Share this page
not bad for government hospital o, hannu yasa ya karba da kansa ya kalli abincin saiya bata yace “take this” kin cire hannunta daga baki Amirah tayi takima kallonsa sai cin yatsu datakeyi tana wasa da kafafunta, he knows bazataci ba bataso, saiya juya yaba Baaba yace “Baaba akwai flask na abinci a office dina za’adan taimakamin dashi” Umma tace “toh Dr”tawuce tafita. Ahankali Marwan yasa hannu a aljihun lab coat nasa saiya ciro leda na new dogon black socks mai dan kauri yabude yacire safan tareda mikemata yace “take put this on a kafanki, always wear sock daga yanzu” left hand nata wanda shine akan cinyanta takai tamikamai still bata kallesa ba, Marwan yace “no bani hannun dama not left” cire hannunta tayi daga bakin tamikamai duk saliva a jiki, tsare hannun yayi da idanu saiya saka hannunsa a aljihun yaciro handkerchief dinsa, ahankali batare da skin na hannunsa yataba fatar hannunta ba yashiga share mata yawun daga hannunta, gently Amirah tadago kanta tadan kallesa da fararen manya manyan idanunta, kawai Ammi ta tuna anytime taba Ammi hannu idan akwai datti ko ruwa ko kasa ko yawu a hannunta sai Ammi tafara sa tsuma ko wani abu ta share hannun tass kafin tabata abinda zata bata, sosai take kallonsa especially glasses dake idanunsa, da lips dinsa dasuke pink yirrr ga kamshi mai bala’in dadi dayakeyi dake kwantar mata da hankali. Tass Marwan ya goge mata hannun saiya saka safan akai tareda dago kansa karaf hada ido yayi da Amirah dasauri Amirah ta maida kanta kasa abin yadan basa mamaki ganin takallesa, bude safan tayi saita shiga sawa a birkice wajen diddige na saman kafa instead of yazauna a kasa zata saka dayan, cikin tattausan murya Marwan yace “wait!” Tsayawa Amirah tayi batare data kallesa ba, hannunsa biyu yakai kan kafan data saka safan, ahankali yakama fatar safan without touching her sai yayi adjusting ya daidaita safan, kaman yana magana da Baby sabida how soft he’s da ita yace “jashi sama toh” ahankali Amirah taja safan sama, Marwan yace “sa dayan” saka dayan tayi same way, yasake gyara mata saiya koma yazauna yabude file nata sai yayi rubutu awani fresh paper, saiya dago yakallate tamaida hannunta baki, a hankali yace “I will ask you some questions inhar kin bani amsa kinyi duk abinda nace baki mana rashin ji ba zan kawo miki Ammi gobe kin yarda zakiyi”? Gydamai kai tayi tana cin hannu tana kallon waje daya, gently yace “stop eating your fingers” ciro da hannun tayi daga baki ta ijiye akan cinyanta, saita shiga ninninke yatsun nata all together Marwan na kallonta saiyayi rubutu ahankali yace “kinsan sunanki”? Gyadamai kai tayi, his eyes fixed on her yace “gayamin sunanki naji” dan bata lokaci tayi kaman mai tunani idan zatai magana murya chan kasa that’s very tiny and slow suna kiran term din a psychiatrict world da bedroom voice idan baka natsu bama bazakaji me zatace ba, murya very very kasa Amirah tace “A…..mirah!”. EPISODE 1️⃣5️⃣ She speaks very low with a very gentle tone da zaka dauka a year old baby ne tai magana, muryanta bala’in dadi, soft charming and adorable da baby yanda zatai magana da zuciyanka bazai amsa ba, sosai Marwan ke kallonta tai maganan tana wasu wired wasanni da yatsunta bazama kace itane tai magana ba, kaman badaga bakinta maganan yafito ba, rubutu yayi yacigaba da kallon gesture datake making, calmly yace “Amirah sunanki but rannan Ammin ki tafadamin asalin sunanki, kinsan asalin Sunanki?” Shima magana yake mata calmly and very gentle baiso yadaurama kanta abubuwa dayawa, gyadamai kai Amirah tayi alamun eh batare data kallesa ba, Marwan daya kafeta da idanu bayako kyaftawa yace “gayamin, menene asalin sunanki” wannan karan maganan ma fitowa yayi daga bakinta like whispering, kaman irin tafadi ma mutum magana a kunne dinnan, tace “Ameenatu!” Wlh bugawa kirjin Marwan yayi dum! Dan shiru yayi ya lumshe idanu kadan taredakai hannunsa yadaura kan goshinsa sannan yazare tareda bude idanun, why is he feeling like this towards this patient? Yasake dago idanunsa yadaura akan fuskanta yana kallonta, wasa take da hannayenta tanadan motsi da kafafunta suma, dakewa Marwan yayi ya danne duk wani abu da zuciyansa kemai yace “dake da waye da waye agidanku”? Tafin hannunta daya shiga zufa ta share a cinyanta saita daga duka hannunta biyu zatakai baki saita tuna abinda yace dazu yahanata wasa da yatsunta tashiga yi saita kalli gefe kaman bada ita akai magana ba, chan da yar kankanuwan muryan tace “Ammi, Miemie da Amirah ne agidan muuu” taja muu din like a baby tai shiru sai kawai this time takai hannun nata baki tafara ci tana kallon gefe, Marwan ya tsaya yana kallonta kirjinsa na bugawa dum dum dum yana maimaita kalan sigan yanda tajero sunansu Ammi, Miemie da Amirah ne agidan mu, irin yanda yara ke gayamaka waya da waye gidansu dinnan sai Marwan yayi circling Babanta cus bata ambato mahaifinta ba, daidai lokacin akai knocking akan shigo Baaba ce da flask dayace takawo mai tace “gashi Dr” nuna mata inda ya ijiye ruwa da magani yayi saita wuce ta ijiye tajuya tafita, sai yadauki wani empty blank paper yarubuta Ameena boldly saiya daga paper yabata yace “take” hannunta datake wasa dashi tazare zata bashi na haggu batare data juyoba saita basa na dama yasa mata takardan ta amshi paper tana kallo yace “mena rubuta anan?” He wants to know idan ta iya karatu koda kadan ne, ahankali Amirah tace “Ameenah” murmushi Marwan yayi yace “good job Ameenah” wani sanyi taji a zuciyanta kaman an goga da kankara yanda yace good job Ameenah, saiya mikamata hannu alamun tabasa yace “kawo” basa tayi ahankali tana kallon agogon hannunsa, saiyasa hannunsa a aljihu yaciro chocolate na cabry diary milk yamika mata yace “that’s all for today take your reward” chocholate din ta kalla sai dawani irin sauri tasa hannu ta amshe, zata bude yace “wait, wait kisha magani kici abinci then chocholate” maganin yakawo yana bude ruwa, yawanci su ne suka ba patient magani da kansu a gidan mahaukata wannan ka’ida ne dan patients akwai wayau basashan magani, gently Marwan yace “haaaa” kin bude baki Amirah tayi dan batason magani ko kadan takai hannuwanta biyu tadaura akan fuskanta tarufe, abin yaso basa dariya, saiya mika mata hannu yace “bani chocholate dina tunda bazaki sha magani ba” dasauri tacire hannayenta dake kan fuskanta da chocholate din ke jiki taboye chocholate din abayanta tana makemai kafada batare data kallesa ba, Marwan yamata wani kallon mamaki da ace this girl is very fine kalan tsiwan dazatayi ko, ataushashe kaman mai lallashinta yace “okay tunda bakiso na amsa chocolate din open your mouth kisha magani, ko bakiso nakawo miki Ammi”? Ahankali tabude baki jin maganan Ammi, dan bugawa zuciyansa yayi sabida yanda tabudemai bakinta that is very clean, hakoranta yan kananu with her very pinkish lips and tongue, maganin guda biyu yasamata abaki tareda samata ruwa ta zuka ta hadiye tana lumshe idanu tai ahhhh, ahankali yace “karkimin amai” yadan kalleta to be honest bata iya expressing happiness ko sadness ko tsana ba, she hates magani tasha taji ba dadi but fuskanta is just d way it is, rufe goran ruwan yayi yace “open your mouth nagani cus you patient are kinda sneaky now adays” bude bakinta tayi ya kalla saiya wuce wajen warmer da Mami tabasa abinci saiya bude, chips ne da eggs da pepped chicken and plantain saiyasaka spoon yazo wajen yabata yace “ea….” Kafin yama karasa magana yaga takawo hannunta takarbi kulan hannunta nataba nasa takarba da sauri tadaura akan cinyanta saitasa hannu tafara cin chips din da egg da plantain, tsayawa Marwan yayi yana kallonta saiya sa hannu yadauki bottle water din yabude yazo wajen ya ijiye mata a gefenta, sai kawai yadena kallonta yabude folder yashiga rubuce rubuce saiya rufe yasake kallonta she’s still eating comfortably kaman batasan da mutum awajen ba, sai yadan sauke ijiyan zuciya since she’s eating today unlike jiya, and yau she’s not running temperature, yajuya zaiyi kofa dawani irin sauri Amirah tamike tabiyosa hannunta daya rikeda chocholate dinta dayan rike da kulan abinci gabanta na faduwa hankalinta natashi bataso yabar inda take, dakatawa Marwan yayi ya tsaya jin tabiyosa yajuyo da sauri yakalleta tana tsaya dab dashi kanta akasa ga kulan a hannunta da chocholate, kaman zata shiga jikinsa ayanda take dab dashi yayi dan jim saiya juya yawuce yace “muje kici abinci” juyawa tayi itama sum sum yanuna mata gadon taje ta zauna tasake tacigaba da cin abincin yana tsaye yana kallonta, she has a very very good appetite dudda bada sauri takecin abincin ba but she’s eating well, tagama takama naman duk tanaci, abinma dariya yaso basa saiya dauke kai yaciro wayansa yana dannawa dan ita kawai yake jira, kadan tarage a abincin tadauki ruwan tasha ta ijiye saiya dago kansa yakalleta ganin tagama kanta akasa saiya maida wayansa aljihu ya matso dab da gadon yasa hannu yadauki gora sai yarufe ya ijiye a gefe yadauki flask din yakalli dan naman karamin data rage, saiya sa hannu yashiga picking abincin data zuzzubar a gadon, ahankali Amirah tadan dago idanunta ta kallesa yana wani irin sanyi takaraji acikin zuciyanta kaman an zuba kankara, rufe flask din yayi ya ijiye ya kalleta hada idanu sukayi dasauri Amirah tadauke kai, baice mata komiba yawuce wajen bayi dasauri tamike tabiyosa yana bude kofa tabisa yajuyo ya kalleta saiya kunna tap yace “come wash your hand” bude tap yayi saitazo tasa hannunta akasa tana wanke hannunta saita bude baki hakoranta suka fito tai wani clapping hannunta under the running tap ruwan yawani tawarwatsa har fuskan Marwan ya tsareta da idanu ahankali yace “wasa da ruwa nace kiyi” dasauri tajuyo ta kallesa sai takai hannun data wanke zatasa abaki yace “don’t, clean your mouth” goge bakinta tayi, yace “wash your hand again” wanke hannun tayi, saiya bude kofa yace “let’s go” ahankali tafita yafito shima, wani takalmi canvas ne wanda shine general shoes dasuke bama patient nasu fari ya dauko a drawer dakin, saiya duka ahankali gabanta agaban gadon, Amirah ta kallesa, bude takalmin yayi yace “put your leg” sa kafanta Amirah tayi saiya samata takalmi da kyau ya kulle igiyan sai kallonsa take kanta trying to put things together, he’s just like Ammi, he is her second Ammi sabida yanda yake kula da ita, same thing da dayan kafan yayi ya kulle, yakalli hulanta ya zauna akanta sosai, yace “let’s go” saukowa tayi yadan tsaya ya kalleta fully kayan looks free ajikinta sai yajuya kawai yawuce yayi kofa tana biye da shi abaya suka fito, lobby yakaita yau drawing a painting ake koya musu, chair yanuna mata yace “sit” zama tayi Malaman na kallonsu da other patients, Malaman takawo mata new board da pen ta ijiye tace “here you go” anatse Marwan yace “I want you to draw anything dakika tuna, stay here I will come back anjima kadan karki biyoni” yafada strictly saiya juya binsa Amirah tayi da kallo zuciyanta yashiga rawa sosai har saida tadaina ganinsa sai kawai takifa kanta a table din tai lamo kaman marainiya tareda lumshe idanu. EPISODE 1️⃣6️⃣ ** Wuraren 1:30PM Saleem yashiga bude idanu shima sabida knocking kofan dakin da Mami tazo tanayi da kanta ne, “Saleem maza atashi lokacin sallan zuhur yayi” da kyar kaman zaiyi ihu ya juya, sai kawai Mami tashigo dakin labulen windows daki tabude dakin yayi haske abinda baiso kenan yabude idanu yatashi zaune kaman zai mata kuka yace “Mamsssss” dakuwa Mami tamai tace “wuce kaje kayi salla Saleem kafito ina jiranka magana zamuyi” dan kallonta yayi kadan saiya tashi ahankali yawuce bayi Mami tawuce tafita daga dakin. Wanka yayi yafito da gangan yakara shiga closet na Marwan yanabin kananun kayansa da kallo, they’re to decent for his liking hakanan dai yazaro wani Zara jean blue da farin shirt na H&M yasaka, yadauki p-cap yarike a hannu yafito yana baza kamshi saiya shimfida dadduma yayi salla yawuce gadon yadauki wayansa yana dubawa miss calls ne dayawa kuma duk na abokan sa ne, message din David yaduba a watsapp yace “Johnson street” yasan abinda abin ke nufi hakan yasa yawuce yafita daga dakin tundaga staircase yake kwalama Mami kira. “Mams, Mams” Mami dake kitchen tare da masu aiki tace “oh ni jama’a Saleem gani nan fa” fitowa tayi daga kitchen takallesa tace “zokai breakfast” baiyi musu ba yawuce yazauna kan dinning wayansa na ringing yasa a kunne yana magana Mami na zubamasa abinci, fried rice tasamai da tea da kaji sauke wayan yayi daga kunnensa yace “you are the best cook Mams” zuwa bayansa Mami tayi kai tsaye yaji hannunta akan kunnuwansa dasauri yakalleta Mami tahararesa tace “kace wani abu wlh saina rankwashi kanka bani dan kunnen nan, ko su Faiza naba suna sawa zaka sami lada, these don’t belong a kunnenka eh Saleem” yanajin nauyin Mami sosai sama da yayan nasa ma, cire an kunnayen tayi takai hannunta ta kwance sarkan shima ta cire kaman zaiyi kuka yace “Mamssssss” zama kusada shi tayi ta tsaresa da kallo tace “Saleem!” Kin magana yayi yaturo baki yana jan abincinsa yafara ci, Mami ta tsaresa da kallo, tace “Saleem wai bakaga mutuwa ake ba yau mune gobe bamu bane, menene amfanin muna sabama Allah da gangan with the little time we have left? Kayi islamiyya kayi boko, d same school dakayi shi Marwan yayi, amman baka aiki da abinda aka koyar daku a islamiyya, we all love you so much we want the best for you mesa kake haka”? Muryan Mami yadanyi sanyi, saiyadan kalleta yace “Mami don’t do the sad voice here please just tell me mekikeso”? Shiru Mami tayi tana nazarinsa, all magananganunn data gamayi ko tabasa basuyi ba wlh kawai dan muryan data chanza ne bai so Abinci ma yakeci abinsa, ahankali Mami tace “aure nakeso kayi Saleem!” Ruwa yakai bakinsa amman saida ya kware yahau tari yana buga kirjinsa yakalli Mami yace “wait wat? Mams mene? Aure? Me?”Ya yunkura zai mike Mami takamasa ta zaunar tace “zauna ban gama magana dakai ba” kaman zaiyi kuka mata dan jiransa ake yace “Mamii please jirana akeyi fa”Mami tace “fitanma saina hanaka” dasauri yace “woh woh woh nooo Mams please my friends are waiting for me” Mami tace “inaso kafito da mata kai aure kaji Saleem” dan dariya yayi yace “seriously Mami”? Sai yayi dariya daya lobar da dimples nasa ciki yace “Mami I hate marriage aure damuwa ne please banso there’s nothing a aure” Mami tace “okay shikenan zanko bar yayanka ya auro maka kowace mata ne yaga dama” zaro idanu Saleem yayi yace “wat? Mams what’s going on”? Cikeda hikima Mami tace “yayanka yace zai samo kowa yaga dama yamaka aure, it took me the whole night to convince him karya maka haka ya banni nizan maka magana kafito da wacce kakeso da kanka dan zamanın nan ba’a yima yaro auren dole saisa na kiraka ina maka maganan amman tunda nima baka daukeni serious ba zan barsa yamaka kome yaga dama” dasauri Saleem yace “no no nooo Mams please, you know how that old man can be trouble ni zaije ya zaboma mata yanda yake jik haushin nan nawama ai wata chan zai dauko a kauye ya auromin”Mami tace “ashe kasan yayanka” dan shiru Saleem yayi yarasa mezaice, Mami ahankali tace “baka da budurwa duk yammatan ka Saleem” wata yar dariyan iskanci yayi Mami batasan tsakaninsa da su ci bane kawai yace “banda shi” Mami tace “to kafara nema zan rokesa na lallabasa yabaka nan da one month” Shiru yayi baitaba sanin zancen aure can make kansa yaji yayi so blank ba sai kawai ya gyadama Mami kai daidai ana sake kiransa yamike da sauri yace “bye Mami I’m taking your car keys” yadauki key motanta yafice harda dan gudu Mami tabisa sa kallo tana karamai addu’an shiriya. Motan Mami yashiga duk iskancinsa hakanan yana tsoron Abba yayomai aure dan yasan karamin aikin yayansa ne wlh ayanda yakejin haushin nan nasa, shi kawai akyalesa abarsa yayi rayuwansa abinsa, taka motan yayi da gudu dan sauri yake he needs to make a quick stop before yaje wajensu David….. Takai kusan 30min ahaka sai tadago ta kalli paper drawing din, saiya dauki pencil tashiga zane, tanatayi ita kadai, Malaman su ne tazo wajen ta tsaya takalli abinda Amirah ke zanawa saitai jim saita wuce cus zata iyama Amirah magana taki cigaba, chan saiga Marwan yataho wajen, kamshinsa kawai Amirah taji saita dakatar da abinda takeyi takai pencil din ahankali bakinta batare data dago kanta ba, kirjinta sai bugawa yake, tahowa yayi wajen kai tsaye yasa hannu yadauki paper datai zane aciki yakai one minute yana kallon abinda ta zana saiya nannade yarike a hannu yace “let’s go” dasauri Amirah ta tashi sai yayi gaba tana binsa abaya da sauri kanta akasa da pencil da hannu duka abakinta tana binsa yabude office nasa yajuyo kalleta yace “shiga ki zauna ki jirani” shiga tayi ahankali ta tsaya yace “zauna” zama tayi sannan yakulle kofan yawuce…… Saleem bai tsaya ko’inaba sai hospital din su Marwan yawuce yayi parking yanadan gajeren tsaki cus he hates coming to the hospital it always remind him of sanda Babansu ya rasu he dies in the hospital, parking yayi yaciro wayansa yanabin wakan dake tashi a motan na Akon yayi dialing number Marwan yanasa wayan a speaker amman harta gama ringing bai dagaba he knew this might happen sai kawai ya kashe wakan yabude motan yafito yawuce ciki yana zuba kamshi yashiga cikin psychiatric ward din yana tafiya da dan sauri, yawanci nurses ne wajen direct hanyar office na Marwan yayi kai tsaye yabude office din yashiga yana maida kofan yarufe daidai yaji ana rike masa gefen riga gam dawani irin sauri yajuyo yakalli side nasa adan firgice, Amirah ce gefen kofan kanta akasa hannayenta na baki da pencil dayan hannun kuma ta rike masa gefen rigansa dashi, ga pink lips dinta dake motsi sosai tana kallon kasa, at first ya bala’in tsorata daga shigansa office out of nowhere wata tarike masa riga saura kadan yayi ihu cus yadauka aljana ce, but sai baiyiba ya tsare fuskanta da kallo especially long eye lashes nata dasuke nan kaman tai fixing da giranta dayake aciki dan idanunta na kasa da pink lips nata dan karami irin na jarirai, ga gashi a goshinta a kwance lublub kaman buzuwa, dan dukawa Saleem yayi yawani leka fuskan Amirah daidai tana tauna fingers nata suka hada idanu, idanuwanta kaman an wanke da madara sabida tsabagen haske baisan sanda gabansa yawani kalan fadi ba rassss! Amirah tadan dakatar da bitting fingers dinta datakeyi ganin fuskan wani daban daba Dr ba but he smells exactly like him dan turaren Marwan Saleem yasaka yafito abinsa, ahankali tasaki gefen rigansa while Saleem cikin wannan care free attitude din nasa yamata wani irin murmushi dayasa dimples dinsa suka lotsa sosai so deep yace “Hi, Hey, Hello Pretty!” Runtse idanunta Amirah tayi da sauri gabanta na faduwa muryansa zaki and so husky saita shiga komawa baya idanunta a kulle ganin wanda bata saniba at all, daidai ana bude kofan office din dawani irin sauri akuma tsorace Amirah ta juyo tana bude idanunta Marwan ne ya shigo da lab coat a jikinsa stethoscope a hannunsa dan wani patient dake having seizure yaje yaduba, ganin Saleem a office nasa yana kallon Amirah da batada wani tazara dashi sosai saiya tsaya chak itakuma Amirah data rude saitayo kansa kaman zata fado kansa looking confuse, cikin very harsh tone ganin zata shiga jikinsa yace “ke!” Tsayawa Amirah tayi chak amman dab dashi har iskan numfashin datakeyi yanaji akan fuskansa, hannunta daya na bakinta saitakai na biyun shima tasa a duka bakinta tana taunawa nervously, Saleem dake binta da kallo bayako kyafta idanu yace “wowwwww!” Cus tayimai wani irin bala’in kyau, yazuba hannu a aljihun wandonsa yana kallonta ko kadan Marwan bai kalli Saleem ba amman yaji yanda Saleem ke kallonta and yaji yanda yafurta wow, wani abu kawai yaji yayi brushing mind nasa sai ya matsa gefe yana kallonta yabude kofa murya ciki ciki yace “let’s go” sum sum sum duka hannun nata na baki tawuce tafita, Marwan yajuya batare daya kallesa ba yace “ina zuwa” baima jira amsan Saleem ba yafice tareda rufo kofan. EPISODE 1️⃣7️⃣ Amirah na tsaye gefen kofan yarufe yafito kawai yawuce yafara tafiya baima kulata ba Amirah tana binsa kaman bindi da sauri sauri dan dasauri yake tafiya, one step nasa shine like 2steps nata, kuma ba ahaka yasaba tafiya da ita ba ahankali yake tafiya but yau dasauri yakeyi har zuwa dakinta, yabude ya tsaya gefe batare daya shiga ba yakalleta yace “get in” zuwa tayi ahankali ta shiga hannayenta na baki, sai yashigo direct ya dauki maganin ta na rana yabata, batai musu ba dan taga kaman he’s angry ta amsa ruwan,ahankali yace “open” bude bakin tayi yazuba ta hadiye da kyar tanashan tuwa, saiyadan kalleta ko kadan batason magani yace “haaa” bude bakin tayi yaduba, yace “stay here, ina zuwa” yajuya zai wuce dawani sauri Amirah ta taso. “I said stay here!” Marwan yadaka mata tsawa da batasan sanda takoma gado da sauri saitama kwanta agadon ahankali ta runtse idanunta takai hannunta baki dasauri tanasha tana numfashi da sauri sauri, Marwan yayi shiru baiji dadin yanda yamata ihu ba at all, but hakanan har cikin ransa baiso Saleem yaganta, there’s nothing arayuwansa dazai taba iyama Saleem shamaki but wannan yarinyar sai yaji kawai he doesn’t want her in Saleem’s space sabida yasan waye Saleem, lumshe idanu yayi yabude saiya juya yayi wajen kofan yabude yafito yamaida yarufe yadan tsaya yayi jinmm saiya shiga tafiya, yana fitowa daga corridor saiyaga Saleem tsaye gaban office dinsa yana kallonsa yanadan murmushi ga waya a hannunsa yanajan gemunsa da dayan hannunsa, Marwan yakarasa wajen yace “why are you here? I’m very busy with patients” bude office nasa Saleem yayi yakoma ciki direct yaje yazauna kan kujeran Dr yayi wani rotating akai Marwan na shigowa yamaida kofan yarufe yana kallonsa sai bai kara magana ba yawuce fridge din yabude yadauki karamin bottle water yadawo yazauna yabude yakai baki yadan kurba Saleem yace “I want your ATM card” kallonsa Marwan yayi wani mugun kallo ma, Saleem yace “kadaisan I’m broke ko kuma bazan iya karban kudi a hannun Mami ba ko dan haka kabani kati nawuce” kai tsaye Marwan yace “anki abayar din kudina bana zuwa club bane”kai tsaye Saleem yace “why am I even wasting my time asking you” drawer table din yajawo yadauki wallet din Marwan, black card dinsa yazara yamike tsaye ya ijiye car key Mami yadauki na Marwan yace “Mami’s car sucks ba waka so ama use your own” yazagayo yawuce yayi kofa yana nunamai card yace “t for thanks, I know the pin don’t worry” yasa hannu zai bude kofan gently Marwan yace “Saleem must you club? Can’t you go just a day without clubbing? What is fun in shaye shaye and the rest? Do you know how many patients are in this facility sabida shaye shaye ya juyar musu dakai”? Dan shiruuuu Saleem yayi sai yajuyo dasauri yadawo cikin office din yajawo kujera yazauna gaban Marwan dake kallonsa yace “actually kasan wani abu little brother”?Marwan yayi shiru yana kallonsa baice komiba, Saleem yace “admit me to this hospital” wani kallo Marwan yamasa Saleem yace “yesss I mean it, listen I’m adicted to shaye shaye zuwa club u know girls” yadan kannemai idanu alamun sex, yace “amman kaga idan kai admitting dina i will be here bazan dinga zuwa ba with 1,2 ko 3weeks maybe na manta da shaye shaye duk kuhuta da wahala ta, the old man shima yadena fushi dani right, yadena rashin lafiya, problem fix, so admit me” yamikama Marwan hannu yace “samin drip do your Doctor thing” dan shiru Marwan yayi sai yace “do you think this is funny kai komi saika maida wasa and fun”? Dasauri Saleem yace “do you think wasa nake? Dude I want to be admitted here, this is me willingly nake baka kaina kai admitting dina ka mannani bangaren yan shaye shaye you guys should help me cus ni on my own can’t help my self, so help me help myself little brother Dr Marwan”Marwan yayi shiru yana kallonsa shima Saleem

Chapter 9 of 16