da wani burin da ya wuce a ce na
ganni gida. Dan gaba daya zuciyata sai bugawa ta ke ban san dalili ba! Amma kuma sai na ga
wani mutum mai siffar buzaye ya kalli na kusa da shi sunyi murmushi. Nidai na ce Allah ya fi ku
idan ma wani abu ne .....
PG 20
Har mun kusa kai wa maini kawai muka ji wani hayaki ya tur nuƙe mu.
Kowa ya kama tari, shawuya kuwa har da suma tuni direba ya tsaida motar dan haka kowa ya
fita .
Amma mai zai faru! Kawai wadanna mutane guda biyu suka cire wasu manyan wuƙake suka
ce kowa ya bada kudi ko kuma wani kayan kuɗi, amma kaf ɗin mu suka ce ba kudi a jikin su,
dan haka nima daman kudin nawa yana cikin dan kan faina ban masa ruƙo na wasa ba saboda
na san zai min amfani.
Ganin zamu ɓata musu lokacin ne yasa ɗaya daga cikin su ya fizge shawuya ya ɗaura masa
wuƙa a wuya ya ce kowa ya fito da kudin jikin sa ko kuma mu yanka yaron nan a gaban ku
kuma kuma mu yanka ku. Ganin haka tuni na tsare har lumfashina yana sarƙewa na saka
hannu cikin jikina na cire duka kudin da Hajiya ta bani na bashi ina karkarwa, dariyar mugunta
ya yi sosai ya ce, "Allah ya so ki munafuka karɓi ɗanki!"
Ai kuwa hannu yana rawa na karbi shawuya ya yin da kowa ya cire abin da ya ke jikin sa ya
mika masu. Abu guda ne ya bani haushi yadda mutum biyu rak suka tsare duka motar saboda
wuƙar da ta ke hannun su .
Kuma yawancin motar maza ne masu yawa amma saboda tsoran mutuwa ba wanda ya yi
wani yunƙurin ceton mu! Bayan mutuwa dole ce idan lokacin ya cika ba makawa sai an mutu
ɗin, to amma kowa tsoran ta ya ke .
Idan ba haka ba ai Sarkin yawa ya fi Sarkin ƙarfi, a tunani na mai bindiga shine abin tsoro tunda
zai iya harbin ka! Amma mai wuƙa za'a iya cin masu ta dabara idan an so yin hakan.
Ganin na shagala da tunani wata da ke kusa da ni ta ce min " kiyi hakuri kin tsorata ko? Sun
gudu fa muje mu shiga mota."
Ban ce komai ba muka dauki hanya kai tsaye direba bai tsaya da mu ko ina ba sai gaidam.
Sauka kowa ya yi ya fara kama hanyar gidan su masu shiga motar wucewa suna shiga
amma Ni kuma bani da ko biyar da zan shiga motar kananma.
Sai na yi tunani na je wani gida kawai na nemi aron waya tunda dai ban mance lambar wayar
mijina ba sai na kira shi na sanar da shi ina gaidam tunda ba nisa ya zo ya tafi dani.
Dan haka na yan ke shawarar shiga gidajen da suke bayan ta shar maini domin na ga ko zan
samu wayar.
Amma kowanne gida na je ma na lura kamar gudu na suke kawai sai na mike da ta fiya saboda
mun taɓa zuwa gaidam so ɗaya da wata makwafciyar mu na ra kota suna amma kuma gidan
yana chan a ƙarshen gari ne.
Sai na fara gwada tafiya ko Allah zai sa na gane gidan duk da cewa na san akwai nisa tsakanin
tashar maini da anguwar kudu a kwai nisa gaskiya. To amma ba yanda zanyi nan ne kaɗai
zanje na samu wayar ƙiran.
Duk da kasancewar gaidam gari ne da kowa ya san shi da girmama baƙo da bashi kulawa
amma yau na ga saɓanin haka a gare su, ina tafe ina mamakin chanjawar ta su.
Ashe dai na tarar da su suna cikin ruɗin shaidan ne domin kuwa zuwana unguwar na tarar
gidan a kulle ba ko a lamun mutum yana rayuwa acikin sa wata ce ta sanar min da ai ta yi
balaguro.
Tsawan lokacin na dauka ina tunanin mafita sai na ji ana kiran sallar la'asar ga yunwa ga ba
kudi dan haka na yanke shawara nai man taimakon abinci, wani gida da naga yara suna wasa.
Koda zuwa kofar gidan kawai yaran suka watse suna gudu suna faɗin kar mu je ta kwashe
mana.
Mamaki ya sa na kalle su na ce ikon Allah wato har yanzu ban dawo kamar mutane ba ke nan
tunda yara ma suna guduna!
Wata maina na samu na zauna na kira wani yaro da yazo wucewa na sanya shi ya karɓomin
ruwa a wani gida na yi alwala na yi sallar azahar da la'asar sannan kuma na ce dan Allah ya
maida butar ya ce su aramin wayar su zanyi ƙira .
Cike da sa'a sai ga matar ta fito ita da yaron ta ke ce masa ya bani wayar amma ya yi a hankali
kar na kwashe masa dan ita tsoro na take . Mamaki ya kama zuciyata fal, har sai da raina ya
sosu duk da cewa na san yadda na ke a bushe dole ne na chanja kama.
Amma kuma bai kamata ana guduna ba tunda dai lalura ce.
Yaro yana bani waya naga ya buga tsalle ya min gwalo, sai matar ta ce masa lafiya kuwa?
Aikuwa yaro yana jin haka sai ya fasa ihu ya fara faɗin ta kwashe min su! Mamaki fal zuciyata
na ce yau zan ga ikon Allah.
Kafin na ce wani abu wuri ya cika makil da jama'a an fara narko min manyan zagi.
Wayar suka warche suna ja da baya maza suna cukume wandon su mata kuma suna
rungume ƙirgin su, na ce " Ikon Allah ! To nidai gaskiya abin da fari dariya ya bani har sai da na
dara na ce wai lafiya kuke kuwa.
Ai kuwa wata tana jin abin da na ce ta ce "Zaki ci ubaki yau kuwa idan baki dawo masa da
kayan sa ba."
Na ce, "Wai wana kaya ne haka bayin Allah ni fa baƙuwa ce wata na zo nema ban sa me ta ba."
"Yawwa munafuka daman ai baƙin ne suke haka dan dai mu kam kaf! Garin nan ba mai
wannan halin! Aha! A mayar masa kayan sa."
Mamaki ya sake lunke min zuciya na haɗiye wani miyau mai shegen zafi na ce,
"Na ce yanzu kun duba kayan na shi ne kunga babu?"
Duka suka yi kaina suna faɗin ba za'a duba ba ba ɗin kalan ki haɗa da sauran ko to ki yi maza
ki maida masi
Wata cikin su ta sa ke cewa, kuma idan zaki mai da mushi ki maida mishi na shi! Sai ku dau
abin mutum na yaro ku sanya masa na babba, shekaran jiya ma haka wata ta yi a chan layin.
Haka suka dinga jifana da miyagun kalamai har ta kai ga sun fara duka na tukunna wata babba
cikin su tace su daina duka na kar su ƙarasa gawar da ba ta su ba garin ne man gira a rasa
idanu.
Dan haka sai na samu rangwame aka ne mo mai nafef aka tusa kai na ciki na ji suna cewa aje
gidan kangar! Chab ! Duk da ban san ina ne ba amma ina jin makwafciyar mu tana bada labarin
wani wurin horo ne da ake kai mai laifi duk girman sa a bashi kashi.
To ni ba wannan ne damuwa ta ba, a'a ta ya ya zan maida abin da ban dauƙa ba tunda na san
shine abinda za'a tuhume ni da shi.Muna zuwa gidan kuwa wasu zaratan sojojin suka sakani
gaba da tambaya suna cewa ina na kai masa kayan sa, amsa ɗaya na ke bayarwa ita ce "
Bansan me suke nufi ba."
Ya sake cewa "Idan baki mayar masa ba wallahi har oga ya dawo daga kananma zaki sha
wahala."
Sunkuyar da kaina na yi bance komai ba. Saboda kalmar kananma da yace yasa naji farin ciki,
kuma Allah ya kawo ogan ko Allah zai sa ya taimaka min.
Ɗaya a cikin su yace da mai tambaya ta " Wai mutanen garin kanamma duka sun koma ne?"
Amsa ya bashe cewa duka sun koma wanda basu koma ba ma yau zasu koma saboda gobe
gwamna zaije ya basu kyauta.
Ni dai shiru na yi bance komai ba har sai da shawuya ya fasa ihu tukunna na tallafo shi.
Sojan ya zura min idanu kamar ya sanni yana ta faman kallona.....
PG 21
Ranar da su basma da su mama fedo Maryam hadiza da su yarima haidar zulfa'u duka suka
dawo daga gashu'wa saboda jin labarin sanarwar koma war kowa garin komai ya lafa.
Shi kuma Nasir cewa ya yi suje amma shi kam ba zai koma ba har sai anji labarin kubra. Dan
haka duka suka dawo gida ba su zauna ba, suka zo suka tarar garin su ya cika taf da jama'ar
garin hamdala suka yi da addu'ar Allah ya sa sun samu zaman lafiya mai ɗaurewa.
Captain Kamal ne ya dubi Captain jamil ya ce, "Wai duk dan basma ta tafi ne ka zama wani
salihi ne haka?"
Murmushi ya yi ya ce, "Kai fa baka da kirki wallahi, daman Chan ni salihi ne ai."
"Haka ne kam amma a wurin basma ne ka ke salihin tunda na ga har wani tsoran ta ka ke ji."
"Kai malam ka gane fa ba tsoro ba ne kawai tsntsar love ne."
Dariya sosai kamal ya yi ya dubi Jamil har ya na nuna shi, "To yanzu ina love ɗin? Yarin yar da
har ta wuce garin su."
"Wai kana tunanin zan barta ne? Ta turamin hoton yayarta fa, ka ga kuwa duk ranar da Allah
ya sa na same ta zan kai mata ita har gida da ga nan sai mu jone."
Ya faɗa yana masa gwalo kamar wasu yara. Sukuma sauran sojojin suna nan suna har ko kin
su ba wanda ya sanya musu baki.
Sai Chan wani babba cikin su ya ce "Yau zamu wuce gaidam sai mu jira gwamna da ta wagar
sa sai mu wuce kananma."
"Ok sir ba damuwa."
Kallon sa ya maida ga kamal ya ce "Ka ga rabon haɗuwa ya sa ke faruwa ko."
Kamal ya ce "To gaskiya abokina ina maka fatan alheri domin na tabbata kana ƙaunar
yarinyar nan fa, gani ɗaya ka mata ka susuce har da jin tsoro kamar wani so ko."
Naushi Jamil ya kai masa , "Wallahi baka da kirki ni ne sokon ko? Ba damuwa zan kamaka
wataran kai ma ."
"Kai haba ai tsoran mace sai dai kai ɗin amma bani ba kam."
Haka suka yi ta zuba zance har lokacin tafiyar su gaidam ya yi suka dauki hanya .
Ita kuwa kubra ganin irin kallon da yake mata ne ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa,
Kamar dirar mikiya haka ta ji maganar sa. "Yanzu ke kina da wannan ɗan ƙaramin yaron kike
aikata irin wannan laifin haka? Bakya tsoron su cutar miki da yaron ki? Ki mayar musu idan har
kin ɗauka musu kayan su kawai dan yau idan OGA ya zo zai wuce zai Miki illah saboda baya
barin irin wannan lamarin da sauƙi tunda ya yi fama da irin masu rigimar ki ba sa mayarwa sai
dai a gaji abarsu."
Kallon sa na yi kamar ha zan yi magana ba na ce " To taya za su mayar da abinda ba su da
masaniya a kai, bayan basu ɗauka ba."
Shiru ya yi ya kalle ni ya jinjina kai irin zaki sani ɗin nan.
Misalin shida na magrib su Jamil suka shigo gaidam suna zuwa kai tsaye bayan sun gaida da
y'an bariki gidan kangar ya wuce saboda yana da abokai kuma idan ya je yana yawan samun
masu laifi harma ya shiga cikin lamarin ya jibgi masu laifi idan sunyi gardama koda kuwa mace
ce bai cika tausaya mata ba. Amma karo guda da ya yi karo da macen da ta wargaza masa
lissafi har ma ya ke ɓari akan ta.Suna zuwa kuwa suka wuce gidan kangar, shigar su ke da
wuya ya samu zancen maganar kubra cike da mugunta ya ce kubani ita zanyi maganin ta.
Ana kawota sai da zuciyar sa ta buga cike da mamaki ya ke kallon ta kamar ya santa, ya sake
tambayar laifin ta a ka sanar masa.
Hannun ya sanya ya ciro wayar sa ya buɗe ma'a danar hotuna kai tsaye kan hoton kubra ya
sauƙe idanun sa. Saurin ɗagowa ya yi ya kalle ta ya sake kallon wayar duk da irin ramar da ta
yi amma kamarta bata sauya ba, ya furta, "Kubra."
Cike da mamaki ta ɗago ta kalle shi. Amswa ta yi cike da mamakin inda yasan sunan ta.
Bata gama mamaki ba ya nuna mata hoton wayar.
Tabbas itace kuwa a acikin wayar. "Ina ka samu hoto na dan Allah?"
Na jefa masa tambayar.
Maimakon ya bani amsa sai yace " Ya akayi kika zo nan?"
Ban ɓoye masa komai ba tun daga shiga ta gaidam saboda ina son ya bani amsar tambayar da
na masa.
Sannu ya min tare da cewa sauran sojojin da su duba wandon yaron.
Aikuwa ana buɗe wandon yaro aka sami komai nasa ya na nan .
Dan haka cike da ɓacin rai Jamil ya ce,. " Wannan abu ƙarya ne fa ruɗun shaiɗan ne kawai,
dan matar nan bata da alaka da wannan lamarin.
Kuma mutane suna amfani da ƙaryar yara ne ba tare da sun bincika ba, mutum yazo yana
buƙatar taimako amma sai a ɓuge da masa sharri a hau jibgar sa.
Dan haka daga yau munyi watsi da wannan batun.
Kawai yara da sunji ana maganar abu shike nan sai su gwada sai ayi Sa'a jama'a su dauki
kururuwar su.
Ba tare da an duba anga babun ba sai dai aga maidowar .
Haka dai ya kashe zancen kuma ya min albishir da gobe in sha Allahu zai kaini har gida .
Murna a wurina har da russunawa na ke ina godiya har na mance batun ina ya sanni nidai
kawai na ganin cikin gida.
Gari yana waye wa kuwa gwamna ya iso dan haka muka dauki hanyar kananma ina gaban
motar sojoji ram, saboda Jamil ne ya bani wurin sa ya koma baya shi ɗin tsabar yadda hanyar
ta ke farkon fita ba titi mai kyau ga yunwar da ta gama cinye ni ban samu cin komai ba saboda
murna, tuni na fara amai ba kakkautawa har sai da muka je garin gada a ka bani ruwa da doya
na gyara bakina na ci kaɗan muka ɗauki hanya sai kanamma cikin farin ciki.
Har wani gashin jikina na ke ji yana kaɗawa yana miƙewa saboda farin ciki na kuɓuta da ga
masifa zan dawo rayuwar farin ciki.
PG 22
Shigar mu ke nan na ji wani farin ciki ya mamaye min zuciyata wani haske na ke gani tar acikin
na mujiyata yana sake haska min gari.
Na kalli shawuya na manna masa kiss a goshin sa, dan ko ba komai na san tabbas yau zaiga
uban sa kuma jinin sa . Farin cikina guda! Idan na tuna duk wannan gwagwarmaya ba wanda
ya kutsa kai cikin gonar Nasir, sai na ji kai na har sa ke huruwa ya ke. Domin kuwa na yi wani
ƙaramin jahadi ne.
Muna zuwa daidai barikin sojojin muka tsaya nan fa na ga yadda garin ya cika da yawan
mutane kowa yana ta har karsa, bani da wani burin da ya wuce na ganni cikin gida.
Amma kuma basu bani damar tafiya ba, kai ni sukayi wurin ogan su domin ya na son ya yi
hira dani ko zasu su samu wani ƙarin bayani game da dajin da y'an ta'addan suke rayuwa.
Na yi iya bakin ƙokarina wajen sanar masa iya abin da na sani, dan haka daga nan aka ce
aje dani gwamna ya ganni.
Mamaki fal raina yau nice zanje gaban gwamna ido da ido saboda wani dalili. Haka suka wuce
da ni wurin sa ya karɓeni cike da fara'a yana nan nan dani saboda farin ciki.
A chan kuwa tuni jamil ya ƙira basma ya sanar mata ta shirya ya zo kananma kuma yazo mata
da wani abun mamaki dan haka yana son kowa ya zama yana gida dan akwai wani batu mai
mahimmanci.
Jin haka ya sa aka yiwa Nasir waya maza ya dawo saboda suna tunanin ƙila ya samu wani
labari na ne da ya ke son sanar musu.
Dan haka kowa ya hallara suka yi zaman jigun.
Bayan gama tattaunawa ta da gwamna muka ɗunguma zuwa gidan baba bala da kwatancen da
basma ta yi masa kasan cewar garin ba shi da wani girma sosai.
Muna zuwa suka ga motar sojoji kusan guda biyar tare da motar gwamna, ai duka sai suka
firgita suka fara tunanin ƙila gawata ce suka zo da ita.
Dan haka lokacin da baba Bala ya musu iso cikin gidan kafin a basu bayani har sun fara
matsar kwallah.
Nikuwa ina Chan mota ina zaune domin ba su bani damar fita ba.
Jamil ya dubi basma bayan an gaisa da kowa ya ce, "Dan Allah kiyi haƙuri.". Tana jin kalmar
haƙurin nan tuni ta rushe da kuka wanda ya yi dai dai sallama ta cikin gidan, duka suka
zubamin idanu suka ka sa koda motsin kirki ne.
Yarima ne ya yi ƙarfin halin ta so wa da gudu ya faɗa jikina tare da ta fashewa da kuka yana
faɗin, "Mommy na baki mutu ba ashe? Daman zan ganki mommy kafin na zama soja na
karɓoki?......."
Ya ƙarahe cikin kuka wanda ya sanya ni nima tuni na fashe da kukan sai kuma dukkan kannena
suka taso suka rungume ni suna kukan farin ciki.
Jani sukayi suka zaunar dani suka ƙarbi shawuya suna ta kallon sa suna hawaye ganin yadda
jariri da shi amma a lamun ra ma ya bayyana a gare shi.
Koke koke ake ta faman yi kamar gidan mutuwa.
Chan na hango Nasir ya na zaune yana ta kallona yana zubar ƙwallah, hannu na ɗaga masa
na masa murmushi kasa jure wa ya yi yazo kusa dani ya ya ƙarbi shawuya a hannun su
Maryam ya rungume amma idanun sa ba su fasa zubar ruwan hawaye ba .
Cinyar mama fedo na kwantar da kaina saboda gajiyar hanya, hannu ya sa yana shafin kai .
Gwamna na ne ya yi gyaran murya ya ce ma sha Allah Alhamdulillah tunda ta dawo gida lafiya,
sai dai amma fa akwai wata y'ar ƙaramar ƙura da na ke son ku kiyayi bankaɗo ta.......
Dukan mu shi muka zubawa idanu domin muji mai zai ce.........
PG 23
Ganin mun maida hankalin mu gare shi shine ya sa ya ɗan murmusa ya ce, "Karku da mu, ba
wata sabuwar matsala ba ce. Abin da na ke son sanar muku shine bana son a yi ta yaɗa
dawowar ki saboda wata afkuwar matsalar, ina son a bar zancen anan saboda bazuwar
maganar da yaɗuwarta zai sa kuma *bayan gangami* a samu wata ƙura. Ma'anar shine
waɗanda kika gujewa zasu iya sake dawowa domin farautar ranki."
Cike da fargaba na ɗaura hannu akai, "Yanzu dukkan wannan wahalar da na sha kuma sai a
sa ke biyoni?" Na faɗa cikin muryar kuka.
"Tabbas kuwa! Abu mafi sauƙi shine dole ki sauya wurin zama ki bar wannan garin har
zuwa wani lokaci."
Baba Bala ne ya kalle shi ya ce, "Mai girma gwamna taya hakan zai faru bayan nan ne wurin
zaman mu?"
"Wannan ba damuwa ba ce ba idan har kun ɗauki shawarar da na baku."
"A'a ai bamu da wata magana sai ta ka mai girma gwamna, yadda ka ce haka za'ayi."
Haka dai suka tattauna suka tsaida magana guda ya ce da baba bala in sha Allahu zai ne mu
muyi zama na gaba .
Amma kafin nan ya ajjiye mana bandir ɗin kudi na naira miliyan guda ya ta fi.
Munyi farin ciki da wannan kuɗin ba kaɗan ba, dan haka haka muka wuni a na farin ciki da
nishaɗin da koke koke wasu lokuta na murnar dawowar.
Sai wajen magrib tukunna y'an uwa da abokan arziƙi suka sassauta zuwa min jaje da barka da
kubuta.
Bayan munyi sallah ne Nasir ya fita ya dawo hannun sa dauƙe da wata leda ya wuce ɗakin
su basma ya ce da yarima ya kirawo ni, banyi wani jinkiri ba domin nima na matsu na ke ɓe da
shi mu ga na.
Bakin gadon na je na zauna na jingina kaina a ka faɗar sa ya sa hannu biyu ya rungume ni
duka a jikin sa ya ce. "Sannu ƙurraty, haƙiƙa mun ga iftila'in da kuma jarrabawar rayuwa. Amma
Alhamdulillah yanzu komai ya wuce . Ga wannan ki ci yadda kika sha wuya wallahi idan na
kalle ki sai ki na sani kuka idan na ga yadda kika rame gaba ki ɗaya."
Murmushi na yi na kalle shi, "Haka ne kam amma karka sawa ranka damuwa sosai da wannan
abinda na ke so da kai shine kawai muyi ta yiwa Allah godiya.
Ya amsa min da kai ya tura min ledar tsire mai ɗumi da lemon ro ba.
Ci na yi kuwa na yi ƙat na sauke numfashi na yi hamdala ga Allah .
Na kalle shi, "Habibi ya kamata na je wurin su mama kar su mana fassara."
Murmushi ya yi sosai har da ɗan darawar sa, "To ƙurraty kije amma ai gobe zamu koma gidan
mu tunda yau Zanje na share mana komai dare na gyara."
" Haba kai kuwa dan Allah ka bari gobe su basma suje su gyara sai ku koma kai da haidar
kuna kwana amma ni kam sai na yi sati biyu na dawo cikin hayyaci na ."
Baki ya riƙe yana kallona, nikuwa na fice da sauri ban saurari ma wata maganar da zai yi min
ba.
Bayan kwana biyu na dan samu sassauci da zuwan masu jaje dan haka Nasir ya zo muka tare
ɗakin su basma saboda yau suna makarantar islamiyya, sai mama fedo ce da su zulfa'u yarima
da haidar ma suna chan islamiyyar su.
Sani gaba ya yi yace na bashi labarin bayan rabuwa da kuma yadda na samu na kubuta.
Haka na zauna na tankwashe ƙafa na fara bashi labari tunda ga kan rabuwar mu da yarima har
zuwa auren da aka ɗauramin, ganin irin kallon da yake min da kuma yadda fuskar sa ta sauya
kala idanun sa su ka ƙanƙance ya sanya tilas! Na tsaida labarin ......
PG 24
Kallon sa na yi cike da mamakin irin wannan kishin, saboda ni a tunanina wannan ba lokacin ba
ne na nuna kishi ba! A'a lokacin ne na farin ciki da godewa Allah.
Amma kuma sai na ga akasin hakan.
"Haba Nasir me ne ne abin ɗaga hankali a wannan maganar? Ai kamata ya yi kayi murna
tunda dai na kubuta."
"Murna fa kika ce kubra? Yanzu kina faɗa min ammiki aure a kan aurena kuma ki ce na yi farin
ciki?" Ya faɗa yana nuna kansa.
Sakwato na yi da baki ina kallon sa, na kuma rasa me zance masa saboda gaba ɗaya ya bani
mamaki .
Daga haka dai ya fice a gidan ga baki ɗaya.
Haka na cigaba da zama a gidan mu ina kuma jin ɗadin gidan saboda kullum su maryam
basma Hadiza suna tare da ni ga su yarima haidar zulfa'u kullu suna nanne da shawuya idan ba
makaranta.
Kwana na uku da dawo wa Gwamna ya sa aka kaini asibitin damaturu aka duba lafiya ta
nida shawuya muka dawo da kuma alƙwarin da gwamna ya min na bamu gida a dtr ɗin domin
mu zauna.
Cike da farin ciki na dawo na sanar da su mama sukayi farin ciki da hakan, sai dai abin
mamakin ko kaɗan Nasir baiyyi farin ciki ba. Dan dana gama tsara masa bai ce komai ba ya fice
ya barni .
Wani abu da ya ke ɗaga min hankali shine yadda ya daina damuwa da lamari na ya ɗena son
ke ɓewa da ni, kuma ko shawuya baya son ɗauka.
Wannan abin ya na taɓa min zuciya! Idan ni yana jin haushi na shi kuma shawuya mene ne
na sa?" Na tambayi kaina.
Dan haka sai na fita safgar sa saboda an tabbatar min ina da hawan jini, ban sanar da kowa
ba saboda kar hankalin su ya tashi.
Dan haka sai na ɗauke tunani na akan sa dan kar ma na je damuwar sa ta sake sanyawa
yawan hawan jinin ya ta'azzara.
Kamar kullum watarana muna zaune dukan mu soja jamil ya zo akayi masa iso har cikin
gida ya ke sanar min gwamna ya sama mana gida wanda zamu zauna har da su mama fedo,
gidan kuma yana jere ne a layi ɗaya kuma ya mallaka min su.
Farin ciki har da ƙwalla ta haka su mama ma suka yi ta farin ciki da jin labarin, amma Nasir ko
ta ri baiyyi ba har muka gama dukkan bidirin mu sai da baba Bala ya yi masa magana tukunna
ya ce Allah ya sanya alheri.
Fita ya yi waje aka umarci basma da ta yi masa ra kiya tunda dai ita da yarima sune suka san
shi. Murmushi ta yi bata ce komai ba ta bi bayan sa.
Bayan sun fita ne ya ke sanar mata abinda ya ke zuciyar sa game da ita.
Bata ce komai ba ta dawo gida da gudun ta kasan cewar ita ce ƙaramar mu, dan haka sai ta
ji kalmar ta yi mata nauyi.
Bayan mun ƙe be ne a ɗakin kwanan mu na ke tambayar ta tsakanin da ta shi akwai wani abu
ko babu, amma sai tayi min shiru ya yinda Hadiza ta ce , " Wallahi aunty ba banza ba fa wannan
yaƙe haƙwara da ya ke mata kawai ta faɗi gaskiya."
Hararar wasa basma ta yiwa Hadiza tare da kunshe fuska cikin hijab. Shi kuwa yarima da yaga
ta ƙi magana ya ce, "Mommy yana sonta fa ɗan yau har ya faɗa mata ɗazun