An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t
FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
04 / 04 /2026
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM?mode=gi_t
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
TUNATARWA!
Rayuwa ba ta tsaya ga wanda yake jin daɗi kawai ba wani lokaci jarabawa ce ke koya mana darasi.
Rayuwa tamkar hanya ce mai lanƙwasa wanda ya yi tafiya da gaskiya, ko da ya yi jinkiri, zai isa, amma wanda ya yi tafiya da ƙarya, ko da ya yi gudu, wata rana zai fāɗi.
Kamar yadda rana ke fāɗuwa bayan ta fito, haka farin ciki da baƙin ciki ke juyawa a rayuwa.
To idan mutum ya manta da gaskiya saboda duniya, me zai amfane shi idan ranar sakamako ta zo? mu gyara ayyukanmu tun kafin lokaci ya kure.
..
TSOKACI
Rayuwa tamkar gona ce; abin da mutum ya shuka shi zai girba, wanda ya shuka mugunta, kada ya yi mamakin girbin nadama.
Giya da sha’awa suna ɗaukar mutum kamar iska mai ƙarfi, suna rufe masa idanu har ya manta da darajar rayuwa da mutuncin wasu. A lokacin da yake wasa da lokaci da dukiya, yana ganin duniya tamkar wasa ce. Amma wata rana sai ya farka ya tarar cewa abin da ya ɗauka wasa ne ya zama bala’i.
Sau da yawa mace marar laifi ce ke ɗaukar nauyin kuskuren namiji. Ita ce ke shan ƙunci, ita ce ke ɗaukar ciki, ita ce ke fuskantar zargin duniya, alhali laifin ba nata kaɗai ba ne.
Hakika, duk wanda ya lalata rayuwar wani saboda son zuciya, to lokaci zai zo da zai nuna masa cewa nadama ba ta dawo da abin da aka riga aka lalata.
Don haka mai hankali ya koyi darasi tun kafin lokaci ya kure, domin kuskure na ɗan lokaci kan iya zama hawaye na tsawon rayuwa.
AFNAN KINAN
PG 1
SUDAN
ATLAS KINGS vs SAHARA UNITED
Filin wasan Khartoum National Stadium ya cika ya tumbatsa kamar teku lokacin da iska ta taso mutane sun zo daga kowane lungu na duniya, tutoci suna girgiza a sama, karar bushe-bushe da ihu suna gaurayawa da kiɗa. sunan Atlas Kings FC na yawo a bakin kowa kamar wata waka da ba ta ƙarewa.
“AT-LAS! AT-LAS! AT-LAS!”
A irin wannan rana ne mutum ke gane cewa ɗaukaka ba ta zuwa a banza, duk wanda ya hau saman tauraro, dole ya taɓa duhun dare kafin hasken safiya.
A ɗaya gefen filin kuma, ‘yan Sahara United suna shirin shiga. Fuskokinsu cike da jarumta, amma kowa ya san dalilin da ya sa filin ya cika yau…
NADIR.
Lokacin da ya fito daga tunnel ɗin ‘yan wasa, sanye da jersey ja da zinariya na Atlas Kings, jikinsa mai ƙarfi ya haskaka ƙarƙashin fitilu. Fatar sa mai kama da chocolate, gashin kansa baƙi an gyara shi cikin tsari na zamani. Sajen da ya tara a jikinsa da kuma a gefen fuskarsa suna ƙara masa kwarjini.
Idanunsa masu nutsuwa amma cike da ƙarfin zuciya sun nuna cewa wannan ba sabon wuri ba ne a gare shi. Duk da shahararsa, bai haura shekaru talatin ba.
Nan take filin ya fashe da ihu.
“NADIIIRRR!!!”
“KING OF ATLAS!!!”
Ya ci gaba da tafiya a hankali, ba tare da hayaniya ba, kamar wanda ya saba da ɗaukaka. Ya ɗaure takalminsa, ya murza wuyan hannunsa kaɗan, numfashinsa a daidaitacce, agare shi, wannan wasa ba wasa ba ne.
Ƙaddara ce.
Alƙalin wasa ya busa ƙaho.
Ƙwallo ta motsa.
Nadir ya karɓi ƙwallo a tsakiyar fili. Da sauri ya juya ya wuce ɗaya… biyu… uku! masu kallo suka miƙe tsaye.
Ƙwallon tana manne da ƙafarsa kamar an ɗaure ta da sihiri. ‘Yan Sahara United suna binsa amma ba sa iya kamawa. Ya ɗaga kai ya hango raga…
BUGU!
Ƙwallon ta tashi sama ta shige kusurwar raga.
GOOOAAALLL!!!
Filin ya girgiza. Mutane suna tsalle suna ihu suna rungumar juna. Sunan NADIR ya cika sararin samaniya kamar karar guguwa.
Amma shi…
ya tsaya kawai ya ɗaga hannunsa sama. Ya kalli sama na daƙiƙa guda, kamar wanda yake tuna cewa duk ɗaukakar duniya tana da asali daga sama.
Bai san cewa a wani ɓangare na duniya ba,
akwai yarinya mai suna AFNAN…
Yarinya wacce zuciyarta ta ƙi ƙwallon ƙafa ƙin da ya fi ƙiyayya tsanani.
@@@@@@ MARROCO @@@@@@@@
Oga Salman ya fito daga ofishinsa yana rike da remote, fuskar sa cike da muhimmanci da jin daɗi Ya kunna babban TV da ke tsakiyar hall ɗin Company su ya ce da murya mai ƙarfi a duniya akwai abubuwan da suke tara mutane kamar zuma ke tara ƙudan zuma. Ƙwallon ƙafa na ɗaya daga cikinsu.
“كلكم تعالوا… شاهدوا المباراة جيداً! سأسألكم عنها بعد قليل!”
(Dukanku ku zo… ku kalli wasan nan da kyau! Zan tambaye ku daga baya!)
Nan take ma’aikatan company suka taru a gaban TV. Wasu tsaye, wasu zaune a gefe, wasu na riƙe tray na abinci amma idonsu a allo sai hayaniya ta tashi.
“نــادر! نــادر! هيااا!”
“نــادر! نــادر! لنذهب!”
Hall ɗin ya cika da ihu, tafawa, tsalle.
Wasu suna rawar murna kamar suna filin wasa da kansu.
AFNAN ta tsaya a bayan layi, tray ɗin ruwa a hannunta. Fuskar ta a dunkule ta tsani ƙwallon ƙafa charff a ganinta, wasa ne na hayaniya da ɓata lokaci , banda hauka ya zaka hurga abu kuma ka bishi da gudu, ta juyo kaɗan kamar za ta tafi sai a allo ta hango shi.
NADIR.
Yadda ya karɓi ƙwallo, yadda ya yi tsalle, yadda jikinsa ya motsa cikin sauri da ƙarfi mutane a hall suka yi ihu.
“وووففف!”
NADIR ya wuce ‘yan wasa biyu, ya ja ƙwallo da ƙafarsa, ya yi tsalle, ya bugi ƙwallon da kai—
GOOOAAALL!!!
Allon ya nuna sakamako:
ATLAS KINGS 3 — 1 SAHARA UNITED
Hall ɗin ya fashe.
Wasu suna tsalle, wasu suna dariya, wasu suna bugun tebur Oga Salman ya yi murmushi, ya ce:
“هذا هو اللاعب الحقيقي!”
(Wannan shi ne ɗan wasa na gaske!)
AFNAN kuwa ta tsaya cak, numfashi ta ya dauke na wasu daƙiƙai ba ta san dalilin da ya sa zuciyarta ta ɗan buga ba ta san dalilin da ya sa idonta bai iya barin allon ba.
Ta haɗiye yawu a hankali, ta ce a ranta:
“Ina tsanar ƙwallon ƙafa…”
“…amma wani Irrin wasa ne wanan yayi kamar tsafi ?”
ba ta sani ba a wannan lokaci cewa
NADIR, wanda duniya ke kira da suna,
shine ƙaddarar da zata shigo rayuwarta ba tare da izini ba.
Oga Salman ya rage ƙarar TV, ya tsaya a tsakiyar hall ɗin hotel kamar wanda zai faɗi babban sirri. Murmushinsa ya ƙara faɗi, ya ce:
“طيب… عندي لكم بشرى.”
(To… ina da albishir a gare ku.) hayaniya ta lafa nan take.
“تيم ATLAS KINGS سيأتي إلى المغرب…”
(Tawagar ATLAS KINGS zata shigo Morocco…)Da ya faɗi hakan, zuciyoyi suka buga.
“…للعب مع فريق PHOENIX UNITED wani irin ihu ya tashi kamar filin wasa.
“…وقد وقعوا عقداً مع شركتنا.”
(Kuma sun yi kwangila da company ɗin mu.)
Oga Salman ya ɗaga yatsansa:
“الأسبوع القادم سيدخلون الفندق، وسأخرج قائمة بالموظفين الذين سيتولون خدمتهم من بينكم.”
(Mako mai zuwa zasu shigo hotel, zan fito da jerin ma’aikatan da zasu kula da tawagar daga cikinku.) Hall ɗin ya rikide.
Wasu suna cewa: “Insha Allah sunana zai fito!”
“Wallahi wannan dama ce na yawo da kula da babban tawagar ƴan ƙwallon duniya !”ana ta murna kamar an raba zinariya.
AFNAN kuwa ta tsaya shiru ta saki tsaki a ranta, ba tare da ta motsa ba “na san sunana ma ba zai fito ba a wannan haukar nan.”
Ta kalli rigarta mai zubin Pakistan wanda yasha omo da rana yayi haske daga jaa ya dawo ruwan ƙasa takalmanta da suka ɗan tsufa, sannan ta tuna da kalaman su ..
Ta juyo a hankali, ta ɗauki tray ɗinta, ta nufi hanyar fita, ta sanya uniform nata
A wannan lokaci aka buga bell ,alamar an tashi daga taro nan take kowa ya watse, kowa da burinsa, wasu suna tattauna yadda zasu burge Oga Salman wasu suna ambaton sunayen ‘yan wasa wasu har suna cewa:
“Idan na shiga jerin nan, rayuwata zata canza.”
AFNAN ta bi ta gefen bango tana tafiya, zuciyarta cike da tunani, ba tare da sanin cewa sunanta yana dab da fitowa cikin jerin da zai girgiza rayuwarta ba.
⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 17 Novel
DISTENY LOVE STORY
1/ 04/2026
PG 2
SUDAN
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
TSOKACI
Rayuwa tamkar gona ce; abin da mutum ya shuka shi zai girba, wanda ya shuka mugunta, kada ya yi mamakin girbin nadama.
Giya da sha’awa suna ɗaukar mutum kamar iska mai ƙarfi, suna rufe masa idanu har ya manta da darajar rayuwa da mutuncin wasu. A lokacin da yake wasa da lokaci da dukiya, yana ganin duniya tamkar wasa ce. Amma wata rana sai ya farka ya tarar cewa abin da ya ɗauka wasa ne ya zama bala’i.
Sau da yawa mace marar laifi ce ke ɗaukar nauyin kuskuren namiji. Ita ce ke shan ƙunci, ita ce ke ɗaukar ciki, ita ce ke fuskantar zargin duniya, alhali laifin ba nata kaɗai ba ne.
Hakika, duk wanda ya lalata rayuwar wani saboda son zuciya, to lokaci zai zo da zai nuna masa cewa nadama ba ta dawo da abin da aka riga aka lalata.
Don haka mai hankali ya koyi darasi tun kafin lokaci ya kure, domin kuskure na ɗan lokaci kan iya zama hawaye na tsawon rayuwa.
AFNAN KINAN
PG 2
MARROCO
Rana ta fito da ƙarfi a garin Casablanca, inda tituna masu ƙanƙanci ke zagaye gida-gida, ƙara da hayaniyar kasuwa da yara ke ta wasanni. A ɗaya daga cikin unguwanni masu cunkoso, gidan su AFNAN tsaya a ƙananan bango na laka, ƙaramin fili, inda ƙaninta biyu ke tsaye suna wasa da ƙwallo, suna dariya mai ƙarfi.
AFNAN ta fito daga ƙofar gidan, tufafin ta sun kasance launin ruwan kasa mai ɗan tsufa, rigar da ba ta da kyau sosai, amma tsafta ta yi kyau. Kafaɗunta sun ɗan lankwasa saboda nauyin kayan wankin mutane da ta ɗauka,
AFNAN ta tsaya na ɗan lokaci, idonta na kallon ƙaninta biyu suna jefa ƙwallon ƙafa a cikin ƙananan filin, suna dariya da wasa zuciyarta ta ɗan ƙara nauyi, domin ta san cewa rayuwar su bata da sauƙi ta matso kusa da su, ta ɗaga muryarta da harshen Larabci mai ɗan tsauri:
“Ya ishe ku wasa, ku tafi makarantar allo yanzu! kada ku tsaya anan, ku tafe karatu kuna wasar banza mara amfani”
Ƙaninta suka tsorata, suka yi dariya amma suka san cewa ba za su iya yin watsi da umarninta ba. AFNAN ta kalla ƙwallon da ta yi wasa da su da ƙyar, sai zuciyarta ta ɗan tsinke , ta ɗauke ball in ta jefar a kwata ..
Ta ja numfashi mai nauyi, ta shiga gida da Yulin wankin ta ajiye zuwa dare zata musu gobe takai musu kafin a biyata haƙƙin ta . sannan ta fara tafiya zuwa Soleil International Guest Company, tana tunanin yadda rayuwar ta za ta canza… kuma tana sane cewa kowanne motsi na yau zai iya haifar da wani abu mai girma a gaba.
Tana tafiya cikin ƙafa, tana kallon titin da ke cike da sauran yara, mutane masu siyarwa da motoci, sai zuciyarta ta cika da ƙarfin hali. A ƙarshen titi, gidan “Soleil International Guest Company” ya bayyana: ginin na zamani, gilashi mai haske da fensir ɗin farar launi, a ciki ma’aikatan baƙi suna zagaye suna ɗaukar kayan abinci, ruwa da abinci da juice kowane ɓangare da aikin su Wannan shi ne wurin aiki na AFNAN, inda take zama karamar ma’aikaciya mai nitsuwa da kwarewa, tana daga cikin masu kula da baƙi ta hanyar basu abinci da ruwa ko wani buƙatar su a ɓangaren aikin ta duty every day mutum biyar ne maza ukku mata biyu wanda ya kasance sun ware ta a cikin su kasancewar bata shiga sabgar su ta son nishaɗi da yawan kai ziyara club domin shaƙatawa hakan yasa wani lokacin suke tafiya su bar mata aikin ba tare da sanin manager su ba , a hakan bata isa taye complain ba domin a banza wahalar da ita zasuyi da barazanar zasu tufka mata sharrin da sai an kore ta ba shakka tana tsoron su .
Da ta shiga cikin ginin Soleil International Guest Company, AFNAN ta ɗan tsaya kaɗan don duba duk inda take tafiya, kowa na aikin gaban sa, raye sign sanan ta shiga apartment nasu tasa uniform masu na ma'aikatar masu kai abinci da amsa kirar masu buƙata abu a dakin su , tsayawa taye a gaban madubi tana ganin kanta cikin Skirt da rigar launin marron wanda ya mata kyau ta kafa cap nata , bazata haura shekaru sha bakwai ba, fara ce mai launin larabawa fuskar ta yayi dai dai da launin garinsu larabawan ƙasar Marroco Murmushi taye mai kyau har sai da farararen haƙoran ta suka bayyana " AFNAN " aka ambaci sunan ta da sauri tasa jakarta a loka ta fito da hanzari , Irfan ce ta ganta da cewa " kiye sauri mujee ana kirar mu a hall " nan suka taho zuciyar ta na bugu bisa ka'ida.
Oga Salman ya fito daga ƙofar babban court ɗin company, sanye da suit baƙi mai tsada, takalminsa na sheƙi yana danna ƙasa da ƙarfi, aka buga bell, nan take hayaniya ta lafa.
Duk ma’aikata suka tsaya layi-layi, kowa ya san matsayinsa, kowa ya san inda zai tsaya.
AFNAN ba ta rikice ba ta san layin da ya dace da ma’aikata masu matsayinta ta taka a hankali, ta tsaya inda ya kamata, ta sunkuyar da kai cikin nitsuwa.
Sai ga HAMLA — yarinya mai gadara, wacce take ganin kanta fiye da kowa ta matso kusa da AFNAN, ta ture ta da kafada, idonta cike da raini, sai ta faɗa da Larabci mai zafi:
“إبتعدي عني! لا تقفي بجانبي يا فتاة غبية!”
(Ki matsa daga kusa da ni! kada ki tsaya gefena ke wawiyar yarinya!)
AFNAN ta ɗan girgiza, ta kalli Hamla na ɗan lokaci, zuciyarta ta ɗan yi zafi… amma ba ta ce komai ba ta daidaita tsayuwarta, ta sake gyara cap nata ta sunkuyar da kai.
A ranta ta ce:
“Ba kowa ne yake buƙatar amsa ba… wasu rainin ma shiru yafi musu zafi.”
Hamla kuwa ta yi tsaki, ta juyo da sauri
Hamla ba ta tsaya gardama ba. Da kafada ɗaya ta ture AFNAN da ƙarfi, AFNAN ta rikice, kafafunta suka cakude, sai ta faɗi ƙasa a gaban kowa.
Nan take wasu ma’aikata suka juya suna kallo, wasu suka fara dariya a ɓoye, wasu kuma ba su ma ɓoye ba “Hahahaha!”
AFNAN ta zauna a ƙasa, hannunta na dama yana rawa. Ta miƙe a hankali, tana mirza hannun nata saboda zafin da take ji Irfan ce ta taimaka mata ta miki ba tare da tace kanzil na Fuskar ta ta cika da kunya, idonta ya cika da hawaye amma ta ƙi su zubo.
A nan ne Oga Salman ya ɗaga murya, tsawarsa ta tsayar da kowa cak ya kalli AFNAN da fuska mai tsauri ya ce da Larabci:
“أفنـان! إلى متى ستبقين بلا عقل؟!”
(Afnan! har yaushe za ki ci gaba da zama marar hankali?!)
AFNAN ta sunkuyar da kai cikin rawar murya ta amsa:
“عفواً سيدي "
(Yi haƙuri ranka ya daɗe…)
Ta ci gaba da mirza hannunta cikin tausayi, idonta na ƙasa, hawaye na taruwa amma ta danne su wasu na girgiza kai kamar abin bai dame su ba, AFNAN ta tsaya nan tsaye cikin kunya da zafi, zuciyarta na cewa:
“Wannan ciwon hannun… ba komai bane idan aka kwatanta da ciwon raini.”
⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️⁉️
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 17 Novel
DISTENY LOVE STORY
03 / 04 /2026
PG 3
SUDAN
08101235739
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
GARGA'DI
Haƙƙin mallakar wannan littafi na marubuciya ne, ban yarda kowa ya sauya min labarin, ya mayar da shi audio, ko ya kwafa wani ɓangare daga cikinsa ba tare da cikakken izinin marubuciyar ba.
Wannan labari ƙirƙira ce daga tunanin marubuciya da zubin alƙalami duk wani suna, hali ko lamari da ya yi kama da rayuwar wani mutum ko wata gaskiya da ta taɓa faruwa, hakan dai daidaituwa ce ta zubin alƙalami kawai, ba da nufin kwaikwayon kowa ko nuna wani mutum ba.
Domin haka, marubuciya na sanar da kowa cewa duk haƙƙin wannan littafi nata ne kaɗai.
© Duk haƙƙin mallaka na marubuciya ne.
NARNAH KANWAR SOJA
08101235739
HIKIMAR MARUBUCIYA
Hikimata abin alfahari na ne, domin rubutu baiwa ce da Allah ke ba wa wanda Ya so. Marubuci na da damar gina duniya da kalmomi, ya tsara rayuwa da zubin alƙalami, ya nuna darasi cikin labari.
Kalma na iya zama haske ga mai duhu, ko darasi ga mai kuskure. Don haka marubuci na rubuta ne domin ilmantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa.
Idan ka ga labari ya yi kama da rayuwa, to ka sani zubin alƙalami ne kawai, domin rubutu baiwa ce da ke tafiya da tunani da hikima.
PG 3
Karfe shidda na yamma, AFNAN ta tattara jakar ta da kayan aiki, ta hau mashine tana tafiya gida hanya ta cika da hayaniya, mutane suna fita-fita, yara suna wasa a gefen titi, amma zuciyarta tana ɗauke da gajiya da tunanin yau da kuma gobe.
Da ta isa gida, ta hango mahaifinta a ƙofar gidan, fuska cike da masifa bai yi sallama ba, bai ɗan nuna murmushi ba. AFNAN ta tsaya, ta ɗan juyo da kai.
“Baba!” ta ce a hankali, tana fatan ya ji ko da ɗan kulawa amma mahaifinta bai kula ba ya kutsa gidan, ya haɗu da buta yayi hurgi dashi, ya fara masifa da muryarsa mai ƙarfi “nagama wahalar amma na dawo basu sallami ne da komai ba!”
AFNAN ta tsaya cak ta san cewa magana zata zo mai zafi, amma ba zata yi kuka ba ta kalli hannunsa, fuskar sa ta nuna rashin kulawa kamar kullum.
A gife kuma Umma ta daura ruwan zafi tana jira dawowarsa, zuciyarta cike da tsoro da fargaba. Amma yau, kamar kullum, ba komai daga hannun sa.
Babu jimawa, mahaifin AFNAN ya ɗaga murya, fuskar sa cike da fushi da gajiyawa:
“Kai! mun gama wahalar yau? Amma ba abin da na dawo dashi… babu komai a hannu! Babu abinci, babu kudi, babu abin da za a ci!”
ya tashi tsaye, kafafunsa sun danna ƙasa da ƙarfi, duk gidan ya girgiza. AFNAN ta tsaya cak, jakar ta a hannunta, zuciyarta na bugawa cikin tsoro amma ba ta nuna masa rauni ba.
“Baba… bani da abin da zan iya yi yanzu…” ta ce cikin murya mai laushi.
Amma mahaifinta bai rage ba ya matsa kusa da ita, hannu ya ɗaga a iska kamar zai kai mata bugu
“Kullum ina gaya muku abinda ya dace Kun san wahalar da na sha, amma komai babu tasiri! kullum kina zuwa aiki a wanan banzan Company Amman basu baki kuɗin da ya dace kafin akai wata ma kuɗin ya ƙare ke fito da miji kin kasa wallahi duk wanda na haɗu dashi sai na bashi auren ke baƙar ƙadddara ”
AFNAN ta sunkuyar da kai, idonta na ƙasa, ta ji wani zafi a zuciya ta miƙe hannunta kaɗan daga ƙasa amma fuskarta cike da rashin jin daɗi duk wanda ya tashi