Share this page
2 / 8
na ta ne ya sanya wani dattijo ya kalle ta ya matse kwallar da ke fita daga idanun sa haƙika dole ya dauki yarinyar nan, sai dai idan ya dauke ta mai zai bata shida bashi ko biyar a jikin sa? Kuma idan ya barta ya yi rashin hankali saboda yarinyar bata wuce irin shekara huɗu ba ɗinnan da dai me wayoce, yanzu haka Allah yasan halin da iyayen ta suke ciki wajen ne manta . Hannu ya miƙa da zummar daukar ta kuma sai ya tsaya chak!! Kome ya gani ko ya tuna......... PG 4 Ganin wasu samari sun tun karo shi ne yasa bai dauki zulfa'u ba, saboda yadda suke kallon ta suna murmushi kamar da sanayya a tare da su. Da sallama a bakin su suka ƙaraso wurin tare da faɗin, "Baba wannan yarinyar ina ka same ta ? Kai ma sha Allah wallahi mun jima muna neman ta tun faruwar abin ga Chan baban ta shi ma ya bazama tun safe ." Kallon su ya yi ya ce, "To bayin Allah wannan dai nima yanzu na ganta kuma ina shirin na dauke ta na ga tana kallon ku kuma kuna kallon ta shine ya sa na dakata da ɗaukar tata. Amma na tausaya mata saboda yarinya irin wannan a wannan lokaci ai hatsari ne a ce bata tare da iyayen ta." "Haka ne baba wallahi an sha wuya matuka ainun kasan da yake abin da ya faru lokaci guda ne shine fa kowa ya tarwatse. Amma bari na ƙira Nasir ɗin yazo ya ganta ko hankalin sa zai kwanta." Ya faɗa yana kara wayar sa a kunnensa . Jim kadan naji ya na sanar da nasir ɗin cikin farin ciki. Aikuwa bai ɓata lokaci ba ya zo wurin, saboda ba nisa tsakanin inda suke da inda ya ke shiɗin. Ita kuwa zulfa'u ganin su faruk ya san ya ta farin ciki domin faruk ƙani ne a wurin nasir dan haka tuni faruk ya rungume ta bisa ƙirginsa. Koda nasir ya zo hannun ya mika ya karɓe ta ya rungumeta a ƙirginsa ya fashe da kuka ya ce, " Babyn mommy, yau na sa me ki jiya na samu haidar, amma kuma na rasa mommy da yarima...." Ya ƙarashe maganar yana sake fashewa da wani kukan kamar mace. Baba tsoho ya du be shi ya ce " yaro hakuri zakayi wannan lokacin da muka tsinci kan mu a cikin sa kowa ya jijjiga! Amma abin da ya fi sauki shine mubarwa Allah komai mu miƙa lamurran mu zuwa gare shi ." Majinar kuka Nasir ya zuƙe ya goge hawayen ya ce "Haka ne na gode baba." Da haka suka yi sallama suka wuce gida . Kowa ya na zaune jungum-jungum kamar gidan ma koki . Ya Fido itace uwa a wurin Kubra sai ƙannen ta mata guda uku wato Maryam da Hadiza da basma. Sai kawu Bala shine uba a gare su wanda ya samo sunan ne daga yaran ƙanin sa da yake gida guda suke zaune. Gefen ya Fido salame ce matar ƙanin kawu Bala sai goggo saratu surukar Kubra wato uwar Nasir da su faruk. Lokacin da su Nasir suka shigo kowa sai da ya mike duk tunani su zasu ga har da Kubra zasu shigo, amma ganin su su kaɗai shine abin da ya sake kashe musu jiki, ya yin da Maryam da basma suka zauna daɓas a wurin don su ko kula da zulfa'u ma basu yi ba sun zaci ba'a samo kowa ba . Jin ana cewa sannu zulfa'u Allah sarki yarin ya ba wayo sanann suka gane ashe an same ta . Jin ana ambatar sunan zulfa'u ya sanya haidar fitowa daga ɗaƙin kaka saboda tun da a ka sa me shi ya ga babu su bai fitoba a ɗakin yana ta faman kuka. Da gudun sa ya rungume ta ya fara kuka, "Babyn mommy mun rasa su mommy da yarima shike nan sun kashe mana su yanzu ba mu da mommy mukam . Jin kalaman sa tuni Maryam da basma suka fashe da kuka domin kamar dama jira suke idanun su fal hawaye. Saboda kaf cikin su ba mai kirkin aunty Kubra tana da hakuri duk da cewa tana da tsiwa amma bata barin su cikin damuwa, komai na su idan tana da halin yi tana musu, hatta ya Fido Kubra ce ke mata dinki lokaci bayan lokaci ita da baba. Baba ya dube su ya ce , "Kuyi shiru in sha Allahu zata bayyana nan bada jimawa ba...." Ya faɗa yana sunkuyar da kansa domin shi kansa ƙarfin halin rashin ɗiyar ta sa yake, musamman idan ya tuna yadda take dauke da juna biyu haihuwa ko yau ko gobe. Maryam ta ce, "Baba taya zamu iya dena kuka bayan ba musan halin da y'ar uwar mu ta ke ciki ba? Ga ciki jikin ta, yanzu baba idan aunty Kubra na hannun mugaye me suke mata a wannan lokacin ........tana kaiwa nan Nasir ya mike ya fice domin idan yana jin irin wannan batun zuciyar sa zata iya bugawa. Haka suka yi ta kokawa har suka hakura suka koma zaman kurame. Dajin su OGA gaba ɗaya Kuka sosai Kubra ke yi na rashin shawuya amma ba shi ba zancen sa har kusan dare. Iya tashin hankali ta shiga ba kaɗan ba! Saboda ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu . Kusan shida na yamma wani mai fuska a rufe ya shigo tantin na su yana rike da shawuya ya mika mata shi bai ce ƙalaba ya juya. Cike da farin ciki ta ke kallon sa amma kuma ta kasa bude shi saboda firgita! Saboda ji ta ke kamar gawa ya kawo mata. Tunawa da yarima tuni ta yaye mayafin da yake rufe ta ga yana bacci abinsa cikin kwanciyar hankali. Ajiyar zuciya ta sauke, Amma kuma yau gaba ɗaya hankali ta ya karkata zuwa ga a halin ta! Ji take yau dole ta je gida ko ta wane hali dan haka ta ƙudirci niyyar yau cikin dare dole ta san abinyi wajen tserewa duk da bata san ko ina ba....... Cikin dare kowa ya kwanta masu tsaro sun baje bindigu ta ko ina saboda su basa bacci haka aikin su yake sai dai da safe ga kuma yadda macizai ke kai kawo a wannan dajin . Amma duk da haka bai hana Kubra ta goyi shawuya ba ta su ɗaɗe ta fito a tantin cikin bakar abaya, saboda kausar ta tafi gurin mijinta ita ma. Cikin sanɗa take tafiya abin da tana duba gaba da bayan ta . Har tayi nisa da tantin saboda yadda take bin lunguna, sai dai kash jin saukar wani abu a wuyanta tuni ta daskare a wurin ta kasa koda motsin kirki .......... PG 5 Jin wani abu mai sanyi ya naɗemin wuya shi ne yasani suman tsaye don tuni zuciyata ta hau dakan luguden uku uku. Sanyi da santsin abin shine ya tabbatar min da cewa maciji ne! Cike da tashin hankali na ƙame wuri guda dan lumfashi ma da ƙyar na ke sauƙewa. Jin yana tunƙarar hayewa kaina ta baya na fasa wani gigitaccen ihun da ya amsa kuwwa a wannan dajin, har na mance mai ya fito dani. Kafin kace Kwabo tuni wasu zaratan maza masu ɗauke da manya bindigu suka kewayeni tare da haske min fuska. Hannu ɗayan ya sa ya kama macijin dake jikina ya jefar tare da tarwatsa shi da albarushi. Ƙarar albarushi ce ta sanya shawuya fasa ihu shi ma, jin haka ɗaya daga cikin su ya ce, "Wato guduwa zakiyi ko? Ashe baki da hankali! Ance Miki ɗan gida ma yana iya fita a wannan ƙauyen ba tare da an masa Rakiya ba bare ba ƙo?" Cike da fargaba na ke sauraran maganar sa mai kama da tsawar aradu a kunnena. Tsawar da ya sake jefamin ce ta sanya Ni tilas na yi magana . " Ba gudu zanyi ba kawai na rasa yadda zanyi da yarona ba shi da lafiya yana min kuka shine na fito nai man taimako. " Na tsara masa wannan ƙaryar da bansan sanda ta shiryuba cikin ƙirjina. "Wuce munafuka ko me ne ne ma dai zamu haɗu watarana idan gudun kike niyya ma,kuma kinsan dokar gidan nan duk wanda muka kama da niyyar gudu kisa ne. Kema kawai na Miki uzuri ne saboda baƙuwace ba don taausayi ba!" Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka na dawo tantin da na bari na zauna ina rafsar kukan bakin ciki. Sai yaushe zan kufce ne a wannan wurin? Ya Allah na ina yarima ina zan ganshi, duk runtsi jikina yana bani ƙila zulfa'u suhadu da Nasir ko a mace ko a raye. Ya Ubangiji na yarima fa? Ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Ya Ubangiji yarima yana cikin wani hali na gudun ceton rai na barshi, Allah kasa yarimana bai mutu ba ya rabbi idan yarima yana raye Allah ka sa da shi da ahalina su samu rangwame na rashi na. Da ire-iren irin wannan tunani bacci yayi nasarar saceta durƙushe da goyon shawuya. *Dajin Fulani* Yarima zaune yana ta muzurai da idanuwa, Fulani zaune gefen sa tana bashi fura amma yaƙi karbar furar. Ta ce "Yaro do Allah ka sha fura kaji. Kuma ka faɗa min suna mamarka sai na kaika gida na san yanzu tana chan tana neman ka." Jin ta ambaci gida tuni ya buɗe baki ya kurɓi furar yana ruwan hawaye ya ce. " Sunan ta Kubra muna ce mata mommy ." "Yawwa yarona kaifa ya shunan ka to do Allah ." Fulani ta faɗa saboda bazata iya tuna sunan da ta ji mamarsa ta na faɗa masa ba. "Yarima." Ya furta a taƙai ce. "Yawwa yarima yarona yanzu anjima zan shirya idan munje shikin gari sai ka hiɗi mani sunan anguwar ku na kaika." Kai kawai ya girgiza ya sake gyara zaman sa idan ya tuna mommy sai ya fashe da kuka saboda ya san ta mutu tunda ya ganta da jini kuma ga jirgi da yan bindiga sun kusa gunta suka gudu Fullo bata hana shi ba saboda tasan dole ya yi kuka duk da cewa yana yaro amma sarai ta san bazai mance komai ba. Misalin biyu na rana ta fita ita da yarima suka fita bakin titi ta tare musu abin hawa suka shiga gari . Garin da har yanzu ko kwatan kwatan jama'ar da suke ciki basu bayyana ba.saboda gaba-daya sunyi hijira duk kan wanda ya ke zaune yana zaune ne dan bashi da wurin zuwa ko kuma dan ya rasa wani na shi yana cigiya. Tunda suka shiga yarima yake hawaye kuma wani lokaci ya yi murmushin fullo ta dube shi ta ce " Ina ne unguwar ku?" "Jar ƙasa kofar samu naka." Ya bata amsa cikin tsananin son yaga ya gansa cikin gidan. Basu yi wata tafiya mai nisa ba saboda basu da nisa da in da suka sauka. Suna zuwa ƙofar gidan su ba kowa dan haka yarima ya kwace hannun sa daga wurin fullo ya afka cikin gida yana faɗin daddy na dawo ina mommy?" Amma shiru dan haka sai yarima ya tsaya ƙyam! Yana mamakin jin shurun ina jama'ar gidansu? Sabon kuka ya fara yi ya juyo sukaci karo da fullo ta ce Ko ba nan ba ne gidan?" "Nan ne basa nan dai ina ga duka sun mutu ne ya faɗa yana fashewa da kuka." Suna tsaye fullo ta rasa abinyi sai wani bawan Allah ya zo wucewa dan unguwar ya gansu ya ce da su ai duka mutanen gidan suna gidan kakan su ƙanin mai gidan ne ya bude yanzu amma ban san inda ya tafi ba. Koda yarima ya ji haka kawai bai tsaya cewa komai ba ya kama hannun fullo tiryan tiryaan sai gidan kakan su. Yana zuwa ya shiga da gudun sa ya yin da fullo ta ke biye da shi domin wannan karon bata tsya baya ba. Ganin sa da sukayi ya sanya duka suka mike daga zaman makoki da suke Wasu na kukan farin ciki wasu na murna da dariya chan ya Fido ta ce "yarima ina ka baromin mommyn ka?" Jin wannan tambayar tuni ya yarima ya sake fashewa da kuka sabo, ganin haka Hadiza ƙanwar Kubra ma ta rungume shi cikin kuka ta ce "Sanar da mu ka ji yarona kaji." Da hannu ya nuna fullo wanda sai sannan suka ganta . Wurin zama aka bata daga bisa aka nemi ƙarin bayani daga gare ta . Itama kukan ta fara kafin ta fara basu labarin haɗuwar su da Kubra da rabuwar su tana kai ƙarshen labarin Maryam da Hadiza suka sume. Nasir kuwa sake maimata kalmar ƙarshen ya ke " Haihuwa a dajin kuma ga yan bindiga?" Ganin yana neman zauce wa yasa malam ya zaunar da shi, gida duka ya dauki kukan mutuwar kubra domin su sun bata mutuwa ne kawai. Hakan kuwa shine yayi dai dai da zuwan dogarai uku suka ce da kubra ta zo a daura mata aure ..........,. Pg6 Cike da firgici na sunkuyar da kaina yayin da zuciyata ta ke min luguɗen dakan ɗaka, saboda ji nake kamar zata tsaga ƙirjina ta fito ga wani azababben zazzaɓi da ya riski dukkan gabobina lokacin guda! " Aure kuma!" Kalmar da na furta cikin zuciyata, wanda yayi daidai da uwar tsawar da ɗaya daga cikin su ya sa ke je fa min. Ciki da damuwa na yunƙura na miƙe na goya shawuya muka dauki hanyar fadar OGA gaba ɗaya. Zuwan mu ke nan na hangi maza shida gefen kujerar sa dukan su durƙushe a gefen sa. Yana nan yadda na barshi ranar ma kamar baya tashi saboda yauma bai juyo ba,wuri na samu na durkushe kamar yadda na ga sunyi. Kamar saukar wahayi haka muke jin sautin Muryar sa cikin sanyi ya ce. "Na so a daura auren kina kusa amma kuma rashin isowar ku da wuri tuni har an gama komai. Dan hakan ku bata kudin sadakin ta da kuma goron ta ku nuna mata mijinta akai ta gidan ta . Allah ya basu zaman lafiya." Tunda ya fara maganar na ke jin wani irin zugi yana saƙƙowa daga cikin zuciyata har zuwa cikin cikina da ya kewani irin murɗawa. Ganin abin da na ke ganin sa kamar wasa yana son zama gaskiya ko na ce ya zama ma shine ya ke sake je fani cikin ruɗani! Jin takun mutum kusa dani ya sani saurin ɗagowa daga sunkuyar da kan da na yi ƙasa. Sai ya ce dani "Ga wannan kudin sadakin ki ne kamar yadda OGA ya faɗa ga kuma goran ki. Sannan wanchen mai ɓakin kayan shine miji a gareki dan haka ta shi muje a ra ka ki gidan ki." Tunda ya fara bance komai ba kuma ban kalli wanda ya nuna min din a matsayin mijin ba saboda bana bukatar hakan, hannu na sa na dauki kuɗin da goran na miƙe domin bin umarnin su. Ganin na miƙe ne yasa duka suka miƙe suka sanya ni gaba saboda sumin rakiya. Haka muka ɗunguma tafiya mai nisa da fadar OGA gaba ɗaya chan wani tanti suka kaini wanda ya fi na wa girma da kuma kayan aiki cikin sa na bukatar mace. Murmushin ya ƙe na yi wanda ya fi kuka ciwo na ce cikin zuciyata "Harda wasu kayan aiki wato ga yar iska mara sanin addini." Ganin na tsaya ina tunani ya sanya ɗaya daga cikin su ya ce ki shiga ciki anjima ango zai zo da kayan amarchi. Ban furta ko kanzil ba na shiga ciki na zauna ina faman sauki lumfar-fashi. A chan kuwa gida da ƙayar a ka shawo kan su Maryam suka farfaɗo daga sumar da sukayi . Shi kuwa Nasir wani irin kuka yake mai tsuma zuciya idan ya tuna da Kubrar sa da irin zaman da sukayi na amana yadda ta ke mai biyayya a gare shi. Amma ace irin wannan rabuwar zasuyi? Ai gwanda ace shine ya mutu ya barta da ya fi masa sauki. Ko kuma ace mutuwa ta yi sukayi mata sallah suka binne to da zaifi samun sukunin da rashin sanin tabbas. Wannan abin shine abinda ya fi ƙo na masa zuciya. Ganin halin da ya ke ciki ne ya sanya MLM ya zo wurin sa ya dafa kafaɗar sa ya ce . "Nasir rayuwa fa daman cike ta ke da ƙalubale mai tarin yawa, saboda ba dukkan yadda kaso kayi rayuwa ka ke samun yi ba. Komai kuma da kake ganin yana faruwa ba wai dan an tsane mu ba ne , A'a sai dan a jarraba imanin mu. Dan haka ina son ka dauki wannan jarabawar da ta riske mu, a wannan lokacin na san dole zaka ji zafi amma idan ka tuna cewa komai Allah ne ya ke tsara shi to tabbas zaka samun nutsuwa a zuciyar ka. Kuma ka yawaita ambaton Allah a koda yaushe hakan zai sanya ka samun nutsuwar zuciya. Da wadannan kalaman Nasir ya samu ya ji wani irin ƙarfi ya riski zuciyar sa tuni kuma a wannan lokacin ya fara ambaton sunan Allah kamar yadda MLM ya ce da shi. Mama fedo ce zaune da yaran na ta a barandar da ke gaban ɗakinta. Hakuri ta ke sake basu ya yinda idanunta suke zubda hawaye saboda tabbas ta yi babban rashi a cikin yaranta idan har ya tabbata Kubra ta bar duniya. Mafi girman tashin hankali kuwa shine ace tana raye amma basu san inda zasu same ta ba. Shin ta ina zasu fara ya kuma zasuyi da yaranta domin kullum sai sun tambayi ina mahaifiyar su, illah yarima da yasan inda ya barta . Shi baya magana sai da adukkan lokacin da ya tuna ba shida wani aiki sai na kuka. Misalin shabiyu rana zulfa'u ce zaune a cinyar Basma ƙanwa ga Kubr. Ta ce "Aunty Basma idan mommy ta dawo zan koma wurin ta saboda na jima ban ganta ba kuma ina son ta haihu na yi gaɗa." Jin kalaman zulfa'u sune suka sanya zubar hawayen basma a ɓoye. Saboda ɗazu mama ta yi musu nasiha cewa su daina kuka sai addu'a, kuma sun yi mata alkawarin haka . Ta ce "zulfa'u yarinyata mommy zata dawo nan ba da jimawa ba, kuma zaki koma hannunta har sai kince inzo in dauke ki. Gaɗa kuma kamar kinyi in sha Allahu saboda mommy zata baki abun yin idan ta dawo ɗin." Ta karashe maganar cikin ƙarfin zuciya, saboda yadda idan ta kalli yarinyar ta ke sake bata tausayi. Kowa ya watse a garin a wannan lokaci sai wanda sukayi saura irin su family Kubra da suke zaman tsammanin ko zasuji labarin ta. Amma jin wannan labarin shine ya sanya malam yanke shawara da su bar garin na wani lokaci. Tunda har yau sojojin sun hana su zaman nutsuwa dan tunda abin ya faru suke musu ihu bayan hari! Dan motsi kadan Zasuyi ta harba roket masu girma suna musu fargar jaji tunda abin ya riga da yafaru to abar jama'a su zauna lafiya mana! Kuma hakan da suke yi ne ya sa duk wani mai son zama yake barin garin. Ko da yaje musu da wannan batun basu ƙi amincewa ba domin gwanda su bar garin su huta da tashin hankali suji da damuwar inda zasu ga Kubra a mace ko ra ye. Nasir dai kawai ya amince ne amma har cikin zuciyar sa kuwa baya son ya bar garin ba tare da ya ga kubra ba. Amma haka suka hada kayan su domin tafiya maihaifar kakannin su Domin su huta zuwa wani lokaci. Kubra zaune ta tafka uban ta gumi ta ji mutum ya shigo ba ko sallama da wasu ledoji a hannun sa ya ajjiye su gefen ta ya ce " Ki dauki Wannan sune kayan amarchin da ake bayarwa a wannan dajin kuma ki sanya a ranki nine shugaban ki idan kina son zaman lafiya ." Jin batunsa na yi dole ma na bashi amsa tunda daga ni sai shi kuma banga wannan zarbaɗediyar abar ba wato bindiga, daman ita na ke tsoro dan haka na ajjiye shawuya gefe na mike cike da ƙarfin hali ina muzurai wai dole Ni gani jaruma na ce " Ko taya zanyi biyayya a cikin wannan auren?" Kallo na ya yi cike da mamaki ya furta " Ban fahimta ba." Sake gyara tsayuwa nayi "Ina nufin aure kan auren da a ka min, taya ina da miji kuma yana raye bai mutuba zan zauna da wani a matsayin miji ?" Dariya ya bushe da ita ya ce, "Kubra!! Wannan doka ce kuma dole ki bi kuma kowa haka ake masa daga lokacin da kika shigo dajin nan idan kina da aure to auren ya watse saboda ke a matsayin sabuwa kike a wurin." Wani malolon taƙaici ya riski allon ƙirjina har ya fara min zugi na ce " To kuwa gaskiya bazan iya zaman nan ba saboda Ni ban taɓa jin wannan lamarin ba sai yau. Kuma bazan taɓa hada jiki da wani ba har sai auren da ke tsanani mu ya inganta." Cike da harzuƙa ya dube ni ya daga hannu ya shimfiɗa mini wani mari Mai zafi wanda sai da na ga wasu taurari suna ya wo. Ba shiri na durƙushe a wurin ina mai zubar da hawayen damuwa . Kallon ta ya yi ya ce zan baki lokacin ki yi nazari kafin na zo na karbi hakkin aurena, na Miki haka ne kawai dan na ga kina jego . Kuma agidan nan ba ki da damar guduwa saboda ko da kin gudu to akwai inda idan harkinje ba hanya sai koguna, kuma mutanen mu ne suke tsallake kowa da umarnin mu! Dan haka zaɓi ya rage na ki. Ko kiyi biyayya mu yi zaman aure ko kuma ki gwada guduwa ki shiga hatsari kamawa, kuma aka she ki........ Yana gama fadar hakan ya kwance ya juya mata baya a kan ƙaramar katifar da yake. Wani irin yanayi ta ji wani abu na son bugeta ta Sume saboda tashin hankalin da ta ke ciki. "Allah ya rabbi ka kawo min sauki cikin wannan uƙubar da nake ciki..... PG 7 Ganin ko ya kula harma ya fara baccin sa hakan ya sanya na tashi daga zaman da na ke na dauki buta na yi alwala duk da cewa ina cikin halin jego. Amma hakan bazai hanani zaman yin addu'a ba, dan haka wuri na samu na zauna na fara kai kukana wurin mahaliccina saboda shi ka ɗai ne zai fidda ni ga wannan ukuɓar dana ke ciki. Tsawon lokaci na dauka ina zubar hawaye gaban Allah ina sanar masa damuwata sai na ga shawuya ya farka na shafa addu'o'in na dauke shi. Nono na fara bashi yana sha ina kallon sa hawayen idanuna suna zuba kan fuskar sa. Da yanzu muna gida da yana cikin net killace cikin kayan sanyi ga yan'uwa sun kewaye mu. Zanci kaza na sha shayi mai kauri na gyara jikina da ruwan zafi! Amma tunda na zo sau ɗaya naga idanun ruwan zafi, abinci kuwa iya ka abincin gado ne wato wake da shinkafa sai su taliya suma kuma duka masu yaji ne. Gari na wayewa ya kawo min kayan abinci masu yawa a cikin harda kayan miya dakuma kifi bushashe. Banyi wasa da rayuwata ba na ajjiye komai a gefe tunda na sanar da mahallici na nasan zai tseratar da ni. Dan haka na zage na daura ruwan zafi na na juye cikin wata kula na daura girki na na dafa taliya da miyar ja wadda ta ji kifi, bayan na sauke na sake daura wani ruwan . Ruwan kular na juye rabi na yiwa shawuya wanka tas farine tas da shi ga idanuwa ma sha Allah kamar na Nasir dan yana matukar kama da shi. Sauran ruwa na ɗiba na shiga dan zagayen da na gani na shiga gayar jikina ba karamin wahala na ci ba saboda gaba daya na yi tsami kasancewar ba kulawa tun farko na sha a zaba kawai daurewa na ke da na fito na samu ruwan ya tafasa shi ma sai na juye cikin kular na sake daura wani na janye wutar saboda ina samu ina kama ruwa da shi wannan na kular kuma shi ne zan dunga sha. Ina so na samu ƙarfi jiki na warware sosai ta yadda zan iya jurewa dukkan wata wahala da zan fuskanta a wajen guduwa dan na ci alwashin tse re wa. A binci na zauna na ci na ƙoshi na sha ruwan ɗumi nan danan kuma ruwan nonon ya fara malalowa domin daman ni daga na haihuwa ba wani jinkiri nono yake zuwa. Dan haka na ki shingiɗe har barci ya yi awun gaba dani abinka da mai jego ba za'a rasa gajiya ba. Kusan kwana shida muka dauka haka har mun fara sabawa da zama wuri ɗaya domin na lura yana da sanyin hali ga kuma ba shi da yawan zaman gida, ranar da muka zauna gida ɗaya muka kusa yini muna dan taɓa hira sai ranar na gane ainahin kamar sa. Fari ne dogo mai tsayi ga jiki gare shi dai dai gwargwado. Ba shi da muni amma kuma bashi da yawan fara'a ya ɗan bani labarin sa saboda ya ce mun mata ɗaya ya taɓayi bai sake wata ba sai yanzu. A raina na ce wannan ɗin ma baka samu mata ba. Daga gare ni dukkan yadda ya so ya ji wani dan labari ban ba shi ba na kance masa na mance komai nawa. Satin mu guda ya fara fita dani bayan gari da nufi na sake da shi domin na lura shi acikin y'an ta'addan ma yana da tausayin mace mai jego . Kowanne na miji yana fita da matarsa yawan shan iska har bakin ruwan da suke faɗa harma wani lokaci wasu suna hayewa domin su samu sakewa da matansu. Kullum mukaje wurin ina lura da dukkan wani

Chapter 2 of 8