Share this page
6 / 9
rasu akace" A sanyaye yake kallon yaron, sai kuma ya mike ya rike hannunsa suka karasa wajen da bokicinta yake tana ta kakabar jiki ta dauki bokicin da jakarta da ta watsar du ta hade tana jan numfashi domin warin abin hawan mata kai yake yi sosai A sanyaye ya ce" Maman twins, ki yafe mana dan Allah" Sosai ta so jan maganar, sai dai mutumen nan tana matukar gannin girmansa, a haduwarsu sau biyu kadai alkhairi ya shiga tsakaninsu , ya kare mata mutunci sau biyu kuma ya rarashi Farid sau biyu, duda shi dinma bata tunanin idan ya girma sosai , ta yiwuma ta girme masa, ama tana gannin darajarsa, dan haka a sanyayen itama ta ce" Ba komai, zamu wuce gida" Ya so su bari ya kaisu, ama ta kiya, a dole ya hakura ya tafi ko kyautar da ya so ba Biyu ta tubure ta kiya, da wannan ya tafi da addu'ar Allah ya sake hada su, shi kam yana son taimakawa matar nan da ƴaƴanta, kamun kanta na matukar birge shi a rayuwa ___________________________________ A gajiye suka dawo gidan tare da Baba lauratu, domin kasa zuwa wajen markadan ta yi sai gidan baba lauratu ta je a nan ta fashe mata da kuka tana fadin an ci mata mutunci, karshe dai Baba laurantun sai ta rufeta fa fada tana fadin ta lura a kan lamarin Biyu sai ta tube a daku da ita, ta ringa sanyaya lamarinta, ina ita ina jifan motar masu kudi, masu kudin nan da daidaiku suka san yafiya da kyaliya ? Idan aka makata a cel yayazata yi kennan? Ta san basu da inda zasu je su kama a cirota , Allah ne kadai ya isa ya yiwa abin tsawa, ta kiyaye Allah ya taimaketa ta fada hannun na kirki Ita kam shanye abinta ta yi a ranta, ama ta san babu maganar na kirki, mutumen banza ne kawai Allah dai ya hada shi da aboki na kirki Da kaza kazar Baba Lauratu ta hasa wutar suyar kosan ta dora kasko ta shiga soya mata da siyarwa ita kuma ta shige ciki ta ja ruwan wanka ta dumama shi ta darje Hasan da Husaini da kanta , har kawunnansu sai da ta wanke da sabulu da soso sannan ta ji dama dama Itama ta yi wankan tamkar zata cenza fata ta fito ta gyara katifarta ta kwonta gashinta a barbaje dan ta samu ta huta, du wata kasala da bacin rai ke taso mata, ta so a bari ya mareta, da sai ta daka tsale ta shatawa jar fuskarsa mari sannan ta ciro sajensa a hannunta walahi! Karyar rashin kunya, ta rasa me yake yawo a kwakwaluwar samarin zamani A ranar dai bata wani sake yadda ya kamata ba, ƴaƴanta kansu basu haye mata ba sun kula ranta a bace sai suke shigowa idan ta kama su shigo din, sunna cen wajen Baba Lauratu sunna tayata ciniki, masha Allah sai zuwa siya ake yi taa ko'ina, dama samari sun fi gane irin haka, sai ragwagin matan da basa girki a gidajensu, sai yara da kwadayin abin ke saka su amso ashirin din iyayensu su siya su laka a hakoransu La'asar sakaliya Baba Lauratu ta gama gyara komai ta shiga ta hau dardumar da Amina ta yi sallah bata ninke ba ta shiga gabatar da sallar itama Tana salamewa ta yi addu'a ta shafa ta waiga barin da Amina ke zaune sai cika take yi tana batsewa Murmushi ta yi ta ce" ko dai na raka ki ki je wajen Baba Mai Shanu ki zane jikansa ne Amina?" Amina ta kalleta jin abinda ta fada da dan mamaki, sai kuma ta sada kanta tana turo bakinta hadi da jan numfashi kasa kasa sosai ta ce" wai bani da kunya" Baba Lauratu ta yatsina baki tana ciro kudaden itama ta ce" To ai ba'a yi abin kunya ba, ki ware uman Mijin shine kawai alkhairi, fushin bashi da dadi ai ko? Tunda dai ba ramawa zaki yi ba ai batawa kai lokaci ne, matso ki ga kuɗaɗen cinikin, masha Allah kasuwa na sonki Amina shi yasa nake ce maki ba dole sai da aikin gwamnati zaki ci abinci ba, baki taba kasawa kika kwashe ba'a siya ba, ama ke kin dage da maganar boko" Amina ta mike kamar an tuna mata tana fadin" Yauwa Baba kin ga tunda na fara kosan ga dubu gomar nan hadeta da ajiyar wajenki, kin ga har kudaden sun zarta wanda ake da muradi na jarabawar nan, sai dai lokaci ya kure, ama ba komai zan ta ajiyewa ana adanawa kafin badi idan ina cikin masu rai sai na kuma ajiyewa na zanna , Baba ina son boko, ko dan kaina ya karra wayewa, bale boko din fa tana biya baba" Baki Baba ta kebe, ita kam bata ga abin matsawa kai da maganar boko boko ba, a yi bokon a gama aikinma ya gagara? Ai kasarmu in dai baka da dogon hannu ko ka san mai dogon hannu ka shiga uku kennan, da zafin a kawo a kawo kawai ya isa ya koreka daga hanyar bokon, ta ce" Allah dai ya fito da miji da kudin na je na sa Lukman lafinta ya dandasa mana gado dandasheshe" Shirun da ya biyo baya ya saka Baba Lauratu karra kallonta, dama ta san a rina, da zarar an mata maganar aure sai komai nata ya tsaya, kamar wace bakin aljani ya aura, ta dauko damuwa ta ɗorawa kanta , a cikin manemanta mutun biyun nan tana gannin idan Allah ya yi aka yi da su ko yayane zasu kular mata da yarenta, domin a cikinsu babu na banza, daga baban Sauda har Muktar sunna da mutunci kuma an sheda sunna da riko da iyalansu da gaskiya, ba yinwa ba matsalar sutura, daidai karfinsu sunna kamantawa, bama kamar matar Muktar mai kanti, babu dashin da bata shiga na anguwa, kwanakin nan harda dashin gidan Baraka na dari uku a wata ta shiga dan tana samu, ama ita sai ture su take yi ta kasa sakin jikinta, idanma a nan take so su zauna da mijin ai ba damuwa sai su yi zamansu, duda da wahala mazan yanzu masu takaici su aminta da haka, ama ai hakan dinma ba laifi bane Ita dai Baba sai da suka ci abincin dare ta yi masu salama ta tafi Amina ta dawo ciki ta dage labulen dakin ta bude kofar dakin sosai, domin yau wani irin zafi take ji, biyuma da duka fara yin barci ta ga du sun rage suturar jikinsu babu mai riga a cikinsu , kowane kuma ya kama gabansa ya kwonta a gefensa dan yau basa so su likuma junna dan zafin da garin yake da shi Sake watso ruwa ta yi ta koma dakin ta dawo baki baki ta kwonta da daurin kirjinta sai hijab dinya da ta jiko ta rufa shi a jikinta ta shiga yin adu'ar tsaro ta tofawa yaren , itama ta yi ta tofa a jikinta sannan ta kwonta tana neman barci Barcin ne ya yi awon gaba da ita a nutse, sai dai a cikin barcin mafarki ne marar dadi ke dawainiya da ita Mafarki take yi wai ita da namiji, mafarkin da ta jima rabonta da yin irinsa A hankali ta ringa ji kan nononta na zafi sosai kamar ana tsikara mata allura, Juyawa ta yi domin gaba daya abinda take mafarkin tamkar a zahiri ne Dakatawar da aka yi na dan lokaci ya sakata sake neman barcin hadi da sauke ajiyar zuciya Sai dai bata jima ba ta ji ana shafar kasanta an kara shafawa Tun tana daukan abin da wasa sai ji ta yi ana mulmular abinda ke gabanta da yatsa ko da mene? Ita dai tana ji abin na sake shigarta dan haka ta kai hannunta cikin magagin barci dan kadewa, ko turewa, Hannunta ne ya yi raf da hannun dake kasanta ,lokaci daya barcin dake idnanuwanta ya dauke sakamakon fizge hannunsa da ya yi ya mike tsaye Wani irin razananen ihu ta saka hadi da wawurar hijabinta da zaninta tana sake ihun kwarto hadi da neman fitowa ko Allj zai bata sa'ar guduwa ta labe Jikinta rawa yake yi, kuka take yi, bata gannin gabanta hakan ya sa ta maku da jikin garun dakin nata ta yi baya ta zice a kas ta tafi a sume Ihun da yarenta ke yi sunna kiran sunnanta ya ankarar da daidaikun mazan dake fitowa dan zuwa masalaci Hankali ne ya fara tashi, domin daya na girgizata ne daya na ihun kiran sunnanta, uwa uba kofat gidanta a bude ham A hankali mazan suka fara dan taruwa a kofar gidan har suka kai mutun hudu, ciki harda yaron liman, shima magidanci ne kuma bai fi gida uku tsakaninsu ba A nutse ya ce" Malan Innusa inaga dole zamu shiga gidan nan, kafin a tado wata macen kar aje wani ne a gidan nasu, duba da kwanakin baya hakan ta faru?" Na'am suka yi da shawararsa, gaba dayansu suka shiga, sai daya da ya koma tado matarsa datijuwa da nufin ko menene mace sai ta fi su karfin taimakawa dan kare hakin musulunci A yannayin da suka same su da ƴaƴanta a dole suka fara bata talafin tsayar da jikin da goshinta ke yi, sai kuma Aban Saudat ya fice da sauri dan ya dauko adaidaitarsa a tafi asibiti Innar Audu itace da yarta suka talafi Maman biyu, sai Aban saudat din da kuma biyu suka nufi asibiti, su kuwa sauran suka je masalacin dan gabatar da sallah Bayan an gama sallah ne yaron Liman ya shaidawa Liman abinda ya faru, da yake baban masalaci ne dake cen tsalake , har sallar juma'a a nan ake yi ya saka Liman anfani da lasifikar masalaci ya dakatar da datawan da samarin baki daya ya shiga nasiha da jan hankali, da neman alfarmar kowa ya binciki ya'yan gidansa ko idan ya kula yaron anguwarsa nada irin halin nan ya fada a sanarwa hukuma su yi gagawar shiga lamarin, yaren sun ce wani ne ya shigo ya taba mamansu ta suma, an sako yarinya a gaba dan an ga miji bai fito ba kuma ba uwa ba uba ba dangin da suka yi jin kai? To b zasu zuba ido sunna ji sunna gani a salwantar da rayuwar yarinya ba, yau koda ace itace ke janyo mazan da rashin kamun kai datawan anguwa ba zasu bari hakan ya ringa faruwa ba bale yarinyar an yi mata shedar kamun kai da kare mutuncin kai! Sosai abin ya taba zukata, ciki kuwa Harda Mai Shanu dake yin doguwar tafiya a kafarsa shi da daidaikun ma'aikatan gidansa su zo har masalacin nan dan yin sallah, idan suka fita sukan zagaya ne a kafa su yi sport sosai dan jin saukin yannayin jiki Hankalinsa tashe ya karasa wajen Liman bayan an sake yin addu'a a raragu sosai yana tambayar wada ake magana a kanta? Liman ya san sarai mahaifinta ya masa gadi, hasalima gidan da take cikin Baba Mai Shanu ne ya malakawa mahaifinta suka fita daga haya suke ciki, dan haka ya sanar masa ko wacece da fadin anma kaita asibitin tafasa, shina yanzu cen din zai nufa Sosai hankalin Mai Shanu ya karra tashi, Tatare suka dungunzuma a cikin motar gidansa da ya sa Baba direba ya je ya dauko sula nufi asibitin Tasafar kowa hankalinsa tashe, zuciyarsa kuwa cike da tsoro da zulumin Allah ya sa wannan shedani bai samu galaba a kanta ba Baba Mai Shanu kam abubuwan dake cikin zuciyarsa yawansu da girmansu Allah kadai ya sani Ya shirya yin gaba da gaba da dangin iyayen yarinyar nan, idan zasu mayar da ita wajensu su mayar, idan ba zasu mayar ba to fa shi zai dauketa koda kuwa bata so! Ya isa haka, zaman tarenma da aka yi ai sai Allah ya tambaye su su da kansu bama dangin na iyayenta ba, sam an yi sake, an yi wasa da lamarin yarinyar nan, shi tunda ya kwatanta ta koma ta nuna ta fi son zama a nan tana gannin dakin mahaifinta da mahaifiyarta sai ya bar maganar, bai san ba baban tashin hankalinta zama tare da Matarsa bane, bai san ba Amina tana tsoron abinda zai taba mutuncinta komai kankantarsa, shi yasa ta iya garinta take tuka tuwonta Sun tarar an gama wanke mata goshin nata ta farfado ama tana kunshe cikin hijabi sai kuka take yi, Aban saudat ya koma gida ya dawo domin bai fito da isashen kudin da aka ce zai biya ba Baba mai shanu ne ya fito da fari kal din carbinsa ya je direct office din baban likitan wanda ya kwana a asibitin kuma bai sauka ba ya nemi izinin ganninsa Likitan na fitowa ya gaisar da Baba cikin mutunci, domin likitan akoy daraja dan Adam, kuma kana gannin Baba ka san akoy hutu a tare da tsohon A tausashe, da damuwa Baba ya ce" Jikata ce aka shiga gidansu jiya, nake so a duba min ita da fatan babu abinda ya sameta" Cike da jimami likitan ya yi gaba ya kirayi likita mace ya sa aka kirawo Amina sula shige ciki dan a dubatan Sosai aka sha daga da ita, domin sake rikicewa ta yi da nuna ba za'a dubata ba, ba zata kunce zanninta ba, sai da Likitar ta rarasheta ta nuna mata za'a duba ne idan bai yi mata komai ba sannan ta amince ta dubata Tare suka fito Likitar ta shedawa Baba cewa Allah bai bashi dama a kanta ba Gaba dayansu sai da alamun nutsuwa ta bayana a tatare da su Fuska a hade Baba ya ce" Amina Wuce ki shiga mota mu tafi gida" Amina da har yanzu bata wani dawo normal ba ta kalli Baba hankalinta na sake tashi ta ce" ASALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 1️⃣0️⃣* Baba Mai Shanu ya ce" Kwarai kuwa, zan fi so Amina ta dawo gidan nan ta zauna kusa da mutane, cikin mata da jama'a yan uwanta, zata fi sakewa ta ci gaba da karatunta har Allah ya kawo miji a yi aure" Irin abin nan na wasu tsofin idan abu ya basu mamaki ko takaici ya yi yana dafe haba ya ce" Aure? Yanzu tsakaninku da huwa rahamanu baku gane yarinyar nan ta gama wulakantar da kanta bane ya sa ta kasa samun miji? To ai mai sunnan iya ko dan gidan na kawota na kawowa kaina fitina da balaki ne, domin a cenma da bata giga ba dan kawai yayansu ya daki kanwarta furduduwa take ko wa? Ta dauki ice tace ko shi ko ita, a haka wani sakarai ne zai dauka ya kai gidan watarana gardama ta hada su ta masa tsinanen duka? Ta zo ta kalli tsabar idona da nace a siyar a raba masu gado a saukewa bayin Allah nauyi a kansu tace aa su ba za'a raba masu gado ba, yarinyar nan a nan na hanneta maganar karatu da tace an ce iyayensu su zo nace me ake da boko? Boko ai lalacewa kennan! Tace da ni ba lalacewa a maganar boko , ilimi ne halal ne a neme shi!, Na kuma yi tataki na mata magana a kan rikon yara har biyu maza, da me zata ciyar da su? Waye zai aureta da yaren nan maza ? Zamanin nan waye zai iya rikon ɗan wani? Ama idona idon mai sunnan iya tace Baba zan iya ka bar min su kawai zan iya! Yarinyar nan gardama a kanta ta sauka kamar a kwakwaluwarta aka rawaito, ni kuwa yaya zan yi na iya rikonta? Ai kawai gidan nata zata koma ta je ta rayu da ya'yan ta ci gaba da gantalinta har ta tsufa, shi kam Uban mai sunnan iya ya yi asarar haihuwa walahi!" "Subahanalah, subahanalah malan, subahanalah, fal yakul khairan au li yasmut malan, yaya da girmanka da hankalinka malan da kanka zaka yi furuci irin haka? Yau kofa yar zumunka *LALATACIYA* ce ai zaka siranta,, harshenka ya bita da addu'a bale mu zahirinta da muka sani yarinyar tana da kamun kai, ba zamu yi shedar badininta ba, ama abinda idannuwanmu ke gani tana dauke da sheda ta alkhairi sosai, to ni a ganina ai rikon ƴaƴan y'ar uwarta da take yi dan tana da zuciya mai kyau ce, ga jajircewa a wajen baiwar Allahn nan, mai zuciyar alkhairi kan yi mata dan talafi a gareta, ka tausasa kalamanka malan a kan yarka" Liman ya fada cike da jin ba dadi a furucin Uba a wajen Amina Sai dai su suka san dadin abinda suke hange, basu san shi ya riga ya yi nisa baya jin kira ba sai da ya kara gyara zamansa yana dan kada kafarsa ya ce" Tototo, Aya, Allahu akhbar, kennan Man liman fadin gaskiyarma matsala ne? To Allah shi kyauta, ama ni kam Mai sunnan Iya ta fi karfina walahi, ba zan iya zama da ita ba" Baba Mai Shanu ya fi kowa jin takaicin bawan Allahn nan, wani irin mamaki ke lulube zuciyarsa da mamakin zumuncin zamani, y'ar zumunka? A gobe kiyama ita zaka gani fa! Itace kake wulakantawa haka? Maganar Liman ce yau ko bariki aka tare a kan yarinyar nan ai zai siranta ya bita da adu'a balle babu wanda zai ce ya taba gani ko ya ga wanda ya gani, shin menene a cikin rikon baki uku kawai? Yarinyarma bata da zubuwa, ko kyauta ka yi mata sai ka zare ido zata amsa, shine har zai kireta da sunnan idan ta gama dadiron? Ta tsufa? A cikin haka? Wannan dan uwa ne ko makiyi ne? Datijantaka da ilimi da salatin annabi da ya yiwa harshensa kawaya ya saka shi tausasa lafuzansa sosai hadi da iya kiyaye harshensa ya ce" Dama mun zo ne dan mun san a yanzu a duniya babu wanda ya kaika kusanci da ita, kuma babu wanda ya isa ya yanke hukunci ba tare da ya tuntubeka ba, Alhamdulilah tunda har ba zaka iya rikewa ba ni zan riketa, har Allah ya fitar mata da mijin ta yi aure, ko bayan raina na san iyalina zata rike min!" Malan Liman ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa, ai ko ni nan zan rike Baiwar Allah mai baban sunna, ka duba ka ga yau a masalaci irin taimakon da suka tara dan ance an tafi asibiti da ita, yanzu haka ana amsar kudin mai dari mai dubu kowa na bado talafi da kuma alkawarin za'a hadu a saka ido sosai dan a kama azalumin dake son karya mana haki a ido, ai in sha Allah yarinyar ba zata tabe ba, sai ta zauna a gidanka Elhaj idan Allah ya fitar mata da miji sai a daura mata aurenta ta yi tafiyarta gidanta" Da aka ce ko yaya ka yi da jaki sai ya ci kasa haka ne, kamar wanda wannan bawan Allahn yake gudun abin alkhairi da rahamar ubangijinsa, shin bai san falalar shafa kan maraya kadai bane a rayuwarsa bale kyautata masa da cireshi a kunci uwa uba ciyar da shi? Shi dai koda ya sani to fa shedan ya yi galaba a kansa a wannan lokacin da lada ke binsa yana zundumawa a guje tamkar mai gudun fanfalaki, a takarkare ya warware wani nadin na arzikin yana nuna hali ma rashin arziki ya ce" Ban taushi numfashinku ba, ba zaku gane abinda ni na gane dangane da yarinyar nan ba, kamar yadda ta fita daga gidan nan dan ta raina rikona da ikona ta gwamace zama a gidan ubanta haka zata koma yanzuma ta ci gana da zaman a cen! Walahi ba zan barta ta je gidan kowa ta zauna ba! Ba da yawuna ba, idan kuwa wata iyakar tawa zata nuna min bismillah sai na ga idan ta samu mijin wanda zai daura mata shi! Ai ta gani da kanwarta ta min rashin da'a yadda muka kwashe da ita!, Itama bata fi karfin hakan ba, babu abinda ya shafeni da barikinta ko kudinta, idan ta bijire min in na kama tsine mata sai ta bi duniya wa bilahilazi!, Alkawarina ne wanann!, Gwarama ta gyara halayarta ta koma ta kama mutuncinta ta zauna ko ta samu mashinshini, idan har ta bar gidan nan da nufin zama wani wajen sai dai idan da auren wani a kanta ne!" Daga Liman har Baba Mai shanu ido waje suke kallonsa Baba bai san lokacin da ya ce da Malan dan iya" Aman Malan me yarinyar nan ta yi maka da kiyaya hala? Ko dai kiyayar ta mahaifinta ce ke shirin shafarta?" Malan Dan iya har huci yake yi ya cire kansa gefe, irin wannan karron iko a hannunsa yake din nan , zai gwadawa Amina bata isa ba, ita din ba kowa bace , idan tana tunanin ta kai wani mataki ne dan tana da gida banzar bazara ce ita! Ya ce" Ba maganar gaba ranka shi dade, ai na yi rantsuwa ne sai dai idan da auren wani zata je gidansa ta zauna!" " Innalilahi wa inna ilaihi rajune, innalilahi wa inna ilaihi rajune, yanzu fisabililahi Malan wannan din ina anfaninsa? Idan fa bata fa maneman a yanzu? Shin baka gane cewa ana so a yaga mutuncin yarinyar nan bane ko me? Wani irin uba ne kai? Anya zaka so a yiwa ƴaƴan cikinka?" Liman ya fada da jimami yana kallon Dan iya Dan iya ya tabe baki ya ce" Liman ba zaka gane ba, mu mutanen karkara munada namu ka'idojin da ba'a takewa, a shekarun fa ta tara kadai laifi ne a kauye, tana yawo waje waje , bata zauna ba, baka san yaron mai garin garinmu sai da ya fito aurenta ba? Mahaifinsa ne da kanda yace aa wannan din ai ta tsufa sai dai ya nemi wata, wannan abu ya min ciwo a rayuwata, kwata kwata bata da sa'ar rayuwa ne!, Da yanzu ta malaki shanu uku ko hudu nata na kanta!, Sai karyar bokon tsiya, wannan din itace maganata, yarinyar nan ba zata je ko'ina ba ta koma ta zauna, wani mutuncin kuma? Kai ni fa dai na rantse bata da shi , kai baka ga rawar kanta ya yi yawa ba?" Baba mai Shanu tunda ya rufe baki da hannunsa yana kallon larkararen rashin ilimi da shirme ya kasa furta koda A ne, yana kallon yadda Malan ke iya kokarinsa dan ya dawo da Dan iya hanya, ama abin ya gagara, du inda ya bila sai ya bile, irin girman zumunci yake nuna masa da irin alkawarin Allah a kan wanda ya yanke zumunci, ama sai ya zile ya nuna masa ai yarinya ta lalace ba za'a iya talafa mata ba, Liman har zufa yake yi, gardama da mai lafiya ce da ita, domin ba za'a kirayeshi da jahili ba yana da nasa sannin daidai gwargwado!, A sanyaye Baba Mai shanu ya ce" Ka yi shiru abinka Liman, ba fa zai saurareka ba" Sai kuma ya fuskanci Dan iya ya ce" Shin yaushe ka yanke aurar da ita? Ina nufin zaka iya bata koda kwana uku ne ta dan saku daga wannan tashin hankalin a gidana?

Chapter 6 of 9