Share this page
8 / 8
ya fice a gidan, ita kuma ta mike ta min gwalo ta shige cikin ɗakin ya rage daga ni sai Nasir. Duban sa na yi cikin kuka na ce, "Kai kuwa mai na maka ka maida zaman auren mu haka? Mai na tare wa rayuwar ka? Wai wanne laifi na maka wanda har ya kai ka saka min da wannan butul cin? Kasan irin gwagwarmayar da na sha domin kare mutuncin ka? Ka san faɗi ta shin da na sha kuwa? Nasir mai yasa ka zama butulu mai bakar zuciya? Ka mance irin soyayyar da take tsakanin mu? Haba Nasir ka tausayawa rayuwar mu mana ko dan yaran ka." Na ƙarashe maganar cikin kuka. Bai ce dani uffan ba ya bini da kallo yana mai shigewa ɗakin matar sa. Bayan na gaji da tsayuwar nima na shige nawa ɗakin ban sake fitowa ba har sai da yarana suka dawo gidan tukunna. A falo muka yada zango muna karatu nida su amma ba ko kunya Nasir ya leƙo kai ya ce mu rage murya muna damun su. Bance ƙala ba ban kuma kalle shi ba. Haidar ne ya ɓata rai ya ce, "Mommy wai kawai dan daddy ya yi aure sai yana mana haka har da ke kuma." Harara na banka masa dole ta sa ya sunkuyar da kansa , Na ce "Haidar baban ka ko me zayyi fa baban ka ne dan haka bana son na ji wani ƙorafi ya fito daga bakin ka indai har akan baban ku zakayi shi." To ya ce badan ya so ba na ce dasu mu tashi mu shiga cikin ɗakina kawai muƙarasa karatun, haka kuma mukayi a chan muka gama har lokacin sallah ya yi. Haka muke ta fama da rayuwar mu ni da yarana a cikin gidan nice da gida sune da isa ita kuma mandiyar ta sa ta samu ɗaurin gindi sai yadda ta ga dama ta ke yi a gidan. Rayuwa mai tafiya ce kamar wasa har an sanya lokacin bikin basma da Captain Jamil, Haka su Maryam ma sun fidda mijin aure Ita da Hadiza saboda duka za ayi bikin a ta re. To dan haka duka hankali na yana kan hidimar bikin ne a matsayina na babbar yayar su, Basma kuwa cewa ta ke ita wallahi aure ya fita kanta saboda yadda Nasir ya juyamin baya duk da irin soyayyar ta ke tsaka nina da shi . Zaunar da ita na yi har ma da su hadiza ɗin na ce musu, "Shi fa aure da kuke ganin sa daman ya ga ji ƙalubale a cikin sa kuma kowanne bawa da ƙaddarar sa a rayuwa, dan haka kuyi ta addu'a Allah yasa mazajen da zaku aura su zama haske a cikin rayuwar ku. Kuma daman dole shi aure wani zama ne na a sa ɓa kuma a gyara ba wai zai kasance irin soyayyar layi ba ne. A'a ya danganta da kalar mijin da kika aura din. dyan haka kuyi hakuri da mazajen ku a ko wanne hali shi yasa zaku ji motsi kaɗan ance sai hakuri fa wance, to zaman auren ke nan daman . Kuma in sha Allahu ina muku fatan alheri a rayuwar ku baki ɗaya." Duka rungume ni sukayi suna kuka wai su wallahi ba su son rabuwa dani. Dariya na yi musu saboda sun fara da wuri na shige toilet ɗi na na barsu a wurin zaune. A ɓangaren Nasir kuwa ba abinda ya sauya daga gare shi a halin sa da matarsa . Amma kuma duk da haka ban rasa komai ba saboda dukkan wani abu da ya samu na taimako jama'ar hijira to gwamna baya mance wa dani har ma da shi kan sa, ba kama layi ba shan wahala namu har gida yake zuwa mana, kuma hakan ya na samuwa ne daga gwamna saboda yana duba wahalar da na sha . Shi yasa a rayuwa ba zan mance da gwamna *mai mala buni* ba saboda ya min alheri masu mugun yawa a rayuwata . Da irin taimakon da na ke samu wajen sa na samu na fita kunyar auren ƙanne na. Biki ya kusa na shirya komai na gyaran jiki domin kuwa wurin shahararriyar mai gayran jikinnan na kai su dukan su wato UMMU HEEBBAT ta gyara min su da kyau ciki da waje kama da kan turaren da amarya ya kamata ta turara a cikin jikin ta da kuma jikin ta waje da abinda zata sha ba mai cutarwa ba masu inganci ba wanda kuma ya fi karfin su ba,saboda wani lokaci ana bawa amare maganin uwargida garin gyara, to ta ina zaku hada maganin da wacce ta saba da wacce yanzu zata fara zai zama guda? Shi yasa da zarar ankai amare zasu fara rawar ƙafa jira suke kawai azo wurin. Tunda an gama haukata su, to ita Ummu HEEBBAT tana kiyaye hakan . Dan haka sun sha gyara sun fito sai ta shin ƙamshi suke ga wani yalƙi da suke kamar sabin babys, kuma duka wannan aikin Ummu HEEBBAT ne. Haka har Allah ya kawo mu ranar bikin dangi kowa ya hallara har da jama'ar gashuwa da kananma duka sun hallara a dtr an sha biki cikin farin ciki kuma dukkan su suma ba a gari bane. basma gashuwa aka kaita saboda jamil ɗin a chan ya ke aiki. Mun sha kukan rabuwa da basma saboda mun fi kowa shakuwa da ni da ita. Har ɗakin ta na mata raki a garin gashuwa, kuma na samu jamil na bashi amanar ta da kaina saboda kaunar da na ke mata ta daban ce. Da kyar muka rabu ranar da zamu dawo dtr ɗin an sha fama tukunna. Amma tijarar da na tarar Nasir ya shuka min a gidan sai da na ji dama ban zo ba. Kuma na saka a raina daman saboda baba Bala ne nake daga masa kafa amma tunda ya bi mutanen kananma duba gonar sa dan haka na ce yau za'ayi dukkan masifar da za'ayi agidan koda kuwa karshen zamana da shi ya zo.......... PG 30 Last book 1 Kallon kallo muka tsaya yi nida Nasir na ce, "Me zan gani haka? Nasir nida gidana har ana min waje da kayan ɗakina." Na ƙarashe maganar ina nuna kaina. Amaryar sa ce ta zabura ta ce, "Eh haka na ke so wannan ɗakin zan koma idan kuma da gaske gidan kine kamar yadda kike tun ƙaho sai ki hana mugani. " Ta faɗa har tana wani kaɗa jiki da hura hanci. Nasir ɗin na kallah, "To ka sanar mata gaskiya a kan gidan idan ma ka ce mata naka ne kuma yau dole wannan ta bar gidan tunda ba gidan tsoho be ne ! Nasir na gaji da rainin hankalin da kake min a cikin gidan nan dan haka wallahi yau ko da zai zama silar rabuwar mu da kai sai ta bar gidan nan yanzu ba sai an jima ba." Na faɗa ina sauke lumfar-fashi saboda ban saba da masifa ba sai da ta riske ni . Kallona ya yi ya watsar ya je wurin amaryar sa ya ce da ita, "Baby kiyi haƙuri bata da hankali kinsan duk wanda yayi zaman daji kansa sai ahankali, gida kuma karki kula ta da wannan shirmen nata da ta ke yi gida dai kin shigo ke nan sai mutuwa." Sakwato na yi ina al'ajabin kalmar shi ta zaman daji ban san sanda zuciya ta zare ni ba na dauƙi wani takalmin sa sawu ciki na kwada masa a bayan sa ita ma na buga mata a kai na ce, "Hauka ka ce ba? Yanzu zaka ga ainahin Hauka ! Fuzgo ta nayi tana ƙokarin kai min duka na buga ta da bango ta fasa ihu! Ganin jini ya ɗan ɓullo a goshin ta sanadin gorjewa tuni ya yi kaina ya lafta min mari tare da faɗin na sake ki kubra! " Chak! Na tsaya da komai na ji kalmar har cikin jikina duk kan gaɓoɓin jikina sai da suka amsa kalmar. Wani tashin hankali ne ya ziyar ci zuciyata saboda ban taɓa jin wannan kalmar a zaman mu ba sai yau. Cike da damuwa na ɗaure zuciyata na haɗiye kukan da yake shirin to na asirin zuciyata na ce, "Na ji na gode sosai amma yanzu abarmin gida!" Take ya fara wani borin kunya dan haka ba yadda zayyi da ni ya ce, "Baby zo mu tafi idan manya sun shiga lamarin ta barmin gida!" Da wannan yaudara ya samu kanta suka haɗe dukkan kayan su suka fita suka barshi a wurin. Ɗakina na shiga na zauna bakin gado na fara rafsa kuka saboda wallahi har zuciyata ina ƙaubar Nasir ban taɓa tsammani zai sake ni saboda wata ba, sai gashi yau ya ƙaryata zuciyata da gurbataccen tunanina. Har ma nayi dana sanin shiga harkar sa. Sai wajen awa biyu suka zo da mai jega ya kwashe musu kayan su ya jefa min shaidar sakin ya yi gaba abinsa. Bayan na sha kuka da godewa Allah akan irin tawa ƙaddarar nazaci bayan gangamin da na sha a dajin idan na dawo gida zan samu salama ashe da ma nayi zamana da sabon mijin da na aura a dajin wataƙila tunanin yarana da iyaye ya sa na zama mai gajeren kwana na mutu na huta! Sai dai kash! Bakin alƙalami ya bushe, aikin gama ya gama. Koda na je wa da mama da batun ta min faɗa sosai amma kuma ita da kanta ta ga rashin kirkin Nasir da abinda ya min,kuma ta ce dani idan har ya zalunce ni na zuba idanu tun a duniya zai ga sakamakon sa. Haka na ci gaba da zama da yarana har tsawon watannin uku kuma koda baba ya dawo bai wani ɗauki zafi sosai a kaina ba. Dan haka na dan samu sukunin rayuwa ya yin da shawuya ya ke da shekara uku a rayuwar sa . Ba laifi ya zama lukuti duk da cewa gaba ki ɗaya shayarwar sa na yi ne cikin tashin hankali. Su yarima da haidar kuwa yanzu suna jss 2 ya yinda zulfa'u ta ke primary 4 Ba zato ba tsammani watarana muka tashi da wata mutuwa wacce ta yi sanadiyar shigar dukkan dangin mu tashin hankali wanda idan kuka cire mama da baba to bawan da ya kaini tashin hankali kai wani lokaci ma har gwanda su mama da baba tunda suna zaune saɓanin nida hankali na ma ya gushe. Tunda dai da zarar na dago kai idan na tuna cewa babu basma a cikin duniyar da na ke sai na sake sume wa,a Gaza gane wa yake dan dama dama tsakanin nida jamil, kamar akan mu aka fara mutuwa. Na shiga wani yanayin da har sai da aka fara sallama rayuwa ta tunkunna na dawo ɗan kaɗan Na sha jinya na lalace amma bayan wani lokaci na samu nutsuwa har ma na fara fita aikin da gwamna ya sama min wanda ya samu ne a lokacin da bani da lafiya, an yi shine amin bazata amma kuma da aka zo aka tarar bana hayyaci na. To da na dawo normal kuma sai na fara rayuwa kamar komai bai faru ba duk da dai cewa akwai tabon a zuciyata. Ji na nake kamar wata sabuwa yadda komai ya ke guda cikin rayuwarmu nida yarana lafiya. Amma dawowar Nasir cikin rayuwa ta, da irin kashin shanun da ya shafamin a fuskar dukkan wanda yazo aure na, shine tashin hankali da ya zama barazana ga rayuwa ta har ya kai ga jama'ar da muke tare duka suna baya baya dani. Ban gama sanin Nasir mugu bane sai da ya min wani mugun sharrin wanda duka duniya ta ɗauka ya barni cikin halin ni 'yasu........ Alhamdulillah anan na kawo karshen book1 In sha Allahu zuwa wata na biyu a sabuwar shekara wato fabarairu zan zo muku da na biyun sa Ku kasan ce dani ta ku Ummu HEEBBAT. Ina muku fatan alheri fans a duk inda kuke na gode sosai da yadda kuke min addu'o'in alheri saboda wannan littafin Ƙarshe. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8