Share this page
bibiyarsa ne domin na tambayesa ina Sulaim da gaske wuta ta ƙoneshi ya mutu, sai dai ƙiri-ƙiri Malik ya nuna bai Sanni ba bai ma taɓa gani na ba, wannan ne ya yi min ciwo har ma tashi da zazzaɓi." Da mamaki Yasar ya ce; "Anya kuwa Naila kinsan wanene Malik? Su Malik fa asalin ƴan ƙasar Abyad ne, domin da harshen da mafi rinjaye kuma mafi wahala na ƙasar Abyad dukka ahalin Gidan su ke amfani, yare ne mai wuyar koya a wajen bare, ko dai kama yake yi miki da waccen Malik ɗin?" Tasan dama ba lallai ya yarda da ita ba, don haka kai tsaye ta karɓi yardar Malik kama yake yimata da waccen Malik ɗin. Nasiha Yasar ya yimata tare da tunamata yaƙinin da mutanen Yankinta suke da shi a kanta, don haka na mayar da kai tayi karatu bakin iyawarta. Kamar zata iya cire komai a ranta ta amsawa Yasar da "to" haɗe da yimasa godiya. Ya na ɗan jima a Gidan kafin a mayar da shi gida. Bayan tafiyarsa dalla-dalla Naila ta zauna ta warwarewa Kaka komai. Kaka tsohuwace mai saurin fahimta da sauƙin hali bata da birkicewar wa su tsofaffin. Cikin hikima ta nusantar da Naila, ko da ace Sulaim yana raye ba Mijin aurenta ba ne, ta tsaya a iya matsayinta ta kuma tsaya tsayin daka wajen manta baya ta fuskanci gaba, kar ta manta haɗakar kuɗin Mutanen Yankin Kakanta, da na Mutanen Yankin Tudu ne ya kawosu Birnin Abyad ba domin komai ba sai don ta yi karatu, saboda daga gareta suke sakaran samun canji, kar ta bari tunanin wanda da zai samu damar ƙara dawowa duniya bata kai matsayin da zai sota ba ya lalatamata tunaninsa har ta kasa zama abinda mutanen Yankinta suke yi min fata. Sufyan da bai gaji arziƙiba, bai kuma gaji sarauta ba ya gujeta balle Sulaim da ya gaji Sarauta gaba da baya tare da tarin arziƙine zai so ta, Karta kuma wahalar da kanta wajen tunanin Sulaim yana raye ko baya raye, ta ƙaddarawa ranta ya mutu, ba kuma zai ƙara dawowa ba har abada! Maganganun Kaka gaskiya ne, amma ɗaukarsu ga Naila a lokaci ɗaya abune mai kamar wuya, amma tasawa ranta zatayi iyakar iyawata don ganin ta fidda mutanen Yankinta kunya. Kwanaki bayannan, ta fara bin gidajen Customominta, ta kuwa yi sa'a hannu bibbiyu suka karɓeta har ta samu kitsa kan wasu, A ranar da kuɗi masu nauyi ta dawo gida. Daga wannan rana Naila ta ƙara himma akan sana'arta, har zuwa lokacin da ranar komawarta Makaranta ya yi. Yasar ne yayimata siyayyar komai. Shi da Kaka da ƙannensa ne sukayi mata rakiya har Makaranta. Kasantuwar Naila a Jami'ar ƴaƴan masu wadatar Birnin Abyad bai sa ta kai kanta matsayi da su ba, kitsonta takeyi ido rufe, kuɗi kuwa kamar anayimata yayyafin su, domin wasunsu biyan fariya da isa sukeyimata ita kuma na karɓa hannu bibbiyu tana godiya. Watanta ɗaya a Makaranta ta dawo tayi weekend tare da Kaka, sannan da bata ajjiyar kuɗin kitson da ta samu ta dinga tara musu. SUFYAN. Babu abinda ya sauya tsakaninsa da Sumaya, yawan ƙorafi, batason wannan, ita wannan take so da dai sauransu. Rashin mafita yasa Sufyan yake lallaɓawa, kuɗi kuma idan ya samu na su Ɗayyib ne. Sumaya sai dai ta samu ɗan abinda ba'a rasa ba. Wata rana taro ya kai Sufyan Companyn Dhahab da suke ƙera Tukwane. Lafiya qalau suka gama taro ya fito, a hanyarsa ta fitowa ya ga mutumin da ya zo Yankinsu a matsayin Kabeer saboda shi dai ya kasa yarda da gaske Kabeer ne. Basarwa ya yi, ya nufi Motarsa. Har ya shiga Mota ya tuna ya manta tabaransa a teburin da ya zauna. Da ɗan zafin nama ya juya saboda aikin dayake jiransa a office. Baya ya dawo yana matse idanuwansa da suka farayimai yaji. Masu tsananin kamanceceniya da Malik, Salman, Kabeer ya gani a waje ɗaya. Ƙara buɗe idanuwansa ya yi gaba ɗaya yana zaresu. Babu wanda ya kallesa a cikinsu har su ka gama gaisawa suka tafi sai wanda yake tsananin kama da Malik ne ya rage a tsaye yana duba wayarsa. Sufyan bai motsa ba sai gumin dayake tsiyayomai, yana cikin wannan halin Maigidanshi Baturen da suka zo tare ya fito daga ɗakin taron, da sauri ya ƙaraso kusa da shi yaja hannunsa har gaban wanda yake kallo. A gabatarwa da Baturen yake yi Sufyan ya ji ya ambaci Malik Dhahab shugaban Companyn Tukunyar Dhahab na ƙasar Abyad. Malik baya kallon fuskar mutum sai cikin idanuwansa, kamar yadda ya koya daga iyayen Gidansa, don haka kai tsaye cikin idanun Sufyan da suka fara canza kala yake kallo Tafin hannun Malik mai girma da faɗi ya miƙawa Sufyan, shima Sufyan ƙasa ya yi da kansa kafin ya ɗago hannunsa da ya jiƙe da gumi tare da yimai nauyi ya miƙawa Malik bayan ya laso laɓbansa don ya tabbatar da harshesa ya na bakinsa bai fita ba. Haɗuwar tafukan hannuwansu waje ɗaya yasa Sufyan ya ɗan ɗago kansa a hankali don satar kallon fuskar Malik, charaf idanuwansa suka faɗa cikin nashi, kafin ya sunkuyar da kansa ƙasa Malik ya ce; "Sufyan Ɗayyib Jalal right?" Ambaton sunansa da salon da yasan dole sai wanda ya sanshi a Yankin Tudu ne zai iya faɗa da kuma Muryar da ya tabbatar masa da dagaske Malik ne a gabansa yasa idanuwansa juyewa numfashinshi ya ɗauke nan take ya zube ƙasa. NAILA. A makaranta ta haɗu da ƙawa ƴar masu arziƙin da take biyanta kuɗin kitso mai nauyi, da style kala-kala take zuwa a wayarta ta yi mata sak irin wanda ta kawo. wannan dalilin yasa suke ɗasawa da ita har sukan yi hirar da ya shafi Kaka da Yankinsu da ita. Amira mai zuwa kitso wajen Naila da suka fi ɗasawa sun riga su Naila gama Exams. Ana saura kwana ɗaya zata tafi Gida ta zo da wani style ta ce Naila mata. Bayan mun gama take shaidawa Naila Babban Birnin Abyad zataje tsare-tsaren Bikin ƴar uwarta, wataƙila idan kitson ya yiwa ƙawayenta su zaɓeta ta zo tayi mu su, domin dalilin da yasa tace tayi mata irinsa kenan. Ko Kakarta ba zata amince ba? Naila Tuna muradinta na son zuwa Babban Birnin Abyad yasa ta ji kamar ta amsata mata kai tsaye sai dai da ta tuna faɗan da Kaka tayimata akan Sulaim, sai tace bata ba, amma ta bari idan taje gida zata tambayeta idan ta amince zata sanar mata.... A akan haka suka rabu. Shin Kaka zata amince kuwa??😄 🔥ZINARE🔥 SASAAL Page 26 Har su Naila gama Exams bata daina tunanin tattaunawarsu na zuwa Babban Birnin Abyad da Amirka ba. Amma ta sawa ranta amincewar Kaka shi ne nata. Ranar da ta koma gida Da murna Kaka ta tarbeta bayan girki-girke ma su daɗi da ta shiryamata, sai da ta huta ta ci abinci, takasa sakowa Kaka zancen zuwanta Babban Birnin Abyad yin kitso saboda tsoron yadda Kaka zata fassara zancen take yi. ★har washe gari ta kasa yi mata zancen tafiyar, Sai Kaka da kanta ce ta kalleta cikin dariyar da ya haɗe da mamaki ta ce; "Me kikeson faɗa kika kasa Naila? Tun jiya ina ankare da ke, karki ji nauyi ki faɗamin zan fahimceki kinji" Murmushi ta yi tana murza goshinta, cikin kame-kame ta ke bata labari yadda sukayi da Smira. Kaka kallon Naila takeyi maganganu Sarki tsafin Yankin Tudu lokacin da ya zo duba Naila na amsa kuwa a cikin kunnenta "Naila zata warke amma akwai jarabawar da ya fi wannan raɗaɗi a gaba, domin zata isa Babban Birnin Abyad, da ƙarfin ikon Allah! Amma daga lokacin ƙullin shekarun da aka kasa warwaresa zai fara warwarewa da kansa, arziƙin da Sufyan ya yi gajen haƙurin ya riskesa zai bayyana, wannan yana ɗaya daga cikin abinda Mahaifiyarsa take kwaɗaitar masa ya gaza fahimtarta, da ya yi haƙuri da zai zama wankakke abisa laifin da Kakannin-kakanninsa suka jima su na aikatawa aban ƙasa, ko da Naila ta warke ta koma Birnin Abyad, Birnin Abyad ba mazaunin Naila ba ne. Ba lallai ki yarda da maganganuna ba, amma daga ranar da sanadi ya kai Naila Babban Birnin Abyad, zaki gasgata batuna" furucin Sarkin Tsafin Yankin Tudu kenan lokacin da ya zo duba Naila, amma Kaka tayi watsi da zancensa acewarta; Boka Ɗan uwan shaɗai ne, don haka babu gaskiya a maganarsa.. Tuna wannan yasa Kaka a zafafe ta ce; "Wallahi ban amince ba Naila, kinsan abinda kike faɗa kuwa? Babban Birnin Abyad har abada ba wajen zuwanki ba ne, karma ki ƙara tambayata don bazan lamince ba na gayamiki" Kaka taƙarasa faɗa cikin masifa! Tsabar masifa har rufe idanuwanta take yi kafin ta fashe da kuka. Birkicewar Kaka lokaci ɗaya da yadda take magana har da su fashewa da kuka ba ƙaramin tsoro abin ya bawa Naila ba, cikin haushin yadda ta hantare ta har da su kuka ta ce; "Kaka kukan me kike yi, ni fa kawai shawararki na nema, bance dole sai na je ba, sannan ke kika ce na gayamiki kar na ji nauyin komai zaki fahimce ni, amma gashi akan kawai na faɗa miki gaskiya shine kike masifa har da su kuka, dama can dai haushina kike ji, daga dawowata zaki sanyani cikin damuwa, na fara ciwo kuma kiyimin sharrin Yankin Tudu nake son komawa, gaba ɗaya kin canza Kaka." Tsit ta yi tana kamo hannun Naila. Ɗan fizgewa Naila ta yi tana cewa; " ki ƙyale ni Kaka, tunda kin fara jin haushina a ɓoye bansani ba, ni ma daga yau babu ruwana da ke" Hawayenta ta share still ba ta saki hannun Naila ba, da sanyi jiki ta ce; " to zauna na faɗa miki gaskiya ina fatan kema za ki fahimceni, ki janye batun zuwanki Babban Birnin Abyad" Son labari irin Naila yasa ta zauna da sauri jikin su na gogar na juna. Abinda Sarkin tsafin Yankin Tudu ya faɗa ta maimatamata sannan ta ɗora da; " Naila bawai na gazgata maganganun sa bane ɗari bisa ɗari, amma a yanzu a jikina nake jin ko dukka maganganunsa ba su zama Gaskiya ba, to baza'a rasa gaskiya ko da yaya bane ciki, duba da yadda su Hindu suke fafutukar dole sai kin koma cikin rayuwar ɗansu, Naila inajin tsoron matsalar da zai ƙara kunnowa rayuwarmu kai a yanzu, ki gafarceni" Da mamaki Naila ta kalli Kaka tana tattare girarta waje ɗaya ta ce; "Saboda iya wannan dalilin zaki haramtamin samun kuɗin da zai sauya rayuwar Yankina? Kinsan nawa za'a biyani Kaka?. Rayuwarmu bazai taɓa cigaba da tafiya a haka ba, dole sai da gwagwarmaya tare da ƙalubale Kaka, baƙin ciki da farin ciki basa dawwama a rayuwar Bawa, idan warware ƙullin ne zai zama cigaban Yankinmu mai zai hana mu tunkari warwaresa ko da hakan zaisa mu rasa rayukanmu, tun da dai dole zamu mutu wata rana. Kaka kiyi tunani tunda na ki tunanin yafi nawa zurfi, ba kuma zanyi yin kaina ba dole zan jira umarnin ki, amma Kaka ki tuna gina kanmu da Yankinmu wajibunne, saboda Yasar shine ƙarfin gwiwar zamanmu a Birnin Abyad, to idan ya mutu fa? ko ya gaji damu fa? Jira zamu yi tayi sai dai wani yayimana gwagwarmaya mu muji daɗi mu ba za muyi da Kanmu ba? Saboda muna tsoron mutuwa? Kaka kiyi tunani a nutse, kuma karki ji shakkar sanar da ni duk abinda kika yanke, In Shaa Allah zan yi miki biyayya kin ji." ta ƙarasa faɗa tana rungume kaka bayan na sumbaci goshinta. Tun a lokacin bugun zuciyoyinsu ya sauya daga tsoro zuwa ƙarfin gwiwa. SUFYAN Da ya farka ya ganshi a gadon Asibiti baiyi mamaki ba. Sumaya tana ganin ya farka ta ajjiye wayar hannunta tana matsowa kusa da shi, sannu take ta nanatamai tana kamo hannunsa. Laƙwas Sufyan ya yi. A hankali ya buɗe bakinsa ya zaro harshensa. "Sumaya kina ganin harshena, yana cikin bakina?" Ya yi tambayar yana karkaɗa harshensa. Da mamaki Sumaya ta ce; "gashinan kana karkaɗawa, maiyasa zaka yimin irin wannan tambayar Baby, relax har yanzu zafin ciwon bai gama sakinka ba, bari na kira Likita" ta ƙarasa faɗa tana sakin hannunsa haɗe miƙewa ta bar ɗakin. Ajiyar zuciya Sufyan ya sauke, sai dai kafin ya yi relax ɗin da Sumaya ta ce, asalin fuskar Malik da babu Tabarau babu komai sai ƙasumbar da shima an ragesa sosai saɓanin jiya da ya cikemai rabin fuska ya bayyana a ɗakin, mai kamannin Salman sak na biye da shi a baya. Jikin Sufyan ne ya saki, tabon tsoron Malik da ya kwana da shi washe gari ya ɓace na dawowa sabo fil, idanuwansa ya kulle gam kamar mai barci. Ido Malik ya lumshe kafin ya saki murmushin da sam bai masa kyau ba saboda bai saba ba, da iya ganin fuskarsa kaɗai zai iya kawar da Sufyan a doron ƙasa ta hanyar bugawar zuciyarsa. Amma Yaron tausayi yake bashi bai san komai ba sai abinda suka ɗorasa akai, ya jima da karantar Sufyan shi ba faɗan kawar da wani ne a gabansa ba, shi dai burinsa ya zama kyakkyawa ya tara kuɗi shima ya zama Dhahab ɗin kansa kamar yadda suke sauraran duk wa su hirarrakinsa ta offishinsa har ma da Gidan da yake kwana. Da buɗaɗɗen muryarsa mai nauyin dake amsa amo da ya dace da kalar siffarsa Malik ya ce "sannu da Jiki Sufyan Ɗayyib Jalal, Allah Ya ƙara afuwa, ga colleague ɗina Uzair ku gaisa" ya ƙarasa faɗa yana nuna Uzair. Sufyan daya kasa gaishesu da sunan ya na barci, kuka ya fasa idanuwansa a kulle, kansa a can gefe. Hannuwansa biyu ya haɗa waje ɗaya ya ɗagashi can sama dai-dai saitin su alamar roƙo. Tsabar kukan da yakeyi kafaɗunsa da ko ina nasa rawa yakeyi. Malik miƙewa yayi zai fita saɓanin Uzair da ya tsaya kallon Sufyan da mamaki. Da taushin Muryar da sam baya kama da na Salman yake tambayarsa da yaren ƙasar Abyad "maiyasa kake kuka?" Damacan Sufyan ba wani sanin Murya Salman ya yi ba balle ya tantance. Sufyan bai amsa ba still yaƙi kallon gefen da Malik ya bar Uzair a tsaye. Sufyan na jin Muryar likita ya ɗan saki ajjiyar zuciya sai dai ƙara jin Muryar Malik a bayansa ya sa ya sume kansa ya karyo kamar zai faɗo daga kan gadon. Hannun Malik Uzair ya ja suka fito waje. Da fuskar tausayi Uzair yake tambayar Malik wanene Sufyan? Maiyasa yake jin tsoron da ya ke sashi sumewa idan ya gansu? "Yankin Tudu, Babban Ɗa namijin Ɗayyib Jalal" Malik ya faɗa yana kallon Diamond Bracelet ɗin hannunsa. Wayar Uzair ne ya faɗi kasa a take gilashin baya da na gaba yayi kwatsa-kwatsa. Dariyar muguntar da ba kasafai Malik ya fiye yi ba yasa ya na kama hannun Uzair da ya sanƙame a tsaye. Wayarsa ya sunkuya ya ɗaukarmai suka bar wajen. Sufyan sai da ya yi kwana biyu yana fama da zazzafan zazzaɓi jininsa har hawa ya yi, baya iya ɗaga kiran kowa, da zarar ya ji motsin ƙofa gabansa yake faɗuwa, hankalinsa baya dawowa jikinsa har sai yaga wanda zai shigo. Likita ne ya zaunar da shi yayi mai faɗan yana so ne ya kashe kanshi? Ko wani abun ake yi mai a Asibitin da yake sashi yawan fargaba? Hannu likita Sufyan ya kamo yana kuka yana bashi labarin su Malik ne suke basa tsoro. A wannan ranar daƙyar Sufyan ya nutsu ya kwantar da hankalinsa tunda likita ya yi masa alƙawarin su Malik ba zasu ƙara dawowa ba. Da yammaci ya dannawa Mahaifiyarsa kira, bayan Sumaya ta tafi Gida ta ɗan huta. Kamar tayi shekaru tana jinya haka Sufyan ya tsinkayi Muryar Mahaifiyarsa. Saitin zuciyarsa da bugunsa yake fita da ƙarfi ya dafe ya ce; "Menene yake damunki Ummeena? Kwanana biyar bani da lafiya babu wanda ya nemeni a cikinku, ashe idan ba buƙatar kuɗi ba, ba ni da wani amfani a gareku" Murmushi tayi kafin ta ce; "Sufyan ɗana na fika shiga halin jinya, domin ciwona ba irin naka bane" gyara zama Sufyan ya yi yana yi mata sannu cikin tausayawa. Kamar daga sama ya ji tace; "Ina ka jefar da makarin sirihin jikin Naila Sufyan?" Kame-kame ya farayi, sauƙin dole na zuwarmasa lokaci ɗaya. Murmushi taƙarayi ta ce; "Sufyan! Malik zai iya riskarka a koda yaushe, amma kafin na baka labari, inaso duk halin da kake ciki karka ɗara kwana biyu baka isa Birnin Abyad wajen Naila ba, duk iya yadda za kayi karka bar Naila ta isa Babban Birnin Abyad ba tare da ta amincewa komen aurenku ba, ko kwanciya ne kayi a ƙasa ka roƙi yafiyarsu, domin Naila itace Makamin tsirarka daga su Malik albarkacin matsayin da take da shi a Dhabah. Karkayi watsi da umarnina kamar yadda kayi watsi da shi ka cigaba da zama da Sumaya, idan ka isa Birnin Abyad duk abinda ka riska ka yi gaggawar kirana domin na baka wasiyyata ta ƙarshe." Tana gama faɗa ta datse kiranta. Shi dai Sufyan bai san abinda ya samesa bayan katse wayar Mahaifiyarsa ba, sai da ya wayi gari yaga Sumaya tsaye a kansa tana kuka.. Daƙyar Sufyan ya daure ya ƙara kwana ɗaya a Asibiti. A gaggauce ya sanar da Sumaya ta shirya kayanta, a kwai aikin da zaiyi a Birnin Abyad. NAILA Suna zaune da Kaka kiran Amira Customarta ya shigo wayarta. Domin Kaka taji komai a sarari ta saka Muryar Amira bayan ta ɗaga. Bayan sun Gaisa cikin zumuɗi take sanar da Naila kitsonta ya yi matuƙar jan ra'ayinsu kuma sunyi alƙawarin biyanta kuɗi masu nauyin gaske. Amma zatayi kwana biyu acan tana yi musu, sannan tayi mata bayanin tace musu tana da Kaka, sun ce zasu turo tikiti da komai mu taho tare. Kallon Kaka Naila tayi tana jiran umarninta. A hankali ta ɗaga kai alamar ta amince!!!!.....😄 Shin Sufyan zai riski Naila.??? 🔥ZINARE🔥 NAFISA ALIYU SASAAL Page 27 Bayan sun yi sallama Naila ta katse wayar, rungume kaka ta yi, ta sumbaci ƙuncinta tana dariya. Kai Kaka ta girgiza jikinta a sanyaye. Kamar Naila bata lura da sanyi da jikin Kaka ya yi ba ta ɗauko waya ina kiran layin Yasar. Da tsananin farin ciki Naila ta basa labari. "Alhamdulillah!" ya furta da daukakkiyar sauti kafin yafara tsokanarta da "Finally yokel sister ta zata leƙa Babban Birnin Abyad, har na hango idanuwanki wallahi" Kaka da ke sauraronsu dariya tasa haɗe da sakin ajjiyar zuciya. Da tsokana Naila suka ƙare waya da Yasar. Da yammaci Kaka Mallam ta kira, ta yi tsammanin zai soki zuwansu Babban Birnin Abyad amma sai taji ya furta "Alhamdulillah" ƙwarin gwiwa da addu'o'in tsari kala-kala ya ƙara bata domin acewarsa; abinda zaiyi sanadin zuwan Naila Babban Birnin Abyad ya daɗe ya na jira kuma gashi Allah ya kawo. Kafatanin kuɗin da Naila take tarawa A banki ta turawa account ɗin mutanen Yankin Tudu. Kafin dare ya yi kiraye-kirayen su sai shigowa yake yi, abun dariyar duk da wayan mutum biyu ake wayan, talauci ya hana da yawansu mallakar wayoyin hannu. Kaka bakinta kamar zai yage, banda "Ameen Ya Allah! Ameen thumma Ameen!" Babu abinda take maimatawa. Ba su daina kira suna Godiya da addu'o'i ba har sai da chajin wayar ya ƙare. A jiyar zuciya Kaka ta sauke, lokaci zuwa lokaci sai ta saki murmushin farin ciki. Kusa da ita Naila ta matso taa zauna ta ce ; "ya ya zakiji idan akace mutanen Yankin mu, sun samu farin cikin da ya fi wannan?" "Zan ji daɗi Naila sama da wanda na ji a yanzu" Kaka ta faɗa da murmushi kwance a saman fuskarta. "To ki saki ranki mu shiga Babban Birnin Abyad, In Shaa Allah ba zamu dawo ba sai da nasarar da zai kawowa Yankinmu gagarumin sauyi." Murmushi suka sakarwa juna. Da yake Yasar ya zo hutun ƙarshen Mako Gida, ziyarar bazata shi da ƴan gidansu suka kai Gidansu Naila don tayata murna. Kaka baki ta saki da ta ji abinda ya kawosu kafin da kwashe da dariya ta na cewa "wai ni kuyimin bayani wani irin arziƙi Naila zata samo a wannan Babban Birnin Abyad ɗin da kowa yake farin ciki, kar fa muje a siyar da mu" Dariya Yasar da Iyayensa suka kwashe da shi, ƙannensa da suka saba wasa da dariya su na tsokanarta. Cikin raha Yasar yake bawa Kaka labarin da zarar ta shiga Babban Birnin Abyad zatasan ko wanda ya yi wanke-wanken rana ɗaya dole ya fito da kuɗi mai tsoka. Ana raha da wasa mukayi Dinner da su Yasar. Sai dare sosai suka tafi Gida. ★washe gari su Naila suka fara kimtsa kayan da zasuyi tafiya da shi, amma har lokacin abinda yake bawa Naila mamaki shine tayaya za'ace zuwansu na kwana biyu ne zai warware ƙullin shekaru aru-arun da ko Kakanta ba haifa ba lokacin, ko dai ta Kaka kashesu za'ayi. ★washe gari daya kamar ranar tafiyarsu, tsaf Naila ta shirya cikin baƙin Abaya haka Kaka irin Abaya ɗaya suka sanya na Company ɗaya. Har Gida ƙanin Yasar ya zo ya ɗaukesu saboda tare zasu wuce da Yasar don haka sai sun fara biyawa Gidansu tukunna A dai-dai lokacin da Motarsu Naila ta gifta ta hangi Sufyan A cikin Motar da take kyautata zaton Taxi ne. Mamakin abinda ya kawoshi ta yi cikin daƙiƙu kafin na tattara lamarinsa na watsar tana danna wayarta. SUFYAN. Ƙwallane ya tararwa manyan idanuwansa da suka ƙara zama farare ƙal lokacin da mai gadi ya tabbatar masa da su Naila sun fita yanzunan ita da Kakarta. Yasan kuma ba Makaranta ta je ba, domin can ya fara biyawa akace sunyi hutu, a hankali ya nemi waje ya zauna ya zaro wayarsa. Bugu ɗaya Hindu ta ɗauka. Ko sallamarsa Hindu bata amsa ba ta ce; "Ka riski Naila?" Jiki a sanyaye ya ce; " a'a" Kuka ta saki na tsayin mintuna shida kafin ta ɗora da; "Son zuciya shine mafarin halakata, bayan tafiyarka muka gano ka yardar da maganin makarin asirin jikin Naila a gidansu kamar yadda Malamin Yankinmu ya sanar mana, maimakon Jalal da Mahaifinka su ga laifinka, sai suka juye laifin akaina, acewarsu duk nina tsiro musu da wannan musibar, sun tisani a gaba da asiri kala-kala kullum cikin ciwo nake, na je wajen Mahaifiyata Ɗayyib ya zugeta ta koroni. Sufyan mafita ɗaya ya ragemaka, ka koma bakin aikinta ka riƙi aikinka da gaskiya da amana, amma a kowani yanayi ka ji tsoron Allah kuma kaji tsoron Malik, domin baya ganinka ba kuma ya tare dakai amma ka sani yana saurararka a duk inda kake a Babban Birnin Abyad kamar yadda malamin duba ya sanarmin, a yanzu amfaninka a wajen Ɗayyib shine ka bincikomai su wanene DHAHAB? banda wannan baka da wani amfani a gareshi, su kuma su Malik suna tare da kai ne domin ganin iya gudun ruwan Jalal, kamar taku ɗaya haka kake da mutuwarka Sufyan a tsakanin Ɗayyib da su Malik, amma abinda na faɗawa Ɗayyib ya hukuntani shine wanɗanda suka ƙirƙiri sabon Dhahab ba abokanan yaƙar su ba ne, saboda suna da damar shafe Yankin Tudu da mutanen cikinta, domin ko kai kanka da kake cikin Daularsu har yanzu mai asalin Dhahab ɗin bai san dakai ba, wataƙila da ya sani da tuni ka jima da ruɓe a cikin ƙarƙashin ƙasa. Ina gayamaka dukka wannan ne domin kayi takatsantsan kamar yadda malamin duba ya sanar da ni, ina nadama Sufyan, ka yafemin. Ba lallai mu sake magana makamanciyar wannan da kai ba, ba kuma lallai ka dawo ka riskeni a raye ba, amma Allah Ne shaida bani da masaniyar komai a kan kisan su Abduh da ahalinsa." Ɗif wayar Hindu ya katse kamar dai waccen ranar. Wayar Sufyan ya bi da kallo yana zare idanuwansa da suka koma jajaye cikin ƙarajin da ya tashi dukka jijiyoyin wuyarsa da goshinsa ya na furta "Ummee! Ummee!! Ummee!!!" A lokaci ɗaya yana ƙara kiran layinta da baya shiga kwata-kwata. Hankali a tashe Mai gadin gidansu Naila ya kiran layin agajin ƙasar. Kafin su iso Sufyan ya zube ƙasa idanuwansa a juye. NAILA. Wannan hanyar da take bi da kallo tsayin shekaru yau gashi zata tunkareshi da ƙarfin ikon Allah. In Shaa Allah anan Free pages ɗin ZINARE ya tsaya. Ga waɗanda suka bibiya ba su da halin biya na gode da comments da addu'o'in ku, ga waɗanda suke da wadatar biya suma ina godiya mai tarin yawa Allah Ya bar zumunci. Kuɗin motar zuwa Babban Birnin Abyad Naira 500 ne kacal, ta wannan account ɗin Nafisat Aliyu Muhammad First Bank 3207955182 tare da tura shaidar biya ta 09132403788,08138665117. Ga masu bibiya kuma ta Arewabooks sai su ɗora. In Shaa Allah zamu cigaba da Posting ranar Monday, 4, August, 2025 da misalin ƙarfe 8:00pm Na gode🙏🏻 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 An dauko wannan littafi daga

Chapter 14 of 15