Share this page
4 / 7
yi dariya kaɗan. “Good girl.” “الابتسامة سنة.” (Murmushi sunnah ne.) ya ƙara da cewa: “كوني مبتسمة دائماً.” i kasance mai murmushi a ko yaushe) ya ɗauki tray ɗin daga hannunta. AFNAN ta ɗan sunkuyar da kai cikin ladabi. Amma a zuciyarta— har yanzu tana jin wani nauyi domin ba ta zo nan don jin daɗin haɗuwa da ‘yan ƙwallon duniya ba ta zo ne kawai… don aikinta ........... https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W 🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬 Who's that girl BY NARNAH KANWAR SOJA 11 / 04 /2026 PG 9 &10 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 HAPPY WEEKEND What if the man who broke you is actually the man you belong to?” Karfe 1:00 na dare. Shiru ya rufe VIP floor gaba ɗaya hasken fitilun na haskawa suna zuba haske mai sanyi a kan carpet mai kauri da ke shimfiɗe a corridor wurin ya yi tsit kamar kowa ya nutse cikin barci. AFNAN ta san cewa kusan dukkan ‘yan wasan sun gama order nasu babu sauran kiran komai tun 12am saboda gajiya, ta jingina a kan desk ɗin reception, ta ɗora hannunta a kai idanuwanta suka fara rufewa a hankali bacci ya fara ɗaukarta sai wayar reception ta fara ringing Tring… Tring… ba ta motsa ba. Wayar ta sake yin kara. Tring… Tring har yanzu AFNAN na cikin bacci sai a karo na uku TRING! ta firgita da sauri, ta ɗaga wayar ta kai a kunne “Hello sir… reception… good morning.” daga dayan bangaren dogon tsaki aka ja sai wata murya mai sanyi amma cike da gajiya ya ce: “Coffee… now. Room 18.” AFNAN ta lumshe ido na ɗan lokaci. “Okay sir.” ta ajiye wayar a hankali… sannan ta sauke ajiyar zuciya ta kalli agogo. 1:00 AM ta ɗan turo baki a ranta ta yi ƙaramar magana cikin ƙasa ƙasa “Wani mahaluki mahaukaci ne me shan coffee karfe ɗaya na dare…” amma aiki aiki ne ba ta da zabi ta miƙe tsaye ta nufi restaurant section, inda ta haɗa cup ɗin coffee mai zafi, sugar cubes, spoon, da ƙaramin biscuit a gefe ta shirya su a kan ƙaramar table mai taya. Kamshin coffee mai ɗan ƙarfi ya tashi cikin iska. AFNAN ta fara tura table ɗin a hankali cikin corridor VIP floor ya yi shiru sosai sai ƙarar tayoyin table ɗin kaɗai ake ji suna gogar carpet a hankali room 18 yana ɗan nisa kaɗan daga reception mintuna goma sha biyar tana tafiya cikin corridor mai tsawo. A ƙarshe ta tsaya a gaban ƙofar Room 18. ta gyara hijabinta kaɗan ta ɗan numfasa. zuciyarta tana bugawa a hankali saboda shiru da duhun dare ba don tsoro ba… sai don gajiya da kuma mamakin wanda yake shan coffee karfe 1:00 na dare. sai ta miƙa hannu ta danna bell. Ding… Ta tsaya tana jira ta sake danna shi karo na biyu ding har yanzu shiru ta ɗan numfasa a hankali a cikin zuciyarta ta ce: "Wane irin mutum ne wannan…?" ta ɗan matsa kusa da ƙofar, tana jiran amsa. a lokacin taji motsin takalma a hankali. handle na ƙofar ya motsa a hankali click kofar ta fara buɗewa kaɗan fitilar ɗakin ta haskaka corridor ɗin. AFNAN ta ɗan ɗaga kai amma har yanzu ba ta ga fuskar wanda yake ciki ba, kofar ta ƙara buɗewa… AFNAN ta ɗan ɗaga kai tana kallon ƙofar… tana jiran a buɗe ba tare da ta sani ba wannan ƙofar da take tsaye a gabanta… ita ce ƙofar da zata sauya rayuwarta har abada. Ƙofar ta ƙara buɗewa a hankali… Hasken ɗakin ya fito ya daki fuskar AFNAN, ya sa ta ɗan lumshe ido na daƙiƙa guda ta ɗaga kai a hankali shi ne. NADIR. Tsaye yake a bakin ƙofar, jikin sa ba riga sai boxer, gashin kansa ya ɗan rikice kamar wanda ya fito daga bacci. Idanunsa sun yi ja kaɗan… kamar wanda bai samu hutawa ba. A hannunsa yana riƙe da ƙofar, amma tsayuwarsa ba ta da ƙarfi kamar yana… tangal-tangal. AFNAN ta ɗan tsaya cak wannan shi ne mutumin da duniya ke ihu da sunansa amma a wannan lokacin, ba sarki ba ne. Kawai wani mutum ne mai rauni. Ta gyara murya cikin ladabi: “Good morning sir… your coffee.” NADIR bai amsa nan take ba sai kawai ya tsaya yana kallonta kallon da ya sa AFNAN ta ji wani abu ya motsa a zuciyarta—ba tsoro ba, ba farin ciki ba… wani abu da ba ta iya fassara ba ya miƙa hannu a hankali, ya riƙe gefen ƙofar da ƙarfi kamar yana neman tallafi muryarsa ta fito a ƙasa, mai rauni: “Come… inside.” AFNAN ta ɗan ja baya kaɗan. “A’a sir… zan iya ba ka a nan” kafin ta gama, sai ya ɗan karkata, jikinsa ya yi rauni kamar zai faɗi, tana mika masa hannun sa na rawa Cup ɗin coffee ya kife ya zube ta firgita. “Sir!” Ba tare da tunani ba ta matsa kusa da shi, ta riƙe hannunsa zafin jikinsa ya buga tafin hannunta , yana da zafi sosai kamar yana cikin wani ciwo. NADIR ya lumshe ido, numfashinsa ya yi nauyi. “Medicine…” ya faɗa a hankali. AFNAN ta shiga ɗakin da sauri tana tallafa masa. Room ɗin ya yi kyau da tsari na masu kuɗi, amma a wannan lokacin ba ta kula da komai ba ta kai shi kan gadon ya zauna da ƙyar. Ta juya tana duban tebur, tana neman magani. “Ina maganin ka sir?” NADIR ya ɗaga hannu kawai… ba tare da iya magana sosai ba yana nuna wani wuri. AFNAN ta bi inda yake nuna—ta buɗe drawer ciki akwai magunguna. Ta ɗauki guda ɗaya, ta juya da sauri “Wannan ne?” bai amsa ba kawai ya ɗan juya kai, kamar yana cikin wani hali da bai san inda yake ba zuciyar AFNAN ta fara bugawa da sauri wannan ba kamar normal ba ne ta matsa kusa da shi. “Sir… ka sha wannan…” ta miƙa masa. Amma kafin ta kai sai ya kama hannunta da ƙarfi AFNAN ta tsaya numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci idanunsa sun buɗe kaɗan… amma ba su da nutsuwa kamar… bai cikin hayyacinsa “Don’t go…” ya faɗa a hankali zuciyarta ta bugawa da ƙarfi wani abu ya sauya a cikin iska shiru ya mamaye ɗakin “Zan kira ambulance…” AFNAN ta faɗa cikin firgici, hannunta na neman wayarta. Amma cikin raunin muryarsa— “No…” NADIR ya ƙara damƙe ƙirjinsa, fuskarsa ta nuna zafi mai tsanani numfashinsa yana fita da wahala, kamar ana danniya a zuciyarsa. AFNAN ta tsorata sosai. “Sir…!” ya miƙa hannu ya riƙe nata da ƙarfi, idanunsa a rufe amma bakinsa ya motsa a hankali “Don’t… go…” almar ta tsaya a kunnenta zuciyarta ta buga ta tsaya cak. Kafin ta sake cewa komai baccin gajiya da ciwo ya kwashe shi hannunsa har yanzu yana riƙe da nata. Jikinsa ya fara yawan zufa, numfashinsa na sauka a hankali amma har yanzu yana da nauyi AFNAN ta yi ƙoƙarin janye hannunta amma ya riƙe ta da ƙarfi sai ta ɗan yi ƙarfin hali, ta bangare hannunta daga cikin nasa a hankali a miƙe tsaye cikin sauri ta nufi bathroom, ta ɗauko towel, ta jiƙa shi da ruwa mai sanyi, sannan ta dawo kusa da shi ta ɗaga kansa kaɗan ta ɗora masa towel ɗin a saman kansa ruwan sanyi ya sauka a fatar sa. A hankali, numfashinsa ya fara sauka. AFNAN ta tsaya tana kallonsa wannan lokacin ba ta ganin shahararren ɗan ƙwallon duniya ba tana ganin wani mutum ne kawai… mai fama da ciwo zuciyarta ta tausaya masa. Ta tuna yadda yake riƙe ƙirjinsa da ƙarfi ɗazu… yadda yake kiran ta kada ta tafi… Ta sauke ajiyar zuciya. “Allah ya sauƙaƙa maka…” ta furta a hankali ta tabbatar ya dan natsu ta juya ta fita daga ɗakin cikin nutsuwa, a corridor, coffee ɗin da ya zube har yanzu yana kan carpet. Ta ɗauko moper ta goge shi a hankali. Shiru ya sake mamaye wajen. Babu wanda ya san abin da ya faru a cikin Room 18 babu wanda ya san cewa daren nan ya riga ya fara sauya komai. AFNAN ta koma reception desk, ta zauna a hankali. Amma zuciyarta ba ta koma yadda take ba. Karfe 6:00 na safe. Haske na asuba ya fara ratsawa cikin gilasan hotel ɗin, yana kawar da duhun daren da ya shige AFNAN ta miƙe a hankali daga reception desk jikinta gaba ɗaya a gajiye. Idanuwanta sun yi nauyi, ƙafafunta na mata ciwo kamar an ɗora mata dutse kai kuma yana sarawasaboda rashin bacci da yawan sintiri da ta yi cikin dare ta kai hannu ta ɗauki hijabinta da jakarta. Da ta kama handle ɗin ƙofar fita sai ta hango su Hamla suna dawowa daga waje, dariya da hira a tsakaninsu kamar ba su san wahalar da ta sha ba. AFNAN ta girgiza kai a ranta. “sun barni da aikin sama da mutum goma…” ta faɗa a zuciyarta cikin ɓacin rai gajiya ta mamaye ta fiye da komai ta hango IRFAN a cikin ma’aikatan safiya. Ta tsaya kaɗan, ta ɗaga murya cikin gajiya: “Room 18… akwai mara lafiya ku sanar da oga naku… Mujib.” IRFAN ya ɗan ɗaga kai da mamaki, amma kafin ya tambaya wani abu AFNAN ta riga ta juya ta ja ƙafafunta a hankali tana tafiya wani dogon hamma ya kubce mata ba ta da ƙarfin tsayawa ko magana ta fita daga hotel ɗin. Iskar safiya ta daki fuskarta, amma ko hakan bai rage mata gajiya ba hankali ta nufi gida da isowarta ba ta tsaya komai ba ta buɗe ƙofa… ta shiga… ta wuce kai tsaye ɗakinta. Ko hijab ɗinta ba ta cire ba ta kwanta kan gado kamar wanda aka jefa. Cikin daƙiƙa kaɗan, bacci mai nauyi ya ɗauke ta amma a cikin wannan bacci— zuciyarta har yanzu tana ɗauke da wani abu… wannan dare… da mutumin Room 18… Karfe 8:00 na safe. Lokacin breakfast. Hall ɗin hotel ya fara cika da motsi—ma’aikata na kai da kawo, ƙamshin abinci yana tashi a iska, wasu ‘yan wasa suna saukowa a hankali suna gaisawa. COACH HAMZA ne ya fara fitowa, sanye cikin nutsuwa, idonsa na duban ko’ina kamar yadda ya saba yana ɗaukar kujera sai MUJIB ya matsa kusa da shi cikin girmamawa. “Sir… akwai wani rahoto.” Coach Hamza ya ɗaga gira kaɗan “me ya faru?” Mujib ya dan ja numfashi. “An ce akwai mara lafiya daga cikin tawagar ku… a Room 18.” Coach Hamza ya ɗan yi mamaki. “Room 18? Who is there?” Kafin Mujib ya amsa YAZID ya shigo, yana cewa: “It’s NAD ” bai gama ba ƙofar hall ta buɗe. NADIR ya fito a hankali. Sanye da farar jalabiyya fuskar sa a kwantar da hankali, kamar babu abin da ya faru daren jiya duk suka juya suka kalle shi. Coach Hamza ya miƙe tsaye. “Nadir?” Suka gaisa da sauri. Coach ya duba shi daga sama zuwa ƙasa, yana son gano wani abu a fuskar sa. “Are you fine, Nadir?” NADIR ya ɗan girgiza kai, ya ɗan gyara tsayuwarsa. “Yes sir… I’m normal.” kalmar ta fito da sauƙi… amma idanunsa sun ɓoye wani abu. Coach Hamza ya juya ya kalli Mujib da wani irin fuska kamar yana cewa: “Me ke faruwa?” Mujib ya ɗan sunkuyar da kai cikin kunya nan take Coach ya matsa gefe ya hango IRFAN. Ya kira shi. “You… come here.” IRFAN ya matso da girmamawa. Coach ya ce: “I’m impressed… but haba, I heard something. Was there any issue last night?” IRFAN ya ɗan rikice. “Sir… wallahi ban sani ba sosai…” sai ya ɗan tsaya, ya ƙara da cewa: “But… Afnan ba zata yi ƙarya ba.” Coach Hamza ya kalli Nadir kai tsaye. “Are you sure you’re okay?” NADIR ya ɗan ɗauke kai gefe, kamar yana guje wa kallon su. “Yes.” amsar gajera amma wannan karon ta yi nauyi. Coach Hamza ya yi shiru na ɗan lokaci. Sai ya ce: “Alrigh" A gefe guda kuma— NADIR ya tsaya shiru. A zuciyarsa yana ƙoƙarin tuna wani abu… wani dare wani kamshi wani fuska da bai gama gani ba. AFNAN. Amma bai san dalilin da yasa zuciyarsa ke masa nauyi ba. A haka ya tsaya na ɗan lokaci… Sunan ya sake dawowa masa a hankali. “Afnan…” ya maimaita a zuciyarsa, kamar yana ɗanɗana lafazin ya ɗan lumshe ido. “Alright… itace ta taimaka min jiya?” ya faɗa a ransa. Wani yanayi ya ratsa shi—ba zai iya bayyana shi ba amma ya danne kamar bai damu ba ya ja kujera, ya zauna ta fara ɗan taba breakfast ɗinsa kaɗan—ba sosai ba tunaninsa ba ya nan yana wani wuri ne daban bayan ya gama ya miƙe tsaye cikin nutsuwa ba tare da ya ƙara magana da kowa ba, ya nufi ɗakinsa. Da ya shiga kai tsaye ya shiga bathroom. Ruwan shower ya sauka a jikinsa, yana wanke gajiya da ciwon daren jiya. Ya tsaya na ɗan lokaci yana jin ruwan na sauka a jikinsa, ya shirya cikin kayan Atlas Kings—jersey mai tsabta, takalma masu tsada, kamshi mai ɗaukar hankali ya tsaya a gaban mirror ya kalli kansa na ɗan lokaci ya ɗan furta a hankali, “…Afnan.” ya girgiza kai. Kamar yana son mantawa ya ɗauki jakarsa ya fita. A waje, tawagar Atlas Kings suna jiransa. Motar su ta shirya. Coach Hamza ya ɗan kalle shi. “Ready?” NADIR ya amsa cikin nutsuwa: “Yeah.” suka shiga mota. Suka nufi filin training. https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W 🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬 Who's that girl BY NARNAH KANWAR SOJA 13 / 04 /2026 PG 10 & 11 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 DAY 2 Karfe kusan daya na rana ta farka , haske ya cika ɗakin, amma ita har yanzu tana kwance kamar jiki ya gaza tashi. Idanuwanta sun buɗe a hankali, kamar wani dutse ne mai nauyi aka cire mata sai yaji ciwo kai ya tsaya kamar ma bata taɓa jin ciwon kai ba sai dai , jiki gaba ɗaya babu ƙarfi, tayi ƙoƙarin motsawa amma wani nauyi ya ja ta ƙasa ta lumshe ido. Hoton daren jiya ya dawo. Room 18 mani mutum mai zafi a jiki… muryarsa mai rauni “Don’t go…” zuciyarta ta bugawa da ƙarfi ta buɗe ido da sauri. “Ya Salam…” ta furta a hankali ta ɗora hannu a ƙirjinta ba tsoro ba ne kawai wani irin ruɗani ne. “Me yasa nake tunanin shi haka…?” ta tambayi kanta ta juya gefe Hijab ɗinta har yanzu yana kanta ba ta ma cire shi ba kafin bacci ya ɗauke ta hakan ya sa ta ƙara jin kanta rayuwarta ba ta da sauƙi babu hutu babu kulawa sai aiki kawai a hankali ta tashi zaune jikinta ya yi sanyi a waje ta ji muryar Baba. “har yanzu bata tashi ba?” muryar tasa ta sa zuciyarta ta faɗi Umma ta amsa a hankali “ta dawo ne da safe ka san aikin dare, dole sai ta samu ishashen bachi ” “Ni ban san wani aiki dare ba!” Baba ya katse ta, “kudi kawai nake so na gani! idan ba haka ba, ta bar min gida ” kalmar ta tsaya a zuciyarta kamar soka, idanuwanta suka cika da hawaye ta sunkuyar da kai “ni yaushe rayuwata zata sauya ne ko kudin adaidaita ba'a bani ba bari wani allowance?” ta furta a hankali ta share hawaye da gefen hannunta ta miƙe tsaye cikin kasalar bachi , FLASHBACK Wace ce AFNAN IBRAHIM? A ƙasar Morocco a cikin wani ƙaramin unguwa mai ɗauke da ƙurar rayuwa da ƙamshin talauci anan ne aka haifi AFNAN ba a haife ta cikin zinariya ba, a a tarbe ta da farin ciki ba. An haife ta ne cikin ruɗani da tashin hankali Mahaifinta IBRAHIM mutum ne mai zuciya mai wahala, wanda rayuwa ta taɓa shi tun yana ƙarami ya gaji ƙaramar gona, amma ya gada da raɗaɗin rasa iyaye, da nauyin kula da iyali da bai shirya ba, mahaifiyarta kuma mace ce mai haƙuri kamar ƙasa, da ake takawa ake zuba mata sharar amma bata daukan wani mataki , duk wani nauyi da zafin rana z sanyi , da ruwa shiru ne makomarta, an taso da ita a gidan marayuba uwa, ba uba… sai Allah kaɗai. Amma duk da haka, ta aure IBRAHIM da zuciya ɗaya ta zaɓi rayuwa mai wahala saboda soyayya Rayuwa ba koyaushe take bi da zuciya ba. Tun kafin AFNAN ta zo duniya an riga an dasa wani guba a zuciyar IBRAHIM. “Idan matarka ta haifi namiji a haihuwar fari arziki zai biyo bayanka har abada ” wannan magana ta zama imani a gare shi ya manta da Allah ya rungumi tsafi da zato lokacin da matarsa ta samu ciki IBRAHIM ya fara kai ta wurin bokaye, wurare masu duhu, wurare da ba a ambaton sunan Allah kowanne yana tabbatar masa da abin da yake so ji. “Namiji ne.” Zuciyarsa ta cika da bege ya fara mafarkin arziki , nasara, sauƙin rayuwa amma ranar haihuwa ta zo, ranar da ƙaddara ta bayyana gaskiya jaririya ta fito, mace Ba a ji “Alhamdulillah” daga bakinsa ba sai ƙiyayya idanunsa suka canza zuciyarsa ta juya a wannan rana ba kawai ya ƙi jaririya ba ya fara ƙin ƙaddararsa. Tun daga wannan lokaci AFNAN ba ta san ɗumi na soyayyar uba ba ta taso cikin sanyi, cikin tsawa , cikin kalmomin da ke yanka zuciya kamar wuƙa IBRAHIM ya daina ganin ta a matsayin ɗiya ya fara ganinta a matsayin matsala gonarsa ta fara lalacewa, amfanin gona ya daina albarka sai ya danganta komai da ita. “Saboda ita ne…” Kalmar da ta zama la’ana a rayuwarta. Amma abin da bai sani ba, ba AFNAN ce matsalarsa ba mantuwar Allah ce. Mahaifiyarta kuwa ta rungume ta da ƙauna biyu nata da wadda ba ta samu ba ta zama inuwa, kariya, da zuciyar da AFNAN ke fakewa a ciki. Amma duk da haka raɗaɗin kalmomin uba ba ya gushewa AFNAN ta girma tana ɗauke da tambaya ɗaya a zuciyarta: “Laifina me na yi…?” Kuma wannan tambayar ita ce ta gina yarinyar da duniya za ta sani daga baya yarinyar da ta koyi yin shiru amma zuciyarta cike take da labari. Rayuwar da ta ƙone zuciya bayan shekaru shidda komai ya sauya ba wai rayuwa kawai ta tsananta ba IBRAHIM ya lalace gaba ɗaya. Gonar da ya gada ta zama ƙasa marar amfani babu albarka , babu ci gaba sai ya fara neman mafita a inda ba ya kamata ba sigari ya zama abokinsa zama a titi, zama da cacca da zaman banza , ya zama rayuwarsa kowace rana zuciyarsa na ƙara duhu kowace ran ƙiyayya tana ƙara girma a ransa. Kuma duk inda ya dosa yana komawa da ita ga AFNAN. “Ke ce musibar da ta shigo min rayuwa!” kalmar da yake furtawa ba tare da jin zafi ba. Mahaifiyarta ZULQIYYA kuwa tana tsaye a tsakiyarsu kamar garkuwa. Mace mai haƙuri da zuciya mai rauni. Ta san mijinta ya ɓace hanya amma ta ƙi barinsa saboda AFNAN saboda gida saboda fata, amma IBRAHIM bai gani ba. Ranar da ya kai AFNAN gidan marayu rana ce da zuciyar uwa ta kusa karyewa. AFNAN tana riƙe da hijab ɗin uwarta da ƙaramin hannu, tana kuka cikin shiru… ba ta fahimci laifin da ta yi ba. “Umma… zan dawo ko…?” ta tambaya da muryar da ba za a iya mantawa da ita ba. ZULQIYYA ta ji zuciyarta ta yage amma kafin ta yi magana IBRAHIM ya juya ya bar su ba tare da ya waiwaya ba. Amma uwa ba ta iya jurewa bai kai kwana ba ZULQIYYA ta koma, ta ɗauki AFNAN ta dawo gida ta rungume ta kamar zata ɓoye ta daga duniya tun daga wannan rana tsanani ya ƙaru abu kaɗan zai faru IBRAHIM ya tashi da faɗa. “Ki bar min gida na! ki fita ki tafi duniya—ba ubanki bane ni!” kalmar da AFNAN ta saba ji… har ta zama kamar iska a kunnenta amma duk da haka kowane lokaci tana jin zafi zafi mai sabo har ya kai wani lokaci… IBRAHIM ya faɗi gaskiyar da ta fi komai raɗaɗi. “Ni ko suna ban taɓa saka miki ba ban taba daukan ke a hannu na ba .” wannan kalmar ta tsaya a zuciyar AFNAN har abada saboda gaskiya ne ba shi ya sa mata suna ba Mahaifiyarta ce ta ɗauke ta cikin ƙauna, ta ce: “AFNAN…” (Ma’ana: kyakkyawan abu, alheri, ni’ima) Sunan da ya saba wa rayuwarta amma ZULQIYYA ta yi imani duk da duhun da suke ciki ɗiyarta haske ce. AFNAN ta girma cikin wannan rikici: Ƙiyayyar uba… Ƙaunar uwa rayuwa mai wahala da zuciya mai ɗauke da tambayoyi amma a cikin shiru ta koyi abu guda ɗaya. Jurewa ############ Ƙauna ta zo amma ba gare ta ba, rayuwa ba ta tsaya ba duk da ƙunci, duk da zafi ZULQIYYA ta sake samun ciki wannan karon… gidan ya cika da wani irin shiru mai ɗauke da tsoro da fatan alheri amma ranar haihuwa ta zo da wani sabon yanayi tagwaye maza nan take gidan da ya daɗe cikin duhu ya cika da murna. IBRAHIM ya yi dariya irin wadda ba a taɓa jin ta ba a gidansu ya ɗaga yara sama kamar ya samu duniya. “Na samu! na samu abin da nake so!” ya saka musu suna cikin alfahari: ZAID… da NA’IM. Ranar farko da AFNAN ta ga mahaifinta yana dariya, amma ba saboda ita ba zuciyarta ta ɗan motsa amma ba ta yi kuka ba ta riga ta saba tun daga wannan rana komai ya canza. amma ba a gare ta ba Ɗakin ya cika da kulawa amma ga tagwayen soyayya ta cika gida… amma ga su kaɗai. IBRAHIM ya zama wani mutum daban a gare su mai yawan dariya mai wasa da yara mai kula dasu, amma idan ya juya ga AFNAN fuskar sa tana canzawa kamar yana kallon matsala. Ba ‘ya ba kowace rana bambanci yana ƙara bayyana Idan ZAID da NA’IM suka yi kuskure “Yara ne.” Amma idan AFNAN ta yi ƙaramin abu— duka ba tausayawa “Ke farar kafa ce!” “Gobarar gida!” “Abin baƙin ciki da bai kamata ya zo duniya ba!” Kalmomin da suka fi duka raɗaɗi. Wani lokaci yana kwace abin da take riƙe da shi yaana hanata wasa da ƙannenta. “Ki rabu da su! ba irin ku ɗaya ba ne ke bakar tsiya ce !” AFNAN ta tsaya a gefe tana kallon yadda mahaifinta ke rungumar su tana kallon yadda yake dariya da su wani abu yana motsawa a zuciyarta ba hassada ba kewa ce. Kewar abin da ba ta taɓa samu ba ta juya ta kalli mahaifiyarta. ZULQIYYA ta san komai. Amma idonta cike yake da hawaye da ba ta iya zubarwa ta rungume AFNAN a hankali kamar tana neman gafara ahankali ta ce: “Ki yi haƙuri ƴa ta” kalmar da AFNAN ta saba ji amma wannan karon— ta ɗaga kai ta kalli mahaifiyarta. Idanuwanta babu kuka sai tambaya a zuciyar ta “shin ni ba ɗiya ba ce…?” A wannan gida , AFNAN ta koyi zama ba a gani ta koyi shiru ta koyi ɓoye zuciyarta domin wani lokaci… zafin bambanci yafi zafin duka. 💔✨ https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W 🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬 Who's that girl BY NARNAH KANWAR SOJA 14 / 04 /2026 PG 12 & 13

Chapter 4 of 7