Share this page
8 / 9
da fadin" Wannan lamari na damuna Malan, yarinyar nan tana da bukatar taimako sosai, da ace zata samu da hankalinta zai fi kwonciya, ga rainon ya'ya bayan ita dinma yarinya ce" Malan dan iya da kansa ke sade yana sauraronsu har Mai Shanu ya gama maganar yana ta dannar harshensa da irin magangannun da yake tufka masa mararsa dadi a zuciyarsa, yana kwabar kansa cewa ya bi a hankali dan ya ci ribar zaman ya fuslanci mai Dambu a yannayin da yake tunanin maganarsa mai ma'ana ce ya ce" Haka ne, Allah gafarta malan da Elhaji gaba daya na ji maganar nan, kuma idan na fahimta da kyau so kuke ta dawo gidan nan ta zauna?" πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ _*NI ZAN LADABI*_ πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* *Page 1️⃣1️⃣* Furucinsa, har zuwa kafiyarsa da yannayinsa, da suturar dake jikinsa , kai harta da kalar fatar jikinsa sai da ta shiga aunawa da idan yana cikin hayacinsa, a hankali da mugun kula ta karra dubansa kasa kasa sosai ta ce" NA'AM?" dukkan yannayinta yana kula, yana kuma hankalta, murmushi ya yi mata wanda ke tabatar mata da kwarai abinda ta ji shi yake nufi, ba gizo kunnenta ke yi mata ba, ba kuma a cikin hali na fitar hayaci ya yi bayani ba Da sauri ta saka hannayenta ta dauke farantin dake ajiye a gabanta ta kawar gefe ta zauna tana tataro dukan nutsuwarta da hankalinta ta ce" Alkali, wasa kake yi da furucin nan ama ko? Ka kuwa ji me ka fada? My big son , My hero, Uban gidan yan siyasa! Uban gidan masu mulkin! Dan yanada baban kowa a banki, shine zaka dauko auren fari kace zaka hada da macen da ta girme shi, macen da ta gama yawonta, macen dake fama da ya'ya, macen da bata waye ba, macen da take tuyar waina da kosai tana siyarwa, macen da bakin fatarta sai ya makanta mutun idan ya matsawa kallonta? Plz ka fada min cewa wasa kake yi da furucinka!" Mamakin abinda bai taba kawowa kansa cewa zai ji daga bakinta bane ya saka shi dora yan yatsunsa biyu saman lebensa, kwana uku da suka shige wanda ya yi maganar nan ya yi masa uzuri ya ajiye shi a matsayin wanda bai yi dogon karatu ba, yana fama da jahilci ya da ya yi aikin dana sani, a yanzu kuwa a wani bigiri zai ajiye iyalinsa? Shi dai sheda ne a kan irin karatun da matar gidansa ta yi, na bokon da na islamiya, shin jahilci shine sani a take sanin ko kuwa wannan din son kai zai kire shi da shi? Turw komai ya yi daga cikin zuciyarsa ya ce" Shin haramun ne aikata hakan?" Hajia kam abinda nema yake yi ya girmami tunaninta, har so yake ya ji idan haramun ne? Kennan so yake yi ya zauna a kan bakansa? Dan kwalin kanta ta cire ta ajiye gefe , lalausan gashin kanta mai dauke da furfura ya bayana a tufke a bayan keyarta da dan karamin ribom ta ce" Ba maganar haramun, shin ina hadi a nan? Idan miji kake son yi mata ka sama mata daya daga cikin ma'aikatan gidan nan mana, in ka raina su ka duba cikin ma'aikatan ka masu takardar gwamnati ka bata mana, ama sai ka dauko jirgi ka hada da mota? Ai ya fi karfinta walahi! Ita kuma ta girme masa a shekaru ai hadin sam bai yi ba, a cenza shi!" Kai ya gyada yana murmushi da tunanin lalle ya yi sake katon raini ya riga ya shiga tsakaninsa da iyalinsa, yana wanzar da rayuwar yanci da ita da shawara a dukkan abinda ya taso masu dan yana girmamata da darajata a rayuwa domin shi a ganninsa mace tana da damar zabi itama a tata rayuwar ba wai sai dai a ringa yanke mata hukunci da an yi niya ba, sai gashi tana neman maida hakan iko da isarta? Tana so ta manta yana raye kuma bai shirufce ba? Tana son take komai ta murje komai ta manta nata usulin?, Koda yake tana iya mantawa, domin halin rashin na dan lokaci ne suka yi kafin Allah ya warware, sai dai zai ji mamaki ainun idan ta ci gaba da nunawa talaka haka , takan manta Allah ya haliceta da ita da wanda bashi da shi, yana iya amshe dukkan abinda take gannin ta malaka ciki jarda jikan nata a lokaci daya kuma ya barta da ranta da hankalinta ta gani da idannuwanta? Kai Allah ya wadaran naka ya lalace! A tausashensa ya ce" To tunda dai ba haram bane ai an wuce wajen, nima da na aureki ai tserayar shekarun dake tsakaninmu nu har kunya na ringa ji a lokacin kar ace na auri yar cikina, gamu kuwa an yi tsayin rai du kanmu ya cika da furfura muna tare, wannanma ai aya ce Hauwau" "Alkali" Hajia ta fada tana tsareshi da manyan idannuwanta gannin ya mike tsaye yana shirin yin gaba ya bar mata dakinsa da itace ta tardo shi Juyowa ya yi fuskarsa a hade sosai ya ce" Look, ki saurara abinda kike shirin yi ko menene! Ki tausasa muryarki a kan tawa, ki saurareni da kunnen basira, Ni Alkali na ce na yanke hukunci Daura auren jikana da Maman Biyu nan da kwana hudu, na baki dama idan kina gagawar a hade da wace yaron ke kulawa matsayin soyaya ba damuwa, idan baki gagawa kuwa lokacin da kila shirya sai a daura masa ita, shi din ai mijin mace hudu ne a sanina, so bana son yawan surutu a kan lamarin nan, kuma na hanneki tarda yarinyar nan da wata maganar da zata zubar da mutuncinki a idaannuwanta, ki sani ya zama wajibi *KI YI MIN LADABIHHHH* , Idan ba haka ba lalle zamu bar abin kunya mai girma a duniya kafin kasa ta birni idannuwanmu!" Yana gama fada ya fice ya rufe dakin ya sauka kasa Hajia kam sai da ta yi summan hucin gadi kafin ta zabura tana sallalami da dora hannunta a saman kanta tana fadain" Walahi talahi ba zai yiwu ba, ni zaka wulakanta? Walahi ba zai yiwu ba, in ni ka fi karfina ai akoy masu yi maka magana, haka kawai dan tsufa ya zo maka sai ka hada yaro da abinda ba shikenan ba? Wani irin zaman aure ne zai iya yi da yarinyar nan? Ko hannunta zai iya tabawa ne? Kuma walahi ba za'a daura auren yar gidan honorable da gagawar nan ba, ni da nake shirya wannan rana ta yadda zan gayaci manyan yan siyasa su zo mu hadu a kashe koren arziki? Ba zaka taba sakani a jarida da yamadidin abin kunya ba, sauran titin zaka ba yarona? Haka kawai marayan Allah zaka wulakanta? Ba zai yiwu ba!" Tana fadan ne kuka na neman kubce mata tana dadana numbobi ABDUL RA'UF din ta fara kira, har sau biyu kafin ya kashe ya maido mata kiran Tana dagawa kuka ta fashe masa da shi tana fadin " ABDUL ko me kake yi ka zo gidan nan a yau yau, walahi Alkali ba zai kasheni ba, walahi ba zai kashe ni ba, bai isa ba, *Ba zan yi masa ladabin ba!*, A kan wannan bukatar tasa ba zan taba sada kaina kasa ba!" Du yadda ya so ya fahimci abinda ya hada su a yau kuma ya kasa, takan yi kiransa da korafin kakan nasa ya yi mata kaza ita kuma ta rama da kaza, ya yi mata nasiha ya hannata maimaitawa, ama bata taba kiransa tana rusa kukan nan haka kamar zata mutu ba, kuma kukan ba wai na wasa bane , irin yadda take yinsa zaka gane daga cen zuciyarta abin ke fita Hankalinsa ne ya yi mugun tashi, ya tabata ko kudi take so ya hannata, ko ya hannata yawon siyasa, a tunaninsa wadinnan ne kawai damuwar da zata rikita Matar Alkali, shi kam yaya zai yi da tsofafin nan ne fisabililahi? Sam basa girma, kulun cikin rikici suke, kuma shine a tsakiya, tsoronsa daya kar ciwon hawan jininta ya tashi, to wai inama shi Mai Shanun yake ya barta tana kukan nan haka? Ko menene ai sai ya rarasheta ya yi hakuri tunda ya fita girma kuma shine namijin ko? Kiran wayar Mai SHANU yake yi ba'a dagawa, ya shiga kiran yaronsa da fada masa maza ya sama masa waje a jirgin da zai juya gida, nanma aka sheda masa a yau dai sai jirgin yawo wanda a kadan zai iya kwasar awani ashirin bai je gidan ba, domin kasa kasa zasu sauka , baban jirgin Ethiopia ne, ya gwamace ya yi hakurin jirgin karfe bakwai din kawai da wahalar nan Sake kiran numberta ya yi ya sameta tana cikin waya Kansa ya girgiza ya jefar da wayar yana adu'ar samun saukin rigimar nan tasu, sunna daga masa hankali, sani ne basu yi ba, bashida damuwar da ta wuce tasu a duniya, yau ko rikicin neman kudi baya daukan hankalinsa irin wannan, shi fa samun kansa ya yi dumu dumu a cikin nema, kuma ya san da kudi da babu rayuwa zai yi normal, ama wadinan biyun da suka rage masa a cikin makusantansaa mafi kusanci da shi sunna taba kwonciyar hankalinsa Jin kukan wayarsa har gagawa ya yi ya dauko, a tunaninsa daya ne cikinsu, sai dai yana dubawa ya ga budurwarsa ce, wace bata san ya yi tafia ba, ya tabata ta samu labarin inda ya zo da numbersa ta nan din ne a wajen Hajia domin bai yi kiranta ba, fushi yake yi da ita, ya rasa rashin sannin ciwon kan nan nata da me ya yi kama, ba zata gane ba, shi fa baya son wulakantar da kai, ita ta dage wai ita yar kasuwa dole sai ta bude saloon? Tace aikin gwamnati yace sai dai ya dauketa aiki ta kiya, yanzu tace saloon ya nuna aa ta je ta bude, shi fa ba zai fita nema ba iyalinsa ta fita nema, idan karatun ne ba zai hannata ba, ta yi har ta ga makirkirin bokon, ama kuma ta yi zamanta, walahi ta fi karfin bautawa wani, kuma ta fi karfin wulakanta kanta a titi kulun tana yawo tana kama gashin wannan tana cudanya da karti wai ita mai saloon!, Yayan bankin yanzu haka na bankinta karamar mai kudi ce ita, idan sun mata kadan ya sake jibgawa, bahi da damuwa da hakan, ba kudin ne damuwarsa ba, a zauna masa a gida *A yi masa ladabi* sannan a tarairaye shi shine damuwarsa, a yadda ya jima da lamari mai girma rike da arzuzumin wandonsa ai dole ya bude filin sukuwa a gidansa ta kowani lungu da sako!, Ama shine dan raini yarinya karama ta ki bin umarninsa? No shi ba zai yarda da raini ba walahi! ( To fah, llale akwoy gwarama, to mu da muka saba da neman na kanmu fa? Ka zo da izala yaro!) Kafin yama ta yi tuni gidan Mai Shanu ya dauki haramar baki, na nesa da na kusa, duk wani wanda Hajia Hauwau ta dan yana jin kunyarsa ko nauyinsa ko sunna abotakata ta kud da kud sai da ta yi kiransa ta dora masa kukan mutuwa da fadin zai sakata a uku ya tona mata asiri, ciki harda Ɗan zumunsa, yaron da yale rayuwa a waje tare da iyalinsa, wanda a kusa kusan nan shine daya kwal yake laluba ya ji sanyi, dangi ne su mararsa yawa dama, sai ga lamari na dauki daidaya, sai ko taron dangin dake nesa sosai wa'inda sai a yi shekaru ba'a ga junna ba, kowa ya labe da iyalinsa yana toyawa yana kwashe abinda zai fishe shi, yau ta gigibo masu iya tasowa a ranar ta kawo su, wa'inda kuwa basa iya zuwa a ranar sun shiga shirye shiryen zuwa, domin ko ba zumuncin haduwa da junna , akoy na waya da kuma hannun Mai Shanu da na jikansa dake samun kowanensu, idan har da gaske ne Mai Shanun zai dauko ruwan dafa kansa kamar yadda Hajia ta fada za'a hafu a yi masa nasiha sannan a fadawa Allah ya kade lamarin, domin babu wanda ya isa ya yi masa dole, sai dai rarashin Tunda Mai Shanu ya fuskanci abinda yake faruwa ya yi murmushi ya kada kansa ya sa Direbansa dauko biyu suka wuce suka bar gidan Bayan sun tafi gidan gonar ABDUL RA'UF Baba Mau Shanu ya saka aka je aka dauki Baba Lauratu aka bata waya suka yi magana, dan haka aka wuce da ita gidansa kamar yadda ya umarta cewa a kaita direct dakin da Amina ta mayar da kanta yar kuryar daki a zo masa da ita Hakan ce ta faru, domin har suka fice a gidan Hajia Hauwau bata sani ba, rana sama kawayenta na danarta da rarashinta da nuna mata cewa lalle hadin naj sam ba zai haifar da alkhairi ba, ai bambancin shekarun ya fi komai daga hankali ga kauyanci, ba zai taba yiwuwa ba matar Gwamna ta kasance a haka ( uhum, su gwamna manya), idan aka yarda aka aurawa Honorable mace irin haka ai za'a samu matsala wajen zabe, ba matar gabam mota bace sam! Dole a cenza ra'ayin mai Shanu, wannan ke daga mata hankali, mijinta mutun ne mai masifar sanyi, a cikin sanyin nasa yake tafka maka abinda zai hadaka da juwa, ko a yanzu irin yadda ake buga masa waya baya dagawa ta tabata yana kallo, baban burinta shine a sakashi a tsakiya a tankwasa shi, idan ya daura auren nan mutuwa zata yi! Kai ama Allah ya tsinewa wata jarabar walahi, tana zaman zamanta, ita ta san tunda ta ki jinnin taren nan ta Mai Shanu da yarinyar nan da walakin goro a miya Takalmin dake kafarta slipars ne, hijabin dake jikinta baki ne sidik mai hannu, sannan ya kai mata har kasa tamkar zai kwasheta ya kifar, sai dai cizawar bakinsa ya sa fatarta haskawa ya zamto duhun fatar tata ya ragu sosai, danma ta yiwa kanta tanadin gyara ne idan ta tashi yin aure, da kalar fatarta mai hasken duhu ce sosai Manyan idannuwanta take karra zubawa a kan Hasan dake kyakyata dariya yana bin bayan Husaini da gudu, sakewar yaron a yanzu na bata mamaki, sosai yake sakewa yanzun bayan shi din mutun ne marar dariya a da, ko a yanzun ba wai cencen bane, ama da sauki sosai da sosai Suturar dake jikinsu ke karra shiga zuciyarta, yau bama ita ta shirya su ba, kuma sun je makaranta tana barcin asarar da ta aura, sai yanzu ta ga shirinsu, masha Allah sai haskawa suke yi cikin shigar gajerun wandunna daidai gwuiwa masu tauri watau gins daya blue, daya baΖ™i, sun ciza sosai da rigunnansu masu kyau masu dogwayan hannuwa, sai takalma kito kafa ciki blue da baki, masha Allah twins dinta har wata sabuwar kaunarsu ke karra bin sasan jikinta, saima idan sun juyo sun kirayeta da Mama, a zaune a wajen nan da take kamar ta yi ta taka rawa, ita kam wani kwonciyar hankali da jin dadi zata nema sama da wannan? Baba Lauratu da ta samu kebewa gefe da Baba tunda suka zo suka tatauna ce ta fito, fuskar nan tata kamar gonar auduga ta ce da Amina" πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ _*NI ZAN LADABI*_ πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* *Page 1️⃣2️⃣* *Asalamu alaikum wa rahamatullah, karshen FREE page kennan yan uwaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°, na gode* Fuskar nan tata kamar gonar auduga ta ce da Amina" Tashi maza ki je Mai Shanu na son magana da ke, Uman Mijin ki sani Mai shanu uba yake a wajen marigayi, Allah ya jikansa ya sa yana cikin rahamar ubangiji shi din mai biyaya ne a gareshi, bale marigayiya, ba zan taba tuna lokacin da na ga rashin kyautawa a tsakaninta da matar Mai Shanu ba du irin baudadan hali irin nata!, Dan haka ki je, ki yi kokarin yi masa biyaya, ko ba komai yanci yake kokarin kwata maki da rufa maki asiri, kasa zai tara maki ba wulakanci ba" Ita dai a tsaye take tana dauraron Baba har ta gama maganarta, haka kawai sai ta ji fargabarta na neman karuwa a kan tunanin abinda ya da suka zo nan, tana jin dadin yannayin wajen sosai, ama jiki sukuku ta karasa ta karra dukawa tana sake gaishe shi Mai Shanu yana murmushi ya ce" Uman biyu rabonki da ki min waina tun ta ranar juma'a, yanzun kikan ki yi min wainarma , bayan ni din ina son waina sosai" Murmushi take yi kasa kasa ta ce" A yi hakuri baba zan yi mai yawa , har sai kace ka koshi " Shima dariyar ya yi yana sake gyara zamansa ya ce" Yauwa, dangane da maganar wajen uncle dinki ne, yau kwaba uku kennan da na je na same shi ni da Malan Liman " Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a hankali ta kai zaune zuciyarta na saka mata abubuwa kala daban daban, baban fargabarta kardai yayan mahaifin nata ya yarda ta koma gidansa, shin yaya makomar rayuwar biyu? Tsoro da fargaba irin ta uwa ke darsuwa a zuciyarta, tunaninta ya kafe ya tsaya a kan murmushi da dariyarsu da ta barsu sunna yi yanzu, idanfa ta koma kuka a gobe? Baba Mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya bayan ya hada abunda ya dace ta sani, ko ba komai ba zai saki baki ya yi ta yi mata bayanin abinda babanta ya fada ba, koda tana yarinya ba zata taba jin dadi ba, sam bai ga anfanin aikata hakan ba Dan haka ya ce" Sharadinsa daya ne tak a kan maganar zamanki a wani wajen, shine ya kasance kuna daure da auren wani a kanki , ki tare a dakin mutumen" Yanzun kam da sauri ta dago ta kalli Baba, dara daran idannuwanta masu dogayen gashin ido take ta kiftawa tana kallon Baba, sai kuma ta sake sada kanta Baba na hankalce da dukkan yannayinta ya ce" Harma ya bamu adadin kwanakin da ya diba bisa adalcinsa cewa nan da sati daya tak, watau nan da kwana hudu, Amina idan baki manta ba na yi ramtsuwar cewa ba zaki koma gidan nan ba, ban sani ba ko ni zan yi ta yin azumin kafara? Ko kina da tsayaye ne?" "Tsayaye?" Ta fada a hankali still tana kikifta ido tana kallon Baba Baba ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa tsayaye, wanda kika tsayar a matsayin mijin da zaki aura, wanda ke zuwa wajenki kika ji kin aminta da son aurensa" Gaba daya sai ta afka a duniyar tunani, Aure? Ita? Nan da kwana hudu? Mutanen da suke tsayen da alamun sunna sonta biyu ta sani a duniya, Aban saudat da kuma Muktar, su din nan su ra sani a sanninta, sai dai bata karasa tunanin nan ba baba ya ce" Lauratu ta min maganar manema aurenki biyu, tun a washe garin da rigimar nan ta faru, Malan Liman ne da kansa ya tuntube su, su dukansu sunna da ra'ayin hakan, sai dai shi daya lokaci ya kure masa duda an nuna ba yanzu tarewa ba, dayan kuwa mahaifiyarsa ce ta yi karan tsaye kan lamarin, bayansu akoy wani ne?" Yanzun kam da hannayenta take dan watsawa, naman gaban goshinta na cakudewa a birkice ta ce" Aa, dama, dama su kadai ne suka ce, suka ce zasu aureni koda da biyuna, suka ce sunna son biyu, bayansu babu kowa" Dan murmushi ya subucewa baba, domin ko a yanzu baba cewa ta yi ba sai ya ji ra'ayin ko tana da wani ba kawai abinda ya yanke a zartar, shine yace da ita lalalala, ko daya ba zai so ace tana son wani ya katse hakan ba, ya fi so ace bata son kowa idan ya so su shirya kansu a gidansu A tausashe ya dubeta ya ce " Amina, idan babu, shin kin yarda ni na zaba maki miji, mai nagarta, wanda zai kula da maraicinki, ya rike yan biyunki, da ke kanki? Ina nufin zaki amince ki yi min biyaya kuwa? Idan har bakya jin zaki iya yin hakan ba zan ga laifinki ba, zan je na fara daukan azumin rantsuwar tun gobe, na san zan jure, ulcern tawa ai zata yi hakuri na yi ibada kar tsoho ya mutu ya je da bashi a kansa" Idannuwanta da suka cika da kwallah ta zuba masa, nazartarsa take yi , karara ta ga lalle da gaske yake, magangannun Baba suka fado zuciyarta, tsoro da fargaba suka shigeta, ta yi shiru ta rasa amsar badawa, hankalinta ya ringa neman karra tashi har sai da Baban ya kuma budar bakinsa a sanyaye ya ce" Amina, shin zaki iya yi min biyaya kuwa?" So take ta tambaye shi waye zai zaba mata? Ko baba direba ne? Ko mai ba shukoki ruwa ne? Ko Usman dan albarka ne? So take ta ji ko wanene, ama girman kunya irin ta cikakiyar budurwa ya danne curiosity dinta, kanta na kallon kasa a hankali ta daga kanta, sai kuma ta bude muryarta bakinta na rawa ta ce" Baba, zai, zai kular min da biyu? Kar kar ya min irin na mijin mamansu, kar sai ka daura auren yace ba zai rike yayan wani ba" Tausayinta zallah ya kama baba, ya kuma yi mata murmushi ya ce" Bari ki ji, bi izinillah zai rike biyu, ke da da hali harta tarkardunsu sai sun koma da sunnansa a kai, ni nan bani da haufi a kan haka, burina dama ki amince, domin na yanke hukuncin a gobe da yama zan daura aurenki bisa wasu abubuwa da suka bilo da take dokata da wace nake tunanin na isa da ita ta yi, ta manta cewa itace a

Chapter 8 of 9