Share this page
tabasa 2yrs, ita ke rike da cake da akwai candles na 34yrs ajiki, suka hau waka. “Happy birthday to you, Happy Birthday to you Happy birthday, happy birthday to Marwan, happy birthday kid bro” kansa yadan shafakai cikeda takaici zai juya Ya Fadila tace “zai gudu” dasauri Ya Ammah tazo ta jawosa tace “zan cimaka mutunci fa Marwan” kaman zaiyi kuka yadan kalli Mami dake dariya na manya tana kallonsu yace “Mami” Mami tace “don’t call me, kasan how long they’ve been planning this? Kowacce tazo gidan nan sabida kai kana wani Mami awajen, menene problem dinka da birthday naka”? Ya Maryam tace “zaunar dashi Ya Ammah ya hura candles nasa” zaunar dashi Ya Ammah tayi tana karban folder hannunsa da labcoat, tace “Faiza take this folder to your Uncle’s room” dasauri Faiza ta amsa tawuce sama, Ya Fadila takawo cake din tana murmushi sosai tace “Happy Birthday Kiddo” wani kallo yamata yace “waye Kiddo”? Ya Maryam wacce Fadila ke bi tace “kahura candle kadena wahalar damu” Mami ya kalla gyadamai kai tayi alamun yayi, baiyi musu ba, ahankali ya hura candle din, sukahau tafi, Ya Fadila ta lakato icing sugar ta shafa masa a fuska tana dariya, Marwan yace “Mami” zuwa wajen Mami tayi kaman zata mata fada sai itama ta lakata ta shafa mai a kumatu tace “happy birthday Son, Allah maka albarka” saita mannamai kiss a goshi, lumshe idanu yayi, Ya Ammah ta rungumesa tace “I love my only brother” Ya Maryam itama ta zauna tace “I love him even more, Faiza kumana hoto” dasauri Marwan ya yunkura zai tashi suka rikesa, Ya Fadila tace “Wlh saika dauki hoto” yahade fuska twins na dariya suka mummusu hotuna, Ya Ammah takama fuskansa tace “smile dan Baby this is what you get idan all yayyinka mata ne” kaman zaiyi kuka yamike zai wuce Fadila tai hugging nashi tace “tsaya kaji ina zaka sabida kai aka hada meeting dinnan fa” dan tsayawa yayi ya kalleta yace “meeting na mene”? Mami ganin yagaji and tasan bazasu barsa yahuta ba tace “sai gobe za’ayi go and get changed yanzu ka sauko let’s do dinner” dan kallonsu yayi duk suna kallonsa, understanding mata is so hard yakasa gane anything, sai kawai yajuya yana magana kasa kasa yace “why do i have to be their younger brother not elder please, i hate this!” Ya Maryam tace “Allah ne yakeso yakama ka kuma ba yanda zakayi”bai kara magana ba yawuce abinsa. Ya Ammah wacce kebin Mami tace “but how’s the girl like Mami?” Duk Mami suke cemata kap dinsu, Ya Maryam tace “banson yarinya mara tarbiya fa wacce zatazo tarabamu da kanninmu, we raised kaninmu together zumuncin mu is thriving so she has to be good and from a good home” ahankali Mami tace “kawai namai sha’awabta ne, tanada hankali sosai, ga kirki, she called me jiya taji ya kafan nawa, kawai ni namai kwadayin yarinyar sabida nasan baida budurwa, kuma naga itama sai Satan kallonsa take, zanso ahada bikinsa dana Saleem suyi aure, he’s 34 why is he still single yakamata yanada yara by now”Ya Ammah tace “ai haka likitoci suke wlh idan bamu tsaya akansa ba auren ma bazaiyi ba dayayi aure zaiyi gwara yaje yakaro course kan wani abu daban karatun likitoci baya taba karewa fa aduniya” duk sukai dariya, Fadila tamike tace “lemme go and bring him down”. EPISODE 1️⃣9️⃣ Sama Ya Fadila tawuce knocking dakinsa tayi batare data bude ta shiga ba, he might be kanninsu but all of them even Mami wacce take matsayin mamansa da mamansu duka respect him, sabida Marwan nada natsuwa, da hankali, they all play and crack jokes but they respect his privacy sosai, sake knocking tayi tace “idan bakace na shigo ba Allah zan shigo abu…” bude kofan Marwan yayi yana sanye da 3qauater wando na common flag dawani dari green sleeve daya kamasa hakan yasa muscles dinsa suka bayyana na hannunsa a mummurde yama baza kamshi da farin glasses din a idanunsa yahade fuska sosai itama Fadila tahade fuska tana kallonsa tace “wai sabida kaga kafimu girma shine you are feeling kaman kaine babba” hararanta yayi kawai yajuya baiyi magana ba, shigowa dakin tayi tanabin ko’ina da kallo dakinsa kamshi sosai everywhere looks clean tawuce bakin gadonsa ta zauna shikuma tana kallon wani English novel dake wajen babba masu irin thousand plus pages dinan mai suna love wreck, tadauka tabude tana murmushi tace “you book warm” Marwan ya wuce closet nasa dan Saleem ya hargitsamai kaya aikin yakeyi, ahankali Fadila tamaida novel din ta ijiye tanabin ko’ina da kallo tace “Doc kasan mene”? Shiru yamata still hakan yasa tamike tashigo closet din ta tsaye gefensa tana kallon yanda yake arranging kayansa tace “Mami wants that girl for you” dan tsayawa yayi chak saiya juyo ya kalleta looking very confuse yace “which girl?” Ya Fadila tace “wacce ta taimaketa a airport” dan gajeren tsaki yayi yajuya yacigaba da abinda yakeyi bai magana ba, sai Fadila tazo gaban closet din ta tsaya gabansa tana kallonsa sosai, ahankali yace “what?” Hannu tasa ta karbi hannunsa tarike cikeda dan damuwa tace “Marwannnnnn” dan rage murya tayi tace “please get married kaji kodan hankalin mu ya kwanta gabaki daya, kagama school you are doing well for yourself, to what is stopping you from getting married? Kobakayi dan mu ba do it for Mami kaji, you know batason takuraka tana sonka da yawa amman batada burin daya wuce kai aure kasami yarinya daga gidan arziki ka aura kaji” shiru yayi baice komiba, Fadila tace “Kanada anyone yet dakakeso tunda bakason wacce Mami keso”? Ahankali yawuce yana tattara kayan laundry kaman bazaiyi magana ba yace “I don’t know” dasauri Ya Fadila tace “I don’t know? What does I don’t know mean? Is that a yes ko no” saitai shiru kaman mai tunani saita zaro idanu tace “akwai wacce kakeso amman baka riga kafada mata ba kenan Marwan is that abinda kake nufi”? Wucewa yayi yashiga restroom abinsa Fadila tai wani tsalle tace “yesss, yessss” saita wuce tabar closet din dasauri tasauka kasa. Around 9 ya sauko yau duk agaidan Mami yau yayyinsa suka kwana, kitchen yawuce yasami Mami na bama Faiza cereal tace “morning Best Uncle” kanta yashafa yace “how are you” tace “fine” ta karbi cereal tafita yace “Mami ina kwana” Mami tace “nace maka we have meeting yau ina zaka kuma”? Ahankali yace “I have patients now anjima idan zaku fara calll me zan dawo” dan jim Mami tayi saita gyadamai kai tace “muje kai breakfast toh” dasauri yace “Mami nadawo zanyi I don’t want to eat this early, or pack for me” yayi magana tuna Amirah dayayi….. Wuraren 10 yakai asibitin parking yayi yafito as usual yana tafiya a nutse dayake yau Friday, wani soft yadi ne ajikinsa dark blue anyi wani simple karamin aiki a wuyan Ya Rabbi yayi wani irin kyau kaman ango, baisa hulaba gashin kansa sun kwanta suna kyalli glasses na idanunsa sunmai kyau, hardly yake rike kulan amman yau yadauki kulan abincin da Mami tasamai da kansa yawuce ciki yana shiga reception yaga Ammi zaune da hijabi har kasa tareda wata yarinya da kusan kansu daya da Amirah zamatafi Amirah kiba saidai Amirah tafisu haske sosai but suna kama tana sanye da black hijab, yana ganinta yagane itane Miemie da Amirah ta rubuta, tunda ya shigo reception din Miemie takafesa da idanu tunda take arayuwanta bata taba ganin namiji kyakkyawa dan gayu irinsa ba ba lab coat ajikinsa so he doesn’t look like a Dr, yana shigowa reception din yadauki kamshi, kallo daya yama Ammi yaganeta batama ganesa ba saiya taho wajen kai tsaye alamun mutum na zuwa towards them yasa Ammi tadago kai itama bata ganesa ba danba lab coat a idanunsa amman glasses na idanunsa yasa tadan dauki fuskan tamike da sauri tace “Doctor ina kwanan mu” anatse Marwan yace “Assalamu Alaykum, ina kwana Ammi” ahankali Ammi tace “lafiya lau” ta taba Miemie dake kallonsa tace “baki iya gaisuwa ba” dasauri Miemie tace “ina kwana” Gyadamata kai yayi batare daya amsa koya kalleta ba yajuya yace “let’s go” dasauri Ammi tace “to” suka bisa abaya har zuwa office nasa Ammi sai kallon wajen take yanda wajen yakeda kyau kaman ba’a Nigeria ba ga patients da uniform suna breakfast mai kyau shayi da bread da egg, ga ma’aikata ana kula dasu, suna ganin Marwan suka fara ihu. “Dr M good morning” hannu yadaga musu yace “morning friends” yabude office ya shiga yace “bismillah” shigowa su Ammi sukayi suka yanuna musu couch Ammi gabanta faduwa kawai yake ta kosa taga Amirah, labcoat dake hanger Marwan yadauka yasaka tareda daukan sthethoscope nasa yace “bari nakawota” Ammi tace “tom” yawuce yafita Miemie tabisa da kallo Ammi ta daka mata duka tace “baki taba ganin likita namiji bane kike binsa da idanu haka” dasauri Miemie tace “Ammi wlh bantaba ganin Dr dan gayu kyakkyawa kaman balarabe ga charisma irinsa ba, Ammi inama ya auri ya Amirah, yaransu will be very fine” Baki Ammi tabude tana kallon Miemie, sai kawai takai hannu ta dan bugi bakinta tace “shirmammiya yimin shiru” Miemie tadan turo baki bata kara magana ba. Ahankali yabude kofan dakin Amirah na zaune bakin gado an gyara dakin tsaf Umma na tareda ita tayi wanka ta chanza uniform Umma na bata abincin data kawo mata taki karba yana bude kofa Amirah tajuyo da sauri ta kallesa sabida kamshin dataji, yana sanye da lab coat baisa botura ba kana ganin blue yadi dake jikinsa wani irin sanyi Amirah taji da batasan sanda tadaga hannunta takai baki ba tana bitting nails nata kafafunta farare tasss dan ba’a Riga an maida mata black sock dinba, Umma tace “barka da zuwa Doctor” karasowa wajen yayi anatse yace “sannu da aiki Umma”Umma tace “takicin abincin” hannunsa yamika yadauki chat na Amirah yana dubawa dan yaga abubuwan da nurses sukai logging in yace “barta zaki iya tafiya” wucewa Umma tayi ta bar dakik yana tsaye wajen yana duba chat nata Amirah da hannunta ke baki tasake dago kanta kaman yar Baby ta kallesa wlh yamata kyau genunaa da sajensa akwance suna shinning yana kamshi sosai wani irin haske taji azuciyanta tareda sanyi juyowa Marwan yayi yadaura kwayan idanunsa cikin nata wani kalan kwarewa tayi da tari sabida tsabagen sanyin dataji sabida yanda ya kalleta cire idanunta tayi tana tarin maida folder yayi yarufe saiya taho ya tsaya gaban gadon daidai tarin na tsayawa hannunsa yasa yadauki black sock dinta dake gefen gadon batare daya kalleta ba yace “baki iya gaisuwa ba sai kallon mutane” dayan hannunta takai tasa abakin tahada duka biyun ko tadanji dama daman abinda takeji cikin yar karaman very tiny bedroom voice din tace “ina kwana” “how are you Ameenah?” Ya amsa da very husky manly voice yana kallon fuskanta ganin wani katon pimple guda daya daya fito mata a kumatu wanda babushi jiya yana gani yasan kuma na menene, shiru tayi takasa magana, saiya sa mata safa a kafa without touching her skin juyowa tayi ta kallesa dukawa yayi saiya dauki canvas nata ya zazzage datti dake ciki yashiga samata yana kulle igiyan yasa mata Second one din saiya mike yakalleta dasauri tadena kallonsa yace “kinaso kiga Ammin ki?” Dasauri tajuyo ta kallesa lumshe idanu yayi yabude yace “let’s go” dasauri tawani sauko daga gadon jikinta har wani tsuma yake dudda fuskanta is normal ba farin ciki nor bakin ciki saiya juya yayi gaba tabisa da sauri yabude kofa yajuyo yana jiranta danya lura bata iya tafiya da sauri ba ficewa tayi yafito yarufe kofan yawuce tana biye dashi har zuwa office nasa, bude kofan yayi Ammi tamike dasauri hakama Miemie Marwan ya matsa yana kallon Amirah yamata alamu data shiga dawani irin sauri ta shiga ganin Ammin wani tsuma jikinta yafara kaman tai shekara bataga Mamanta ba kawai saita wani irin kwasa da gudu tai wani tsalle kaman yarinya tawani rungume Ammi ta kankame Ammi gamgam tana manna fuskanta sosai a kirjin Ammi kaman zatasha nono, batace anything but kalan hugging Mamanta datayi says morethan enough, she misses mahaifiyarta, kankameta Ammi tayi idanunta na ciko da hawaye sosai duk yanda Ammi taso kartai kuka amman takasa sai hawaye tana shafa bayanta tace “Amirahhhhh” Miemie ta share hawaye tana kallonsu she’s so happy taga sister ta, Marwan yadade yana kallonsu dazai shigo office dinne amman saiya maida musu kofan yarufe yawuce they need the time. EPISODE 2️⃣0️⃣ Ammi taciro Amirah daga jikinta da bataso ta barta taga yarinyar kaman ma takara kyau ne tana bin jikinta da kallo tundaga sama har kasa tace “Yammatan Ammi ta” tsare Ammi Amirah tai da idanu tana kallonta batako kyafta idanu, Miemie tace “ni barakimin magana ba ko” kallonta Amirah tajuyo tayi saita shige jikin Ammi dasauri tai lamo amman still tana kallon Miemie dake murmushi sosai, Ammi tacirota daga jikinta ta zaunar da ita cikeda kulawa irin na mahaifiya ta taba uniform din tace “wayake samiki kayan nan Amirah”? Ahankali tana kallon Ammi da yar karaman muryan tace “ni” Ammi tace “an ina”? Ahankali tace “bayi” Ammi tace “wanka fa waya miki”?ahankali tace “ni”Ammi tace “da me da me nace babu kyau namiji ko mace su taba miki idan sun taba kiyi ihu ki gudu ko kiyi cizo sannan ki sanar dani” ahankali Amirah ta nunama Ammi boobs da wajen fitsari, cikeda hikima Ammi tace “wata ko wani yataba?” Girgixama Ammi kai tayi alamun a’a, wani ijiyan zuciya Ammi tasauke tace “Alhamdulillah ,Alhamdulillah” Ammi takai hannunta tadaura gefen fuskanta tana murmushi sosai hawaye naso su kara zuba amman ta tsaresu tace “bari Dr yazo saimu tafi gida ko”sake hawa jikinta Amirah tayi ta kankame Ammi wlh kaganta zaka dauka nono zatasha she’s super clingy to her Mom, Knocking kofan akayi Ammi na kokarin cireta taki fita daga jikinta tai lamo Marwan yabude kofa tashigo batare daya kallesu ba yamaida kofan yarufe Ammi tabisa da kallo kawai taji zuciyanta ya natsu da Dr ganin diyarta is fine babu wanda yayi kokarin cutar da ita a facility or take advantage of condition na yarta na rashin wayau da shirme haka, zama Marwan yayi ahankali Ammi tace “Doctor Marwan” dan dago kansa Marwan yayi dan baitabama tunanin Ammi zata rike sunansa ba ko ta kirasa in full hakaba, baki Ammi tabude zatai magana but she’s so emotional saitai shiru kafin tace sauke iniyan zuciya tace “this past kwanakin nan sune the saddest day of my life” Ammi takai hannu ta sharce hawayen daya zubo mata hakan yasa Marwan yasauke kansa kasa Ammi tace “banda tunanin daya wuce is y’ata fine? Taci abinci? Tana ina? Yana wajen wa? Yarinya na bata magana, what if wani ko wata take advantage of condition nata kaganta ba uhm ba uhmhum ba wayau ba…..” Ammi tai shiru sabida kuka dayake cinta, Ammi tasauke sauke ijiyan zuciya tace “naga diyata she is fine, healthy, babu abinda yasameta, she looks healthy than yanda takema a gidana, zzzabin yatafi nobody took advantage of her, she’s well taken care of and it’s all thank to you Dr Marwan, dan haka nagode nagode, Allah yayi Albarka sannan Allah yabiyaka nagode” dakin duk akai shiru, ahankali Ammi tace “zan iya tafiya da ita ai ko Dr?” Dan shiru yayi saiya dago kansa yakalli Ammi yace “before that akwai maganan danakeso muyi dake”saiya mike yazagayo yayi wajen kofa yace “Maryam keda Amirah ku biyoni” dasauri Miemie tamike tana mamakkin yanda yakirata cikeda izza kaman yana kiran kanwarsa, ahankali Ammi tadaga Amirah daga jikinta tace “bi Miemie kuje zamuyi magana da Doctor gani nan zuwa” awani kalan shagwabe Amirah takara kwakwume Ammi, Marwan na kallonta kai tsaye yace “come with Maryam Amirah” ba musu tasaki Ammi ta taso, saitazo sai yayi gaba wani room yabude kayan wasa ne adakin da tv saiya bude yace “ku zauna anan” shiga sukayi yamaida kofan yarufe yawuce yakoma office din Ammi tabisa da kallo tace “ina fatan komi lafiya lau Dr”ahankali yace “eh, sit here” yanunama Ammi kujeran dake gaban table hakan yasa Ammi ta taso tazo wajen gaban tazauna Marwan yazauna yana bude locket saiya ciro zanen da Amirah tayi daya linke yamikama Ammi yace “Ameenah tai zanen nan” ahankali Ammi tasa hannu ta karba saita shiga warwarewa batamasan Amirah tai zane ba Ammi ta zana tsafa akasa ga Daddy yana kaimata punches da duka dasauri Ammi tarufe zanen takalli Marwan dake kallonta tace “Dr Amirah tai zanen nan? Bata taba zane a agida ba banmasan ta iya Zane hakaba”ahankali Marwan yace “kids like her nada talents da dama da bazama kasani ba sai randa zasuyi zakaita mamaki, and yara irinsu nada wani irin memory da basa mance abu, she might not be verbal but she has many ways na communicating abu example this drawing datayi” Marwan yayi shiru sai chan yace “I know this is your private life and baikamata nasani ba, but did you know what this means for yara irin su Amirah the day dasuka fara samun takardan zane su zana abin nan”sai Marwan ya karbi paper ya warware yakalallo Ammi yace “it means this is matsalan dake damun Ameenah! I believe I can help Ameenah get better but I can’t do it without your help dole saikin taka rawan gani a nema mata lafiya, please answer me sincerely” yayi shiru kafin kai tsaye Marwan yace “idan mijinki na dukanki agaban Ameenah yakeyi?!” Sauka tambayan yayi a kunnen Ammi kaman saukan aradu, bawai tambayan yana dukanta ko ba’a dukanta yayi ba no kai tsaye yamata tambayan cus he’s sure anayi ne sai Ammi takasa magana, ahankali Marwan yace “I am sorry I know my question might be somehow on your ear, amman condition din Amirah shine wannan, akwai cases na children dasukai withnessing domestic abuse, ana dukan iyayensu agabansu dayasa suka shiga depression, wasu suka sami ciwon hauka etc” Marwan yace “I read history nata she was okay as kid but around 6/7yrs kika dawo da ita hospital dinnan akan she hardly talks, ko a school batason mutane, she’s so clingy towards you batason ta barki even for a second, that means alokacin brain dinta yafara wayau tafara understanding someone is hurting her mother or her mother is always sad ko abu makamancin haka am I right?” Lumshe idanu Ammi tayi hawaye na fitowa saitasa hannu ta sharce ahankali tace “Dr are you saying nine sanadin da Amirah take haka?” Ahankali Marwan yace “not entirely but kin dauki 70% na dalilin dayasa she’s like that”Tashi Marwan yayi saiya wuce wani drawer saiya dauko wasu abubuwa kaman roba kaman ceramic amman all of them brain ne guda biyu yace “can you touch this” hannu Ammi tasa ta taba na farkon Marwan yace “what did you feel?” Tace “karfi” yanuna mata dayan alamun ta taba ta taba tace “taushi wannan” Marwan yace “good I want you to picture brain na Amirah as mai taushin nan”Ahankali yace “yawanci a matsalan kwakwalwa duk wanda zakiga yakeda tabun hankali kokuma wani matsala na kwakwalba abu daya zuwa biyu ko uku ne, na farko akwai heredity inhar a danginka kunada mai ciwon hauka so likely a lineage naki ko family naku akwai Wanda zai dauka, sai nabiyu family, family plays a big role good or bad a ciwon hauka now this is inda Ameenah tashigo, don’t forget nace ki dauki brain na Amirah as soft one dinnan, Allah yana halittan mutane with different features, akwai mutane masu taurin rai, taurin zuciya karfin hali da sauransu, akwai mutane masu sanyi zuciya, hakuri, peaceful marasa damuwa, Example now Amirah and Maryam are siblings amman Maryam looks tough a inda Amirah take, Amirah is a child dakika haifa that’s so soft consider her an egg, she’s so dalicate abu kadan zai iya tada mata da hankali sabida haka Allah ya yota, that girl loves you more than anything and all of a sudden tana yar karaman nan maybe she witnessed kullum mahaifinta ke dukanki her little delicate brain couldn’t take it and boom” Marwan yadauki brain din ya wurga a kasa saiya fashe ga abubuwan brain din sun tarwatse Ammi takalli abin Marwan yace “this is brain na Amirah, her brain doesn’t function well sabida she’s traumatize with abinda take gani a gıda saisa she doesn’t act normal, ganin mahaifinta triggers her anxiety, she’s always clingy towards you cus she feels that’s her own way of protecting you idan tana jikinki nobody can hurt you babu wanda zai taba mata Mama, she’s scared, afraid of mutane she feels kaman za’a daketa they might hurt her yanda ake miki, gani mutane da yawa na daga mata hankali, she’s constantly not at peace, she’s always sensing danger around duk inda take, hallucinating it, she’s never at peace saisa bacci kemata wahala koda yaushe she’s thinking or imagining you might be in danger, she’s sad from abubuwan dataga ana miki saisa she grew up not to know yanda ake smiling ko wani abu her face is always straight da sauransu, low speech tone, her voice is always low, she hardly talk, very attach to you dake kadai take yarda aduniya, all this are signs na Schizophrenia spectrum disorder, wanda particularly trauma during childhood, can disrupt healthy brain development and trigger symptoms na schizophrenia, that’s why kike ganinta she’s not a normal girl as she should be kaman sauran yara yammata of her age”duk yanda Ammi taso ta daure takasa tafashe da kuka sosai gaban Marwan, wlh da gaske ne ilimi ba karya bane, bata taba sanin cewa yaro yataso yana ganin fadan iyaye, dambe ko ana dukan mahaifansa yakansa yasami trauma dahar kwakwalwansa zata buga ba sai yau, brain na kowa daban akwai wanda baida karfin zuciya da abu kadan koda tsoro ne zaisa kansa ya tarwatse, Ammi tabasa tausayi saiya sauke kansa kasa yayi shiru, Ammi takama bakin hijabinta ta share fuskanta tace “bantaba sanin i could be the reason why diyata is like this ba sai yau Doctor and it breaks my heart so so much Ya Allah! Ninaja y’ata is like this” Ammi ta share hawaye, da kyar tai shiru muryanta yayi rauni sosai tace “Doctor Marwan can she be fine? Ana warkewa”? Ajiyan zuciya Marwan yasauke yace “lemme answer you as a Muslim cewa duk cuta nada magani banda mutuwa da tsufa so yes, as a Doctor kuma idan mutum yakamu da schizophrenia ba’a warkewa amman ana warkewa” ahankali yace “what I mean by ba’a warkewa shine inhar zata koma tacigaba da ganin mai dukan ki ko ana dukanki still you are in pain or you are sad she will always be coming back to square one, she will not be fine, ana warkewa idan har an kiyaye duk wani abu dazai dinga triggering anxiety nata, if you’re the problem you need to be in a space with her dazata tabbatar cewa you are 100% safe and happy hakan zaisa she will be relax and calm tafara sakewa, then in my side as the Doctor I will take my part na giving her therapy, teaching her how to manage her anxiety, how to overcome her fears dasauransu, your daughter have high chance of getting better she’s still young she’s just 20, zata warke and act like any other kids kawai yawan magana hira da sauransu sune ahankali ahankali zatazo ta saba da yi”Ammi tai shiru sai chan tace “it’s all my fault and kome zanyi zanyi dannaga Amirah tasami lafiya, akwai bukatan ta zauna a asibiti?” Gyadamata kai yayi yace “yes I want to monitor her for 21days that’s 3weeks and see progress chat nata, in those days inaso ki dinga zuwa ganinta after every 3-5days, before yanzu kitafi talk to her and kigayamata kinaso tanemi lafiya taji sauki, what I mean is for the first time I want you kiyi magana da Amirah kaman kina magana da an adult not yarinyaShe understands things sama da yanda kike tunani, just talk to her, and pray for your daughter’s health addu’an mahaifiya babban abune, pray for her to be strong minded, tazama yarinya that can live and depend on kanta even without you being there, just pray hard kibarma Allah komi” Ammi tadade tana kallon Marwan dake magana gabaki dayan rayuwanta bata taba ganin matashi ko likita mai hikima daya

Chapter 11 of 16