cike da hayaniya, amma a gare ta komai kamar shiru ne tana isa gida, ta sauke kayan aikinta ta shiga kitchen ba ta jin yunwa, amma dole ta dafa rayuwa ba ta tsaya saboda damuwa.
AFNAN ta shiga gida a hankali, jikinta har yanzu a sanyaye saboda gajiyar aiki ta ajiye jakar ta kusa da kujera, sannan ta zauna a ƙasa kusa da Umma wadda ke shan shayi.
Umma ta ɗaga kai ta kalleta.
“AFNAN… me ya faru? fuskar ki kamar wadda ta dawo daga yaƙi.”
AFNAN ta sauke numfashi mai nauyi.
“Umma… sun ce zan fara aikin dare.”
Umma ta ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙa, sannan ta ɗan matsa kusa da ita.
“kin ce aikin dare?” AFNAN ta gyada kai.
“Eh… kuma gaskiya bana so na fi son aikin rana dare yana bani tsoro kinsani Umma.”
Umma ta ɗan shafa kanta da tausayi.
“Ya 'yata… wani lokacin rayuwa tana kawo abubuwan da ba mu so, amma su ne suke buɗe mana ƙofa ta alheri.” AFNAN ta ɗan kalleta Umma ta ci gaba:
“Ki ɗauke shi a matsayin jarabawa wata rana zaki tuna wannan lokaci ki yi murmushi.”
Kalaman Umma sun saukar mata da nutsuwa kaɗan.
Ta ɗan gyada kai a hankali
“Lafiya? Me kuke tattaunawa haka?”
Umma ta amsa da murmushi.
“AFNAN ce… sun ce zata fara aikin dare.”
Baba ya tsaya na ɗan lokaci.
Sai fuskar sa ta canza zuwa farin ciki.
“Da gaske?” AFNAN ta ɗan yi mamaki duk da cewa ba sabon abu bane a gunsa
“Eh Baba…”
Baba ya zauna yana murmushi.
“Amma wannan abu ne mai kyau fa.”
AFNAN ta ɗan ɗaga gira.
“Mai kyau?”
Baba ya gyada kai.
“Eh. Na san irin waɗannan ayyuka… akwai allowance mai kyau a ciki wanchan lokacin ma ai an kara miki albashi .”
A haka yayi ta magana yana farin ciki har yaban gidan umma dai na bata hakuri da cewa ai zai wuce " wai ke yau nema kika fara aikin dare , haba dai Afnan ƙwallon ƙafa gaba daya yasa kin zama wani irri , zan fita na amso kayan wankau ke tabbatar kin dafa wanan saiwar sai na dawo"
Hannunta na motsawa a hankali tana haɗa girman , amma zuciyarta tana can — a kan jerin sunayen nan.
Night shift VIP guests Ƴan ƙwallon ƙafa ta sauke numfashi a hankali.
“Ya Allah…”
ta furta a zuciya bayan ta gama, ta fito daga cikin gidan sakamakon ana ta sallama sai da ta isa ƙofar gidansu ta tsaya cak wani kyakkyawan saurayi ne yana tsaye a gabanta jikinta ya ɗan ja baya kaɗan.
NURA.
Ya jingina da bango kamar wanda ya daɗe yana jira fuskarsa cike da murmushi.
Idonsa yana kallonta kai tsaye.
Sai ya gyara tsayuwarsa, ya ɗan matsa kusa da ita.
Ya ce cikin Larabci mai laushi:
“أين كنتِ يا حبيبتي؟ لقد اشتقتُ لكِ كثيراً…” (Ina kika je ya ƙaunata? na yi kewarki sosai…)
AFNAN ta ɗan ɗaga kai ta kalle shi ba tare da ta yi murmushi ba.
NURA ya ci gaba, yana kallonta daga sama zuwa ƙasa kamar yana nazari sai ya ce da ɗan wasa a murya:
“ما هذا؟ أين نور وجهكِ؟” (Menene haka? Ina annurin fuskar ke ) ? ya ƙara matsowa kusa kaɗan.
“من الذي أزعج أميرتي؟” (Wa ya ɓata ran sarauniyata?)
AFNAN ta ji zuciyarta ta ƙara nauyi.
ba wai maganganunsa ba ne suka taɓa ta ba…
amma saboda ba ta cikin yanayin da zai fahimta ta kau da kai a hankali.
Ba ta son ya ga abin da ke cikin idanunta.
NURA ya ɗan lankwaso yana ƙoƙarin haɗa ido da ita.
“تحدثي معي…” (ki yi magana da ni…)
Amma AFNAN ta girgiza kai kaɗan.
Ta ce a hankali:
“Ba komai…”
Sai ta yi yunƙurin wucewa amma NURA ya ɗan tare hanya kaɗan, ba tare da ƙarfi ba cikin murmushi:
“ko da yaushe kina ɓoye min damuwarki.” sai ya ɗan rage murya:
“Ni ba baƙo ba ne a rayuwarki, Afnan.”
kalaman sun tsaya a zuciyarta na ɗan lokaci…
ta tsaya shiru ta ɗaga idonta a hankali ta kalle shi.
Amma wannan karon…
idanunta ba su ɗauke da hasken da ya saba gani ba cikin rauni:
“Wasu abubuwa… ba kowa zai fahimta ba, Nura.” sai ta kauce masa ta buɗe ƙofar gidan ta shiga ciki ta rufe ƙofar a hankali a bayanta.
NURA ya tsaya a waje murmushinsa ya ɗan gushe ya kalli ƙofar na ɗan lokaci kamar yana tunanin wani abu a cikin gidan kuwa…
AFNAN ta jingina da ƙofar bayan ta rufe ta lumshe idanu zuciyarta na bugawa a hankali ta san ranar da ke tafe ba za ta zama kamar sauran ranakun rayuwarta ba.
AFNAN ta buɗe ƙofar gidan… sai ta ga shi NURA tsaye, murmushi a fuska kamar bai tafe ba jikinta ya ƙara yin nauyi, zuciyarta ta cika da ƙara.
Ba tare da ta iya jurewa ba, ta fashe da kuka.
Kuka na rarrashinta daga ɗan lokaci, tana jin zuciyarta na taushi.
NURA ya matso kusa, ya ɗan rungume ta da bubbuga bayan ta yana cewa
“Ke… kwantar da hankalinki ina tare dake a kowane yanayi bazan taɓa juya miji baya ba ”
Amma AFNAN ta yi ƙoƙarin mayar da hankali, tana cewa a murya mai rauni:
“an ƙara samun night duty kuma na tsani banason ganin ƴan ƙwallon ƙafa…”
NURA ya ɗan murmusa, ido cike da natsuwa, sannan ya ce cikin Larabci:
“هيا يا أميرتي… اهدئي. العمل عملكِ، والباقي ليس كرة قدم.”
(Haba, Sarauniyata… kwantar da hankalinki. Aikin ki ne, kuma ba ƴan ƙwallon ƙafa bane su damu da ke.) Maganarsa ta saukar mata da zuciya, ta ɗan shakata Ya ci gaba:
“Ki saurara, duk abin da ke nan yanzu… aikin ki ne. Idan baki so, ki ɗauka a matsayin aiki kawai.”
AFNAN ta ɗan shiru, murmushi ya fara bayyana a fuskar ta.
Har ta nitsu, zuciyarta na jin sauƙi a haka ya ci gaba da ƙarfafa mata guiwa ita kanta tana mamakin me yasa take tsoron wanan aikin a wanan lokacin ko duk tsakar ball ne amma a haka ya mantar da ita da maganar sa ne kwantar da hankali ta , ta shiga gida, hannunta na riƙe da ƙofar, amma idanunta sun haska ƙaramin murmushi mai taushi.
NURA ya tsaya a waje, yana kallonta na ɗan lokaci, murmushinsa ya ɗan ɓace, amma idanunsa sun bayyana cewa ya yi farin ciki da ganin ta nitsu.
https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t
FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
09 / 04 /2026
PG 07
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
GARGA'DI
Haƙƙin mallakar wannan littafi na marubuciya ne, ban yarda kowa ya sauya min labarin, ya mayar da shi audio, ko ya kwafa wani ɓangare daga cikinsa ba tare da cikakken izinin marubuciyar ba.
Wannan labari ƙirƙira ce daga tunanin marubuciya da zubin alƙalami duk wani suna, hali ko lamari da ya yi kama da rayuwar wani mutum ko wata gaskiya da ta taɓa faruwa, hakan dai daidaituwa ce ta zubin alƙalami kawai, ba da nufin kwaikwayon kowa ko nuna wani mutum ba.
Domin haka, marubuciya na sanar da kowa cewa duk haƙƙin wannan littafi nata ne kaɗai.
© Duk haƙƙin mallaka na marubuciya ne.
NARNAH KANWAR SOJA
08101235739
MORNING – MOROCCO
Mohammed V International Airport
Time: 11:15 AM
Haske na safiya yana saukowa a saman titin jirgin sama. Iskar safiya mai ɗan sanyi tana busowa a hankali yayin da jirgin ya sauka cikin daidaito, kofar jirgin ta buɗe.
Sai aka fara fitowa team ɗin Atlas ɗin, suna dariya suna tafa hannu kamar jaruman da suka dawo daga yaƙi magoya baya a airport suna ihu:
“Atlas! Atlas! Atlas!” gaba daya sun cika gun a kewaye da security
Coach Hamza Benyoussef ya fito yana murmushi, yana ɗaga hannu yana gaisawa da jama'a. Yan wasan suna rungumar juna, wasu suna tsokanarsu:
“Wallahi ka ga yadda ka rasa waccan chance ɗin jiya!” “ni? Kai ne fa ka zame!” dariya ta cika wajen, wani saurayi ya sauko daga ƙofar jirgin a hankali.
Shiru ya ɗan sauka na ɗan lokaci.
Sanye yake da white shirt mai haske black jeans, a idanunsa kuma akwai black glass mai ƙara masa kima.
Tafiyarsa a nutsuye take — kamar wanda ya san darajarsa.
Wannan shi ne Nadir Al‑Atlas.
Fuskarsa kyakkyawa ce, gashinsa ɗan lanƙwashe, jikinsa kuma cike da ƙarfi irin na ɗan wasa ya ɗan cire glass ɗin kaɗan, idanunsa suna haske kamar ketowar ranar alfijir, daya daga cikin teammates ɗinsa Yazid
“Ga shi nan! Mr. Handsome ya iso kai sai a ƙarshe !”
Wani ya ƙara cewa:
“Ka kula fa, idan ka sake murmushi duk 'yan matan Morocco za su taru a airport!” duk suka dara
Nadir ya ɗan gyara glass ɗinsa yana murmushi kaɗan — murmushin da ke nuna kasaita da nutsuwa........
A wannan lokacin ne masu camera da ‘yan jarida suka fara taruwa.
Flash!
Flash!
Ana ɗaukar hotuna babu kakkautawa.
“Nadir! Nadir! Look here!” wasu daga cikin ‘yan jarida suka kira saboda sauran ƴan wasa kowa yayi pose na daukan hoto Amman girman kai baya son tsayawa gashi da afarinjin yan wasa sai kirar sa suke hannu kawai ya daga masu Amman suka ƙara rudewa " King of Atlas "
Sai jami’an tsaro (escort) suka kewaye Team Atlas domin kare su daga cunkoso.
Daga nan aka raka su zuwa wajen wata ƙatuwar mota mai alfarma wacce aka yi wa alama da sunan ATLAS.
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga motar.
Nadir ya shiga na ƙarshe. Kafin ya shiga, ya cire glasses ɗinsa na ɗan lokaci, ya kalli sararin Morocco… kamar yana jin wani sabon labari yana jiransa.
Motar ATLAS ta fara motsawa a hankali daga filin jirgi…
Hotel Casablanca – Morocco
Bayan sun isa Hotel Casablanca, anan ne aka shirya musu masauki na kwanaki da zasu yi a Morocco. Ginin hotel ɗin ya kasance babba kuma na alfarma, fitilun ciki na kyalli suna ƙara nuna tsadar wurin.
Da motarsu ta tsaya a ƙofar hotel ɗin, sai aka buɗe musu ƙofa cikin girmamawa. Oga Manager Salman da kansa ya fito ya tarbe su da murmushi a fuska.
“Welcome to Casablanca Hotel,” in ji shi cikin ladabi.
Dukkan ’yan wasan Atlas Team suka sauka daga motar, wasu na dariya, wasu na ɗaukar hotuna da waya, wasu kuma suna musayar zolaya tsakaninsu.
Manager Salman ya ɗan matsa gaba, sannan ya nuna wasu mutane guda biyar da suka tsaya cikin tsari.
Ya ce:
“Waɗannan sune ma’aikatan da zasu kula da bukatunku daga safiya zuwa rana. Duk abin da kuke buƙata, ku sanar da su.”
Mutanen suka sunkuyar da kai cikin gaisuwa. suka gabatar da kansu daya bayan daya
Sai kuma Salman ya juya gefe guda, inda wasu mutum biyar suka sake matsowa gaba.
A cikin su ne Afnan take tsaye.
Salman ya ce:
“Waɗannan kuma sune ma’aikatan dare. Su zasu kula da dukkan bukatunku daga dare zuwa safiya .”
A lokacin ne idanun wasu daga cikin ’yan wasan suka ɗan tsaya a kansu, musamman kan Afnan, saboda nutsuwar ta da kyakkyawan tsari da take da shi.
A gefen su kuma, Nadir ya tsaya duk da kasaitarsa, bai ce komai ba. Sai dai ya ɗan cire glass ɗin kaɗan yana kallon wurin kamar wanda yake nazari.
Ɗaya daga cikin abokan wasansa ya ɗan taɓa shi yana zolaya:
“Nadir, ka daina wannan kallo kamar kana scouting ne!”
Suka fashe da dariya.
Shi kuwa Nadir ya ɗan yi murmushi kaɗan kawai, sannan ya mayar da glass ɗinsa ya sa a idanu.
A gefe guda, Afnan ta tsaya cikin nutsuwa tana kallon su… ba tare da ta san cewa wannan zuwan nasu ne zai sauya rayuwarta gaba ɗaya ba..
Duk suka gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya, suna faɗin sunaye cikin ladabi da murmushi. Fuskokinsu cike da farin ciki, domin ba kowane lokaci ba ne mutum zai tsaya a gaban manyan celebrities na duniya — musamman taurarin ƙwallon ƙafa irin su ATLAS KINGS.
Wasu daga cikin ma’aikatan har ana iya ganin yadda farin cikin ya cika su; murmushi na fita a bakunansu, wasu ma suna ɗan karkarwa saboda jin daɗin ganin waɗanda suka saba gani a talabijin kawai.
A gefe guda kuma, NADIR ya tsaya cikin natsuwa, hannayensa a aljihun wandon black jeans ɗinsa, Ya ɗan ɗaga kansa kaɗan kamar wanda ya saba da irin wannan kulawar. A gare shi, wannan duk wani abu ne da ya zama ruwan dare.
Lokacin da mutum huɗu suka gama gabatar da kansu, sai AFNAN ta matso gaba a hankali.
Tafiyarta cike da nutsuwa, amma a cikin zuciyarta kuwa bugun zuciya yana ƙaruwa. Hannunta na ɗan rawa kaɗan, amma ta daure ta tsaya tsayin daka.
Ta ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa, sannan ta fara magana da Larabci cikin muryar da ke nuna ladabi:
“اسمي أفنان عبد الكريم،
وأنا من ضمن الموظفين المسؤولين عن خدمتكم ليلاً،
من حيث الطعام والشراب وترتيب احتياجاتكم.”
(Sunana Afnan Abdulkarim. Ina daga cikin ma’aikatan da za su kula da bukatunku da daddare — abinci, abin sha, da gyaran muhallinku.)
Yayin da take magana, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Amma duk da haka ta daure, tana ƙoƙarin kada a lura da tashin hankalin da ke cikinta.
Ba kamar sauran ba, fuskar AFNAN a haɗe take ba ta yi dariya ba ba ta nuna farin ciki ba.
Kuma ba ta ɗaga idonta ta kalli kowane ɗan wasa ba.
Kawai ta faɗi abin da ya dace, cikin natsuwa da kamun kai.
Wani daga cikin 'yan wasan ya ɗan yi murmushi yana kallonta, amma NADIR kuwa bai ma motsa ba. Ya ɗan karkatar da kansa kaɗan, kamar yana dubanta ta bayan gilashinsa.
A zuciyarsa ya ce a hankali:
"Strange…"
Domin duk sauran mata da suka gan shi suna yawan ƙoƙarin burge shi ne amma wannan yarinyar ke ko kallonsa ma ba ta yi.
Wani abu kaɗan ya motsa a zuciyarsa — ba mamaki ba ne, amma curiosity.
Sai ya ɗan ɗaga gira kaɗan, yana kallon yadda AFNAN ta ja baya ta koma cikin layin ma’aikata kamar babu abin da ya faru ba tare da ta sani ba…
Wannan shi ne karo na farko da idanun NADIR suka tsaya a kanta.
https://chat.whatsapp.com/BOMe7dusdzuADbV7T5nkI0?mode=gi_t
FOLLOW MY CHANNEL FOR MORE UPDATE
https://whatsapp.com/channel/0029VaaF1DmKmCPRg2CFJ90W
🧬🧬⚽AFNAN⚽🧬🧬
Who's that girl
BY
NARNAH KANWAR SOJA
10 / 04 /2026
PG 08
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
HAPPY FRIDAY
What if the man who broke you
is actually the man you belong to?”
A haka taron ya watse.
Ma’aikatan da ke kula da tawagar da rana suka fara jagorantar ‘yan wasan zuwa ɗakunan su, suna nuna musu inda komai yake a hotel ɗin su kuma tawagar dare ciki har da AFNAN aka sallame su su koma gida domin su huta kafin dare ya yi.
AFNAN ta fita daga hotel ɗin tana tafiya a hankali jikinta kamar an ɗora masa dutse nauyi duk wani abu da ya faru yau yana yawo a zuciyarta , a zuciyarta tana ta maimaita abu guda ɗaya
"me yasa ni? me yasa sunana ya fito?" ba wai tana tsoron aiki ba… amma aikin dare ne da zai sa ta dinga mu’amala da ‘yan ƙwallon ƙafa kai tsaye wannan shi ne abin da take son gujewa.
Har ta isa gidansu.
Gidan su ƙarami ne, amma cike da rayuwar iyali kamar yadda aka saba, tana jin muryoyin iyayenta suna magana a ciki kamar suna jayayya sai zuciyarta ta ɗan matse ta tsaya a bakin ƙofar na ƴan daƙiƙu, idonta ya cika da wani irin baƙin ciki.
Ta sauke numfashi a hankali sannan ta furta a ranta, "da me zan ji guda ɗaya…?" ko a gida bana samun natsuwa.
A ƙarshe ta buɗe ƙofar ta shiga ta shiga, ta hango BABA zaune a kujera yana shirin fita fuskar sa a ɗaure kamar koyaushe.
AFNAN ta tsaya cikin ladabi, ta ce a hankali:
“Baba… barka da safiya.” amma bai ma kalle ta ba kamar bai ji ta ba.
Ya miƙe tsaye kawai, ya ɗauki makullin sa, ya nufi ƙofar fita bai amsa gaisuwar ba bai ce komai ba ya fita ya bar gidan.
AFNAN ta tsaya a wurin kamar an dasa ta.
zuciyarta ta ƙara yin nauyi domin ba wannan ne karo na farko ba…
AFNAN ta tsaya a tsakiyar ɗakin kamar wadda aka cire mata ƙarfi har yanzu zuciyarta tana nauyi saboda yadda Baba ya fita ba tare da ya amsa gaisuwarta ba.
Sai ta ji muryar UMMA daga madafarsu
“AFNAN… kin dawo ne?” ta share idonta da sauri, ta nufi madafar ɗin a hankali.
UMMA tana tsaye tana jujjuya sandar a tukunya, ƙamshin talken towo yana tashi a cikin ɗakin da ta juya ta kalli AFNAN, nan take ta gane akwai damuwa a fuskar ‘yarta ta ajiye , ta matso kusa da ita.
“Me ya faru ne ‘yata?” ta tambaya cikin tausasawa wannan tambayar kaɗai ta isa ta karya zuciyar AFNAN idonta ya cika da hawaye ta ce da murya mai rauni
“Umma… sun saka ni a aikin dare", ta ɗan yi shiru na daƙiƙa, kamar tana nazarin maganar.
AFNAN ta ci gaba da cewa:
“Na roƙe su su sauya sunana… amma suka ce ba zai yiwu ba ni fa bana son aikin dare… musamman da waɗancan ‘yan ƙwallon ƙafa.”
UMMA ta ɗaga hannunta a hankali ta goge hawayen AFNAN cikin murya mai cike da hikima:
“ke ‘yata… kada ki ji tsoro haka.” ta ɗora hannunta a kafadar AFNAN.
“wannan aiki ne kawai kuma Allah ne ya kawo miki shi, tun jiya nake rarrashin ke da maganar nan” ta kalli Umma da idanu masu cike da tambaya
“Ki tuna… ba dukan mutane ke samun irin wannan damar ba. Idan suka saka ki, to sun ga kina da ƙwarewa.” ta ɗan yi murmushi “kuma ai ba ke kaɗai ba ce akwai sauran ma’aikata tare da ke.”
AFNAN ta sauke numfashi a hankali, zuciyarta tana fara samun sauƙi.
UMMA ta shafa kanta kamar tana lallashi ƙaramin yaro.
“sai ki je ki huta sare ma zai zo da sauri.” ta ƙara cewa cikin murmushi:
“kuma ki tuna… Allah yana tare da ke.”
A wannan karon AFNAN ta ɗan yi murmushi kaɗan ƙaramin murmushi mai cike da godiya ta rungumi Umma a hankali.
“Na gode Umma bazan sake miki korafi ba .”
“Allah ya tsare ki ‘yata.”
AFNAN ta juya ta nufi ɗakin su, zuciyarta ba ta da nauyi kamar da sai dai ba ta san cewa…
**daren nan da take tsoro… shi ne daren da zai fara canza rayuwarta gaba ɗaya ba....
Karfe shida na yamma…
Bayan AFNAN ta fito daga wanka, ta yi sallah cikin natsuwa, ta ɗan tsaya a bakin ƙofar gidan iskar yamma mai ɗan sanyi tana busa gefen hijabinta a hankali.
Titinsu ya fara shiru, amma zuciyarta kuwa tana bugawa da sauri haɗin ɗan tsoro da kuma wani irin nutsuwa ta ɗan taka gaba kaɗan, tasan da kafa zata tafe sakamakon ba kuɗin ukada take dashi ba, nnan ne ta hango shi.
NURA.
Tsaye yake kusa da babur ɗinsa, ya jingina da shi kamar wanda ya saba jiran mutum ɗaya tak a duniya.
Da ya ga AFNAN, sai murmushi ya bayyana a fuskar sa. Idanunsa sun ɗan lumshe kamar wanda ya ga abin da ya daɗe yana jira ya gyara tsayuwar sa , sannan ya ce cikin larabci mai laushi:
“مساء الخير يا حبيبتي… هل أنتِ جاهزة؟ تعالي، سأوصلكِ.” (barka da yamma habibty… kin shirya? zo, zan kaiki.)
AFNAN ta tsaya cak na ɗan lokaci hannunta ya riƙe gefen hijabinta, zuciyarta na bugawa kamar ana dokawa a ƙirji ta ce cikin sanyin murya:
“NURA… ai ba sai ka wahala ba.” ya yi ɗan dariya kaɗan irin dariyar da ke fitowa daga zuciya ya girgiza kai “sai na wahala.”
Sai ya ɗan matso kusa, yana kallonta kai tsaye cikin ido “domin wannan wata ɗaya…” ya ɗan tsaya, sannan ya ƙara da larabci:
“كل ليلة سأوصلكِ بنفسي.”
kowace dare zan kai ki da kaina ya ƙara da murmushi mai ɗan taushi
“Ba wai saboda babur ɗin nan ba… saboda ke koda ƙafa zan na kaiki mu fara lissafi DAY 1".
maganar ta sa AFNAN ta ɗan sunkuyar da kai fuskarta ta ɗan yi ja kaɗan ta kasa ɓoye ƙaramin murmushin da ya bayyana a lebenta hankali ta matso ta hau bayan babur ɗin.
NURA ya kunna babur ɗin, sautin injin ya katse shiru na titin.
Iskar yamma ta fara bugawa yayin da suke tafiya cikin duhu da hasken fitilar gaban Babur nasu
AFNAN ta riƙe gefen babur ɗin, zuciyarta cike da wani irin nutsuwa mai daɗi ba ta san dalili ba amma a wannan daren ta ji kamar wannan ɗan tafiya da NURA zai zauna a cikin tunaninta na tsawon lokaci,
ta kusa shiga dare mafi wahala a rayuwarta.
*******
AFNAN tana shiga cikin hotel ɗin da natsuwa kai tsaye ta wuce locker room, ta ajiye jakar ta sannan ta saka uniform tare da ƙaramin apron ɗin ma’aikatan hotel.
Ta gyara karamin hijabinta a gaban mirror, ta ɗan numfasa a hankali karfe 7:00 na dare lokacin aikinta ya fara.
Ta hau desk na masu kula da baƙi na dare, ta karɓi shift daga wanda ya gama aiki kafin ta. Littafin rubutu da order list duk aka miƙa mata.
Har yanzu zuciyarta tana ɗan bugawa saboda sabon aikin da aka ɗora mata 9pm, ayar desk ɗin ta yi ƙara.
AFNAN ta ɗauka cikin ladabi.
“Reception… good evening.”
A can ɗin aka ji murya.
Order ne daga Room 9 — ana buƙatar abinci.
Jacob, ɗaya daga cikin ma’aikatan restaurant, ya ɗan leƙo ya ce:
“AFNAN, wannan order ɗin naki ne ke kai su Hamla sunyi sign kuma basa nan .”
ta gyada kai, ba yau ta saba da halin su ba
Ta nufi restaurant section, inda aka riga aka shirya abincin: grilled chicken, salad, bread mai laushi, da juice mai sanyi.
Ta ɗauki tray, ta jera komai cikin tsari a kan ƙaramin table mai ƙafafu, sannan ta tura shi a hankali zuwa lift.
Lift ɗin ya ɗaga ta zuwa floor na VIP rooms.
Zuciyarta na bugawa kaɗan ta isa Room 9.
Ta gyara hijabinta kaɗan, sannan ta danna bell.
Ding…
Babu amsa ta sake danna shi.
Ding, wani dogon saurayi fari sosai ya bayyana a ƙofar idanunsa masu haske, fuskar sa cike da murmushi mai annuri.
Shi ne YAZID, ɗaya daga cikin ‘yan wasan Atlas Kings ya tsaya kallon AFNAN na ɗan lokaci kamar ya yi mamaki.
AFNAN kuwa ta tsaya cikin ladabi ta ce cikin larabci:
“مساء الخير سيدي… هذا طلب الطعام الخاص بك.” (barka da yamma sir… ga abincin da kuka yi order.)
YAZID bai ɗauki tray ɗin nan take ba.
Sai ya tsaya yana kallonta da mamaki saboda
yawancin mutane idan sun ga celebrity kamar su, sukan cika da farin ciki ko dariya amma AFNAN kuwa…
fuskarta a haɗe take ba wani murmushi ba wani nuna excitement.
YAZID ya ɗan karkatar da kai yana murmushi ya gane itace da sukazo bata ko kalle su ba,
ya ce cikin larabci:
“ألا تبتسمين؟” (Ba ki yin murmushi ne?)
AFNAN ta ɗaga kai kaɗan ta kalle shi a yanzu ta lura sosai
YAZID kyakkyawan saurayi ne, fari sosai, dogo, kuma murmushinsa yana ɗaukar hankali ta ce a hankali:
“Afuwa sir…” YAZID ya