faɗin mai kika masa baiwar Allah?
Daga zuwa wuri .
Nidai na yi zuru zuru na kasa cewa uffan ga kowa....
PG 12
Wani irin kallo jama'ar wurin suka bi ni da shi dukan su,hankali na ya yi matukar tashi na fara
ƙokarin yin magana domin na kare kaina.
Mai gari ya ce da ni " Ke baiwar Allah! Daga zuwa har kin fara jefo mana masifa! Wacece
ke? Daman kune irin tsofin Mayun nan na cikin daji da kuke bibiyar al'umma kuna lamushewa?
To ahir ɗinki tabbas kin zo wurin da zaki karɓi hukunci dai dai da abinda kika aikata.
Tunda kalaman bakin sa suka fara furzuwa zuwa masarrafin jina tuni hantar cikina ta yi
muguwar kaɗawa, har wani jiri na ji yana neman ɗi ba na.
Na so ace mutuwa ta zo min nida shawuya a wannan lokacin ko zamu huta da wadannan tashin
hankalin .
Kuma da na san cewa haka zata faru da mu to da kawai zan bayyana kaina a lokacin da y'an
ta'addan suka bayyana a wurin bishiyar nan .
Amma sai dai kash! Bakin alƙalami ya bushe baya bata dawo wa.
Durƙushewa na yi duka a ƙasa na ce.
"Wallahi ban san wannan maganar da kake yi ba, kuma bani da alaƙa da ita.
Hasali ma da zaka ji labarina da zaka......." Tsawar da ya daka min ce ta sani tilas na shanye
sauran maganganun bakina. Sai ya ce,
"Muna fuka bamu nemi jin komai daga gare ki ba, dan haka ki kama bakin ki sake yin wata
magana anan wurin tamkar ƙara wa kanki laifi ne.
Shirun dole ce ta riske ni bani da wata mafita sai wacce Allah ya kawo min.
Yarima ne zaune ya haɗe kai da guiwa yana tunanin mahaifiyar sa. Fedo mahaifiyar Kubra ta
dube Maryam ta ce Kinga Maryam lamarin yaron nan kullum damuna ya ke wallahi, kar ya je
wata cuta ta kama shi. Damuwar da ya yi ko yayan sa bayyi ba.
Maryam ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce " Mama dole ya ka sa mancewa saboda waya
san a irin yanayin da ya ganta , kuma mama tunda kika ga ƙarancin shekaru irin na yarima ya
kasa mance wa da wannan lamarin wallahi mama aunty Kubra ta shiga wani mummunan
yanayi kafin su rabu..... Ta ƙarashe maganar cikin kuka saboda daman neman kukan ta ke yi.
"Haba Maryam yanzu mene ne abin kuka saboda Allah bayan kuma ke ce wacce zaki
rarrashe shi. Amma kuma kina yi a gaban sa ta ya shi kuma zai samu sauki a cikin zuciyar sa?"
"Mama zan kiya ye." Ta furta a chan ƙasan maƙoshin ta.
Miƙewa ta yi jiki ba ƙwari ta nufi inda yarima ya ke ta ɗago da kansa ta rungume shi ta ce
"Yarima yarona kayi hakuri in sha Allah mommy zata dawo kuma ba abin da zai faru da ita."
Ɗago rinannun idanun sa ya yi ya ce ; "Aunty Maryam sunyi mata rashin adalci kuma sai na je
na ƙarbo ta! Aunty Maryam ki taimaka ki sani a ajin sojoji dan Allah na koyi yaƙi na je na ga ni
ko sun kashe min mommy ko tana wurin su." Ya faɗa yana durƙusawa a gaban ta.
Cikin raunin zuciya ta dube shi tace ; "Tashi yarima zan kai ka in sha Allahu kaji, amma ina son
ka de na sanya damuwa sosai a ranka saboda idan ka kamu da cuta to bazasu kar ɓe ka ba
suma sojojin a wurin aikin na su.
Jin ta ambaci ba zasu ɗauke shi ba tuni ya ɗan saki fuska ya ce "To aunty indai zasu dau ke ni
na je na dawo da mommy na daina daga yau."
Murmushin ta yi ta kalle shi "Yawwa yarona haka na ke son ji."
Suna tsaka da hirar sai ga zulfa'u ta shigo da gudu hannun ta dauke da Sweet tana tsalle ta ce
cikin gwarancinta, "Atti na, baba ya bani Sweet ba jan baki ba mommy zan ajjiyewa."
Dariya Maryam ta yi ta ce "Shike nan ɗiyar mommy wato ni bazaki bani ba ko? Ai bazan Miki
wanka ba gobe ."
Tsalle ta fara yi tana shirin kuka tana cewa "Bana sho ni wanka zaki mun gobe na je ba mommy
sweet!" Ta faɗa tana maƙe kafaɗa.
Janyo ta Maryam ta yi jikin ta ta rungume su duka su biyun .
Yayin da mama ta ke gefe tana kallon su cikin tausayawa har sai da ƙwalla ta fito mata ta yi
saurin goge wa..........
PG 13
Suna rungume jikin ta Nasir ya shigo gidan, kallo ɗaya ya yi masu ya gane halin da suke ciki
dan haka cikin sauri ya saki hannun yayan yarima wato haidar ya juya waje saboda tabbas idan
ya tsaya sai yaji hawaye zai zubo masa .
Haidar yaro mai Shekara goma sha huɗu. Ya dube su ya ce "Aunty Maryam har yanzu ba su
dena kukan ba?"
Daga masa kai tayi a lamun basu dai na ba.
Kallon su ya yi ya ji wani mugun tausayin su ya kama zuciyar sa, sai dai ba yadda zayyi da
lamarin tunda haka Allah ya tsara musu sai ya ce da su. "Dukkan wanda ya sake mana kuka ko
mommy ta zo ɓoyeta zan yi nida daddy muna ganin ta bazan kawo ta wurin ku ba.
Jin ya ce haka duka suka ce "Yaya haidar mun daina ka yi hakuri."
"Yawwa yaran mommy to na ji, kuyi murmushi na gani ."
Murmushin suka yi suka kalle shi shi ma ya mayar musu ya ce "To kuje wurin kaka fedo ku
zauna ku bar aunty Maryam ta huta kunji ko."
Kai suka kaɗa suka wuce shi ma ya je ya gaida kakar su ya shige dakin sa.
Zama ya yi a bakin ƙaramin gadon da ya zama wurin kwanan sa tun ɓacewar mommyn su, duk
da cewa yarima ya ga halin da mommy ta ke amma bai kai shi damuwa ba saboda yadda
mahaifiyar su ta ke nuna musu so da ƙauna duka ba wariya farin ciki ya wanzu a familyn su a
lokacin da mommyn su ta ke nan. Saboda shine yaro na farko da suka haifa tunda ya ta shi bai
taɓa ganin faɗan su ba bare hayaniya, kuma kowanne a cikin su yana nuna masa so har ya kai
ya samu ƙanne mommy bata daina sa shi jikin ta ba kamar yadda daddy ya mai da shi abokin
sa . Saboda yana ganin hakan shine zai taimaka masa wajen kula da tarbiyyar sa.
Ko abinci na safe da dare dukan su suke haɗuwa su ci a babban faranti .
Jingina kansa ya yi da bango ya daki bangon yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Ya ce "
Allah ya wadaran sojojin garin mu da suke zaune kamar mata a zo a ci garin da kuke tsarewa
da yaki har a dauki ganima amma ku ka sa komai!!! Yau da ni soja ne a yau zan ɗibi zuga na
baza dajin da aka san suna nan muyi bata kashi na duba uwata!!
Mommy kina ina!!! Ina zamu ganki mommy kewarki ta kama mana zuciya mommy, idan kin
mutu mommy ko gawarki a kawo mana mugani!!!"
Ya faɗa cikin ƙaraji da ihu dan ya mance yanzu ya gama yiwa ƙannen sa faɗa.
Dukkan abinda ya ke faruwa baba Bala ya na bakin ƙofar ɗakin zama ya yi dur shan yana
hawaye ya kasa shiga dakin ya rarrashe shi.
Kubra ta since goyon ta ko zasu ga ƙaramin goyon su tausaya mata, amma da suka zo mai gari
yana ganin sawayen ta ba faratu ya kaɗa baki yana riƙe haɓa ya ce "Wato da maitar ki ta motsa
kika rasa abin ci sai kika cinye fara tanki.
Bari yanzu zamuyi maganin ki yana gama faɗa ya na ƙiran wani mai suna Yakubu da ya kawo
barko no da wuta a turare ta da shi .
Jin abinda ya ce yasa ta figita ta gigice ta ce cikin kuka " Dan girman Allah komai zaku mun
karku haɗa da wannan yaron da bai san komai ba a duniya ko baku tausaya min ba to ku
tausaya masa. Ku rike shi idan kun gama min hukun ci sai ku bani ."
Ina gama fadar hakan na ga duka sun ja da baya wata mace gajeruwa daya gefe ta ce , "Allah
Ya tsare mu riƙe yaron mayya, salon Ya je ya cinye mu wato mu rike shi shike nan kin samu
dama, to baki isa ba. Ai ke ba abin tausayi ba ce! Mayyar mace ai muguwa ce.
Dan haka me gari mafi sauki abin da zamu mata shine a bude ƙasan ta a watsa mata yajin zata
yi bayani da bakin ta ita mayya ce ko ba ita ba ce.
Kallon ta duka jama'ar da ke wurin suka yi suka ce tabbas wannan shawarar ta yi kuwa maza
kuyi mata aiki cikin gaggawa kafin ta ƙame mana bakuna da ƙafafu!
Ai kuwa suna jin haka suka afka kaina suka wangale min zanin ya yinda duka mazan wurin
suka juya baya suka watsa min wani yaji .
Wata irin ƙara na sake ta a zaba ga jego ga barkwano har suma sai da na yi domin azabtar da
Ni da suka yi sai dai Allah na yi ihu kamar zan zare shawuya yana na shi ihun ina ji amma ba
damar daukar sa .
Saboda na kasa zama na kasa tsayuwa kuma awannan halin suka yo kaina da tambaya suna
cewa mayya ce ke ko ba ita ba ce .
Tsabar azaba da masifar da na ke ciki na san idan na ƙaryata hakan wata azabar Zasuyi min na
ce "Mayya ce tabbas na jima ina cinye mutane!""
Salati suke baki dayan su suna tsine mun aka fara kawo ruwa ana kuzamin ina sake yin wani
ihun, ganin zasu cutar da Ni dayawa ya san ya na shiga haukar da gangan na dauki wani ita ce
cikin rumfar nan aikuwa na sauke wa wacce ta sanya min ya ji. Ganin haka suka yi baya na fara
bin su duka da duka ina faɗin duka yau sai na cinye ku ba mai kwana a duniya!!
Sai da na tabbatar sun baje na dawo na dauki guntun jarkar ruwan da suka bari na dunga
wanke gabana da ruwan ina hawaye har na dan samu nutsuwa na dauki shawuya yana gefe a
ya she ga shi jikina duka ya jiki idan na sanya shi dole ya kamu da yaji ko mura ... ....
PG 14
Haka dole na tsaya har kayana su kaɗan sha na ɗan kara shawuya a gefen cikina na kama
hanya domin na bar wannan ƙauyen. Saboda ban san me zasu min gaba ba, gwanda na bar
wurin ko zan samu wata mafaka tunda dai na shigo gari na bar daji.
Da wannan tunanin na kama hanya tafiyar kilo mita guda da rabi ta kawo ni wani babban birni
wanda ban san sunan shi ba, amma bisa ga dukkan alamu garin na ta'alawa ne ko kuma
jama'ar Nijar. Saboda yadda na ke ganin yawancin su kayu kan su a naɗe kamar dai buza ye.
Haka na kutsa cikin garin tare da Bismillah domin neman tsari da ga dukkan sharri.
Kusan magrib na samu wata rumfa a cikin. Wata tasha na fake saboda ban san ina zan nufa ba,
sai kuma tsoro ya cika min zuciya, saboda na san halin mutanen da suke rayuwa a cikin tasha
yawancin su ba na gari ba ne.
Sai na chan ja shawara na fita na sake nausawa cikin garin ko zan samu mafaka.
Wani gida na hanga ga dukkan a lamu gidan na masu hannu da shuni ne dan haka na shiga ba
ko wani ɗar na fara doka sallama cike da sa'a kuwa wata mace kiwon madara da bota ta fito
cikin wani tsadadden leshi ta kalle ni ta amsa min. Abinda ya sanya na ji kwarin guiwa shine
yadda ta amsa min ɗin ba wata nuna kyama ko kuma rashin son jama'a. Dan haka na fara koro
mata ƙudirin da ke zuciyata na son wurin fakewa kafin gobe saboda ina cikin tashin hankali
kuma ban san ina ne nan ba, amma dai na san sunan garin mu kuma idan na samu mota har
gida zan iya gane wa.
Shiru ta yi wanda har sai da na fara tunanin ko ba zata taimaka min ba ne sai chan kuma tace,
"To na ji dukkan bayanin da ki ka min, sai dai yanzu duniya ta lalace ba gaskiya. Amma duk da
haka ba zan barki cikin wannan halin ba zan taimake ki, abin da na ke so da ke shine ki sanar
min da abin da kike so. Na farko na taimaka miki saboda ke mace ce kuma bana son na ga
mace cikin tashin hankali a duk inda ta ke.
Idan kuma kin zo da niyyar wani munafurci ne ko yaudara to Allah ya na ganin ki kuma ya mai
da miki kanki .
"Wallahi Hajiya ba zaki sa me ni da ko ɗaya daga ciki ba in sha Allahu.
"To Allah yasa ina saura ranki."
Ta faɗa tana gyara mayafin da yake ka faɗar ta.
Dago da kaina na yi na dubi shawuya cike da tausayawa na sake mai da kallo na gun Hajiya na
ce, "Wannan nake son a fara taimaka da riga saboda tunda yazo duniya bai taɓa sanya ko da
wando ba ne. Sai kuma idan da abinci ataima kamin da shi saboda wallahi na kai tsawon mako
guda ban ci komai ba.
Sai abinda ya samu cikin kariyar Ubangiji na rayu nida wannan yaron da na raɗa nasa suna
shawuya.
Jin kalamai na tuni na ga tausayi ya wanzu a
fuskar ta, ta kuma jin jina min ta ce, " Muje da ga ciki."
Ta faɗa tana mai juyawa na bi bayan ta cike da farin ciki yau ɗaya zan samu nutsuwa a rayuwa
ta na ci abinci na zauna wuri ɗaya ba tare da wata fargaba ba, tunda dai na ga a lamun
tausayina a wurin ta.
Ciki muka shiga ta kaini wani ɗaki kamar dai dakin sauƙar baƙi wuri ta nuna min na zauna ta fita
jim kadan ta dawo da abinci shikafa da miya harda nama ga wani haɗin shayi mai kauri ta ajjiye
min.
Ta sake fi cewa ta dawo hannun ta dauke da kayan sawa na wa da kuma na shawuya masu
kyawun gaske.
Farin ciki fal zuciyata kamar zanyi ihun murna na durƙuhe a wurin ina hawaye ina godiya .
"Ba komai baiwar Allah ki ci abinci ."
Ta faɗa ta na fita a ɗakin .
Ai kuwa ban yi ƙasa a guiwa ba na fara aikawa cikina abinci sai da na ji na yi hani an tukunna
na ture gefe guda na dauki kofin shayin da na ɗaga sai da na shanye na sauke, wata zufa ta ke
sai na yi hamdala ga Allah .
Mai makon na sanyawa shawuya kaya sai na mance da wannan batun kawai na hau kallon sa
ina masa waƙa abinka da uwa da ɗa.
Shikuwa ƙuru ya yi yana kallona domin ko dariya bai fara ba, idan yana yi ma ban sani ba tunda
ban taɓa samun nutsuwa ba sai yau.
Har wajen minti talatin tukunna Hajiya ta shigo ta dube Ni ta ce, "Ga bayi nan cikin ɗakin kiyi
wanka kiyi ma yaron ki shi ma sai ku sanya kaya ."
Da to na amsa mata ta fita na ta shi na shiga cikin bayin na ga komai yadda yake na san kan
abin tunda dai ni ma y'ar zamani ce kuma wayayya ƙaddara ce ta mai dani haka! Ruwan zafi na
haɗa na sanya shawuya na masa wanka tas bawan Allah yana ta kallo na shidai na ajjiye shi
gefe guda nima na fesa wanka harda su gasa jiki. Na sake dauraye shi fes muka fito zuwa
ɗakin kayan na sanya shi ma na saka masa na shi.
Ba laifi mun ɗan farfaɗo sosai sai dai uwar rama a gareni kam ba magana, saboda kallo ɗaya
zaka min ka ɗauke kai !
Tuni na ji wani irin bacci mai nauyi ya kamani dan haka sai na kwanta kamar wani gida na samu
ba wata fargaba, aikuwa bacci ya ce salamu alaikum.Na jima ina bacci tukunna na farka na ga
Hajiya zaune kusa da ni ta yi min murmushin.
Na ce "Dan Allah kiyi haƙuri wallahi ban san baccin yazo min ba."
"Kai haba dai ai shi bacci baya sallama karki damu. Yanzu kina a jahar Nijar ne kuma cikin garin
zinder. "
Idanu na zaro ta re da furta, "zinder!!"
"Tabbas kuwa."
Ta bani amsa.
"Hajiya ji na yi abun ya yi nisa nifa y'ar jahar Yobe ce kuma a ƙaramar hukumar kanamma.
"Chab! Gaskiya kina ne sa. Amma me ya kawo ki nan? Kuma me yasa kika faɗa cikin wannan
halin?
Shiru na yi kamar ba zan ce komai ba, saboda ban son na tuna koda tsinke ne a cikin labarin a
binda ya faru da ni amma ya zama dole na sanar mata halin da na ke ciki.
Dan haka na tsunduma ƙogin mummunan labari na farko har zuwa yanzu.
Banyi mamaki ba ganin fuskarta sharkaf da hawaye, saboda na san labari na ya chan chanci a
yi masa kuka.
Saboda na fuskanci ƙalubalen da ni kaina ban taɓa tunani ba.
Ta tausaya min matuka sosai yadda kukasan y'ar uwar ta ta jini.
Cewa ta yi da ni, " Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu idan mijina ya shigo gida anjima
zamuyi magana, kuma zaki koma gida da yardar Ubangiji."
Na yi farin ciki mara misaltuwa sosai da sosai dan banyi tsammani samun haka daga gare ta
ba.
Amma kuma babu abinda ya fi ɗaure min kai kamar yadda na ji wayar da Alhaji mijin Hajiya ya
ke yi da dare bayan ya shigo gida........
PG 15
Wani irin yawu na haɗiye da na ji batun nasa saboda na san ko shakka ya ganni ko ya ji labari
na to tabbas nida shawuya gudun mu ya zama na banza! Tunda abinda ya ke nema ne ya
samu har gida.
Kamar na gudu idan na tuna da irin wayar da yake yi saboda kalaman sa babu Allah a ciki
Tunda na ji yana cewa ina zai samu mace mai ɗayen jego ya haiƙe mata kuma sanan ya bada
jinta tunda ba zai iya bayar da matar sa ba!
Ban san me suka ce masa ba dai na ji ya sake ce mu su zai duba lamarin.
Kuma na san tabbas yau Hajiya zata sanar da shi zuwana. Abin da zai ji kawa shine kaya ya
tsinke a gindin kaba!
Ni kadai na ke ta batun da ba ni da mafita. Shin ko sulalewa zanyi na gudu ne a cikin daren
yau? To idan na gudu kuma me Hajiya zata fassara Ni?
Idan kuma na zauna har garin Allah ya waye to tabbas na san Alhaji zai so ya ganni!
Da wannan tunani dai na ke zaune har na fara jin ya kamata na sanar da mahallici na domin
shine komai na wa a duniya ta da kuma lahira ta.
Alwala na yi na hau darduma na fara karatun Alkur'ani cikin ƙasa da murya tunda dai ina da
sauka a kaina dan haka na yi ta karatu har zuwa wani lokaci da bacci ya fara cin ƙarfina,
addu'o'in ne man tsari na yi na sanya sakata a ɗakin domin ji na ke cikin dare ma Alhaji zai iya
zuwa ya same Ni dan haka sai da na sa sakata na kwanta.
Basma ce ta ke ta faman tafiya bakin titi hannun ta dauke da manyan ledoji na kayan ɗanyen da
ta siyo a kasuwa hannun ta ɗaya kuma rike da hannun yarima har sun zo zasu gifta wata mota
ta jam'ian tsaro ta ji yarima ya kwace hannun sa daga na ta motar ya nufa da gudun sa ya sha
gabansu wanda tilas direban motar ya ja wani wawan burki! Ganin abinda yarima ya aikata tuni
ta shiga damuwa saboda da sun buge shi ya zatayi ? Kuma ta san halin sojojin nan da masifa
shin yanzu wanne hukunci zasu ɗauka a kanta tunda zasu ganshi ƙarami ne ƙila suce ita ce ta
sanya shi .
Tuni wani soja ya duro daga saman motar ta su ya tun kare shi, kafin ya yi magana yarima ya
fara magana kamar haka,. "Yawwa zo ka kashe ni tunda ko ina kuna nan kuna yawo amma kun
ƙi karɓo min mommy daga hannu y'an ta'addan da suka sace ta! Ka kashe ni don Allah na huta
da wannan damuwar! Kashe ni ko zan dai na tuna halin da mommy ta ke ciki. Bana son rayuwa!
Na ce bana son rayuwa!!
Ya faɗa cikin amo mai sauti! Wanda dukkan wanda ya ke kusa sai ya juya.
Ga baki ɗayan su sojojin sai da suka tsaya suna kallon yarima, ni kuwa ƙamewa na yi da
tunanin irin hukuncin da yaron zai jamin.
Amma cikin iko na Ubangiji sai na ga ɗaya daga cikin sojojin ya zo kusa da shi ya durƙusa ya
rungume shi ya na hawaye.
Cike da mamaki na saki ledar kayan hannun na suka zube ƙasa saboda ban taɓa ganin soja
yana kuka ba. Kuma ance suna da taurin zuciya ba sa kuka da wuri.
Amma kuma sai ga akasin haka a wurin wannan sojan.
Ya ce "Yarona ka yi hakuri mommy zata dawo gida ka ji, ka tuna min yadda na rabu da uwata
amma ban samu ko ganin gawarta ba. Haƙika uwa uwa ce, idan har wannan yaron zai damu da
uwar sa to tabbas uwa ba abin ya da wa ba ce. Haƙika na tausayawa wannan yaron saboda
yana cikin maraicin uwa, kuma wallahi da da yadda zanyi a yau sai na je na dawo da mahaifiyar
sa. Amma sai dai kash! Nima umarni na ke bi.
Ya faɗa yana ƙarewa sauran sojojin kallo .
Wani daga cikin sojojin ya ce ina wacce kuke tare? Ko kai kaɗai ne?
Wata irin faɗuwar gaba ta riske ni saboda na san dole sai sun min tsawa kuma ban kaunar ko
da kallon soja ne a rayuwata bare magana da shi.
Dan haka yarima yana nuna ni na fara mazari ina ƙifta idanuna.
Kalaman sojan ne suka daki masarrafin da ke kai min sauti, wani yana yi na ji gaba ɗaya ya
riski zuciyata saboda ba haka ka tsammachi muryar ba.
Dan na zaci zan ji ta kamar sauƙar aradu ne.. amma kuma sai na ji ta cike da sanyi da nishaɗi
wanda har sai da na lumshe idanuna na bude.
Ganin ban ce komai ba wani daga sama ya rattaɓa min tsawar da sai da na take ledar kayan
miyan.
Da in ina na fara magana, "Don Allah kuyi hakuri yana cikin damuwa ne wallahi bani na sanya
shi ba. Kuyi hakuri."
Murmushin na ƙasan ya yi ya ce "Ka ma shi ku tafi ki sanar min da gidan ku an jima zan so
wurin baban sa idan yana nan."
Sanar masa na yi cike da fargabar abinda zayyi na kama hannun yarima na su ri kayan miyan
na yi gaba ba ko wai wa ye.Sauri na ɗinga yi har muka dawo gida.
Koda mama ya Fido ta ganni cikin wannan halin ta san akwai abin da ya faru, dan haka duka
suka tsare ni da tambaya.
Banyi ƙasa a guiwa ba na sanar musu komai da ya faru.
Kowa ya yi mamaki a kan abinda yarima ya aikata.
Dan haka Hadiza ta kama hannun su ta ce "Karka sa ke wasa da rayuwar ka da sun buge ka
fa? Bana son irin haka.
Shi kuwa faruk kasa cewa uffan ya yi har sai da aka ce wani soja yana magana a bakin ƙofa
tukuna ya yunƙura ya fita saboda baba baya nan dole shine zai wakilci gidan .
Koda gari ya waye kubra ta kasa samun sukuni, jin an taɓa kofar ba ƙaramin tashin hankali ta
shiga ba da ƙyar ta samu ta buɗe.
Ganin Hajiya dauke da manyan fulasai na abin ƙaryawa ya sa dole na ƙirkiri murmushin dole
tare da russunawa na gaida ta .
Amsawa ta yi cikin sakin fuska ta kuma sanar min da na ci abinci zata zo muyi magana anjima
idan na gama.
Ko da ta fita sam na kasa sanya abinci a bakina saboda sai na ji kamar an sanya min wani abu
acik. Amma idan na tuna da halin kirki irin na Hajiya sai na ji kawai bazata sanya min komai ba,
kuma ƙila bata san ma mijin na ta yana aikata wani mummunan aiki ba.
Da haka na ƙudiri niyyar cin abincin.
A falon Hajiya kuwa Alhaji ne zaune yana waya cikin raɗa yana cewa, "Ranka ya daɗe in sha
Allah komai ya zo karshe.......
PG 16
Shigowar Hajiya ya sanya shi ƙatse wayar yana faɗin "Hajiya bari na je na dawo wani lamari ya
ta so min da wuri."
"To Alhaji kuma na ce maka muna da baƙuwa mai neman taimako amma da ka tsaya ka ganta
ai."
"Kash! Hajiya ina ce a gidan zan kwana? Maganar nan abarta idan na dawo ma yi ta."
"Shike nan yadda ka ce, Allah ya dawo da kai lafiya."
Da Amin ya amsa ya na saɓa binjima a ka faɗar sa ya fice.
Cike da damuwa ta zauna a falon saboda ta so ace ya ji batun ta sun taimaki wannan baiwar
Allah da ta ke neman taimako.
A ɓangare Kubra kuwa abinci ta ci ta ƙoshi saboda ta miƙiwa Allah lamurran ta duka!
Shigowar Hajiya ne ya sanya ta ta yi zuru tana jiran taji mai zai faru.
Hajiya kuwa zama ta yi gefen ta ta ce, "Kubra, ina me baki haƙuri saboda Alhaji ya fita cikin
gaggawa bai tsaya ya ji batun ki ba,