Share this page
5 / 8
na so ace ya tsaya na sallame ki yau kin ko ma ga ahalin ki. Sai dai kash! Ya fita tun bai ji ba kuma ba zai dawo ba sai dare. Dan haka don Allah kiyi hakuri zuwa gobe sai ki ta fi." Tunda ta fa ra batun ta na sauƙe wata kyakkyawar ajiyar zuciya saboda na ji akasin abinda na ke tunanin ji. Ganin ni ta ke saurare sai na yunƙura na buɗe baki na ce "Hajiya na gode sosai da taimakon da kike min ko na ce ki ke kan yi. Amma idan ba damuwa zan iya ta fiya ba tare da Alhaji ya dawo ba, tunda wallahi iya taimakawa a rayuwa kin taimaka min. Tunda na shiga wannan halin ba wanda ya taimake ni kamar ki." "Haka ne, ina son ki haɗu da Alhaji ne saboda ki samu ta go mashi mai yawa. Amma idan kina son tafiya gida sai na kaiki na sanya ki a mota ki tafi. "Yadda kika ce Hajiya ni mai biyayya ce." "Na fuskanci kina son zuwa gida kuma daman dole ki so hakan duba da irin yadda kika sha gwagwarmaya. An jima yarona yarima zai zo sai ya kai mu ta sha." Jin ta ambaci sunan yarima sai da zuciyata ta doka! Ya Allah na ko yarima ya rayu? Ko ina fullo ta yi da shi? Tuni na ji kamar na yi tsun tsuwa na je gida. Ganin ban ba ta amsa ba ne ya sa ta ce, "Bari na shiga na shirya kafin ya zo." Kai na gyada mata a lamun to sai ta wuce cikin part ɗin su na koma cikin sabon tunani. Koda haidar ya fita ya samu soja tsaye gaisawa sukayi da shi ya ne mi da ya ga na da mahaifin su. Sai ya sanar masa baya gida amma idan ya dawo zai raka shi wurin sa kawai ya basu layin sa . Kafin sojan ya yi yunkurin bayar da layin sai ga baba Bala da Nasir ɗin sun dawo . Ganin soja a wurin sai da zuciyar Nasir ta buga yana fatan ace labari kubra aka zo masa da shi. Bayan sun bashi wuri ya zauna ya ke sanar musu da dalin zuwan na shi. Yana son ya ji ya abin ya ke daga bakin manya. Labarin suka ba shi tun daga farko har ƙarshe da kuma abinda fullo ta sanar musu game da Kubra ɗin. Koda ya ji komai ya yi matukar girgiza sosai Dan haka ya miƙe tsaye yana mai mai ta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirrajiun. Tuni suka shiga halin ɗimuwa suna son sanin me ya ke faruwa. Kallon su ya yi ya ce baba haƙiƙa mun tafka babban kuskure wallahi . Saboda duk lokacin da muka gaza haɗuwa dasu to muna shirya musu kwanta bauna ne daga baya. Ina mai ɓakin cikin sanar muku da ce wa bayan fitar su ba jima wa cikin daji jirgi ya sanya musu wuta duka sun ƙo ne. Kuma bana raba ɗayan biyu matar nan sun dauke ta, dan da basu dauke ta ba da tabbas ta bayyana yanzu. Nasir jin kalaman sojan ya yi kamar wutar garwashi wanda bai san sanda ya chakumi wuyan sa ba amma kuma ko kalma ɗaya bai furta ba ya faɗi ƙasa kamar gawa......... PG 17 Ganin ya zube ƙasa ya sanya haidar ru gowa da gudu ya sanya hannun sa ya tallafi baban su yana faɗin " Daddy dan Allah ka tashi Karka barmu yadda mommy ta barmu, ƙarya ya ke mommy bata mutu ba. Daddy Please! Ya faɗa cikin wani irin kuka me sauti har sai da jama'ar gidan suka fito. Baba Bala kuwa ya ka sa komai jikin sa sai mazari ya ke yana kaiwa da kawo wa, chan tukun na ya ce da sojan, "Bawan Allah me ne ne gaskiyar lamarin maganar nan ta ka." Soja ya gyara tsayuwar sa tamkar ba shi ya kawo tarzo mar ba. Ya ce " Baba ina zato fa na ce tunda mun jefa musu wuta kuma sun ƙone, idan har ta na ciki ka ga ai sai dai hakuri amma idan bata ciki to ƙila tana wurin su a raye ko wani wajen." Baba ya yi shiru na wani lokaci Sannan ya ce, "Shike nan mun gode da ziyara Allah ya sa tana raye." "Amin baba. Amma ba shi kaɗai ya kawo ni ba idan ba damuwa ina son ganin yayar yarima saboda akwai wata tambaya da zan mata ." Badan dai soja ba ne da ba abinda zai hana baba Bala yi masa rashin daraja, amma ba yadda zayyi tilas ya haɗa shi da basma ya yi da daidai da lokacin da Nasir ya farfaɗo da ga sumar da ya yi. Sannu suka fara masa suka shiga da shi gida saboda har jama'a sun fara taruwa. Basma kuwa ƙuru ta yi gaban soja tana jiran me zai ce mata. "Ina son ki bani lambar wayar ki ko wata lambar da zan sa me ki. Saboda akwai wasu bayanai da na ke nema a wurin ki amma yanzu na ga baki da nutsuwa sosai." Shiru ta yi na wani lokaci dan harga Allah ta ji haushi da ya tsayar da ita a wannan lokacin da suke cikin damuwa, kuma shine silar komai da ya faru a yanzu." Lambar ta ambato masa ya sanya cikin wayar sa ya yi gaba ta shige gida. Koda suka shiga jajan ta lamarin suka yi ya yinda mama ta kama kuka wiwi wai tunda yace haka ta san zayyi wuya a ce Kubra na ra ye. Haka su ka yi ta lalla shin ta har ta ɗan tsa gai ta. Kubra zaune tana jiran zuwan Hajiya da yarima domin su Kaita ta sha, shawuya ta dauka ta fara masa waƙa kamar haka. Shawuya bawan Allah ne. Shawuya ɗan gatan mama. Allah ya so mu da nisan kwana yarona. Zamu gida ka ga daddy da sauran yayye yarona. Dariya ya ɗan ɓangala ai kuwa kubra ta yi da murna yau yaron ta ya yi dariya. Lamari kamar wanda a kansa ne ta fara haihuwa. Wajen sha biyu hajiya ta shigo ta ce ta zo su tafi dan haka da murna ta fito ta dauki shawuya ta goya a bayan ta. Kayan da ta cire daman ta daure a leda dan bata son rabuwa da su ko dan tarihi. Suka kama hanyar fita zuwa gun motar yarima . Tunda ta ga kallon da yarima ya ke mata sai ta ji hantar cikin ta ta ƙada saboda na kasa fassara ya nayin kallon na sa. Har mun shiga Mota da Hajiya sai na ji ya ce. "Dear, ai ba sai kinje ba kawai zan kaita. Saboda ta chan zan wuce sch ne." Wani abu na ji ya chaki zuciyata kamar na yi ihu tun ban san me Hajiya zata ce ba. "Yanzu kana nufin na sauƙa zaka yi koma yadda ya kamata?" Tabbas kuwa dear zan kai ta mana badai Yobe zata je ba? zan sa ka ta motar difa daga nan sai su kaita maini ko kuma ta shiga ta garin su darect kawai ." "To yarima amma dan Allah kayi wa direba bayani sosai kar ya barta ta sha wuya ya yi ƙokari ya sanya ta motar garin su da wuri da su ke difan." "Ok Dear." Kallon su na tsaya yi na ke kallon Hajiya. Kamar ta san ina cikin ta shin hankali ta ce, "ki kwantar da hankalin ki wannan zaiyyi komai kamar ina nan kuma in sha Allahu zaki je gida a yau ba sai gobe ba. Ba dan ma ba ƙasa ɗaya muke ba ta kin sanar da zuwan ki a wayar jama'ar gidan ku. Amma ga wannan ta faɗa ta na bani wasu ƙudi wanda zasu kai naira dubu ishirin. Hannu na sanya na karba ina godiya ta re da share wata ƙwallar da ban san da zuwan ta ba sai ɗumin ta da na ji kan fuskata. Fita ta yi ta na ɗaga mana hannu har muka ɓace wa ganin ta . Kallo na na kai kan shawuya na sha kansa a cikin zuciyata na ce "Allah ya raya min kai ya kaimu gida lafiya shawuya. Jin sautin yana waya ne ya sanya ne ɗagowa da kaina domin na ji mai zai ce, Kalmar da ya ambata ita ce ta yi sanadin daukewar lumfashina na wucin gaɗi. Bayan wani lokaci na samu damar haɗiye wani mugun ya wu hannu na daura bisa kaina na furta " Na shiga uku! Ya Salam! Haba dan Allah wannan wacce irin masifa ce..... Wawan birkin da yaci ne ya sanya ni sake tabbatar da batun da na ji ya na yi ya zama gaskiya.. Shike nan nikam na shiga uku ina jin har abada bazan koma ga ahalina ba....... PG 18 ganin yan ƙokarin chusa kan motar cikin wani wawa ke ken gida tuni na tuna da maganar da ya yi a waya. *Daddy ba wata matsala ga ta na kawo ta* Wani hawaye na ji suna zubomin ya yinda ya yi dai dai da tsayuwar motar cikin rumfar ajjiyar motocin gidan. Fitowa ya yi ya bude inda na ke ya ce na fito fuska ba walwala. Ba yadda zanyi haka dole na sa ƙafa na fito riƙe da shawuya a hannuna. "Bi yo ni .". Ita ce kalmar da ya furta min wanda ta daki dukkan sassan jikina. Haka na dunga binsa a baya har muka kai ga wasu manyan faluna na gani na faɗa kuma gidan yana da zurfi sosai mun wuce manyan falo sun kai biyar, daga bisani muka bi wani korido muka kurda ta wata ƙaramar hanya muka iske wani ƙaramin falo. Wani jibgegen mutum ne hakim ce a zaune kam wata kujera fuskar sa dauke da murmushi, idan ka kalle shi ba zaka ce ya yi kala da mugayen mutane ba. Saboda cikar zatin da Allah ya masa kuma ga shi da kwarjini a ido. Hannu ya miƙawa wanda ya ke zaune tare da faɗin, "Daddy gata nan kuma ba wanda ya ganmu mommy da kanta bata san ma ka ganta ba tunda tana ta mitar rashin tsayuwar ka ." Dariya ya yi mai sauti sannan ya ce, "Ai shine da lilin da ya sa na ƙi tsyawar domin bana son ta zargi wani abu ko daga baya amma kaga yanzu komai normal. Kai dai abinda zan ja maka kunne ka tabbatar ka sake riƙe mana sirrin mu har zuwa lokacin da zamu fita cikin wannan masifar." Da to ya amsa masa ya fita ya barni zaune . Duk jikina ya mutu na kasa ko da kwakkwaran motsi ne ga shi ruwan hawayena ya kasa dai na zuba, sanadin magan-ganun su. Na sallama wa rayuwa yau kam tabbas amma ma fi tausayin yaro na da zai kai shi gida ni ya kashe da zan amince. Amma sai dai kash na san hakan bazata samu ba, damuwa ta ɗaya ce, ko shakka babu wannan mutum idan ya haikemin kafin ya kai ga biyan buƙatar sa a wurina zan mutu tabbas! Saboda bani da wani kwaliti jiki duk yunwa da gajiya. Ke nan idan na mutu shawuya zai kai kaɗai a shanye wa jini. Zuciyata tana gama bani amsar ƙarshe na fashe da wani uban kuka wanda zaka dauka duka na ake yi. Ganin abinda na ke yi ne ya sanya Alhaji yin murmushi ya kalle Ni ya ce, "Sorry da kin bar kukan haka dan ba zai Miki amfani ba kam. Ban so na Miki komai ba amma kuma ya zama dole na yi hakan ko dan ceton rayuwar ahalina. Dan haka kiyi hakuri ki dauki wannan a matsayin ƙaddarar ki." Yana gama faɗar haka ya mike ya na fadin "Ki huta ga kaji chan da kayan more rayuwa ki ci ki koshi zuwa dare sai mu haɗe." Saman be ne ya haye abinsa, kallon dinning table ɗin na yi wanda ya ke cike da kayan more rayuwa na dauke kaina, domin ba kaza ba ko ɗawisu a ka ban awannan lokacin ba zan iya ci ba. Yadda ya barni haka ya dawo ya wuce ni ko motsin kirki banyi ba har wajen Yamma ina zaune in banda sallah da na yi ita ma da taimama na yi ta saboda a kwai wani lungu kafin mu shigo ɗin na ga ƙasa dan haka chan na je na yi na dawo na yi sallah. Na shiga tashin hankali matuka ainun ganin dare ya fara kawo kai ga kuma yunwa da ta ke addabar cikina har ta shafi shawuya ya fara kuka saboda bai samun nono mai kyau a wuni yau ɗin ba. Da yanzu ina Chan wurin dangina a na ta murna a na maraba da dawo wata, amma wannan yarima bai kyauta wa mamar sa. Ya Allah yadda ya ci amanar da maihaifiyar sa ta bashi Allah ka to ni asirin su ka ce ce ko da yaro na ne....na hakura da rayuwar nikam koda na koma gida ba lalle na rayuwa tunda zuciyata ta gama shaƙar bakin ciki na san da wuya na jima bata buga ba.... Na karshe maganar ina kuka mai cin zuciya. Basma ta na zaune ta ji wayar mama Fido ta na kukan neman taimako dan haka tuni ta dauka saboda ba su cika barin ƙira ba ko za suyi katari da labarin Kubra. Tana ɗagawa ta fara da Sallama. Shiru ta ji ba amsa kuma daga baya a ka ce, "Basma ce?" "Eh ni ce wa ye ne?" Ta mayar da amsa. "Sojan ki ne." Ya faɗa cikin murmushi. Wata faɗuwar gaba ce ta riske ta jin ya ambaci kalmar sojan ki ne, ta ya ya zama na ta? Ta tambayi kanta. "Kina jina kuwa basma?" "Eh ina jinka soja." Ta faɗa cikin ƙosawa da wayar, saboda haushin ko wanne jami'i ta ke ji da shugabanni, suna ji a na kwashe jama'a basa bin ka du da wuri har sai rayuka sun salwanta. "Basma ina son idan kin samu nutsuwa muyi wata maga na ne." Ya faɗa cikin sauti ƙasa ƙasa kamar mai raɗa. "Ina jin ka ko yaushe zaka iya faɗa saboda bani ba samun tsuwa har sai ranar da aunty Kubra ta dawo gida." Shiru ya yi na wani lokaci Sannan ya ce , "Karki damu zata dawo in sha Allahu." "Kai da ka ce ta mutu." Ta jefa masa tambayar. "Ina tsammani fa na ce basma." Ya faɗa cikin sanyin murya har sai da ya sa ta ɗan dara Jin sautin darawar ta ta ne ya sanya shi yin murmushi ya ce "Shike nan ki huta zuwa wani lokaci zan dawo idan kun samu nutsuwa. Amma ki sani wallahi da na san inda aunty Kubra ta ke to da tabbas zanje na dawo da ita har gida kodan farin cikin ki." Ajiyar zuciya ta sauƙe tana jinjina masa duk da ta san ƙila da wata manufar ya ke haka, amma zan ba shi lokacin na ji ƙarshen gudun ruwan sa . Sallama ya yi mata ta ajjiye wayar ta kwanta tana na zarin kalaman sa. A na shi ɓangaren kuwa yana gama wayar ya saki wani ƙayataccen murmushi har sai dai na ge fen sa ya ɗan taɓa shi ya ce "Ya de Captain Jamil, ko ka faɗa soyayya ne?" "Hummm! Kamal wallahi ba zan ce komai ba a yanzu amma dai kam na san ina daf da faɗawa cikin soyayya. Sai dai da yake ban saba da yinta ba ko kuma in ce ban taɓa ba har wani tsoro na ke ji ni kadai idan na tuna ta." Dariya sosai wanda a ka ƙira da kamal ya tuntsure da ita ya da fa ƙa fadar Captain Jamil ya ce. "To kuma me ne ne abin tsoro? Kai dai akwai wani sauna wato idan ba a filin da ga ba baka da wani kuzari." "Eh daman na miji ai yaƙi a ka san shi da shi. Da haka dai kamal ya yi ta tsokanar sa har wani lokaci. Ganin ba wani sarki sai Allah yasa ta gyara zaman ta amma kuma sai ta tuna cewa ta gwada buya mana ko Allah zai sa ta tsira idan da rabon rayuwar ta zatayi tsayi. Da wannan tunanin tashige wani lungu wanda ba lalle a san da mutun ba a ciki. Dan haka da Alhaji ya dawo ya sha mamakin rashin ganin ta awurin. Amma ko kaɗan baiyyi tsammanin zata buya ba ko ta gudu tunda dai ya san gidan nan daga shi sai a halin sa suka san kan gidan. Amma wani abun mamaki duk yadda ya ne mi ya ganta ya rasata, har ya fara haɗe gumi yana ƙiran ke baiwar Allah wallahi kiyiwa kanki ƙiyamar laili ki fito tun kafin na kamaki! Amma shiru. Iya ta shin hankali ya shiga a wannan lokaci dan haka ya ƙira yarima ya ke sanar masa ko dai yazo ya tafi da ita ne. Amma yarima ya ce sam bai dawo ba ya dai sake dubawa tunda dai bawan da ya ke iya shiga gidan sai shi sai Hajiya su suka san password ɗin gidan . Abin mamaki dai Alhaji ya rasa kubra kuma ya gaza tafiya gida daman shirin sa shine idan ya biya bukatar sa da ita sai ya wuce gida da sa fe ya kaita wurin oga! Amma kuma ga shi ta kwafsa masa. Saboda haka ba yadda za'ayi yabar gidan har sai ya ganta koda zuwa gobe ne tunda dai ya san ta na gidan . Wayoyin sa ya kulle duka saboda kar wani ya kira shi ma data gidan sa. Hajiya kuwa iya tashin hankali ta shiga na rashin dawowarsa gida ga wayoyin sa duka ba sa shiga. Ta damu yarima da yaje ya duba ko yana dayan gidan amma sam ya ce ba wani abu sun yi waya ya ce aiki ne ya masa yawa. Dan haka dole ta koma part ɗin ta. Shi kuwa ya faɗa mata haka ne dan ta barshi tunda dai ya san inda daddy ya ke amma dai bai dauka zayyi amfani da ita ba ne iya abin da ya sani zai kaita wajen oga ne a maimakon Hajiya da suka so a abasu wanda tsautsayi ya jefa daddyn su ciki kuma yana addu'a ya rabu da su lafiya kafin su cutar masa da mommyn sa. Gari na waye wa Hajiya bata yiwa yarima magana ba ta fice kai tsaye gidan Alhaji ɗayan ta na zuwa ta sanya hannu ta bude ta shiga. Shi kuwa yana cikin falon abin duniya ya masa yawa dai yau yayi da na sanin rashin sanya cct Camera a wannan ɓangaren. Kuma ya yi haka ne saboda ko da wani abu zai faru irin haka wataran kar Hajiya ta je ta kallah kuma dai gashi yau da yana nan da ya masa rana . Jin sautin shigowar mutun ne ya sanya shi ɗagowa cikin firgita sai kuwa ya yi arba da Hajiya, tuni ya miƙe ya fara in ina yana mata sambatu na karya. "Wallahi ina cikin damuwa ne ban son koma wa gida ki shiga ta shin hankali." "Haba Alhaji ko wacce irin damuwa ce ai gwanda ka dawo gida ka kwana kusa dani....." Jin sautin Hajiya ya sanya kubra ta miƙe da ga buyar da ta yi dan dole ta fita dan idan Hajiya ta ganta tabbas zata samu fita daga wannan gidan. Tunda daman ta galabaita ga kuma yunwa ga shawuya suman sa biyu kafin waye War gari bata san mai ya dame shi ba ga shi ko kuka bayyi ba bata san me ne ne matsalar sa ba. Dan haka fitar ita ce mafita kawai Alhaji yana yiwa Hajiya daɗin baki kawai sai ji ya yi kubra tana faɗin . "Hajiya ki taimake ni wallahi zai kashe Ni ......!" Cike da ɗimuwa hajiya ta juya ta dube ta cikin tsantsar mamaki ta ce "Kubra! Wa ya kawo ki nan " Bata samu damar magana ba saboda Alhaji ne ya yi zaraf ya ce . "Gwanda da kika bayyana kanki matsiya ciya! Ai yanzu kin gani tsintacciyar mage........ Halin ki na taimakawa al'umma ya ja ana neman raba ki da mijin ki, ya faɗa yana goge ido tsabar iya munafurci.. Ta shin hankali ne ya ziyarci zuciyar Hajiya gaba-daya ta ka sa gane inda ya dosa .... Ita kuwa kubra ka sa koda motsin kirki ta yi......... PG 19 Ganin irin sharrin da Alhaji ya ke neman yi mata ne ya sanya ta dur ƙushewa a wurin da take. Hajiya ta kalle ta ta sake maida kallon ta a wurin Alhaji ta ce "Me ya haɗa ka da Kubra? Wa ya kawo ta nan? " Ta jera masa duka tambayoyin. Sanin cewa Hajiya mace ce mai kishi Dan haka tuni ya shirya irin ƙaryar da zai mata. "Ban san ya akayi ta zo ba, kuma abinda ya ban mamaki shine yadda ta hanani ta fiya gare ki jiya ban san irin ƙarfin asirin ta ba." Ya faɗa cikin muryar kuka wacce tuni Hajiya ta ruɗe duka tunanin ta ka sa gane mata wannan shiryayyiyar magana ce, wanda dukkan mai hankali ya kamata ya gane ƙarya ce domin idan ba rami mai ya kawo rami? Amma saboda tsantsar kishi irin na Hajiya ga shi ta ji ya ambaci asiri da son rabashi da shi ai bata yi wani tunani ba ta nufi kubra cikin damuwa, ita kuwa Kubra bata ce da ita komai ba saboda ya riga da ya ɗaure ta da jijjiyar jikintaTa na zuwa wurin kubra bata ɓata lokaci ba ta wanke ta da mari hagu da dama. Wanda ya sanya kubra zubar wasu hawaye Masu zafi, amma kuma bata da bakin magana. Hajiya ta fara mata masifa, "Lalle tsintacciyar mage bata mage! Ni kubra! Ni zakiwa haka? Duka alherin da na miki, da kar ɓar da na miki na baki wurin kwana sutura abinci! Duka da abinda zaki saka min ke nan." Jin kalaman ta duka sai suka sanyawa zuciyata damuwa na ji kamar da gaske na aikata mata laifi, cikin ƙarfin hali na bude baki na fara mata magana cikin dusa shewar murya. "Hajiya dan Allah ina son ki saurare ni, bazan yi ƙoƙarin ka re kaina ba a gare ki domin ba lalle ne ki fahimta ba. Amma sai dai yadda na same ki mai taimako na ji matukar baƙin ciki da kika kasan ce mai watsar da ladan ki tun ba ayi nisa ba. Dukkan wanda ya yi abu domin Allah koda anbi shi da sharri ba zayyi go ri ba. Idan har domin Allah a kayi , amma duk da haka ina roƙon Allah da ya bar miki ladan ki, saboda tunda na faɗa halin da na shiga ba wanda ya min abinda kika min na alheri kamar ki. Dama mu mata muna da wannan raunin duk yadda muka kasan ce da saurin tausayi amma ba mu da wuyar zubar da ladan sai mu fara da ba gori ba. Amma ina roƙon ki dan girman Allah taimakon na karshe da zakiyi min ki fitar da ni cikin gidannan, sannan ki tuhumi mai gidan ki domin bai kamata yadda kike da hali na gari kin zaune da wanda baki san ko waye ba." Na karashe maganar cikin kuka ina zuƙe majinar wahala. Tunda na fara magana Hajiya bata ce komai ba kuma duk jikin ta ya mutu da magan ganu na dan haka shiru ta yi tana nazarin kalamai na. Ganin haka ya sanya Alhaji zabura min da cewa. "Muna fuka wato har kina da bakin wa'azi? Ke ce fa kika zo da kanki har kina cewa a nuna miki hanya? Ai daga nan sai gidan gyran hali." Hajiya wuce muje idan munje Chan ta faɗa Miki yadda ta shigo . Ita dai Hajiya kasa magana ta yi, har sai da ta jinjina lamarin a zuciyar ta sannan ta ce , "Ko ma me ne ne yanzu ta bar mana gida bana son sake ganin ta bare ma mu yi zaman shari'ar har ta samu damar rabani da kai ɗin. Dan haka kawai yanzu ta bar gidan! Ta faɗa cikin faɗa da masifa . Ganin haka Alhaji ya yi kanta ya fara faɗin "To muna fuka a yi gaba maza yallah ! Allah ya so ki da kin shiga uku! " Ita kuwa kubra ba ƙaramin daɗin ta ji ba da jin kalaman Hajiya dan haka ta goya shawuya ta fara shirin ta fiya sai dai kuma kash! Bata san hanyaa ba . Ganin ta tsaya ne Hajiya ta du be ta ta ce "Me kike jira kuma." "Hajiya wallahi ban san hanya ba ." Hajiya ta juya ta kalli Alhaji, kafin ta yi magana ya yi zuruf ya ce, "Hajiya ba zaki fita hanyar munafukar nan ba wai ?" Kallon sa ta yi har sai da ya tsargu da kallon da ta ke masa sannan ta ce da kubra bi yo ni. Ta yi gaba kubra ta bi bayanta ta na hamdala a zuciyar ta. Har bakin ƙofar gidan ta raka ta tace, "Allah ya ki ya ye hanya Allah ya rabani da ke har abada! Idan ma kina da gaskiya ke ta sha fa ! Idan ma baki da na barki da Allah." Duk kalaman ta sun fa ɗa cikin zuciyata na ce da ita ba tare da ja juya ba. "Allah ya biya ki da gidan aljanna." Na wuce na kama hanyar wani babban titi da ba abin hawa da yawa kasan cewar birnin Nijar daman bai cika cin ƙo so da yawa kamar irin su Kano ba, tafiya mai nisa na yi na tare mai abin hawa na ce ya kaini tashar difa. Kai tsaye ya dauki hanya ya kaini ina zuwa tasha kuwa na samu mota mutun guda ya rage dan haka na afka cikin farin ciki. Hanya muka ɗauka ina hamdala Allah ya kaimu lafiya. Ta fiya muke cike da kwanciyar hankali amma Ni kuwa bani

Chapter 5 of 8