Share this page
4 / 7
ta musamman hasalima a tare da shi muke barci a gado ɗaya." Murmushi baturen likitan yayi sannan ya zare glass ɗin idonshi tare da duskantarsu da kyau sannan ya ce. "A halin yanzu kulawar da kuke bashi sam ba ita yake buƙataba, yana buƙatae farin ciki da tarairaya, sannan yana buƙatar abin da zai dinga bashi ƙwarin guiwa, saboda rauninsa yayi yawa sosai." Cikin lafiyayyen turanci Papie ya ce da doctor. "Du abin da ka lissafo babu wanda muka rageshi da shi, muna yi mashi duk abin da ya dace, sai de idan wasu sharuɗɗan daban zaka bamu." "Sorry freind, shin yanada mata ne ko budurwa?." Tambayar ta zo musu a bazata, sai da suka kalli junanau sannan suka haɗa baki wajen faɗin. "A'a babu." "Good, to yana buƙatar mace arayuwarshi, amma macen jaruma mai taurin zuciya, wacce zata iya tafiyar da rauninshi ta bashi gwarin gwuiwa haɗi da kulawa." Kalaman doctor sun haska wani abu a cikin kawunansu, su duka biyun hotonta ne ya gilma musu, amma sai suka maze suka ci gaba da sauraren doctor. BAYAN KWANA BIYU. Kwanan Najma biyu a asibiti aka sallameta bayan anyi mata du abin da ya dace, anbasu kayan dressing ingantatu akan du bayan sati ɗaya za'adinga wanke ciwon ana canza dressing. Godiya da sanya alkairi Ale Idi yayi, sanan suka kwashi inasu-inasu sukai gida. Har zuwa lokacin Najma bata nuna ta damu da ciwon da ke jikinta ba, hasalima tafi damuwa da damuwar Abdul da ke ƙara girma a zuciyarta, tana jin muddin zata haɗu da shi babu abin da zai hanata aiwatar da ƙudurinta, yanzu haka Allah-Allah ta ke ta warke ta koma aiki tasan acanne kawai zata dinga ganinshi. Tattara kuɗaɗen da Mommcy ta basu suka yi suka aje gefe, basu taɓa ko sisina saboda shawarar da Inna ta bayar cewa a aje sai Najma ta samu sauƙi. Yanzu du wannan hayaniyar ta ragu sosai, duda ba komi aka fasa ba, musamman habaice-habaice da ya riga yabi jikinsu, ana zama a zagaye Najama kowa na son yi mata fira dan ganin ta sake ta koma yanda ta ke a baya. Yanznma Lawisa ce ke basu labarin wani saurayi da ta taɓa yi ya biyota kan hanya, shine dan taƙi kulashi kawai ya kama zaginta, harda jifarta da munanan maganganu, aiko ta kanainaye shi da dinga ɗirma ihu ta tara mashi mutane tace rasin ɗa'a yayi mata, nan matasa suka lakaɗa ma shi shegen duka suka barshi a wajen. Buɗar bakin Najma sai cewa ta yi. "Idan nice ke sai na fara ɗauke fuskarshi da zafafan maruka da zasu makanta ganinshi, sannan in laƙa ma shi shairin da babu wanda ya isa ya fitar sa shi, sai na tabbatar da na rabashi da du wani farin ciki na rayuwarshi sanan in kyaleshi." Sai kowa yai tsuru ana kallon yanda ta ke magana a kausashe har tana taune busasun laɓanta. Daga kuma wannan maganar bata sake magana ba har tsayin kwanaki biyu. Mahwish. Sai da ya shafe kwanaki huɗu baya huyyacinsa, a rana ta biyar ne ya farko, daga yanda yaga kwarin idanuwan Mommcy sun zurma can ciki, ya tabbatar da ya jima a kwace dan sosai yake ganin ramar da ta yi, duda a kimtse ta ke ciki wani arnen leshi me tsada a ido zaka fahimci kwayun da ta yi, amma shi kallon farko yaga rashin nutsuwa a tattare da ita. A hankali ya ɗaga hannunsa sai tin inda ta ke tsaye bayan doctor kaɗan, da sauri ta matso kusa da shi tare da saka hannunshi cikin nata ta matse da ɗan ƙarfi hawaye na silalo daga gefen idanuwanta, sumbatar hannunshi ta yi tana jin yanda tsananin ƙaunarshi da tausayinshi ke zagaye jinin jikinta, da ace tana da dama, data cire ciwon daga jikinshi koda na kwana ɗaya ne, shima ya huta yayi sayuwa kamar kowa ba tare da ciwo ba. Sake sumbatar hannunshi ta yi, tana jin yanda hannun yai lagai a cikin nata, sosai ta ke tsananin tausayin Mahwish musamman yanzu da take ganin rauni na sake baibaye rayuwarsa ba kamar baya ba, yanzu sam bashi da wani karsashi, tana son ganin tilon ɗanta ya watayawa kamar kowanne ɗa. Bayan Doctor ya gama dube-dubensa ya ma fitar da magungun da za'a bashi a lokacin bayan ya saka wani abu a cikinsa, sai ya fice yana jinjina lamarin Mahwish ɗin, ba shi ba duka doctors da nurses da ke aiki a wannan asibitin sun san Mahwish da lalurarsa, muddin su na ƙasar ba'a rufe sati ɗaya ba tare da ankawoshi cikin halin ciwo ba, su kansu likitocin su na mamakin yanda har zuwa wannan lokacin ya ke a raye bayan irin baƙar wahalar da ya ke sha tun tasowarshi. (Sun manta da Allah ne me yin yanda ya so a kuma lokacin da ya so, babu me kashewa sai shi, kuma babu me rayawa sai shi, babu mai jah da al'amarinsa buwayi gagara misali Ubangijin hallitu baki ɗaya mai raha da jin ƙai.). Mommcy ce ta taimaka ma shi yayi brush sannan ya yaɗansha tea shima ɗan kaɗan, sai ayaba da yaci kwaya ɗaya shikenan haka ta haɗa ma shi maganin, to fa anan ake yinta, dan sam Mahwish bai ƙaunar magani a rayuwarsa, duda kuwa ya zama abokin rayuwarshi dan ƙa'ida ne kullum sai ya sha su tun daga safe har dare, kullum sai anyi dambarwa da shi akan shan magani kamar wani ƙaramin yaro. Yanzunma kauda kai gefe yayi tare da marairaicewa ya wani sake narke noƙaƙƙiyar muryarsa irinta marasa lafiya sannan ya ce. "Please Mommy bana so." "Sorry Love ni kuma ina so please." Ta faɗa itama a marairaice kamar yanda ya yi. sake shagwaɓewa ya yi sannan ya ce. "Ni fa Mommy na ɓata da ke, yanzu sa Papie nike shiri dan haka ba kece za ki bani ba." Yan da yai maganar ya sakata mirmusawa ba shiri sanna ta ce cikin mirmushi. "Haba Love, sarai nasan halinka fa, shima Papie ɗin idan ya zo zaka ce kun ɓata ne, dan haka tun da mun ɓata maza amshi ka shanye ko in zane ka." Ta yi maganae tana ɗaga hannunta ɗaya sama alamar zata kai suka, shi dariyama ta bashi, idan akwai abin yasan ba zata iya yi ba sam a rayuwarta, bai wuce dukanshi ba, matar da ko tsawa bata iya yi mishi bare kuma duka, ko kallon banza taga ana yi mishi sai inda power ta ta tsaya, saje taƙune fuska yayi tare da ɗora hannu ɗaya bisa kai kamar zai rusa ihu sai kuma ya ce. "Shikenan tun da kin daina yi na, bani insha amma daga wannan ba zan sake shan wani ba." Yanzu kam sosai tai dariya ganin yanda yayi zuba mashi kwayoyin ta yi a hannu tare da bashi ruwa, har lokaci da alamun dariya akan fuskarta. Dariyar da ta sanyaya ran Mahwish har ya shanye magungunan ba tare da yaji antakurashi ba kamar kullum, kamar yanda ta ke a yanzu haka ya ke da burin ganin fara'arta a kullum, murmushinta na matuƙar sakashi farin ciki. Duda sam baya jin daɗin jikinshi hakanan yai ta mazewa suka ci gaba da dira, ko Doctor da ya zo da takardar sallamarshi sosai yayi mamaki da ganin yanda Mahwish ɗin ya ware kamar ba shi, fatan samun sauƙi yayi mishi sannan ya sallamesu. Sai da suka jira Alhaji Muzaffar ya zo sannan suka ɗunguma suka yi gida. Akan hanya su na tafene kawai amma sam hankalinshi baya kansu, yana kan abin da tun da ya buɗe ido yake so ya ji wani bayani amma ya ji shiru, magana ce ta kubce daga bakinsa ba tare daya shirya ba. "Wai Mommy ina wannan yarinyar Najwa ya jikinta ta farka kuwa." Ɗif su dukansu suka yi tare da zubawa Mahwish ido, a daidai lokacinne motocin suka tsaya a kusa da sashensu, basu ce da shi komi ba illa sunkutarshi da Papie ya yi suka fice zuwa sashensu. A saman luntsumemiyar sofa ya zaunar da shi, yayinda Mommcy ta danna oder da ke shedawa ma'aikatan kitchen ana nemansu da gaugawa, ma'aikata ne su biyu mata kowace hannuwanta riƙe da ƙaron tire, cike da girmamawa suka aje tare da jiran umarni, da hannu Mommcy ta sallame su, bayan ta tsiyayi ruwan tattaciyar kwakwa me sanyin ta miƙawa Papie, murmushi ya sakar ma ta sannan ya nufi bakin Mahwish da cup ɗin, shima tattausan marayan murmushi ya sakar musu su duka biyun sannan ya kirɓa a sanyaye yana jin yanda sanyin ya ratsa du wa ta gaɓa da ke aiki a jikinsa.....✍🏻 Taufa, ina team Mahwish ina Team Najma, shin mi kuke tunani game da waɗanan mutanen biyu masu mabanbanyan zukata.❓❓❓❓ YAUDAI IDAN BANGA COMMENT DAYAWA BA GOBE BABU UPDATE DAMA ZAN SHIGA BUSY. NI CE TAURARUWARKU MARYAM SYAR ⭐⭐ https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 8 Lokacin da wannan sanyin ke ratsa shi bai san buɗi baki ya ce da Papie. "Ina Najwa, ta ji sauƙi." ba sai da ya sake ganin sun kalli juna sai kuma suka haɗa baki, yayinda Mommcy ke faɗin. "Ai taji sauƙi an sallameta." Shi kuma Papie sai ya ce "Allah ya yi mata rasuwa." Komi na Mahwish ya tsaya ne cak da aiki, jin maganganun da kowannensu ya faɗa, amma a yau kuma ayanzu karo na farko a rayiwasa daya iya mallakar kanshi, bai ce komi ba kamar yanda bai furta komi ba sai cigaba da kurɓan sassanjan juice ɗinshi da ya yi daga wajen Papie. A ranar ma haka suka sakashi tsakiyarsu, ko wanenase na lelenshi har yayi barci, sannan suma hankulansu suka kwanta, domin sosai yau ya basu mamaki, akaro na farko daya nemi son jin wani abu suka hanashi, kuma ya maze ba tare da komi ya faru ba, sai wani fata gami da yaƙini ya lulluɓesu, sai suka ji inama ace zai ɗaure a haka, ya zama kamar kowane mutum, sai de abin da basu saniba shine, ba'a dawwama cikin ƙunci, kamar yanda ko wane lamari ke da mafari haka ya ke da ƙarshe, abu me muhimmanci shine a kyautata zato. A washe gari Mahwish da kanshi ya tashe su a sallah, yana jin zafin kasancewarshi a tsakanin farin cikin su biyun, yana fata da addu'ar Allah ya kawo sauyi a cikin rayuwarsa, sauyin da zai sake sauya lamurra su daidaita, sosai ya ke tausayawa bayin Allahn iyayensa da suka sadaukar da komi nasu a kanashi, abu muhimmima lokacin su da ya shiga yai bake-bake. Cikin Ikon Allah ba'a ɗauki tsayin lokaci ba jikin Najma ya soma kyau, dan har an warware ɗinkunan da aka yi ma ta, sai dressing da ake yiwa wajajen raunika, a ranar da idon Najma ya sauka akan wawaka-wawakan ciwukan da aka ji ma ya, sosai ta yi mamakin yanda ta rayu, musamman yankan wuƙa hae waje biyu da ta gani a cikinta, hakan ya saka ta kasa shiru ta ce "Mama ya aka yi ban mutu ba, kinga ciwon kuwa." Yanayin yanda ta yi maganar ya bawa Innoninta dariya, domin yarintarta ta fito fili, shafa kanya Inna Laraba ta yi sannan ta ce. "Oh ke Fatsima in banda abin ki cuta ai ba mutuwa ba, kuma ciwon ba babba bane sosai a nan ne kike ganin shi babba, amma sam bai huda ta ciki ba." Gwauron numfashi Najma ta sauke sannan ta ƙara cewa. "Kenan yankewa na yi, ko garin ya oho mani, ashe bai shiga ciki ba shiyasa babu zafi." Daga kuma wannan maganar bata sake cewa komi ba sai a washe gari data fama ciwon kafaɗarta, kallon Mama Saudah wacce ke goge ma ta jinin ta yi sannan ta ce. "Mama miyasa ciwon babu zafi amma anan ina jin zafi sosai." Ta yi maganar ta re da nuna saitin zuciyarta. murmushin yaƙe Mama Saudah ta yi sannan ta ce. "Ai dama anan za ki ji zafin tun da kafaɗa ce kuma ta hannun dama." Shima bata sake ceqa komi ba sai lumshe idanuwanta da suke har lokacin a launin jah ta yi, sai kuma a washe gari da Inna Tabawa ke ma ta fifita a saitin kunun gyaɗar da aka dama ma ta. "Inna kinsan mi?." Ta yi maganar tana watsawa Inna idanuwanta. "A'a Faɗima sai jin faɗa. "Ina jin zuciyata na tururi kamar yanda wannan kunnun ya ke, mi zan sha ta daina yi min zafin, ina jin har hayaƙi na futowa daga bakina." Duda gaban Inna Tabawa sai da ya faɗi, kuma tsoro ya lulluɓe ta amma sai ta aro bargon jarumtaka ta yafa, sannan ta ce tana dariya. "Yo Faɗima ai kece baki shan ruwa me saiyi, da ace kina shan ruwan sanyi kuma kina zama cikinsu Lawisa kuna zance da yanzu ta daina hayaƙi. "Inna miyasa kuke ɓata min suna wai, ni nafi so ku dinga kirana da Najma, ko kuma kuce Fateema amma wai sai inji kuna cemin Fatsima ko Faɗima." Dariya Inna ta yi sannan ta ce. "Yo in banda abinki ta ina bakunanmu zasu iya furta wannan suna irina ƴan gayu, wannan ai sai su Saudah su da suka sha iskar ajin boko." Ɗan yatsine fuska Najma ta yi, kamar ba zata sake cewa komi ba sai kuma zuwa can ta ce. "Wai Inna wannan ɗan gayun wanene shi, ina jin muryarshi me daɗi na cemin kar in rufe idona, kuma bani ganinshi.?" "Wani bawan Allah ne da yaganki sadda kika ji ciwo shine ya taimakeki ya kaiki asibiti." Inna ta bata amsa tana fatan firar ta tsaya iya nan. A ranar sosai Najma ta sake da ƴan gidansu sukaɗanyi fira, dan firar da re da ita aka yi kowa ka kalla yana cikin farin ciki, Ale Idi ma daya dawo daga aiki ya taradda su ahaka sai shima ya zauna, nan firar ta dawo tashi inda ya dinga basu labarai akan ƙuruciyarsa da irin wahalhalun da ya sha, a ranar anyi nishaɗi sosai dan basu suka tashi ba sai da dare ya raba sannan. Haka rayuwa taci gaba da garawa har aka kwashe sati uku Najwa na jinya. Alhamdulillahi jiki yayi kyau sosai, wajaje ɗaiɗaya ne basu idasa warkewa ba daga jikinta, sai dai kuma akullum zuciyarta na sake tafarfasa ne akan Abdul, idan akwai wanda ta ke da burin gani bai wuce shi ba, bawai tana son ganinsa dan wani abu ba, tana son ganinsa ne saboda aiwatar da ƙudurinda ya hana zuciyarta zaman lafiya. 𝘼𝙗𝙙𝙪𝙡 Kwana biyu ya kwashe yana zuga company amma bai samun ganin Najma, bayan ƙudurinshi a kanta akwai zazzafar soyayyarta da ke hanashi sukuni, kasancewar company da ta ke aiki yana kusa ne da nasu company shiyasa sam baya jin wahala wajen bibiyarta musamman a lokacin tashi. Cikin sa'a yau ya hangi Khadija ƙawarta na tahowa ita kaɗai, da sauri ya kalli dafafun tantabarun da ya shafe kwanaki yana sakawa aka dafa ma shi yana yawo da su, har zai ɗauka ya zuba maganin sai kuma ya fasa yai saurin fitowa ya tunkarota. Sosai ta tsorata lokacin da yasha gabanta, ganin shine yasa ta haɗiyi kakkauran yawu sannan ta ce. "Yah Abdul barka da marice." "Barkanki dai Khady fatan kina ƙalau?." Iya yau kaɗai da magana ta haɗasu direct babu wani shamaki, yau gata ga shi babu Najma wacce ke shiga tsakiya tai bake-bake. A maimakon ta amsa shi kai tsaye sai ta lankwasa da kai gefe ɗaya tare da lankwashe murya sannan ta ce ciki da iyayi. "Yah Abdul ya aiki, wai baka jin rana ne kullum sai ka fito wajenan, ko dan sabida lafiyarka ai ya dace ka rage zama cikin rana." Shafa somar kanshi yayi fuskarshi ɗauke da murmushi ya ce. "Wallahi ko Khady gashi kuma ita wacce nike yi dominta sam bata damu da ni ba." Taƙune fuska ta yi cike da gulma ta ce. "Ummm ai kanama ƙoƙari, ni kaina da nike ƙawarta rufe ido ta ke ta zabgagamin rashin mutumci, amma ban damu ba saboda nasan wata rana zata gane amfanina dole, kawai de nafi jin zafin yanda ta ke wulaƙanta ne wallahi." Fuskarshi ce ta sauya jin abin da Khadija ta faɗa, sai yaji ranshi yaɗan sosu amma sai ya maze. "Kinga ko dama yanzu zan tambayeki ita, wai tana ina ne kwana biyu ina kewarta sosai wallahi." Riƙe haɓa Khadija ta yi sannan ta ce. "Ai yanzu Najma ta sauya hali ace har a saka ranar aurenta amma shine ba zata nemeni ba, nima sai jin labari nayi a wajen wani yayanta da muke maƙotaka da shi." Ta lailayo ƙarya ta maka ma shi, tana fana yin nasara akanshi ko da so ɗaya ne a rayuwarta. Wa ta iriyar mummunar dokawa gabanshi yayi, a rikice ya soma tambayarta inane gidansu, yana ji yayi kuskure da bai taɓa bin bayanta ba yaga gidansu. "Lallai Abdul haryanzu baka san wacece Najma ba, itafa da kake gani bata yarda da kowa ba dan wallahi bamu taɓa hirar koda sunan unguwarsu da ita ba, muna dai aiki tare amma ban san inda ta ke ba." a wannan karon ta faɗi gaskiya dan sam Najma bata yarda a shiga rayuwarta, bata damu da kowa ba a wajen aikinta kamar yanda bata so a shiga rayuwarta. "Yanzu ya za'ayi ki haɗa ni da wanda zata aura ɗin ina da wani muhimmin saƙo da nike son isarwa gareta." Wannan karon aɗan hasale Khadija ta ce. "Haba Abdul tayaya kana namiji zai yarda ka bashi saƙo ya kai mata, ai gara ni ka bani sai insan dabarar da zanyi imbashi ya kai ma ta." Ɗan jimmm yayi da farko, amma ganin bai da wa ta mafita ya saka shi amincewa da zancen Khadija, da ace yasan mi zai je ya zo da koda wasa bazai bari koda ganinsa Khadija tayi ba, da ace yasan abin da ke tunkaro shi, da tun farko ya shafawa kanshi salama daya fahimci Najma bata yinshi, amma me rabon shan duka... Koda suka isa gaban motarshi tsaida ta yayi awaje, ya shiga tare da ɗaukar maganin ya barbaɗa yanda ba za'a gane ba sanna ya rufe ya gyara komi tare da buɗewa Khadija front sit, kai tsaye ta shiga ta zauna tana fatan cikar muradinta na mamaye zuciyar Abdul, wanda a kallon farko ya yi nasarar sace zuciyarta, kamar yanda Najma ta sace tashi zuciyar. Bardir ɗin kuɗi ya ɗauko kusan guda biyar ya miƙa ma ta, da rawar jiki ta amshi kuɗaɗe, sannan yai mata bayanin saƙon da ya ke son bata ta kaiwa Najma harna tsayin sati ɗaya, sannan bayan ta bata ta tabbatar da tayi amfani da shi. Da ace Abdul yasan mi zai je ya zo, da bai yarda da Khadija ba har ya aiketa wajen Najma, ba tare da sanin shi ba ya jefa rayuwarshi cikin wani hali, wani hali wanda bai taɓa kawoshi cikin lissafin rayuwarshi ba, ya rusa gobenshi da hannunshi ta sanadiyar biyewa son zuciya, dama masu iya magana sukan ce. "Shi shairi ɗan aike ne, ko ya tafi sai ya dawo, sannan kuma idan zaka gina ramin mugunta ginashi ɗan kaɗan, dan wata rana kai ne wanda zaka zurma a ciki." Haka Abdul ya rabu da Khadija yana maimaita ma ta kalmar ta kula da saƙon kuma ta bayar da shi cikin lokaci, da ya sani da bai nuna ma ta muhimmancin saƙon ba, domin kuwa mummunan tunani ne ya ɗarsu a ranta, tinanin da zai taka rawa wajen ruguje rayuwar Abdul. Mahwish. Satinshi biyu baya ƙasar inda suka tafi hutu shi da sanyin idanuyarsa kuma kwarin guiwarsa wato mahaifansa, cikin ikon Allah jikinshi bai wani tsananta ba, duda du bayan kwana biyu sai yaga likita. Sanye ya ke cikin baƙar jacket me hula, hular ta rufe har kansa kasancewarta me ɗan girma babu laidi, hannunsa riƙe da gorar ruwan zamzam ya ke taka ƙafafuwan matattakalar benen yana saukowa, yayinda saurarin mahaifansa ke mayar da ƙafafuwansu a du inda ya ɗauke ta shi, hannu ya saka tare da hanye hukar rigar nan take innocent face ɗinshi ta bayyana, ya ƙara haske sosai fiye da baya, gashi yaɗan yi kumari duda ba wa ta ƙiba ce da shi ba sai tsayi ma sha Allah du ciwo ya gama tsotse shi, dandazon ƴan jarida da masu manyan muƙamai ne suka zo taryarsu cikin nuna kulawa ta musamman. Ba su suka bar airpot ɗin ba sai da suka kwashe awa ɗaya da rabi su na gaisawa da mutanen da suka zo taryarsu, fuskar Mahwish ɗauke da sassanyan murmushi ya ke duban tarin jama'ar da suka zo domin su, acan ƙasan raunananniyar zuciyarsa ya ke fata da burin ganinta, wannan fuskar data samu wani matsuguni a can wani lungu na zuciyarsa ta lafe tai luf, daidai da secon ɗaya bai daina jin motsin ta ba a sashen zuciyarshi, haka kawai ya ke jin kwarin guiwa ta musamman na mamaye shi, musamman idan hotin jaruman idanuwanta waɗanda babu rauni ko tsoro a cikinsu ya gifta a cikin kanshi, haka kawai ya ke jin tana da muhimmanci a rayuwarsa, yana ji a cikin jini da ke gudana a jikinshi cewar ita za ta zama babban jigo a gareshi, sai de tayaya? ɗayan ɓarin daya jima da mutuwa a zuciyarshi ya ke jefo ma shi wannan tambayar adu sanda tunaninta ya addabeshi, yanzu haka da lafiyayyun zuƙa-zuƙan motocinsu ke ketawa a saman shimfiɗaɗɗiyar kwalta, hankalinshi na waje ta glashin motar yana buri da fatan sake ganinta koda so ɗaya ne, ya ƙudurta a zuciyarshi tabbas idan ya sake ganinta zai je ya yi ma ta godiya, godiya ta musamman akan wani abu data bashi wanda akaf yawon ƙasashen da suke yi aka gaza samo ma shi, wato ƙwarin guiwa, hakan ya ji zuciyarshi ta dage wajen addu'ar ganinta a yau a kuma yanzu babu jimawa. Ale Idi ne tsaye da hula a hannunshi yana sakawa, yayinda Mama Saudah ke taimakawa Najma wajen saka sabuwar rigar abaya marar nauyi wacce Ale Idi ya ɗauki Lawisa takanas suka je kasuwa aka sayo ma ta su dayawa. Sai da aka saka reza aka farka saitin kafaɗarta inda ke da ciwo, yau ne lokacin da likitan asibitin LAGOON HOSPITAL VICTORIA ISLAND ya ɗiba musu dan sake duba ta tare da sake gwaje-gwaje, idan komi yayi normal shikenan basai ta sake zuwa ba idan kuma akwai wa ta matsalar zasu sake treting ɗinta. Fatan alkairi ƴan gidan suka bisu da shi, domin kuwa Mama Saudah da Inna sun so zuwa sai de ba hali saboda asibitin ta manyan masu kuɗi ce hasalima sai da id card ake shiga, Ale Idi da Najma kawai ke da shi. Allah sarki rayuwa, yau Ale Idi ne kw tafiya a sanyaye yana tarairayar Najma da daɗaɗan kalamai, mutumin da a satikan bayan ya ke jifarta da ɗima-ɗiman ashariya, bama ita kaɗai ba, kusan yanzu ya daina zagin kowane ɗa a gidan abubuwa da dama ya rage sosai sai wanda ba'a rasa ba, run faruwar wannan lamarin ya koma wani slite da shi, ita kanta Najma da bawata walwala gare ta ba tana yawan tambayarshi wai miyasa yanzu ya koma wani iri ko baida lafiya, a kwai ranar da yayi ɓaran-ɓarama yace da ita. "Faɗima ni da nakusa ganin mutuwar ƴa ta a gaban idanuwa na ai dole jikina yayi sanyi" da manaki ta tambayeshi wacece ta kusa mutuwa sai Lawal da ke zaune shi da ƙaninshi Ibrahin suna ƙirgan kuɗin cinikin shago yayi karaf ya ce. "Zainabubu ce me mashin yakusa bi takanta ranan wajen masifa shine fa jikin Baba yai la'asar gaya mutuwa ƙwaraƙwatan itama ƴar jakar uban bakiga ta yi la'asar ta kom salaha ba." Ya yi maganar yana kallon Bubu data marairace kamar da gaske. Kusan sau biyar ana tsayar da ɗan sahun daya ɗauki

Chapter 4 of 7