bata lokaci yamata bayanın rashin lafiyan Amirah, sannan yakaranci Amirah yagano matsalan Amirah like this doctor right here for the past almost 20yrs kenan, kawai saitaji Marwan yashiga zuciyanta sosai, ahankali tace “nagode Marwan nagode kwarai, Allah yamaka albarka” gyadamata kai saiya mike yace “go and meet her” wucewa tayi yayi Ammi ta mike tana bin Marwan da kallo yabude kofa ya tsaya Ammi tazo tawuce sannan shima yafita yakai Ammi dakin.
WHAT DO YOU GUYS KNOW ABOUT CHILDHOOD TRAUMA???
ITS VERY BAD YARA KANANA SUNA GANİN IYAYENSU NA DAMBE KO FADA, PLEASE PARENTS TAKE NOTE AND NEVER TRAUMATIZE ABINDA KIKA HAIFA!!!
EPISODE 2️⃣1️⃣
Budema Ammi kofan dakin dasuke ciki yayi yahada idanu da Amirah datai lamo ta kwanta ajikin Miemie kaman itace kanwar Miemie, Miemie kuma itace yayan, Miemie na playing game da wayanta na candy crush Amirah na kallo, kana ganinsu kaga siblings dakeson juna dakeda hadin kai, inhar babu Ammi to tasan Miemie, idan kuma akwai Ammi, Amminta kadai tasani, hada idanu dasukayi yasa Marwan yadauke kai yawuce yana rufo musu kofa Ammi ta shigo dakin, ahankali Amirah tacire idanunta daga kofan ganin Ammi ta tashi daga jikin Miemie Ammi tazo ta zauna zata shiga jikinta sai Ammi tace “tsaya tsaya Amirah, magana zanyi daku dukanku especially ke Amirah”Amirah ta kalli Ammi asanyaye, Ammi tadan sauke ijiyan zuciya maganan namata nauyi sosai abaki amman ta tattaro duka natsuwanta tace “hospital ba shine wajen daya kamata nayi irin maganan nan daku ba amman dole anan zanyi ta da ku cus is very important” Ammi tasakeyin shiru, saitace tana kallon duka yaran tace “Amirah bata gama cika shekara daya aduniya ba mahaifinta yarasu ta sanadiyyan hatsari dayayi!” Ammi tai shiru saita kalli Amirah tace “Babanki was hardworking and he’s doing very well, baiyi makaranta kaman Yayansa Baban ki Miemie ba dan Babanki dan boko ne, sannan shine kannin Babanki, trailer yake tukawa yana zuwa su lagos da sauransu ahaka Allah yabudamai yasai nasa trailer yafara tafiya da ita kafin yarasu yanada trailer guda uku tasa ta kansa, gidan mu dinnan nasa ne, da motoci biyu wanda an saida Babanki Miemie yasai sabo da kudaden, da sauran kudin gadon ki duk yana wajensa”Ammi tai shiru saita sauke ijiyan zuciya tace “bayan Babanki ya rasuwa tun kafin nagama takama Babanki Miemie yaje yasami Umma ta kafin tarasu kan zai aureni sabida ke marainiya, menene, menene, Umma ta yarda da hujojin daya bayar dudda raina bai soba amman da Umma tamin bayani nima naga gaskiyan ta, mace ce diyata, bakowani namiji zai yarda najemai da yarinya ba, sabida ke na yarda na auresa badan ina sonsa ba ko wani abu kawai Umma tadage sabida tagansa babba yanada hankali, ga ilimi zaiyi kasuwanci da gadonki kudin hayayyafa duba da iliminsa menene menene itada yayana dai saida sukasa nai auren, tunda nai auren banjin dadi, gashi immediately saina sami cikin ki Miemie, saisa dake da ita shekara dayane banbancin ku” Ammi tai shiru duk tana kallon yaran dake kallonta tadan fuzar da ijiyan zuciya tace “cin mutuncin yau, daban na gobe daban Amman ina hakuri na daure ganin Allah yariga yabani yara mata da kansu yake daya to ya zanyi idan ban hakura na zauna ba? Natafi wazai kulamin da ku Maman Baby ko ganinku bata kaunar yi, banda komi, gadon duka ya amshe yana hannunsa, nasan kun riga kun sani mahaifinku mutum ne mai saurin kai hannu, so yakan dokeni” tai maganan tana kallon Amirah dake kallonta batako kyafta idanu, saita kalli Miemie ahankali tace “nasha tunani da dama but among reason dake hanani daukan mataki harda ke Miemie, nakanyi tunani idan nabar gidansa aurenki fa? Nine mahaifiyanki I need to stand akanki na shirya ki na koyarda ke zaman gidan miji, yaya kenan?”Ammi tai shiruu tace “as yarana banda abokan shawara ayanzu sai ku, ko yayana ban sanar da shi abin nan dazan fada muku yanzu ba sabida bazai barni ba, kunakeso na sanar sabida kune hakkin ku ke kaina” Ammi tai shiru kafin ahankali tace “inaso na rabu da Babanku auren mu yakare gabaki daya kun yarda?” Duk sukai shiru suna kallonta, Miemie ce ta iya breaking silent din tace “Ammi kika rabu da Daddy yazakiyi? Ina zamuje? Yaya baida kudi balle muje gidansa, I’m sure Daddy bazai taba baki gadon Amirah ba har gidan ma dudda gidan Amirah ne ina zamu?” Murmushi Ammi tayi tace “banson gadon yarike, gadon nata ma duka yarike, akwai wani fili da Baban Amirah yabani tun yanada rai, Yaya naba alokacin ya ijiyemin takardun suna wajensa zan sa adaga filin asa akasuwa konawa na samu zansai karamin gida haka abarayin unguwan su Yayana, sai na miki siyayyan kayan daki dan nasan narabu dashi zai iya cewa bazai siya miki komiba, na rike na neman maganin da asibitin Amirah, sai na ja jari nakama wata sana’a sabida na iya kula da Amirah in sha Allah, kun yarda?” Ahankali Miemie tace “na yarda Ammi, Ammi you’re a good woman, Daddy baya sonki at all, babu amfanin zama da wnada bai sonka, sabida mu baikamata kiyita cutuwa ba, I know halin dana shiga rannan dakika sume akasa, I’m with you and I pray Allah yasaka miki da abu mafi alkhairi, sannan Allah yabiyaki hakurin dakikayi all this years sanadiyan mu” Ammi ta lumshe idanu tace “Ameen Ameen, thank you Maryama na” saita kalli Amirah tace “kin yarda na rabu da Daddynku Ameenatu? Bazai kara tabani ba, he will not have power over me, zamubar gidansa and live far away kinason haka”? Gyadama Ammi kai tayi alamun eh, murya chan kasa yar karama kaman mai tsoron magana tace “I don’t like him” murmushi Ammi tayi saita kama hannunta tarike tace “kinsan menakeso kimin yanzu Ameenatu na?” Girgixakai Amirah tayi alamun a’a, Ammi tace “I want you to stay here kiji sauki completely, Dr Marwan is a good Dr, inaso ki sami lafiya Amirah, kizama daidai dakowace diya mace sa’an ki, kafin nan nikuma da Miemie munsai sabon gida, mu koma sabon gida, Daddy ki will never touch me again, nor beat me, or make me sad, we will always be happy, sannan muyi aure da bikin Miemie, zan zo jibi, upper jibi sainazo na daukeki mukoma sabon gidan mu just me and you da Miemie ko kinason haka ko?” Tadade tana kallon Ammi saita gyadama Ammi kai alamun eh, Ammi tace “kidinga bude baki kina magana, biggest buri na aduniya is naga kin warke, inhar kin warke I will be very happy babu abinda zai kara damuwa, kinason Ammin ki ta kasance cikin farin ciki?” Gyadama Ammi kai tayi alamun eh, Ammi tace “naganki kin warke shine zaisa naji farin ciki, promise me you will be fine daga yanzu tunda ba Daddy”? Ahankali ta gyadama Ammi kai tace “I promise” murmushi sosai Ammi tayi tace “toh bari nakama gashin nan ahankali zan miki kinji” gyadama Ammi kai tayi Ammi ta kwantar da ita akan cinyanta tafara mata manya manyan kalaba, gashinta tsantsi, wuraren 12 Ammi tagama saita maida mata hulan goshinta yadan fito tayi kyau, Ammi tace “muje toh” Ammi na rike da hannunta suka fito daga dakin daidai Saleem na saukowa daga sama ward nasu, he’s feeling very sick today, sai amai yake gawani kalan tunanin Amirah daya addabesa, baisan yarinya ba, baimasan sunanta ba amman ko kulle idanu yayi ita yake gani wlh, ganinta tareda wata mata dayana gani yasan mahaifiyanta ne saida gabansa yafadi, gawata yarinya da kusan kansu daya da Amirah, she look a bit older or bigger than Amirah ma.
Knocking yaga Matar tayi suka tsaya, muryan Marwan sukaji a nutse daga ciki yace “come in” bude kofa Ammi tayi ta shiga kaman Amirah taji ajikinta ana kallonta dan dago idanunta tayi karaf tahada idanu da Saleem daya tsaya chak yana kallonta dasauri tadauke kai kirjinta na bugawa sosai itada Miemie na shiga cikin office din.
Marwan na magana dawani male patients ne, daidai sun gama su Ammi suka zauna patient din yafita, Ammi takalli Marwan tace “Dr zamu tafi Amirah zata zauna anan kuma tayi alkawari zata dinga shan magani dan ta tsani magani, sannan zata dinga jin magana, bazatai komi dabe dace ba ko Ameenatutu nah”? Gyadama Ammi kai tayi tai lamo jikin Ammi kaman marainiya, Ahankali Marwan yace “that’s okay” Ammi tace “akwai wani kudin da za’a biyane?” Cikeda girmamawa yace “no babu” Ammi tace “to shikenan bari muje, tashi muje Miemie” mikewa dukansu sukayi harda Amirah dasaurinta Ammi zatai magana , calmly Marwan yace “sit down Ameenah” komawa Amirah tayi ta zauna amman tai tsuru tana kallon Ammi da Miemie dake tsaye, Ammi saita bude jakanta tabata wata yar leda dake cikeda snacks harda cincin tace “kiyita ci kinji zanzo jibi i promise kinji yarinya na” gyadama Ammi kai tayi jikinta duk yayi sanyi sai Ammi kawai tajuya dasauri tafice cus wani abu yazo mata wuya kaman tai kuka dasauri Saleem yaboye awani lungu ganin mahaifiyar yarinyar tafito tana tafiya dasauri.
Daidai Miemie dake waigowa tana kallon Amirah idanunta yacika da hawaye zata fita itama Marwan yace “Maryam” dasauri Miemie tajuyo bakinta nadan rawa tace “na’am” yawani kalam cika mata idanu saiya juya taje gaban table dinsa da sauri ta sauke kanta kasa takai bayan hannu tana goge idanunta tace “gani” he just wants to help them baisan yazaiyi ba kuma yasan Ammi zata hana saiya bata envelope yace “kiyi transport” dan kunya ma yakeji yace “suyi transport”kasa karban kudin Maryam tayi tace “La munad…..” wani kallo Marwan yamata da batasan sanda takasa karasa maganan ba tasa hannu ta amsa, tama rasa mezatace tace “Allah amfana Yaya” saita juya tasake kallon Amirah saita mata waving hannu alamun bye, itama tafice duk Saleem na kallonsu taje tasami Mamanta awaje suka wuce, ahankali yadafe kansa yace “what’s wrong with me Man? Why am I so interested in mad girl”?
EPISODE 2️⃣2️⃣
Fitowa yayi daga lungun yataho office din Marwan, instead of yayi knocking saiya bude kofan kai tsaye idanunsa fix on Amirah da kanta ke kasa tana wasa da duka hannuwanta hulanta yadan zame baya kadan gaba gaban kitson da aka mata yafito, sai jelan kalaba daya yafito ya kwanta awuyanta har zuwa bayanta, tayi wani irin kyau kaman ka saceta ka gudu, dago kansa Marwan yayi jin an shigo office dinsa ba knocking ba sallama yaga Saleem ne he look sick but ya tsare Amirah da idanu da kaman batamasan yana wajen ba, abu yaji ya tsaya masa azuciya yanda yake kallonta, hakan yasa yamike tsaye yakalli Amirah da kanta ke kasa yace “let’s go” kallonsa Saleem yayi Marwan bai kallesa ba, wlh jiyake kaman zai haukace sabida Amirah abu kaman anmai asiri, ahankali yace “can i talk to her please Doc?”Wani kallo Marwan yamai zaiyi magana amman sabida Amirah saiya kasa kawai yabude kofa daidai Nurse Nucy tazo wajen yace “take her to her room please” dasauri Nurse tace “okay Dr, let’s go” takai hannu zata kama Amirah, wani ihu Amirah ta tsandara zata fada jikin Marwan yadan koma baya strictly yace “follow her nace” ahankali tajuya tabi Nurse kana ganinta kasan she’s not happy saiya dawo office dinsa yamaida kofan office din yarufe, yashigo zai wuce yaje yazauna sai Saleem yakama hannunsa ahankali yace “Marwan wlh I’m serious I lov…..” Marwan bai bari yakarasa maganan ba yace “menene yarjejeniyan damukayi ni da kai before I admitted you? You can just go around and be trying to talk to my patient da haka muke bari maza suyi ai da yanzu asibitin yayi loosing integrity nasa, can’t you see that she’s sick? Bakaga abinda tayi just now ba? What are you trying to do? Ka tsorata ta?” Asanyaye Saleem yace “amman ai zaka iyasa ta dinga yarda dani kaman yanda kasa tabi nurse din chan zaka iyasa nima ta yarda dani” wani kallo Marwan yamai zaiyi magana sai ahankali Saleem yace “I love her Marwan!!!” Wani kalan bugawa kirjin Marwan yayi, wlh takardu yake shirin dauka amman saida yazubar dasu saiya duka dasauri jikinsa yahau rawa yana daukan papers din yana kokarin controlling kansa, Saleem dabai lura da komiba yasami waje yazauna kan kujera yayi shiru cikeda damuwa yace “I know you might not believe me but wallahi wallahi I love her, you know this Marwan, Tunda nake bantaba soyayya ba, bantaba ganin wata inaso ba wlh, but this girl I saw her once shima by accident nazo wajenka a office shikenan, the moment na kulle idanuna ita nake gani, what’s funny is ko sunanta ban sani ba ma, I know nothing about her, I know she’s sick but I just don’t care, I really, really just love her, imagine I’m in this hospital nasa ka kwantar dani just because of wacce nagani for just few seconds, I don’t know what’s going to happen but please Marwan help me kaji, I want to marry her, I don’t care about batada lafiya or wani abu ni ko kanjamau takedashi ina sonta ahaka and I want to marry her, I want to make her my wife, please Doc Bro make her talk to me nasan this is not our agreement, I know, I just want her ko hi ne tacemin ko zuciyata taji sanyi please” yayi maganan yana kwanciya akan dogon couch din yana kallon saman dakin, Marwan da tuntuni yake aduke yamike tsaye da kyar, yanaji kaman zuciyansa zai fito daga kirjinsa sabida yanda yakeji, har wani duhu duhu idanunsa ke masa wlh, tashi zaune Saleem yayi dasauri saiya mike tsaye yazo inda Marwan yake jin baice komi ba gashi yanaji kamna zai zare, yakalli Marwan daya sauke kansa kasa yana hade haden wasu takardu a file, saiyakai hannunsa yakama hannun Marwan ahankali yakai saman kirjinsa yace “Marwan kaji yanda kirjina ke bugawa, I have no one but you, I don’t have someone like Mami in my life dazan gayama matsalata take sona har zuciyanta and she will see to it nasamu solution to my problem no, nataso a hannun Matan Yaya na wacce she doesn’t care about me, I have no one to tell Marwan, you’re all I got, please help me, I really, really love the girl, wlh, wlh ina bala’in sonta” ahankali Marwan yadago idanunsa dasuka dan kada kadan ya kallesa amman yadake sosai bazaka taba gane halin dayake ciki ba, cikeda karfin hali yazubamai idanu, wlh saiyaji yabasa tausayi, baitaba ganin Saleem suffering and struggling like this ba plus he looks very very sick kaman harda withdrawal syndrome ma kedamunsa na alcahol, ahankali yace “why are you putting me in a very tight spot Saleem why? I’m a Dr here I’m not meant to be arranging meet and greet na patients dina suyi soyayya, soyayya can be dangerous for masu matsalan brain especially if it sour saiya kara juya kansu, to be on a safer side we don’t welcome it, why Saleem? All my patients are under my care and watch why are you making me do this eh? Why me”? Ahankali Saleem da muryansa yayi rauni sosai kaman zai mai kuka , yace “sabida nasan duk duniyan nan you’re the one person dazan iya kira dake sona tsakani ga Allah dudda baciki daya muka fito ba! Nasan babu abinda bazaka iyamin ba, idan is against law na asibitin muyi soyayya komu kebe I saw her parents sunzo dazu, stand for me lemme inaso naga iyayenta na nemi aurenta, I want to marry her Marwan!” Yayi maganan daidai Abba na sallama tareda knocking yana bude kofan office din dan tunda aka kwantar da Saleem baizo yadubasa ba, karaf maganan a kunnensa, ya tsaya jikin kofan yace “you want to marry wace Saleem?!”.
EPISODE 2️⃣3️⃣
Dukansu juyowa sukayi suka jin magana da muryan Abba, da ace any one of them zai lurada Marwan hatta yanda numfashinsa ke fita ya chanza he started breathing kaman wanda is about to faint, dukansu babu wanda ya iya magana ganin Abba, tura kofan Abba yayi yashigo office din yana gyara babban rigansa dake jikinsa dayasha aiki, yataho har zuwa wajen table din sai yasa hannunsa kawai yakama Saleem yajawo hannunsa Saleem yabiyosa dan ba karfi ajikinsa ma, cikeda so dan wlh Abba na son kanninsa ba kadan ba yace “Abubakar Saleem mekace just now”? Tsare Abba yayi da idanu still baice komiba, Abba dasauri yace “kanason kai aure naji kace?” Gyadama Abba kai yayi yana lumshe idanu yabude, Abba baisan sanda yace “Alhamdulillahi Rabbil Alameen” yasake kallonsa yace “wacece yarinyar dakake so ka aura? Yar wani gida ne”? Shiru Saleem yadanyi saiya kalli Abba muryansa ya kwanta sosai kaman batasa ba yace “Abba nima ban santaba, rannan danazo nan wajen Marwan na ganta”yadanyi shiru saiya kalli Abba yace “the only reason nazo hispital dinnan sabida na amshi katin Marwan ne dan banda kudi, ina bude office dinnan na ganta and my heart skipped for a moment” yayi shiru all memory na Amirah da abinda yafaru rannan na dawomai kaman yanzu ne akeyi, asanyaye yace “Yaya wlh itan dana gani yasa nace a kwantar dani, for the first time naji sense of responsibility, naji I want to be a better person for her, I really want to let go of my bad life and set up a good one and become responsible person for wacce nakeso” Abba dake kallonsa yace “da kyau Saleem very good”Abba yace “wacece? Nurse ce ko likita?” Dan lumshe idanu Salesem yayi yace “Yaya mara lafiya ce itama anan, i don’t even know her name” Abba ya tsaresa da idanu sosai kafin yace “Saleem duk wanda ke cikin facility nan idan ba Dr ko nurse, ko wani ma’aikaci ba it only means ko yan shayeshaye kokuma mahaukata koba hakaba”? Dan ijiyan zuciya Saleem yasauke yace “Yaya ko gurguwa ce ni ita nakeso, I don’t care about her condition Yaya, ita nakeso ka auramin!” Saleem yafada adan zafafe dan he’s damn serious he’s not even ready ya saurari duk wani wanda zaice mai mahaukaciya ce, menene menene ko matatta ce ba mahaukaciyaba yanason abinsa,
Abba yadade yana kallon Saleem yana nazarinsa, Saleem is a very stubborn yaro tun yana yaro, ayanda take maganan nan idan bai masa abinda yakeso ba tsaf zaiji agari Saleem yaje yayi aure.
Ahankali ya juyo yakalli Marwan dake bude bude folder yana cicciro takardu wanda ko ganin takardan bayayi da kyau tsabagen yanda kansa yadauki zafi Abba yace “Marwan” ijiye takardun Marwan yayi yace “na’am Abba” Abba yace “wacece yarinyar wani ciwo ke damunta?”Abu Marwan yaji aransa yakai kusan 20secs baice komiba chan saiyace “ahhmm bata magana ne haka Abba, rashin son mutane da sauransu” Abba yayi dan jimmm yana tunani saikuma yakalli Saleem dake kallonsa looking very serious, sai Abba yamaida kansa yakalli Marwan yace “yakake ganin za’ayi Son? Do you think with condition na yarinyar zata iya aure”? Wannan karan hannu Marwan yasa yaja kujera yazauna danji yayi kaman zai fadi saiya dauki pen yabude wani file kaman yana rubutu dan baiso yakara making eye contact dako Abba ko Saleem zasu iya gane something is going on with him, da yar karaman murya yace “I dont know Abba is her parents that can decide that” Abba yadanyi jim yana tunani yace “kuma hakane, how about kabani number mahaifinta?” Ahankali Marwan yace “bamu da number mahaifinta” Saleem saiya juyo shima ya kalli Marwan din dayake rubuce rubuce kaman da gaske, Abba yace “to zaka iya bani address na gidansu yarinyar”? Hannu yasa yadauki file na Amirah dake kan table nasa saiya mika ma Abba batare daya dago kai ba dasauri Saleem yamike yasa hannu ya karbi folder, hannunsa har rawa yake tsabagen kosawa, yabude folder Amirah, the first abu daya gani was sunan Aminatu so is that girl dayaga file nata a dakinsa rannan itace oh what a destiny.
Dasauri yawuce address din yace “ga address din Yaya ka dauka saikaje ka gayama Babanta” karba Abba yayi yana karanta address din yace “nasan layin nan sosai ai, zan nemi mahaifinta in sha Allah kam” saiya rufe folder yaba Saleem, daidai pager na Marwan na ringing dasauri yamike batare daya hada idanu dasu ba yace “Abba bari naje inada patients” Abba yace “to, to, toh kaje nima bazan wani jimaba zan tafi” Dasauri Marwan yayi kofa yabude yafita.
Juyowa Abba yayi yakalli Saleem cikeda so yace “Saleem kasan abinda kakeyi kuwa? Kasan menene auren wacce batada cikakken lafiyayyan kai kuwa? Don’t just think of now? Think about your future kids da sauransu, are you sure”? Ahankali Saleem yace “Yaya nizan zauna da ita ba wani ba, yaran kuma nawane, ko gurguwace inasonta ahaka, idan kuma wannan ma bazaka tsayamin ba zan fita na nemi wayanda zasu tayani neman aurenta” Saleem yayi maganan cikeda rashin kunya da rashinji, Abba yayi shiru yana kallonsa yazaiyi maraya ne Saleem, kuma amana, dan kallon Abba Saleem yayi jin yayi shiru ganin fuskansa yanuna baiji dadi ba saiyace “I’m sorry Yaya, this days the only thin danakeyi is tunani, mesa zan kamu da son wacce ko sunanta ban sani ba banda yanzu danaga folder ta, soyayya magani ne and she can be fine, I sincerely love her and I will take care of her, Abba she’s the most purest girl aduniya, she’s like a dewdrop, very clean, fragile and pure” Abba yayi shiru yana kallonsa kaman ba Saleem ba ahankali yace “shikenan I will meet mahaifinta this weekend, ya jikin naka”? Ahankali yace “fine” tashi Abba yayi yace bari naje toh.
Abba nafita yasake bude file din yana dubawa yana karance karance.
Marwan na fita wani Dr daya gani yaje yatayasa duba patient din yafito da sauri yawuce motansa yabude yashiga yarufo thank god motan tinted ne babu mai ganinsa, glasses yacire da sauri yana wani irin nishi kaman mai asthma kirjinshi namai zafi, Allah yasani shi baisan takamaiman meke damunshi ba, is against ethics na profession nasa wato likita ya tsaya yana soyayya da patient nasa, patient dinsa is under his care, why would he harbor love feelings towards yarinyar da bamatasan menene love ba or understand menene so. Shi baisan ko sonta yakeba that’s one, menene toh numfashinsa ke nema ya tsaya sabida Saleem ya nuna yana sonta zai aureta ahaka? Why is he feeling kaman zai mutu? Is he truly in love with Amirah? How? Why? And his brother too is inlove with her! Ya runtse idanunsa, daidai wayansa yahau kuka, ciro wayan yayi yana maida glases nasa ganin Ya Ammah ce saiyaki dagawa harya katse, wayan yashiga ringing Mami ce this time hakan yasa yadauka kafin yayi magana Mami tace “kana ina Son is time for the meeting” dan jim yayi saiya kalli agogon hannunsa, murya chan kasa yace “Mami is already time for juma’a daga masallaci sainazo” ahankali Mami tace “toh shikenan Allah kaimu lokacin, meya sameka why is your voice so down”?Ahankali yace “kaine kedan ciwo” Mami tai shiru kaman bata yarda ba tace “kadawo gida kasha magani ka kwanta” daga background din yaji muryan Farida tana Mami I want to talk to Uncle M, wayan yacire yasa a speaker ya ijiye kancinyasa Mami tace “ga Farida zatai magana dakai” ahankali yace “okay” yanajin muryan Mami tana cewa fitinanniyan yarinya.
Farida tai dariya tana daukan wayan ashagwabe sosai tace “Uncle M” ahankali yace “Anty F”strictly Marwan da muryansa bata fita da kyau yace “I’m at work banson shirme so what’s the matter?” Tafiya tashigayi he could feel tafiya take yaji karan tarufe kofa ahankali tace “cikina ke ciwo and I took maganin nan is not stopping” kawai saita sakin mai kuka yayi shiru, saiyasa hannu yadauki wayan yacire a speaker ya kara a kunnensa ahankali yace “ask Faiza to make tea for you I will come back soon saina miki allura okay, stop crying ki kwanta and rest” Gyadamai kai tayi tace “ohkay” katse wayan yayi kansa na sarawa, yakai 10min ahaka sannan ya kunna motan yaja nasallacin juma’a yatafi.
EPISODE 2️⃣4️⃣
Yaune rana na farko dayake zaune yanajin hudba amman zuciyansa zafi yake masa kaman yayita kuka haka yakeji, sai kawai yafara kiran sunayen Allah hakan yasa yadanji natsuwa, shi baimasan sanda yafara sonta ba? Baisan mesa yakesonta ba? Amman jiyake kaman zai mutu sabida what ever is happening, ahaka akai salla aka idar sannan yafito yana tafiya ahankali yashiga motan sa yaja zuwa gida, horn yayi Musa yabude masa gate yakarasa yayi parking
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 16