motsi saboda na samu hanyar kufcewa. Amma abin ya fi ƙarfin tunani na
saboda mugun tsaron da yake a wannan dajin ! Haka na ke lallaɓa rayuwata ina ta ka tsan-tsan
da komai.
Abu na farko da ya fara daga min hankali shine yadda wannan mijin nawa da ban san sunan shi
ba ya fara neman hakkin auren sa a gare ni! Na shiga damuwa da firgici da na fahimci lamarin,
saboda a tunanina zan samu wata damar tserewa kafin ya amfana
dani.
Nasir ne zaune bakin gadon su da Kubra idan ya kalli kayan ta da yake ajjiye a kan gadon
wanda ta goge ta ce shine zata sa gobe suje gidan Hajiyar sa. Wani hawaye Mai zafi ya ke
zubarwa idan ya tuna yadda sukayi rayuwar su cikin farin ci da ƙaunar juna.
Baya mance ranar da ta ke ce masa idan ta haihu tana son su koma wata jahar daban da zama
domin ta gaji da rayuwa a wurin da ya ke da fargaba
Duban ta ya yi ya ce "Haba ƙurraty na, ai komai kika ga ya faru to rubutacce ne shi. Dan haka
ko ina zamuje idan har Allah ya tsara wani abu zai faru ba fata ba to tabbas sai ya faru."
Kallon sa ta yi cikin yanayi na sanyin jiki tace " Haka ne Habibi amma wallahi sam wannan garin
ya fita a zuciyata saboda wallahi bana son abinda zai tarwatsa min zuri'a ko ace na rasa ka !
Saboda ina matukar kaunar ka Habibina yadda baka tsammani.
Murmushin na yi dajin batun na ta na karshe na ce "Haba ƙurratul aini na, Ba sai kin fa ɗa ba na
fi kowa sanin haka kuma in sha Allahu ba abinda zai faru."
Sake gyara zaman sa ya yi bayan ya dawo daga duniyar tunanin matar sa ya dauki kayan ya
sanya cikin durowar kayan ta ya rufe ya yi maza ya fita a ɗakin domin komai zai iya faruwa da
shi idan har yana kallon dukkan abin da ya shafeta.
"Ƙurraty! Allah ya bayyana min ki in sha Allahu baki mutu ba."
Nasir ya faɗa yana share hawayen idanun sa.
Ganin kwana biyu ya matsa da zancen ne na buƙaci da ya zo muje wani ƙauye mana to domin
muma musha amarchin mu Chan tunda haka ne. Bai yi musuba ya amince min, kuma na sanar
da shi na fison ƙauyen da sai an tsallake ƙogi saboda na ga duniya Nima.
Ya ce dani ba damuwa gobe na shirya mutafi.
Hakan kuwa ta kasance tun safe na ke shirin fita saboda ni kadai na san me na shirya cikin
zuciyata
Kamar misalin ƙarfe goma na safe ya zo ya ce dani Bismillah,dan haka muka dauki hanya muna
tafiyar ƙafa har zuwa bakin ƙogin da yake da ta zarar ba nisa ba ce sosai a wurin su amma kam
zai kai kamar kilo mita guda da rabi.
Koda zuwan mu ya sanar da su inda zamuje ba su hanamu ba suka sanya mu cikin
kwale-kwale ya yin da wani farin cikin ya riski zuciyata don ji nake komai ya zo karshe.
Amma mai zai faru tuƙawa biyu akayi na ji wata murya mai sauti cikin amo ana cewa "Ku
dakata!! Ku dawo da su!!!!!.............
PG 8
Wani irin yanayi na ji ya ziyarci zuciyata kamar zan zauce. Saboda koda wasa banyi zaton wani
zai kawo min cikas a cikin wannan tafiyar ba.
Shi kansa wanda ake laƙabamin da sunan mijin nawa maganar ta bashi mamaki sosai. Saboda
yadda na ga yayi sakwato da baki.
Ganin masu kwale kwale sun juya suna mayar da mune yasa na ji cewa shike nan haƙata bata
cimma ruwa ba.
Koda muka koma bakin ruwa sai cewa ya yi shi wanda yayi ƙiran ke nan, "Baka bani shaidar fita
ba, ko kuma baka da wata shaidar zaka fice ne." Nida ban san kan komai ba sai na tsaya ina
kallon su.
Saurin sanya hannu ya yi cikin aljihun sa har yana kyarma ya ce, "Dan Allah kayi hakuri tabbas
nayi laifi kuma idan OGA gaba ɗaya yaji zai dauki mummunan mataki a kaina. Mance wa na yi
sam gaba daya."
Wata irin dariya ya bushe da shi kafin ya ce " Baka da matsala da ni, banga laifin ka ba koda ka
mance da kanka ne saboda dukkan wanda ya mallaki mace kamar wannan tabbas ya gama
samun rayuwar farin ciki.
Asha amarci lafiya."
Murmushin gefen baki na yi cikin zuciyata ina ayyana yadda zanyi kawai.
Shi kuwa mijin nawa ce masa ya yi godiya na ke shugaban mahayan ruwa.
Da haka muka dauki hanya cikin taf ke ken kogin da ya ke da faɗi da tsayi! Kuma ga nisan
tafiya sosai har sai da na ƙosa kuma na fara jin jiri saboda yadda ruwan ya ke juyawa.
Amma da yake sannu sannu bata hana zuwa sai dai a jima ba aje ba. Dan haka dai gamu
bakin karshen ruwa mun samu hayewa. Hamdala na yi bayan mun sauƙa y'an kayan da ya
dauko a matsayin kayan zaman amarchi su ya dauka muka sauka baki daya da su. Sai dai nan
ma fa akwai tsirarun y'an ta'addar masu shigar da mutane sai kuwa wasu da matan su kamar
dai yadda muka fito.
Nesa sosai ya yi damu saboda na lura baya son hayaniya dan haka munyi nisa da su yadda
ko ɗuriyar su ba ma ji bare gani.
Hakan kuma ya min da ɗi.
Wani karkashin wata bishiyar da bansa me ce ce ba muka zauna muka ajjiye kayan mu ya
sauke bindigar sa ya ajjiye ta a gefen kayan, ya samu wuri ya kwanta ya ce dani "Wuta zaki
hada ki dafa mana abinci da ruwan wanka kafin dare ya yi miki domin yau ɗin nan zaki bani
haƙƙina ko ni ko ke cikin dajin nan.
Wata fargaba ce ta riski zuciyata amma da na tuna Allah sai na ji na samu ƙwarin guiwa. Na
kalle shi na ce, " Yanzu ina zan samu makamashin hada wuta a wannan dajin?"
Idanu ya daga ya kalle Ni ya ce " Ki zaga baya kadan zaki samu kirare sai ki dauko."
Idanu na zaro kamar da gaske na ce "Kai ! So kake a sace maka ni? Taya zan shiga wannan
kwararon neman kirare?"
Zaune ya tashi halamu ya harzuƙa da tambayar tawa " Ke ni barci zanyi! Waya ce Miki ana
sace mutum a wannan wurin duk wata tafiya ƙalilan jama'ar mu suna nan sun yada Zango, dan
haka ki saki jiki ki yi abin da ya ke gaban ki kafin lokaci ya ƙure miki." Ya faɗa yana jan tsaki tare
da ko ma wa kwanciyar sa ya juya min baya.
Kunto shawuya nayi na sanya shi a nono ya sha ya ƙoshi na bashi ruwa na mayar da shi. Jin
gurnanin mijin na wa ya yi bacci ya bani damar daukar wata ƙaramar gora mai dauke da ruwa
na sanya ta cikin goyan ta gaba na ɗaure kyam! Na sake sanya wasu zanin na sake daure wa .
Ban ma tuna ta batun cewa mutanen su suna gaba ko kuma ta ina zan fara ba, na kalle shi na
masa kallon karshe ina jin wata irin faduwar gaba tana kai ko mo cikin zuciyata!
Amma wani ɓarin na zuciyata cike ya ke da jajircewa.
Dan haka na sanya gabana
yamma na fara takuna cikin hanzari bana tuna komai sai Allah da na ke ambato cikin
bakina.............
PG 9
Hanya guda na dauka ba ko fargaba tafiya na ke cikin sanɗa kamar wacce ƙwai ya fashewa a
cikin ta. Kusan tafiyar minti talatin na yi kafin duhu ya fara shiga na magrib amma kuma ban ga
kowa ba ban ji motsin komai ba, dan haka sai na fara sauri gudun wani abu ya faru tunda na
san makoma ta a wannan lokacin idan an ka ma ni.
Chan na yi nisa da tafiya na hago wani haske gaba wanda yasa zuciyata bugawar tara-tara a
maitan na sha kwanar wata bishiya domin kaucewa wannan hasken.
Amma me zai faru ji na yi kamar na sake kai kai na wajen wani hasken na sake saurin boyewa
cikin wasu ita tuwa ina kutsa wa zuciyata cike da fargabar kar shawuya yayi min kuka a wannan
halin da na ke ciki! Ta cikin ita ce na ke sanɗa da ya ke akwai hanya na ke ƙurɗa ɗawa ina bi
ina sake ni sawa da tafiyar. Chan kuwa yana farkawa yaga wayam ba ni ba labarin girki dan
haka ya sake kishin giɗa yana faɗin lalle wannan ba ta nai mi zaman lafiya ba, yau zata sha
wuya hannuna alƙur'an
Jin shurun ya yi yawa ne ya sanya shi leƙa ko wanne saƙo da lungu amma ba ni ba a lamuna
cike firgici ya rasa abin yi, dan haka sai ya fara kwaɗamin ƙira amma shiru . Hakan ta sa ya fasa
wata ƙara da ta amsa ƙuwwar dajin kuma dukkan wanda ya yi haka an san akwai matsala. Dan
haka tuni zaratan maza suka bayyana dauke da makamai cike da ɗinuwa ya ke sanar musu da
rashin gani na dan haka tuni suka afka dajin domin nema na.
Banyi aune ba naga na fita daga duhuwar kuma ba hasken dan haka ƙafa mai naci ban baki
ba ai kuwa na rufa da gudu saboda kar wani ya haske ni ba wurin ɓuya. Ina ta faman gudu na ji
na afka cikin wani rami wanda zurfin sa zai kai gaba uku na rijiya .
Allah yaso ban faɗi kan goyon ba, ganin haka sai na ji kamar na samu wata dama ce da zan
huta a wannan wurin.
Sauƙe goyan na yi na sanya shi a nono bawan Allah tuni ya chafke ya fara sha . Wasu guntun
hawaye ne suka zubo min daga na mujiyata saboda na san dole akwai masu bi na. To amma ya
zanyi na fita cikin ramin nan ba tare da taimakon wani ba? Kuma dukkan wanda zai taimake ni
tabbas sai dai masu nema na.
Jin sautin tafiyar wasu runɗuna suna faman mita cikin wani kalar yare yasa na ƙandare daga
gefen ramin na gama yanke kauna da rayuwar duniya domin tabbas na san kamani za su yi !
Kuma laifina kisa ne kai tsaye, salati na fara domin samun na ga na cika da kalmar
shahada.Nan da nan nafara jin sawayen su suna tsaye bakin ramin suna cewa da harshen
Hausa.
Duk inda ta ke ka tabbatar kun ne mota ba tausayawa ko a wanne hali kuga ganta ku aiwatar
da hukunci yadda ya ke.
Wata murya na ji kamar ta wanda ake ƙira da mijina ya ce " A'a Sadau su ka wo ta wuri na
nine ya kamata na dauki matakin a hannuna saboda tsantsar yaudara da cin amana da ta min ."
Haka ne Barde na ji amfada da kakkausar murya .
Sun jima suna saƙa da warwara ɗaya daga cikin su ya ce yanzu mene ne abin yi a wannan
lokaci? Ga dare ya yi ga bamu san ta ina ta ke ba tunda ba wani labarin ta bakin tafƙin da
jama'ar mu suke.
Haka ne kam inji Sadau.
Yanzu kuje baya ku zauna ku kuma kuyi gaba dan haka nida Sadau a bakin ramin nan zamu
waye muka ta ina zata tsira .
Wani irin murɗawa cikina ya yi nan take wata gudawa ta so kufce min amma Allah ya rufa asiri
bata fito ba, wani irin zafi jikina ya ɗauka ga wani tururi da yake fita ta maƙo gwarona yau kam
na san ta wa ta ƙare. Ban damu da rayuwata ba kawai na damu da shawuya ne dukkan gudun
da nake ina yi ne domin sa, da ni kadai ce wurin su zan zauna. Amma ba zai yiyu na haifi ɗa
daga tsatson daraja ya ra yu cikin y'an ta'adda ya zama ɗan ta'adda shi ma.
Kamar rawar aradu haka na ji wata murya na faɗi shugaba munga wata a lama a baya mu afka.
Ai kuwa tuni na fara jin sawayen su suna komawa baya cikin ƙaraji da hucin son haɗuwa dani.
Suna tafiya na fara tunanin yadda zanyi na fita domin dama ce na samu na tsere daga
hannun su tunda sun koma baya, amma abin takaicin shine ya zanyi na fita........
PG 10
Ganin sun ta fi kawai na fara tunanin mafita yadda zanyi kamar wa ha yi na fara kai hannu na ji
akwai irin ramuka ƙananu ta ciki dan haka na kama su na ke takawa kamar mai hawa tsanin
ginin haka har Allah yasa na fito da kaina bakin ramin. Ganin ba kowa na yi saurin fitowa sai dai
duk jikina ya yi min tsami ga yunwa ga jikin jego, tunawa da nayi da irin uƙubar da zata sa me ni
a wannan wurin idan ban bar sa ba shine ya sanya na ji wani irin ƙwarin guiwa ya zomin. Tuni
na fara tafiya ina sauri sauri gudun faruwar wani abu har na yi nisa da wurin . Na yi tafiya mai
nisa kafin na iske wata bishiya wacce ta ke da ci ya yi busassu a ƙarƙashin ta. Dan haka nan na
zube na zauna ina sauke lumfashin wahala tao kuma yunwar da ta ke sake ta so min kamar
zanyi amai. Kuka na fara ina tambayar kaina tambayar da bani da amsar su.
Shin sai yaushe zan fita a wannan dajin da babu wani a lamun titi ko abin hawa ?
Wa zai ce ce ni a cikin wannan dajin?
Me na yiwa Allah da haka ta ke faruwa dani?
Wacce irin ƙaddara ce da bazata same ni ba sai da na ke cikin wannan yanayi na jego ga yaro
ƙaramin bai san kansa ba?
Haka na yi ta faman tambayar kaina abin da bani da amsar su. Sake goge hawayena na yi a
karo na barkatai, ina tsaka da wannan tunani na hago wasu motoci da hasken su ya ke ba mai
yawa ba suna nufo ni, tuni na mike na gudu bayan bishiyar na goya shawuya a bayana. Kamar
jira suke na buya suka hasko wani Haske mai yawa ya mamaye dajin kuma motar ta na tunkaro
inda na ke amma ta gefen hagu na.
Har sun kusa wuce ni motar su ɗaya ta tsaya, cike da masifa ɗayan ya kurma wani mahaukacin
zaki ya daki bayan motar ya ce "Oga wannan motar fa ta samu matsalar dan bazata ta shi ba
yanzu gaskiya sai zuwa safiya."
Wata murya na ji ya ce " To yanzu mene ne abinyi ke nan?"
"Kwana ya kamamu fa oga."
Dariya ogan ya yi ya ce " Baka da hankali ke nan me zai sa mu kwana anan wurin da tsakanin
mu da hanya bai wuce kilo mita biyar ba, kuma kasan jami'ai zasu iya biyo mu tunda sun ga
inda mukayi. Dan haka kawai mu sanya wa motar bom mu barta a wannan wurin idan sun zo ta
sheƙe su garin bincike ."
"Haka ne Oga ka kawo shawara dai dai kuma ya batun tsare hanya domin kama matar barde
da aka sa mu?"
Jin kalmar sa
ta karshe ce ta sanya na saki wani fitsari a tsaye wanda ban san ina jin sa ba ma har haka.
Shiru na wani lokaci na ji ya ce "Da safe sai mu koma amma yau kan ba koma wa saboda a
kwai yuwar su biyo mu."
Ni dai ina tsaye kamar gawa a gefen daman su. Daga idanuna na yi na hangi wani ƙasurgumin
maciji ya nufo Ni daga jikin bishiyar da nake ra ɓe. Kuma idan na yi gigin matsawa tabbas zasu
ji motsina saboda ciyayin da suke ƙasa.
Haka ina ganin macijin yana tun karo ni, tuna wa da maganar wata tsuhuwar layin mu nayi da ta
ke cewa idan maciji ya hau kan ka baka motsa ba to bazai cutar da kai ba. Saboda zai dauka
yana kan bishiya ne.
Dan haka tuni na dauki wannan Shawarar tunda wuri ya ƙuremin dan har ya hau kaina . Haka
na daskare wuri guda har ya bi jikina ya sauka ƙasa, kuma Haka ya yi daidai da tashin motocin
su sunyi gaba.
Suna tafiya kuwa nima na ce banga wurin zama ba tunda har da su bom.
Dan haka na dauki sabuwar hanya ina ɗin gisa ƙafata da ta min tsami. Tafiya na yi iya tafiya
wacce ban san iyakar ta ba, dan har farin wata ya fara haska sararin samaniya.
Kwatsam na tsinci kaina cikin wani lambu na tumatir.
Aikuwa abin nema ya samu wai matar soja ta haifi dan sanda , zama na yi dirshan na fara cikin
tumatir din nan kamar an aiko ni har sai da na ji na ƙoshi tukun na bari.
Guntun ruwan gorar na dauka na sha na ajjye na koma gefen lambun da baka jin sautin komai
sai na kukan tsun tsaye haka ne ya tabbatar min da cewa a kwai tafki kusa ko kogi.
Dan haka na yanke shawarar na kwana a nan gudun kar na je na afka cikin ruwa!
Ina zaune na sanya sahwuya gabana saboda na sumto shi daga bayan na kwantar shi kan abin
goyon, sai kuma na fara aikin nawa wato kuka saboda yadda idan na tuna cewa a wannan
lokacin kowacce mace tana ƙrakashin kulawar mijin ta ne shi kashi yaron komai talaucin gidan
su yan zu yana sanye cikin kaya da kuma shinfiɗa mai laushi! Amma ban da mu da muke
talatainin dajin ga kuma fargaba.
Na ƙarashe maganar ina rushewa da kuka mai tsanani, ban san iya lokacin da na dauka ina
tunanin ba har bacci ya dauke ni, ban farka ba sai waje asuba dan haka banyi ƙasa aguiwa ba
na dauki guzurin tumatir saboda gaba na goya shawuya muka dauki hanya saboda bai farka ba
bare na bashi nono ya sha .
Na yi tafiya mai nisa har gari ya yi haske ban tsayaba a dokar dajin, kawai na ji kamar sautin
takun wani abu yana bin bayana cike da firgici na juya cikin tashin hankali na ke kallon abinda
na kalla wanda ya sanya ni yin na dama da guudwar da nayi....
PG 11
Zare idanuna na yi sosai saboda daman Allah ya albarka ce ni da manyan mganai, dan haka
cike murya kakkaura irin yadda na ji su Barde suna yi na ce "Mu bil adama zaku yiwa haka? To
idan ba ku maida mu bakin titi ba tabbas kun gama zama gawa da kuda ayyukan ku."
Shiru ya yi tunda na fara maganar yana ɓari sai da na sake masa wata uwar tsawa sannan ya
ce cikin in ina...
"A yi ha ha ƙur rrri dan Allah ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, wallahi nidai ban taɓa
kowa ba a wannan dajin saboda Ni kaina a tsorace na ke aikina."
"Kai!!!!! Dakata min me ka ke yi a wannan dajin na mu ."
Na faɗa cikin ƙwarin guiwa.
Yana karkarwa ya ce idan ba damuwa ya ke jinnu kiyi min rai mu bar wurin nan kuma koda y'an
ta'adda sun bayyana, to ki ɓoye ni idan ina baki amsar......ya ƙara durƙushewa a wurin .
Jin ya ambaci sunan y'an ta'addan tuni hanjin cikina ya kaɗa na ce " Ba zan boye ka ba!! Sai
dai ka yi ƙoƙari ka kai mu inda ba zasu gan ka ba domin ka bani amsa .....amma da zarar sun
bayyana anan zan Barka... Na faɗa ina kwashewa da dariya kasa kasa gudun ko suna kusa su
jini
"Muje ya ke bil jinnu."
Shine abinda ya faɗa kawai ya yi gaba cikin farin ciki na bi bayan sa domin ina tunanin haka
ta ta cimma ruwa.
Tafiya kaɗan mukayi muka shiga wata shimfiɗe ɗen lambun na yalo wani kewaye kamar ɗaki
muka samu muka tsaya ya kalle ni ya ce.. "Anan muke fake wa kuma ba sa zuwa nan ."
"Kai ya shafa." Na furta ina fadin me ka ke yi a dajin mu da har kuka kashe mana goɗiya?"
"Ranku ya ɗaɗe wallahi Ni mai aikin lambu ne kuma ban san komai a kan kisan ba ."
Kallon sa na yi cike da gajiya a jikina kuma ga shi bana so na nuna masa tsantsar gajiyar da ta
ke tare da ni saboda kar ya fahimci ni ba aljana ba ce.
Sai na ce masa "Ba ruwan ifriti da maganar ka!!! Abun da ya ke bukata kawai shine ka kaini
cikin garin ku da ya ke kusa wanda diyar godiya ta bayana ba zata gaji ba a ya yin ta fiyar.
Kuma kar ka bari wani bil'adama ya ganmu haka yana da ga cikin abinda zai jawo ka rasa ranka
!!!!! "
Sunkuyar da kai ya yi ya ce cikin in ina "in in Allah ya ya yarda ba zasu gan mu ba ."
"Ka tsira!! ." Na furta haka cikin ƙaraji.
Juyawa ya yi domin mu tafi na fakaice shi na cire yalo uku na boye cikin kaya na. Muka dauki
hanya ta cikin wasu lunguna da motoci ma baza su iya bi ba kuma mutum ma da kyar yake
kutsawa. Lallai irin hanyar nan sai wanda ya santa kaɗai ne zai ga ne ta.
Munyi tafiya mai nisa na fara hango bakin titi kuma da wani gari chan gefen sa sai na ga kuma
ya tsaya ya ce "To ya ke bil jinnu anan matsalar ta ke kuma. Saboda anan kam dole bil'adama
zasu ganni.Ya faɗa yana russunawa.
Na ce da shi " Babu wata matsala! Muje kawai ...."
Koda muka fara shiga garin sai na fuskanci cewa garin ba babban gari ba ne ƙauye ne kuma
ba shida wani girma.
Dan haka muna kaiwa wajen gidaje na ce da shi "Dakata! Anan zamu rabu, dan haka ka juya ka
koma kar kuma ka sake ka wai wa yo! Yin hakan yana nufin kana wasa da rayuwar ka ne."
Da to ya amsa min ya kama hanyar dajin da muka baro ba ko waiwaye dariya na ji ta kubce
min wanda rabon da na yi ta inda ta nutsuwa ce na irin wacce na yi da sunan aljana ba tun
ranar da zamu rabu da mijina. Ba zan mance ranar ba kam tabbas.
Yana kishin gide ya ce dani. " Ƙurraty na, na ɗago idanuna na dube shi na yi masa kyakkyawan
murmushi na ce "Na'am hubby."
"Ƙurraty wallahi ina sonki ɗayawa ranar da zaki haihu kawai na ke tunawa idan na tuna da
yadda mata suke shan wuya a wajen haihuwa, wallahi ƙurraty sai na ji kamar na karɓa miki
saboda bana son na ganki kina shan wuya." Ya ƙarashe maganar tashi yana langwabar da kai .
Murmushin na yi na kalleshi na bude baki " Allah sarki mijin ƙurrat haka Allah ya tsara mana mu
mata karka damuwa muyi ta addu'a Allah ya kawo ta da sauki ."
"Haka ne ƙurraty amma gaskiya ba zan iya tsayawa a asibiti ba wannan karan dan haihuwar
zulfa'u kusan kuka na yi , ke na yi ma saboda bayan kin haihuwa na dunga hawayen da ban
san na me ne ba."
Murmushin sosai na sake masa ƙasan zuciyata kuma ina farin ciki da alfaharin irin yadda na
samu miji mai sona har tsawon wannan lokaci da na haifa masa yara uku zan yi na hudu bai
rage wani abu da yake na soyayya ta a zuciyar sa ba.
" Karka damu hubby in sha Allahu zan haihu lafiya lau kana bacci sai dai na tashe ka ka ga
yaron ka ko yarin ya ......
Wuri na samu na zauna bayan dawo wa daga duniyar tunanin da na afka ciki tabbas na san
yanzu mijina yana cikin wani hali. Haihuwar da yake mata fargaba yau ta zo min cikin wani halin
da ko ni ba zan iya cewa ga irin yadda na sha a zabar ba. Saboda sawun Giwa ya take na
Raƙumi.
Ganin zaman ma ba shida amfani ya sanya na ta shi na dauki hanya na sake kutsawa cikin
kauyen ina tambaya har na isa gidan mai gari .
Na nemi na gana da shi aka ce min sai zuwa sallar Ishaa na dare zai dawo .
Haka na zauna na ci yalo da tumatir na bawa shawuya nono ya sha bawan Allah duk ya rame
sai yanzu na ga asalin ramar da ya yi har sai da na yi ƙwalla saboda dukkan wani ƙashi na
jikinsa kana ganin sa za ne, har wani ƙaton kai ya yi . Lulluɓe shi na yi na rungume shi acikin
jikina ina faman sana'ar da ta zamo min abin yi wato kuka. Sai naji an dafa kafaɗa ta baya,
saurin juyawa na yi na kalli wata baiwar Allah ta ce min kije fada mai gari ya na neman ki.
Tsabar damuwa ban san ma sanda daren ya yi ba har suka yi sallah da yake ina cikin halin jego
ba ni da damuwa a kan sallah amma fa ina bukatar kama ruwa domin duk jini ya ɓata min jikina
har ya bushe idan ban da ƙarni ba abinda na ke yi.
Alfarma na ne ma wurin matar ta kuma amin ce min na shiga daga cikin gidan ta na wanke
jikina na kama dukkan inda na san ya ɓaci na wanke na baza zanin ya ɗan sha sannan na
daura shi may fito muka dauki hanyar fadar garin koda na je wurin a cike ya ke da jama'a kamar
za'ayi wani taron, shiga ta ke nan na hangi wannan bawan Allan da ya taimaka min ya shigo
dani gari . Yana ganin fuska ta ya mike ya na nuna ni, luuuu ya zuɓe kasa sumamme!
"Tashin hankali!" Shine abinda na furta a bakina ya yin da sauran jama'ar wurin duka suka yo
kaina suna faman salati da salallami suna