Share this page
7 / 8
da muka raka shi." Ya faɗa yana dariya. Jin batun yarima ya sa ta tashi ta gudu ɗakin mama fedo . Dariya sosai mukayi Maryam ta dubi yarima, "kai kuma wato harda gulma ka yiwa aunty basma ko? Ai nan gaba bazata sake neman raki yar ka ba wurin soja." Dariya ya yi ya ce, "Ai kaka zai ce ta je dani." "Sai na ce masa ka zama mai gulma ai." Dariya duka mukayi wan da ya yi dai da da zuwan mama fedo ta shigo tana faɗin, "Mai yaran suke shiryawa ne suka wa re ni gefe." Murmusawa na yi na ce,. "Mama muna shawarar auren autar ki ne." "To bari na koma wurin auta kuyi shawarar." Ta mayar da ƙafarta waje." Sauri na yi na ce "A'a mama mungama ki shigo." Murmusa ta yi ta shigo ta zauna muka ci gaba da hira har dare ya raba. Anan ne kuma suka bani labarin yadda yarima ya ku buta. Na yi farin ciki sosai da irin yadda ba fulata na ta riƙe min amanar da na bata, kuma na yi akwarin in sha Allahu zai kai mata ziyara idan na warke.Bayan kwana biyu baba Bala ya sa me ni da batun ya kamata na koma gidana idan na yi kamar sati kuma sai mu fara shirin koma wa dtr ɗin. Ban ƙi ta shi ba na ce in sha Allahu zan sanar da Nasir ɗin. To amma Ni har fargabar yiwa Nasir magana na ke akan ko ma war , tunda dai na ga dukkan yadda ya ke son na koma gidan yanzu ko zancen ba ya yi . Kuma bai sake ce min yau she zan koma ba. Amma duk da haka na ɗaure na sa me shi da maganar bayan ya zo sun gaisa da baba Bala na sa haidar ya tsayar min shi, saboda idan ban tsayar shi ba nema na ma ba zayyi ba zai wuce. Abin mamaki abin ɓaƙin ciki shine kalmar da ya furtamin wacce sai da ta afka Chan ƙasan zuciyata. Har ma na yi da na sanin yi masa maganar. Ina ce masa nasir ya kamata gobe na koma kafin mu tare sabon gida ya aika min da wata harara, amma duk da haka sai na ce da shi "Yaron nan har yau ba shi da suna balle yanka yaushe za'ayi masa?" Cike da izza ya dube ni ba ko kunya ya ce, "Kubra! Wallahi ba dan na san kina da ciki ba kika fita Allah da wannan yaron ba wa bane ni sam......" Ya faɗa yana yarfe hannu. Cike da bugawar zuciya na kalle shi har wasu hawaye masu zafi na ce, "Nasir! Kasan mai ka ke faɗa min kuwa ...........a fusace ya juyo cikin masifa............. PG 25 Cike da mamakin maganar ta sa ta tsaya min cikin zuciyata! "Haba Nasir wai me ya ke damun ka ne? Me ya sa kake min haka ne? Nasir ko ka daina sona ne ban sani ba?" Na ƙarashe maganar cikin sautin kuka. Kallona ya yi ya zauna gefen wani itace, "Kubra lafiya kalau nifa amma wallahi gaskiya zan sanar miki tunda kika ce kinyi aure kan aure na wallahi ina da shakku a zuciyata! Saboda taya zan yi farin ciki da matar da ta haɗa jiki da wani bayan ta na da aurena? Haba kubra kimin adalci mana idan na ce miki har yanzu kina zuciyata zaki yadda." Wani irin tashin hankali ne ya riski zuciyata na kalle shi na sake kallon sa cike da mamaki! "Nasir yau ni ce ka ke gudu? Nasir ka mance irin tarin ƙaunar da na ke maka ne?" Ban bari ya ji wani bayanin na ba na juya cike da ta fasar zuciya na shige ɗakin su basma,har wasu taurari na ke gani suna hana min ganina sosai. Gadon na faɗa na kwanta ina wani irin kuka mai tsuma zuciya. Shi kuwa gidan sa ya wuce cike da damuwa domin har ransa ya ke jin ba ɗaɗi akan abinda ya min, amma kuma idan ya tuna kalaman sadauki abokin sa, sai yaji kawai ko ma mai zai faru ya faru. Ganin halin da nake ciki ba mai ɓullewa ba ne yasa na fara sanar da mahallici na halin da na ke ciki, saboda shine gatana a duniya da lahira. Haka baba ya maida ni gidan Nasir ba tare da jin ta bakina ba. Bai ce komai ba ganina a cikin gidan sa tare da yaran sa, dan haka nima na cigaba da zaman shirya kayan ƙaura zuwa dtr ɗin haidar ne ya ke taya ni haɗa kayan ya yinda yarima ya ke ta yiwa shawuya wasa sai ga basma ta shigo. Da farin ciki na tar ɓe ta ta zauna ta da fa ka faɗata. "Aunty za'a koma binni." "Basma kamar ban taɓa zaman gashuwa ba?" Na faɗa ina riƙe haɓa . Dariya sosai basma ta yi. "Aunty yanzu dan Allah taya zaki haɗa gaashuwa da dtr kuma? Taya state da local government zasu yi ɗaya?" "Basma ke nan ni a wurina duk ɗaya ne fa tunda dai rayuwar gayu ce kuma nima na iya ɗaukar gayun ba shike nan ba." "A'a aunty duk dahaka sai kin kula sosai kar su gane ke y'ar ƙauye ce su raina min ke, kin san su da jiji da kai fa mutanen dtr." "Haba ke kuwa ai kowa kika gan shi wuri to tilas ya san yadda zai zauna da ma'abota wurin domin gujewa raini, karki damu." "Yawwa aunty na haka na ke son ji ." Sai wajen dare muka gama haɗa kayan duka muka loda su gefe cikin gidan, kwansilik basma ta yi mana wanda yarima ya taya ta cura mana yaji jajjage ya sha manja sosai yaji komaibya sha maggi, har da salat ta yanka mana a ciki . Bajewa mukayi muna haɗiɗiyar sa basma ta kunna waƙar salim smart na Allah ya jiƙaina idan har ba ke wa'aɗin rayuwata ya zo karshe. Rerawa ta ke tana cin dan sulut din kamar ita tayi wakar kallon ta na tsaya yi har sai da ta fara min dariya. Ta ce " Aunty wai dan Allah ki daina kallona." "Bazan daina ba basma, Wato irin kin fara soyayya ɗin nan ko? Shine kike nuna min." Na faɗa cikin zolaya. Kunya ce ta kama ta sai ta rufe idanu kasan cewar ta mai kunya sosai. Bayan sati guda da komawa ta ne muka haɗa komai mu da su mama fedo da baba Bala da basma mukayi ban kwana da jama'ar garin mu ba tare da sun san garin da zamu koma ba. Saboda tsaro. Mun sauƙa lafiya gida kuma ya yi masa Allah a anguwar sabon fegi ya ke kusa da ladabi suya. Gidan su mama gida ne mai dauke da ɗakuna uku da falo a tsakiya wanda ya ke kunshe da toilet a kowanne ɗakin sai karamin kitchen da kuma wani bayi a waje da kuma tankin ruwa babba. Haka gidan da na ke ya ke shima sai dai shi har da wajen ajjiye mota da kuma wurin dinning table. Farin ciki gaba ɗaya ya bayyana a fuskokin mu amma banda Nasir . Kwanan mu uku ya koma kananma ya ce zai je ya dawo. Amma shurun sa har wajen sati biyu kuma layin sa baya shiga. Kwatsam basma ta na zaune a kayi sallah ma da ita tana fita sai ga Captain jamil, dan haka na ce ta yi masa iso kawai falona . Bata ɓata lokaci ba ta sauke shi kuwa, yarima ya je wurin sa suka gaisa saboda dukkan sanda ya zo sai ya nemi shi, ya ce yana matukar kaunar sa. Amma bazan mance kalaman da na ji jamli ya na faɗawa basma ba wanda har suka sanya ni kasa tsayawa ya tafi na ji gaskiya lamari. Har sai da na fito wurin da suke zaune.......... PG 26 Fitowa nayi ina riƙe da baki tsabar mamakin abinda na ji jamil ya na faɗa, ban yi ƙasa aguiwa ba na doshi wurin su , amma kuma sai na ji bai kamata ba kawai sai na waske na yi hanyar da zata sada ni da kitchen. Koda na shiga kitchen ɗin mu kasa taɓuka komai na yi tsabar farin cikin da ya mamaye min zuciyata, Allah dai ya sa kunne na dai dai ya ji min ba zolayata ya ke ba. Aikin dole na kama yi ganin bai dace na sake koma wa ta gaban su ba. Kusan awa guda ina zaune cikin kitchen ɗin tukunna na ji fitar su a falon dan haka da sauri na dawo falo na zauna ina tsumayin jiran basma. Bata jimaba ta dawo cike da farin ciki a kan fuskar ta. Kasa jure nawa farin cikin na yi na mike na same ta tare da riƙe hannun ta na ce, "Basma, sanar da ni dalilin da yasa kike farin cikin nan." Murmushi ta yi, "Aunty sai kin bani tukuici tukunna." Murmushi na yi na kalle ta "Karki damu zan baki." "To aunty shike nan, na san ma kinji ai amma dai bari na sanar Miki. Gwamna ya. Ce da ke da baba da mama fedo bana azumin sai a Saudiyya." Ta faɗa tana rungume ni. Sa ke rungumeta na yi muka yi ihun murna har sai da su haidar suka fito a ɗakin su suna kallon mu. Suma da muka sanar musu murna suka hau, yarima kuwa har da rawa wai zan kawo masa bindigar roba da mashin. Haka dai muka yi ta farin ciki nida yaran daga ƙarshe muka ta fi gidan su mama muka yada zango. Mama da muka sanar mata harda hawayen farin ciki. Baba ma ya yi farin ciki sosai Sai dare muka koma gidan nida basma ita ce muke kwana tunda Nasir bai dawo ba. Zama na yi bakin gadona na dauki wayata na fara gwada layin Nasir na waya amma shiru baya shiga, na gwada ya kai so biyar amma amsar ɗaya ce. Haka kurum na ji zuciyata ta yi min zafi, na so ace wannan farin cikin da Nasir zamuyi shi. Amma ya maida kansa ge fe, kuma hakan ya yi mugun tsayamin a zuciyata. Saboda tsawon zamana da shi bamu taɓa samun saɓanin da zai kai ya yimin yaji ba, amma yanzu ya yi min a lokacin da na fi bukatar sa a gefe na. Haƙiƙa ina kaunar Nasir domin zamana da shi ma ya fi ƙarfin a ƙirashi da soyayya sai dai ƙaunayya. Amma ga shi yau ya juya min baya, baya ko tausayin halin da na ke ciki. Ina amfanin kishi akan abinda baka da tabbas. Na ƙarashe maganar tare da goge hawayen da ya ɓurtso da ga Idanuna. Ban san ya zanyi da shi ba ya daina guje min da zanyi, shi kuma ya gaza fahimta ta. Ya Allah ka shiga lamarin wannan zaman na mu. Amin na ji basma ta faɗa tare da da fa ka faɗa ta. Dago idanuwa na yi na dube ta . Ban ce komai ba na sake sunkuyar da kaina ƙasa . Wuri ta samu ta zauna ta ce, "Aunty wai yanzu har fushi Nasir ya ke Miki? Duk irin halin da kika shiga bai gani ba? Ko da kuwa a ce auren da a ka Miki wani abu ya faru ai ya kamata Nasir ya yi haƙuri." Shiru na yi na wani lokaci Sannan na ce. "Basma haka ƙaddarata ta zo ni kuma da ga wannan gangamin sai Wannan. Amma bana son su mama su sani kinji ." "In sha Allah aunty ba wanda zai ji, kuma Allah zai kawo Miki mafita da wuri." "Allah yasa haka my lovely sister na." Bamu jima ba gwamna ya turo a ka je da mu muka bada passport a kayi dukkan shirin da ya kamata saboda ba zamu jima ba zamu ta fi. Kananma muka je mukayi sallama da 'yan uwa da abokan arziƙi sannan muka wuce gashuwa nan ma mukayi sallama da 'yan uwa. Sai da ya zama saura kwana uku tafiya Sannan Nasir ya dawo dtr. ba yabo ba fallasa, saboda yana kula yaran sa ba kamar baya ba da su ma ya yi watsi da su. Amma ta fanni na ba abinda ya sauya hatta shimfiɗa idan muka hau Chan ƙuryewar gado ya ke wuce wa ya kwanta. Ban taɓa yi masa magana ba saboda ina jira na ga gudun ruwan sa. Ashe kuwa ruwan na sa yana mugun gudu ne da tozarci da yaudara har ma da rashin sanin daraja ta. Wannan ruwan na shi ya yi guda da zuciyata fiye da yadda nake zato. Kuma shine abu na farko da Nasir ya min na ji ma tsane shi a duniya tsana mai yawa....... PG 27 Sai da lokacin tafiya ya rage saura awa biyar, sannan ya ce dani yana son muyi magana. Cike da farin ciki na sa me shi ina fatan maganar da zamuyi ta kasan ce alkairi murabu cikin kewar juna. Amma kalaman da yazo min da shi ya tarwatsa dukkan tunani na. "Kubra, ina son ki ajjiye hankalin ki da kyau ki saurari abinda zan faɗa miki ciki lumana." Ajjiyar zuciya na sauƙe cike da damuwa saboda yadda na ga fuskar sa na san tabbas akwai damuwa. "Ina saura ranka mijina." Na faɗa cike da fargaba da neman sulhu. Sa ke tamke fuska ya yi ya ce, "Magana ce akan tafiyar ku a matsayi na na mijin ki sai dai ki zaɓa, tafiya umara ko kuma zaman auren ki! Wanne kika ga ya fi miki, ya rage na ki." Kamar sauƙar aradu naji sautin maganar ta sa har cikin kwakwalwata. "Nasir me na maka haka? Wanne laifi na ke da shi a wurin ka? Shin Nasir ashe lokacin Zaizo ka tsaneni irin haka? Yanzu tafiya Makkan ne ka ke min ɓakar maganar a kan ta?" Duka na jero masa tambayoyin . Shi kuwa ko a jikin sa bai wani damu ba ya sake kishin giɗewa a jikin gado, wani takaici ya kama zuciyata kamar na shaƙo sa na kama duka! Dan haka cikin ƙaraji na tashi ina huci na ce, " Kayi dukkan abinda ka ga yada ce! Tunda dai haka ka ce!" Fuuu na fice na bar masa ɗakin. Bai ce dani uffan ba har na bar dakin, falo na je na zauna na fara rero sabon kuka kamar wata amaryar da ake son rabata da iyayen ta. Ana haka su mama fedo suka zo ita da su Maryam saboda na musu alƙwarin da safe Zanje ban je ba kuma shawuya baya jin daɗi shine suke tunani ko jikin ne . Ganin halin dana ke ciki sai sukayi turus! Suka tsaya, waskewa nayi na fara ƙokarin goge fuskata kamar ba komai na ce dasu su ƙaraso mana, shigowa sukayi suka zauna duka jikin su ya yi sanyi. Mama ce ta ce, "Kubra, me ya faru? Lafiya kike kuka?" Shiru na yi bance komai ba saboda bani da abin faɗa, chan kuma sai dabara ta faɗo min, "Mama wallahi idan na tuna wahalar da na sha da yadda rayuwa ta bani wahala nida yaron nan sai dai na ji hawaye yana zuba daga idanuna." Na shimfiɗa musu wannan ƙaryar kawai don bana son su san halin da muke ciki. " "Haba kubra me sa zaki sa ka kanki cikin damuwa bayan kuma kin samu 'yancin rayuwa. Don Allah ki dena, saboda zaki iya kamuwa da cuta idan har zakina bibiyar Abun arai." Kalaman mama ke nan da suka faɗa cikin masarrafin jina. "In sha Allahu mama zan ki ya ye hakan." Na bata amsa cikin sanyin murya. Gefe guda kuwa su basma Maryam Hadiza ne duka suka zauna kusa dani duk sunyi kalar tausayi. "Yawwa kubra Allah ya muku albarka dukan ku." Da Amin muka amsa mata. Sannan ta ce dani idan Nasir yana nan tana son suyi magana da shi. Dan haka kai tsaye na je na sanar da shi ba tare da na tsaya na saurari abinda zance ba. Bai jima ba ya fito yana murmushin munafurci yana gaida mama kamar ba shi ba, dukan su suka gaida shi cikin sakin fuska illah basma da tasan halin da ake ciki. Har da yiwa mama fatan zuwa ayi a sa'a kamar ba shi ne ya gama min tijara a ɗakin ba. Mama ta dube shi. "Nasir Yakamata a yi wa yaron nan suna kafin mu tafi.Sunkuyar da kai ya yi ya ce, "In sha Allahu mama zuwa gobe zan saka masa." "Yawwa Nasir, Allah ya maka albarka." Da amin ya amsa ya miƙe ya fita . Hakan kuwa akayi ana gobe ta fita ya ce da mama sunan yaro Ahmad ya yi masa sunan rana ba takwara ba ne . Na yi farin ciki sosai duk da cewa bai kawo abin yanka ba, abinda yasa bai dame ni ba kuwa shine, sunna ce mai ƙarfi, ba waji bane sai anyi. Kamar yadda wasu suke ɗaukar cewa dole ne har ma idan ba ayi ba ana dauka kamar an aikata sa ɓo. Haɗe dukkan kayan mu mukayi domin asubar fari zamu tafi Kano Chan zamu hau jirgin yamma. Nasir na samu yana kwance yana latsa wayarsa yana ta famar sakin murmushi ga dukkan a lamu chat ya ke yi abin sa. "Ina son magana da kai ." Sai dai na furta ta sau uku sannan ya ce "Ina jinki." "Nasir na zaɓi ta fiya Saudiyya idan har yanzu kana kan bakar ka, domin ba zan taba cewa su mama bazan tafi ba saboda ka hanani. Amma idan zaka iya sanar musu da kan ka sai na haƙura." "Allah Ya tsare hanya ." Shine ka ɗai abin da ya furta min ya juya ya kwanta abinsa." Ba yabo ba fallasa na ɗan ji sauƙin damuwar da ta ke cikin zuciyata. Cike da farin ciki jirgin mu ya ɗaga zuwa Saudiyya. Ibada muke cikin farin ciki da kwanciyar hankali kullum sai munyi waya da su basma da Maryam da Hadiza, a wurin su na bar yaran nawa dukan su. Kwanci ta shi asarar mai rai bamu yi aune ba har watan Ramadan ya zo karshe amma da yake anan zamuyi sallah, wayar da mukayi yau na ji Muryar basma cike da damuwa amma kuma na yi nayi ta sanar min komai amma sam ta ce ba komai. Dan haka hankali na ya yi matukar tashi da zaƙuwar zuwa gida. Shigar yamma mukayi wa dtr dan haka har wani sauri nake na kai ga gida. Muna shiga na ga wata mata hakimce kan kujerar falona, Nasir ya na gefen ta suna shan dariya saboda kallon da suke yi a waya ya ɗauke masa hankali. "Nasir! " Na furta cikin ɗaga murya sosai. Firgigit! suka juya suka kalle ni. Idanun sa kawai na kallah na ga tsan-tsar rashin gaskiya a idanun sa......... PG 28 Sororo ta yi matar ta wani yatsina fuska tana faɗin, "Baby wai yau daman zata dawo ne baka sanar min ba?" Kallon ta ya yi ya kasa cewa komai ya sake kallona ya fara yaƙen dole yana faɗin, "Har kun iso ne?" Ban kula shi ba na wuce ɗakina kai tsaye ina jin kamar na shaƙo shi na yi ta duka har sai na ga baya motsin kirki na bar shi, amma kuma wata zuciyar tana ta bani hakuri. Biyo ni ya yi ɗakin ya zauna bakin gado ya ce, "Kubra bayan kin tafi abubuwa da dama sun faru kuma wal........" Hannun da na ɗaga masa ne ya sa shi yin shirun dole, "Bana son jin komai Nasir daga gare ka! Kawai abinda na sani shine tunda dai gida nawa ba naka ba ko? To ko matar ka ce ko ma ƙaruwar ka ce ka fita min da ita ayu ba sai gobe ba!" Ina hana fadar haka na wuce toilet ɗin da ya ke cikin ɗakin na rufe na fara kuka mai cin zuciya. Shi kuwa daga nan wucewa ya yi wurin matar ya bata hakuri yadda take ta masa masifa ya samu ya bata hakuri ta wuce ɗakin dake gefen nawa wanda a baya shine matsayin turaka. Gidan mu ya shiga ya yi wa su mama sannu da zuwa gefe guda kuma su Hadiza suna masa kallon banza game da cin amanar da yayi min. Sai wajen magrib yara suka dawo a makaranta suka mana oyoyo suna ta farin ciki, kayan tsaraba na cire na basu kowa na shi da su jallabiya da su huluna sallayoyi da sauran su. Kusan tara na dare ya samu baba bala ya ce da shi ya na neman ya fiyar sa ya yi masa laifi amma kuma ba laifi. Baba Bala ya ce ba komai ya sanar masa, dan haka ya zuƙa masa ƙaryar wai daman ya ce baya son tafiyar saboda bazai iya jurewa ba na ce da shi ya yi aure to shine bayan na tafi ya haɗu wata bazawara suka daura aure harma ta tare. Baba Bala ya ce ba kamai ai tunda ita ce ta zaɓi hakan, kuma ma sunnar Annabi ce ai Allah ya yi muku albarka. Ko da baba ya je wa da mama da zancen ta yi matukar mamaki, don ta san halina ba na wani abu ban sanar da ita ba. Amma kuma ta ce ba damuwa ai tunda ita ce tace ayi hakan. Ina shiga gidan da safe na samu mama fuskar ta ba walwala, na dube ta "Mama mai ya faru na ganki haka?" "Ba komai kubra." Ta ce dani Sai kuma ta ce. "Kubra banyi tsammani zaki yanke hukuncin wani abu baki sanar min ba, amma tunda har ya riga da ya faru shike nan. Sai dai ki sanin ki guji zama gida da kishiya gida guda idan ba dole ba, saboda anfi samun matsalar zaman. Ki na da damar cewa Nasir ya yi aure amma da baki bashi damar haɗa ki ba, ba wai ina zugaki bane ." Sakwato na yi kamar wata gunki. "Mama ban gane me kike nufi ba , taya zan bawa Nasir damar aure har da zaman gidana." Na sanar mata haka. Murmusawa ta yi ta ce "Koma mene ne ai abinda ya riga ya faru ya faru tunda Nasir ɗin da kansa ya ce kince sai kin tafi sai dai ya kawo wata gidan. Kinga kuwa ai ga watan Allah ya baku zaman lafiya. " Mama ta faɗa tana gyara ɗaurin kallabin ta. "Haba mama wallahi bani ce nace masa ba wallahi karya ce yamin kawai! Kuma wallahi bai isa ba! Nidai bamuyi haka da shi ba. Kuma wallahi yau zata bar min gida." Na faɗa ina miƙewa tsaye. Mama ce ta ce na dawo na zauna. Bayan na zauna ne ta ne mi sanin gaskiyar lamari kuma ban ɓoye mata komai ba yadda muka yi da shi ranar da su ka ganni ina kuka a gobe tafiya. Mama ta jinjina lamarin sosai da sosai ta kuma yi min nasiha da nayi haƙuri na bi komai a hankali. Zuciyata na ji ta yi min sauƙi na tashi na tafi gidan . Ina shiga na ci karo da ita tana ta wanin hura hanci ta tura ɗan kwali gaban goshi kamar zai faɗi. Ta tsare min hanya da gangan dan haka sai na kauce ban kulata ba, amma ta mangaje ni. Kallon ta nayi murmushi ɗauke a kan fuska ta na ce, "Bani wuri na wuce karmashashiya, saboda ke baki kai na haɗa jiki da ke ba shi wancan ɗan tauren da ya ajjiye ki shine sa'a na." Zaburo min ta yi saboda daman jira take dan haka hannu na sa ha hankaɗe ta gefe na wuce ciki abina. Ko minti goma ba ayi ba Nasir ya shigo yana huci kamar zai dake ni. " Duk abinda zakiyi kar ki kuma dukan baby! Idan maganar gida ne kuma ta zo ke nan na fa sa chan jawar!" Ya faɗa yana nuna min yatsa. Shawuya da yake gefe kuwa sai miƙa hannu ya ke kamar zai kama shi yana ta ɓangala dariya. Cike da masifa Nima na zabura na ce, " To munafiki ! Wallahi baka isa ba sai ka bar gidan nan ɗin kuwa. Ko ba duka ba ! To yanzu na fara. Butulu kawai irin ka. Na faɗa ina mai zama abakin gado ina rusa Kuka. Fice wa ya yi yana guna guni. Dan haka na bi shi cikin ɓacin rai har bakin ɗakin Babyn inji shi na ce "Ke baby kike ko ma Babyn roba ce azo a fice min daga gida wallahi ba gidan sa ba ne idan ma bai sanar Miki ba to maza azo a fice min daga gida!" Na faɗa cikin ɗaga murya jin haka yasa duka suka fito zuwa falon. Ta zuwa zata min wani iyaye na dauke ta da mari na mai da ita gefe shi ma da yayo kaina na hankaɗe shi na yi ya faɗa kan kujerar da ke bayan sa. Saboda kamar wata zaki na ke jin kaina a lokacin. Ganin na burkita su da masifa ina shiga ina jefo mata kayan ta zuwa falo yasa ya fice ban san mai ya shirya ba sai da na ga baba Bala har gida ya shigo ransa a matukar ɓa ce... PG 29 Sai da hantar cikina ta kaɗa ganin irin kallon da baba ya ke je fo min da shi, ita kuma makirar tana ganin sun shigo ta zuɓe ta kama ihun ƙarya tana cewa wayyo cikin ta. Baba Bala kai tsaye inda na ke ya nufo ni kuma na sunkuyar da kaina ban yi tsammani ba na ji an wanke min fuska da marin da rabon da na sha shi irin sa har na mance,. Cike da mamaki na ɗago idanun da suka rine min zanyi magana amma baba ya hanani sam! Ta hanyar ɗaga min hannu. Dan haka dole na haƙura da maganar naa durƙusa a wurin ina sauraran abin da zai ce. "Ke da kanki ki ka umarci mijin ki da ya ne mamaki abokiyar zama kuma a gidan ki, dan haka wallahi baki isa ba zama yanzu ta fara a cikin gidan nan! Kar ma na sake jin wannan batun na faɗa miki. Daga haka ya juya

Chapter 7 of 8