Share this page
da take gyara dogon gashin kanta mai cika da tsaho a gefe ba tace komai ba, sai ƙwallar da yayiwa ganinta yana. Ba ta da abin cewa, tunda burinta macaccen burine a zahiri, amma a baɗini rayayye ne a cikin zuciyarta tunda da shi zata mutu. Tasan ko da Sulaim ya na raye ba lallai ya so Mace irinta ba. Sai dai Mutuwarsa ya sa tanajin ƙwarin gwiwar da wataƙila ya na raye da zai iya auranta suyi rayuwar farin cikin da take hasashe. Tasan dole wata rana, irin wannan ranar zata zo domin bazata dawwama a haka ba tayi aure ba, shiyasa tayi alƙawarin sawa kanta jarumtar amsar duk Namijin daya zo mata a matsayin Mijin aure, tunda son Sulaim a cikin zuciyarta ba Ɗan adam ba ne irinta balle ta yaƙeshi. Kusa da ita Kakarta ta zo ta zauna tana kamo dukka hannayenta daga tazar gashin da takeyi. Cikin tausayin jarabawar da yake samun Nailan akai-akai ta ce; " karki kiyi kukan zuci ke kaɗai Naila ki fito da shi sarari muyi tare" Naila tanajin haka ta saki Kukan daya maƙalemata tuntuni. Sun kai minti Talatin a haka kafin Kakarta ta jata Ɗaki. Manne da juna suka zauna kan Naila kwance a samar Kafaɗarta. A hankali Kaka ta ce; "Ba na jin tsanar Sufyan a raina duk da labarin ɗabi'unsa marasa kyau da nake ji a bakin mabanbanta Mutune, sai dai ina tsoron wani irin ƙulli Hindu ta ƙulla da har zaisa ta amince ki auri Ɗanta. Hindu Ƴar masu rufin asirce a Yankinsu, dalilin haka ta ƙulla makircin da ya haramtawa Habeebah yayar Mahaifinki auren Yayaanta saboda talaucinmu, domin sana'ar Ɗinki muka gada daga Iyaye da kakanni, dalilin wannan baƙin cikin Habeebah ta rasa ranta. Babban burin Hindu a waccen lokacin shine ta auri Ɗan babban Gida, Allah Kuma ya cika mata burinta. Babban Ɗa ga Ƙanin Sarki Yankin Tudu na wacce lokacin Ɗayyib ya nuna yana sonta, har sukayi aure. Abinda yake bani mamaki da tsoro shine idan har Hindu zata guji Ɗan uwanta ya auri Habeebah saboda Talaucin mu tun a waccen zamanin, wani dalili ne zaisa yanzu ta bari Ɗan da ta haifa a cikinta jinin Sarautar Yankin Tudu a wannan zamanin da burika suka yi yawa ya aure ki duk da ƙin amincewar da mutanen Masarautar suka nu na kamar yadda na samu labari?" Naila ba tace komai ba sai ƙara ƙanƙameta da tayi da dukka hannayenta, a haka barci ya fara ɗaukarta. Sai da aka kira Sallar la'asar sannan suka miƙe, kowannen su zuciyarsa ba daɗi. Har dare ya raba Kakar Naila ta kasa runtsawa, sai kai da take girgizawa lokaci zuwa lokaci saboda zuciyarta dake hasaso mata ai gara Halayyar Hindu da Halayyar mutanen cikin Masarautar Yankin Tudu. Hannuwanta ta sarƙe waje ɗaya, Allah Ya ɗauki ran Mahmoud da Mahaifiyar Naila a tsakankanin Shekaru kaɗan kuma Allah ya jarabceta da mugayen Ƴan uwan uwa da na Uba gaba ɗaya idan aka cireta ita kaɗai ba bu wanda ya ke son Naila ko ya raɓeta sai domin buƙatar kanshi. Idan har ta zuba Ido Naila ta auri Sufyan to tabbas taci amanar Naila ba kuma zata yafewa Kanta ba, dole ta samo mafita ko da kuwa zai kaita ga gaban Sarki Hammam ne, don Masarautar Yankin Tudu tamkar Masarautar Uƙubane ga baren cikinta har ma da Ƴaƴan cikinta. Naila shafa gefenta ta yi taji ba bu Kaka. A hankali ta miƙe, a tsakar gidansu ta hangota ta na zarya. Da sanyin tafiyarta ta ƙarasa bayanta. Cikin taushin harshe ta fara magana; "Lokacin da na wayi gari ba bu Sulaim ya ƙone, na ji raɗaɗi a raina, da na zo na rasa Mahaifi sai na ƙarajin raɗaɗi amma ba irin wanda naji lokacin da na rasa Sulaim ba. Da rasa Mahaifiya sai na ƙarajin raɗaɗin da sam ba shi da haɗi da irin waɗanda na ji a baya. Abin nufi zafin rasa abu a zuƙatan mu na da alaƙa ne da yanda matsayin abun yake a wajen mu, saboda haka nasan abinda kike ji Kaaka, amma karki bari hukuncin Ubangiji ya hanaki barci wajen tunani har ki kasa neman mafita a wajen Shi. Zuciyata mai kaushi ce akan abinda ba na so Kaaka. Auren Sufyan ba ya nufin komai gareni balle har ya hanani barci, abu ɗaya na sani, idan abu mara daɗi ya sameni kuma na jure na yi haƙuri to tabbas Ubangiji Zai musanyamini da mafi alkhairinsa." Naila ta ƙarasa faɗa da siririn kuka tana ƙanƙame Kakarta. Itama Kakaa da rawar murya ta ce; "Hakane Naila, amma ki sani zanyi iya yina don samar miki mafita domin nasan Hindu dole ta na da wata manufa, Naila ba na son rasaki, ke kaɗai nake gani na ji daɗi" dukkansu kuka suka sa, su na ƙara ƙanƙame juna a haka Naila ta jata suka koma ɗaki. Sun ɗauki tsahon mintina a haka kafin Naila ta ce; " Maiyasa ki ke tsoron Masarautar Yankin Tudu, ko saboda kashe-kashen da akayi shekarun baya ne?" Kai Kaaka ta girgiza tana lumshe idanuwanta labarin asalin Masarautar kamar yadda Marigayi Mijinta babansu Mahmoud ya bata labari na dawo mata, fuskantar Naila ta yi ta ce, "kinsha tambayata wanene Abduh Dhahab su wanene ƴan uwansa ban taɓa baki labari ba, amma yau zan baki ko don ki fuskanci gaba" ```MASARAUTAR YANKIN TUDU``` Sarki Musa shine Sarki na farko da ya kawo sauyi mai girma a Yankin Tudu lokacin Mulkinsa. Daga wannan lokacin mutanen Yankin suka samu ƴanci da sauƙin abubuwa da dama, da shigowar gwamnatin sama-sama cikin lamuransu. Sarki Musaa yana da ƴaƴa da yawa Maza da Mata daga Uwaye daban-daban amma wanda ya yi zarra a cikin su kuma ya fi ƙarfin arziƙi shine ABDULYASAR MUSA DHAHAB, Abdulyasar su biyu Mahaifiyarsu ta haifa, kafin Allah Ya ɗauki ranta. Matsi daga Kishiyoyi da asirce-asirce kala-kala da har ya yi sanadiyar mutuwar ƴar uwarsa, shi kuma yake fuskanta azaba daga ɓangaren kishiyoyin Mahaifiyar su bayan ranta ya sa Mahaifinsa Musaa ɗaukeshi daga cikin Ƴan uwansa zuwa Babban Birnin Abyad wajen Abokanan Kasuwancinsa don yin ilimin zamani dana Addini. Anan Babban Birnin Abyad Abdulyasar Dhahab ya yazama Babban Ɗan kasuwa. Kasuwanci Zinare yakeyi da taimakon Bature Francis Ɗan Aminin Mahaifinsa da ya ɗorasa a hanya har yazama hamshaƙin mai Arziƙi. Dalilin wannan Kasuwanci na Zinare da ya ɗauka da matuƙar muhimmanci sama da Abokanan Kasuwancinsa ya sa suka sauya mai Suna daga Abdulyasar Musaa zuwa Abdulyasar Dhahab. Bayyanar Abdulyasar Dhahab a Yankin Tudu a matsayin hamshaƙin ɗan Kasuwa babban abin alfahari ne a wajen Mahaifinsa Sarki Musa. Bayan dawowar Abdulyasar, babu wanda yasan dalili Gaba mai ƙarfi ya sarƙe a Masarautar tsakanin ƴan uwa biyun da suke aminai wato Sarki Musa Jamil Kakan-Kakan Ɗayyib Mahaifin Sufyan. Abdulyasar bai jima da dawowa ba Allah Ya amshi ran Mahaifinsa Sarki Musa. A waccen lokacin anso naɗa Abdulyasar a matsayin magajin Mahaifinsa ko dan ƙarfin arziƙinsa amma ya nuna bayaso da suka takura ya tattara ya gudu na ɗan lokaci. Dole aka naɗa Yaya ga Sarki Musaa Mahaifin Sarki Hammam. Ƙarfin arziƙin Abdulyasar Dhahab da taimakon shi ga Talakawa Yankin sai ya shafe sunan kowa a Masarautar su kamar shine Sarkin Yankin. Lamarin ya na sosa ransu matuƙa, wannan dalilin yasa suka fara kaiwa dukiyarsa hari ta kowacce siga tare da alƙawarin kaishi ƙasa ko ta halin ƙaƙa. Su na cikin wannan yanayin matar Abdulyasar Dhahab ya aura bayan dawowarsa ta haifa ɗa Namiji Ubaidullah. Da taimakon Iyalinshi bayan ta haihu saboda kwaɗayin abin duniyar da sukayi alƙawarin za su ba ta na kaso maiyawa, ta taimaka musu suka kai Abdulyasar ƙasa, duk da haka Abdulyasar Dhahab bai bar rayuwar Ɗanshi Ubaidu ya lalace kamar yanda suka so ba, ya miƙa amanarshi hannunshi abokannan kasuwancinshi suka tafi da shi can wata nahiyar, shi kuma ya cigaba da gwagwarmaya da azzaluman Masarautar su. Ubaidu bai tashi dawowa Yankin Tudu ba sai da kowa ya fara mantawa da shi, da kyakkyawar Matarsa da Ɗansa mai kama da shi Abdullah(Abduh Dhahab) ya dawo, lokacin Abduh har zama ƙaton saurayi, har da ƴar Yayar Matarshi Aysha da Mahaifiyarta ta mutu suka dawo Yankin Tudu. Ga dukiya mai tarin yawa da Ubaidu Dhahab ya dawo da shi. Dawowar Ubaidu Dhahab da dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar da babu ma su irin siffarta a Yankin Tudu ya yi matuƙar sosa ran maƙiya Masarautar. Maimakon su yaba sai suka hau kushewa da aibata Ubaidu Dhahab ya auro bare mai kyan da zata kashe shi ta kwashe dukiyar da ya tara. Duk Abdulyasar na sane da su sai dai bai ce komai ba, sai jikansa Abdullah da yaja a jiki. Sanin matsawar Abdulyasar ya na raye ba zai barsu su kai Ubaidu ƙasa kamar yadda su ka kaishi ba, ya sa suka fara shayar da shi guba a sirrince ta hanyar amintacciyar hadimarshi. Cikin ruwan sanyi suka kashe Abdulyasar ba tare da kowa ya ankara ba, sai daga baya Mutanen gari suka ji ƙishin-ƙishin. Mutuwar Abdulyasar ba iya Ubaidu da Iyalansa kawai ya taɓa ba har da mutanen gari, saboda alkhairinsa. Bayan wani lokaci suka dawo kan Ubaidu. Duk da sun kashe Abdulyasar sun kasa kai Ubaidu ƙasa ta cikin ruwan sanyi kamar Mahaifinsa, sun tusawa ɗanshi Abdullah ƴaƴansu ya aura yaƙi yarda, saboda alƙawarin auren da ke tsakanin Abdullah da ƴar Yayar Mahaifiyarsa Aysha da suka taho tare da ita. Babu yadda su ka iya, haka suka haƙura Abdullah ya auri Aysha. Daga wannan lokacin ne suka ƙara duƙufa wajen ganin bayan Ubaidu ko ta halin ƙaƙa, da suka ga sun kasa, sai suka bishi har Gida suka yi mai kisan gillar da ya tashi hankalin mutanen Yankin. A lokacin Iyalinshi Mahaifiyar Abduh Dhahab Nanaah tayi ƙururuwar abi mata haƙƙinta amma babu wanda ya saurareta sai ɗanta Abduh Dhahab da ya tayata fafutuka, sai dai shima a lokacin ba shi ƙarfin yin komai. Baƙin cikin hakan yasa ta tattara kayanta ta bar Yankin Tudu aka nemeta aka rasa. Shima Abduh tattara komai nashi ya yi ya bar masaurata zuwa Gidan ɗaya daga cikin gidan da Mahaifinsa ya gada a wajen Abdulyasar Dhahab tsakiyar Talakawa. Daga wannan lokaci Abduh Dhahab ya barrata kansa da masaraurar Yankin Tudu, ya dawo kamar kowanni ɗan gari. Ba bu tsinke daga dukiyar Ubaidu da ba su ga bayanshi ba. Duk da wannan abubuwan da suka faru Ɗayyib da yake nunamai tsananin ƙauna ya na tare da shi. A sabuwar Unguwar da Abduh ya dawo ya yi sababbun Amanai, Mallam, Mahaifin Malik da kuma Mahaifinki Mahmoud, duk da sun girmewa juna a shekaru hakan bai hana amintarsu saboda hali da ya zo ɗaya. Abduh ya na da buri mai zurfi, da kuma kishin Yankinsa, ya na son ya kawowa Yankinsa cigaba, kamar yadda Kakanshi da Mahaifinshi sukayi yunƙuri Allah bai ƙaddara ba. Wannan dalilin yasa ya fara tunanin mai zai ƙirƙiro sabo da zai kawowa Yankinsa cigaban da kowa zai amfana??? Abduh ya share sama da wata ya na tunanin abinda zai ƙirƙiro amma ya kasa samun mafita. A wani dare Ubangiji ya sanya masa tunanin ƙirƙirar Tukwane. To amma ai akwai mutane ma su ƙera Tukwane da yawa, ƙirƙirarsu kaɗai ba zai zama wani sabon abu da zai ja hankalin mutane ba, dole sai ya haɗa da wani sabon abinda mutane ba su san da shi ba. Har ya gama saƙe-saƙensa a wannan rana bai samu mafita ba. ★washe gari har Iyalinsa Aysha da ke ɗauke da tsohon ciki ya tuntuɓa itama ba bu wani basirar da ya zo mata. A haka Abduh ya ƙara shafe wata ya na tunanin abinda zai sa Tukwanensa su zama ma su jan ra'ayi da kwaɗayin mallakar su a wajen Mutane. Ya na cikin wannan tunanin sana'ar Kakanninsa na Zinare ya faɗo mai. Mai zai hana ya yi wa nashi Tukwanen laƙabi da Tukwanen Zinare, ya tambayi kansa, hakan zai zama sabon abu a wajen mutane, kuma abin rububi domin ko da mutum ba shi da niyyar siya zai so ya ga yaya Tukwanen Zinaren su ke, daganan wataƙila yaji sun yi mai ya siya. Da ya yi shawara da iyalinsa ɗari bisa ɗari ta amince, amma daga baya da ta fuskanci ɗan abinda ya rage mu su suke samu su ci, su sha Abduh yakeson kwashewa ya kafa sana'ar Tukwane sai ta nuna sam bata yarda ba, dama can lallaɓawa takeyi ta gaji da talaucin da suke ciki shine yanzu zai ƙara kwashe abinda ya rage ya yi jarin Tukwane da shi. Da lallaɓawa da kuma nuna mata gagarumin nasarar da zasu samu, cike da yaƙini Aysha ta amincewa Abduh. Da zallar basirar ƙere-ƙeren da ya koya a wajen a Abokansa na bakin Kasuwar Iyakar Yankin Tudu, Abduh ya ƙera Tukwanen da ya yiwa laƙabi da Tukwanen ZINARE zuciyarsa cike da ƙwarin gwiwa da kuma yaƙinin ko bai siyar ba a take wata rana zai siyar. Lokacin da mutanen Yankin suka ga Tukwanen da Abduh ya ƙera dariya suka bushe da shi haɗe da faɗin " Abduh ya zo da abinda ba shi da wani amfani zai zallar yaudara, shikenan dan Kakansa da mahaifinsa sunyi kasuwancin ZINARE sunyi arziƙi, sai ya ce shima sai ya yi, to ai zasu ga waɗanda za su siyi waɗannan ruɓaɓɓun Tukwanen na sa, wai Tukwanen ZINARE tunda ya ɗauka kowa Mahaukaci ne irinsa." Tsaf surutansu yake dawowa kunnen Abduh, ya na kuma sukarsa, sai dai ba shi zaisa ya ja da baya ba, sana'ar Tukwanen Zinare ba gudu ba ja da baya. A ranar ta farko da Abduh Dhahab ya fita da Tukwanen Zinare Kasuwar maƙotan Yankinsu ba bu wanda ya siya, da ya tarkatosu ya dawo Gida sai mutanen Yankin suka dinga yi masa dariya. Matarshi Aysha da baƙin ciki ta kwana, dalilin haka ta tashi da naƙuda washe gari. A hannun mai maganin gargajiya Aysha ta haifi Sulaim. Kallon fuskar jaririn kaɗai ƙarfin gwiwa yake ƙarawa Abduh Dhahab haka Aysha domin bai bar komai na Kakarshi Mahaifiyar Abduh Nanaah da basusan inda take ba, kamar ita ta haifeshi. Da yawa idan suka shigo Barka da hassadar kyan jaririn suke barin Gidan. Tsahon lokaci Abduh Dhahab ya cigaba da gwagwarmayar fita da Tukwanensa Kasuwanni ba tare da gajiyawa ko ƙosawaba. A haka ya shafe shekaru biyu ya na wannan bautar babu wani cinikin arziƙi. Matarshi Aysha ta sha yunƙurin guduwa saboda talauci ya na lallaɓata ta haƙura. A cikon shekaru na biyar ɗin da ya yi yana bautar bin Kasuwanni Allah Ya amshi roƙonsa aka siye Tukwanensa tsaf, har da neman ƙari. Addireshin Yankin Tudu yake ta basu tare da yi musu alƙawarin ƙera wasu Tukwanen ma su yawa ga waɗanda suka nuna su na son sari domin siyarwa. Lokaci da rana Abduh Dhahab ya tsayar mu su, tare da alƙawarin ba za su bar Yankin Tudu ba tare da iya adadin Tukwanen Zinaren da suke buƙata ba. Da tsananin farin ciki ya nufo Gida, sai dai ya na zuwa ya tarar Aysha ta gudu, sai Sulaim da ya tarar da takarda a hannu. Abduh ya yi kuka shi da Ɗanshi kafin su haƙura su fuskanci rayuwarsu da sam babu walwala a ciki. Ba ji ba gani Abduh ya ke ƙera Tukwane. Ranar da ya rage saura kwana biyu ranar da ya yi alƙawarin kafa Kasuwar Tukwanen Zinare ya cika bai runtsa ba kwana ya yi kaiwa Allah kukansa.... Wane fata kuke yiwa Abduh Dhahab da masu irin zuciyarsa??? SASAAL 09 ★Washe gari Abduh ya tuntuɓi Abokanansa su Ɗayyib, Mahmoud( Mahaifin Naila), Mallam da Mahaifin Malik su fito da Kayan sana'ar su idan da rabo sai su sayar batare da sunyi wahalar bin Kasuwanni da suka saba ba. Ga mamakin Abduh babu wanda ya yi yunƙurin tankamai, kamar ma ba su san abinda ya ke faɗa ba. Kunya suke ji su fitar da Kayansu azo ba'a siya ba ayi mu su dariya. Mahmoud Madinki ne, kayan yara da na manya dinkakku yake bi Kasuwanni yana siyarwa, Mallam kuma Qur'ani da littafan addinin musulunci yake fansarwa, Mahaifin Malik kuma maganin gargajiya yake siyarwa. Ɗayyib ne kawai baya sana'ar hannu taƙamaimai sai abinda ba'a rasa ba. Da Abduh ya fuskanci inda suka dosa sai ya nuna kamar bai damu ba, amma har cikin zuciyarsa baiji daɗi ba. Da yaƙini Abduh ya share ƙaton filin Ubaidu Mahaifinsa da kaɗai ya rage filinsa basu wawashe ba, ya jere Tukwanen da ya ƙera. A gefe ya shimfiɗa buhu shi da Sulaim suka zauna bakinshi bai gajiya ba da ambaton Sunan Allah. Har lokaci ya fara tafiya babu wanda ya zo daga waɗanda sukayi alƙawarin zuwa. Mutanen Yankin sai suka fara leƙoshi su na dariya, bai nuna ya gansu ba, balle su gane abinda suke yi mai yana sukar zuciyarsa. Yunwa da ƙishi ne yasa Abduh Dhahab yunƙurin miƙewa tunda yasan ko yunwa zai kashe Sulaim ba zai yi magana ba. Har ya miƙe hayaniyar mutane daga nesa ya dakatar da shi. Fuskokin mutane ƙalilan ya gane a cikinsu amma ragowar duk yawon kasuwannin da ya gamayi bai taɓa ganin su ba. Waɗanda sukayi alƙawarin zuwa siyan Tukwanensa ne, bakin Abduh kamar zai yage wajen tarbar su, kafin shuɗewar hour ɗaya sun yi ciniki sun siye Tukwanensa gaba ɗaya. Mutum ɗaya a cikin su ne ya tambayi ina zai samu fansar Qur'anin akan sari?. Abduh Dhahab manta abinda su Mallam suka yimasa ya yi, ya nufi hanyar Gidajensu da sauri kamar zai tashi sama, batare da tunanin za'a iya sace masa Ɗansa ko dukka kuɗin cinikin da ya yi ya zuba a ƙarƙashin buhu ba, shi dai burinsa ya kira Abokansa ayi musu ciniki. Jiki na rawa, Mahmoud da Mallam da Mahaifin Malik suka nufo Kasuwar Tukwanen Zinare da Kayansu. Da rububi akan siye kayan har sai da suka ƙara komawa Gida suka ɗebo wasu. Mahaifin Malik ne kawai maganin gargajiyarsa ta ɗan yi ragowa. Bayan Kasuwa ta tashi kowa ya adana kuɗinsa bakin kowannen su a washe, sai suka ɗaga Abduh Dhahab sama suna dariya jindaɗi da waƙeshi da waƙe kala-kalan da ke nuna jarumtarsa da dagiyarsa. Daga wannan rana Abduh Dhahab ya kafa Kasuwar Tukwanen ZINAREN da kafatanin mutanen Yankin su ke amfana da shi. Bayan komai ya dai-daita Abduh Dhahab ya fita wani Yankin ya auro Mairam. A dalilin Mairam Mahmoud ya ga Mahaifiyar Naila ya aura saboda yawan zuwa Gidan da takeyi, kafin daga baya Abduh Dhahab ya haramtawa Mairam shiga ko ina, don dalilin shigarta Gidan Mahmoud ne aka fara samun masu zugata, ta dinga yi masa Satar kuɗi tun da baya bata sai tayasa aiki.. Halaccin Abduh Dhahab yasa Mahaifin Malik ba shi Malik ya dinga yi masa hidima, tunda lokacin Sulaim ba shi da ƙarfin da zai taimakawa Abduh da wasu hidindimun. A sirrince ba tare da sanin kowa ba Abduh Dhahab ya ƙirƙiri Makarantun boko da na Islama da Asibitoci a Yankin da taimakon abokanan kasuwancinsa na Babban Birnin Abyad, amma babu wanda ya sani nima Mahmoud ne ya sanar da ni ko Ɗayyib bai sani ba. Ya damƙa amanar komai a hannun Mallam ne saboda shi kaɗai ne mai ƴan uwa masu ƙarfin arziƙi a Babban Birnin Abyad da Sarki Hammam da mutanen gari zasu gamsu taimakon daga garesu yake, amma a baɗini Mallam ko ƙofar Gidajen Ƴan uwan nasa bashi da matsayin zuwa. Abduh Dhahab ya yi hakane don kawar da idon mutanen Masarautarsu akan lamuransa duk da sun san yana samun kuɗi amma ba su isa su ƙiyasta iya adadin abinda yake samu ba. Abin mamakin duk da wannan girman halaccin na Abduh Dhahab ga mutanen Yankinsa bai sa sun ɗagamai ƙafa ba, a wasu lokutan sai su ce "ai Mahaukaci ne, banda Mahaukaci wanene zai zaɓi sadaukar da iya Gadon da Mahaifinsa ya barmai domin ya yi suna ya burge mutanen gari?" Babu wasu kalmomin su na ɓatanci da baya dawomai amma bai taɓa damuwa ba domin yasan a sannu zasu gane ranarsa. Mutanen Yankin Tudu a ɓangaren halayya mutane ne ma su son kansu, butulci da rashin damuwa da damuwar Ɗan uwansu. A ɓangaren siffa kuma Usul ɗinsu suna da kyan fuska da haske fata, manyan idanuwa buɗaɗɗu, yalwataccen kashin kaa da kaurin jiki, mafi akasarinsu ba su da tsaho daga gajeru masu faɗi da jiki sai masu matsakaicin tsaho da kaurin jiki, idan kaga mutum da siffa saɓanin wannan to Mahaifiyarsa ko Mahaifinsa ba asalin ɗan Yankin Tudu bane. Kamar dai ke Naila baki da irin siffarsu sai irin gashin kansu haka Sufyan ɗan wajen Ɗayyib shima ba laifin yana da tsaho da ginannan jiki amma duk da haka ya sirko da irin ƙibarsu da idanuwansu, dukka saɓanin Sulaim ku ke domin Sulaim ba shi da siffa ɗaya na mutane Yankin tudu kalar fatarsa idanuwansa, tsayuwar ginannen jikinsa tun yana yaro dukka ba irin nasu bane, shi yasa suke ganin a kaf faɗin Yankin babu Matashin da daya girma a raye zai shafe Tarihin duk wani Matashi ɗan ƙwalisa a Yankin Tudu. Sai shima Malik irin hasken fatarsu da idanuwansu ya ɗauko amma sam siffarsa tsayuwarsa kamar sun aroshi daga Mahaifiyar Abduh Nanaah da Sulaim yake kama da ita. Wannan dalilin yasa Abduh ya ke son Malik har ranar da waɗanda ba'asan su waye ba, sukayi nasarar kaishi ƙasa. Wannan shine asalin labarin Abduh Dhahab da Masarautar Yankin Tudu, sai kuma abubuwan da suke waɗanda ba ni da sani akai ```DOWAWAR LABARI``` Idanuwan Naila da suka ɗanyi jaa ta lumshe tana ƙara ƙanƙame hannun Kaka, itama Kaka ƙara ƙanƙame hannun Naila tayi cikin kuka ta cigaba da magana; "Su na kashe junansu abisa son zuciyarsu, ba tare da wani haƙƙi ba. Ba su taɓa nuna ƙin bare ya shigo cikinsu kai tsaye ba sai a kanki Naila, saboda talaucinmu. Shiyasa nakejin tsoro da fargabar kar kema su kashemin ke a banza, domin bani da ƙarfin gwiwa da dukiyar da zan jaa da su." Da ƙarfin gwiwa Naila ta girgiza mata kai tana rungumeta cikin taushin lafazi ta ce; "bazan mutu ba har sai lokacina ya yi, idan kuma lokacina ya yi ko ba na cikin Masarautar Yankin Tudu Allah zai ɗauki raina Kaka, batun cewa a'a ko ki kai kanki gaban Sarki Hammam abisa ƙin amincewarki duk mu haƙura mu gayawa Allah, In Sha Allahu zai sauƙaƙa mana." Da haka sukayi barci hannunsu ƙanƙame da na juna. ★washe gari Kakar Naila ta tattauna da Ƴan uwan Mahaifin Naila kan su bawa Iyayen Sufyan haƙuri Naila ta kammala Makarantar sakandare tunda saura wata bakwai. Da yake babu Allah a lamuransu sai suka taso mata bakinsu a haɗe, acewarsu su kansu basu da tacewa duk abinda Shugaba Ɗayyib ya yanke dole shi zasu haƙura su bi. Zuciyar Kakar Naila na tafasa ta nufi Gidan su Sufyan kai tsaye. Bayan sun gaisa Kaka ta koro bayanin abinda ke tafe da ita.. Wani irin kallo Hindu take yimata da soyayyun idanuwanta da suke ƙananu a tsaitsaye farare ƙal. Murmushi ta yi kafin ta ce; "Haba Ummu Habeebah(Kaka) ai da baki zo da kanki ba, Ni dai ina neman afuwarki akan abinda ya faru shekarun baya, sannan na fuskanceki amma bazan iya yanke hukunciba tunda Maigida Jalal( Mahaifin Ɗayyib) shi ya tura mutane da kanshi nemarwa Sufyan auren Naila. Ki bari Mahaifin Sufyan ya dawo In Shaa Allahu zan isar da saƙonki" godiya Kaka tayi mata tana yunƙurin miƙewa. Da sauri Hindu ta dakatar da ita ta hanyar faɗin; "Bari na kawo miki abun motsa baki mana" kai Kaka ta girgiza haɗe da cewa; "bakomai Hindu, fuskantata da kikayi yafi komai yimin daɗi, Allah Ya ƙara arziƙi" duk da haka Hindu bata bar Kaka tabar Gidan batare da abinda tayi niyyar bata ba. Dama kuma tuntuni ta tanadeshi ne domin tasan har gaban abadan Mahaifiyar Habeebah bazata taɓa ƙaunarta ba. Bayan Ɗayyib ya dawo Ko zancen Hindu bata yi masa ba, sai shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad da suke yi domin duba Gidan da Sufyan zai zauna da Naila saboda a gaggauce takeson ayi komai duniya tasan tasan da zaman ɗanta. A ɓangaren Kakar Naila bayan ta koma Gida ajjiye Tufar da Hindu ta bata tayi a gefe, ta na bawa Naila labarin abinda ya faru. Murmushi mai tsayawa a iya saman laɓɓa Naila ta saki zuciyarta a raunane. Da nishaɗi Kaka ta ce "kinji daɗi ko ba ki ji ba Naila?" Naila sai da haɗiye abinda take ji sannan ta ce "na ji daɗi Kaka Allah Ya

Chapter 5 of 15