Share this page
kulata ne. Magiya da nacinta ba dare ba rana ne ya dawo da soyayyarsu har ya fara yunƙurin tarar Mahaifansa da batun ta, tare da shawarar da ya yanke na sawwaƙewa Naila kafin ya aiwatar da ƙudirinsa a kanta. Cikar Sufyan shekara ɗaya a ma'aikatar Dhahab yasa sukayi mai kyautar da ya hanasa runtsawa. Waya kuwa kwana sukayi suna yi da Ɗayyib, cikin isa Sufyan yake bada umarnin abinda za'ayi da kuɗin. Ba bu lissafin yinƙurin yin wani abu na cigaban Yankinsu a kason kuɗin da duk wani kuɗi da yake turawa sai Gidan Sarautar su da aka ƙara ƙawatawa, musamman ɓangaren Mahaifansa Ɗayyib da ɓangaren Kakansa Jalal. Ba bu wani tsarin tallafi da suka tsiro da shi a matsayinsa na Ɗan Yankin da ya samu cigaba a Babban Birnin Abyad sai dai mutanen gari su gani a jikin Iyayensa, ƴan Masarautar su da Gidajensu, duk da mummunar talaucin da suke fama da shi. Har lafiyayyen titi aka shimfiɗa daga farkon shigowa Yankin Tudu har ƙofar Masarautar su. A ɓangaren Ɗayyib da Sufyan ya fara samun kuɗi Gidan Game ya buɗe ƙato matasa su samu kuɗi suyi ta bugawa Yara kuma su sato kuɗin Mahaifansu. Abun takaicin sai Matasa da Iyayensu sun sha wahala sun ƙera Tukwane sun samu an siya daƙyar sai Ƴaƴan su kwashe kuɗin su gudu gidan Game ɗin Ɗayyib. Cikin ƙanƙani lokaci shima ya fara zama hamshaƙi. Dukka wannan facakar sai dai ƴan uwan Naila da Kaakarta su ji labari, kamar dai gama garin mutane ba surukan Sufyan ba. Ɓullowar batun auren Sumaya da Sufyan, ya tayar da ƙura a tsakanin Hindu da Ɗayyib don sai da sukayi faɗan da ya kaita ga tafiya Gidansu. Ta kafe bata yarda da auren ba matsawar ita ta haifi Sufyan domin malaman tsibbunta sun sanar da ita sakin Naila zai rusa komai, haƙurin mutanen da suka zubawa Sufyan ɗin ido ya na zaluntarta har suka ɗaukesa aiki zai ƙare daganan suyi masa ɗaurin talalar da zai mutu a ɗaure. Sam Ɗayyib bai yarda da batun Hindu ba, acewarsa ɗaukakar Sufyan daga Allah ne, babu wata Naila don haka dole su bar Sufyan ya rayu da abinda yake so. Ankai ruwa a tsakanin su har sai da Jalal Mahaifin Ɗayyib ya shiga faɗan da suke yi a sirrince don bakowa ba ne yasan Hindu bata gidan ba. Sai da Mahaifiyar Hindu ta saka baki, sannan ta yarda da auren amma da sharaɗin ko zai saki Naila sai lokacin da ta yarjemai. A kan haka suka bar zancen. Da tsananin rawar kai Sufyan yake rabon katin aurensa ga Manyan ma'aikatarsu. A cewarsa ma bai taɓa Aure ba. Labarin auren Sumaya da Sufyan sai da yaje har kunnen Bushra, ba tare da ɓata lokacin ba ta naimi Yasar ya toshe duk wata hanya da Naila za ta iya jin labari, saboda kar hakan ya kawomata tsaiko a jarabawar da take zanawa. Kuma da zarar ta gama ya shirya mata tafiya Yankin Tudu. A rabon Invitation card da Sufyan yake yi ne, Baturen da yake sama da shi ya bashi shawarar ya shirya katin gayyata na musamman ga GM wataƙila ya samu alheri mai yawan gaske. Da yake Sufyan ɗan son banza ne a daren ya biya kuɗi mai yawa aka shiryamai katin gayyata na musamman. Washe gari kafin ya shiga office ya miƙawa ogansa ya bawa GM ba tare da nutsuwa ya yi tunanin maiyasa tunda ya ke aiki a Dhahab bai taɓa ganin GM ba, ko da gilmawarsa ne. Gaba ɗaya sai Sufyan ya matsu ranar Aurensa ya zo, irin shagalin da ya tanadi maƙudan kuɗi za'ayi a Yankin Tudu na sanyashi jin alfaharin da bai taɓa jiba. Ɗayyib da su Sarki Hammam da ya yi kwantan ɓauna kamar yana tare su ne su suka zo Birnin Abyad Gidansu Sumaya naimawa Sufyan aure. A take Iyayen Sumaya da suka matsu da komai suka ce sun bashi sati mai zuwa a ɗaura aure su tafi da Ita Yankin Tudu su je can suyi Biki, a maimakon wata ɗaya da suka tsara da Sufyan tun kafin zuwan Iyayensa ya yi rawar kan buga katin gayyata. Iyayen Sumaya sun ce su basu da wani shagali da zasu yi bayan ɗaurin Aure. Abin takaici daga Ɗayyib har da muƙarabansa da suka zo Birnin Abyad tare ba bu wanda ya tambayi ina ƴarsu Naila Ƴar Yankin su take? a wani yanayi take ciki?. Kowannen su fuska ya yi yana dirzar duniyar da ya samu. Da rawar jiki Sufyan yake ƙara bawa manyansa haƙurin matso da lokaci kusa an samu akasi. Wa su sun nuna zasu je wasu kuma tambayarsa suka yi babu wani shagali da za'ayi ranakun da zasu biyo bayan ɗaurin auren da zasu iya zuwa? Da sanyin jiki ya sanar da su na Yankin Tudu tunda yasan ba lallai su je ba. Ga ɗumbin mamakinsa washe gari ya samu saƙo GM ya ce ya amsa gayyata amma ba zai samu zuwa ɗaurin aure ba, sai dai na Yankin Tudu da za'ayi In Shaa Allahu. Sufyan ihu yasa ya na tsalle, har ya fara hango irin ƙafafa da zafin kan da zai yi, inama da Naila tana wajen ya nunamata ko babu ita shi ya zama kafin Allah a Dhahab sai dai ta mutu da baƙin ciki. Cikin walwala da son Daular da ya ke iya canza tunanin ɗan Adam lokaci ƙanƙani su Ɗayyin suka cika sati guda a Birnin Abyad. Ranar Ɗaurin aure Irin fareren Turawan da suka zo ɗaurin auren Sufyan da Sumaya a Birnin Abyad ne yasa bakin Ɗayyib yaƙi rufuwa. Bayan komai ya lafa sun keɓe Ɗayyib ya murmusa cikin alfahari ya ce; "Sufyan ina alfahari da kai akanka na fara samun cikar burina na tsayin shekaru, kaga Ubangidana ko, sam bai halarci ɗaurin aure nan ba kuma nasan yana gari, dama ina sane da shi, tun daga kan takardun da na ce ya samar maka ya ƙauracewa waya dani, to dama haka rayuwa take, yau ina jina na daban ya ya ma kace sunan wannan Ma'aikata taku mai albarka." Ya ƙarasa faɗa yana kafa lemo mai tsada a baki. Sufyan da ke murmushin isa ɗan dariya ya yi kafin ya ce "DHAHAB" Azababben tari ne ya sarƙe Ɗayyib lemon da ya kurɓa ya soma biyomai ta hanci da baki... NAILA; A dai-dai lokacin da Tari ya sarƙe Ɗayyib Naila ta kammala haɗa kayan tafiya Yankin Tudu....✍🏻 Wanene General manager company sarrafa shinkafar Dhahab da Sufyan yake aiki a ƙarƙashin shi?😄 Maiyasa ya zaɓi zuwa wata ƙasar shagalin ta ya murnar ma'aikacin da ya ke ƙasan-ƙasansa duk da girman matsayinsa. Yaya zaman Naila a Yankin Tudu zai kasance shin zata dawo ko bazata dawo ba? Kaaka tana raye ko bata raye? Wani 🔥🔥 ne zai kama a Yankin Tudu? Next page In Shaa Allah [7/25, 8:47 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL *CHAPTER 3* *YANKIN TUDU🔥* Page 20 NAILA; da ƙananun kayan Calvin Klein ta yi sauƙaƙaƙiyar adon da ya dace da siffarta ya kuma haska kyanta. Fuskata ƙunshe da murmushi take kallon mutanen Birnin Abyad, farkon zuwansu Birnin ita da Sufyan na dawomata. Rashin banbancin da ke tsakanin fatarsu ta ɓangaren murjewa a yanzu yasa ta ɗan faɗaɗa murmushinta. Ashe komai zai sauya, ashe itama zata zama ƴar gayu kyakkyawar Macen da zatayi alfahari da kanta wata rana. Dogon mota mai kyau ta hau, idonta tsaye ƙyam a kan hanyar Babban Birnin Abyad. A wannan karon tana alaƙanta kallon hanyar da Yasar da Bushra da suke can tare da Sufyan, murmushi ta yi data tuna abinda su Bushra suka ɓoyemata, duk da Bushra tasa Yasar ya ɓoyemata koma sai da taga komai a shafin Sufyan kamar yadda take bibiya lokaci zuwa lokaci. Babban sauyin da ta samu a komawarta Yankin Tudu shine jirgin da ta bi a maimakon Mota da taimakon mutumin Bushra bayan isarta Airport. Cikin ɗan tsoron da ya mamaye ranta saboda hawarta jirgi a karon farkon kenan jirgin su ya ɗaga zuwa Iyakar Yankin Tudu da Babbar tashar da filin saukarsa ya ke. SUFYAN; Da hanzari ya nemo ruwa ya miƙawa Ɗayyib, haɗe da nanata kalmar "sannu" da yake tayi ba ƙaƙƙautawa. Ɗayyib ya ɗauki tsahon mintuna ya na tari, fararen idanuwansa da suka ƙara haske saboda daular da ya samu na kwana biyu ya juyewa zuwa jajaye marasa kyan gani. Da salon murya da Sufyan bai san Mahaifin nasa da shi ba ya ce; "Kasan menene DHAHAB" cikin rashin fahimtar ina ya dosa Sufyan ya ce; "Zinare mana Baaba" "Sufyan ina nufin kasan mafarin ƙirƙirar Dhahab, tunda kake a duniyarka ka taɓajin mai inkiyar banda Ahalin Marigayi Sarki Musa" cikin rashin fahimtar abu da wuri Sufyan ya ce; "Waccen Dhabah ɗin ai zuri'arsu ta mutu Baaba, waɗannan turawa ne ba ma ƴan asalin ƙasar Abyad ba ne, kusan dukka manyan da suke samana Turawa ne." Ɗayyib cikin rashin gamsuwa ya ce; " Wanene mamallakin ma'aikatar ba ina nufin GM ɗin da zai zo shagalin bikinka ba, tunda ance suna da reshe da yawa, asalin mamallakin Dhahab ɗin nake nufi gaba ɗayanta, kasan sunansa da inda yake da zaune" Sufyan ido ya zaro cikin mamaki ya ce; " Babaa ba ni da issue da duka waɗannan abubuwan da ka lissafo burina kawai na samu kuɗi, Ni ma na zama Dhahab ɗin kaina, tunda na lura sunan ya na da wani ɓoyayyen sirri, shine kawai." Kamar talabijin haka Ɗayyib ya zubawa bakin Sufyan ido, zuciyarsa kuwa Allah Ne kaɗai yasan faɗinta da sirrikan data ƙunsa. Da kaushin murya ya ce; "Daga ranar irin ta yau kafara saka lissafin abinda na tambayeka a cikin ƙwanyarka, domin ba ra'ayi ba ne ko ganin dama ba, tilas ne musan su wanene masu Dhahab, aikinka zai fara daga yau Sufyan!" Ɗayyib yana gama faɗa ya miƙe jiri na ɗibansa sama-sama. Kafaɗa Sufyan ya ɗaga alamun ko a jikinsa, shi ba shi da wannan ra'ayin da dai maganar kuɗi ne da kyau to da sai iya inda ƙarfinsa ya ƙare, amma ace duk Kuɗin da ya tara sai ya je yana binciken abubuwan da basu shafesa ba, why not ya ba shi shawarar ƙirƙirar wani hanyar da zai ƙara tara dukiya shima ya zama Dhahab ɗin da'akewa kokawa shekara da shekaru har ake salwantar da rayuka duk domin a kawar da su. SUMAYA Tasha gyara kyanta da farin fatarta sun ƙara fasowa. Sufyan daya ganta kamar ya siɗeta bini-bini ya kirata a waya su share mintina suna hira. Kayan alfarmar da zai fitar da Sumaya ta zama ta musamman sama da yadda Ubaidullah ya kawo Kakar Sulaim Nanaah Yankin Tudu aka tanadarwa Sumaya da taimakon Ɗayyib da kansa aka fitar da adon kayan da ya dace da Masarautarsu. Bayan komai ya kammala tsirran ƴan uwan Sumaya da kansu yake rawar Ƴar uwarsu tayi dacen gidan kuɗi da Sarauta suka fara shirye-shiryen tafiya Yankin Tudu. Ranar Alhamis da ya rage saura kwana biyu shagin Yankin Tudu suka ɗugunzuma dukkansu, abin birgiyar daga Company su Sufyan aka turo da motoci na alfarmar da zai kaisu Airport. Sarki Hammam da ya jima da yin kwantan ɓauna domin tsiratar da rayuwarsa da samun bayanai murmushi yake saki cikin ransa ya na mamakin ɗabi'unsu. WAIWAYE Shekarun baya... Labarin da Dattijo Junaid ya bawa Sarki Hammam, labari ne akan ɓarnar da su Ɗayyib suka kwashe shekaru su na yi a ɓoye. Bayan rasuwar Dattijo Junaid Sarki Hammam ya shiga ɗimuwa da zullumi. Saboda yasan shi ma wata rana matsawar zai yi tsayuwar tsayin daka akan gaskiya to tabbas zai bi sawun su Dattijo Junaid ba da jimawa ba.. Rasuwar Bashar ya ƙara jefa zuciyarsa cikin ɗimuwa, musamman da ya ji ƙishin-ƙishin ɗin ba fa mutuwar Allah da Annabi Bashar ya yi ba, ana zargin Ɗayyib ne ya shaƙamai guba. A hutun da Sarki Hammam ya tafi Babban Birnin Abyad bayan rasuwar Bashar ya haɗu da Malik, ya kuma gano Dhahab ɗin da su Ɗayyib suke kokawar sai sun ɓaddashi ya na nan daram a Babban Birnin Abyad, amma kamar yadda Malik bai sanar masa wanene yaƙara kafa Dhahab daga cikin zuri'ar Marigayi Sarki Musa ba, shima bai zurfafa dole sai ya sani ba. Sun yi taƙaitacciyar tattaunawa da Malik. A cikin tattaunawarsu Malik ya bashi shawarar ya shiga jikinsu Ɗayyib domin sanin motsinsu, ya zubawa zaluncinsu ido har zuwa lokacin da Ubangiji zai ƙaddara ƙarshensu. Idan kuma suka yi zaluncin da ya ratso da haƙƙin wani to ya sanar masa, shi kuma zai yiwa kowaye a cikinsu hukunci dai-dai da abinda ya aikata.. Bayan dawowar Sarki Hammam daga Babban Birnin Abyad sai ya zama ɗaya daga cikin Informer Malik a cikin Masarautar Yankin Tudu, da ma Yankin baki ɗaya ba tare da kowa ya ankara ba... *YANKIN TUDU* NAILA; lokacin da jirgin su ya sauka a iyakar mafarin shiga Yankunan su, murmushi ta saki, zuciyarta na azalzalata tanajin ƙarfin gwiwar da bata taɓa jiba. Cikin kasuwar chanjin wajen da yake kusa da Airport ta shiga aka canza mata kuɗin ƙasar Abyad zuwa na ƙasarsu, bat rage ko sisi ba. Kuɗine masu yawan gaske don haka ta zuba su a cikin jakar da ta tanada domin su. Masauƙin baƙi ta nufa na canza Suturar jikint zuwa Abayar da suka fi amfani da shi a Yankin Tudu duk da wanda bata da ɗan bambanci. Drivern da ya ɗaukosu ita da Sufyan shekarun baya shi ya ƙara ɗaukarta. Da shi da Motar tasa duk sun tsufa sun jeme. Gudu yake yi amma sai take ganin kamar baya sauri saboda yadda ta matsu ta riski Kaka ta ga ko ita yaya ta koma? Hirar yadda Yankinsu ya koma Driver yake yimata muryarsa a raunane da yadda Sufyan ya ke kashe Kuɗi a iya Masarautarsu da mutanen cikinta. Naila bata tsawaita magana da shi ba, saboda yadda zuciyarta take suya. Lokacin da suka shigo Yankin Tudu batasan sanda dariyar da ya bayyana jerarrun haƙwaranta ya kufcemata ba. Suna isa ƙofar gidan Kaka da zumuɗi ta buɗe murfin motar, kuma tayi sa'ar babu mutane. Duk suna cikin Gidajen su sai tsirran da ba'a rasa ba. Da taimakon shi ta sauko da kayan tsarabar da ta jibgo. Kuɗi ma su nauyi ta ɗauko ta bashi da sunan kuɗin da ya ɗaukota. Ƙasa ya zube yana kuka cikin shesheƙa ya ce; "Allah Ya aramin ranar da zan saka miki da abinda kikayimin Allah Ya haska gabanki Ya haska bayanki, Na gode! Na gode!!!" Kai ta girgiza mai haɗe da kutsawa Gidan Kaaka. Murnarta ce ta koma ciki sanda tayi ido biyu da yadda Kaaka ta rame ta lalace fatarta ta yamushe kamar babu ruwa a jikinta. Da farko Kaka bata gane Naila ba, sai daga baya, da gudu ta taso garin ta iso inda Naila ta ƙame a tsaye ta zube ƙasa saboda tuntuɓen da ta yi. Da sauri Naila ta ƙarasa suka ƙanƙame juna, tana kuka itama Kaka tana kuka. A haka Drivern ya gama shigo mata da kayanta. Kaka kallon Naila tayi ta shafa fatarta sai ta fashe da kuka, ta yi haka ya kai sau uku, kafin ta miƙe tayi hanyar waje. Naila bayanta tabi da kallo tana share hawayebta. Jakar kuɗin da ta zo da shi ta adana tana sakin murmushi. Layi-layi Kaaka ta bi tana kuka tana cewa; "Ya ku ƴan uwana mutanen Yankin Tudu ku fito ga jikata Naila ta dawo daga Ƙasar Abyad, ku fito ku ganta Mutanen Yankin Tudu" Kafin ka ce me, dangin Mahaifin Naila, da mutanen gari daga kowani ɓangare sun cika Gidan. Kowannensu idan ya yi dariya sai dai kaga haƙoransa ya cika masa fuska saboda rama. Maza da mata haka suka cika Gidan Kaka. Da Naila ya kalli fuskokinsu da yadda suke dariyar da yake nuna irin farin cikin da suke ji sai ta fashe da Kuka. Suma da yawansu sai suka saka kuka suna zayyanomata labarin irin talaucin da suke ciki. Tsabar da ta taho da shi a take ya ƙare wa su ma basu samu ba. Bayan kowa ya watse Mahaifiyar Kabeer da ta kasa tafiya ta matso kusa da Kaka, da ƙaramin murya take roƙon ita bata samu ba su taimaka mata, da Naila ta kalleta ta tuna da ɗanta Kabeer ɗaya fita Zakka a ƴaƴansu saboda zafin naima sai ta fashe da kuka, da sauri ta miƙe shiga Ɗakin Kaaka na ɗauko kuɗi ta bata. A wannan dare kwanan labari Naila sukayi da Kaka cikin kuka mai taɓa zuciya. Da ƙarfin gwiwar Kaaka dana Yasar Naila ta yanke shawarar ƙin zuwa Gidan su Sufyan idan ya ji haushi ya bata takardarta ta. ★washe gari labarin dawowar Naila da shirye-shiryen shagalin bikin Sufyan da ƙin zuwan Naila gaishe da Mutanen Masarautar Yankin Tudu ya bazu ko ina, har kunnen Hindu mahaifiyar Sufyan da Kakansa Jalal. Ƙura ba taƙara tashi ba, sai da Naila ta ɗebi dubban mutane Yankin suka shiga Kasuwar Maƙotan Yankinsu abisa shawarar Kaaka suka siyo ɗayyan abinci a farashi mai rahusa. Aka fara rabawa Talakawan Yankin. A wannan rana sai da hankalin duk wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu ya tashi, domin ɗabi'ar da Naila ta tsiro da shi ɗabi'un Zuri'ar Marigayi Sarki Musa ne. Labari bai tsaya a iya Yakin Tudu ba har kunnen Sarki Hammam, Sufyan da Ɗayyib da suke can Birnin Abyad suna shirye-shiryen tahowa. Sufyan kishine ya kamashi, shi kuma Ɗayyib da yake komai nasa a lissafe yake tafiya, a take ya alaƙanta kalan taimakon da Naila ta da mamallakin Companyn Dhahab da ɗansa yake aiki, kenan dole akwai ɓoyayyen dalilin da yasa aka ɗauki Sufyan aiki kai tsaye, saboda ko maƙaho a Yankin Tudu yasan irin taimakon da akace Naila ta yi yasan irin na jinin Marigayi Sarki Musa ne. Domin su ne suke taimako da gumin su, su kuma kawowa mutanen Yankin su cigaba da ƙwaƙwalwar su. Lokacin da labari ya riskesu su na Airport, don haka suka matsu su iso ayi shagalin biki agama su kawo ƙarshen komai. A can Yankin Tudu wajensu Naila Ba bu tsangwama babu nuna waccen nawa ne, wannan ba nawa bane, Naila ta bada umarnin su kasafta abincin a tsakaninsu. kuka da addu'o'in Tsofaffi, Maza da mata, Matasa, da Yara ne yake ta tashi tare da kabbarorin su ta ko ina. Maimakon sanya idon da bindiddigin auren Sufyan sai Mutanen Yankin suka mayar da hankali wajen yiwa Naila addu'o'i da fatan nasara mai ɗorewa. A wannan rana Naila ta wuni cikin jindaɗi da soyayya daga ɓangaren Mahaifi harma da ɓangaren Mahaifiyarta da suka samu labari. Kaf kuɗin da Naila ta ɗauki shekaru tana bautar yin kitso da wanda Bushra da Yasar suke bata ta tattara ta bayar aka siyi kayan Abinci, sai abinda ba'a rasa ba daya ragemata ta bari a jikinta, tana addu'ar Allah Ya kawo ninkinsu. Barci mai cike da nutsuwa suka yi ita da Kakaa. Ranar da su Ɗayyib suka sauka wanda ya yi dai-dai da ranar cin kasuwar Zinare Naila da Mutanen Yankin sukayi shawara sukayi shawarar rushe Gidan Game ɗin Ɗayyib, da suma ƙiris suke jira har da matasan da suka ƙara ganin mutuncinta saboda abincin da rabawa Iyayensu, tsanar Ɗayyib ya yi kane kane a zuciyarsu. Bayan gama cin Kasuwa kowa ya addana abinda ya samu suka taru suka rushe ƙaton wajen da Ɗayyib ya kewaye da langlanga. Sannan Mazansu da Matansu sukayi tattaki har ƙofar Gidan Sarki Hammam da saukarsu kenan sukayi ƙorafin basason Gidan Game da Gidan Rawa lalata masu Yanki yake yi!. Kayan Game ɗin cikin wajen da suka rusa babu wanda ya taɓa ko ɗaya, Matasa majiya ƙarfi ne suka Tattaro suka zuɓe a ƙofar Masarautar Sarki Hammam. Da yake bikin Sufyan suke burin suyi hankali kwance sai Sarki Hammam ya fito ya basu haƙuri. Ɗayyib mutuwa ne kawai baiyi ba. Jalal Mahaifinsa da muƙarabansa a ranar suka shirya taro a kan Naila saboda sun samu labarin ita ta kitsa komai, tare da bawa Sufyan umarnin sakinta da gaggawa, da shawarar kama Naila da Kakarta suka fara yankewa sai dai hakan zai tunzura mutanen Yankin da dama can a gajiye suke ayi tashin hankalin da ba sa so, shine suka yanke shawarar Sufyan ya saki Naila. Hukuncin su Jalal gagarumin rigima ya tayar domin Hindu a take ta nuna Sumaya ba ta yimata ba idan kuma Sufyan ya sakeni sai ta tsinemai. Sumaya dake lulluɓe cikin mayafi bata fuskanci duk abinda yake faruwa ba, ita da ƴan uwanta sai zare ido sukeyi. Jalal ne ya daki ƙasa kai tsaye ya ce ƙaryar Hindu ya na so kafin rufuwar mintuna Talatin takarkar Sakin Naila ya isa ga ahalinta. GIDAN KAKA Sarki Tsafin Yankin Tudu da su Jalal suka butulcewa saboda ɗaukakar da Sufyan ya samu ne yasa Maza majiya ƙarfi masu ƙarfin tsafi a Jikinsu su yi gadin kaf faɗin kewayen Gidan Kaka saboda Naila. A ɓangaren Matasan Yankin suma ƙofar Gidan Kaka suka mayar majalisar su har da abin shiffiɗar kwanciyar su saboda tsaron kar a biyoni cikin dare, Ni ma kuma ban gajiyaba wajen ambaton Ubangijin halittu. NAILA; bayan ta huta suka ƙarayin waya da Yasar ya kuma ƙaramata ƙarfin gwiwar kar ta gajiya nasara na nan tafe In sha Allahu kafin dawowarta. Da bayin Gidan Sarki Hammam Mata ta ɓangaren Jalal suka isar da saƙon Jalal na sakin Naila a gidan Kaka da rufa ido ɗaya a cikinsu da dama don abinda aka turota da ragowar kenan ta ɗauke wayar Naila. Su Naila ba su ankara ba sai bayan tafiyarsu. A daren Ɗayyib ya yi duk wani bincike shida Sufyan da ƙwararren masanin na'ura mai ƙwaƙwalwa a Masarautar amma basu ga alama ɗaya daya haɗa Naila da Ma'aikatar su Sufyan ba. Cikin ɗacin hali Sufyan ya farfasa wayar ya cire layin ya karya. ★washe gari layi-layi fadawan Sarki Hammam suka bi suna gayyatar mutanen Yankin filin wasannin ƙarshen mako don gudanar da shagalin bikin Sufyan. ★ Ranar da ya kama shagalin bikin Sufyan da Sumaya. Sufyan ya yi ado na kece raini duk da ba haka yaso ba Naila ta ɓatamai komai. Sarakuna daga Yanki-Yanki ƴan kasuwa da ƴan siyasa, su aka warewa waje na alfarma har da wajen da GM ɗin Sufyan da sukayi waya suna kan hanya zai zauna. A cikin Dattawan da suka je gudun abinda zai biyo baya har da Mahaifin Kabeer da ya tsufa ya yanƙwane saboda wahala. Lokacin da taro ya yi taro motocin Ɗayyin da Sufyan ya sabunta suka tafi taro GM ɗin Companyn sarrafa shinkafa ta Dhabah. Isowarsa Motar da Gm yake ciki da saukarsa daga Mota duk akan idanuwan Mahaifin Kabeer. Dark blue suit mai nauyin kuɗin gasken daya kwantawa farin fatarsa da kakkaurar jikinsa ya sanya. Gashin kansa dake amsar gyara na kwance luf. Lokacin da ya fara takawa, Mahaifin Kabeer da yunwa tasa ya ranƙwafa ya yanko wajen da aka hanasu ƙetarawa saboda su talakawa ne da gudu. Cikin ihun da ya haɗe da kuka ya ke faɗin; "Ashe Malik zai cikamin alƙawarin da ya ɗaukarmin! sai dai ya shammceni, da na san irin wannan alfaharin yake nufi da na tattara masa dukka Ƴayana ya tafi da su. kabeer Ɗana ashe da gaske zaka dawo garemu bayan mun cire rai, lallai Allah Abun godiya ne." Cak Kabeer ya tsaya haɗe da buɗe dukka hannayensa da ke fitar da wani irin ƙamshi. Cikin soyayyar Uba da Ɗa kabeer ya rungume Mahaifinsa. Babu wanda bai miƙe ba, babu kuma wanda bai razana ba daga waɗanda suka san Kabeer har waɗan da basu sanshi ba. Da wani irin fushi Ɗayyib yake taka ƙasa kamar zai hudasa, gaban Sufyan da shi ma yake tsaye kamar mutum mutumi ya tsaya ya na kai hannunsa saitin ƙugun wandonsa. Da zafin zuciyar azabar dake neman halakasa tashi ɗaya ya ce; " Lallai ban haifo ɗa ba sai soko kaicona! Nasan Malik ya ɗauke Kabeer ya inganta masa rayuwarsa da turomana shi a irin wannan lokacin domin ya nuna mana iyakar mu, kuma ya yi nasara. Amma idan har Malik zai mallaki dukiyar da zai sauya rayuwar Kabeer, Kabeer kuma ya sauya taka kai kuma ka sauya namu to tabbas su na da Ubangida, Uban gidan da ya kamata ace kasani tuntuni, amma sai gashi ko Kabeer ɗin ma baka sani ba Balle kuma Ubangidan su, daga yanzu har zuwa ajalinka ba zan taɓa yafe maka ba Sufyan har sai ka gano min wanene DHAHAB 🔥????? Ɗayyib ya ƙarasa faɗa yana yankar ƙuncin Sufyan da wuƙar da ya zaro a ƙugunsa, a take jinin kumatun Sufyan ya yi tsartuwar da ya fallatsa har saman fuskar Ɗayyib....✍🏻 Barka da Jumu'a. [7/27, 9:52 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 21 Sufyan kansa ya sunkuyar ƙasa, raɗaɗin yankar da Mahaifinsa ya yi mai a kunci da yankar da Kabeer ya yi

Chapter 11 of 15