Share this page
you disrespect my wife? Ba ke kikace zaki girki bakiyi ba kuma kikahau zaginta agaban jama’a on her daughter’s wedding day, ke maisa bakida mutunci, you’re a very very useless woman saisa kika haifi that useless, foolish, dumb headed girl dinchan!” Wlh zagin daya mata ko kadan baimata zafi ba, amman na Amirah yamata zafi da ciwo arai. Faduwa gaban Ammi yayi tadan kalli kofa cus tasan the way fada da ihu ke triggering condition din Amirah gashi daman bawai shiri suke da Babanta ba dan baya gamaciji da ita, cikeda damuwa da dan sassauta murya Ammi tace “Daddy dan Allah kayakuri kadena daga murya Amirah na falo kasan ba ishashen lafiya ne da itab….” Tasssss! Yadauke Ammi da mari mai zafi kafin Ammi ma tadawo hayyacinta yasa duka hannayenshi ya hankadata ga ruwan wanka dake kafanta jikake tasss Ammi tafadi akasa sosai, Daddy na huci sosai yace “nikike gayama maganan banza? Sabida mahaukaciyar yar da kika haifo bazanyi magana dake ba? Who do you think you’re? Are you telling me how I should behave because of that dumb mental girl”? Dan bude kofan dakin kadan akayi hakan yasa Ammi dataji kaman kafanta ma ya murde tadago kanta takalli kofan shima Daddy yajuyo jin an bude kofa, Amirah ce tabude kofan dakin amman kanta akasa sai yakushin hannayenta biyu take cikeda karfin hali Ammi ta kakalo murmushi tace “Amirah banace idan ina magana da Daddyn ki kidena shigowa ba, go and watch your cartoo….” Cikeda zafin zuciya Daddy cikin tsawa yace “ubanme kikazo yi anan wuce ki koma inda kika fito ja’ira dakikiya, mahaukaciya kawai” ko motsi Amirah batayiba saima cigaba da susan hannunta datakeyi, sosai ran Daddy yabaci azuciye yajuya zaiyi kanta cikin fushi yace “badake nake magana ba kikeyi kaman badake nake ba, nace kibar wajen nan” dudda Ammi naji kaman tai targade akafa amman ganin zaiyi kan Amirah wani karfine yazo mata ta yunkuro tama kasa mikewa tsaye takai hannunta takama hannunsa arude tace “Daddy dan Allah karka tabata dan Allah kayakuri, bawai batajin maganan ka bane, ba cika gane maganan take ba dan Allah kamata afuwa, don’t beat her please” wani kalan juyowa Daddy yayi sabida bakincikin yanda Ammi tarikemai kafa baiyi wata wata ba kawai ya fizge kafansa ya tokare Ammi aciki, Amirah dake yakushin hannunta tawani kalan buga kanta akofa jikinta yafara kyarma, Daddy na ihu sosai yace “maganan banza maganan wofi dani kike magana zanyi maganin ki toh agaban diyar naki nagama dake nakoma kanta tunda you’re becoming bold” kawai yashiga dukan Ammi tun Ammi na daurewa bata ihu tashiga kokawa dashi tanason kwace kanta tafara ihu. Sosai Amirah tadinga buga kanta akofa cikin yar karaman muryanta tana “Ammi……Ammi…Ammi…” dukawa Daddy yayi yakaima Ammi naushi a hanci yace “zan miki jina jina yau ba nikike maidawa karamin mutum ba”wani kalan juyawa kan Amirah yafara, har rotating idanunta suke in circular motion da kanta kaman lizard, plate na tangaran da Ammi tabata abinci dazu tagani anan dakin kawai saita taho ta duka tadauka jikinta ko’ina rawa yake ta taho wajensu dukansu babu wanda ya lura da ita, batai wata wata ba tadaga plate din da duka karfin da Allah yamata na duniya kawai tabugama Daddy plate na tangaren akansa wani irin mugun mahaukacin bugu saida tray din ya tarwatse jikake ratsatsaaa!!!! ihu Daddy yayi sosai, sai jini, yashiga juyowa amman kafin ya idasa juyowa ya zube akasa a sume bayako motsi Ammi tazaro idanunta ta kankare tsabagen tsorata da mamaki, awani irin haukace Amirah ta duka tadauki a piece of broken plate din from kasa mai sharp mouth Ammi da muryanta baya fita tace “Am…..Am….mirah Amirah” Amirah was not her self tai inda Daddy ke kwance a sume zata chakamai kwalbal Ammi takama hannunta, Amirah tai wani ihu “ahhhhhhhhhhh” ta fizge kanta zatai kan Daddy Ammi batasan sanda tasa karfi tai kan Daddy ta tare sa tana bude hannuwanta ba tana goge hancinta dake jini tace “ni zaki kashe ai ba Babanki ba Amirah, maza chakamin kwalban kinji saimu mutu mubar miki duniya!” Dakatawa Amirah tayi amman har lokacin tana rike gam da kwalban jikinta na rawa sosai tana huci, taki kallon Ammi tana wani irin nishi kaman zata shide na zuciya tawani kankame kwalban dayasa jini yafara fita daga hannunta Ammi tamike da kyar tana dingishi tayi kanta, hannunta takama zata cire kwalban amman tayi tayi takasa sai numfarfashi take tana kallon Daddy har lokacin, Ammi tafashe da kuka kawai tarungumeta tana shafa kanta sosai tace “it’s okay, babu abinda yasamen eh Amirah, calm down please, bagani nan ba eh, Ammin ki lafiyanta kalau!” ko kadan she wasn’t calm Ammi tadago tasake kai hannunta kan nata tace “bani kwalban kinajin ciwo” amman ina Ammi takasa karbe kwalban nan daga hannunta tsabagen yanda ta kankame kwalban gam gam. EPISODE 3️⃣ Ganin tana bata lokaci akanta ga Daddy ya suma jini nabin kansa yaşa ta share fuskanta tass sai kawai ta barta tadauki hijabinta dake kan gado tasaka tadawo inda Daddy yake gabanta na faduwa tana addu’a Allah sa wani abu bai samesa ba, taduka takai hannunta ta taba wuyansa taji yana numfashi, zanin jikinta tayaga ta kulle kansa inda ke fitar da jini tadago kanta takalli Amirah dake tsaye tarike kwalban gam that’s very sharp tana kallon Daddy, she’s ready ta chakamai again sabida Ammi ne kawai tadakata, kan Ammi kawai ya kwance tama rasa mezatayi akwai jama’a agidan na biki, tafita yanzu taje tace gashi gashi zasu iya kashemata yarinya, Daddy ya suma ne probably sabida shekaru sunja but he won’t die zai farfado, wayanta Ammi tashiga nema taganshi chan kan gado bazata iya barin Daddy tajeba. Dan motsi Daddy yayi ajikinta yana shirin bude idanu wani asalin ihun rashin kan gado Amirah tayi tayo kansu wani sakin Daddy Ammi tayi akasa tamike tana dingishi dasauri Ammi ta tareta ganin yarta ta birkice tace “ke Amirah, Amirah, Ameemee, bagani ba babu abinda yasameni, if you use this on him zai mutu kınası Allah ya konaki”? Ina at this point ko Ammi ma kaman bata ganeta kokawa tashigayi da Ammi sosai zatayi kan Baba daya bude idanu tasss sabida ihun da Amirah tayi yana ganin jiri jiri yana kallon Amirah da Ammi ke faman rikewa tana daga hannunta zata chakamai wukan wani mugun faduwa gabansa yayi ashedai yarinyar nan hauka take sosai tuburan tuburan dan baitaba ganin outburst nata haka ba yadauka ai haukan shiru shiru da solobiyanci takeyi, ashedai hauka take muraran, aiko dasauri yashiga dadadafa bango dan yanda yakeson rayuwanshi bai shirya mutuwa yanzu ba, yanaso yamike yakasa kafin yaci nasaran tashi, wani irin tura Ammi Amirah tayi tai kan Daddy, Daddy ya bala’in firgita ya kurma ihu yana dingishi yace “wayyyyyo jama’an Annabi zata kasheni, bazaki riketa ba Zainabu” Baba yayi kofa daidai ana bude kofa aka shigo Miemie ce idanunta sunyi ja alamun bacci, dawani irin sauri Daddy yace “riketa Maryama zata kashemiki Daddy” arude Miemie ta tare data biyo Babansu gadangadan tace “Ya Amirah” takai hannunta tariketa ta dasauri, wani tureta Amirah tafara kokarin yi taki barinta, Ammi tafito daga dakin wajen kofa dasuke da kyar, Miemie na ganin Ammi dudda tana fama da rike Amirah saida tace “Ammi meyasameki”? Tahowa wajen Ammi tayi tace “faduwa nayi” Ammi takai hannunta zata karbe wukan tace “bani” wani ihu Amirah tayi taki basu da kyar Ammi suka karbe wukan, rawa jikinta yafara sosai ga jikinta da Ammi taji yadauki zafi kawai takamata ta kankame tace “bani spirit da audugu Miemie kiga” dasauri Miemie tai ciki tafito da audugu, Ammi tai juyin duniya tabude tafin hannunta da kyar tabude tazuba mata spirit a yankan wani irin ijiyan zuciya Amirah tasauke tahau motsi da hannun alamun abin yamata zafi amman babu wani reaction a fuskanta, jin yanda zuciyanta ke bugawa sannan har lokacin jikinta na rawa yasa Ammi tashiga shafa bayanta tace “Amirah, Mirah ya isa kinji, calm down kinji, bani ruwa Maryam” dasauri Miemie tawuce takawo ruwa a cup tazo wajen ta duka tace “Ammi gashi” tai maganan tana kallon Amirah dake jikin Ammi ta manne fuskanta a kirjin Ammi gabaki daya, Ammi ta karbi ruwan ahankali ta ijiye gefenta tasa hannu tadaura saman kanta tace “taso ga ruwa sha” kin dago kanta Amirah tayi, Ammi tai shiru kawai, Miemie tace “tsaya Ammi” tai murmushi tace “Ya Amirah sha ruwa calm down Daddy ya tafi”shiru Miemie tayi tana ganin ko kallonsu batayiba, saita kalli Ammi ahankali, Ammi keeps hiding it bataso su sani but tasani sarai Daddy na dukanta, from fuskan Ammi tadagani tasan dukanta yayi abinda yasa jikin Ya Amirah yatashi kenan hartamai haka, she just hates Daddy, tarasa maisa baya daraja Amminsu. Koda Baba yafito tabaya yazaga yashiga bangarensa har lokacin baya gani da kyau idanunsa dishi suke masa har lokacin kuma jini na diddiga, bedroom dinsa yashiga Maman Baby yagani wajen wardrobe dinsa tana maida zinarenta dan anan take boyewa bai dauka zai ganta a bangarensa ba salati tabuga ganin sa haka tace “Innalillahi wa innailaihi raji’un, hatsari kayi ko mene meya sameka Sweetheart?” Tai maganan tana zuwa wajensa dasauri ta taresa, ahankali yace “bani first aid box” dasauri tace “toh toh” tawuce tadauko tazo ta ijiye bakin gadon while Daddy na karasa cire suit na jikinsa, yazauna bakin gadon Maman Baby tazuba spirit tazo tafara goge jinin goshinsa Daddy yace “aashhh ahankali” dasauri tace “to, amma hatsari kayi ne?” Yana runtse idanu sabida zafi yace “mahaukaciyar yarinyar chan ce!” Chak Maman Baby ta tsaya tace “mene? Wannan jakan yarinyar tamaka haka?” Gyadamata kai Daddy yayi rai abace Maman Baby tace “aiko saina hallakata yau dan kutumar ubanta mijina zata kashemin ni zatasa atakaba, zata gane” Maman Baby tajuya zata wuce dasauri Daddy yarike hannunta yace “kinga zonan karkije yau hauka take sosai idan taje kema ta illata ki fa? Sumewa fa nayi warwas da yankani zatayi fa” Maman Baby tace “mene?”Daddy yace “daman tana haukacewa sosai haka” cikin fushi Maman Baby tace “ni bantaba gani ba, Alhaji gaskiya abin nan yayi yawa wlh bazan iyaba kadauki mataki ina dalili, ka aikata gidan mahaukata mana tabar mana gidan mu yara irinsu ba warkewa zasuyi ba tunda har takai shekaru ashirin da daya bata warkeba kakoga ai ciwon harna abada ne dan haka ka wurgata asibiti ta karasa rayuwanta achan muhututa, hakanan yar wasu zata hallakaka na cikinka basu hallakaba sai wacce bataka ba ina dalili iyye, inada yara ta kashemin kai waye zai zama ubansu, gaskiya taje chan gidan yan uwanta gidan mahaukata” shiru Daddy yayi kaman mai tunani chan yace “banki takiba Giwa amman gaskiya bazan miki karya ba bazan iya kashe kudadena akanta ba kinsan nawane asibitin mahaukata kuwa?” Dasauri Maman Baby taduka agabansa kaman mai kneeling ganin ya yarda da maganan kudi yake tunani tace “tsaya wlh ko sisi bazaka kasheba, ko jiya jiyan nan saida nagani a news cewa NGO na UNICEF sunzo sunyi renovating physciatrict world na Teaching hospital sun kawo kwararrun likitoci sunce zasuyi free komi na 2yrs duk wani mai ciwon hauka zai iya zuwa, project din is about making mahaukatan dake yawo a street sun Sami magani da kulawa, ka kaita wajen ka zubad da ita chan su karata”Daddy yace “are you sure komi free ne dan kwandalata bazai yi ciwo akanta ba Billahillazi” Maman Baby tace “da gaske nake nima ina zan barka ka kashe kudi akanta yoh menene amfaninsa” Daddy yace “shikenan Allah kaimu zan samo kattai dazasu daddauremin ita su dauketa su samin a mota saidai uwarta tamutu wlh amman saita tafi asibitin mahaukata” wani murmushi Maman Baby tayi dan batada burin daya wuce taga Ammi na bakin ciki, yanda Ammi keson mahaukaciyan nan rabata da ita sai yakusan kaita lahira sabida bakin ciki. Har wajajen 2 nadare Ammi bata runtsa ba Miemie harta sulale tai bacci anan kasa a gefensu, Amirah idanunta biyu har lokacin ta kankame Ammi kanta akan kirjin Ammi jikinta yayi zafi sosai, kawai tarikice, Ammi tai juyin duniya yarnan tasaketa amman Amirah taki, yawanci ciwonta yatashi this is how she becomes, lumshe idanu Ammi tayi tashafa bayanta ahankali tace “I am fine Aminatu, kinji Mamana, I am fine wlh, faduwa fa nayi baki gani ba, kuma bawani abu babanki yaminba abu yazo ciremin awuya fa eh, sakeni muje gado ki kwanta” taki sakin Ammi saima kara kankameta datayi, haka Ammi ta barta, ahaka bacci yadauketa ma sabida ta daku a hannun Babansu tagaji. Kiran sallan asuba yasa Ammi tabude idanunta batamasan ya akayi bacci yadauketa ba, kwance taganta kusa da Miemie dake bacci itama dasauri ta tashi zaune tana waige waige jin cingum dinta Amirah bata jikinta, zaune taga Amirah ga yawu na dilalowa daga bakinta she always does this idan tana zazzabi, dasauri Ammi ta taho wajenta ta kai hannunta wuyanta jikinta kaman wuta tace “Innalillahi Amirah, Amirah” amman batako motsi tashi Ammi tayi tana dagata takamata sai bayi ruwa mai dumi kadan tahada tana cire mata kaya Ammi tashiga watsa mata ruwan sannan tamata brush tadauki towel tafito da ita Miemie tagani zaune cikeda damuwa tace “Ammi mukaita asibiti” dasauri Ammi tace “eh abinda zanyi kenan, hadomin tea nabata Miemie” fita Miemie tayi daga dakin, Ammi ta ijiyeta agado tawuce wardrobe vest Ammi tadauka da pant sai wata gown na atampa da hijab, tsaf Ammi tasamata kayan bamata da karfi at all, Ammi ta fe samata body spray, Miemie takawo tea Ammi tace “ijiye tea kizo muyi salla” Ammi tadagata tasa akan dadduma tace “muyi salla” tama kasa tsayuwa Ammi ta zaunar da ita azauna tai sallan, suna idarwa Ammi tadauki tea tadeba a spoon takai bakinta kauda kai tayi takisha Ammi tace “dan Allah kisha Amirah” hannu tasa ahankali ta ture hannun Ammi alamun bataso sai kawai ta kwanto ta kwanta ajikin Ammi, Ammi tadagata ahankali tace “rikemin ita Miemie bari na shirya” dasauri Miemie ta karbeta yau batai musuba, Miemie cikeda so takai cup na tea bakinta tace “Mai dadi nahadamiki fa, nasamiki madara dayawa sha kiji” kauda kanta tayi sai kawai ta kwanto tadaura kanta akan cinyan Miemie ahankali tana lumshe idanu jikinta zafi radau, Miemie tashafa bayanta ahankali tace “in sha Allah zakiji sauki kinji”. Fitowa Ammi tai daga bayin dasauri Amirah tayunkuro idanunta sunyi jajir na zazzzabi, Ammi tace “kwanta ba inda zani” Miemie tace “kwanta Ya Amirah Ammi kaya zata saka yanzu” sake komawa tayi ta kwanta dudda idanunta ba karfi amman sai in Ammi take da idanu, shiryawa Ammi tayi tsaf cikin atampa mai kyau da hijab dinta har kasa tadauki jaka tadaga kasan kayanta taciro wasu kudi 30k, tasaka a jakan sannan tadauki wayanta taduba account nata 10k gareta tai shiru. Saitazo dasauri Amirah ta tashi zaune ganin Ammi, takama Amirah tataso da kyar Ammi tace “samo mana keke Miemie” dasauri Miemie tadauki hijab dinta tace “toh” tafice. Wani maroon hijab mai hula a goge tsaf Ammi ta warware tasakama tana gyara zaman hijab din, yamata bala’in kyau, Ammi na kallon idanunta tace “bari asaka kwalli a idanun nan” Ammi tamika hannu tadauki kwalli tana shirin budewa Amirah ta kifa fuskanta a wuyan Ammi alamun bataso sai kawai Ammi ta ijiye, crocks tasamata pink masu cute charms a sama na spelling din Barbie wanda aikin Miemie ne ita ta mammakalasu, saiga Miemie tashigo tace “Ammi nasami keke muje” Ammi tace “bazaki zauna kiyi karatu ba exam gareki ba”? Dasauri tace “Ammi dan Allah zan biku” Ammi bata ce komiba, kawai takama Amirah da kafa takeja kawai jikinta nadam rawa suka fito Miemie ta kulle kofansu ta taya Ammi suka kama Amirah har kofar gida suka saka ta a tsakiya keken yajasu tana jikin Ammi har sukakai general asibiti wuraren 7:30. Dudda sammakon dasukayi haka mutanen dake wajen sunfi 100, Ammi tasami waje ta zaunar da ita tana share mata baki da handkerchief Miemie ta zauna Ammi tace “bari nabada katinki” tajuya dasauri Amirah takama hijabin Ammi tawani tsandara ihu da saida gabaki dayan GOPD yadauka aka jujjuyo ana kallonsu tawani mike Miemie ma tamike jikin Amirah har kyarma yake yawu na fitowa sosai, sai kawai dasauri Ammi tazauna tana bama Miemie katin tace “kai katin wajen chan Maryam bazata bari naje ba taga jama’a zata fara kuma” dasauri Amirah tawani rukunkumi Ammi sai kallonsu ake, Miemie taje gaban kanta, tabada katin matar dake wajen takarbi katin tabude tace “Aminatu Adamu, what is wrong meyakawo ki ganin likita?” Dasauri Miemie tace “bani bane y’ayatace, gatachan batada lafiya” tanuna Amira dake jikin Ammi fuskanta a kirjin Ammi dake kallon wajen, Matan ta kallosu saita cigaba da rubutu tace “okay meke damunta?” Shiru Miemie tayi tarasama mezatace kawai saita taba kanta ahankali tace “tanada matsalan uhmm amman zazzabi take” tai shiru, Matan takarasa rubutu sannan tabama Miemie katin back tace “likitansu will be here by 9 zaku jira, consultation is free amman zaku biya kudin number” Miemie ta Gyadamata kai tace “okay nawa ne?” Matan tace “ga account counter chan achan zaku biya 5k” gyadamata kai Miemie tayi tace “nagode” Miemie tawuce wajen Ammi tace “Ammi doctor zaizo by 9, ance musai kati achan 5k” jakanta Ammi tabata tace “ciro kudi kije ki saya” 5k Miemie taciro tawuce tabiya tasayo sune number 21 tadawo rike da number, akwai different consultation rooms awajen kusan guda 10, it’s all depends on Dr da akai booking dinka zaka gani cus wasu nata shiga ana jiransu sunesai shiru har yanzu. Suna zaune awajen har 10 Dr baizoba jikin Amirah zafi gadan gadan abin haryasa tafara making some wired sounds, gashi tahana Ammi ko motsi dan batason mutane ta chukuikuye Ammi kaman zata koma cikinta. Wuraren 10 wani arnen mota 2025 Tesla dark blue yayi parking awani parking space da musamman akasa UNICEF PHYSICIANS gawasu special securities dake gadin wajen, security ne yazo dasauri yabude masa kofa yana murmushi sosai yace “welcome Dr M”wani caramel skin color guy ne da zaka iya kiran kalan fatansa fari but ba fari bane and bazaka taba iya kiransa black ba cus he’s not, zaune yana sanye da riga da wando dark brown na Ralph Lauren dasukamai wani irin kyau abinka da mai dan hasken fata, yanada saje mai yawa dake a kwance dayazo har gemunsa duka a kwance sai pink lips that her full and meaty irin asalin real masculine mouth garesa that’s damn sexy, idanunsa na cikin white glasses wanda madubin jiki are very thick kana gani kasan yanada asalin matsalan idanu cus at a glance zakasan glasses din are medicated, dan ijiyan zuciya yasauke he hates Sundays cus outpatient department is stressful her prefers working a inpatient ward, yanada dogon hanci da gira baki cikake, Ya Allah he’s damn cute and skin dinsa is so fresh. Ahankali yafito daga motan yana kallon agogon hannunsa, yanada tsayi da kuma full jiki na d’a namiji kakkarfa kuma kosasshe, security yace “barka da zuwa Dr” gyadamai kai yayi yana janye idanunsa dagakan agogon yabasa car key ahankali, security yayi murmushi, Dr yawuce yana tafiya a nutse, security yashiga motan yayi parking properly sannan yadauki wasu files dake dayan seat din da aka rubuta confidential akai, da sethoscope, saikuma labcoat dinsa da wajen Aljihun akwai rubutun UNESCO Dr Marwan, yafito yamaida kofan yarufe sannan yashiga tafiya dasauri, yana shiga cikin asibitin babban Nurse din tace “Dr Marwan yazo?” Gyadamata kai security yayi Nurse din tace “start coming here according to your number for your vitals, Dr ku yazo” tanuna 5rows of chairs wanda harda nasu Ammi cus sune Dr Marwan zai gani. EPISODE 4️⃣ Nurse din tawuce tazauna tana shouting number 1… Ahankali security yabude office din ya shiga babu kowa a office din, ba datti dudda wannan is just office dayake shiga every Sunday dan ganin outpatient amman dudda haka office din kamshin sa yake, asalin permanent office dinshi yana cikin physiatrics ward, ijiye komi yayi a inda yakamata, office din yayi kyau kaman ba office na asibitin gwamnati ba ga kujera da table mai kyau ga gadon duba patient gakuma another doors guda biyu wanda daya bathroom ne dayan kuma another door ne na shigowa ciki from outside, yana makala labcoat nasa a hanger aka bude dayan door din security yadago kansa kafin ya shigo har kamshin sa yashigo, anatse yashigo cikin office din yabi ko’ina da kallo cus idan yaga datti daya ko kura consultation din dabazaiyi kenan ba yau, ahankali yakaraso wajen hanger security ya matsa masa, hannu yasa yadauki lab coat yana sakawa, security yajuya zai fita batare daya dago kansa ba yana saka boturan rigan cikin muryansa datake murdadda a bit hard, subtle, but still yana nuna masculinity nasa yace “ya jikin Mama”? Dasauri yajuyo saiyayi murmushi sosai yace “taji sauki sosai kaman ba itaba tace na gaidaka” still har lokacin baice komiba sai security ya tsaya yana kallonsa. “Any problem with the job”? Dasauri yace “no no no, wlh inason aikin nan bazan taba mance alkhairin dakamin b….”“tell the nurse I’m seeing 15 patients today I need to be somewhere” ya yanke maganan sa cus bayason godiya kwata kwata shi haka yake, dasauri Security yace “angama Dr” yabude kofa zai fita kaman daga sama ahankali Dr Marwan yace “be good Kamal” dan jimm yayi saiya juyo yakallesa yaga harya zauna yabude files dayazo dashi, murmushi yayi yace “I promise Ya Marwan” yabude kofan yafita, Nurse ta kallesa yadan matso sAbida kar patient suji yace “yace 15 patients zai gani yau” dasauri Nurse takalli wajen gabaki daya patients sunfi 30 wanda suke nasa ba abun ta aikasu wajen wani likita ba cus duk masu matsalan kai ne shine likitan su, inhar bai gansu ba saidai su kara dawowa nextweek Sunday, cikeda takaici tace “wlh Dr Marwan sai ahankali sabida yasan abinda yakeyi ne yake yanga haka haba dan Allah, bayan an gama jiransa sai yanzu yake zuwa, kuma yace patients kadan zai gani” tai maganan tana kallom jama’an tace “number one go inside” tamike itama tana deban files na patient 15 dayace zai gani ta shiga office din tafito. Ammi duk suna zaune awajen suna kallon kofan office na likitan, Miemie takalli Ammi data damu sosai tace “Ammi” kallonta Ammi tayi sai ahankali tace “bakijin yunwa akwai biscuit ajakana kici” murmushi Miemie tayi tace “banajin yunwa Ammi” kusan 10min number one yadauka yafito nabiyu yashiga duk suna zaune awajen patient number 15 yashiga, lokacin kusan 12:20 Nurse din tamike tazo gaban kujerun su ta tsaya tace “ahhhm Dr nada emergency please bazai iya dubaku ba saidai ku dawo next week Sunday” wajen ya kaceme da hayaniya kaman za’a daki Nurse, ran Miemie yayi matsanancin baci wlh, tace “wlh asibitin gwamnati baiyiba ba Ammi especially idan suna dan rage muku kudi ayita muku wulakanci” ahankali Ammi data fara tunanin yanda zatayi Amirah taga likita dan jikinta sai uban zafi yake tace “Miemie rikemin Amirah ina zuwa,” taciro Amirah daga jikinta dako bude idanunta bata iyayi tsabagen zazzabi, Miemie tariketa da sauri Ammi tamike ta tashi dagakan kujeran, one thing is dazaran ba ajikin Ammi takeba tasani, bude idanunta Amirah tashiga yi kadan daidai Ammi takarasa mikewa, azabure tawani yunkuro ta mika hannu zata kama hijabin Ammi tareda kurma wani mugun ihu da saida duka wajen da ake hayaniya kaman za’ayi fada yadauka jikake tsit! Kowa yayi shiru! Daidai Marwan yasa hannu zai bude kofa yafita yaji ihu that’s very sharp mai ratsa jiki hakan yasa ya tsaya chak, saiya juyo yadubi kofan wajen da patients suke anatse yana duba agogon hannunsa. Dasauri Ammi tajuyo tariketa tace “Amirah, ganinan Amirah” wani irin numfashi Amirah takeyi kaman zata shide batada one single karfi, Nurse tabar masu rigima da ita tazo wajen su Ammi dasauri hannunta takai ta taba goshin Amirah wanda Ammi da Miemie suka rike saida ta tsorata jin zafin da jikinta yake tace “ina zuwa Hajiya ku riketa da kyau” saita mike dasauri tawuce office din tai knocking tareda bude kofan, tsaye ta gansa dab da kofan kafin tai magana yace “who scream like that?” Dasauri tace “wata yarinya ce Dr, her condition is really bad, dan Allah kadubata Dr, wlh Mamanta tabani tausayi, yarinyar is running temperature and I think she’s non verbal cus Maman and the sister do most of the talking” dan shiru Dr Marwan yayi sai yasake kallon agogon sa yace “okay” dasauri nurse din tawuce

Chapter 2 of 16