Share this page
3 / 9
sarra yake tare hancinsa dan yana gudun wani habon ya same shi Wayar da yake yi bai katse ba haka kuma bai daina kallonta ba da yarenta dake kallonsa suma Da haushi ta sake kureshi da kallon raini, a ganninta idannba wulakanci irin na y'ayan masu kudi ba ta yaya za'a maka salama kana kallon mutane ka kasa koda amsa amincin da aka nema maka a wajen ubangijinka? Baki ta tabe ta ce" Ban san ko kana jin hausa ba fan saurayi? Ama dan Allah mahaifinka ko mai gidanka nake son gani, watau mai kampanin nan! " Kallon da yake mata da kuma dan juyar da kansa da ya yi ya waiwaiga hagu da damansa ya sakata bi itama da kallo, sai ta sake dubansa ta shiga tunanin ko kurma ne? Da wani bacin ran ta budi baki ta ce" Bawan Allah shin kai kurma ne? Ko kana daya daga cikin masu wulakanta mutun a wannan kampani? Koda yake kasancewarka a wannan kujerar ta yiwu kai din makusanci ne ga mai kampanin, ka fada masa cewa Allah ya halice shi, shi ya halice mu, ka fada masa cewa babu wanda ya san gobe sai Allah, idan da sanninsa ake wulakanci a karkashinsa Allah ya saka min wulakantani da aka yi har aka zagar min y'ayana!, Idan ba da sanninsa ake yi ba ya gagauta yin bincike ya tace ya rauraye! Wadannan din y'ayana ne! Yayana ne ! Ba bara.........." Idannuwanta ta rintse sai kuma ta bude ta dora da fadin" Ba barayi bane su, ina kafa kafa da abina, ina kuma fadawa Allah, yau koda sun iya hali irin na bera idan har an san ciwon haihuwa za'a kiyayi zaginsu da shi, idan kuma an san gobe ta Allah ce za'a kiyayi aibatasu da laifinsu na yanzu, domin laifin wani na iya kasancewa laifinsa na gobe!, Bai san me zai zama gobe ba, idan har shi din magidanci ne da ya san menene haihuwa to fa zai kiyaye ya saka tsari a tafiyarsa.....ka fada masa ni din uwa ce da hawayena ke zuba na ciwon wulakantamin y'ayana da aka yi, na san kai baka haifa ba bale ka sani dan girman Allah sak...................................." Dif ta dauke wuta a lokacin da ya mike daga cikin kujerar da ya lume ya tura kafafuwansa cen kasan tabel din office din , ashe irin zaman nan ne ya yi wanda ake tura kaffafuwa karkashin table a dafe kujerar, zama ne na masu tsayi ba gajeru ba gaskiya, shi yasa sam bata gane tsayinsa ba har sai da ya mike a yanzu Idan har ya mata magana a iffice din nan to fa takardun dake zube saman table dinma sun masa Wajen wayar tafi da gidanka ya nufa ya daga ya karra a kunnensa dannan ya shiga dadana numbobin da yake sin kira Cen kasan makoshinsa ya iya furta" EH " sannan ya ajiye ya kuma juyowa ya jinginar da bayansa jikin garun ya sake fuskantarta yana sauraronta Shiru ne ya dauki wajen, sosai shiru ana kallon kallo Kasa kasa Husain ya ce" Mama mu tafi kar ya zane mu " Hasan dake masa kallon da yake masu ne ya sake jan hijabinta yana fadin" Mama lets go please" Lebenta ta dantse cike da takaici, ta fa gane ba kurma bane tsagwaron wulakanci ne irin na yaren zamani, idan zata rantse ba zata yi kafara ba ta tabata wannan din ta girme shi nesa ba kusa ba, rashin kunya baya karewa a duniya! Juyawar ta yi, ba dan komai ba sai dan ta san ko menene uban gidansa ya jita!, Ta bar wajen ne dan ta kare mutuncinta, abinda ya so faruwa dazun ba zata so ya tabata a kanta a gaban Ζ΄aΖ΄anta ba, abin nan ta ji hirarsa a wajen yan school dinsu, tabas a dazu ta tsorata da ta ga za'a dasa mata shi Gana take sunna biye da ita har suka idasa sauka Bata tsaya ta kula kowa ba sula nemi ficewa a baban filin kampanin har an fara kiraye kirayen sallar magariba "Asalamu alaikum Hajia" muryar wanda ya kawo mata agaji a dazu ta daki dodon kunnenta da yannayi na ja baya ba matsewar waje ba Juyowa ta yi sai ta ga daya daga cikin ma'aikacin wajen rike da ledoji jigi jigi kusa da likitan A tausashe sosai ya furta" ki yi hakuri na san ke matar aure ce, ba wani abu bane dama dan na tambaya ne Ina fata ya saurareki?" Amina ta juyar da kanta tana shaΖ™ar iskar magariba dake hurowa a sanyaye ta ce" Ban samu ganninsa ba, sia dansa, na fadawa Ι—an nasa sakon na san zai sanar masa" Dan jim ya yi , sai kuma ya ce" Dansa kuma?" Amina ta gyada masa kai tana dubansa A hankali ya ce" Ai shine mai wajen fa, shi daya muka baro a ciki" Sai da ta saki baki da mamaki, ta waiga ta sake waigawa ta kuma kallonsa, ama sai ta barawa kanta abinda ya bata mamakin a zuciyarta , karshema sai zuba ido tana kallon yadda yake ta kokarin sai Hasan ya bashi hannu ama ina, a murtuke fuskar nan du inda rigima take ta tatare a saman fuskarsa, Husaini ne ya sake sosai da shi yana amsa tambayarsa, sai kuma ta juya ta fice gannin Aban saudat ashe dai bai tafin ba ta karasa tana kawar da fuskarta gannin ya fito a adaidaitar yana tambayar lafiya kamar wace ta yi kuka? Gannin ana miko masa ledojin ta juyo da mamaki tana fadin" Yaya kuke gannin salon zai je? Yaya kuke hangen cakwakiyar lamarin? Ku zo mu je sistersπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜ πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ _*NI ZAN LADABI*_ πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Wa'inda suke da matsala da harkar banki zasu iya turo kati ta numberna, ko su yi pos in sha Allah, kuma a kan number nawa kamar haka 93811618..... Sai kun zo Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* *Page 0️⃣4️⃣* Da mamaki a saman fuskarta ta ce" Aa ba namu bane wannan fa" Mutumen nan dai ne rike da hannun Husaini dan nesa da su kadan yana fuskantar Aban saudat aa tunaninsa ko mai gidanta ne ya ce" Asalamu alaikum, dan Allah na biyo bayansu dan na karra bada hakuri, sannan ku yi hakuri ku amshi kayan nan, an samu matsala ne na rashin fahimta in sha Allah hakan ba zata kuma faruwa ba" Tsayen da take kallon bayaninsu take yi da mamakin ko menene abinda ya sa wannan mutumen biyosu mai daraja ne, shi din da kansa mai tausayi ne mutumen, a sanyaye ta girgiza kanta ta ce" Aban saudat ba zan amshi kayan nan ba, ga dai kudin a irga abinda suka kama sai a cire harda na biscuit din da ya ci" A nutse ya ce" Ama ai Aban aboki yace ki amsa ki yi hakuri ki amsa " Husain da sauri ya kalleshi yana fadin" Aa fa, ba abanmu bane wannan, akace abanmu ya rasu ko Mama?" Shiru ta yi tana kallon bakin Husaini, yaron ba dai surutu ba , kuma ba rashin kwaba bace haka Allah ya halice shi da saurin sabo da shegen surutu Masha Allah "Ay sorry ai na zata abanku ne , ama ki menene a dai yi hakuri, ni na kasa hakura ne dan na ga dan uwan aboki sai huci yake yi, " Gannin baban mutun ba wani karamin saurayi ba yana ta masu magiya a kan abinda ba shi ya bata ba ya sakata dan rage tsayinta kadan ta yi masa godiya sannan ta shige adaidaitar ta jinginar da kanta a jikin abin adaidaitar ta yi ta lumshe idannuwanta, a haka take jin magangannunsu har ta ji ya tada babur din sun dauki hanya Ana fitowa daga masalaci sunna karasowa kofar gidansu A daidai lokacin ne matarsa watau innar saudat ta fito zubar da ruwan wankin da ta yi, kasancewr anguwar ba wai mai duhu ce cen ba ya sa idannuwanta duka sauka a kan mijinta dake sauko da ledojin nan yana ajiyewa a kofar gidan Amina Baban abinda ya sakata sake zuba masu ido gannin Aminar na binsa da kudi tana magiya ama mijinta wanda ko tau naira dari da ashirin ce ya bara mata na cefanen safe da yama nata da Ζ΄aΖ΄ansu yana nuna ba zai amshi kudin nan ba? Lalle yau abinfa take zargi ne zai tabata kennan? Juyawa ta yi wuuuuu ta shige ciki zuciyarta cike da sake saken irin yadda zata bullowa al'amarin Sunna shiga cikin gidan ta rufe ruf sannan ta bude baban dakin tana saka kayansu hadi da kunna wutar nepa da fatan samun wuta dan zafi take ji sosai Du da alwallah suka shigo suka shinfida abin sallah, itama ta fice dan dauro tata alwallar Tana zuwa ta shiga gabatar da sallarta a nutse, sai da ta gama sannan ta wuce ta bude kayan Macaronin da ta siyo masu ta dauko ta shige kicin dinta ta kunna fitilar kwai domin kicin din bata da fitila ta shiga dahuwar gagawa ta hade komai ta tsayar da ruwan miya ta koma dakin tana idasa fitar da abubuwan dake ciki Ido kawai ta zubawa garin kayan kwalam da makulashen da aka zuba a wata ledar shake, sai makaroni da shinkafa irin na leda masu tsadar nan kala daban daban a wasu ledojin shake summa wa'inda a sanninta dai ba ita ta saka a cikin kayansu ba Ajiyar zuciya ta sauke ta mayar gefe tana sake duban Husaini gannin sai kallon ledar kwalam da makulashen yake Bata bashi ba ta daure sosai ta ajiye gefe Da wuri wuri ta gama girkin lokaci daya tana gyaran kayan miyar da danyen naman da kifin da zata yi anfani da su , so take ta gyara su tun yau kar su kai gobe su cenza warinsu domin bata da freeza bale ta saka Juyewa ta yi a baban faranti ta ajiye masu karkashin karamar fankarsu da abin firfitu ta kama ruwan wanke hannu da na sha da yaren suka dibo ta ajiye Hannayensu suka wanke suka shiga cin abincin bayan sun yi adu'a Basu jima a kan cin abincin ba suka tatare ta kwashe komai da kanta ta darwaye abubuwan da suka yi amfani da shi da ruwan rijiyarsu mai kyan gaske sannan ta dawo ta zauna ta kirayi yaren Gabanta suka zauna su biyun, ta tsura masu ido irin yadda suke kama ita da kanta ta yannayin girman jikinsu da kuma kamanin idannuwansu kawai take bambance su A hankali ta ce" Waye ya baku izinin fita daga bayana bayan tafe muke tare da ku?" A tare suka kwashi magana wannan na cewa dan uwansa ne wannan na nuna dan uwansa Kausasa muryarta ta yi sosai ta ce" Ba zaku fadi gaskiya ba kennan?" Jiki a sanyaye Hasan ya ce shine, sai kuma Husainin shima ya ce shine, lokaci daya kuma sai Husainin ya dora kansa a gefen kafadar dan uwansa ya fashe da kukan da ya kusan sakata karaya harma ta rarasheshi bayan ta dauri aniyar yi masu fada da nasiha ne, koda zata yi rarashin ba yanzu ba, dan haka ta jure sosai tana kallonsa ta ce" Kai mike daga jikinsa kuma ka kama min bakinka ka yi min shiru! Yaya nace maku a kan abinda aka bakuma bale wanda kuka gani kuka dauka? Yaya na ce maku a kan haka?" Da sauri Husain ke rufe bakinsa dan kar ya kuma fashewa da kukan stlll yana son bada amsa ga kuka na hanna shi, dole Hassan ne ya ce" Kin ce ko bamu abu aka yi kar mu ci sai mun nuna maki, kin ce mu daina amsa bale idaan muka ga abu ko na waye kin ce kar mu yarda mu taba ko mu dandana , ba kyau, daukan abinda ba naka ba babu kyai, sata ne, sata kuwa kin ce haramun ne" A sanyaye Amina ta ce" Ba nice nace haramun bane Fadeel, Allah ne ya haramta sata, du wanda ya yi sata a hukuncin adinin musulunci ance a datse gundugwuilar hannunsa, " " Wayo Allahna hannuna, Mama walahi ni ba sata na yi ba, dauka na yi nace zaki biya shine na ji ina kwadayin abin na bude na diba kadan" Husain ya fada a raunane yana shirin kuma barke mata da kuka , abinka da wanda ya aikata laifin Ajiyar zuciya ta dauke tana fuskantarsa ta ce" Farid babu kyau, haramun ne, Allah ya haramta, ko me kake so a duniya ka fada min, in dai bai fi karfina ba in sha Allah zan yi maka shi, ka ji?" Kai yake gyadawa da sauri, hakama dan uwansa, Sai da ta tabatar sun gane fushinta a kan wannan lamari, sannan ta dawo nasiha a tausashe sai kuma ta saka suka yi salar isha'i suka kwonta Kamar yadda ta saba tunda ta salaci sallar asuba ta dora kaskon tuyarta a tsakar gidan ta shiga aikinta da murhu biyu da itace ba da gaz ba Safiya na yi aka ringa buga mata gidan daidai ta taso biyu ta sakasu yin wanka d shiryawa Zuwa ta yi ta tambayo waye, kafin ta bude Da fara'a suka gaisa ta yi baya ta bata hanya ta shigo hannunta rike da Saudat da ko ido bata wanke mata ba Kujera yar tsuguno ta mika mata tana mata murmushi ta koma ta ci gaba da toya wainar matar Mai shanu domin ta gama tashi tuni ta zuba a kwanon nan ta kilace Murmushi Innar Sauda ta yi tana fadin" Oh Amina ke kam jinninki ya hadu da mai gidan abanku, bayan kasa ta birni idoma bai yada ke ba, da ba dan Baba Mai shanu ya tsufa sosai ba ai da aurenki ya yi ya cencaneki sosai, ama yanzun idanma ya aureki anya zai iya da ke?" Amina ta dan katse zuba kulin ta kalleta da dan mamaki, sai kuma ta yi murmushi bata ce da ita kanzil ba ta ci gaba da zuba kulin wainar Haushi ne ya kamata a ranta tana ayana ' shegiya mai shegen taurin kan tsiya, maganarma ba zata yi min ba dan bakin hali!' Murmushi ta yi a bayane ta ce" Um, maza? Maza? Kin ga tunda na gama sallah na zo na tsaya nake jira ki gama ki bude dan na shigo na amshi wainar naj sadaka na ba yar nan, ki duba ki ga abanta a jiya naira ashirin daya da ya banu tun safe bai kuma waiwayarmu ba, wannan lamari na maza da me ya yi kama? Namiji ba kama gida, ba fara'a idan ya shigo gida bamu isa mu yi wata walwalar ba sai idan ya fice, shi kulun a babu yake, ko so yake na je wani wajen na samo mana ne?" Amina ta zuba masu wainar isashiya ta miko mata harda miyar da ta sha kayan hadi na gargajiya sai kanshi take a hankali ta ce" Allah shi kyauta" Maman sauda ta amsa tana ajiyewa gabansu da yin godiya ta ce" Ke kika san Allah shi kyauta, wai shine harda yin budurwa a cen bayan layi, ai nace ba damuwa ta kula shi idan har ya kawota sai mu ci idonmu baki daya" Amina ta yi murmushi tana idasa zubawa a kwanon Matar mai shanu ta kilace shima sannan ta zauna tana gadin miyar har ta daidaita ta zuba masu isashiya a dayan kwanon ta hade komai a cikin kwondon da take mika masu ta zubawa biyu suka zauna sunna karyawa sannan ta shige wanka Da ta fito ta shige ciki ta cenza tufafinta cikin shigar riga da sket na atampa ta zurmuka katon hijab dinta mai ruwan kasa har kasa mai hannuwa ta daka dan kwali sannan ta dake fitowa jin ana salama Ummu salma ce ta zo tambayar gyaran amarya , nan suka yi magana suka gama ta tafi harda bada rabin kudin Innar sauda kam kallonta kawai take yi, gata dai baka ce ita ama ko ita ta fita kyan gani, ita da kanta tana matukar kaunar kalar fatar Amina, ga shegen nutsuwa da dan uban miskilanci du yadda ka so ka daki cikinta ba zaka samu abin fada ba sai dai ka gaji ka hakura, Tare suka fito daga gidan na Amina ta rufe komai suka yi gaba neman abin hawan da zai mikasu gidan mai Shanu, da kallo ta raka su har suka bacewa ganninta, Tsaki ta ja a fili a ranta kuwa tana ayana' Yarinya karama ba miji ba komai aman ta gaje komai na anguwa, idan gyaran jiki ne ita, kitso ita, komai ita, kowa mutunci yake da ita! To walahi baki isa ki shiga gidana ba ki hanna min zaman lafiya da kwonciyar hankali da rawar gaban hantsi a gidana!' A hankali ta mikawa mai adaidaitar kudinsa tana kallon kofar baban get din da aka wangale ba'a rufe ba A nutse suke tafe yarenta na rike da wasu kayan itama tana rike da wasu suka wuce baban get din sula gaisa sosai da mai gadi sannan suka dauki bangaren Baba Mai Shanu Wani irin ja ta yi ta tsaya a lokacin da idannuwanta suka sauka a fuskar yaron nan na jiya wanda aka wulakantata a kampaninsa ta kai kara ya mayar da ita yar iska dan rainin wayo ya fito daga cikin wata galeliyar mota ya ja ya tsaya yaba karewa gidan kallo jikinsa sanye da dakakiyar shada ruwan sararin samaniya sai haska ido take fuskarsa daure yana kallon wani gayen dake masa hira yana ta nunawa yana dariya ama shi sai binsa da kallon nan na raini yake yi baya bashi amsa Mutuwar tsayen da ta yi na yan sekwani ne da sauri ta juya da nufin komawa Husain ya kalleta ya ce" Mama ina zamu je?" Daburcewa ta so yi sai kuma ta juyo gannin Baba direba ya taho da dan sauri hannunsa rike da wata jaka ya wuce su fuuuuuuuu yana sauri gaisuwarma sama sama ya iya yi mata ita A hankali ta ce" Baba ko dai yau Baban baya nan?" Baba direba ya ce" Yana nan yana ciki fa, jikansa ne ya zo yau ai ba kanta ki taho mana" "JIKANSA?" ta furta a saman lebenta, ta taho? Ta sake tambayar kanta, Abinsa ya faru a jiya ya dawo mata sak sak , irin abinda ya faru ya dawo mata, kwarai riketa da kokowar da take yi a kan idannuwansa ya koma ta kuma bishi ta dora daga inda ta tsaya A hankali ta rike kwondon da kyau a lokacin da ta ga ya juyo barin fa suke da nufin shigewa ciki Dan kallon second daya takk ya maka masu mai shige da harara ya dauke kansa ya shiga tatakawa ya shige ciki Da ido ta raka shi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce" πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ _*NI ZAN LADABI*_ πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* *Page 0️⃣5️⃣* Da ido ta raka shi, kasa kasa ta ja tsakin jin haushi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce " Kumu je mu ba Saliss gayacen ya kai sakon Baba, yau bakine da shi ba zamu shiga mu dame shi ba" Gaba daya yaren basu so hakan ba, bama kamar Hasan, du miskilamcinsa da rashin son mutanensa sunna shiri sosai da Baba, koda yake baban ne datijo mai datako da iya mu'amalantar mutane kala daban daban, yakan zauna da Hasan ne da irin mood din da ya zo masa, idan yan hirar ne su taba kadan ana nasarwa, idan yan a zauna a kalli junnan ne sao su wuni a haka bai ce masa ufan ba, to shi da ya zauna da jikansama suka yi zaman lafiya bale hasan jariri, ga dai jikan nasa a yanzu ya kawo mizalin da ya dace ace ya ajiye iyali shima ya yi nasa gidan da mace zata dora tukunya ta masa sannu da zuwa idan ya dawo daga nema, ama sai gidan ba macen a ciki, shi gana dayama tale takensu da kakarsa ba wani dada yardarsa da kasa suka yi ba, ya dai zuba ido ne yana kallonsu Gaba daya sakon ta ba daya daga cikin yaren dake aiki a gidan wato Saliss suka yi tafiyarsu tare da yaren Salis ya nufi baban falon Mai Shanu ya yi salama sannan ya ja ya tsaya daga kofa, domin ya san yau madame na wajen ba zai so ya shige kansa tsaye ba ya samu matsala Mai Shanu dake zaune cikin sasaukar shiga ta hausa , lalausan yadi kansa sanye da hula ya sake waigowa kofar yana fadin" An amsa salama malan Salisu ka ja ka tsaya ka shigo mana?" Salis ya daga labule ya shiga da salama a bakinsa a karro na biyu ya karasa direcy gaban Mai Shanu yana kokarin dukawa da kayan dan ajiyewa wata murya mai cike da nutsuwa, furuci kasa kasa sosai, cike da cikaken aji da wayewa ta furta" Ka kai dining mana kar ka ajiye a nan" Mai Shanu ya dubeta sai kuma ya kalli Salis ya ce" Aa ya ajiye min a nan, wannan kamar kanshin Wainar maman biyu?" Salis ya ajiye din kansa a kasa sosai ya karra nutsuwa ya ce" Eh itace ta ajiye ta koma tace zata mika biyu makaranta ne" Dan jim ya yi sai kuma ya gyada kansa yana furta" ALLAH ya anfana, ya saka da alkhairi, ya yi mata albarka" Salis ya ringa amsawa sannan ya mike ya tafi Bayan fitarsa da kamar minti biyar Hajia ta kuma dagowa ta kalli mijinta a karro na hudu tun bayan maganar da ta yi ya take ko kallo bata ishe shi ba, ya wani kama yiwa yarinyar dake aikata aikin nan da kudin da yake tura mata godiya kamar wace ke ciyar da shi sadaka! Kanta ta cire ta maida kan Jikanta, abin kaunarta , farin cikin zuciyarta , abin alfaharinta taba cire gilas din karin ganninta hadi da ajiye jaridar hannunta ta ce" Cencenta ce ke nemanka ido rufe , ba kai bane ke nemanta *ABDUL RA'UF!*" Sau daya ya dago daga rubutun da yake yi a wani litafi ya sauke dubansa a kanta, sai kuma ya dauke dubansa ya maida cikin litafin ya sake dasa alkalaminsa ya

Chapter 3 of 9