Share this page
3 / 7
wacce ita kaɗai ce ta fita zakka a cikin tarin ƴaƴan gida, bata faɗa haka kuma bata sa'insa da kowa, idan su na hayaniyarsu ko dambe takan kallesu ne kawai ta wuce wani lokacin kuma ta girgiza kai tace Allah ya kyauta, idan sun dame ta kenan. Sai yanzu da Inna ta basu wannan taƙaitaccen labarin suka soma hasko yanda sam bata bada damar da ranta zai ɓaci, ko mi za'ayi ma ta kuwa, kodai ta wuce tabar wajen ko kuma ta share mutum har yayi ya gama. Sharce zufar da ta ke to ma shi Ale Idi yayi, yayin da hankalinshi yai ƙololuwa wajen tashi, nan take labarin irin wahalhalun da kakaninsa masu irin lalurar suka sha ya haska a cikin kanshi, cikin rasa abin yi ya kalli Inna sannan ya ce. "To Inna yanzu minene mafita?." "Mafita ɗaya ce Idirisa dole sai de abin yanda na ce, ai kai nasan baka mance kakaninka da irin faman da suka yi ba, abin da zai fi shine kawai a dage da addu'a kafin a soma laluben mafita." Jikin kowa a sanyaye haka suka fice daga ɗakin aka bar Najma ita da Ale Idi yana rarrashinta. Mama Saudah ce ta ɗauko ledar abincin da Najma ta kawo ta aje gaban Inna Sabuwa tana sharce hawaye sannan ta zauna tare da dafe kai. Abincin da ake rububi kanshi idan aka kawo sai gashi yau babu wanda abincin ya isa koda kallo, hatta ƴan matana gidan jikunansu a sanyaye ya ke haka sukaita rarraba ido jikunansu a sanyaye........✍🏻 MARYAM STAR⭐⭐ https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t 💗💗💗💗💗💗 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 5 Har aka yi isha'i su na a wannan yanayin, a ranar ko firar dare basuyi ba haka kowa ya je ya kwanta tun da wuri. A safiyar ranar litinin, motoci ne su biyu akan haryar da sam bata da kyau sai ramuka da kwazazzabai, gudu kawai suke sharara kowa na ƙoƙari wajen ganin ya wuce ɗan uwashi, abin da ya basu mamaki bai wuce yanda suke sake dosar hanga ɗaya ba, a daidai wajen wa ta ƴar ƙaramar bukka da ke can cikin surniƙin daji suka ci birki, ko wannensu ya fito da sassarfa tare da nufar bukar gadan-gadan, kafaɗunsu na gogar na juna suka shiga bayan sun karanto wasu kalmomin surkulle. Ƙaton baƙi ƙirin ɗin mutum ne me mummunar hallita zaune akan iska idanuwansa a waje, wa ta murya ce marar daɗin amo ta karaɗe wajen tare da faɗin. "Mi ke tafe da ku." Waige-waige suka soma yi amma basuga kowa ba, kuma wannan mutumin na gabansu babu alamun shine yayi maganar dan yana a yanda suka iske shi. "Hhhhhhhhh ba zaka tu taɓa ganin me magana ba ƴan samari, ku faɗi buƙatunku kai tsaye kunzo inda za'a biya muku su." Abdul ne ya soma magana. "Sunanta Najma zuciyarta nike so a mallake min sai yanda na yi da ita, ina so ta kamu da matsananciyar soyayyata wacce zata zautar da ita." Shima Muhasin a daburce ya furta. "Mahwishi, so nike a idasa bugar da bugaggiyar zuciyarsa, ina so yaci gaba da jinya har tsayin rayuwarshi, sannan a janye hankalin iyayenshi daga gare shi, ina so inzama ɗan gaban goshi a MUZAFFAR FAMILY, ina so in zama ɗaya daga cikin masu faɗa a ji." Shima ya karanto buƙatarshi kamar yanda Abdul ya karanto. A maimakon waccan muryar yanzu sai suka ji tashin muryoyin mutane biyu mace da namiji su na faɗi. "Buƙatarku zata biya, kusa a ranku anyi wannan angama, muddin kuka cika sharriɗai babu makawa komi zai faru cikin ƴan kwanaki, amma muddin aka saɓa sharaɗi koda guda ɗaya ne, la shakka aiki zai baci sanan a kwai bi baya." Kallon junansu suka yi duda basu san juna ba sai suka saki murmushi a tare sannan suka ce. "Mun amince." Rufewar bakinsu ke da wuya suka hangi wannan mutumin ya motsa gami da buɗe idanuwansa, ruɗewa suka yi gaba ɗayansu, ganin wuta na fita daga idanuwanshi, bakinshi kuma ya buɗe lokaci ɗaya wasu ƙulluka suka bayanna akan dogon harshensa me rassa biyu, ko wane reshe ya aiko da maganin wajen mutum ɗaya. "Ku ɗauki wannan maganin ku tabbatar kun bawa waɗanda kuke son halakawa da mallaka a cikin naman fararen tantabaru, ku basu suci har na tsawon kwanaki bakwai, sannan karku kuskura ku sake haɗuwa da junanku, idan hakan ta faru komi zai lalace, lalacewar komi kuma na nufin ladama marar amfani, ku tashi ku je, idan buƙata ta biya zamu zo da kanmu mu amshi ladar aiki. Jikunansu na rawa suka ɗauki magungunan sannan suka fice, a gaban motocinsu suka tsaya su na kallon junansu, sai kuma ko wanensu ya juya ya shiga mota suka sake yin tsere a hanya. Sun tafi ne kowa da ƙudurin aiwatar da aikinsa, ba tare da sun san wa ta ƙaddarar ta riga da ta gifta a tsakanina ba, wa ta ƙaddara da basu yi zaton zuwanta a yanzu ba da wataƙila basu je wajen boka mushiriki ba. Najma. Yau tun farar safiya Ale Idi ya rarrasheta akan ta samu ta ci wani abu, amma ko bakinta bata iya buɗewa bare ta amsa shi, sai idanuwanta da suka kaɗa sukai jazur babu wannan haske me burgewa a cikinsu, da taimakon Mama Saudah aka canza ma ta kaya, suka nufi asibiti, da fatan alkairi duka mutanen gidan suka bi su, wasunsu na sharce wahaye, da suka isa daidai bakin hanya inda zasu tari abin hawa, sai Najma ta kwace hannunta daga na Ale Idi ta soma takawa cikin sassarfa, Ale Idi har ya tsaida abin hawa si yaga ta tafi, ba shiri ya sallami me abin hawan ya biyo bayanta yana tambayarta, ba tare da yasan suna taka wani tsani bane daga shi har iya wanda ƙaddara ta zartar a kansu a wanan ranar, jerawa yayi shi da ita su na tafiya akan ƴafafuwansu har suka yi nisa sosai suka bar unguwar, ta layin da ke shaƙe da ma'aikatu suka gibta, a daidai nan ne suka cimma ƙaddararsu. Najma na bayan Ale Idi suka zo giftawa ta gaban wani Company sai suka iske anata tafka rigima, mutane sai guduwa suke yi, yayin da a daidai lokacinne Najma ta ɓacewa Ale Idi wanda hankalinshi yai masifar ta shi, juye-juye ya ke yana kwalla kiran sunanta cikin dandazon mutanen da ke gudu, amma ba tare da saninsa ba ya ke komawa baya, yayin da ita kuma ta yu gaba bisa ga umarnin zuciyarta. Mahwish Bayan antafka mahawara shi da Mommcy da ya ce mata zai fita ya zaga gari ya ɗansha iska, tuburewa ta yi akan babu inda zai je, amma ya nace ma ta, daga ƙarshe dai ya samu ta amince amma da sharaɗin tare zasu fita, cikin ƴan mintuna ta sa aka shiya musu motoci na alfarma tare da securitys kusan motoci goma, cike da farin ciki suka fito hannunshi cikin nata su na tafiya su na ɗan tafa hira, haka ma'aikata sukaita zubewa miƙa gaisuwa gami da addu'ar samun kafiya ga Mahwish. Lokacin da lafiyayyun motocinsu suka fice daga gidan suka haura kan kwalta, wani abu ne ya shiga warwarewa daga can cikin zuciyar mahwish, yana ji wani abu me muhimmanci na gab da kusantarshi, sai ya ji ya ƙagu su ƙarasa wajen da abin ya ke, haka yai ta danna alamar sanarwa ta cikin motae yana bada oder a canza hanya, a daidai lokacin da suka kusanto wajen, ji yayi raunanniyar zuciyarahi ta ƙara sauri wajen dokawa, alamar sanarwar akwai matsala nan gaba kaɗan securitys suka dannan amma sai ya basu alamar ci gaba da tafiya ba tare da shi kanshi yasan abin da yake yi ba, daidai lokacin da ya zuge glashin tare da danna alamar tsayawa idonshi ya tsallake tarin mutanen da ke guje-guje a wajen ya sauka akanta ita kaɗai, ita kaɗai ɗin da tarin mamakin da aljabin ganin yanda hankalinta ke a kwance ya kusa sumar da shi, sai de komi ya tsaya ne a sa'ikinta ya hangi wa ta kakkaifar wuƙa daga gani sabuwa ce dal tai masauki a gefen cikinta, ƙyas idonshi ya ɗauki hoton yanda ta rintse ido tare da dakatawa da tafiyar, da dannan alamar umarnin fitowar Securitys da zagayeta da mutanen wajen sukai da hakalin Mommcy daya kai wajen da taga ɗanta ya maida hankalinshi bayan taga tsananin ruɗu gami da tashin hankali akan fuskarshi, ƙara itama ta saki ganin yanda mazaje biyu suka soki matashiyar budurwa a wajaje mabanbanta da wuƙaƙen hannunsu, atare ida, Mahwish da gurds suka isa wajen a gigice. Bayan guadrs sun yi nasarar watse matasan ta hanyar harbin iska da bindugunsu, da sauri Mahwish ya isa wajen, saƙala hannunta Najma wacce jiri ke ɗiba ta yi a na wani matashi wanda ta kira da balarabe tayi, sannan gwuiwoyinta suka sake, ta ɗurƙushe a wajen, a lokacin ba ita ke da iko da gangar jikinta ba, zuciyarta ce ke riƙe da ita, shine dalilin da ya hanata kaiwa ƙas tuntuni. Jajayen idanuwanta ta saka a cikin nashi a saman ballanta da ke makyarkyata ta furta. "Abbana, ka nemo min shi tare muke." Yasan shi me rauni ne, zuciyarshi bata da ƙarfi sam amma sai yaji wani ƙarfi nan take na tsaga ƙirjinshi yana dira akan zuciyarshi, da hannuwansa ya ɗauke ta cak jininta malala a ƙasa, yana ƙoƙarin juyawa da sauri Ale Idi ya riƙe kafaɗushi idanuwansa na soma zubar da kwalla ya furta kalmar. "Ta mutu ko, ƴa ta ce ita." A lokaci ɗaya bayan faruwar abubuwan da suka faru a baya, Mommcy ta ji wani abu me nauyi na kwaranyewa daga zuciyarta yana bin isa, tsanar talaka shine wannan abu, kallon yanayin rauni da sadaƙarwa a karon farko daga fuskar Ale Idi ya sanyata jin ta yi nasara tayi nasarar ganin rauni akan fuskar talakawan mutane masu tsananin son kansu, masu ganin sun fu kowa wayo. Bata san ya akai ba sai cintar muryarta ta yi na faɗin. "A'ah bata mutu ba she is still a life, muje hospital." Ta faɗa a tausashe tana kallo yanda hawaye ke gudu akan fuskar Ale Idi. Idan kunyi comment yanda ya dace zan sa muku page 6 zuwa dare idan kuma naga sai a hankali zan barku da halinku🤓😠 NI CE TAKU MARYAM STAR ⭐⭐ https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?mode=gi_t https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 Chapter 5&6 Ɗazu nayi mistake zan saka 4 sai na saka 5, zanyi wannan a matsayin 5&6 Ale Idi wanda jikinshi ke rawar tashin hankali ya shiga motar jikinashi na rawa, gidan baya Mahwish ya nufa da Najma yayinda idonshi ke ƙur a kanta yana ganin yanda ta kafeshi da nata idanuwan waɗanda suka yi jazur kamar gauta, du lokacin da idanuwan na ta suka shanye kamar zasu lumshe sai ita kuma ta ware su sosai tare da sakin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya, wani abu ne ke sake buɗewa a ƙirjin Mahwish. "Mommynah, kin san mi." Ya faɗa ba tare da ya janye idonshi daga kan Najma ba. Mommcy da ta riga ta ruɗe ganin yanda jini ke kwarara daga jikin Najma ta kalli ɗanta da a yanzu ta ke gani wani abu a tattare da shi, wani abu wanda kullum shine fatanta akanshi, wani abu mai muhinmanci a rayuwarshi wanda baya da, wato kwarin gwuiwa. "A,a son ban sani ba minene faɗamin, da sauri please." "Ina jin sauyi sosai a zuciyata idan ina kallon idonta, a,a ba idonta ba Mommy cikin idonta akwai wani abu kina iya ganinshi." Da jin abin da ta faɗa sai Mommy ta zauɗo kanta sai tin fuskar Najma, iya ganinta bata ga komi ba, sai de ta jinjina tsananin jarumta irinta yarinya. "Banga komi ba son, bana ganin komi sai tarin jarumtaka a tattare da ita." A kuma daidai lokacinne motocin suka tsaya a harabar hamshakin asibitin( LAGOON HOSPITAL VICTORIA ISLAND). Da sauri nosis suka iso da gadon ɗaukar marar lafiya aka ɗaura Najwa da Mahwish ya ɗauko a hannuwansa cikin jini, ko da ana tura ta akan gadon hannunsa na cikin nata su na tafiya a tare, lokacin da aka nufi ƙofar emergency da ita, anan ne aka zage hannunsa daga cikin na ta, sai de mi zare hannunta daga cikin na shi keda wuya ya ji wani irin jiri na ɗaukarshi, ba shiri ya duƙa a wajen yana haki gami da maida numfarfashi, cikin alamun soma galabaita ya ce da Mommcy. "Ruwa." Ko bayan da ya sha ruwan bai dawo daidai ba, sai ma soma rikice da jikinsa yayi nan take aka bashi gado. Ale Idi kuwa nan bakin ƙofar emergency ya zauna tare da rafka takumi, nan take wani imani da tsoron Allah ya shige shi, ganin yanda lokaci ɗaya komi ya faru, daga wayewar garin yau zuwa fitowarsu gida da afkuwar lamarin kwata-kwata ba a wuce awanni huɗu zuwa biyar ba, sai ya dinga hango Najma a jiya daya taras ta dawo gida, da yanda ya bita a guje yana zaginta har bakin titi, sai kawai kuka ya sake kwace ma shi, a fili ya dinga furta. "Faɗima ki yafe min, nasan na gaza wa rayuwarku ta wajaje da dama amma da yardar Allah daga yau na canza, na canza ta sanadiyar ƙaddarar data same ki Faɗima". Wasu ma'aikata maza ne biyu suka zo inda ya ke zaune cikin tausasa harshe suka soma rarrashin shi da kalamai masu tausasa zuciya, da ya ke aikinsu ne nan da nan suka samar ma shi da ƴar nutsuwa, abin ka da asibitin masu kuɗi, harda sassanya ruwa da abin motsa baki suka aje ma shi, sai de bai iya taɓa komi ba illa ruwa me sanyi, shine ya shanye ruba ɗaya har da rabi, yana ganin kira na shigowa wayarsa da numbobin ƴaƴansa data Mama Saudah amma ya kasa ɗauka, dan bai san yanda zai soma yi musu bayani ba. Mama Saudah. "Bai daga ba ko Lawisa, ni dama nasan ba lafiya ba, jikina yana bani ku barshi kawai mu gani zuwa anjima a sake kira ƙila aci sa'a ya ɗauka." Jiki a sanyaye Lawisa ta ce. "Gaskiya ko ni na fara zargin da wani abu, idan ba haka ba tayaya za'ayita kiran kayin Baba amma baya ɗauka, Baban da a kira na farko yake ɗaukar waya koda kuwa flashing ne, to kodai inbi bayansu asibitin in gani." "Eh wallahi Lawisa da gaskiyarki garadai a bi baya aga ko lahiya, bari in ɗauko babur ɗina sai mu je mu gani." Sauran matan gidan ma du sunyi na'am da Lawal da Lawisa su je su duba amma sai Mama Saudah ta ce. "A'a Lawal ni ina ganin zaifi kawai a haƙura mu jira dawowarsu, kasan dai halin Babanku idan da matsala ai da tuni ka ganshi nan ya dawo ko ya kira waya mu barwa anjima mu gani." "A'a Mama bara dai mu je ɗin ko hankalinki ya kwanta kema, bamuso kina wannan kukan wallahi." Cewar Lawisa tana gyala mayafi suka wuce ita da Lawal, da fatan alkairi kowa ya bisu sannan suka dawo su na tattaunawa akan lalurar Najma, da kuma yanda za'a samo mafita cikin sauƙi. Aƙalla Lawal da Lawisa sun je ƙananun asibiti kusan biyar amma sam basu samu ganin Ale Idi ba, haka sukayita zagaye haɗi da tambaya ko wani ya gansu, amma ba wani labari, har ma'aikatar sa Najma ke aiki sai da suka je, amma aka hanasu shiga, du magiyar da suka yi ba'a barsu ba hakanan suka juya gida jiki a sanyaye, yayinda suke ta sake kiran number Ale Idi amma sam bata shiga kwata-kwata, yanzu wayar a kashe ta ke. LAGOON HOSPITAL VICTORIA ISLND Likitoci kusan su uku ne suka fito su na sharce gumi, daidai lokacin da Alhaji MUZAFFAR da Mommcy suka ƙaraso wajen, yayinda shima Ale Idi ya taso cikin rawar jiki yana tambayar. "Doctor ta mutu ko, nasan ta mutu ai.! Sai ya soma share hawaye, amma mi sai Doctor ɗin ya dafa shi tare da faɗin cikin harshe nasara. "Na taya ka murna abokina, tana a raye bata mutu, mun gama yi mata ɗinki ta samu raunuka masu girma sosai, yanzu haka idanuwanta biyu munyi ma ta allurar barci amma bata amshi jininta ba, zata iya kai awanni biyu jafin ta fara aiki a jikinta, zaku iya ganinta amma banda hayaniya da surutu." Ale Idi tare da Mommcy suka sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya, da sauri ta damƙi hannu Alhaji Muzaffar suka rufawa Ale Idi baya. Kwance ta ke saman gadon asibitin, cikinta da cinya harma da kafaɗunta nannaɗe da bandeji, fuskarta ta sake jin jazur idanuwanta ma haka, ta kafe waje ɗaya da ido tana kallo babu ko ƙiftawa. Alhaji Muzaffar mutum ne me damuwa da dauwar nash kawai, baya sanya damuwar wasu a kanshi, a karo na farko a rayuwarsa da ya ji zuciyarsa ta cike, irin cinkewar da ta ke idan yaga Mahwish a cikin yanayin ciwo, al'ajabi gami da mamaki lulluɓe a saman kamilalliyar fuskarsa, fuskarsa wacce a waje babu wanda yasan damuwa ko farin cikinshi, iya iyalanshi kawai, su kaɗai ne suke gani damuwa akanta amma banda bare. Ciki de izza ya soma takawa zuwa wajen Najma data tsare Ale Idi da ido tana yi mishi magana amma sautinta bai fita. Karo na farko da yaji bakinshi ya ambaci sunan wa ta bare da kalmomin "Ƴata." ba iya shi da furucin ya daki kunnenshi a bazata ba, hatta Mommcy sai da ta ware idanuwanta a kanshi, kiran sunan bai ishe shi sai da ya ƙarasa wajenta ya ɗan ranƙwafa tare da shafa kanta da aka zame hular saboda wawakekiyar yarkar da aka yi ma ta. Tsigar jikinshi ce ta soma tashi ganin yanda ƴar ƙaramar alhaki ta iya jure waɗanan manyan raunukan da ya ke gani, farko da Mommcy ke sanar da shi zuwanta asibiti da abin da ya faru bai kawo komi ba, amma yanzu da yaga yarinyar da hannayensa suka soma ƙirgen iya adadin shekarunda ba zata wuce ba, sai ya ji wani abu ya harbi dakakkiyar zuciyarsa, da kuma ya kirata da sunan ƳATA sai wani fata ya lullube zuciyarshi, fatan da shi kanshi bai san na minene ba, yanzu kuma da ta saka idanuwanta a cikin na shi, sai da zuciyarshi ta yi rawa, jarumta, juriya gami da ƙarfin hali ya ke gani kwance a cikinsu, abin da kullum ya ke buri da mafarkin gani a cikin idon na shi ɗan. Dafa kafaɗarshi Mommcy ta yi ganin yanda ya kafe yarinyar da kallo. "Kaima kana ganin abin da Mahwish ya ce min ya gani a tattare da ita ko." Ba tare da ya ɗauke idonshi daga kant ba ya ce. "Tabbas na gani." Wayar da Ale Idi ya soma yi ne ta sa suka ɗago su duka suna kallonsa. Waya ya ke da Inna Tabawa yana sanar da ita su na asibiti sun yi hatsari ne a hanya, kuka ta fashe da shi tare da tambayarshi wace asibitice suke gatanan zuwa. Dawo da kallonsa yayi wajen su Mommcy sai ya tambayesu cike da girmamawa. "Ranku ya daɗe nace ya sunan asibitin nan iyalaina na nan tafe zuwa dubiya." Mommcy ce ta faɗa ma shi sunan sannan ta ƙara da tambayarshi miye sunan unguwar ta su sai ta aiki driver ya je ya ɗauko su. Wani yanayi ne ya gifta akan fuskar Alhaji Muzzafar, ba tare da ya ce komi ba ya soma takawa cike da izza ya fice. Jiki a sanyaye Mommcy ta bi bayanshi, ɗakin da aka kwantar da Mahwish ta nufa, tana buɗe ƙofar ta iske Papie zaune akan kujera ya tsurawa Mahwish wanda na'urori ke aiki ta ko ina a jikinsa ido, zama ta yi itama tare da kafe Mahwishi da ido, tsintar muryar Alhaji Muzzafar ta yi yana faɗin. "Ki basu iya adadin kuɗaɗen da zasu ishesu jinya, amma karki kuskura ki sake kusantarsu, suɗin talakawa ne, bana son wa ta alaƙa ta kusa kota nesa ta sake haɗaku." Cike da girmamawa ta gyaɗa kai, a can ƙasan ranta ta na jin wani iri, ta sani bama ita kaɗai ba du wani wanda ya ke cikin MUZZAFAR FAMILY basa hulɗa da talakawa, saboda wani lamari daya auku a can baya, haka kawai sai ta ke jin kamar zasu rasa wani abu wanda suka jima su na nemane a tattare da waɗannan talakawan, kamar zasu aikata kuskure idan suka nisance su......✍🏻 TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR. Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13 𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉 𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐ 💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪 𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻 𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 7 Kamar yanda Mommcy ta ce, driver ta tura bayan Ale Idi yayi ma shi kwatancen gidanshi, babu ɓata lokaci ya tafi ya kwaso mutanen gidan kusan su goma sha, tun ciki motar su ke baza ƙauyanci sunata sambatun kyawun motar da kuma girmanta. Lokacin da suka isa asibitin kuwa, bakunansu a buɗe suka soma santin kyawun asibitin, sai de lokacin da suka yi tozali da fuskar Ale Idi suka ganshi a sanyaye, sai suka dawo hayyacinsu suka cigaba da jimanta lamarin. Dukaninsu sai da suka sha kuka sosai ganin yanda kamar Najma ta sauya nan take, dan ma lokacin da suka zo barci ya ɗauketa, Mama Saudah ko sai da aka fidda ita waje dan kuka ta yi sosai, sama-sama Ale Idi ya basu labarin abin da ya faru, sosai suka yi addu'ar samun sauƙi ga Najma suka kuma nemi ya nuna musu waɗanda suka taumakesu, bai musa ba ya nufi haɗaɗɗen word ɗin da aka kwantar da Mahwish sai de du magiyar da sukasha ba'a barsu sun shiga ba, dan murɗa-murɗan securitys ne kusan guda biyar ke gadin ƙofar, hakanan suka koma suka ci gaba da tagumi. Najma bata farka ba sai marice lis lokacin an maida ƴan gidansu, daga Inna Tabawa sai Mama Saudah shima Ale Idi ya tafi yaɗan huta dan zazzaɓi ne rau a jikinshi. Mommcy ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da wa ta madaidaiciyar jaka, nan suka gaisa da Mama Saudah suka kuma yi ma ta godiya sosai na irin taimakon da tai musu, amsasu tayi da babu komi sannan ta miƙawa Mama Saudah da take ganin kamar Najma kwance akan fuskarta, jakar kuɗin tare da yi mata bayani akan kuɗin jinyar yarinyarta ne me gidan Alhaji Muzaffar ya biya. Har kuka sai da Mama Saudah ta yi ganin yawan kuɗaɗen bayan taimako da suka yi na ceti ran Najma suka kawota asibiti cikin lokaci. Mommcy ta juya ta fice tana sake kallon jar fuskar Najma, tana fatan daina jin abin da ta ke ji akanta, tunda ƙaddara ce ta haɗa su kuma ita ce ta rabasu a yanzunan. Sai de abin da bata saniba shine, wannan ƙaddarar me tsawo ce, hasalima yanzu za'afara ba'ayi komi ba, haka zalika bayan nan akwai wani wajen inda zata sake haɗasu, ba tare da su kansu sunyi tunani ba. Kusan lokaci ɗaya Najma da Mahwish suka farka, sabanin ita data farka tana jinta garas saboda allurar kashe zugi bata sake ta ba, shi da matsanancin ciwo ya farko, kwararrun doctors ne zagaye da shi sunata faman aikinsu, yayinda Mommcy ta kwantar da kanta akan cinyar Papie ta shiga rero kuka kamar ƙaramar yarinya. Likitocin sun yi iya yinsu akan shi amma sai a hankali, da kyar suka shawo kanshi matsalar, hakan ya saka bayan sun fito suka nemi ganin Papie. Ko da ya je bayani suka yi ma shi akan yanda ciwon kullum yake ƙara gaba, zuciyarshi na ƙara raunana, ta yanda ba lallai ya iya sarrafa kanshi ba saboda raunin da ta yi, da buƙatar su samo wanda zai iya kula da shi, sam basu gane bayanin doctor na samo wanda zai kula da shi ba, dan haka sai Mommcy tayi karaf ta ce. "Waye wanda zai kula da shi fiye da mu, muna bashi duk wata kulawa

Chapter 3 of 7