemo me gyara a sauya ƙofarnan kar a shigar muku gida ayi ɓarna." Ganin Ale Idi ya soma yin gardama ya saka shi kamo babbar rigar jikinshi ya saka jakar, dan a jininsu ya ke yawan kyauta, kyautarma irinta manyan kuɗaɗe masu nauyin gaske. Basu rabu ba sai da ya amshi number Najwa a wajen Ale Idi dan ita tuni tai shigewarta gida abinta. DA DADDARE. Kwance ta ke a ɗakin Inna Tabawa, babu abin da take yi sai juyi, tunani fal zuciyarta, tunanin mutumin da ya tsaya ma ta cak a rai, kafin Inna ta yi barci har saukowa ta yi daga kan gado ta nufi wajen Innar tana faɗin. "Inna riƙe hannuna kiji, kina jin wani abu ko." kama hannun nata Inna ta yi amma bata ji komi ba. "Fatsima wani abu ne ya sami hannun na ki nidai bana jin komi." Maganar inna ta tabbatar ma ta da lallai ita kaɗai ta ke jin abin da ke a hannun na ta, ganin barci bazai ɗauketa ta sauƙi ya saka ta tashi ta ɗauki wayarta da ke cike da caji fal, ta kunna tare da lalibo indian film ta soma kallo, kira ne ya shigo wayar tata, mamako bayyane akan fuskarta ta ɗauki kiran bayan wancan ya yanke wani ya sake shigowa. Mahwish Da wa ta iriyar murna ya koma gida, tun akan matattakalar bene ya soma kiran iyayensa, yayin da suke a zaune su na shirin kiran wayar driver dan jin ko lafiya har yanzu basu dawo ba, sai suka cinkayo muryarsa cikin maɗaukakin farin ciki yana kiransu, mamaki damɓare akan fuskokinsu suka soma tambayarshi abin da ya faru. Da farko runguma ya kai musu su duka biyun sannan ya daidaita zamansa akan cinyoyinsu kamar wani ɗan ƙaramin yaro, a wannan karon dariya yake kyalkyalawa sannan ya ce. "My Loves kun san wani abu, wallahi na ganta, bafa a mafarki ba a zahiri har kama hannunta na yi na matse a cikin nawa, Mommy kin ji wani da nike ji a nan." Ya faɗi yana ɗaura hannunta a saman zuciyarsa da yanzu take bugawa normal, sannan ya ɗaura da faɗin. "Ina jina cikin farin ciki sosai my Papie, ashe tana nan?." Fuskokinsu a sake suka tambayeshi. Wai wacece wannan. Shiru ya gifta a tsakaninsu lokacin da ya basu amsa da Najma ce, nan take suka gane wacce yake nufi. A ƙasan ran Alhaji Muzaffar sai da ya ji wani abu ya motsa, wani abu dabai wuce rashin jin daɗin yanda wa ta yarinya ta sake shigowa rayuwar ɗansu a karo na biyu ba, kamar wancan karon, wannan ma talaka ce, talaka marasa tausayi bare tsoron Allah, talakawan mutane masu tsananin son kansu. (Acewarshi amma ba ni ba.) Alƙawari ya ɗaukarwa zuciyarshi akan ba zai bari ba, ba zai sake sakaci da rayuwar ɗanshi a karo na biyu ba, dole zai ɗauka tsatstsauran mataki, matakin rufe ƙofar du wani abu da zai sake kusanta ɗanshi da talakawan mutane, amma a zahiri sai ya ƙawata fuskarshi da murmushi gami da jerawa Mahwish tambayoyi a nutse. Kaf Mahwish ya basu labarin komi babu abin da ya rage a ciki hatta rungumar da yayiwa Najma, abinka da ɗan gayu sangartacce shalelen iyayensa, saima kallonsu da yayi tare da faɗin. "Wallahi har yanzu ina jin ɗumin tafin hannunta a nawa hannun." sai ya kai hannun saitin fuskarshi ya shafa, sai kuma ya janye tare da kaiwa akan fuskar Papie yana faɗin. "Ka ji ko Papie, har yanzu akwai." gyaɗa kai kawai Papie yayi dan shi bai ji komi ba illa sanyi da tafukan hannayen suka yi. Shafama Mommy yayi, ita kam a maimaikon Papie sai jinjina kai tayi cikin....... SAURA ƘIRIS MU GAMA FREE PAGE https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 10. Na sadaukarda wannan page gaba ɗaya ga fans ɗita wato LATEEFA MUHAMED HASSANA, wacce aka fi sani da Last born, wato a gaskiya ina matuƙar jin daɗin comment na ki sister, ita ce the first a du lokacin da nai update da take fara comment and like, gashi jiya har nick name ta bami RYAM STAR, ina matuƙar godiya sosai siste, Allah yabar tare ina yinki over three billion dollars💞🌹. Cikin biyewa shirmenshi ta ce. "Aiko dai son ga ɗumi nan gwanin daɗi." Dariya mai cike da nishaɗi ya yi sannan yakai ma ta sumbata a goshi cike da farin ciki. A daren ranar su na kwance akan makeken lafiyayen gadonsu, babu abin da ke tashi sai sassanyar muryar Mahwish yana basu labari, ba akan komi ya ke basu kabarin ba illa akan Najma, yarinyar da ta tafi ta kaso me tsoka na zuciyarshi ba tare shi da ita sun saniba, hannayenshi na cikin na mahaifanshi kamar kullum suna yin hakanne dan gudun kar su farka suga babu shi, saboda sun san akoda wane lokaci ciwonsa na iya tashi. Wani abu ne ya me kama da fata ya lulluɓe zuciyar Mommy, sai ta ke jin inama ace abin zai tabbata, badan komi ba sai dan farin cikin ɗanta, tillon ɗanta da zata iya sadaukar da komi nata akan farin cikinshi, sai de tasan hakan ba mai yuyuwa ba ne duk kuwa da irin son da Alhaji Mizaffar ke yiwa Mahwish ɗin, ta jima da sanin cewa babu wa ta dangantaka ta kusa ko ta nesa da ke shiga tsakaninshi da talakawa, tun bayan faruwar abubuwanda suka sauya komi, ciki harda rayuwar ɗansu da take a rikice da tarin ƙalubalen ciwo, ciwon da dashi ya zo duniya amma faruwar wani lamari ya ƙarawa wutar ciwon fetir, fatanta ɗaya Allah ya shiga lamarin ya nuna ƙarfin ikonsa akan zuciyar mijinta me tsananin tauri gami da riƙo, tana fatan samun sauyi a wannan rayuwar tasu, su koma kamar yanda suke a baya, walwala da dawwamar farin ciki ya sake lulluɓe su. Tambayar da Mahwish ya jefawa Papie ce ta dawo da ita duniyar zahiri. Tambayar inda aka aje ma shi wayoyinsa da sai su ɗauki tsayin lokaci bai yi amfani da su ba ya jefawa Papie. "Wayoyinka su na wajena my son a ɗauko ne." Da alamar ƙaguwa ya amsa ta, tare da sake matsewa Papie yana yi ma shi raɗa a kunne, wacce ta saka Alhaji Muzaffar murmusawa, har fararen haƙoranshi suka fito, sai ya kama ɗayan hannun bayan Mommcy ta tashi dan ɗauko ma sa wayoyinsa, a hankali ya shafa kan Mahwish ɗin tare da faɗin. "Farin cikinka shi ne nawa, kayi abin da kake so my lovely one and only son." Sumbata ya mannawa hannun Papie tare da maida ma shi amsar shima yana ƙaunarsa. Ko da Mommcy ta miƙo ma shi wayoyin saboda sangarta sai ya umarceta ta kunna, bayan ta kunna ya amsa bayan ya bata sumbata sannan ya bawa Alhaji Muzaffar, Jerarrun lambobin wayarta daya jima da hardacewa tun lokacin da ya amsa a wajen Ale Idi ya shiga karantawa Papie a nutse, shi kuma ya shiga saka number yana jin wani abu na ƙoƙarin taso ma shi, amma yana ƙoƙari wajen dannewa, ɗansa ne fa, ɗansa da yake fafutikar yawon ƙasashen duniya dan kawai ya nemo ma shi abin da zai saka shi farin ciki, dolene ya daure zuciyarsa na ɗan wani lokaci kafin ya aiwatar da abin da yake ganin shine daidai a lissafinsa. Kiran farko ba'a ɗauka ba sai da aka sake kira sannan aka ɗauka, kafin Mahwish ya ce wani abu sai da ya ja dogon numfashi sannan ya sakeshi tare da. "Assalamu alaiki warahamatullah." A yanda sallamar ta shi ta dira a ƙunnuwan Najma bata san sanda zuciyarta tai wani tsalle ba, saura kaɗan ta ɓalle allon ƙirjinta ta fito waje. Sai da ta saita muryarta sannan ta amsa da tata lallausar muryar. "Wa'alaika salam." A tare Mommcy da Papie suka kai dubansu ga Mahwish da ya wani lumshe ido yana sake ƙanƙame hannayensu a ƙirjinsa saboda tsabar yanda muryarta ta saita ma shi nutsuwa, tare da dirar ma shi da wani abu a cikin jinin jikinshi. (Oh Allah kana gani, dan tsabar shegantaka irinta ƴaƴan gata a tsakiyar gadon iyayensa zai yi waya, uhumm ma ji ma gani ai muje zuwa 🥺😁🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️) Bayan sallamar ya ɗauki lokaci ba tare da yace komi ba, ba kuma dan ya rasa abin faɗar ba, sai dan yanayin da ke sake lulluɓe shi a duk sanda sautin fitar numfashinta ya daki dodon kunnensa duda wayar na riƙe a hannun Papie amma du wani motsinta yana iya jiyo shi. Kamar yanda ya yi shiru baice komi ba haka itama ta zaɓi yin shirun tana sauraren bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta tare da motsinshi. "Ya jikin ki?." Ita ce tambayar da ta daki dodon kunnenta a bazata. A zuciyarta ta same maimaita tambayar, sai ta ɗora ta a wani mizani na daban, a zaronta yana iya ganin yanda jiki da zuciyarta ke tsalle a sanadiyar kusancinta da shi a wayar, sake danƙar zanin jikin gadon ta yi a cikin tafukan hannayenta da suka sake yin ɗumi, kafin a hankali bakinta ya furta. "Alhamdulillah." Sa'ilin da muryarta ta sake dira masa a kunne sai kawai ya zare hannayensa tare da dira ƙasa yai tsalle haɗi da juyi, gaba ɗaya farin ciki ya baibaye shi, ga wani ƙarfi da yake ji na mamaye mataciyar zuciyarsa, datse kiran Papie ya yi ganin abin da Mahwish ke yi kamar wani ƙaramin yaro, ba tare da ya shirya ba ƴar siririyar dariya ta kubce ma shi, sai kawai ya girgiza kai tare da tashi zaune. Sosai Mommcy ke ƙyaƙyatawa da ganin abin da Mahwish yayi, haka kawai sai ta ji ta samu sukuni, wannan tsoron gami da fargabar du sun kama gabansu. A rana ta farko tun bayan shuɗewar wasu sheƙaru da afkuwar lamari, Mahwish ya kwana cikin matsanancin farin ciki, farin cikin da tarin dukiyar Alhaji Muzaffar ya gagara siya ma shi tsayin shekaru. Da amsa kuwar amon sassanyar muryar Mahwish Najma tai barci, waɗanna gajerun kalaman na sa taƙaitattu sun saka nutsuwa a hargitsatsiyar zuciyarta ta samu nutsuwa fiye da zaton mai zato, a washe garin ranar sai da ta makara sallar asubahi, dama gidan ba kowa ke tashi sallar asuba ba, sai randa aka yi katari wani ya farka da wuri, daga ita sai Inna ke yin sallar asuba cikin jam'in akan lokacinta, amma har Ale Idi sai garin Allah ya waye ya ke fitowa ayi layin shiga kewaye tare da shi, saura ƴaƴan gidan kuwa wasu har takwas na safe su na sallah saboda shagala. Hayaniya da kacaniyar gidan ta dawo, dama abin da ya faru da Najma ne ya shafi walwalarsu ganin yanzu ta ji sauƙi sai aka koma gidan jiya, hayaniya da iface-iface tun a farkon layi ana jiyo su, ɓangaren Ale Idi an samu cigaba dan yanzu na rage abubuwa da dama, ba kamar yawan faɗa da zagi, duda yana ɗan taɓawa saboda abin ya bi jikinsa, yanzu kuma ciwon daya dameshi bai wuce na zaunawa yaita yabon wannan matashin me suna Mahwish ba tare da bawa ƴan gida labarinsa da irin kyawun halinsa, yayi shawara da Inna Tabawa akan tulin kuɗaɗen da Mahwish ya bashi a gyara ƙyauren gida, sai ce mashi ta yi ya dakata da batun ƙuɗaɗen nan gaba zasuyi amfani, andai ɗauki ɗauri biyu ciki waɗanda Alhaji Muzaffar ya bayar aka yi amfani da su wajennjinyar Najma amma daga nan ba'a sake taɓa kudaɗenba, to dama Ale Idi ido ga naira bare hasu yana gani tuluguji, ai sai hankalinshi ya sake kwanciya. Da lokacin kari ya yi haka kowa na gidan aka hallara kwai da kwarkwata, Najma ce ƙarshe fitowa saboda barcin da ya ɗauketa, sai da ta bi du wani babba ta gaisar sannan ta zauna fuskarta washe da annuri, nan aka shiga tambayarta yanayin jikinta, da annuri akan fuskarta ta soma bawa kowa amsa da jiki ya warware, haka aka zauna ana karyawa ana raha, yau dai harda Najma a cikin masu kwasar dariya, akwai kyakkyawar alaƙa me tsafta a cikin iyalan Ale Idi, matsalarsu ɗaya yawan faɗa da kuma ruwan ashariyar da suke yayyafawa kamar ɗiyan maguzawa, idan aka cire wannan ahaline masu haɗin kai sosai gami da ƙaunar junansu, su na ware lukuta dan su zauna da ɗiyanzu ayi fira ayi raha, abin gwanin burgewa. Sai wajajen ƙarfe goma kowa ya watse aka shiga sabgogin da aka saba, masu nema suka bazama, masu aikin gida suma aka saka haramar yi. ABUJA NIGERIA. ASOKORO Zaune ta ke akan sofa, yayin da hannayenta ke

Chapter 5 of 7