Share this page
5 / 7
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 BACK FROM FLASHBACK AFNAN ta riga ta saba kalmar nan ta “bar min gida” ta zama kamar iska a kunnenta ba sabo ba ne ba sabon zafi ba ne amma duk da haka zuciya ba ta taɓa sabawa ba. A hankali ta fito daga ɗaki, kanta a ƙasa, jikinta har yanzu a gajiye ta hango IBRAHIM a tsaye a tsakar gida ta durƙusa kaɗan cikin ladabi: “Baba… ina kwana…” bai amsa ba sai wani irin harara mai kaifi ya watsa mata, kafin ta ɗaga kai ya fara “Har yanzu kina nan kina kwance kina bacci wata asara!” ta tsaya shiru. “Kin san talauci yana cinye ne amma ke kin kasa fita ki nemo kuɗi kina bachi kamar tsohuwar mayya” ya matsa kusa da ita. “Ina kuɗin aikin jiya? Ko kina raina ni ne da tun dawo war ke baki kawo su ba?!” Zuciyarta ta faɗi. Idanuwanta suka cika da ruwa ba ta ma san lokacin da hawaye ya fara zubowa ba sai kalmar da ta fi komai zafi ta fito daga bakinsa “Munafuka ƴar iska haihuwar asara !” numfashinta ya tsaya wannan kalmar ita ce abin da ta fi tsana a duniya. A hankali, cikin rawar murya ta ce: “Baba… wallahi ba a bamu komai ba kaye hakuri …” kafin ta gama ya tashi da masifa. “Ke ƙarya zaki min?!” ya sunkuya ya ɗauki takalmi ya wurga mata da shi. AFNAN ta ja baya da sauri takalmin ya bige bango ya faɗi ƙasa zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta juya da gudu ta shiga ɗaki kusan zai biyo bayanta da kaɗan ya rage ya doke ta amma sai ya tsaya Ya juya cikin haushi yana hura iska kamar wanda yake neman wanda zai huce wa zuciya. “Banza! mara amfani” Ya fita yana ci gaba da zagin banza da wofi. A cikin ɗaki AFNAN ta jingina da bango hannunta na kan ƙirjinta numfashinta yana fita da sauri hawaye na sauka a hankali. Amma ba kuka take yi ba kamar hawaye ne kawai ke fita zuciya kuwa ta riga ta gaji a hankali ta zauna ƙasa ta ɗora kanta a gwiwarta ta furta cikin murya mai rauni “Ya Allah" Ta tsaya tana kallon AFNAN a zaune a ƙasa, hawaye a fuskarta, zuciya cike da nauyi ta girgiza kai a hankali “banda abin ki me sabo a ciki…” ta faɗa da murya mai laushi amma cike da gajiya “ya kamata kin saba…” AFNAN ba ta ɗaga kai ba, kalaman sun shiga kunnent amma ba su sauka a zuciya ba “kin zo kina kuka…” Umma ta ƙara da cewa, “ki tashi kafin ya dawo ya ƙara miki na jiki.” Sai numfashin AFNAN kawai ake ji a hankali. Umma ta matsa kusa kaɗan “Ki je ki debo ruwa…” “daga nan kuma ki wuce gidan Malam Nazir… kin ji? jiya sun aiko suna buƙatar a wanke musu kaya.” ta ɗan tsaya, sannan ta ƙara "sai kin dawo… ki wuce aikin hotel ɗin ki.” Kalmar ta faɗi cikin sauƙi amma nauyinta ya sauka a zuciyar AFNAN kamar dutse. Umma ta juya. Ba don ba ta ji zafin ‘yarta ba amma ta san rayuwa bata bari a tsaya ana kuka AFNAN ta zauna na ɗan lokaci ta ɗaga kai a hankali. Ta share hawayen fuskarta da bayan hannunta numfashi ɗaya mai nauyi ta sauke. Ta miƙe tsaye. Jikinta har yanzu a gajiye amma zuciyarta ta riga ta saba da tura kanta gaba ta ɗauki guga. ta fita waje ba tare da ta ƙara magana ba. A rana ta ja… lokaci ya wuce ba tare da AFNAN ta ankara ba sakamakon wanke yayi mata yawa , a gidan Malam Nazir ta shafe lokaci tana goga kaya har hannunta ya fara ja, jikinta ya ƙara yin nauyi lokaci bai tsaya jiran ta ba sai da rana ta fara dusashewa kafin ta ɗaga kai karfe shida da rabi. Zuciyarta ta buga. “Ya Allah…” Ta faɗa a hankali, tana jin yadda lokaci ya kubuce mata kamar ruwa a tafki ba tare da ɓata lokaci ba , ta tattara kayan da gaggawa, ta ɗaure su, ta miƙa musu, sannan ta juya da sauri , gudunta bai tsaya ba sai gida Ta shiga kamar iska, ta ɗauki ruwa, ta watsa a jikinta cikin hanzari, ba tare da nutsuwa ba. Ta sa doguwar rigarta, ta ɗaura hijab ɗinta da hannu mai rawar gajiya. Umma na tsaye a gefe tana kallonta “ki tsaya ki ci abinci” AFNAN ta girgiza kai “zan makara Umma…” muryarta a gajiye amma cike da tsoro domin ta san makara ba ƙaramin laifi bane a wajen aikin nan ta ta jira amsa ba ta juya da sauri ta fita daga gida. Iskar yamma ta bugi fuskarta, amma ba ta tsaya jin ta ba. Gudunta take yi, zuciyarta na bugawa, ƙafafunta na ƙara jin nauyi har zuwa lokacin da ta hango NURA tsaye yake da babur ɗinsa, kamar wanda ya saba jiran ta da ya gan ta murmushi ya bayyana a fuskarsa. “Habibty…” Ya kira ta da muryarsa mai laushi. AFNAN ta tsaya na ɗan lokaci numfashinta yana fita da sauri babu lokacin magana. NURA ya fahimta bai tambaya ba kawai ya ce “Zo… hau.” ba tare da ɓata lokaci ba ta hau babur ɗin ya kunna suka tashi. Iska tana bugawa a jikinsu yayin da suke ratsawa cikin hanya zuciyar AFNAN na bugawa ba don gudu ba , amma saboda rayuwa da ke tura ta gaba ba tare da hutu ba a bakin hotel NURA ya tsaya ya sauka da sauri ta kalle shi na ɗan lokaci. “Na gode…” Ta faɗa a hankali ya ɗan murmusa “ki kula da kanki.” ta juya ta shiga cikin hotel ɗin ba tare da ta sani ba, wata sabuwar rana ta fara kuma wannan rana ba zata zama kamar ta jiya ba. AFNAN ta shigo cikin hotel da sauri numfashinta yana fita da ƙarfi, zuciyarta na bugawa saboda gudu da kuma tsoron makara ta taka reception idanuwa suka juya kanta. Oga nasu yana tsaye fuskar sa babu annuri “Yanzu kika ga lokacin zuwa aiki?” ya faɗa da murya mai kaifi AFNAN ta tsaya cak kanta a ƙasa hannunta na rawa kaɗan. “Sir… afuwa…” kafin ta ƙarasa, ya katse ta. “Afuwar ki bata biya min lokaci! Wannan hotel ba gidan wasan yara bane!” A gefe su HAMLA suna tsaye suna kallonta suna ɗan murmushi na raini wasu har suna dariya a ƙasa-ƙasa. Zuciyar AFNAN ta matse junyar ta rufe ta gaba ɗaya saboda akwai mutane masu shiga da fita Idanuwanta suka cika da hawaye— amma ta ƙi su zubo ta ƙara sunkuyar da kai. “Sir wallahi” “shiru!” ya tsawata “Idan baki iya aiki ba, akwai waɗanda suke jira wanan opportunity in !” kalmar ta soki zuciyarta a wannan lokacin ƙofar hotel ta buɗe. YAZID. Ya shigo cikin nutsuwa, yana ɗauke da class ɗinsa nan take ma’aikata suka fara gaishe shi: “Good evening sir…” “welcome sir…” ya amsa cikin murmushi. Yana karɓar key, sai idanunsa suka sauka kan AFNAN ya tsaya ya ɗan ɗaga gira. Kamar yana tuna wani abu. Ita ce yarinyar da bata murmushi nan everytime AFNAN ta ɗan ɗaga kai a hankali idanunta suka haɗu da nasa nan take ta gane shi. Wani ɗan kunya da mamaki suka haɗu a zuciyarta YAZID ya juya ya kalli oga nasu. “Is there any problem?” ya tambaya cikin nutsuwa Oga ya ɗan gyara tsayuwa. “A’a sir… just a small issue ” YAZID ya katse shi da sauƙi. “It’s okay let her be.” muryarsa ba ta da tsawa amma tana da nauyi nan take wajen ya yi shiru. Oga ya ɗan sunkuyar da kai. “Okay sir…” AFNAN ta tsaya kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba a karo na farko namiji ya tsaya mata kamar Nura ta ɗan ɗaga kai ta kalli YAZID hankali ta ce: “Thank you…” muryarta ƙasa-ƙasa. YAZID ya ɗan murmusa ba tare da ya ƙara magana ba ya juya ya tafi amma murmushin yana nan a fuskar ta ta tsaya na ɗan lokaci ta ja numfashi a hankali. Ta share hawayen da suka kusa zubowa ta juya ta koma aikinta. Cikin dare hotel ya sake yin shiru. VIP floor ya nutse cikin bacci mai nauyi. Ko motsin takalma ba a ji sai ƙarar AC da ke busa iska a hankali. A reception kowa ya samu wuri ya kwanta ko ya jingina gajiya ta yi musu yawa wayar ta fara ringing… Tring… Tring… HAMLA ce ta miƙe a kasala, ta ɗauki wayar. “Reception…” ta faɗa cikin muryar bacci. Daga ɗaya ɓangarenmuryar sanyi: “Coffee. Room 18.”Hamla ta ɗan ja baki. “Okay sir…” ta ajiye wayar ta juya ta kalli sauran. JOHN ya buɗe ido kaɗan. Dukansu sun san ma’anar hakan Hamla ta ɗan yi shiru. ta kalli inda AFNAN ke jingine bacci ya ɗauke ta sosai. Gajiya ta bayyana a fuskarta. John ya ɗan motsa. “Wake her up…” ya faɗa a hankali. “Her duty.” Hamla ta ɗan ɓata fuska. “Eh… ai aikinta ne.” ta matsa kusa da AFNAN. Ta girgiza ta kaɗan “Afnan…” babu motsi a ƙara girgiza ta “Afnan! Ki tashi… Room 18.” AFNAN ta motsa kaɗan amma baccin ya yi mata nauyi. Idanuwanta sun buɗe rabin. Sai ta sake rufewa Jikinta ya gaji sosai. Hamla ta ja tsaki ta miƙe tsaye. “No… ni zan kai.” Ta faɗa cikin ɗan girman kai. John ya kalle ta. “Are you sure?” ta ɗaga kai. “It’s my turn.” ta faɗa da larabci cikin ɗan ƙarfi. Amma a zuciyarta ba aikin bane ya dame ta. wani abu ne daban , a gefe guda AFNAN ta juya kaɗan a kan kujera tasake nutsewa cikin bacci ba ta san abin da ke faruwa ba. HAMLA ta tsaya a gaban ƙofar zuciyarta na bugawa kaɗanba don tsoro ba, sai don wani abu da ta kasa fassara ta gyara jikinta, ta ɗaga tray ɗin coffee ta danna bell. Ding bai ɗauki lokaci ba ƙofar ta buɗe. HAMLA ta ɗaga kai sai ta tsaya cak. NADIR. Babu riga a jikinsa kamar dai yadda ya saba baison tufafi Hasken ɗakin ya sauka a kan jikinsa, ya bayyana tsari da ƙarfi jiki irin na wanda ya saba da wahala, da nasara. HAMLA ta kasa janye idonta. Kallon ya wuce na mamaki ya shiga sha’awa. Numfashinta ya ɗan rikice zuciyarta wani buri ya motsa “da ace…” Amma kafin tunaninta ya nisa muryarsa ta katse komai. “Coffee?” Ya faɗa a hankali, idanunsa suna kallonta kai tsaye kallon nan mai nauyi. mai cike da kwarjini. HAMLA ta ji jikinta ya ɗan sanyi ta miƙa tray ɗin da hannu mai ɗan rawa “Yes… sir…” NADIR bai karɓa nan take ba ya ɗan matso kaɗan. Idonsa ya tsaya a kanta. Kamar yana bincike ya tambaya cikin sanyi: “Aren’t you the one from last night?” kalmar ta tsaya a kunnenta zuciyarta ta bugawa da ƙarfi ta rikice ta san yana nufin wani amma ba ita ba ta haɗiye yawu. Kai tsaye ta girgiza kai. “No… Kalmar ta fito da sauri ba tare da tunani ba. NADIR ya ɗan tsaya Idonsa bai bar nata ba kalmar yana neman gaskiya a ciki amma bai ce komai ba ya karɓi coffee ɗin a hankali. “Alright…” Ya faɗa cikin sanyi ya juya ya shiga ciki ya rufe ƙofar. Click. HAMLA ta tsaya a wajen numfashinta har yanzu ba a daidaita ba. Amma a zuciyarta abu ɗaya ne yake: Ba ta ji daɗi ba saboda ta gane bai gan ta ba ba ita yake nema ba 💔✨ 🔥 https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W 🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬 Who's that girl BY NARNAH KANWAR SOJA 15 / 04 /2026 PG 14 & 15 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 DAY 4 FATE STRIKES Duk sun yi sign night shift ta ƙare kowa ya watse wasu cikin hira, wasu cikin gajiya, wasu ma da dariya amma AFNAN ta fito ita kaɗai jikinta a gajiye kamar kullum zuciyarta kuma cike da tunanitana warware wa tana sakawa yau kuma ko ya zagaye da Bana ba a bata komai ba , anyar ta yi shiru. Iskar safiya na busawa a hankali, tana ɗauke da sanyi mai taɓa fata. AFNAN na tafiya a hankali… kafafunta na ja sai dogon hamma take, ta buɗe baki kaɗan ta rufe idonta na ɗan lokaci. A wannan daƙiƙar ƙaddara ta motsa wata mota ta fito da gudu daga gefe birke ya kufce ke a alamar tsayawa wani mutum daga nesa ya yi ihu “Ke guje !!!” amma lokaci ya riga ya kure AFNAN ta ɗaga kai idanuwanta suka buɗe cike da firgici haske ya bugi idanunta zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci motar ta kwashe ta a jikin gini sanan ya bugu da kefen wani shago Jikinta ya tashi sama kaɗan ta faɗi ƙasa da ƙarfi booom, komai ya tsaya mata na ƴan dakiƙu ta kasa gane shin a duniya take ko a lahira kafin ta yanke jiki hannun ta ya fadi ta suma , jni ya fara zubowa a gefen kanta a hankali hijab ɗinta ya ɗan zame. Idanuwanta a rufe jikinta babu motsi mutane suka fara taruwa “Subhanallah!” “an buga ta!” “A kira taimako , ambulance” motar ta tsaya can gaba amma wanda ke ciki bai fito nan take ba wannan lokaci a nesa kaɗan wani mota ya tsaya sakamakon an fara chunkusu , Hayaniya ta fara tashi a wajen mutane suna taruwa wasu suna kallon jikin AFNAN da ke kwance a ƙasa, jini na fita a hankali daga gefen kanta. “Ku kira ambulance!” “ta bugu sosai!” Amma kafin wani ya ɗauki mataki wata mota ta tsaya da ƙarfi kusa da wajen. Ƙofar ta buɗe da sauri. YAZID ya fito cikin gaggawa, fuskar sa cike da firgici. “Move!” ya faɗa da ƙarfi mutane suka ba shi hanya Idanunsa suka sauka kanta sai zuciyarsa ta buga ita ce yarinyar jiya wadda ya mata magana akan rashin murmushi tamkar koyaushe bata cikin walwala Yazid ya sunkuya da sauri, ya ɗaga kanta a hankali. “Hey… can you hear me?” babu amsa numfashinta na fita da wahala jinin yana ƙaruwa zuciyar Yazid ta cika da tausayi. “Damn…” Ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauke ta a hankali kamar wani tsunma ya cire mata hijjab in ya daure mata kanta dashi saboda jinin ya rage zuba, ya nufi motarsa ya buɗe ƙofar mota ya kwantar da ita a seat ɗin baya ya shiga Motar ta tashi da gudu Hanyar ta zama kamar ba ta da nisa. Bugun zuciyarsa yana ƙaruwa. Idanunsa lokaci-lokaci suna kallon madubin baya inda AFNAN ke kwance ba motsi. “Stay with me…” ya faɗa a hankali. Kamar tana ji Bayan mintuna kaɗan motar ta tsaya a gaban wani private hospital ya fito da sauri, ya buɗe ƙofar baya. “HELP!”a’aikatan asibiti suka fito da stretcher suka ɗauke ta da gaggawa. “Emergency!” suka shige da ita ciki Yazid ya tsaya a waje numfashinsa na fita da ƙarfi hannunsa ɗauke da jinin ta kaɗan. Ya kalli hannun nasa ya ɗan rufe ido a zuciyarsa tambaya guda: “Why her…?” Cikin mintuna kaɗan likitoci suka shigo da gaggawa. “Emergency case!” suka ɗauke AFNAN zuwa ɗakin kulawa an tsaftace jinin an daure raunin da ke kanta aka saka mata drip komai cikin sauri, cikin ƙwarewa a hankali numfashinta ya daidaita jikinta ya kwanta kamar wata yarinya da ta gaji da rayuwa likita ya fito ya kalli YAZID. “She’ll be fine… but she needs rest. At least 12 hours kafin ta farka.” Yazid ya sauke ajiyar zuciya. “Thank you.” bai tsaya tunani ba ya biya duk kuɗin da ake bukata ba tare da tambaya ba. ——— Ba a jima ba labari ya fara yaɗuwa. “Celebrity ya kawo wata yarinya hospital…” mutane suka fara taruwa wayoyi suna ɗaukar hoto wasu suna rada “ba shi bane"” “Eh… Yazid! A mma shi bai damu ba ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin ya ɗan buɗe ƙofar kaɗan ya kalle ta. AFNAN tana kwance idanuwanta a rufe fuskar ta yi lagwai kamar wacce ta shekara a kwance a wannan karon ba ya ganin ma’aikaciyar hotel yana ganin yarinya mai rauni ya rufe ƙofar a hankali. Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya tafi ya koma hotel a shiga ɗakinsa kai tsaye ya shiga bathroom ruwan shower ya sauka a jikinsa yana wanke gajiya, amma ba tunani ba. Bayan ya gama ya fito Ya cire rigar jikinsa… ya tsaya a gaban mirror ya ɗauki towel ya goge fuskarsa ya girgiza kai. “Focus…” a yau training na jiransa amma a zuciyarsa akwai wani abu da bai gama fahimta ba me yasa wannan yarinyar… take shiga cikin tunanin sa haka? " Baban Na'em kasan bata taba haka don Allah kaje Hotel in nasu yanzu dube har yamma ta gabato amman Afnan bata dawo gida ba wanan ba halin ta bane " hararra ya ballata mata " ba halin ta bane hali nane kinan ne nace kar ta dawo To Allah yasa ma ta tafe har abada kar ta dawo ta mutu a chan kowa ma ya huta " " INNALILLAHI WAI'NA ILLAHIN RAJION" abinda tace kinan ta tashi tace Allah baka haƙuri bare naje na duba ta da kaina ta" bata gama magana ba ya zabura" Allah ya isa idan kika fita ban yafe ba " yabar gidan Umma ta zauna ta buga uban tagumi sai ga hawaye a idon ta " shin laifin waye nice da na haife ta ko kai da ka bani cikin ta, Allah ya riga ya bamu me yasa Ibrahim ka sanja akan haihuwar Afnan , Allah ya kare min ke a duk faɗin inda kike " " Assalamu alaikum" ana daff da kiran magriba saiga ta tashigo da leader magani da bendage a goshin ta " Wa alaike ke kuma don kutumar ubanki daga ina kika kike ke kuma daga inda kika fito daman bamu gayyaci ke duniya ba kikazo " cewar Baba dake shirin fita zuwa dabbar sa ta bayan sallah magriba " Baba daman nayi hatsari ne shine shine " shine me me yasa baki mutu ba ko kin shiga duniya ba shegiya munafukar banza ai da motan ya kwashe ke kin mutu na huta da haihuwar asara " wani ihu ta buga mai razanarwa wanda saidai ya girgiza saboda hakan bai taba faruwa yana magana ko motsi bataye sai gashi taye ihu ta wuce da gudu cikin dakin su ...... Umma ce dake sallah tana jinsu sai hawaye taye sallama ta rungume Afnan zata rarrashin ta " A'a Umma me zake cemin kinajin sa ya tsini min yau kuma cewa yake dama motan ya kashe ne ya huta Umma me nawa Baba me laifi na shin na hallici kaina ne ko zan iya sauya ƙaddara ta tabbas da ace na mutu na huta wallahi da na mutu na mutu kawai" sai kuka " bazan hanaki kuka ba kiye kuka Afnan wallahi bazan san zafin da ƙona da zuciyar ke take ciki ba amman Uba kine dole ke ha'kura, kiye masa biyayya ina mike fatan ke samu mijin aure nagari wanda zai share miki wanan bakin ciki Allah yasa iyakar ƙaddara ke kinan"................ Jama'a kamar nayi kuka , bare na tsaya da typing NARNAH KANWAR SOJA https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W 🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬 Who's that girl BY NARNAH KANWAR SOJA 17/ 04 /2026 16 & 17 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 ✨ Ku garzayo ku ci gajiyar wannan dama nesa ta zama kusa, ilimi yana hannunku! ✨ QUEENS OF ELEGANCE CREATION 👑✨ 📢 Albishir ga masu sha’awar koyon sana’ar hannu! Da ƙaramin jari za ki fara kuma ki samu albarka 💰 🎓 Muna gudanar da ONLINE CLASS mai sauƙi da araha 📌 Abubuwan da za ki koya: • Sarka da kunne (Necklace & Earrings) • Earring resin • Frame making • DIY Clock • Ecocraft • Gypsum work • Siliya work • Beads (Bead work) • Glitters work • Abaya designing 💸 Kowanne class: ₦2,000 kacal! 🔥 Kar ki bari a baki a baya – ki koyi sana’a ki dogara da kanki! 📩 Tuntuɓe mu yanzu don fara registration! 0708 874 7068 AFNAN THIS PAGE IS FOR U AISHATU USMAN ENJOY "Assalamu alaikum" Ta amsa tana ɗan sunkuya da kai tana kakkaucewa kai tsaye ya zauna akan saman dutse kofar dakin ya fara magana kamar yana karkarwa " Umma Barka da dare yanzu Zaid ya kira ne wai Afnan ba lafiya kina nema na " eh Nura tana ciki zata fito ku gaisa kasan wanan lokacin ne Baban naku baya gida naci don Allah ka taimaka kaje min gun aikin ta kaye musu report taye hatsari ko hutun sati biyu ne su bata " Yana sauraron rabin maganar hankalin sa na kan kofar ko zata fito " to Umma badamuwa Allah ya sawwaka" Afnan ce ta fito ta na dafa kanta dake juya mata kamar wainar fulawa a kasko nuna suka gaisa , ganin haka Ummah ta shiga ciki ta barsu " Sannu habibty garin ya haka ta faru" nan ta kwashe komai ta gayyamai paper hannun ta ta bashi yakai office na manager su haka kuwa akayi ganin bata son yawan magana yace " sai da safe ya juya ya tafe ciki da damuwa da alhinin rayuwar Afnan ......... ## Yazid ne ya sauka daga taxi da yahau a bakin asibitin yana shiga direct dakin ta ya nufa sai dai ganin wata tsohuwa ce a ciki ya bashi mamaki yana juyawa ya hango wata Nurse yake tambayar ta ko akwai abin da ya faru da patience nasa da ya kawo da safe bai samu dawo wa ba sakamakon yau sun fara wasa su na farko , " amsar da ta bashi ne ya bashi mamaki har ya kuma cikin hotel in da cewa " who's that girl " Yana shigowa Nura na fitowa daga office na Manager nan suka gaisa karon farko da yaga celebrity a rayuwarsa jikin sa na karkarwa har ya dawo gida yana tunanin ganin Yazid da irrin kwarjinin sa da kamallar sa tabbas Yazid yana daga cikin ƴan wasa masu matukar muhimmanci da farinjinin mutane wanda kusan ana kirar NADIR za'a ce Yazid kuma shi kaɗai ne me gayawa NADIR duk maganar da yake so ba tare da shakkar sa ba ..... DAY 5 Bayan reception ta karɓe korafi Afnan an sauya sunan ta da wata ma'aikaciyar wacce ta kasance babban macce ce

Chapter 5 of 7