Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ ꨄ Ɗan...ɗano 🤫😢........ Unexpected and Surprising 🔥💥 Our official trailer for the incoming ƘARSHEN ƘADDARA.... 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. This Book is dedicated to you *NA'EEMERH SULAIMAN SARAUTA NIMCY LUV* 1&2 ★... The writer's of MIKIYA TA DABAN DUNIYARMU RAMIN KURA KAREN BANA ƘAUNA BIYU JALAAL AREEF SO DAN RAYUWA DUHU na dukan DUHU And Now ƘARSHEN ƘADDARA ★ ꨄShin ta ina ya kamata ace ma na fara muku ne?,saboda nasan kan kowa ze kulle ne da tambayar ta ina ƙaddara take da ƙarshe???. Ehhhh lallai kuwa wannan nazartaccen littafin yaci suna mu ƙira shi da suna ƘARSHEN ƘADDARA. Saboda ita kanta ƘADDARAR tana gwada zuciya ne, ba don ta karya ba, A ahh sai don ta shirya ka zuwa wani mataki mafi ƙololuwar girma da daraja, don Kalmar ƙaddara bata gama garin mutane bace. Ita kanta yawaitar ambatar kalmar ƙaddarar tana zama ne tamkar ana mana washin KWAƘWALWA neeee. Se dai da yawan mutanen da ƙaddarar ke ci sukan tambaya kansu da cewa. _Amma me yasa ita ƙaddarar take cin mutane marasa laifi?_ Sedai amsar anan itace abinda ALLAH ya rubuta zai faru da rayuwar ɗan Adam, komai ƙarfin halinsa, komai tsarinsa, komai wayonsa. Dole akwai wani labarin dake sanja hakan kwarai, Anan ina son mu sani cewar wannan kaddara ce abin da ALLAH Ya rubuta, hakan na nufin babu wanda zai kauce masa kenan, duk kuwa iya gudunka duk iya saurin ka, sedai mu sani ba nufin ALLAH bane ya zaluncemu ba. Sedai mu sani cewar ALLAH yana da hikimarsa nayin hakan a cikin duk abinda yaga dama, Domin Ƙaddara tana koyar da mu abubuwa da dama… ★.. Ta farko- Rayuwa ba ta tafiya yadda muke so sai dai yadda ALLAH Ya so. Ta biyu- Kowane abu da ke faruwa ko da zafi yake, to tabbas akwai alheri a cikin hakan idan akayi hakuri aka jure, Ta uku- Mutum ya kasance mai haƙuri da godiyar ALLAH kan duk lamarin daya gindaya masa, saboda duk lokacin da kaddara ta same ka kayi hakuri kayi juriya ka kumayi gwagwarmaya karka taɓa bari ka sare don hakan yana cikin jarrabawarka shima. Mutane da yawa suna fuskantar tarin ƙalubalai a cikin rayuwa, wasu rashin lafiya ne, wasu kuwa rashin aure ne, wasunmu kuma suna fama da talauci ne me zafin gaske, saboda kar bawa yaga tarin ƙalubalai na bebeye dashi yaga kamar cewa ko duniyar tana mantawa dashi ne, to maganar gaskiya anan ita ce ba kai kaɗai bane, duk wanda ka gani me rai a cikin wannan duniyar to lallai tabbas yana fuskantar ƙalubale, sedai na wani yafi na wani tsanani... ALLAH yana gwada bayinsa da hanyoyi daban-daban ne domin ya ga wanene zai yi haƙuri, wanene zai ci gaba da yin addu’a. ƘADDARA bata nufin ka zauna babu ƙoƙari. A’a, Ka yi ƙoƙarinka, ka nemi ilimi, ka nemi arziki, ka nemi aure, saidai sakamakon na hannun ALLAH ne. Sabo da manyan mu sukan ce damu kada mu bari rayuwa ta koya mana baƙin hali. Idan ƘADDARA ta rufe ƙofa guda, tana buɗe wata da kuka bai bari mu gani ba... ꨄ Kada ka bari ganin wani yana samun nasara ya sa ka watsar da damar da kake da ita. Abinda ALLAH ya ƙaddara naka ne, to kuwa lallai naka ne don nasarar ka ba zata taɓa wuce ka ba. Ka nemi Albarkar iyaye, kuma ka nisanci hassada,duk ƙanƙantarta kuwa. Amma kuma kada ka taɓa barin ka gayyato bakin ciki cikin rayuwarka, ‎ kada ka zama me aje nauyin da wani ya ɗora maka shi, kada kuma ka bari kalaman wani ya dameka, ‎Kar ka taɓa bari kunci, baƙin ciki da damuwa su sama matsugunni su zauna a zuciyarka tamkar baƙon da yasamu gurin zama. ‎ ‎Me yasa zaka ɗauki nauyin kalaman wani? ‎Me yasa zaka aje abin da ya faru da kai ka maida shi ciwo a zuciyarka?...... ‎‎Idan kana cikin jinya, ko kana fuskantar ƙalubale da barazana ka ringa tuna abu ɗaya, ‎ALLAH baya gwada bayinsa don ya hallaka su, amma Sai don ya gafarta musu, ya ɗaukaka su ya kuma koya musu ƙarfi da gwagwarmaya tamkar RAYUWAR AMEENERH SHEHU USMAN.... ‎ Tabbas ‎akwai darussan rayuwar da ba zaka taɓa koyarsu cikin nishadi da Jin daɗi ba sai ka shiga ƙunci. ‎To me zai sa ka bari damuwa ta fara cinye zuciyarka idan ba za ta warware komai ba? ‎Damuwa ba ta kawo mafita sai dai ta ƙara nauyin zuciya. ‎Ka saki zuciyarka ka bar komai a hannun ALLAH, ‎ka kuma dage da addu’a. Domin ALLAH yana tare da kai fiye da yadda kake zata.A wannan zamanin ‎ƙaddara idan ta same ka, kaddara ce. Amma idan ta faru ga wani namu, sau da yawa mu kan dauke ta ne a matsayin iskanci ko kuskure. A fahimtar gaskiya a duk duniya dan adam bashida na biyu ba kowa bane yake iya gane asalin zahirin mene ne ƙaddara acikin rayuwar mutum Rayuwa da kake gani a waje ba ita ce cikakkiyar rayuwar zuciya ba. Tun daga ranar da aka halicci zuciya a cikin jiki, ALLAH ya bai wa mutum ikon sarrafa tunaninsa, Daga nan ne ya zama ba kowa ne zai iya fahimtar damuwa ko farin cikin wani gaɓa daga cikin rayuwarmu ba, Saboda haka idan ka ga wani yana rayuwa cikin ƙalubale, ka sani ba lallai ka fahimci abin da yake ciki ba, Idan ba za ka iya taimaka masa ya fita daga halin da yake ciki ba, kuma ba za ka iya saka shi cikin addu’arka ba, to mafi alherin shi ne ka bar shi cikin mutunci ba tare da sukar rayuwarsa ko halin da yake ciki ba inda ZAN BA KA SHAWARA.... To shi ne ka guji zama da Mutane masu yawan janjanin magana, domin ba tare da sanin kaba suna rage maka ƙarfin zuciya ne, su kuma iya hana ka ci gaba. Hulɗa da su na iya mayar da rayuwarka wuta, domin kullum suna kallon ɓangaren mara kyau na rayuwa, suna yaɗa damuwa da rashin kwarin gwiwarka. ★Amma idan ka kusanci masu godiya da yarda da ƘADDARA, zaka ga rayuwarka ta cika da nutsuwa da farin ciki, Mutane masu zuciya mai kyau suna ƙarfafa ka, suna sa ka kaɗa baki da murmushi harma su wanzar da farin ciki cikin rayuwarka, suna kuma nuna maka cewa rayuwa tana da daraja duk da ƙalubale sun cinye ta, to waɗan nan mutanen su ne abokan tafiya na gaskiya, domin suna kallon alheri a dukkan yanayin da kake a ciki, suna kuma karfafa ka ka ci gaba da neman nasara tare da gwagwarmaya. Domin sune rayuwa ta yar dasu, mu zaɓi irin mutanen da muke hulɗa da su. waɗanda idan ka zaɓi masu kuka, zaka sha wahala. Idan ka zaɓi masu godiya, zaka sami kwanciyar hankali ne da nasara, don haka mu kusanci masu son farin ciki da nasararmu, domin su ne za su taimaka mana har zuwa lokacin da zamu gina makoma mai kyau. To amma duk hakan baya faruwa se anyi hakuri da ƙaddara, domin duhu baya dawwama, haske zai zo duk runtsi, ‎Abin da ya same ka bai wuce rubutacciyar ƙaddara ba, sedai me???. Wata ƙaddarar da kuɗinmu muke sayenta. Ehhhh lallai tabbas da kuɗinmu muke sayenta... Saboda muna fifita addinin kiristoci fiye da namu a wannan zamanin. Shin ba kun matsu kuji ta yanda muke sayen mummunar ƙaddara da kuɗinmu ba?,mu kuma zaɓeta da kanmu da hannuwanmu ba?, To nidai AMMEY LAYLERH nace babu ruwana AMEENERH SHEHU USMAN wacce akafi sani da *DR MEENERL itane zata banbance mana me hakan ke nufi.... Kun shirya a kafta???.... _Kun shirya jin ta yadda da kanta ta zaɓa mummunar ƙaddarar?, ta hanyar kin bin dokoki da darajar dake cikin aure?, ta fuskanta tarin ƙalubalai masu tarin yawa, cikinsu kuwa har da ƙaddarar AURE AUREN mazan data dinga yi mabanbanta?, Ƙaddarar Fyaiɗen da rashin daraja AURENTA da ya hau kanta, wannan shi ne matakin farko kuma shi ne wasa farin girkin nata_. *Kun shirya jin ta yadda ƙaddarar nata zata zo ƘARSHEN kuwa?*. Dan dai idan nace *ƘARSHEN ƘADDARA* is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta *ƘARSHEN ƘADDARA* ba zan iya cewa an barki a baya SIS. Don It is going to be a hit, that I promise you. Saboda tafiyar *ƘARSHEN ƘADDARA* da banbanci da sauran littattafai na baya, yeah banbancin kuwa ma shi ne about 90% na littafin ƘARSHEN ƘADDARA is based on true life events ne, musamman daga farkon sa zuwa gaf da ƙaresunsa, karshen sa ne kawai zai zama fiction ta yacce zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shi ne from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share ruwan hawaye, so get ready to do both💃🤸......... ♡♡♡ ꨄ Tsaye Matashiyar matar da kallo ɗaya za ka yi mata, ka fahimci shekarunta na aihuwa ba zasu wuce Ashirin da biyu da yake gogayya da rayuwarta ba, tsaye take gaban Madaidaicin mirron ɗakinta me kyau da tsari, wanda yake a gyaren da kallon farko zakama ɗakin da wacce take tsaye gaban mirron ka tabbar da cewar me tsafta ce, tun daga yanayin yadda ɗakin nata ke a tsaftace tsaf, jikinta kuma na ɗaure da wani blue towel se faman shafe shafe take yi kyakkyawar fuskanta, wacce take ɗauke da zallar farin cikin fitanta aiki na farko yau da zata fara, wanda kai da ganin yadda take cikin farin cikin zaka tabbatar da cewar lallai wannan aikin nata me girman matsayi ne a cikin ranta, soson powdern dake hannunta take sake goggawa chocolate ɗin fatar fuskanta, wacce ta zarta mu ƙirata da baƙa sedai bata kai mu ƙirata da fara ba kuma, wannan dalilin yasa muka bata chocolote ɗin kai tsaye. Lipstick ta sake ɗauke tana gogoma lips nata wanda take suka ɗauki shining na kyau da sheƙin abinda aka goga musun, eyeliner ta sake ɗauka tana gyara eyelashes nata again kuma tana ci gaba da gyara duk abinda be mata ba, har zuwa dogon wuyanta shima da take sake gyareshi da soson powdern. Ta ɗan ɓata lokaci me nisa a nan tsaye a wurin, kafin ta miƙe ta nufa gaban wedrop nata me shida, irin me madubi da katifar nan ba laifi suma sun yi kyau babu ƙarya, kayan ta shiga bi da ita tana research da idanunta na wanda ya kamaci ace ta saka, haka har idanunta suka sauƙa akan wata lafiyayyar abayarta black, wacce take ta cikin kayan lefenta ce kuma bata taɓa sakata ba, don haka kai tsaye takai hannunta tana tare kayan dake ƙasa da sama kasancewar rigan itane a tsaƙiyan kaya, ahankali ta janyota bayanta ta ɗan gyaggyara kayanta da suka zamo wosu kuma suka yi ciki. Zame towel ɗin dake jikinta tayi bayan ta zira wata sitred riga daga jiki linor, kana ta ɗora abayar tare da komawa gaban madubi tayi Rolling kanta da vail ɗin da bai kai ya kawo ba na abayar, tsaf kuwa tayi kyau ta kuma karɓu cikin shigan daya mata wani kalan kyau na musamman. Turaren dolcy nd gabbana ta feshe ilahirin jijinta dashi, kana ta wuni nufi ƙofa tana taku ɗay ɗay kamar bata taka ƙasa ba, tin kafin takai ƙofar parlourn ta take famar kwala ƙiran. "Baby!Baby!!Baby!!!" Tana ci gaba da tunkarar ɗakinsa tana sake tunkaro ƙofar bedroom nashi, tana ci gaba da mitar ta "Haba Baby har yanzun baka tashi bane mun makara fa?" Tayi maganar tana wani ɗan zazzaga parlourn irin a matse ɗin nan take, "To wllh sedai ka biyo napep don Wllh nidai tafiyana zan yi....." Takai ƙarshen zancen nata tana kaiwa zaune saman kujerarta me kyau, ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani jijjiga jiki. Babu jimawa sega takun tafiyarsa nan na tunkaro inda take zaunen, zama yayi kusa daf da ita yana ɗan kishin gida daga zaunen da yakai, fuskansa da murmushi sosai ya ce. "Kai My luv yanzun duk wannan zumuɗin fara aikin ne haka?, to yanzun dai a taimakeni da abinci don yunwa nake ji...." Fuskanta ta saki kaɗan tana miƙewa,babu jimawa se gata ta dawo hannunta riƙe da cooler na abincin data yi tin farar safiya, ajje musu tayi tana buɗe cooler'n kai tsaye ƙamshin couscous ɗin data ma lafiyayyen haɗi na dukar hancinan su. Wani ɗan lumshe idanunsa yayi yana sake jin ƙaunar matar nasa na sake bebeye shi, ta iya komai na cikin rayuwa tin daga kama kan kula da kanta, Mijinta, cikinsa, haƙƙinsa, da duk wasu al' amura nashi. Saƙƙowa yayi yana me furta. "ALLAH yama Meenoh na albarka, ya saka miki da gidan aljannarsa mafi tsada..." Wani kallo ta masa wanda ya saka shi kusan sarƙewa da yawun da ya taho kai tsaye daga cikin maƙoshinsa, don shi kaɗai yasan iriyar masifar ƙaunar da yake ma wannan baiwa tashi, gaba ɗaya jinta yake a ko ina na jikinsa, jinsa yake daga kanta ya gama aure IN SHA ALLAHU, domin duk abinda yake so yi masa take kai tsaye babu shamaki, a natse sukaci abincinsu cike da ƙaunar junansu... ruwan swan suka sha me sauƙin sanyi kasancewar ita da kanta ta saka musu dokar hana shan ruwa bame sanyi ba sosai, daga nan ya miƙe yana ce da ita _just 15 minutes_ kanta ta ɗaga mishi tana sakar masa murmushin daya kusan kashesa da ransa, da yar sassarfa ya nufi bedroom nata don babu jimawa kuwa se gashi ya dawo sanye cikin tattausan shigar shadda brown color, wacce ta masifar amsar nasa jikin, don sosai daga ita har shi suke da wani irin sahihin kyau me sanyi da nutsuwa, ba wai irin me ɗaukar hankalin nan... Kallonta yayi daga sama zuwa ƙasa ganin yacce ya tafi ya barta haka take, don haka yace "Baby ya naga ke baki shiryo bane?" Kallonsa tayi ta kuma kalla shigar dake jikinta tana miƙewa tsaye, tsadaddar wayarta me ƙirar _TECNO POP 9_ ta ɗauka tana cewa. "Kaga muje don ALLAH Ya Ahmad lokaci na ƙurewa kaga wannan shi ne karo na farko kar inji a makare...." Tayi maganar tana ƙoƙarin ficewa a parlourn, hannunta ya ɗan jawo yana dawo da ita baya, cikin komawa seriously nashi yace. "Yanzun don ALLAH Meenoh ke idan na ƙyaleki seki fita a hakan?" Cikin yanayi na ɗan fusatuwar data soma tace. "So what idan na fita a hakan Ya Ahmad?, kalla ka gani a suturce nake fa!, ko kuwa illa ka gani tattare da shigan dake cikina?, ya zaka fara abu kamar wani wanda be waye ko ya shiga class ba?" Ta ƙarasa maganar tana fita a ɗan kamar fusace, da sauri ya biya yana bama zuciyarsa hakuri akan cewar wannan ɗin ba komai bane sharrin shaidan ne. Lokacin da yake fitowar kuwa har me gadi na ƙoƙarin buɗe mata get zata fita ta tara napep, saurin dakatar dashi yayi yana isa ya kamo hannunta cikin nasa yana kallar tsaƙiyan cikin idanunta yaje... "Oya les't go!, ko in na barki kin fita ke kaɗai kinsan hospital ɗin ne?, kuma wurin wane zakije?..." Se ya ɗan shiru daidai lokacin da yake buɗe mata gefen me mazan banza a motar, shi kuma yana komawa driver sit ya zauna, Ahankali yakai hannunsa yana lakatar dimple nata da yake gefe guda yana cewa. "Bestien Besty rigima..." Daga haka yaja motar tasa me ƙirar GLK bugun 2025/2026 suna barin harabar gidan, hannunsa na cikin nata ɗaya yake driving ɗin wa'azin Marigayi *SHEIKH MUHAMMAD AUWAL NASEER ALBANY ZARIA* Na tashi a cikin motar me suna *IN KASAN WATA* Sabo da sosai yake son wa'azin Malamin, sabo da matuƙar feɗe gaskiyar sa da yake yi.... Haka har suka isa katon private Hospital ɗin da anan ne yayi duk wasu cuku cuku ya nema mata aikin nata, tin da suka shigo cikin harabar asibitin take kallar tsari da yanayin ta aka tafiyar da ginin wurin kawai na yi mata hundred percent. Ci gaba da bin komai da ido tayi a cikin zuciyarta tana ayyana lallai Ahmad na manyan mutane yana kuma da hannu da manyan, in banda hakan ta yaya ita AMEENERH SHEHU USMAN ta taɓa zata ko tsammatar cewar zata taɓa aiki a ko me kama da wannan asibiti ne, amma se gashi sanadiyyar Mijin nata yau wai ita ce da aiki a wannan tsadaddar asibitin da a da sedai ta hangeta daga nesa nesa, wanda koda a tunani bata taɓa kawo cewar zata zama ɗaya daga cikin ma'aikatan asibitin ba, don ta san cewar ko aikin zatayi tofa sedai ta ƙare a na gwamnati, wanda inta sama aikin ana gwamnatin ma kenan ita nata yayi kyau, amma se gashi yau ata sanadiyyar Mijin nata yau gata a matsayin ma'aikaciyar asibitin, Ikon ALLAH fa kenan, Lallai ta sake yarda cewan Ikon ALLAH shi ne gaba da komai. Wata doguwar ajiyar zuciya ta kawo lokacin da yake farkar da ita daga tunanin data ɗan shilla. Ƙafanta dake cikin wani vk shoe ta fara zirowa me laushi sosai plat me kalan jikin miski, kafin ta fito a natse tana buɗe kofofin hancinta ta shaƙi iskan cikin asibitin da kyau idanunta a lumshe, zagayowa yayi daga mazaunin nasa yana dawowa ta setin da take, tare da kama murfin motar ya zuba mata kyawawan idanunsa, wani numfashi ta ɗan shaƙa tare da buɗe idanunta tar kuwa se akan Babyn nata, wata iska me ɗan nauyi ya fesar yana sarƙe hannunsa a ƙirji tare da sakar mata da wani tsadadden murmushinsa me kyau. "Les't go idan DR. Meenerl ta gama abinda take yi...?" Taji muryan mijinta abin sonta da bata taɓa haɗa shi da kowa, wanda suke yau kimanin watanni Bakwai kenan da aure, amma idan ka kallesu zaka iya shan cewa sun kai irin fin shekarun nan ne a auren, bawai don zaka gane hakan bane ata siffar jikkunansu, A ahhh sedan ta iriyar shaƙuwar dake tsakanin nasu, amma kai idan har ta suffar jikkunan nasu ne tsaf zaka iya ƙiransu ma budurwa ne da samrayinta. Fitowa tayi suna jerewa a tare suka soma tafiya suna ƴar firarnsu suna ƙaramar dariya ƙasa ƙasa, duk wanda suka haɗu dashi a hanyar kuwa seya sake waywayensu koda ya wuce, don yanda suka matuƙar dace da juna. A gaban wani babban office suka tsaya yana zaro wayarsa ƙirar iphone ya saka ƙira a wata number, wayar second yayi yana datse ƙirar, babu jimawa sega wata nurses ta ƙaraso tana musu iso, gaba tayi suka take mata baya har zuwa babban parlourn dake cikin office ɗin, ruwa da lemu ta kawo musu tana ajjewa gabansu bayan ta sake gaidasu, fita tayi ta wata ƙofan daban can kuma babu jimawa sega wani hamdsome guy ya fito sanye cikin labcoat na likitoci sky color, wuyansa rataye da Patient screening hannunsa cikin handglov kansa da surgical cap, zama yayi kujeran dake fuskantar su fuskansa da murmushi sosai, "Barka da zuwa abokina, na ɗan ɓata muku lokaci ko?" Yayi maganar yana miƙa masa hannu tare da sake cewa yayi hakuri wata Surgery ce ya shiga ta gaggawa, "Ba komai DR BILAL" yace masa yana dawo da dubansa kan Meenal. gáidashi a mutumce tayi duk da bawai ta san shi bane ko ta taɓa ganinsa da mijin nata, bayani ya masa game da cewar ita ce Meenal ɗin. Kansa ya ɗan shafo yana cewa "Okay to Ma sha ALLAH, zamu duba mu gani duk dai takaddun nata da kyau, amma duk da aka zan sake gwada ta ko na mako guda ne. Kuma daga gobe In sha ALLAHU zata fara zuwa, yanzun kuma za'a mata interview ne..." Yay maganar yana jan landline ta parlourn ya saka ƙiran wata babbar likita, babu jimawa wata gaggaɓar mata ta iso, nuni ya mata da Meenal yana ce da ita, "Dr pooja jeki da Meenal zaki mata interview a fannin surgery...." Cikin harshen turanci ya mata bayanin kasancewarta Christian ce, fuskanta da yanayin da murmushi me kyau ta kama hannunta cewa "les't go My freind!" Murmushi ta nata tana mara mata baya suka fita, shi kuma suna yin hannu yace zai je wurin aikinsa don har kamar ma yayi late. Har parking car's ɗin DR BILAL ya raka AHMAD.... Lokacin da Dr pooja ke can tana ma Meenal interview tuni shi har ya jima ma da barin cikin hospital ɗin baki ɗaya, kuma Alhamdulillah sosai tayi ƙoƙari dan tiyatan Ɓera ne tayi, kuma cikin ikon ALLAH bayan allurar baccin da akama ɓeran ta masa tiyatan cikin taka tsantsan da kuma tsoro, amma cikin iko na Ubangiji tana kammalawa sega ɓeran nan na motsi harma yana ƙoƙarin tashi ya gudu, wata nannauyar ijiyar zuciya daga ita har Dr pooja ɗin suka saki ita tana godiya wa ALLAH,ita kuma tana cewa. "THANKS JESUS...." daga nan suka ci gaba da ƴan ababuwa har ƙarfe sha biyu da kusan rabi, kafin ta ɗebeta suna komawa office ɗin Dr BILAL, sedai tin kamin Meenal ɗin ga kawo kanta taga Dr pooja ɗin tayi hanzarin yowa baya tana dafe goshinta da zuciyarta, na irin alamar nasha da kyar ɗin nan kafin

Chapter 1 of 14