kaina se ka mutu...." Ko kallar inda yake bai yi ba ya faɗa cikin motar yana mata reverse yabar wurin. Kansa kawai Dr Bilal ɗin ya girgiza a ransa yana cewa. _ALLAH ya taro ka ABDOUL-MAJEED...._ daga nan yayi cikin asibitin.....
★..
Tun da ya ɗauko ta daga Asibitin ta rufe kanta a ɗaki take kuka, kuka irin wanda ke gasa da soya zuciyar me yin sa, kukan baƙin cewa wai ita AMEENEERH SHEHU USMAN yau ƙaddara ta tsara mata ke ɗauke da ciki!, cikin wanda ya mata fyaiɗe tin da ganan watan cikin huɗu da kwana biyar ɗin da abin ya faru, ta gwada paisoning ɗin kanta yafi sau uku, idan ta tuna ko ta mutu bawai ta huta ko ta tsira bane, Wannan dalilin yasa ta gama tsarama kanta za ta tsaya ta fuskanta rayuwar, tayi gwagwarmaya ta jure ta daure ta cinye duk wani maɗacin da duniyar da abinda ke cikinta zata basu, ta gode ALLAH da tin da abin ya faru ko sau ɗaya Ahmad ɗin be taɓa koda kwatankwacin kusantarta bane, Idan kuma ta tuna cewar zasu rabu ne a duk lokacin da cikin jikinta ze bayyana tana jin kamar ba zata iya jurema hakan ba. Ahmad ɗin da tunda ta rufe kan nata yake ta famar Safa da Marwa kamo ɗakinta kamo ɗakinsa, yana cewa ta buɗe masa don ALLAH!, ta buɗe ze yafe mata komai, ze dawo suci gaba da gudanar da rayuwarsu irin ta baya, ze manta komai, ze shafe komai kamar komai ɗin kuwa be taɓa faruwa ba. A lokacin da maganganun nasa ke dukar cikin kofofin kunnenta kuwa kukanta tsananta yake, tana jin ta gama yafe kanta ta kuma haramta daga gare shi, yin Duniyar yayi ta buɗe masa amma ta ƙi ya, Dole ya kira Ya Sadeeq yazo har gidan amma taƙi saurar kowa daga cikinsu, Ina samm bata jin zata iya buɗe musu wannan ƙofar, ko kuwa so suke ta buɗe tace musu ciki ne da ita?, cikin da ba na mijin taba?, haba abin yayi munin da bata jin zata taɓa buɗe musu wannan ƙofar a dai daidai wannan lokacin ɗin.Suna tsaka da wannan danbarwar sega ƙarar jiniyar ƴan sanda nan ta gama karaɗe ilahirin gidan baki ɗaya, wanda jiniyar gaba ɗaya ba ƙaramin tasar hankulansu yayi ba,se dai banda ita. Don jima tayi kamar an yaye nata dala ne bisa kanta, tasan zasu tafi da ita ne bisa mutuwar mutumin da tasan ita ce sanadin hakan. A ruɗe Ya Sadeeq da Ya Ahmad ɗin suka isa ga harabar gidan, Suna zuwa wani baƙi murjejen ɗan sandan da kana kallonsa kasan babu imani tattare da shi yace. "Ina mai laifin kisan take?" Wani kalan mugun shock ne ya ziyarci Ya Sadeeq da bai san da zancen komai ba. Don haka ya duba Inspector ɗin tare da furta. "Ƴallaɓoi ko dai kun yi ɓatan kai ne?" Jajayen idonsa Inspector ɗin ya zaroma Ya Sadeeq ɗin yace. "Ba nan ne gidan AMEENEERH SHEHU USMAN ba?, Matar AHMAD IBRAHIM SHAREEF?" tin da ya kama hasalin cikakken sunanta Ya Sadeeq ɗin ya gama sallama wa, Kafin ya juya ga Ahmad ɗin don yana buƙatan ƙarin haske dangane da maganar kisan da tazo masa a matuƙar bazata kwatsam lokacin guda. A takaice Ahmad ɗin ya bashi labarin abinda ke faruwa daga jiya zuwa yau, har musabbabin ƙiran da ya masa ɗin kuwa. Jikin Ya Sadeeq ɗin ne ya fara wata kalan rawan tashin hankali. Kafin ya kalla Inspector ɗin yace. "Ƴallaɓoi zaku iya tafiya dani, domin wacce kuka zo wurin nata bata da lafiyar da ko fitowa da kanta ba zata iya ba, amma ni yayan tane, zaku iya tafiya dani duk hukuncin daya kama nata a min ciki kuwa koda rataya ce...."
"Gani nan da lafiyana Sir!, ni zaku kama domin kuwa ni ce mai laifin!!!..."
Haka baki ɗayansu suka tsinkayi muryan Meenal ɗin data fito da fuskanta duk abin hawaye ya gama bushewa, idanunta tsabar kuka kuwa sun zurma sunyi ciki. Ahmad ne yayi hanzarin shan gabanta yana me furta. "Wa ya baki umarnin ki fito?" Kai tsaye tambayar da ya fara cilla mata kenan, "Sabo da ni aka zo nema!, kuma ko da ace ban fito ɗin ba dole zasu fito dani........" Ta sake faɗi tana ƙoƙarin nufar kwalawan. Kyakkyawar Garkuwa Ahmad ɗin ya bata ta hanyar tare gabanta da yayi daga shirin miƙa kanta ga kwalawan da dake, Zuciyarsa harya fara tafasa yace "Zaki koma ne ko se na saɓa Miki?" Ya sake faɗi daidai janye san da wani police yayi daga gabanta. Ya Sadeeq ne ya iso gabansu yana sake shiga tsaƙiyar police ɗin da ita. Cikin ɗan yanayin fusata yace."Na ce muku da nine wanda zaki tafi ba ita ba amma" Ganin renin hankali da wasa da aikinsu da duka su biyun ke yi ne ya saka Wannan ƙaƙƙarfan police ɗin buga musu tsawa, yana me furta "I like that..." Daga haka yama macen dake tare dasu inkiyar ta kama Meenal ɗin, hakan kuwa akayi ta kamo hannunta tana zira mata Onka. Wani irin rinewa idanun Ahmad yayi zuciyarsa na ƙoƙarin masa bindiga. Kafin ya isa gabanta ya ce. "Abin da kike zaɓa kenan?, kariyar da muke shirin baki kika ture Meenal?, Kika zaɓa tozartamu da ƙasƙantar damu a idon duniya?...." Ya faɗi hawaye na zubo masa. Hannayenta duka biyun dake cikin onkar ta sa tana goge nata kwallar da ya ciko nata idon, kafin cikin ƙarfin gwiwwa da yaƙi ni tace. "Ko da ace ban yi hakan ba bazan taɓa tsira ba Ya Ahmad, dole gaskiya tayi halinta, dole komai ya bayyana, Me bi wannan ita ce zata iya zama magana ta ƙarshe da kai Ya Ahmad, domin kuwa na san koda na fito bayan gaskiyar komai ya gama bayyanuwa doke zaka rabu dani, domin abinda ke ɗauke a jikina da kasancewar sa ɗan duma ko an ɓoye se ya bayyana. Abinda kawai nake buƙata daga gareka shi ne Adda'a da fatan Alkhairi, tare da Adda'ar zaɓin abinda shine mafi Alkhairun mu garemu. Tabbas dukkan ayyuka suna tabbata ne da niyya,kuma Lallai ko wanne mutum yana samun sakamako ne na abinda yayi niyyar, Ubangijii ALLAH yana gani kuma shi ne wanda zai bani kariya, karka ji komai, domin nie a yanzun babu abinda nake jin ɗin kuwa... Face na bayyana gaskiyar abinda yake akwai ciki kuwa harda bayyana cikin dake jikina daya kasance na wannan dabbar ne...." Ji da ganinsa ne suka nema ɗaukewa lokaci guda, me take nufi da cikin jikinta?, tana nufin ciki ne ke ɗauke a cikin cikin nata irin na haihuwar ɗan mutum dai?, me ya sa shi da ita bata taɓa fada masa ba?, me yasa be taɓa lura da hakan ba da suna zaune gida guda har cikin yayi wannan watannin a jikinta be sani?, Haba No wonder ranar yayi ta kallarta, ramar tayi yawa, zafgewar bici ace ta iyaka damuwar da take a cikinta bace, shi kuwa me yasa be tsaya ya fuskanta matarsa ba, me yasa fushinsa gare ta har ya bari yaja lokaci haka?..... Kansa ya riƙe yana ɗan jujjuyawa yana ambatar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un a cikin kansa. Idanunsa na dishi dishin lumshewa yake ja baya yana cewa kar ta masa haka, karta yarda ta sako maganar cikin nan, nashi ne!, na shi ne!!, Ze amsa yana son ta yana son duk wani abu daya kasance tsatson tane.... Yana ji yana gani suka tafi da ita, tafiyar da ita ce farko da kuma ƙarshen rayuwa da duk wani farin cikinsa, tafiyar data tafi ta barshi na har abadan da dama ta riga ta gama ambata mishi, Kuka ya saki a wurin tamkar wani ƙaramin yaro yana buga kansa da jikin biyar settline ɗin dake tsakar compound ɗinsu, Ita kuwa zuwa lokacin idanunta sun gama ƙaiƙashewa sun bushe babu alamar hawaye, domin zun riga da sun gama zubar da iyaka ruwan da zasu gama zubar wa ɗin, sun soye kuma yanzun sun ƙaiƙashe, bata jin kuma akwai abinda ze sake sakata kuka yanzun. Da kanta tana layi tana komai ta shige cikin motar suka buga suka bar gidan da ita. Ya Sadeeq ne yayi hanzarin yin kan Ahmad ba wai dan shima tashi zuciyar na cikin sauƙi da nutsuwa ba, sedan haƙurin daya gama bata ya jure ya taya ƙanwar tashi gwagwarmaya, ya taya ta yaƙin har se inda ƙarfinsa ya kare shi ma. Ciki ya shige da Ahmad bayan ya ƙira gidansu ya sanar da iyayensa abinda ake ciki, kafin kiftar ido sega mahaifinsa a gidan, wannan ne ya saka Ya Sadeeq ɗin tafiya shima domin ya fara binciken Inane inda aka kai ƙanwar tashi. Se dai duk wata HEADQUARTERS ɗin daya sani dake cikin garin KANO ya gama zagayesu, se dai babu ita babu me ko alamarta. Sosai hakan ya tashi hankalin sa goshin zuhr ya isa gidansu, Daga yanayin yacce mahaifinsa ya ganshi a jigace ne yasan cewar ba ƙalau ba, seda ya fara shan ruwan da Baffan ya bashi ɗan huta kaɗan kana yake tambayarsa ko lafiya?... Kora masa bayanin duk yacce ake ciki yayi, se dai ya ɓoye zancen cikin da yaji ta furta kuwa, tin da bai da tabbacin hakan ne koba haka ba, ALLAH sarki take Baffa shima ya shiga wani kalan zallar tashin hankalin da ba'a sa masa rana. Kafin ka me se gashi har ya haɗa kan almajiransa ya saka su sauƙar Alqur'ani me girma, cikin gidan ya wuce yake gwaggo Sadiya ta dafa shinkafa jallop kamar kwano uku, tana gunguni tana komai ta miƙe ta ɗora don wllh ita ta tsani wannan saka aikin na Baffan, da sai kana zaune kwatsam se ɓallo maka da aiki bayan kana murna ka kammala naka, gashi babu damar musu don duk tsiyarta tana shakkarsa ai, ɗan kwalin dake ƙoƙarin zame mata ta gyara tana cewa. "Se ka bani kuɗin kayan miyar ai dubu uku..." Ganin kuma yana kallonta da kanta yasa ta tsargu don haka tace "To ai kowacce kwana kayan miyar dubu take ci, amma ba sai ka bada kuɗin mai da magi ba muna dasu...." Ta ƙare maganar da susar kan da kana kallarsa kasan bana gaskiya bane, don kar a gano ƙaryar data labta ne. Kansa kawai ya jijjiga ya fiddo ukun harda ƙarin ɗariya biyar yace ganan yacce zefi isa ma, yasa kansa ya fita. Yana fita ta ƙira Bilkisu dake daki ta bata 1500 bayan ta zare dubu biyu, tace a mata malkaɗe bashi ɗaya kulli uku na ɗari biyar biyar gida uku, iya zallar tattasai da da tarugu. Shimar nata ta koma ta ɗauko a cikin ranta tana ma Ummar nata fatan shiriya, don duk maganar da suka yi tana jin su. Fita tayi taga gidan har ga gota Baffan nata da sai da ta masa sannu ya ƙiranta, wanda se da ya saka gabanta faduwar ko tambayar ta baffan nasu zaiyi, duk da dai bawai hakan yake mata ba. Tsugunne takai tana cewa "Baffa gani!" Dubu ɗaya ya zaro daga cikin aljihunsa yace ta taho da ciyawan shayi ta ɗari biyar ta dafa mishi shayi me ɗan dama, bayan ya tambayeta ai suna da sugar tace ehhhh kana yace to ta riƙe ɗari biyar ɗin, godiya ta mishi tana miƙewa ta tafi aikar nata.
Babu jimawa ta dawo ta wuce ta bama Ummun nata markaɗen, kafin itama ta nema tukunyanta me kyau me ɗan girma ta ɗora, koda uwartata ta tambayeta me zata yi, tace Baffa ne ya sakata dafa masa shayi, yi tayi kamar tayi magana amma kuma ta fasa tana ɗaukan wata babban tukunya itama ta ɗora. Kafin kace me sega gidan ya ɗauki ƙamshin girkin gwaggo Sadiyan, ita kuwa tuni dama Bilkisu ta gama dafa shayin ta juye a wata babbar cooler. Ta nemi wankakkun ƙananun kofuna ta ɗora a kai ta ajje daga bakin ɗakin Baffan nasu ta shirya a gurguje ta wuce Islamiyya, ita kuma dama Shareefah tana school dake Monday ce tana can ba kuma zata dawowa ba se Friday, weekend kawai take zuwar musu. Bayan idar da sallar la'asar Baffa ya saka manyan almajirai fitowa da abinci da shayin da aka dafa, nan gardawan ciki suka ringa zuzzuba musu abincin da shayin, bayan sun kammala ci aka kuma taruwa aka yi adda'an ALLAH ya kawo musu komai da sauƙi...
★..
Tafiya yake cikin yanayin da kai baka isa ainihin gane masa ba, domin kuwa wannan moody face ɗin nashi da kullum haka zaka ganta babu murmushi balle dariya, ita ba'a ɗaure ba ita kuma ba'a sake ba. Gaba ɗaya tin da ya kama kallar labaran maka yarinyar da tayi sanadiyar mutuwar ɗan gidan senator Garba Aliyu na Yaya a kotu, yaji hankalin sa ba'a kwance ba. Ya rasa abinda yake masa daɗi haka kawai kawai, a ransa tunani yake don me yasa ba asibitin zasu kai ƙaran ba?, ai ba iyaka yarinyar bace likita a cikin asibitin, me yasa basu kai kowa ba se ita? Sune jerin tambayoyin da yake tama kansa. Gaba ɗaya lissafinsa nemar kufce masa yake akan al'amarin, gani yake idan har be shiga cikin case ɗin ya kwatarma da yarinyar ƴan cin ta ba to shima yana da nashi kamisho ɗin zunubin ne. Wayarsa ya fidda ya saka ƙiran Dr BILAL lokacin da yake kaiwa zaune cikin motarsa, lokacin kuma wajajen tara da rabi ne na dare. Wayan nata ring baya ɗauka don haka kai tsaye kawai yama motan key ya fita daga gidansu. Asibitin ya nufa directly, Lokacin da ya isan kuma goma saura, ganin motar Dr Bilal ne ya bashi tabbacin yana cikin asibitin kenan, kai tsaye office na Dr Bilal ɗin ya nufa ganinsa da yayi zaune gaban computer yana ta famar aiki ne ya saka shi jan tsuƙa, ya ƙaraso ya zaune yana janye computer ɗin dake gabansa yace. "Uban me kake da kana kallar ƙirana baka daga ba?" Wani kallo Dr Bilal ɗin ya watsa masa yana furta. "Aikin daka aiken ɗan renin sense kawai, bani computer na woni aiki me muhimmanci nake, ƙirarka kuma ban gani ba ne Malam...." Seriously ya dawo yana fuskantar Bilal ɗin, kafin cikin ɗan ƙaramin sautu yace. "Ƙarin bayani zaka bani game da ita...." Daidai nashi Dr Bilal ɗin ya dawo yana me furta. "Game da?..." Don shi ma bai gane ko waye yaje nufi a kai ba. "Ita yarinyar da case na su sen Garba Aliyu ke kanta...." Wani numfashi Bilal ɗin yaja yana me furta yanzun ma shi ne aikin daya riƙeni, don da magribar nan Yayanta yazo cikin asibitin yake tambayana game da ita, wai kwalawa sunje har gidan mijinta sun tafi da ita, kuma ya duba duk wata headquarters na ƴan sanda bai sama labarin taba, bayan tafiyansa nima nake kallar labaran kama ta ɗin da aka yi shi ne ma dalilin da yasa na yi busy kenan..." Wata iska daga cikin bakinsa ya fesar tare da miƙewa tsaye, yana cewa "Kafin zuwa wayewar gari kayi gaggawar gano inda suka ɓoyeta,nd kuma shi ina banzar mijin nata yake da har zasu shigar masa har cikin gida su tafi da ita, da ba zai dakatar dasu ba...."
"Yayi duk yacce zeyi dan ya bata kariya shi da Yayan nata dana ce maka yazo, amma Ita yarinyar ne ta ƙi aminta har ta bayyana kanta gare su...."
Kafaɗunsa ya ɗaga alaman bashi da damuwa ya fice, shi dai abu daya kawai yasan zai tsaya mata akai shi ne kare martaba haƙƙinta na wacce aka zalumta...
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
Unexpected and Surprising 🔥💥
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
Page 13&14
_YA ALLAHU ME IKON ZARTAR DA HUKUNCINKA AKAN KOWANNE RAI ME NUMFASHI, GASHI A YAU WASU SUN TAƁO MAKA NI MARYAM WANNAN BAIWAR TAKA DA BATA DA GATAN KOWA SE NAKA, DON HAKA NAKE KAWO MAKA KUKANA AKAN DUK WANI MUNAFIKIN DAKE SON GANIN BAYANA, DA HAƊA MIN TUGGU DA MUNAFINCI AKAN MAGANGANUN DA NI BAN SAN NA FAƊE SU!, YA ALLAH KA SAKA MIN, KA KUMA BI MIN HAƘƘI NA AKAN KOMA WAYE... ALLAH KA TSAYA MIN ADUK WANI LAMARIN DA ZAI TASO IRIN HAKA, DOMIN NI KAI NE GATANA KUMA ABIN DOGARO NA, DONNI DA KAI NA DOGARA BAWA KO WANNE KATO KO KATUWARBA,YA WADUD KA SHIGA CIKIN LAMARIN..._
_KU KUMA MUNAFIKAI KUJI TSORON ALLAH WLLH ,IDAN KUMA BURINKU WANI YA TOZARTANI TO KU SANI IN SHA ALLAHU BA ZAKU TAƁA GANIN BAYANA BA DA IKON RABBIL ARSHIM AZEEM... DA WATAN AZUMIN ALLAH KUN TASHI HANKALI NA KUN KUMA SA HANKALI NA YA TASHI BA KAƊAN BA, KUJE KUMA NA BARKU DA ALLAH, SHIRUN KUMA DA NAYI BA INA NUFIN NA TSORATA BANE, KAWAI BANA GAGGAWAR ƊAUKAR MATAKI NE DA KAINA, INA BARMA ALLAH YA ZARTAR DA NASHI IKON NE, DOMIN NASAN IN YA TASHI YAFI NAWA ƘARFIN IKO KO MATAKIN DA ZAN ƊAUKA,DON HAKA KUCI GABA DA GASHI ALLAH YANA KALLON KU BABU RUWAN AMMEY LAYLERH 🤸💃_
♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ A can gidan su ameenatou kuwa da kuma Mijinta Ahmad tabbas sun kwana suna baƙin ciki da alhinin iftila'in daya faɗama Meenal ɗin a daren jiya, tabbas sun sake yarda da ake cewa zaɓi guda ɗaya mara kyau a cikin rayuwarka na iya janwo maka shekaru na gajiyawa da nadamar rayuwarka na har abada, Shi sa masu iya magana suke cewa ka zama mai taka tsantsan aduk wani al'amarin daya danganci rayuwarka. Domin rayuwar tana jujjuyawane cike da tarin abin mamaki da al'ajabi, ta yanda wani lokacin zaka shiga kwanakin da suke nauyaya maka rai,har kayi tunanin ba zasu taɓa ƙare maka ba. Har ka wayi gari wata rana kana son kayi sabuwar rayuwa, sedai lokaci ba zai taɓa baka wannan damar ba, domin shi da kansa lokacin ba zai taɓa baka damar hakan ba,don lokacin daka gama ɓatawa na baya ba za su taɓa dawo maka ba, ta yanda wani lokacin karshen abu shi ne farkon nutsuwar zuciya. Kamar yadda masu hikima suke yawan cewa, karka jira ƙofa ta buɗe bayan ta rufe maka, sannan ka gane babu rufewar data fito daga ALLAH face tana ɓoye da alkhairinsa akan ta. Abu na farko daya kamaci ace kowanne bawa ya gane anan shi ne ka sani cewar, abu na farko daya kamata ka fara yafewa shi ne ka koya daga kuskurenka don ka sake gyara kuskurenka harma kaci gaba da ƙoƙari. Kada kabar kuskurenka ya zama sarƙar yanke ƙauna,ka mai dashi gyara zuwa matakin gaba na ingantacciyar nasarar ka, don masu iya magana sunce, Rashin nutsuwa yana farawa ne daga nisantar mutum da ALLAH, tsoron ALLAH kuma shi ne sirrin kowanne farin ciki na gaskiya..... Idan har duniya da abinda ke cikinta suka soka da gyara to maza kayi gaggawar gyarawar kuwa, idan kuma ta ƙiƙa to ko zata sake baka wata damar seka sha baƙar wahala da fafutuka sannan. Daga nan labarin ameenatou ya fara.....
Yanda taga daren wannan rana haka taga wayewarsa masu cike da almara da irin ƙarfin iko na Ubangiji, lallai idan har bawa beji tsoron mahaliccin saba to kuwa yaji tsoron hukuncinsa, don idan yaso ka da ramane fa kuskuren saɓa masan da kai ke farawa tin daga nan gidan duniya, idan har shi wannan bawan me zuciyar nagartane seya gyara, nadamar rayuwa da dana sanin biyema son zuciya da kuma rudin zamani shi ne abu na farkon daya farawa dirar mata, A cikin zuciyarta take zubar da hawaye bawai don yana fitowa daga cikin idanun taba, A ahhh yana daga can cikin zuciyarta yana mata illar da tafi zubar shi azaba, cinnaku da kukan sauro sune abu na daya fara addabar rayuwarta, wanda take jin kamar ta sare da rayuwar ta huta haka nan, Sedai kuma kamar yacce hausawa ke cewa wahala bata kisa sedai asha baƙar hawala a hannunta, tuna wannan kawai da tayi ne yasa har taji a ranta cewar sauyin rayuwa da munin ƙaddara ba zata taɓa barin su kaita ƙasa ba, bare sauyin rayuwar data samu kanta kwatsam a ciki besa taji zata sarema rayuwar ba, sai ma wani
ƙarfin imani dana zuciyar karɓan kowacce iriyar ƙaddarar da tazo mata da hannu bibbiyu, wannan kwana ɗayan da tayi a cikin cell a kulle da har a da take jin kamar ba zata iyaba, saboda rayuwa ce da ko a idon zuci bata taɓa ko tunanin hasasoma kanta ba ko da a mafarkin tane da. Rayuwar data tsinta kanta a ciki se taji tama tata rayuwar nauyin da kamar ba zata kai labari ba. Amma ƙarfin imanin daya shigeta na danne hakan take. Hasken daya haske mata idanune ya sakata motsawa tare da kare fuskanta da duka hannuwanta biyu, Wata police macece tace ta fito se famar wani kukkumbura take tana cika tana batsewa, domin ku su duka jami'an ba hakan suka so ba daga yarinyar, don da a son samu ne se ta samu kamar kyakkyawar sati guda cif a kulle ba tare da ko sauron waje yasan inda take ba, sedai wanda ta tarar a cikinsa amma kash wani ya musu kutse a cikin tarkon nasu, wanin da suke da tabbacin tsaf ze iya saka a dakatar dasu a aikin nasu, dakatarwar kuma ta har gaban abada, domin shi kansa yaron nada wani irin karfin iko a cikin garin bare kuma azo kan mahaifinsa da yake kamar father's ne na manyan mutanen da duk suke jin sunkai a garin Kanon. Fatar bakinta tayi wani kalan bushewan da har tsagawan hawala tayi, idonta yayi zurfin da ya sake fitar da iyaka zallar jigatuwar da tayi, domin tin da suka wullota ko ruwa babu wanda ya bata bare abinci, domin sen Garba Aliyu na Yaya da Matarsa Haj Madina kamar kwangila kisan tane suka bayar suma. Shi ya saka ko a jiyan ziryan Yayanta biyu amma suka ce su bama su san wata me wannan sunar ko me kama da ita. Ana haka sega wannan Gabjejen bakin police ɗin ya fito, wanda sarai Ya Sadeeq ɗin ya gane sa don haka ya nufi wurinsa yana cewa don ALLAH ya taimaka ya faɗa masa inda Meenal ɗin take. Amma haka wannan police ɗin yay mirsisi yace shi baima taɓa ganin kome kama dashi ko wata can ba se yanzun daya fara ganinsa, Wannan abu shi ya sake rikita Ya Sadeeq ɗin, barin ma da sauran ƴan uwansa ma suka goya masa baya wai shi bama ya gari ai yanzu ya dawo, Nan fa suke neman haukata kan Ya Sadeeq ɗin...
Tunanin wannan police ɗin ya dakata ne daga lokacin da wannan macen police ɗin take fitowa da Meenal ɗin,
ɗago ƙananun idanuwansa da suke a matse kamar na ƴan Japanese yayi, yana sake tsayar da kallonsa akan Meenal ɗin da lokaci guda harta sanja saboda mummunar halin da take a ciki, ga yunwa da ƙishin da suka gama wajigata. Wata nannauyar ajiyar zuciya police ɗin yayi ganin kamar Wada damar ce ALLAH ya kawo musu, masu ƙarfin ikon faɗa da nera biyu sun haɗu akan case guda ɗaya, se yake jin a ransa cewar hakan ma kamar dama ce ALLAH ya kawo musu ta yanda zasu jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu a wannan gaɓar. Da wurin zama ya mata nuni yana sassauta zuciyarsa akan tsananin son abin duniyar da yake da. Zama tayi a inda ya nuna mata ɗin tana ta baza idon taga ta inda Mijinta ko Yayanta a cikinsu wani zai ɓallo, don tasan kaf duniyar babu masu zuwa wurinta daya zarta su. Se dai zama da kamar 30 minutes ɗin da tayi bata ga kowannensu daga cikin su ne ya sakata ɗaga kanta ta kalla police ɗin dake tsaye, mamakin Mutumin da kuma jin kansa na sake kashe sa, ehhhh mana ai dole yace jin kai mana yace a fito masa da yarinya kuma ta fito sama da 30 minutes be ce mata komai ba. Ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 14