masifa zaice ittace baƙar ƙaddarrsa tunda ya haife ta ya talauci bala'e yake sauka akan sa bai ƙara rigi abin arziki ba...
A haka ta shiga ɗaki taja Labule ta kife akan guiwarta tana rusar wani kuka da Babo hawaye
A ɗaki kuma, Umma ta ɗan shigo kusa da ita, ta ɗan dafa kafaɗarta : “Ki jure… haka rayuwa take… amma ki tuna, nagarta da basira zasu sa komai ya zo miki, idan da sabo kin saba da wanan maganar me zaisa ke ta da hankali ke ke fita ko zaki samu mana wani abinda zamu ci”
AFNAN ta ɗan yi murmushi a ranta, ta ɗan miƙe kai, bayan ta fito daga ɗakin, AFNAN ta tsaya cak, zuciyarta na bugawa cikin nauyi. Kalaman mahaifinta sun shiga zuciyarta kamar ƙugiya mai kaifi:
“Dukan ku! Haihuwar asarar, duk na talauci! aikin da kike zuwa na banza ne! Sai wata za a ba ku kuɗi, wanda ba zai wuce shinkafa biyu ba!”yana tafiya, ya bar gidan cikin shiru amma fushinsa ya barsu cikin ɓacin rai.
A cikin ɗaki, Umma ta zauna a gefen tebur, idonta na ƙasa, tana kallon su. Yara biyu, ƙananan ‘yan uwan AFNAN, suna kuka cikin ɓacin rai fuskar su cike da yunwa, hannayensu sun fara rawa.
AFNAN ta tsaya kusa da su, ta ɗan rufe fuskar ta da hannunta ta kalli burodi ɗaya da ruwa da suka rage, zuciyarta na cike da damuwa ta ji wani irin zafi a ciki, ganin yadda rayuwar su take cike da rashin kulawa, talauci, da wahala.
“Duk wannan… duk saboda rashin samun dama… da rashin taimako… amma wata rana… wata rana…” ta ce a ranta, tana ƙoƙarin rike kuka.
Daga gefen ɗakin, Umma ta ɗan tsinke hannu, ta ce cikin murya mai rauni:
“Ku jure, yarana"
AFNAN ta ɗan yi murmushi kaɗan, ta ɗan matsa ƙaninta cikin ƙauna, sannan ta ɗan zauna kusa da su, tana mai cewa a ranta:
“Ko da yake duniya bata bani sauƙi… zan tsira. zan tsira da kaina… kuma wata rana, zamu bada labari”
Washegari, Ba komai a gidan AFNAN ta farka da yunwa a ciki, tana jin rauni da gajiya sosai ta fita daga gida, zuciyarta cike da nauyin yunwa yayin da take tafiya, tana tunanin Ummah da rayuwar ta a baya, yadda take ƙaunar taimakawa amma ba ta da iko.
Ta shiga maƙobta, ta fara musu aiki, tana ɗaukar abubuwa da sauƙi, hannunta na rawa saboda yunwa da rauni. Ta samu ɗan hatsi, kadan kaɗan da ta tazo gida, ta fara dafawa su ZAIN, zuciyarta na cike da rauni, numfashi mai raɗaɗi. Idonta ya ƙasa, amma ta ci gaba da aiki, tana kallon yaran da ke jiran abinci da tsananin yunwa.
AFNAN ta ɗan matso kusa da kofa, ta ɗan girgiza kai a hankali, zuciyarta na cewa “Haka rayuwa take…
SUDAN
Sudan Khartoum National Stadium. NADIR ya zauna a cikin ɗakin dressing room, yana shan ruwa bayan nasarar da suka samu akan Sahara United. Jersey ɗinsa ja da zinariya ya ɗan danshi da zufa, gashi baƙi mai tsabta ya dan faɗi a fuska, amma idanunsa sun cika da nutsuwa da ƙarfin zuciya.
“Another win… another day,” ya ce a ransa, yana dan murmushi. Amma kamar kullum, zuciyarsa tana neman sabbin abubuwa da excitement.
Bayan ya fito daga dressing room, sai ya ji wasu matasa suna hira a club ɗin da yake zuwa: maye mata, kuɗi, motoci masu tsada — abin da NADIR yake so sosai. Ya shiga motarsa mai kyau, ya tafi club, inda kiɗa ke girgiza ginin, mutane suna rawa da dariya, mata suna kallon sa.
NADIR ya yi nuni da cewa, “Babu abin da zai tsaya a gabana… duniya tana nan a ƙasa ta.”
Nan ƴan team nasu suka ƙarasu aka chigaba da nishaɗi samun cup..
🤗🤷🤷🤷🤷🤷🤷🤷🤷
https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t
FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 17 Novel
DISTENY LOVE STORY
04 / 04 /2026
PG 4
HAPPY WEEKEND
ENJOY YOUR DAY
SUDAN
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
HIKIMAR MARUBUCIYA
Hikimata abin alfahari na ne, domin rubutu baiwa ce da Allah ke ba wa wanda Ya so. Marubuci na da damar gina duniya da kalmomi, ya tsara rayuwa da zubin alƙalami, ya nuna darasi cikin labari.
Kalma na iya zama haske ga mai duhu, ko darasi ga mai kuskure. Don haka marubuci na rubuta ne domin ilmantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa.
Idan ka ga labari ya yi kama da rayuwa, to ka sani zubin alƙalami ne kawai, domin rubutu baiwa ce da ke tafiya da tunani da hikima.
SUDAN
MORNING
Karfe shidda saura ya miƙe daga gadon ya juya yaga Falisha na bacci ya kai da kai ya shiga toilet tsarki ya wanke fuskar sa yayi ya mayar da t-shirt nasa da gajeren wando sa , ya juya ya fita ya barta kwance ya fita yana murza idon sa yana buƙatar ya isa gida yayi wanka me kyau ya sauya rigar nan jinsa yake a takure ɗaukan Cup nasa yayi ya fito mutane suna bashi hanya kamar sarki yana wucewa.
“King of Atlas! gd morning sir ” wani ya yi ihu daga baya.
NADIR ya ɗaga hannu kawai, murmushi a fuskarsa amma idanunsa suna nuna gajiya kaɗan. kowa da abinda yake kira sa dashi nan ya shiga motar sa driver da na jiran sa , ajiyar zuciya yayi saboda ya tsani media yasan da cewa tsaff zasu iya neman inda yake ganin ba komai ya lumshe idon sa sakamakon bachin ma bai ishe shi ba saboda yasha barasa ba kaɗan ba..
Motar Rolls-Royce ɗin ta shigo cikin Royal Palm Estate a cikin Khartoum a hankali, fitilun titin estate ɗin suna walƙiya a kan jikin motar mai baki kamar madubi tsaro a bakin gate suka miƙe tsaye suna girmamawa.
“Barka da dawowa, Sir.”
Driver ɗin ya yi parking a gaban babban villa ɗin NADIR kofar motar ta buɗe a hankali, sai ya fito a sanyaye ma’aikatan gidan guda biyu suka yi saurin matsowa.
“Barka da dawowa, Master Nadir.”
ya ɗan ɗaga hannu kawai alamar gaisuwa ya saba da wannan rayuwa ba tare da tsayawa ba ya wuce cikin babban hall ɗin gidan. Chandeliers masu walƙiya suna rataye daga sama, ƙasa kuwa marmara ce mai tsabta kamar ruwa.
Ya nufi private wing ɗinsa — ɓangaren gidan da kowa ba ya shiga sai da izini acan ne aka shirya masa komai na rayuwar alfarma.
Ya ajiye cup ɗin champagne ɗinsa a kan wani table na crystal, inda wasu award suke rataye a cikin glass da ƙaton albulm nasa dake. Nuna cewa yaci world cup 2017sannan ya wuce cikin makeken bathroom ɗinsa.
Toilet ɗin ya fi wasu ɗakuna girma bangon sa marble ne fari mai ɗan launin gold. Madubai masu tsawo suna haskaka ɗakin, gefe kuma akwai bathtub mai faɗi kamar ƙaramin pool a cikin bathtub ɗin, ruwan wanka yana cike da kumfa masu laushi, petals na flowers suna yawo a saman ruwa, kamshin turare mai sanyi yana cikewa a cikin ɗakin.
NADIR ya cire kayan jikinsa a hankali, ya shiga cikin ruwan wankan.
Zafin ruwan ya ratsa jikinsa kamar yana cire duk gajiyar da ya tara daga wasan jiya
Ya jingina kansa a bayan bathtub, ya lumshe idanu ,numfashinsa ya fita a hankali awannan lokacin ya ji natsuwar gida natsuwar da ba a samu a filin wasa ko a cikin hayaniyar duniya.
A hankali ya furta a ransa:
“Home…”
Ruwan kamshi da flowers suna motsi a hankali a saman ruwa, yayin da NADIR ke jin daɗin hutun da kuɗi da nasara suka kawo masa ruwan ya riga ya sauƙaƙa masa jiki, gajiyar da ya tara daga wasan yau ta lafa kamar ba ta taɓa wanzuwa ba.
Ya miƙe daga cikin bathtub ɗin, ruwan yana zuba daga jikinsa a hankali ya sauko kan marmara mai santsi.
Ya ɗauki towel mai kaushi na alfarma daga kan rack ɗin zinariya, ya nade jikinsa da shi. Kamshin turaren wankan da flowers har yanzu yana biye da shi.
Ya nufi gaban babban mirror ɗin da ke cikin bathroom ɗin da farko ya ɗauki brush ya fara goge haƙoransa cikin nutsuwa, yana kallon kansa cikin madubin.
Bayan ya gama, ya ɗauki wani ƙaramin towel ya goge gashin kansa da kyau.
Sai ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito zuwa cikin bedroom ɗinsa a tsakiyar ɗakin akwai dogon mirror mai tsawo daga ƙasa har sama.
Ya tsaya a gabansa na ɗan lokaci.
Tsayin jikinsa ya bayyana sosai a cikin madubin.
NADIR saurayi ne mai kyau sosai hancin sa tsaf kuma daidai, bakin sa yana da siffa mai kyau, idanunsa farare masu zurfi suna ƙara masa kwarjini. Fatar jikinsa mai launin chocolate tana ɗaukar hasken ɗakin tana ƙara masa kyau.
Jikinsa kuwa irin na ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne — tsoka mai ƙarfi, kafadu masu faɗi, da ƙirji mai kyau wanda gym ya gina tsawon shekaru ya ɗauki dryer daga kan dressing table, ya fara busar da gashin kansa a hankali.
Iskar dryer ɗin tana motsa gashin sa baƙi mai santsi, har sai da ya gyara shi cikin salon zamani, da ya gama, ya kalli kansa a madubi na ɗan lokaci.
Wani murmushi mai sauƙi ya bayyana a fuskar sam ba wai saboda kyawunsa ba…
Sai dai saboda ya san cewa rayuwa tana tafiya yadda yake so.
NADIR ya ɗauki wayar.
Da ya duba screen ɗin, sai murmushi ya bayyana a fuskar sa.
MOM ❤️ ya ɗauka nan take.
“السلام عليكم يا أمي.” a ɗaya ɓangaren kuwa aka amsa da murya mai cike da farin cik.
“وعليكم السلام يا حبيبي… مبروك الفوز!”
( Wa alaikum salam ya ɗana… murna da nasara!)
NADIR ya yi murmushi yana shafa gashin kansa.
“شكراً يا أمي.”
(Na gode Mama.) sai aka ji wata murya ta shiga daga gefen ta.
“افتح الفيديو يا بني.”
(Buɗe video call ɗin mana ɗana.)
NADIR ya ɗan yi dariya kaɗan ya kunna video call nan take fuskar MOM da DADDY suka bayyana a screen.
Suna zaune a wani ɗaki mai sauƙi amma mai tsarki — a bayan su ana hangen hasken Madina ta taga.
DADDY ya yi murmushi mai girma.
“نحن نعلم منذ البداية… أننا أنجبنا ذهباً.”
(Mun sani tun farko… cewa zinariya muka haifa.)
Sai MOM ta ɗora da farin ciki.
“أنت تستحق الكأس… بل الكأس هي التي تستحقك.”
(Koffi ne ya dace da kai , bawai kai ne ka dace dashi ba.)
NADIR ya ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa a duk duniya babu abin da yake girmamawa kamar iyayensa , ya ce cikin nutsuwa:
“دعواتكم فقط.”
(Addu’arku kawai nake buƙata.)
MOM ta ɗaga hannunta cikin salo na addu’a.
“الله يحفظك يا ولدي.”
(Allah ya tsare ka ɗana.)
DADDY ya yi murmushi yana cewa:
“نحن فخورون بك.”
(Muna alfahari da kai.)
NADIR ya ji wani irin daɗi ya ratsa zuciyarsa.
Duk hayaniyar duniya, duk farin jinin da yake samu amma kalaman iyayensa su ne suka fi masa daraja ya ce cikin girmamawa:
“سأزوركم قريباً إن شاء الله.”
(Zan zo na ziyarce ku nan kusa in sha Allah.)
MOM ta yi murmushi.
“ننتظرك يا حبيبي.”
(Muna jiran ka ɗana.)
Da ya kashe call ɗin, NADIR ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon screen ɗin wayarsa ya sauke numfashi a hankali rayuwarsa cike take da nasara…
amma bai san cewa a ƙasar Morocco wani abu ne daban zai jira shi ba.
Abu da zai sauya komai.
AFNAN.
Yana ajiye wayarsa a kan table ɗin gefen gadonsa.
Sai wayar ta sake runguma da ringing.
NADIR ya ɗan kalli screen ɗin ba tare da gaggawa ba.
COACH HAMZA
Ya ɗan kauda kai kamar wanda ya gaji da kiraye-kirayen bayan nasara wayar ta kusa yankewa kafin ya ɗauka.
“Hello, Coach.”
A ɗaya ɓangaren aka ji muryar Coach Hamza mai cike da kuzari.
“Congratulations, champ.”
NADIR ya yi murmushi kaɗan.
“Thank you, coach.”
Coach Hamza bai ɓata lokaci ba, ya shiga magana kai tsaye.
“Get ready… Morocco is calling you.”
NADIR ya ɗan ɗaga gira kaɗan.
Coach ya ci gaba:
“Next week we are flying to Morocco zan turo maka da flight ticket ɗinka yau ko gobe. The whole team will be there.”
NADIR ya ɗan jingina da kujerar da yake kai.
Ya sauke numfashi a hankali kamar wanda yake jin sabon ƙalubale yana zuwa.
“Alright coach… I’ll be ready.”
Coach Hamza ya yi dariya kaɗan.
“I know you will. Atlas Kings need another victory.”
NADIR ya kalli kofin zinariya da ke kan shelf ɗin ɗakinsa haske daga fitila yana walƙiya a jikinsa.
Ya ɗan murmusa.
“Don’t worry coach…”
Ya ɗan yi shiru na daƙiƙa guda, sannan ya ce cikin tabbaci:
“Another victory is calling me.”
Coach Hamza ya yi dariya mai gamsuwa.
“That’s the spirit see you soon.”
Call ɗin ya ƙare.
NADIR ya tsaya a tsaye a tsakiyar ɗakin nasa mai girma.
Idonsa ya sauka kan golden cup ɗin.
Sai ya ɗaga shi a hannu, yana kallon haskensa.
“Morocco…”
ya faɗa a hankali.
Bai san cewa wannan tafiya ba wai wasa kaɗai zai je yi ba.
A can ne ƙaddararsa zata jira shi.
AFNAN.
FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 17 Novel
DISTENY LOVE STORY
08 / 04 /2026
PG
SUDAN & MARROCO
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
HIKIMAR MARUBUCIYA
Hikimata abin alfahari na ne, domin rubutu baiwa ce da Allah ke ba wa wanda Ya so. Marubuci na da damar gina duniya da kalmomi, ya tsara rayuwa da zubin alƙalami, ya nuna darasi cikin labari.
Kalma na iya zama haske ga mai duhu, ko darasi ga mai kuskure. Don haka marubuci na rubuta ne domin ilmantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa.
Idan ka ga labari ya yi kama da rayuwa, to ka sani zubin alƙalami ne kawai, domin rubutu baiwa ce da ke tafiya da tunani da hikima.
🔥
Bayan ya gama waya da Coach Hamza, NADIR ya ajiye wayarsa a kan table ɗin gefen gadonsa ya ɗan miƙe a hankali, ya duba agogon da ke rataye a bango lokaci ya ja cikin nutsuwa ya nufi dining area na private suite ɗinsa.
A kan babban marble dining table, an riga an shirya masa karin kumallo na masu abu kamar yadda yake saba.
Plate ɗin farko na ɗauke da scrambled eggs masu laushi da aka yi da butter a gefe akwai grilled sausages masu kamshi da aka yayyafa musu black pepper.
A wani ƙaramin plate akwai croissant masu laushi da aka shafa butter, sai pancakes masu zuma suna ɗan ƙyalli a ƙarƙashin hasken ɗakin.
A gefe kuma akwai bowl na fresh fruits — strawberries, apples, grapes da slices na orange masu ɗauke da ɗan ɗan sanyi a cikin crystal glass kuma akwai fresh orange juice mai ɗan sanyi.
NADIR ya zauna a kujerar dining ɗin yana ajiyar zuciya, ya ɗauki fork da knife a hankali kamar yadda aka koya masa tun yana ƙarami.
Ya fara da eggs, yana cin su a nutsuwa, yana jin daɗin kamshin butter da pepper.
Bayan haka ya ɗauki croissant ɗaya, ya tsoma shi cikin zuma kaɗan kafin ya ɗan cije shi kamar yadda aka saba da shi, ba ya cin abinci cikin gaggawa , komai nasa cikin natsuwa yaki baison yawan motsi,
Bayan mintuna kaɗan ya ɗauki glass ɗin orange juice, ya sha a hankali har ya sauke shi ua goge bakinsa da napkin ya miƙe daga kujerar, ya koma bedroom ɗinsa ya buɗe walk-in closet ɗin da ke cike da kaya masu tsada.
Idonsa yana zagawa cikin shelves da drawers, yana duba abubuwan da zai buƙata domin tafiyar da ke gabansa.
Ya fitar da wasu kaya masu muhimmanci.
Jersey ɗinsa, sports wear, sneakers masu tsada, da wasu casual clothes ya tabbatar komai yana cikin tsari.
Da ya gama, ya rufe closet ɗin.
cikin nutsuwa ya dawo kan gadonsa mai siffa royal bed, a ɗauki wayarsa ya kunna flight mode.
Ba ya son a dame shi idan zai huta.
Ya jefa wayar a kan pillow gefensa aannan ya kwanta a kan gadon ya lumshe idanunsa.
jikin sa ya saki gaba ɗaya cikin softness na gadon.
Numfashinsa ya fara tafiya a hankali.
Cikin ƴan mintuna kaɗan…
NADIR ya nutse cikin bacci mai nauyi.
MOROCCO
Babban hall ɗin hotel ya cika da ma’aikata kowa ya tsaya a gaban notice board, wasu suna tura juna domin su ga sunayen da aka liƙa.
Wannan ba ƙaramin abu ba ne.
Tawagar Atlas Kings za ta sauka a hotel ɗin nan.
Saboda haka management ya fitar da sabbin shifts na ma’aikata — waɗanda za su kula da ‘yan wasan wasu na dariya wasu na addu’a.
Wasu kuma zuciyarsu na bugawa kamar za ta fito.
“Ya Allah ka sa sunana ya fito…”
“Insha Allah zan shiga VIP service…”
“Wallahi idan na shiga jerin nan rayuwata zata canza!”
Hayaniya ta cika wurin agefen board ɗin kuwa…
AFNAN ta tsaya shiru ta matso a hankali.
Idonta ya fara bin jerin sunayen.
Sunan sashen su na Food Service Department.
Ta bi layin sunaye ɗaya bayan ɗaya zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci.
Idonta ya faɗa kan suna guda.
AFNAN IBRAHIM
An rubuta shi cikin Night Shift – VIP Guest Service (Football Team).
Idonta ya faɗaɗa numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci ta sake kallon sunan kamar tana zaton kuskure ne.
Sai ta girgiza kai a hankali cikin mamaki
“مستحيل… كيف يحدث هذا؟” (Impossible… ya za a yi hakan?)
Ta sake matsowa kusa da board ɗin.
Idonta na sake duba sunan har yanzu yana nan ba mafarki ba ne.
Ta ɗan saki numfashi a hankali.
Sannan ta ce cikin murya ƙasa:
“أنا… في دوام الليل؟” (Ni… a night shift?)
Ta girgiza kai.
“هذا غير ممكن wannan ba zai yiwu ba) zuciyarta tana tunan “ni da na tsani ƙwallon ƙafa…
yanzu ni zan yi aikin kula da ‘yan ƙwallon duniya, kuma kowa yasan bana son aikin nan dare ?”
A gefe kuwa wasu ma’aikatan suna tsalle saboda farin ciki.
“Sunana ya fito!”
“Alhamdulillah!” “VIP service! na shiga!”
Amma AFNAN ta tsaya shiru zuciyarta cike da tambayoyi ta kalli sunanta sau na ƙarshe..
Kafafunta na ɗan karkarwa yayin da take ratsa cikin ma’aikatan da ke cike da murna.
Wasu suna dariya wasu suna shirin kiran iyalansu amma ita kamar ana ja da ita ne zuwa wani wuri ta nufi ƙaramin corridor da ke kaiwa office na Sir Auwal.
Shi ne Operations Manager na hotel — mutumin da ke kula da dukkanin ma’aikata da jadawalin shifts kuma shi ne ya rubuta wannan jerin sunayen.
AFNAN ta tsaya a bakin ƙofar ofishin.
Ta ɗan bugi ƙofar a hankali.
“Come in.” muryarsa ta fito daga ciki.
Ofishin ya cika da ƙamshin turare mai tsada.
Fayiloli da takardu suna jere a kan teburi.
Sir Auwal yana zaune yana duba laptop ɗinsa da0 ya ɗaga kai ya gan ta, ya ɗan yi murmushi.
“Afnan… lafiya?” amma kafin ya ƙara magana…
ta riga ta yi magana cikin gaggawa.
“Sir… don Allah.”
Muryarta tana ɗan rawa.
“Don Allah ku cire sunana daga list ɗin nan.”
Sir Auwal ya ɗan ɗaga gira cikin mamaki.
“Wane list?”
“Night shift… VIP service…” ta haɗiye yawu kafin ta ƙarasa.
“Don Allah… bazan iya ba kasan banason aikin dare kuma kuma .” maganar ta daskare a maƙokoronta
Ofishin ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sir Auwal ya jingina da kujerarsa yana kallon ta sosai sai ya ce cikin Larabci da murmushi kaɗan:
“لماذا؟” (Me yasa?)
AFNAN ta sauke idonta ƙasa.
“أنا لا أحب كرة القدم…” (Ba na son ƙwallon ƙafa…) ta ƙara da sauri.
“kuma… aikin dare ba nawa ba ne.”
Sir Auwal ya ɗan yi dariya a hankali.
“Afnan… kina bani mamaki.” ya ɗan matsa gaba kan teburi.
“Wasu ma’aikatan suna roƙona na saka sunayensu a wannan list ɗin.”
sai ya nuna takardun da ke gabansa.
“Amma ke kuma kina roƙona na cire naki.” ta yi shiru.
Hannunta na riƙe da uniform ɗinta kamar mai jin sanyi
“Kin san akwai allowance na musamman ga duk wanda zai yi wannan aikin saboda tare zaku na fita gari dasu ?” ta girgiza kai a hankali.
“ban damu ba, sir.”
Sir Auwal ya ɗan yi murmushi mai ma’ana.
“A gaskiya… dalilin da ya sa na saka sunanki ba allowance ba ne.”
AFNAN ta ɗaga kai ta kalle shi.
Sai ya ce a hankali:
“Saboda kin fi yawancin ma’aikatan nan na good service iya English duk da secondary kika gamasosai.” ya ɗan ɗaga yatsansa.
“Kuma tawagar da za ta zo akwai turawa a cikin shiyasa muka zabe wanda suka iya jin yaren su ba kowa ya iya larabci ba”
Ta yi shiru.
Maganar ta tsaya a makogwaronta.
Sai ya ƙara cewa:
“Na yi tunanin za ki taimaka min.” ya yi murmushi mai ɗan tausayi.
“Amma kin ƙi bani haɗin kai.” kalmomin sun shiga zuciyarta ta sauke idanunta ƙasa hankali hawaye sirara suka fara taruwa a idanunta.
Ba ta so ya gani.
Ta ɗan juya fuskarta kaɗan.
Sai Sir Auwal ya numfasa a hankali.
“Afnan…”
Muryarsa ta yi laushi.
“List ɗin nan an riga an tura shi zuwa management.” ya girgiza kai kaɗan.
“Bazai yiwu a sauya shi ba.” zuciyarta ta yi wani irin faɗuwa ta ce cikin rauni:
“Don Allah sir…”
Amma ya katse ta cikin tausayi.
“Ki ɗauki wannan a matsayin dama.” ya nuna ƙofar da hannu.
“Wata rana za ki gode min.”
AFNAN ta tsaya na ɗan lokaci kamar wadda take so ta ƙara magana amma kalmomin sun ƙare.
Ta goge hawayen da suka fara zubo a hankali ta juya ta fita daga ofishin ba tare da ta sake magana ba a corridor ɗin hotel ɗin…
ta tsaya na ɗan lokaci zuciyarta cike da wani irin nauyi.
Ba ta sani ba cewa…
wannan night shift ɗin da take gudu daga gare shi
shine Ƙaddara da zai canza rayuwarta har abada.
https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t
FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
My 17 Novel
DISTENY LOVE STORY
08 / 04 /2026
PG 6
SUDAN & MARROCO
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
HIKIMAR MARUBUCIYA
Hikimata abin alfahari na ne, domin rubutu baiwa ce da Allah ke ba wa wanda Ya so. Marubuci na da damar gina duniya da kalmomi, ya tsara rayuwa da zubin alƙalami, ya nuna darasi cikin labari.
Kalma na iya zama haske ga mai duhu, ko darasi ga mai kuskure. Don haka marubuci na rubuta ne domin ilmantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa.
Idan ka ga labari ya yi kama da rayuwa, to ka sani zubin alƙalami ne kawai, domin rubutu baiwa ce da ke tafiya da tunani da hikima.
🔥
A haka AFNAN ta ƙarasa aikin ranar bata san yadda ta gama ba jikinta a sanyaye, zuciyarta kuwa cike da wani irin nauyi da ba ta iya bayyana.
Ta fita daga hotel ɗin a hankali, tana tafiya a cikin titi mai