Share this page
2 / 8
tana dason wanda yasan darajarta๐Ÿ˜‡,kuma badai isah da ixxah ba๐Ÿคจ๐Ÿ˜Ž,niko nace"mallawan maliey kenen....tun fil'axim akan haka aka sanku....๐Ÿ˜๐Ÿ˜… Hmmm yohhh niko nace"tohh ni maman teddy ko yanake oho๐Ÿค” Kune dai kukasanni,don haka basai nayi sharhi ba๐Ÿค— Kar dai ku manta maman teddyn kuce....๐Ÿ˜…๐Ÿ˜ Haka su ummah shattu suka dunga xama,amma hajiya babba bata da alaman fitowa...don su basu san wainan da ake toyawa ba,don hajiya babba nacan ana fama daitah akan tafito wajenmu,amma sam ta'ki futowa,acewanta ita sam baxata ha'da xuri'a da bugaje ba. Ganin haka yasa wannan dattijuwan fitowa daga 6arayin hajiya,inda take shaida mana cewa"hajiya babba batajin da'di,kuma kuma ta samu bacci ne...nan ta karke maganan dacewa"amma nan da gobe dakanmu xamu xo mukawota wurin hajiyan... Godiya su innata sukayi,inda haka muka mi'ke ha'di da nufowa gidana... Sosai muka yaba da tsarin gidan,dakuma girman sa,don ba'karamun mamaki mukayi daganin irin wannan gida ba. Ni kaina ban kawo cewa"maccido nada wannan mahaukacin dukiya ba... Tun daga wannan rana,muke xaune cikin lafiya nida mahaifinki...sosai yake nuna mun so da kulawa,inda ya samun ma'akata masu yawan da xasu ringa'ka mun hidima... A cikin su kuwa harda uwani,wanda ya daukota daga gidan hajiya babba. Sosai muke zaman lafiya da ma'aikatan gidana...don ni macace mai yawan surutu da barkwanci...don haka suke tsananin kaunata... ________________________________ Sati na biyu da aure,maccido yace mun xai kaini na gaida hajiya,kuma acan xan mata wuni,in yadawo wurin aikin sa sai ya dauko ni mudawo gida tare.... Cike da farin ciki na shirya,inda nace mawa uwani ta shirya itama muje tare,don naji da a hannun hajiyan take... A haka muka shirya duka ha'di da nufan gidan hajiya babba... A wannan rana ne na fahimci yanda hajiya babba ta dauke ni a zuciyanta,don wannan rana naga wulakancin da ban ta'6a gani ba... Ciki da fara'a muka shiga falon hajiya babba, inda na sameta xaune kan 2 seater,dayan '6angarenta kuma wata mata ce,wayyayyiyar gaske,irin wa'annan matan da sukaci boko har suka gaji,wanda suke neman maza ido rufe... Ko arzikin amsa sallaman bamusamu ba,inda cikin sayin jiki na duka har kasa na gaishe da hajiya babba.... Amma kallona batayi ba,illah ma cike da tsawa da masifah ta hau cewa"kehhh.....matsa ki bani wuri...kina tunanun xan kar6eki a matsayin suruka!!! Tohh lallai kinyi kuskure....jubiki da allah,gayyar yunwa...tohhh ni nan dakika gani,inkin malleke shi,tohh ni nafi karfin ki makirah.... Nan tanisa ha'di da kallon maccido wanda gaba 'daya maganan hajiya babba bai masa da'di ba... Kai kuma saunawa xan fa'da maka baxan yarda wannan busasshiyar taxama suruka ta ba..amma ka kiji...tohh kutashi kubarmun gida...ranan daka amince da auren binta ne xaka iyah shigomun cikin gida.... Ku tashi kufita nace....hajiya babba tace" cike da tsawa...yayin da doc.binta ke gyafe tana sakin murmushi,itah ala dole tayi kamu da uwar miji.... Kallon ta nayi,inda lokaci guda idona ya ciko da kwallah,uwani ko ganin halin dana shiga yasata,saurin girgixamun kai alamun kar nayi kuka akan maganan hajiya babba... Nan maccido yafara ba hajiya hakuri akan tayi hakuri,kallon shi batayi ba,illah fixgixga batare da tace mashi komae ba... Bai kuma bin ta kanta hajiya babba ba,yajuyo ha'di da mana sallama sannan ya nufi wurin aikin sa.... A wannan rana nasha wulakanci a wurun hajiya babba, amma sam ban nuna na damu ba,inda rashin nuna damuwata yakara bakanta ran doc.binta... Haka rayuwa ta cigaba...inda shekarata daya a gudan maccido na haifoki,kuma har alokacin hajiya babba bata daina nuna mun kiyayya ba.amma sam ban duba wannan,tunda maccido yana nuna munso matuka....a wannan shekara kuma sai danaje wurin su baba na,inda kan na haifeki sai da naje sau biyu...wanda har alokacin munawwarah bata xoba...kuma taji labarin nayi aure....a nijeriya kusa dasu....amma bashi yasa ta nemeni ba... Ba karamun murna Abbanki yayi ba dana haifeki,inda nan take yasa maki suna NANA KHADIJA...wato sunan hajiya babba... Hajiya kuwa bakaramun bakin ciki tayi ba,dajin hauhuwa ta... Kwanan ki uku a duniya ne,ina xaune a kan gado na,a bedroom...inda nake goye dake abayana.... Kattawan maxa ne suka shigomun bedroom ba ko salllama,fuskan su duka a rufe da wani bakin kyalle....ihun su uwani nakeji,inda nan take na hau salati...amma kafin na farga tuni wani daga cikin su ya shakamun wani powder a fuska... Wanda tundaga nan ban kuma sanin halin da nake ciki ba,sai farfadowa nayi naga ganni a rugar har'do.... To be continuedโœ๐Ÿป #share to another groups... Maman teddy ce.... 08081202932. this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Iwj6uv5L9np0NWOuHwBELo Typing....๐Ÿ“ฑ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION...* _kungiya masu aiki da naxari da ilimi_ *DIJAMAH 'YAR FULANI* _Story and writting by..._ *MAMAN TEDDY๐Ÿงธ* Episode 9&10 Facebook@maman teddy.com... Wattpad...Aysha maman teddy... Mamanteddy@gmail.com.... *~GARGA'DI~* *_Ban yarda wani ko wata suyi amfani,wajen juyamun labari tako wani siga ba tare da sani na ba.yin hakan kuskure ne..._* Wannan labarin 'ki'kirarrene,babu fasahan wani acikin ta,inkinga tayi shige da rayuwanki toh akasi aka samu...๐Ÿค— *DEDICATION* *Dedicate to you Aysha Abdulkarim...(momy kg...)salmah Aliyu...(momy show...)wannan pagen taku ce...kuyi yanda kukeso da shi...kaddai ku manta maman teddyn ku ce...๐Ÿงธ* Ina maku barka da wannan rana mai albarka... ุงู„ู„ู‡ู…ู‘ูŽ ุฃูŽุจู’ู„ูุบู’ ุนู†ู‘ูŽุง ู†ูŽุจููŠู‘ูŽู†ุง ูˆุดูŽูููŠุนูŽู†ุง ูˆุญูŽุจููŠุจูŽู†ุง ุฃูุถู„ูŽ ุงู„ุตู„ุงุฉู ูˆุงู„ุชุณู„ูŠู…ู ุŒ ูˆุงุจุนุซู‡ู ุงู„ู…ู‚ุงู…ูŽ ุงู„ู…ุญู…ูˆุฏูŽ ุงู„ูƒุฑูŠู…ูŽ ุŒ ูˆุขุชู‡ู ุงู„ูˆุณูŠู„ุฉูŽ ูˆุงู„ูุถูŠู„ุฉูŽ ูˆุงู„ุฏุฑุฌุฉูŽ ุงู„ุฑููŠุนุฉูŽ ุงู„ุชูŠ ูˆุนุฏุชู‡ู ููŠ ุงู„ู…ูˆู‚ูู ุงู„ุนุธูŠู…ู ุฌู…ุนุฉ ู…ุจุงุฑูƒุฉ ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน Allah kasa mana abarkan wannan rana,kabamu ikon aikata abu mafi kyawu a rayuwan mu,ka nisan tamu da shirrin mutum,ko shaidan....Ameen ya Rabbil ixxaty...๐Ÿคฒ๐Ÿป *_____________________________* Bu'de idon danayi akan na yadikko ne,wanda take tsaye akaina...tana min firfita ta da wani langa langa abun fifita...gyafe guda kukan dijamah nakejiyowa,inda wasu daga cikin fulanin suke ri'ke da itah... Ganin na bu'de ido,yasa yadiko cike da farin ciki,ta hau godiya ga allah, ta harshen su ta fulatanci... Bin su kawai nake da ido,don bana fahimtan abun da take cewa"... Magana tayi takuma ta harshen fullo...inda cikin hanxari wata mata tayo cikin bukkan,ha'di da isowa gareni har inda nake kwance takawo mun deeja...a hankali kuma cikin hausan ta wanda bai fita tafara cemun"ki bata nono take bu'kata tun jiya,sai yanxu muka samu kika farfa'do....don haka maxa kibata ai ma tayi ha'kuri... Babu musu na Amshi deeja nafara bata nono,inda a raina nake tunanin ta yadda wa'innan mutanen suka tsiratar dani daga wannan axxaluman mutanen,wanda bansan wanda ya turosu wurina ba. A hankali komai yake dawomun,inda nan take na hau xubar da hawaye mai dacin gaske... Yadikko ne ta dafani ha'di da bani baki,akan komai na dauke shi a matsayin kaddara... Haka na kwana uku a cikin rugar har'do,inda kullum wannan fulanin suke dawainiya dani da kuma kehhh deejamah... A wannan rana da muka cika kwana uku ne,mai gari wanda yake yayane wurin yadiko,yayo kiran na... Haka na isah wurin mae gari,inda anan yake shaidamun da yanda suka ha'du da ni,kuma da yanda suka taimakeni a hannun. Bayan sun bar dani gidan maccido, basu tsaya dani a ko'ina ba,sai a kusa da wannan rugan... Inda su mai gari na hanyar ta dawo wansu ruga daga cikin gari...nan suka ga wannan mutayen na janye da ni...abunka ga mara gsky,ako'ina sai ya nuna kansa... Kunsan fulani ba tsoro..cikin tsawa da kuma hausan su wanda bai fita,su kace" waye wannan,mai kuke anan wajenn... "Cikin muryan 'yan ta'adda suka maida ma mai gari da magana ta hanyar cewa" kai tsohon najadu bar wurin nan,kasheta xamuyi,inkuma ka6ata mana rai mu ha'da da kai... Cikin xafin ran sunan da suka kira mai gari yace"tohhh bari kugani,xare sandan su duka sukayi,inda suka nufi wainnan 'yan ta'addan... Ganin fulanin sunnufo su,kuma sun san bafillatani ya kasheka ya kashe banxa,musamman irin na daji irin wa'innan,yasa su saurin sakin ummah,inda sukayi wurgi da deejamah,suka kwasa da gudu ha'di da shigewa ta cikin dajin... Bun bayan su sauran xasuyi,nan mai gari ya taresu,hadi da cewa" su barsu,suyi saurin ceton ran wannan bayin Allah... Haka ko sukayi,inda da shigowan su,cikin ruga.suka sauka a bukkan yadikko...a haka sai da aka kwana guda sannan umma ta farfado... Nan mai gari ya nisa, ha'di da tambayan ummah daga inda ta fito... Shiru ummah tayi,don ita sam batasan ko'ina a nan najeriya ba,ita dai tasan tana najeriya... Nan ta basu amsa da daga nijeriya take... Shiru mai gari yayi,kan daga bisani yace" ae nan duka sunan shi najeriya...amma wani gari muke nufi kike? Ganin umma bata da Amsa yasata cewa" ni ba 'anan nake ba,ni 'yar asalin garin agadas ne,aure ne yakawo ni nan. Nan na xauna ta fara basu labarina komai da komai... Sosai mai gari da sauran mutane suka tausaya mun,inda nan suka shaidamun suma basu san birni ba,kuma basu gane daga inda nake ba,saboda sunfi rayuwansu a cikin ruga... Haka mai gari yace"na kara hakuri na xauna tare dasu har Allah ya kawo ranan da xan ha'du da dangina,ko miji na... Sosai nayi farin cikin xama da su...fulanin kirki. Kewa daya nayi,shine kyewan baba da guggo,sai kuma halin da maccido yake ciki a yanxu...amma duk inna kalleki sai naji gomma da allah ya barni dake... A haka nacigabada rayuwa a wannan ruga,inda a haka kika girma a cikin wannan ruga. Kuma su yadikko su suke maki fulatanci,kinji yanda akayi kk iya yaran fillo,don ni ban iya ba...sai dai na biku da ido,amma yauda gobe xaman tare yasa har na fara fahimtan wasu abun... Nisawa umma tayi ha'di da kallon dijamah,wanda kuka takeyi sosai,tausayin ummah yagama kamata,cikin sauri ta mi'ke cike da yarinta tafara cewa"ummah ki tashi mugudu,kar su abbana suxo su tafi damu,hajiya ta turo aka shemun ke... Goge kwallan idonta umma tayi,inda ta kamo hannun dijamah ha'di da cewa" a'ah deeja ba hajiya ce ta turo wa'innan mutane ba,nima bansan waye ba... Sannan kuma dama ayau xamu bar wannan rugar har'do... A hankali umma ta mi'ke ha'di da nufahn kasan gadon karan bukkan,inda ta fito ma wa da dijamah kayanta na saken fulani guda uku... Sai kuma nata kala biyu... Saida su ka tabbatar da kowa ya shiga cikin bukkan sa,sannan suka fito ha'di da barin rugar har'do... Tafiya sukeyi suna waiwayon wannan ruga,inda suke tunani ranan da wowansu wannan ruga... _____________________________ Tafiya suke cikin dare,inda a haka suka isah tasan cikin gari. Batare da umma tasan inda xata ba,ta kutsa kai cikin wata mota dataji ana cewa"Adamawa... Shiga sukayi,inda saida dijamah ta ganta a cikin mota,ta hau tambayan umma tana da shede ne... Nan umma ke shaida mata,tana da kudin da uwani ta basu,dakuma wanda sukayi ciiniki a lumo... Safiya tayi masu ne,acikin garin Adamawa,inda dijamah cike da farin ciki take bin garin da kallon sha'awa... Sai da umma tasha fama,sannan drivern ya amshi kudunta,don kudin nasu bai kai ba... Ware ware ta suka hauyi,inda wasu samari ganin suna wareยฒ yasasu tambayan inda xasu? Batare da wani tunani ba,umma tace"ruga...!!! Shiru sukayi inda suka ce,wani ruga kenan mama? Rugar ya windo....ko rugar surbajo.... Nan umma tace"Rugar surbajo.... Nan suka sa su umma a abun hawa,ha'di da biyan masu kudin,wanda badon kowa suka biya ba,sai don dijahmah.... Gaba daya dijamah tagaji,ga wani irin mahaukacin yunwa da takeji,tun tana daurewa har takasa,inda a haka suka isa wannan ruga,...bayan sun sauka daga abun hawane,suka fara takowa daga 'kasa,don isah cikin wannan ruga,wanda tafi rugar har'do wayewa... Nishi dijamah ta hauyi samaยฒ inda umma cike da ru'du tafara wareยฒ n ruwa...amma sam babu ruwa a wurin,wulkawn mutum ma babu bare,ruwan. Tun dijamah na fitar da numfashi,har ta kasa,inda lokaci daya numfashin ta ya 'dauke...kuka umma tasa ha'di da kiran sunan dijamah...amma sam babu alaman numfashi a tare da itah... Daiยฒ wasu tsofaffin fulani,wanda da'alama mata ne da mijinta,sukaxo wucewa.... Cikin axama matan tayo inda umma ke a durkushe,nan ta hau tambayan ta daga innah take??? Kasa magana ummah tayi,illah cewa da umma take" don allah ku taimakamun kar dijamah ta mutu,'ya ta ce.... Duka ta harshen fulatanci suke maganan. Wannan tsohon ne yayi saurin ci6an dijamah ha'di da nufah cikin ruga da itah,wanda da isan su suka nufi cikin bukka ha'di da kwantar da dijamah... *_____________________________* *Cikin garin.....* *GARIN ADAMAWA* Wani tan'kasheshen gida ne na ganj,wanda girmansa yasa turawa ke kiranshi da estate house... Gida bakaramun gida ba,wanda girman sa.ma,baxai fasaltu ba... Sojoji kuwa xasu kai kimanin fiye da 50 xuwa sama,ko wannan su na kewaye da wannan gida...wanda da 'alama tsaron gidan sukeyi...licrout da sauran securities,wanda ba sojoji ne ka'dai ke tsaron gidan ba.... Jiniyan jami'an tsarone najiyo daga bayana,wanda yasani saurin jirgawa daga bakin tan'kamemen gate 'din danayi nisa wajen kallo... Wasu motoci ne ke biye dana GEN.SUFYAN TABAWA... Inda motocin sun kaifi 15 ke bin yanshi,wasu a gaba wasu kuma a baya... Bayan anware tankamemen gate 'din ne,nayi saurin shugewa...daga ciki... Hmm gidane wanda daga waje ashe banga komai ba....arxiki nadaga ciki.... Bude mawa hajiyan nashi mota akafarayi,inda sauran securities suka bude ma sauran side dun... Cike da ixxa da jida issa da dukiya ta fito,tana ciko wuya...wanda kayan dake jikinta kadai ya isah yasa katafi duniyan tunani....jikin nan kuwa ta ko'inah yasha zinarai.... Niko nace"JUSTICE MADINA KENAN.. Uwar gida kuma amarya a wurin General sufyan tabawa.... Fitowa yayi cikin shigarshi ta alfarma,inda ya juyaga 'yar tasa wanda saukan su kenan daga 'kasan,nan yace mata"welcm back to nijeria my kid...!!!ya kika ga new house 'din mu na nan? "Ya tsina fuska yarinyan tayi,inda cike da mulki tace" ba laifi dad,amma kayimun laifi guda 'daya... "Kallon ta justice madina tayi,hadi da cewa" okay my baby mai yafaru,mai kuma ya6ata ran baby na...ta fa'di tana sakin mata 'kayataccen murmushi...wanda bamai ganin sa,sai 'yan 'ya'yan nata... Cikin basarwa a kuma wula'kance" 'yan nata tace" dad yace mun kid...bayan ni ba kid bane yanxu,ko mom baiga na'kara girma bane...? Don haka yabani ha'kuri. Nan ta karke maganan ha'di da turo 'yar mitsilan bakin ta. Cikin rayuwansu ta 'yan cin da suka saba,dad yayi dariya ha'di da shafa kan 'yar tasa,sannan yace" eyyah sowie my dear meenash...baxan karaba... Justice ne tayi"murmushi, inda meenash tayi wani barander da xai sada tada sitting room...batare da tace" ma dad komai ba... Bin bayanta sukayi,inda ma'aikatan gidan ke auki 'kame masa,yayin da wasun su ke kaimasu gaisuwa... Basu ta kansu ba sukayi cikin falon tasu,wanda tagaji da kayan alatu da more rayuwa... Ganin babu meenash,afalon yasa justice haurawa saman stairs,don tasan can tayi,yayin da a zuciyanta take cewa"ohhh meenash 'yar daru kenan...har yanxu fushi take,ala dole batason nijeria... Kaman ko tasani zaune ta samu meenash a kan wani super cushine,inda 'yan aikin part 'din ke xube a gabanta suna kwasan gaisuwa da mata barka da dawo wa. Kallon su batayi ba,inda take cike take batsewa... "Justice ne tayi saurin nufo inda take,ha'di da xama gyafenta,ta jawota ha'di da xaunar da itah a jikinta. A hankali kuma daiยฒ kunnen ta,ta hau yima magana.inda batare danaji abun da tace ba sai dai maganan meenash naji tana cewa" No mom bana son nan 'kasan,kawai mukoma Abroad plz.... Kuma innan kasan nada da'di mai yasa ya Aliyu bai dawo ba....???? To be continued....โœ๐Ÿป Kaman yanda kuka sani,wannan littafin ta kudi ce,haka ne,xaki turo #100 ma wannan numbern...idan VIP ne #200 transfer #200 duka ta wannan number... MTN....xaki turo ta nan 09137392680. Idan airtel ne ta wannan numbern 08081202932. *#share to another groups...* Maman teddy ce... *MANAZARTA WRITERS ASSO.๐Ÿ“˜๐Ÿ–Š๏ธ* _Kungiya masu aiki da naxari dakuma ilimi..._ ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ *DIJAMAR 'YAR FULANI* ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ *Story and written by:* *Maman teddy๐Ÿงธ* _Episode 11_ Facebook@mamanteddy.com Wattpad Aysha Maman teddy... Mamanteddy@gmail.com *~DEDICATION~* Dedicate to you my dear fans...๐Ÿ˜๐Ÿฅฐwannan pagen taku ne,kuyi yanda kukeso da shi๐Ÿค— _________________________ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู… Kallon ta justice madina tayi" inda a hankali ta kai hannun ta ha'di da shafa kan 'yan nata,wanda Ashekaru batafi 11 yrs ba,nan tace mata" eyyah my baby,ya Aliyun naki shima xai dawo very soon kinji...? Don haka plz ki kwantar da hankalin ki,nasan duk don baki saba da kasannan bane,shiyasa kike kin ta,but inkika yi 'yan kwanaki nasan xakiji son nijeria sosai my dear... Justice madina ta 'karke maganan ha'di da bin 'yan nata da kallo,kuma dason amince wanta... Shiru meenash tayi,batare da tace mawa mom 'din nata komai ba. Don itah tana nan akan bakan ta nakin amincewan xaman ta nijeria.... 'Bangaren dijamah kuwa,sai dai muce alhmdllh,don ansamu nasaran farfa'do wanta...inda umma tayi matukar farin cikin haka... Wannan kuwa tsofaffin sun jajirce matuka,inda ummah ke ta masu godiya... Bayan dijamah taci abunci ne,yawindo..ta kalla umma ha'di da tambayan daga inda suke...? Ada umma taso rufema wa yawindo komai da yashafesu,amma ganin karamcin da sukayi masu yasa umma baiyana mawa yawindo da mai gidan nata komai....inda ba'karamun tausaya mawa ummah da dijamah sukayi ba.don yawindo harda kuka,abunka da rigima ta tsofaffi๐Ÿ˜‚ Tun daga wannan rana,yawindo da mijin ta,wanda dijamah kekiransa da baba suka basu umma bukka.inda lokaci guda rugan nan kowa yasan dijamah... Don tuni tayi sababbin kawaye a wannan rugan surbanjo...inda yawindo ta dauki dijamah kaman jika,don har wasan jika da kaka takeyi mata...haka ma baba,don su basu ta6a haihuwa ba,tun da sukayi aure,inda yanzu har tsufah ta riskesu.... Wannan kenan... _____________________________ A kwana a tashi babu wuya gamai rai...cike da mamaki nake bin dijamah da kallo,don a yanxu taxama cikakkiyar mace" wanda kyawun 'yamma tanci ya bayyana mata sosai,don yanxu xatakai shekaru 15 a duniya...gaba daya ta saje takoma bafullatan usul,inda take 'dauke da kwaryan nono,wanda da'alama xata fita ruga ne,taje cikin kasuwan cikin garin Adamawa... Bayanta ummu ne,itama dauke da kwaryayen nono...dasauran fulanin rugan nasu,wanda dukan su sauri sukeyi don su isa kasuwa da wuri... Kafin su isah kasuwan cikin garin ne,idon dijamah yasauka akan wani sabon company,wanda da'alama ba'a da'de da bu'deta ba,cikin harshen fulatanci tace ma ummah" ummah wannan kuma mene ne,gida ne...? Murmushi ummah tayi hadi dace mata"a'a dijamah masana'anta ne...inda ake sarrafah abubuwa.da kirkire kirkire... Cike da hauka da wauta dijamah tace" yehhhh ummah kafin a tashi kasuwa xanje na ga cikin sa,aradu 'kamshi naji daga can wurin,ummah kila wurin madafi ne ko...? Umma ne tayi saurin kallon dijamah ha'di dacewa" a'a dijamah karkije kinga mu ba'ki ne...kuma nace maki ba wurin madafi bane,masana'anta ne... Tun daga nan dijamah batakuma cewa" komai ba,inda a ranta ta kwallafah son xuwa cikin wannan company,don acewanta wurin saida abunci ne,dasuke gani a wurin kasuwa... Niko maman teddy nace" tohhh dijamah kodai kwadayi xa'aje ayi ne...๐Ÿคฃ Kwance yake wanda daga shi sai gajeren wando ajikin sa da singilite...fari be Tass kuma kyakykyawa na ajin karshe,dogo ne amma ba can ba,irin wa'innan mazan ne da'ake kira da segxy guys... Fuskan sa kewaye da siririn saje...dagani basai ance maka ba,xakasan irin wannan butters din ne... Wanda mata ke deting da rushing din sa,wanda su mata kebin su,basu ne ke son su ba...cika yake yana batsewa,fuskan sa 'daure tamau,wanda da ganin sa kasan irin maxan nan ne wanda basa son raini...sam... Gyefe guda kuma wata budurwa ce...rike da hannun shi tana masa magiya,wanda da alama sun gama masha'an su ne,don Aliyu haidar shaharrarrene wajen keta ma 'yam mata hadi,amma ga wanda yasani,don a duniya kowa ganin mutumin kirki ake mai,don shi akwai yawan kyauta,sadaka,taimakon marasa karfi,don haka ne,kowa yasan shi,inda Abokanshi kemai kirari da dollars... Shi mutum ne wanda inyayi sex dake baya kuma 'karayi dake,sai dai wata...irin wa'innan maxan ne harijai...masu yawan bukata,kuma shi sam baya da ra'ayin aure,don yace har yanxu baiga irin matan datayi mai ba... Da sam ba haka yake ba,bai mu'amala da matan banxa,sanadin fara wannan dabi'a tasa sanadin wata da ake kira da Basmah,wanda ita tafara sa Aliyu haidar a wannan hanya,don ita tafara neman bukata a gareshi,don dama itah watsattsiya ce...tun daga nan abun ka ga mai yawan nema,shikenan suka fara wannan mu'amala,inda ita ala dole son shi take,kuma so da aure,wanda shi ko sau 'daya bai ta6a tunanin ta a matsayin matan auren sa....inda ita basma 'yar kawan mahaifiyan sa ce,aminiyan ta sosai wato justice madina.kuma Aliyu ne dan justice madina na farko,inda daga baya ta haifi meenash,wanda sukenan 'ya'yan da Allah yabasu... Wannan shine ta'kai taccen labarin Aliyu haidar.. Budurwan dake gyefen sane mai suna sobrina takai hannun ta gana Aliyu tana murxawa cike da salonta na jawo hankalin sa gareta...inda shikuma gogan kallon ta baiyi ba,illah ma cewa dayayi cikin masifah,sobreen out....!!! "Cike da rashin xuciya irin ta karuwan mata ta kara matsawa kusa dashi,wanda ko kaya babu a jikin ta,kai bakin ta kai xata ha'de da nasa,inda ya kauda kai ha'di da hanka'de ta gyafe...ganin yaki saura ranta yasata fara cewa" plz im sorry my baby...im so sorry....kallonta bai yi ba,illah daukan laptop din sa da yayi,wanda yake kan bedside drowern dake gyefen sa... Cike da dacin rai sobreen ta fara xubar da hawaye,don ita sam bata gansu da Aliyu haidar ba,tana matsanan cin bukatan sa alokacin...don haka nan cike da kuka take cemasa" plz Aliyu i will give my self... Kallon ta baiyi ba,illah mikewa da yayi yanufi privacy don ya tsaftace jikin sa... Bayan yayo wanka ne,yafito sanye cikin rigar wanka,hannun sa kuma 'dauke da karamun towel ,wanda yake goge sumar kansa da shi... Ganin sobreen ta saka kayanta,wanda da'alama tafiya xatayi,yasa shi jawo bedside drower ha'di da wurga mata ku'din da yakai kimani #200k. A hankali ta kai hannun ta,ta dauka,inda ta kuma matsawa kusa dashi,ha'di da manna mai kiss a tattausan lips din sa,sannan ta fito daga bedroom din nasa... Shiko Aliyu haidar bayan kammalawansa ne yafito daga bedroom din,inda yake sanye cikin shigarsa ta suit wanda yakuma bayyana haiban sa da kwarjinin sa...wata 'yar aikin part din nasa ne,tayi saurin xubewa ha'di da gaishe sa,kallon baiyi ba,illah nufan dirning area,inda aka jeramasa abun cucuwa,wanda kalolin su bama xasu kirgu ba... Xama yayi akan 'daya daga cikin kujerun dirning dun,inda ya ajiye brief case 'din sa,akan wani kujeran.... Nan cikin hanxari cookern taxo ha'di dafara serving nasa... Bawani cin abuncin yayi ba,don sauri yake ya isah,companyn sa,wanda yake da bakin da xasu xo wurin sa.... A hankali ya maida kallonsa ga wrist watch din dake manne a tsitsiyan hannun sa,inda yaga kusan 10am...karamun tsaki yayi,ganin lokacin dayace ma'aikata su hadu a mitting room yayi,gashi ya makara,kuma bayason African time... Mikewa yayi cikin hanxari ha'di da nufan company n nasa... Dijamah kuwa dataga ta kammala saida nono,kuma wasun su basu saida ba,kawai sai ta yanke shawarar xuwa wannan company. Inda batare da kowa yasani ba,ta dauki 'yar mayafin ta,wanda dashi da babu duka 'daya...ta nufi wannan company n dataga an rubuta... *ALIYU HAIDAR COMPANY LIMITED....* Nufahn inda taga motoci na fitowa tayi,wanda cike da tsawa wani security yayi mata magana da cewa" keehhhh mai xaki shiga kiyi anan... Kallon shi tayi,wanda sunan yayi mata tsawa ne,amma ko 'darr bataji ba,nan kanta tsaye tace" naxo inga irin wurin ne... Cike da kyankyanin ta don karnin nono takeyi ba kadan ba,wanda nan securityn yace"kehhh wuce kiban wuri babu inda xaki shiga... Yana gama fa'damata yasa koma wajen tsayuwansa,inda 'dayan securityn dasuke tare yake binta da kallon,aranshi kuwa cewa yake ko mai yakawo wannan bafullatan dajin nan ohooo.... Kallon ta sukeyi,ha'di da bin saken jikin ta na fulani da kallo...wanda yasha nono ga datti da yayi har ya gaji.... Tohhh kaman yanda kukasani free page xai ending a page 15...don haka yana gab da 'karewa... Ga mai son cigaban wannan littafi xai turo #100...idan VIP ne #200 transfer ma #200...duk ta wannan numbers... Idan MTN ne ta wannan...09137392680. Idan kuma airtel ne ta wannan xaki turo..08081202932. Plz share to another groups.... Maman teddy ce๐Ÿงธ https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION๐Ÿ“˜๐Ÿ–Š๏ธ* *Kungiya masu aiki da naxari da ilimi...* ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ *DIJAMAR 'YAR FULANI* ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ *Story and written by:* *Maman teddy๐Ÿงธ* _Episode 12_ Facebook@mamanteddy.com Wattpad@nafee kaxaure...... Mamanteddy@gmail.com *~DEDICATION~* Dedicate to you my dear fans...๐Ÿ˜๐Ÿฅฐwannan pagen taku ne,kuyi yanda kukeso da shi๐Ÿค— _________________________ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู… Kasa tafiya dijamah tayi,inda take tsaye tana wareยฒn son shiga cikin wannan companyn na *~ALIYU HAIDAR COMPANY NIGERIAN LIMITED...~* Fiye da munti talatin tana tsaye,inda wa'innan securities din kallon ta basu sakeyi ba...illah ma cigaba da harkokin su da sukeyi... 'Bangaren Aliyu haidar kuwa,bayan yagama meetting da ba'kin nashi ne,wanda turawa ne,dakuma manyan gomnati sukaxo akan suna son abasu shares na wannan company, wato suna son asusa hannun jarin su.... Bai amince da bukatun su,sai dai yace masu" suje nan da mako guda su dawo...akan xaiyi tunanin akan lamarin...sosai sukaji da'din laramcin da Aliyu haidar yayi masu...inda basu '6ata dogon lokaci ba,suka bar company nin.... Bayan tafiyan su ne,yatara ma'aikatan masana'an tan,inda yasa P.A nasa yakuma masu bayanin abun da xa'a kuma gyarawa a cikin company n. Sosai ma'aikatan suke godiya da 'kara tunatar dasu...don kowa yasan halin sir Aliyu haidar... Abu 'kan'kani xakayi yace" ya a sallameka,asamo masa wani makofin ka...irin wannan halin nasa ne yasa suke masifan tsoron masa gargada acikin wannam company nasa... Bayan yagama abun da xaiyi ne,ya nufi parking space na company n,inda ya 'dauki motansa,'kirar accura....2021. Nufan tanfatsetsen gate din company n yayi don yafita daga cikin ta,inda nan idonsa ya sauka akan dijamah, wanda suke kiciยฒn hanata shigowa cikin company n... Bangaren dijamah kuwa ganin wa'innan securities sun hanata shiga,kawai sai ta fakaice idon su tayo cikin wannan company... Inda cikin hanxari wannan securityn ya kai hannu ha'di da jawo mayafin jikin ta,gani ya fixge mayafin nata ne yasa shi dakatawa,don a ganin sa xata dakata da shiga cikin wannan ma'aikata,amma sai yaga ko ajikinta,kara kutsa kai take ciki abun ta...dayan securityn ne cikin xafin rai,dakuma ganin batada galihu ya kaimata mari. Wanda daiยฒ a idon

Chapter 2 of 8