Share this page
7 / 9
Idan ya so ni zan dawo maka nan da kaina da maganar aurenta, domin nima alkawari na daukarwa kaina ta gama zama a gidan nan ita kadai!" Dan iya kallon Baba mai Shanu yake yi, so yake ya kara kafewa ya kara zilewa, sai dai gaba daya mutumen yanzu da ya zo masa a tausashe sai ya kasa yi masa musu Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ai ka isa da ni Elhaji, ba damuwa tana iya daukar har sati daya ta huta din, duda na san karya ne bata da wata damuwa, ama bayan nan idan bata samu mijin ba ta tatara ta koma rayuwar ta da, ba zata hanna kowa zaman lafiya da gidansa ba" Malan Liman gyada kai yake yi yana karra kallon mutumen, Baba Mai Shanu kuwa harda godiya da nunin ya gode da akai masa wannan alfarmar Ai kam kamar ya sani, alkhairin aka yi masa mai tsoka, yan dubu dubu sababi dal kafin su tafi, sunna daukan hanya shima ya dauki tasa hanyar ya nufi kasuwa dan ya yi sare sare, ba zai yarda ba matarsa ta ga kudin nan ta rabashi da su da jarabar lalurar yara! Mai Shanu ya jima a wajen su Malan Liman sunna tatauna maganar nan, karshe suka rabu bisa shawara daya tak, wace ta yiwa Malan liman dadi har cikin zuciyarsa, ya kuma dauki alkawarin daukan kwana uku yana fadawa Allaj da sake neman zabin Allah a kan lamarin Koda ya koma gida wajen hutunsa ya je ya dauki alkur'aninsa ya shiga tilawa, dan sosai zuciyarsa ta tabu da wannan lamari, hankalinsa ya tashi sosai da wannan abu, tausayin kansa ke lulube shi, da tunanin abinda dan Adam ya zama Baima koma saman hajia baba ba, bai sani ba dan rikewar kafar nan harda su docter ya zo ya dubata tana ta zubawa jikan shagwaba a waya ya mata alkawarin zuwa ya dubata shima, danma tafia ce ta fado masa wace dole shi da kansa zai je, a kan maganar taki ce da yake son buda kampaninsa na kansa dan ya fara fitar da takinsa yana siyarwa sannan yana anfana shima waa kansa Sarai Baba ya lura maganar da ya mata kan ta ja yarinyar a jiki bata yi, hasalima tunda ta yi wunin dayaa bata fita ba a na biyin shi da kansa da ya sauko bai sameta a gidan ba, Bai nuna damuwarsa ba ya kama hannun biyu suka wuce da kansa ya masu rakiya makaranta sannan ya bada damar idan baba Lauratu ta zo a barta ta shigo wajen Amina dan ta fada cewar a jiyama ta zo bata samu shiga ba, da wannan Amina ta wuni tare da baba dake karra tausarta da nuna mata hakan ya fi mata alkhairi, kuma da ta ji baba ya mata shiru a kan tafiyarta gidan yayan mahaifinta itama ta yi shirun kawai, ta tabata zai waiwayeta ko me ya yanke, sosai ta yi mata nasiha cewa ta yiwa matar gidan biyaya, ko menene ta tabata idan har bata taka dokarta ba ba zata wulakantata ba, kuma fa ba laifi tana da dan mutunci fa, kawai sun kalubalanceta ne Ita dai dadin da ta ji na gannin Babar ne, sosai suka wuni sunna shan hirarsu har yama ta yi baba ta mata salama zata tafi, a nan ne ta roki alfarmar ta biya ta sanarwa Firdausi, tace mata ba sai tace zata zo ba dan ta san ba barinta mijinta zai yi ba, ta fada mata babu abinda ya sameta, zata zo da kanta daga ta samu sararin hakan A wannan ranarma idonta idon Hajia bai hadu ba, Hajiar fa tamkar babu mutun a gidan haka ta mayar da ita, bata damu da lekata ba, bata damu da ita ta lekota ta gaisheta ba, takan fita dan ta gaishetan ama bata taba cin sa'ar haduwa da ita ba, yaranta kuwa sun zama sai hange, to sai hange mana sukan tare da Baba sai dai ta ringa jiyo dariyarsu da guje gujensu, karshema wani gem ya sa aka kafa masu tafkeke ya sa ana koya masu idan suka fito daga karatun islamiya yana zauna yana shan dariyar saurin fushin Hasan da kuma saurin kulan Hisaini, kamaninsu daya ama halayarsu sun sha bamban sosai, irin nutsuwar da yake kara ji da shawarar da ya yanke a zuciyarsa ya sa yale karra shirin hakan a ransa Yau kwanansu uku cif a gidan, a irgensa yau saura kwana hudu cif maganarsa da Dan iya, haka kuma a dazu da asuba sun sake zantawa da Liman kam maganar adu'ar da ya saka shi yi, ya sake tabatar masa shi kam alkhairin abin kawai yake gani , duda kwarai ya san akoy kalubale sosai , ama ya tabata alkhairin zai fi rinjaya idan aka tsananta da addu'a Shi yasa ya shirya fara tarban bama baman da ya san zasu tunkaro shi, harma ya sa aka kai abincin karinsa dakinsa sannan ya aika gayatar matarsa dakin nasa dan su karya Cikin wani rantsatswn lesh mai ruwan ash Hajia ta shigo falon mijin nata na sama da salama a bakinta Tafia take yi da classs, harufan manyan mata na yi mata wasali a goshinta Daurin kalabinta na wayayiyar mace ce, AC kuwa ya kara kwontar mata da kalar fatarta A nutse ta gama serving dinsa abinci ta ajiye a gabansa cikin plate a ranta tana ayana' Allah ka sa na ji alkhairi, wannan hade fuska haka a wajen alkali ba lafia ba' Baba Mai Shanu kuwa bai taba abincin ba, abinda le cikinsa ya fi cin abincin mahimmanci a yanzu Dan haka ya fuskanceta a nutse bayan sun gaisa sosai da sosai ya ce" Hajia Hauwa, dangane da maganar Abdallah ce, na yi masa Mace, kuma ina son daura auren nan da kwana hudu bi'izinillah, idan ya so a hankali kya yi taron bikinkkkkkkkkkkkkkk" Kwarewar da ta yi da ruwan jus din da ta kai bakinta zata surba ya saka shi saurarawa yana kallonta Tari ta ringa yi a hankali tana dan fifita fuskarta har ta daidaita, sannan ta dube shi da idannuwanta da suka dan cenza launi domin ba taron gangan bane ta ce" Sorry Alkali, na kwaru ne, to ama yaushe aka tsaida maganar auren da gagawa haka? Jiyama fa mun hadu da Honorable din a wajen taron yaye yan makarantar bording da suka samu shiga Universityn Kasar Spanish" Baba Mai Shanu ya ce " Aya, Allah ya sanya alkhairi, ai bama da y'ar gidan Honarable Alhasan Kwongilar bace, wannan sai daga baya, idan luwa ya zama wajibi sai a hade, yanzun da *MAMAN BIYU* ne nale magana......." Kaka kara kaka, lamarin fa ba karami bsne, rigimar ba ta nan bace, wai cakwakiyar idan kin san ba zaki jura ba karki fara bi, wannan rigima ta ina zata bile? Ba ga mahadan ba , ba ga wa'inda za'a hadan ba..........Rigiji gabji Dankaro da gudu ki turo naki katin ko shedar transfer ki same ki tsundum a gidan NI ZAN LADABIHHHH, sai ki min ladabi ki bi alkalaminsa, domin nima ladabin nake yi masu dan su bani danar fahimtar *WA ZAI YI LADABIH* a kokowar! Barka da yau😌😍😍😍😍😍 πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ _*NI ZAN LADABI*_ πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°* *Page 0️⃣9️⃣* Bakinta na bari ta ce" Baba gida?" Carbin da yake ja ya hade ya daka a aljihun doguwar rigarsa fara sannan ya juya wajen da yaren suke ya masu nuni da su je mota gasunnan zuwa Juyawa suka yi suka nufi motar dan basa wasan musu da Baba A lokacin ya fuskanceta sosai ya ce" Eh gidana nake nufin ki wuce mu je mu ajiyeki, daga nan yau ba dai gobe ba zamu je mu samu dangin mahaifinki, yayansa daya daa na sani wanda da shi muka salaci gawar marigayi na masa magana a kanki, daga yau in sha Allah kin gama zama a gidan nan ke kadai, idan cen din suka ce zaki koma sai ki koma, idan gidan iyalinsa zaki koma sai ki koma, ama ba zai yiwu ki je gidan nan ke kadai ki yi rayuwa ba, zuwa yanzu na fahimci kin gane hatsarin hakan ya fi jin dadin gurbin da iyayenki suke zaune, ba zaki taba damun zaman lafiya ba mudin kina zaune ke kadai, babu wanda ya san mai zuwa maki gida da nufin cutarwa, idan na farko Allah ya kubutar da ke, na biyu Allah ya kubutar da ke, na uku ba'a san da wani shirin zai zo ba, idan ya barki a iya keta hadinki da sauki sauki, wa ya san ko yana fama da wata cutar? Idanfa Allah ya yi ke din mai kwai ce a kusa?, Wannan din gardame ce marar anfani, an riga an san ke kadai ce, Yaren nan ba zasu tare maki komai ba Amina, rayuwar y'a mace abin a bata kariya ce komai girmanta, yanzun shige mu wuce" Gaba daya tatareta suka yi suka hannata wani yinkurin bijirewa tafiyar, a hankali take tafe jikinta a mace tare da mugun tunani da tsoron abubuwa biyun dake shirin tunkaro rayuwarta Na farko gidajen yan uwan mahaifinta biyu ne kadai wa'inda suke shakikai a gareta, Kanninsa da yayansa Yan magana suka ce, abinda ya koro kura daga rami ta fada wuta ya fi wutar zafi Bayan rasuwar iyayensu babu gidan da basu gwada zama ba, suka gwamace zamansu su kadai daga ita sai yar uwarta A lokacin da suka zauna a gidan yayan mahaifinsu karen gidanma ya fi su daraja, babu abinda duka isa su raba , kasancewar gida ne na mata uku kowace da Ζ΄aΖ΄anta a gefe tana kalar nata ikon da kalar tata rayuwar, sai suka zamto kamar kishiyoyi ne na hudu aka zubo masu, abinci wannan basa samu sai ace ya yi kadan ne ba zai isa da su ba, abin takaicin yayan Aban nasu kuwa tunda ya nuna takardar gidansu yake so ya siyar ya raba masu gafo suka nuna basa so a siyar sunna so a barsu a kwana biyu , hasalima basa so a siyar da gidan a bara masu watarana wani sai ya shiga, gida dai nasu ne gadonsu ne mata suke, a yanzu idan suka siyar da shi sunna iya kade kudin ya zamto ba gurnon, ba kudin, idan halin rayuwa ya same su ina zasu je su zauna? To fa wannan lamari sai ya kular da shi, shi dai bai fito ya nuna ga dalili ba ama tun daga lokacin ya kawo ido ya zuba masu, in me za'a yi masu a gidan nan babu ruwansa, sau uku baban dansa na zane Firdausi tamkar zai kasheta da bulala da tatakawa da kutufo da komai, tun tana tunanin abu ne da zai wuce har ya gagara wucewar , aka zo aka yiwa Firdausi aure ko tsintsiya basu saka mata ba, a nan ta so siyar da gidan dan yi mata kayan daki mijin ya kiya yace aa shi zai yi mata, mafarin gabar family dinsa da Firdausin kennan, sam basa sonta basa kaunarta, gashi ana yin auren bai jima ba ya rasu suka tatarota suka watsar ta fito da cikin biyu Karshe dai zaman gidan yayan mahaifinsu gagararsu ya yi domin ga ciki ba zasu juri duka ba , suka koma gidan kannin mahaifinsu, wanda sai da suka gwamace kida da karatu, ashe tsohuwar gaba ke nanake a zuciyar bawan Allahn sanadiyar hanna shi auren dadiron matar da kowa ya san ba zama take yi ba, aurenta uku ana kamata da maza a gidajen, karshe dai ya bige da binta a haka aka aura masa itan suka zo suke zaune, har yanzun itace matarsa wace ta ja rantsuwar ba shi ba yayansa ko a kiyama! Ta kuwa hau ta zauna sai gasu sun fado gidansu, watau ta samu , sai da ta kai ido da ido matar nan ta nuna idan zaman lafiya suke so sai sun zama abokanan shashancinta, a ranar da kafafuwansu suka gudu , sanadiyar bak'ar wahalar ta saka Fido nakudar dole ta haihu a hannun Baba Lauratu, inda dangin mijinta suka bada abin yanka kawai suka nade hannayensu, ana gama sunna babu wanda ya kuma waiwayar yaren nan, su kuma sun daukarwa kansu alkawari zasu rike, Allah ya raya ya basu abinda zasu ciyar su shayar, su tufatar, su yiwa tarbiya! Tun daga lokacin ya zamto sai su kwashe wata daya ko biyu basu leka iyayen nasu ba, abinda ya sake yiwa Amina mugun tabo a zuciya shine haihuwar Fido ko a leke, suka barsu da kansu sai baiwar Allahn nake dake tare da su, dan auren Fido na biyu kiri kiri yayan mahaifinsu yace tafiya zai yi bashi da lokaci, aka ce a yi jiran dawowarsa sai a daura yace kawai limamin anguwar ya daura, wannan shine silar siya mata wulakanci a wajen mijinta, domin idan ya tashi gorinsa hadawa yake yi harda wannan Sai dayar damuwar itace Hajia, Walahi Amina na matukar tunanin zama da matar koda na awa daya ne bale na rayuwa tare da ita Ita dai ba zata ce ga ranar da wani abu marar dadi ya shiga tsakaaninsu ba, ama irin yadda ta san Hajiar da kyamar lamarin talaka tana tsoron zamantowa abar kyama a cikin gidan Tana tsoron kasancewa a karkashin Hajiar dan bata san wani irin zama zata yi a gidan ba, a kadan ta shekara uku tana yiwa Baba Mai Shanu waina tana kawo masa, ama maganar fatar baki bata hadata da matarsa bale godiya ko kamanta ta dan da zamanta, daidai da yin wainar shinkafa Baban ne yace da ita Hajia na son wainar shinkafa, ita kuma sai take yi dan kara girmama shi, ta fi tsoron zama da matar a cen kasan zuciyarta dan tana tsoron mutuncinta da son kare ratuwar Ζ΄aΖ΄anta Ama idan ta yi duba da abinda ke neman haye mata fa? Lalle da wata wahalar gwara wata Tana cikin tunanin nan suka karaso gidan Hankalinta du ba a jikinta yake ba ashe har Baba ya bada umarnin a kai su Malan Liman gida su kimtsa su karya zai zo zuwa karfe goma su wuce gidan iyayenta Sai da Hasan ya sake tba fuskarta ta dube shi a zabure , sai kuma ta shiga duban cikin gidan da datijan dake kallonta da tausayawa Malan Liman ya ce" Idan kin samu masauki, kafin ki kwonta ki tabatar kin rama sallar dake kanki , ki yi addu'a sannan ki kwontar da hankalinki, in sha Allah karshen fargabarki ta zo" Kai ta gyada a sanyaye sannan ta sauko ta shiga tafia a hankali Biyu na rike da gefe gefen hijabinta Baba ne a gaba, kadan kadan yana amsa gaisuwar daidaikun ma'aikatan dake aiyukansu na safe har suka shige falonsa A babar kujera ya mata umarnin zama sannan ya nufi sama cikin tafiyarsa a hankali na baban mutun mai shekaru irinsa A nutse ya tura kofar dakinta ya shiga da salama Hajia dake kwonce dan yanzu ta gama doguwar adu'ar da takan zauna ta yi bayan sallar asuba har sai rana ta fito sannan ta sake watsa ruwa ta kwonta dan so take ta fan huta kafin a jima wajen karfe goma ta fita cen wajen taron da suke yi yau dan ba mata masu fama da yoyon fitsari talafi da sunnan kungiyarsu A hankali ta dago tana kallon mijin nata Annurin musulunci daban yake, shi annurin musulunci tausasashe ne, ni'imarsa kuwa bata da iyaka, wannan bawa mai yawan sallah da nafila da ambaton Allah ya fi mata kowani namiji kyan kallo a duniya, annurin dake fita a murmushinsa kuwa ya fi mata komai dadina zuciya, gashi dai ya tsufa, fuskarsa du yabar tsufa ta bayana abinka da dogon mutun kuma fari tsufansa na gagawar nunawa, bale shi din ya kai tsufan shekara saba'in a duniya ai an sha ruwa, ama irin yadda yake da kuzari daidai gwargwado da kokari irin nasa na sakata jin nutsuwa a zuciyarta Murmushi ta sakar masa tana karra jan hular kanta ta rufe gashinta da furfura ta kusan hadewa tana fadin" Alkali yau kai fa kanka? Na so sauka fa sai barci ya ci karfina" Murmushi ya yi ya karasa bakin gadon ya zauna a ransa yana tunanin yau da gobe kayan Allah, tsufa labari, gashi yanzu shine kusan ba ruwansa da wannan lamari da ya yiwa naci a da, ita dinma da ta kasance cingan sarkin nacin miji a yanzu ba wannan a gabanta , abubuwan dake gabanta sun fi wannan fado mata a rai, kuma ana zaune, ana matukar kaunar junna da kula da junna, idan daya ya ce wash dan uwansa kaan rikice ya susuce A hankali ya kamo hannunsa tana sake fuskantarsa, duda kwana biyu sun yi yar tsama a kan maganar ABDUL RA'UF ta nuna cewa shine bai yi masa magana ba da tuni ya amshi tayinsu ya masu biyaya, sai a yau take jin ta yafe , kanshin turaran miskinsa mai taushi na mata dadi a hanci ta ce" Fari mai farin gemu ko yinwa ake ji?" Murmushi ya yi yana kallonta ya ce" kakar Fari bana jin yinwa, zuwa na yi da magana" Sake fuskantarsa ta yi tana sauraronsa dan ta san ko meye yana da mahimmanci a zuciyarsa A tausashe ya ce" Magana ce a kan Yarinyar nan, yarinyar nan marainiya ce, tana fama da kanta da neman hanyar da zata kare mutuncin kanta, sai dai hakan na neman gagara, har ya zamto wani marar jin tsoron Allah na dira mata gida da yara, ina so ta dawo gidan nan ta zauna har Allah ya fitar mata da mijin aure" A tausashe ta ce" Wa kennan?" Mai Shanu ya ce" Uman biyu nake magana a kai" Dan jim ta yi tana dan tunani, sai kuma ta sauke Ajiyar zuciya ta ce" Allah shi kyauta, to kuma Kakan Fari sai an nemi shawarata dan wannan? Ta zo mana ga cen bangaren su Nana sai ta zauna tare da su" Yana kallonta ya ce" Nana kuma?" Hajia ta gyada kai tana kallonsa Mai shanu ya girgiza kansa ya ce" Duda suma bana zaune da su a matsayin bayi ko wasu da na fi a duniya, ama su din masu aikina ne, ita kuma jikata ce, yarinyar nan na mutuntani tamkar ni na haifi mahaifinta, a nan tare da mu zata zauna " Naman goshinta ke dan tatarewa tana kallonsa, ta jima kadan a haka tana nazartarsa, sai kuma ta tabe bakinta tana kawar da kanta gefe ta ce" Ba damuwa, ama sai dai ta zauna a dakin kasa ba nan sama ba!" Murmushi ya yi a bayane ya mike ya kama hanyar fita , sai kuma ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Idan kina da fita yau ki ajiyeta gefe ki kula da ita, zan so ki rarasheta dan kin san me ake nufi da abinda aka so yi mata" A tausashe ya yi maganar, sai dai wani irin gundumemiyar guduma da ta daki kirjinta ta hanna mata kyakyawan motsi ta raka kofar da ya ja mata da kallo A hargitse ta so mikewa dan bin bayansa, kwata kwatama ta manta shekarun yanzu da na da ba daya ba , sai daa ta ji kafafuwanta sun wani irin rike mata ta saka hannunta tana rike abin gadon hadi da rintse idannuwanta a bayane ta shiga karanta dukkan adu'ar da ta zo bakinta sannan ta koma ta zauna a bakin gadon Ido rufe ta shiga tunani a cen kasan zuciyarta da tarin takaici, ta zauna? Kar ta fita? Sabon salo kiran sallah da usur, yaushe rabonta da irin haka da shi? Me zata yiwa yarinyar da shekara ashirin da biyar kadai ta bata a duniya? Menene yarinyar bata sani ba? Yanzu shi dan ance an dira mata har wani daga masa hankali zai yi? A tunaninsa zata zauna har wannan shekarun bata san hanyar kashe kishirwarta bane? Itace MAI SHANU zai ringa jerawa wulakanci kala kala dan kawai an santa fa hakuri (🧐), walahi ba zai yiwu ba, bafa zai yiwu ba, bara kafarta ta saki ta sauka ta tarda shi a yi wace za'a yi! Ina dalili wai zai ringa caza mata kwakwaluwa ? Kiri kiri ya ki tankwasa fitinanen jikansa da ya yi gadon halinsa! To daga shi har shi din ba zai yiwu ba, gashinan yarinyar da yake nema ko jiya sai da ta mata maganar daga ce masa kwana biyu bai leka gidansu ba ya daina dan kiran da yake yi mata , gashi ya hannata kiransa kowani time yace baya so yana cikin aiki ko cikin jama'a ko ibada ta shagaltar da shi, wai a haka yana son yarinyar be kowama ya sani? Ita kam ta gaji da fitinarsu walahi! Baba bai sauko daga dama da wuri ba, sunna nan zaune dai Babar ma'aikaciyar gidan ta zo ta wuce baban dakin kasa da yan mata biyu a bayanta bayan sun gaisa duka shiga gyaran dakin, domin babu mutane ciki ba zai rasa kura ba, Sai kuma dakin kusa da shi nanma aka gyara tsaf har bayi aka wanke tasss Sunna gamawa suka bata kys din dakunnan biyu suka ce in ji baba , baban nata ne dayan kuwa na Ζ΄aΖ΄anta Ita dai amsa ta yi tana shafa kan Hasan da har yanzu fushinsa bai sauka ba sai cije lebe yake yi baya kula kowa A haka aka kuma kawo masu abinci shake da plate baba da cokula, ga jus da ruwan sanyi aka ajiye masu cike da kula da mutuntawa Da kyar ta samu Hasan ya yarda ya sauka dan cin abincin, shima dai sai da yace sai dai idan tare zasu ci, a dole ta ringa fan tsakura tana kaiwa bakinta , su kuma sunna ci sunna korawa da Jus A haka Baba ya sauko, cikin shigar manyan kaya na daraja a jikinsa, sai kanshi yake yi ga hula ya kafa a kansa Sosai ya ji dadin gannin sunna cin abinci, da kula sosai ya ce" Idan kun gama ku shige ciki ku huta kin ji Uman biyu?" Amina ta amsa kanta a kasa , biyu kuwa suka ringa yi masa adu'ar a dawo lafiya har ya fice a falon yana amsawa Gurin Man Liman suka je suka dauke shi da motar suka wuce gidan Iyayenta, watau yayan mahaifinta, wanda yake da dan teburinsa a kofar gidansa, sun tabata ko yayane zasu same shi a gida warhaka, sai dai idan rasuwa ko wajen daurin aure ya tafi, koma ina ne in sha Allah ya yi niyar sai ya hadu da shi a yau Sun taki Sa'a, sun samu Malan dan iya a gida , a kofar gida yan kukula kayan sana'arsa saman tabarmarsa A mutunce suka gaisa da junna, domin ya san waye MAI SHANU farin sanni, bai taba zuwa gaishe shi bai masa alheri mai girma ba A saman tabarmar suka zauna, Mai Shanu na tsokanarsa cewa yaya haka ya tsufa? Shima yana yar dariya da fadin to yaua za'a yi neman na gero kadai ya isa ya tsufar da talaka Mai shanu ya ce Allah ya dafa mana, suka amsa da amen A nutse Mai Shanu ya shiga bayanin abinda ke tafe da su, a tausashe da kalar fahimtarwa ya ringa fahimtar da shi abinda yake dauke da maganar , har ya dire aya

Chapter 7 of 9