Share this page
tayi ƙorafi sai ya ce mezatayi da sutura ita da ba fita na ke yi ba, kitso kawai yake zuwa, shi dama kuma ba ya son idan zataje yiwa Mutane kitso ta yi kwalliya kar wani ya ƙwacemasa ita, shi ya fi son ya ganta ta yi ado da kayan da ta taho da shi saboda hakan na tunamai da Yankinsu. A kwana a tashi Ruwaida ta fuskanci Sufyan cutar Naila yake yi domin kuwa duk ta rame tayi duhu saboda ƙewa da damuwa. Shawarar Naila ta fara ɓoye kuɗinta Ruwaida taba ta, idan sun taru za ta rakata ta siyi suturun sawa, idan Sufyan ya tambayeta ina ta samo ta ce ita ta siyamata da kuɗinta. Bayan kwana biyu Sufyan ya jera kwanaki uku ya na tambayar Naila kuɗi sai ta ce babu, da ya ga dai dagaske ta ke babu kuma aljihunsa ya yi ƙasa sai titsiyeta da tambayoyi, ƙarshe tana Madafi tana girki ya shiga ɗakinta ya bincike har sai da ya samu kuɗin da take ɓoyewa. Ta na tsaye ya shigo Madafi da kuɗin a hannunshi kafin ta yi magana ya kwasheta da mari cikin zafin rai yake masifar yasan Ruwaida ce take zugata, wallahi ta ci darajar itace take naimomata customers da sai ya ci mutuncinta ya wulaƙantata. Sufyan ya yi tunanin ganin sauyi ko wani gagarumin ɓaci rai a saman fuskar Naila, amma sai ya ga akasin haka kamar baiyimata komai ba, cikin neman magana ya ce "gaba zakiyi da ni saboda nayi miki faɗa ko,? to wai Naila saboda wa nakeyin wannan karatunnan? Saboda ke nake da ƴaƴan da zamu haifa, Naila saboda tsoron kar mu zo mu tara ƴaƴa babu kuɗin kula da su yasa kikaga na daure har yau ban kusanceki ba, duk wannan bai sa ki tausayamin ba haba Naila sai a fara zugaki ki na ɓoyemin samunki." Murmushin mai ciwo Naila ta yi ta kalli fuskarshi ta ce; "matacce ai ba shi da ran yin rigima da rayayye, idan kuma kasan yau ai ba kasan gobe ba, dalilin baiwar kitson da Allah Ya bani yasa ku ka kawoni Birnin Abyad, ga shi kana mora har ka na da ƙarfin halin yin iko da shi. Ba ni da ƙarfin yi ma iyaka amma lokaci zai yi maka a yanayin da baka taɓa tsammani ba"....✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 ( ```The Gripping family saga with high Caliber) ``` SASAAL 14 Sufyan sak ya yi a tsaye har Naila ta gama magana ya kasa ce mata komai, har na ɓacewa ganinsa. Bayan tafiyarta kafaɗarsa ya ɗaga A ganinsa mai zai jiyewa takaici? kuɗi ne dai dole ya karɓesu saboda da su ya dogara. NAILA ★washe gari kamar ko yaushe bata koma barci ba, sai da ta gama Breakfast. Ko da koma barci ta farka misalin tara na safe, ta fito Parlo a yadda ta jera abincin haka na samesa Sufyan bai ci ba. Tasan ya yi hakane saboda kuɗaɗents da ya karɓe, a karon farko hawayen takaicinsa su ka zubomata, bata tsawaita zubda hawayenta ba, bata kuma hana cikina abinci ba. Bayan ta ci na ƙoshi na fito harabar Gidan shan iska. Yasar ta hango ya na yunƙurin fitowa, da farko ta yi niyyar guduwa saboda ba ta son haɗuwarsu, amma da na tuna taimakon da ya yi msta ranar da accident ɗin sashen Ruwaida ya faru sai ta jirkirta. Yasar manazarcin halayyar Ɗan adam ne, kuma likita a babban Asibitin Birnin Abyad. Gaishesa kawai ta yi ta matsar da kanta gefe. Matsowarsa kusa da ita ya sa ta juyo tana zare ido. Yadda ta zare ido na ne ya sa shu saki dariya ya na shafa tarin sumar kanshi da ya tattara wajen ɗaya ya ɗaure kamar Mace. Ba bu zato ta ji ya ce; "Maimakon zama haka mai zai hana Mijinki ya naima miki gurbin karatu a jami'ar su, idan ma ba shi da hali ki naimi izininsa ni zan biya miki Fisabilillah." kalamansa sun wanke dattin da ya jima danƙare a cikin ƙwaƙwalwar Naila na tsahon lokaci, maganarsa abun dubawa ne a gareta, kuma shawara ne mai kyau amma tuna Sufyan ya sa ta ce; "mijina ba zai yarjemin ba" ta faɗa da murya da ya bayyana rauninta. Yasar ya kai wa su daƙiƙu ya na kallonta kafin ya murmusa da cewa; "idan Mijinki ya na da sauƙin kishin da zai barki zuwa Gidajen da maza da mata su ke rayuwa, kamar Campus ɗin su Ruwaida kiyiwa Ɗalibai kitso, to babu dalilin da zai sa ya hanaki naiman ilimi. Menene amfanin neman da ba zamu gina gobenmu da shi ba?" Kamar talabijin haka Naila ta zubawa fuskar Yasar mai tsananin haske da kyau ido, ba haskensa da kyansa ta ke kallo ba, gaskiyar da ya faɗa take gani a saman fuskarsa. YASAR Duk da ya san Naila ta gamsu ɗari bisa ɗari kuma ta yarda da maganarsa amma tana kwakwanton naiman mafita sai ya ƙara ce mata; "ga hanya mafi sauƙin warwarewa kanki komai, ki fara naiman izininsa a kan na ce zan biyaki kuɗi mai yawa ki kitsamin kaina, ki ji mai zai ce, idan ya ce a'a sai ki san dabarabar da za kiyi ki tambayesa izinin naimar miki jami'a, idan kuma ya ce eh, kin samu hanyar da zaki tafi Jami'a cikin sauƙi, ki nutsu ki warware komai dalla-dalla za ki fahimce ni da kyau". Cikin nauyin baki Naila ta yi mai godia. Har ya ɓacewa ganinta bata daina kallon hanyar da yabi ba. Yinin ranar a tunani ta ƙaresa domin ta kasa yarda Sufyan ba ya kishinta, shi da ya ce kishin ta ne ya ke hanashi siyamata kaya kar wa su, su ga kyanta, duk da tasan ba ya sonta sosai kamar kuɗin da na ke samu, amma ta yarda da zancensa. Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa ta miƙe ta ƙarayin wanka, kayan dai da ta taho da su daga Yankinmu ta saka, duk sun ƙode sun jeme. SUFYAN; Sufyan kayan ciye-ciye da ice cream kala-kala ya siya mu su shi da Sumaya, har sun dawo sunyi lecture ya tuna rashin siyawa Naila kaya zai ƙara tunzura ta, har ta ɓullo da wata dabarar tara kuɗin a inda ba zai gani ba balle ya ƙwata, musamman wajen Ruwaida, kuma siya mata kayan zai kawar da tunanin ba ya sonta ba ya son farin cikinta a ranta. Bai naimi rakiyar Sumaya ba ya tafi, kusan rabin kuɗin da ya ɗaukemata ya siyamata kaya da su ba dan ransa ya so ba. Da ya dawo Makaranta da Kayan Ƙiri-ƙiri Sumaya ta nuna ƙishinta, ranar ko ƴar hirar da su ke yi a kan hanya ba su yi ba, bakinta a gaba take tuƙi, takaici da kishi na nuƙurƙusarta. Ko da ta sauke Sufyan kafin ya yi mata sallama ta figi mashin ɗin ta. Jiki a sanyaye Sufyan ya shigo gida. Da Sufyan ya shigo bai bawa Naila kayan da ya siyo ba, ɗakinsa ya wuce da kayan ransa fal kokwanton ko dai gobe ya kaiwa Sumaya, saboda bai ji daɗin yadda su ka rabu ba. Jikinsa ba kuzari ya tsakuri abincin da ta girka, itama Naila tata fuskar sam ba fara'a. Bayan ta tabbatar ya huta ta sako masa hirar neman izininsa zata yiwa Yasar moƙocinsu kitso tare da bayyana masa irin kuɗin da ya ce zai ba ta. Ga mamakinta Sufyan ko alamar banbanci tsakanin jinsi Namiji da na Mace bai nuna ba yace ai neman kuɗi ne babu Matsala. Zuciyarta da jinina na gudana da sauri-da sauri ta tambayesa izinin komawa Makaranta, kai tsaye ya ce mata; "ba ni da kuɗi, ko kuɗin da kike ba ni kike yiwa baƙin ciki Naila?" Muryarta ta na rawar kukan da ya tahomata tana ƙoƙarin dannewa ta ce; "ance ba sai ka biya ba za'a samomin Scholarship" kamar an tsikaresa haka ya miƙe ya na masifa kamar zai taune harshensa. Sai da ta bari ya gama kumfar bakinsa, sannan ta miƙe haɗe da cewa; "zuwa Makaranta da sunan naiman ilimi sai zama aji ɗaya da Maza, amma kowa da Mazauninsa, ba bu kuma tilas ɗin mu'amalantar juna, iskanci ne. Amma zuwa Gidan da Maza su ke rayuwa da sunan sana'a haɗe da kama kansu na kitsa saboda za su bani kuɗi mai yawa shi ba Iskanci ba ne Sana'a ce ko? Idan ka rayu a matsayin miji a gareni sannan ka zaɓi zaluntata da duƙushemin rayuwa wacce riba za ka samu Sufyan?" Ƙasa ya yi da kansa, ganin ba shi da mafita sai ya fara lallashinta haɗe da garzayawa ɗakinsa a hanzarce ya kwaso kayan da ya siyo mata yake kokwanton ba ta. Kamar zai yi kuka haka yake magiyar gwadata ya ke yi kamar yadda akasarin Maza suke yaudarar Mata da sunan gwaji. A cewarsa idan banda gwadata ya ke yi ta ya ya zai yarda ta yiwa Yasar kitso sai ka ce ba Musulmi ba, shi kansa Yasar ɗin ai ba mutumin ƙwarai ba ne, idan ban da haka ta yaya zai ce Matar aure ta yi mai kitso. Da ire-iren waɗannan kalaman ya so yaudarata. Ba bu daɗin bakinsa ɗaya da ya samu gurbi a cikin zuciyar Naila, amma ta ji daɗin kayan da ya siyomata. Kamar komai ya wuce haka ta nunamai, domin ya ƙara shashantar da ita sai ya fara ragewa kanshi zafi kamar yadda ya saba. Bayan ta koma daƙina kuka da ya sanyamsta ciwon kai ta yi, ba ta da wanda zats buɗewa zuciyarta ta zazzage masa dukka damuwarta sai dai tasha kukanta ita ɗaya a ɗaki. ★washe gari da Sufyan zai fita Makaranta Cikin dabara ya ke ja mata kunnen rage mu'amalantar Ruwaida idan ba haka ba zata kaita ta baro. Abinda bai sani ba Kalaman Ruwaida ga Naila ma su taushi ne haka zuciyarta da niyyarta dukkan ma su kyau ne a kan Naila, idan ma cuta ce Ruwaida ta rasa wacce zata cuta sai irin Naila. Naila Ba ta ce mai kanzil ba har ya bar Gidan. Da ga ranar ta ƙauracewa zaman harabar Gidan saboda Yasar, idan ka ganta a waje to Ruwaida ce ta haɗata da customer, ko kitso idan aka biyota Gida a living room ta ke zama su yi. A hankali a hankali Naila ta fara rama mai busar da Mutum tambayar duniya idan Ruwaida ta yi mata sai na ce mata"ba komai". Sufyan ya haramtamata gaisawa da Kaka kullum sai ya ce ya kira Ɗayyib Mahaifinsa ba ya samu. A kwana a tashi cikin hikimar Ubangiji suka shekara ɗaya da rabi a Birnin Abyad. A ɓangaren Sufyan ya canza ya ƙara haske ya yi kyau sak mazaunin Birnin Abyad, saɓanin Naila ta da ta bushe ta rame idan ta yi dariya sai haƙora su cikamata fuska. Ta ƙara samun customers wa su ta je Gida tayi musu wa su kuma su biyota Gida, duk tarin kuɗin da take samu Sufyan ne yake kwashewa domin akwai ranar da ta ɓoye kuɗi a wajen Ruwaida, har ya titsiyeta da tambaya. Bata ɓoye masa su na wajen Ruwaida ba, a ranar sai da ya yi mata dukkan da ya hanata motsi. Bayan ya fita Makaranta ya kira Mahaifinsa ya yi mai bayani. A take shima ya sanar da Uban Gidansa, washe gari jami'an tsaro mata suka zo har Gidan su ka jawa Ruwaida kunne haɗe da karɓe kuɗin da na ke tarawa, bayannan su ka yi mata tsakani da ni. Ruwaida ta na tsoron abinda zai taɓa karatunta. Ba tare da ta nemi ƙara ganin Naila ko tambaya ta sane abinda aka yi mata ko ba na sane ba, ta tattara Kayanta ta tashi bar Gidan, sai ma su kwashe kayanta kawai Naila ta gani. Tun da ga lokacin sai Naila ta ƙara zama kamar sha-sha-sha. Ga shi Yasar tun da ya ya bata shawara na yi watsi da shi har take gudun haɗuwa da shi ya tattara lamarinta ya watsar ko haɗuwa sukayi ta gaishesa daƙyar ya ke amsawa. Yasar bai ƙara tsanar Naila ba sai da ya ji labarin abin da ya faru tsakanin Sufyan da Ruwaida. Daga wannan ranar ko gaishesa Naila ta yi baya amsawa. Abubuwan da su ka faru da Naila sun sa ta yi losing hope, sai ta ke ganin sakarwa Sufyan komai ya yi iyakacin zaluncin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwata shi kawai ya fiyemata sauƙi. Da ga wannan dukan farkon da Sufyan ya yimata ya mayar da ita kamar jaka, akan abu ƙalilan sai ya zaneta, ɗai-ɗaikun ranaku ne baya kai hannunsa jikinta, ga dabaru da ya ɓullo da shi, haka zai sakamata videon tsaraicin wa su ya ce ta nutsu na kalla irinsa zata yimai. Da farko gardamar bazan yi ba ta yi mai, ai kuwa ya kamata ya yi mata dukan tsiya, abisa tilas ɗin rashin zaɓi ta fara bin umarnin Sufyan. A haka su ka ƙara shafe shekara ɗaya cikin uƙuba da tsanani, ba ta gaisawa da Kaka, ba ta da abokin hira, domin wacce ta tare a ɓangaren Ruwaida sai da Yasar ya ja mata kunnen kar ta kuskura ta kula Naila idan ba haka ba zan ƙulla mata sharrin da Allah ne Kaɗai zai wanke ta. Da kuɗin guminta Sufyan ya ke rayuwa, da kuɗin guminta ya ke tari a Bankin da Ubangidan mahaifinsa ya yi mai jagora ya buɗe, da kuma kuɗin guminta ya ke yiwa budurwasa Sumaya siyayya. Ita kuma ko cikakken Suturar sawa ba ta da shi, idan ta yi dariya tsananin munin ta sai ya bayyana saboda rashin namar fuska har wani yamushewa fatatar ta yi. Sufyan ma ya kance ba ta da abinda zai mora a jikinta duk ta rame sai ƙasusuwan da zasu jimai ciwo, da wannan yake fakewa sai dai ya tuɓe ya yi ta umartata tana yimai abinda zai gamsar da shi. A ɓangaren Sumaya da Sufyan soyayyar su kullum ƙara armashi ya ke yi saboda basa ɓoyewa junansu komai sai na ɓangaren da ya shafi sirrin su, Sumaya ko sunan Naila bata son ji a bakin Sufyan wannan dalilin ya sa baya yi mata hirar ta. A yammacin wata asabar Naila ta shirya zuwa Gidan ƙawayen Ruwaida da ta taɓa kaita, domin ba ta muzantata a wajen kowa ba, dukka ƙawayenta waɗanda su ke kiranta ta yi musu kitso ba su daina ba, Ruwaida ce dai kawai ta ƙauracewa haɗuwa da ita. Ta na fitowa na haɗu da Yasar, da ta gaishesa daƙyar ya amsa yana gyara zamansa a han ɗan tudun da ya ke zaune. Naila bata yi nisa da Gidan su ba, ta hango lafiyayyen mota mai farin gilashin da mutum zai iya ganin na ciki, fuskar Salman ta gani kamar dai yadda ta gani a farkon zuwanta Birnin Abyad. Da gudu ta tunkari mota da ya ke tafiya a hankali ta na kuka haɗe da magana da iyakacin ƙarfin muryarta; "Salman na san kai ne ka tsaya ka cikamin alƙawarina na roƙeka, ina shan wahala ka taimakeni ba ni da kowa a Birnin Abyad ka ji ƙaina ka faɗamin ina SULAIM yake? da gaske ya ƙone ya mutu?" kamar yadda Naila ta yi tsammani bai tsaya ba tana ji tana gani su ka haɗa ido cikin ido da mutumin da ta ke ganin sak Salman sannan yaƙarawa Motarsa gudu ya barta a wajen. Ƙasa ta zube ina kuka. Yasar da ya ga komai kuma ya kasa jurewa nufo inda Naila ta ke ya yi, ya kamo hannunta ya kawota har harabar gidansu. Cikin taushin murya ya ce; "Naila menene ya ke damunki, ka faɗamin gaskiya daga ina ki ke(ma'ana Yankinta) " kasa magana ta yi saboda shesheƙa. Naila ta ɗauki mintina a haka, kafin ta daki ƙirjinta saitin zuciyarta inda ke ji kamar zai fashe, sannan na fara magana sheshekar kuka na tare ta; " ina shan wahala🥹, ina so na koma Yankina, ina ji kamar zan mutu..."✍🏻 [7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c 🔥ZINARE🔥 SASAAL 15 Tana na gama furta ciwo da raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyata, sai ta ƙasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfina. Kamar talabijin haka Yasar ya zubamata fararen idanuwansa. Ta kai wa su daƙiƙu tana kuka, kafin ta cigaba da magana; "Sufyan ya na ganamin azaba, ya na dukana, ba ya barina na mori kuɗin da na ke samu. Ruwaida ita ce take taimakamin kuma ya yi mata sharri saboda ina tara kuɗi a wajenta ta bar gidan nan. Ni marainiya ce, ba ni gata kuma ba ni da ƙarfin yin komai ka taimakamin na koma Yankina" Kai ya sunkuyar ƙasa saboda tausayi ya jima a haka kafin ya ɗago ya ce; "Ina ne Yankin ku Naila? Kuma maiyasa ƴan uwanki tunda sun san ba su da halin da za su iya taimaka miki a ko wani lokaci su ka ba wa Sufyan ya taho da ke har Birnin Abyad? Wannan gangancine mai girman gaske" Ba bu ƙarya a maganarsa amma ƙaddara ta riga fata. Cikin sanyin yanayin da ya ɗan fara shigar Naila ta ba shi labarin Yankin da ta fito. Amma ba ta ba shi labarin dalilin da yasa ta ke bibiyar mutumin da ta ke zargin Salman ba ne. Yasar ya gamsu da bayaninta, amma sai ya ƙara jefomata tambayar "maiyasa ki ke kiran Mutumin da ya wuce ɗazun har ki ke cewa ya taimaka miki? Wanene kuma Sulaim ɗin da kike tambayarsa ɗan uwanki ne? Ki faɗamin gaskiya idan da hali zan iya taimakawa." Ƙur Naila ta yiwa Yasar da ido, tarihin abinda ya faru na kusantowa ganina kamar a lokacin su ke faruwa. Waje ta samu ta zauna Yasar ya biyo bayanta. A baya labarin Yankinta da mahaifanta sun mutu kawai ta faɗamai da rashin adalcin danginta na ɓangaren Uwa da na ɓangaren Uba, amma tunda ya nuna zai taimaketa ta koma Yankinta to dole ya san asalin inane Yankin Tudu da kuma surƙullen da ya ke cikinsa. Kamar Yasar ya na ganin komai haka ta ke ba shi labari tun da ga lokacin da ta yi wayo har zuwa mutuwar Salman da abubuwan da suka faru bayan nan har aurenta da Sufyan da kuma manufar Mahaifansa a kanta. Mamaki ne zalla a saman fuskar Yasar, banda yana da ilimin nazatar Ɗan adam da kai tsaye zai ƙaryata Naila, wani irin Yanki ne wannan? Wa su irin mutanene ma su ƙaracin basira ne a Yankin? Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa Yasar gajarta tunaninsa. Cikin alhini ya ce; "Tabbas! Naila akwai DHAHAB CITY a Babban Birnin Abyad, Unguwar da wani mashahurin mai arziƙi ya gina, Shekaru goma sha biyar baya. Ahalina ne ma su tsauri da tsantseni domin dai-dai ma su gadin alƙaryar Dhahab ababen tsoro ne, sai dai shi ba sunanshi Abduh ba sunansa Muhammad Dhahab kuma a zahirin da mu mutanen gari mu ka sani Ɗan asalin ƙasar Abyad ne, amma wa su na cewa ba shi da asali babu wanda yasan gaskiya. Duk wani mai hidima da ma'aikatan Company's ɗin su, su na da record ɗin komai na sa, rayuwar su ba bu sakewa sam duniyar su tamkar daban ya ke da namu, ba bu wanda yasan sirrinsu sai makusantan su, Tun shekarun baya na naimi aikin tsaron sashen Mahaifiyar Muhammad Dhahab a yanar Gizo kamar yadda na ga an wallafa saboda ma su irin ilimina ake nema, amma saboda sun kasa samun cikakken bayani asalin ni ɗan inane da kuma inda Mahaifana su ke zaune, sai su ka fasa ɗaukata duk da cancanta ta, na yi kuka a waccen lokacin saboda albashin aikin ninkin wanda na ke samu a yanzu ne sau huɗu. Gane rashin samun cikakken asalina ya sa suka hanani aikin sai na tattaro Mahaifana na tara kuɗi na siya mu su Gida a Birnin Abyad, saɓanin daa da su ke zaune a bayan gari. Sai dai duk da na yi haka samun aikin sai ya gagareni haka na gaji na haƙura. Bayyanar Simbi ahalin Gidan Muhammad Dhahab a Asibitin mu sai ya dawomin da burina na baya, wannan dalilin yasa na fara bibiyarta ta taimakamin saboda zan ƙara samun sakewa wajen taimakawa mahaifana har na samu na yi aure, amma sai Simbi ta wulaƙantani dalilin da ya sa nayi zuciya kenan na haƙura da aikin. Amma Naila dole yanzu zan ƙara zage damtse har Simbi ta saurareni, saboda shigata Dhahab zai bayyanarmin alaƙar tarihin Yankin Tudu da rayuwar su, fatana ki tayani da addu'a." Baki, hanci, da ido dukka Naila ta saki tana kallon Yasar, cikin kokwanto ta ce "menene sunan wanda aka ce shine Mijin Simbi mutumin da ya ke yimin kama da Salman?" Ɗan dariya Yasar ya yi kafin ya ce; "A binciken da na yi Simbi sam ba ta da Miji, kuma wanda ki ke gani sunansa Uzair, ba shi cikakken lafiya sosai saboda ya taɓa ciwon da ya yi shekara shida a kwance kafin ya warke, bansan wani ciwo ba ne, amma na samu bayanin ne da ga Yayan Ruwaida amintaccen ma'aikaci a kamfanin su, shima a sirrince ya faɗamin don haka ki kiyaye" kafin ya ƙarasa tuni Naila ta ɗora hannuwanta dukka biyu a kan bakinta alamun ba bu wanda zai ji. Dariya Yasar ya yi kafin ya ɗora da nasihar ta kwantar da hankalinta da ƙarfin mulkin Allah sai sunyi nasarar shiga Dhahab ko a masu goge-goge ne. Naila sai ta ji dukka ƙuncinta ya yaye sai ta ke ganin kamar komai ya zo ƙarshe, da wannan farin cikin sukayi sallama ta koma ciki ta yi wanka ta ci abinci. Gidan kitson da bata je ba kenan ta kwanta barci. Daga wannan ranar Naila bata ƙara ji daga Yasar ba gaba ɗaya ma sai ta daina ganinsa. Da farko ta ɗan damu sai da ya ba da gajeran saƙonsa na suturar sawa ma su kyau da kayan ciye-ciye ya risketa ta kwantar da hankalinta. Babban akwatinta ta sauko da shi, na ɗura kayan a cikin gudun kar Sufyan ya gani saboda ya kusa dawowa. Ta na kici-kicin mayar da akwatin hotonta da na Sulaim da ta sa aka wanke mata ƙaraminsa ya faɗo, da sauri ta ɗauke saboda har ga Allah batasan ya na cikin aljihun bayan Akwatinta da ta taho da shi ba, kuma tasha zuba kuɗi a ciki na kwashe amma hoton bai taɓa bayyana kansa ba. Da wani irin farin ciki ta ke kallon hoton. Batasan ta ɗauki lokaci a haka ba sai da taji Muryar Sufyan a bayanta, dama kuma da ɗayan key ɗin Parlon ya dawo tafiya Makaranta. Firgitarwar da bayyanar Sufyan a lokacin da bata yi tsammani ba ne, yasa ta saki ƙara haɗe sakin ƙaramin hoton ƙasa, kallon hoton Sufyan ya fara yi sannan ya yunƙuro dasauri zai ɗauka ransa na suya, kafin ya cimma hoton tuni ta yi hanzarin ɗaukewa tana zare ido. Fes Sufyan ya ga waɗanda suke jikin hoton, ciwon da ya jima da shafesa a tarihin rayuwarsa ya yunƙuromai. Cikin ɗacin zuciya ya fara dukanta ya na ƙwallo da ita, ya na cewa; "ba ni hoton nan wato amanata ki ke ci ko? Shi yasa kullum bakya ganin kyawuna, kina maƙale da wannan hoton shaiɗanin da ya addabi mutane duk da ba ya raye, wallahi idan baki bani ba sai na kusa kashe ki" maganganun sa ba su ƙarawa Naila komai ba sai ƙaimin ƙara dunƙulewa da ta yi da hoton waje ɗaya, idan ya kasheta ma ai ta huta da uƙubarsa. Har ya gama dukanta bata warware daga ɗunƙulewar da ta yi ba, cikin azabar kishi ya sa mukulli ya kullota yana huci... Kuma ya yi rantsuwar ba zai buɗeta ba har sai ta bubbuga da kanta ta yarda bashi hoton ya ƙona sannan ta ba shi haƙuri. Haka Naila ta kwana ta wuni kulle, inda Allah Ya taimaketa akwai kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da su, idan ta ɗanci sai ta kora da ruwan banɗaki ta ɗoro alwala ta kaiwa Ubangiji kukanta. A haka ta shafe kwana uku tana manejin abinda Yasar ya bata tana korawa da ruwa kuma cikin hukuncin Ubangiji sai ta ji na ƙoshi. A ranta take faɗin; Banda shirmen Sufyan idan har shi da ya ke a iya haka yana ganin yafi ƙarfina to ina ga SULAIM da ya

Chapter 8 of 15