kuma taga lokacin data furta thanks jesus, ta motsawar mukwallonta, tana kama hannunta suna saurin barin wurin, suna yin ta bayan window me girma, tsaiwa tayi bayan ta saki hannun Meenal ɗin dake ganin Ikon ALLAH, "Thanks god Sir MAJEED!! be ganmu ba...." Ta furta tana sake sakin wata ijiyar zuciyan. office nata ta wuce da Meenal ɗin, suna isa ta saka ƙiran Dr BILAL. Nan take bashi labarin ai taje zata shiga office nashi ta tarar da Sir MAJEED a ciki yau dai jesus ya tseratar da ita, dariya bame yawa ba Dr Bilal ɗin dake tare da Sir MAJEED ɗin har kusan daf ya saki, can ƙasa ƙasa yana satar kallon inda MAJEED ɗin ke zaune daya wani sha mur sosai yana cike wasu takaddun da shi ne abinda ya kawo shi cikin asibitin da seya kusa shafe rabin shekara be leƙo taba,dan hakan nema yasa ba kowa ne ya masa cikakken sani a matsayin me hospital ɗin ba, mafi yawancinsu ma sukan danganta asibitin data Dr Bilal ɗin ne, idan kuwa kaga mutum ya masa farin sani a cikin asibitin to kuwa tabbas babbane me girman matsayi kamar dai Dr pooja ɗin da ta ganshin a yanzun, wanda mamakin ganin san da tayi har yaso bata mamaki, wanda ita a karan kanta sau da dama takan sha mamakin yadda aka yi Majeed ɗin ke mata kwarjini bayan kuma schoolmate nata ne, tare suka yi karatu a ƙasar Oxford amma yanzun ya wani girme mata ya zama magidancin dole, duk da dai dama magidancin ne kuwa, harda ƴar sa ƴar kimanin 7 year's. Fesar da iska daga bakinsa Dr Bilal yayi yana datse ƙirar bayan kallon da yaga Majeed ɗin na jifarsa dashi, komai kuma be ce masa ba, wanda dama yasan hakan cewa zata faru tin da hakan shi ne kusan ɗabi'arsa. Miƙewa yayi yana nufar hanyar barin office ɗin, seda yaga yakai har bakin ƙofar kana ya masa gwalo yana cewa. "Maye dai yaci kansa banza miskilin tsiya da baƙar zuciya, yanda mutum yaƙe baƙi haka ma zuciyar tirr da MAJEED DAWOUD ISHAQ...." Yana kai nan ya fice a guje daga office ɗin baki ɗaya,ɗan yasan tsaf shi idan ya tashi yaɓo tashi baƙar maganar ze kusan kashesa da ransa. Kai tsaye office na Dr pooja ya wuce saɓunta gaisuwa tsakanin su suka yi, yana amsar document ɗin da pooja ɗin ke bashi, dubawa yayi yana cewa ta kwana ma gidan sauƙi bara kawai ya bema Majeed ya shigar da file ɗin cikin jadawalin list na ma'aikatan asibitin, seda Dr pooja ta ɗan waro ido har tana gaza yin shiru tace. "You don't see any problem with that, do you Dr?" Murmushi yayi yana fita kawai dan ya fahimci tsaf pooja ɗin zata bashi ciwon kan da Majeed ɗin ke yawan cewa tana bashi. A lokacin da yaje masa da zancen duba file ɗin daya masa wani kallo yana ma turar da laptop ɗin dake gabansa gefe daban, kafin ya wani kalle sa yace. "Kai me yasa ba zaka shigar ba,halan ka haɗu da cutar kuturtace bana da masaniyar hakan, to bara kaji indai se na shigar da wannan cikin jadawalin list ɗin ne, to kuwa ko waye sedai ya mutu be sama aiki anan ba...." Daga haka yasa kansa yana ficewarsa, ko ina be kalla ba ya shige motarsa yana ma yin reverse yabar cikin asibitin.
Ƙarfe biyu daidai Ahmad ya dawo asibitin suka wuce bayan ya sake jaddada godiyansa ga abokin nasa Dr Bilal, har gaban motarsu ya sake rakasu daga ita har shi suna sake jaddada godiyar su, tana cewa ya sake miƙa mata godiyarta ga Dr pooja. Daga nan kai tsaye gidan Hajiyarsa yakai Meenal ɗin, duk kuwa da yanda gabanta ke faɗuwa da haɗuwar nata da hajiyar san, don tasan bame kyau bace, amma bata nuna masa komai ba har suka isa gidan, hong yayi get man ya buɗe musu get ɗin yana cilla hancin motar nashi cikin haraban gidan nasu, Motar Abbansa daya gani a gidan ne ya bashi tabbacin yau babu inda ya fita kenan, duk da dai dama be ganshi a Company ba, wanda da ya zata ko wani wurin yaje, ashe duk ko ina ne ma beje din ba. Ajiyar zuciya me kyau na ziran da tayi itama tayi ganin motar Abban, don tasan ko babu komai ta kuɓuta daga bakaken maganganun hajiyar Ahmad ɗin....
Da sallama ɗauke a bakunansu daga ita har shi suka shiga parlourn gidan, wanda mutane uku ke zaune a babban ƙaryataccen parlourn, magidancin jarida ce ɗauke a hannunsa yana dubawa, yayin da magidanciyar matar ke zaune tana fuskantar plasma da ake haskaka labaran Duniya, se wata matashiyar da ita kuma ke kwance saman 3siter tana lallatsa wayarta, wanda sallamar su Ahmad ɗin ya saka gaba ɗaya attention nasu dawowa kansu ciki kuwa harda hajiyar da tana kallon sa tare da Meenal take ta ɗauke kanta bata sake kallar inda suken ba. Zaune matashiyar ta miƙe tana gyara hulan dake kanta dake ƙoƙarin zamewa, fuskanta da fara'an ganin Meenal ɗin ta miƙe tana nufosu tana cewa _Oyoyo Meenally'n babban Yaya...._ ta isa gare su tana rumgume Meenal ɗin da ita ma ta rumgume Fatiman, A kunyace ta ƙaraso tsakiyan parlourn tana ɗurƙusawa gaban Abba da yake tace da ita ta koma saman sofa, gáidashi ta shiga yi a girmame tare da Hajiyar da take wani amsata a ciccure, wanda hakan ma tasan albarkacin Abba ne taci, se lokacin kuma Ahmad ɗin ke ƙarasowa cikin parlourn shima yana zama daga ƙafafun Abban nasa ya gaida shi, kafin ya juyo a natse ga mahaifiyar nasa, "Hajiyata barka da rana, fatar kin wuni lafiya...." A daƙile ta amsa may da "Lafiya Alhamdulillah" kawai tana ɗauke kanta daga garesa. Fatima ce ta Abba yace ta wuce dani ɗakinta,hakan kuwa yamin daɗi ba kaɗan ba muka wuce abin mu, babu jimawa sega Ya Ahmad ya shigo mana da abincin da na tabbata ni ya kawowa ma. Da ido na masa alamun ya ka min haka?, shima da idon yamin alamu da sabo da hakan hakkinane... Murmushi kawai nayi kuma kamar abin haɗin baki muka saki dariya a tare, be zauna ba ya fita sakamakon shigowar ƙira cikin wayarsa ya fita, dake tayi salla a can asibitin se kawai ta zauna sukaci abincin, koda suka kammala kwanciyar ta tayi a gadon Fatiman take nannauyar bacci yayi awon gaba da ita, wanda ta jima yi, don se bayar la'asar sosai ta tashi sallarn ta fara yi kuma zuwa lokacin Fatima bata nan, wanda take da tabbacin Islamiyya ne ta tafi, fita tayi zuwa parlourn Hajiyar, har lokacin Abba na zaune a parlourn amma babu Ahmad, Hajiyar kuma bata parlourn sema motsinta data fara juyowa a kitchen don haka kai tsaye ta nufa kitchen ɗin, A ɗan tsorace ta mata sannu tana ce da ita ta kawo ta mata aikin, wani banzan kallo ta wurgo mata tana jan tsaki tare da nuna mata hanya alamar ta bar mata wurin, "Don ALLAH kiyi hakuri Mami ban san abinda na miki ba wllh..." A wani irin fusace kuwa ta juye tace. "Baki san abinda kika min ba?, tun da ke muna fuka ce gadon munafurci taya ya zaki san abinda kika min kuwa, tin da kin gama mallake min ɗa babu kowa a gabansa in ba ke ba, gashi yau watanni Bakwai kenan da aurenku, ban ga alamar komai tattare dake ba, halamar sedai aci aje masai kenan ke ba matar ƙaruwa bace out....."
Ta wani ƙarashe maganar nata da tsawa tana korar ta a kitchen ɗin, wani abu me kama da ruwan hawaye ne taji sun ciko idonta, don haka babu musu ta fice, sa'an ta ɗaya Abba baya parlourn don haka ta shige ɗakin Fatima ta zauna a gefen gadon ta tana dafe kanta da hannayenta. Jin Shigowar Hajiyar har ɗakin Fatiman ne ya saka gabanta yayi wani irin faɗuwa, yawun bakinta na ƙafewa ƙaf, take taji kanta ya sara mata, don haka a cikin zuciyarta ta shiga nanata kalmar INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN... Tamkar sauƙar aradu haka taji muryan Hajiyar tana cewa. "Wllh³ bazan taɓa son ki ko na amsheki a matsayin surukuwata ba Meenal, sabo da na tsanake!, bana sonki!, bana ƙaunarki, gaba ɗaya so kawai kike ki haukatar min da yaro baya da aiki se naki,yanzun fa duba har aiki ya samo miki a asibitin *4&4 SPECIALIST HOSPITAL* wanda ni nan babu kalan roƙon da ban masa ba akan ya samowa Fatima amma yaƙi, se gashi ke dake ke kece ya samo miki tashin farko, ko shawartana beyi da maganar ba, sabo da ga makiyiyarsa se yanzun naji ya a faɗama ubansa ni ban kai ba, ban kuma isa ba...., To ki sani wllh se nayi duk me iyuwa na rabaki da Ahmad kamar yadda kike nemar rabani dashi kema....." Fuuuuu daga haka tasa kai tana ficewa har wani hucin bala'i da masifa take. Kuka tayi me rai da lafiya a wurin tana roƙon ALLAH ya ganar da Hajiyar Ahmad ta gane gaskiya, tana nan zaune har bayan sallar magrib amma hawayen be dena zubo mata ba, jin motsin kamar za'a shigo ne ya sakata saurin faɗawa toilet ɗin Fatima ta wanko fuskanta tana gyara yanayin ta sosai, don tasan Ahmad ne , tin da taji shigowar Fatima da kuma lokacin da Hajiya ta dakatar da ita daga shiga ɗakin ta aiketa makota. Idanunsa ya zuba mata da kallon farko ya gane cewar kuka tayi, zama tayi a sofar dake daf da gadon Fatiman kwara ɗaya, inda ya ƙaraso har wurin a natse daf da ita yana zama tare da janyo ta jikinsa. "AMEENERH?" Haka taji ya ambata sunanta da full name nata kafin ya sake jefa mata tambayar "lafiyanki kuwa? Ko wani abu akayi miki?" Tsaye ta miƙe
sannan calmly ta goge hawayen idonta da bayan hannunta daya sake zubo mata, kanta ta jinginar a jikinsa tace. "Babu abinda aka yi ya Ahmad bacci nayi, kuma kasan idan nayi bacci tsakanin sallar la'asar da magrib da ciwon kai yawanci nake tashi..." Ta faɗa da sanyin murya and I can swear I saw him relaxed. Kanta ya ɗago bawai don ya gama yarda ba wani abu Hajiyarsa ta mata ba, fuskar sa cike da concern ya furta. "Kin tabbata?" Yana saka idonsa cikin nata don sake tabbatar da hakan. Vail nata dake gefe a tashe ya ɗauko mata yana ɗora mata samar kanta yaje suje. Babu musu kuwa ta bi bayansa don dama hakan take ta jira tin ɗazun, koda suka fito babu kowa a parlourn don dama Abba be dawo ba, yasan kuma dama ba sosai ya fiye dawowa idan yayi sallar magrib ba se anyi isha'a yake dawowa gaba ɗaya. Hannunta ya kama ya nufa sashen Hajiyarsa da ita, wanda gabanta keta sake faɗuwa amma babu yacce ta iya ko tace ba zata ba, haka ta bishi tana zaune samar darduma suka isa, sallama yayi bata amsa ba taci gaba da laziminta, tsugunne yakai gabanta yana ce da ita zasu wuce. Da hannu ta masa alamar suje duk da beji daɗi ba amma haka yaja hannun Meenoh ɗin nashi suna wucewar su. Gidan gaba ya buɗe mata ɓangaren me zaman banza ta shiga ya rufe ya zaga ya shiga driver sit yana tada motar suka bar gidan. A wurin gashin wasu zabbi ya tsaya fita yayi babu jimawa se gashi ya dawo hannunsa ɗauke da ledoji biyu, ɗaya ta gashin zabbin ce, ɗayar kuma fruits ya sai musu kasancewar yaga kamar na gidan sun kusa ƙarewa. Sannu ta masa tana amsar ledojin ta miƙa ta baya, daga nan yaja suka wuce gida, be shigo gidan ba ya fita don baya son ya shigo beyi sallar isha'a ba, shima kusan irin Abban nasa ne, yafi gane idan yayi isha'a ɗin ya shigo gidan shima, ita ce ta shiga da ledojin ta ware fruits ɗin a fridge ta rage wasu zabbin ma ciki don tasan da safe ba sai ta musu girki ba, ta ware musu kuma wanda zasu ci idan ya shigo. Karfe tara saura ya dawo, wanka ta taya shi ya fara yi kafin su fito cikin shigar kayan shan iska, don itama tayi bayan tayi sallah'n isha'a. Se baza ƙamshinsu suke, a natse suka kammala cin nama da youghout ɗinsu kafin su zauna suna kallar Film na HAQ a tare a laptop nashi, don duk Film sabo daga fito yake sauke musu su kalla. Har wajajen sha biyu saura kana suka kammala suna ta mayar da yacce film ɗin yayi kyau, ya kuma tsaru, don ba ita mace ba ko shi kansa da yake namiji Film ɗin ya taɓa masa zuciya, gashi kuma akan addinin Musulunci aka yi Film ɗin, har yacce wasu mazan ke wulaƙanta matayensu na gida idan sun ƙara aure, da yacce Ƴaƴan wacce ake zalumta suke ƙin iyayensu maza, saboda kuntatama mahaifiyarsu da ake, haka dai sukayi ta maida yadda suka tsara Film ɗin. Ɗan kwantar da kansa a kan kafaɗarsa yayi, wanda ya saka Meenal ɗan juyowa ta kallesa, shima kallon nata yayi yana wani kashe mata idon daya sakata lumshe nata, matso da fuskansa daf da nata yayi zata ɗan koma baya kaɗan yakai hannunsa ya kama waist nata daya saka ta jin yirrrr, tsigan jikinta na tashi bakinta yama kissing yana cewa. "In sha ALLAHU bazan taɓa kasancewa miji irin Abbas ba, don zalumcinsa yayi yawa, ya kuma cuci Yami Ghautam da yawa tare da yaranta. Idonta ta sake lumshewa tana jin tabbaci akan duk maganganunsa akan ta, ta kuma yarda dashi samm bata da haufi akan mijin nata, daga nan ya tashi da ita suna wucewa bedroom nasu, don har ta fara bacci a jikinsa, kwantar da ita yayi shima yana kwanciyar gefen ta tare da janwota yana shigar da ita cikin jikinsa, ta buɗe baki da niyar masa magana ya haɗe bakin, dole ta tsaya da kyau tana bashi kulawan daya kamata, sune har wajajen karfe ɗaya da rabi basu yi bacci ba, seda suka tsaftace jikinsu kana suka kwanta tana lafe a jikinsa tana sakin ijiyan zuciya me ɗan zurfi. Daga nan wani daddaɗan bacci me cike da SO da ƘAUNAR da suke ma junansu ya kwashe su, washegari har kusan a makare suka tashi, don se a gida ya jasu sallar subhi. Daga nan basu komawa tayi ƴan gyare gyarenta ta sake gasa musu namansu na jiya suka karya dashi, sedai yau ɗin ma dai kalan jiya da doguwan riga ta bubu ta fito, se sani ƙaramin vail, har ze mata magana kawai ya kyaleta suka fita. Ajje ta yayi yau be shiga cikin asibitin ba ta wuce ita kaɗai.....
_Byu byu hayya hayya ya take ne?, fatar dai wannan ɗan littafi nawa ze amsu a wurin ku, kamar yacce kuka saba amsar duka littattafaina..._
_Idan naga reactions naku akan littafin zan fara sakinsa nan bada jimawa ba IN SHA ALLAHU....._
_ALLAH yasa wannan salon labarin da muka sanja ya muku, don labari ne akan irin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin gidajen rayuwar aurenmu zahiri da kuma baɗininsu, da yacce wasu mutanen su da kansu ke siyar ƙaddararsu da kansu da kuma hannayensu...._
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
Unexpected and Surprising 🔥💥
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
_My NAINERH TARH, My Ƙaunar ƙaunata My aminiyar kwarai mutuniyar kirki Uwar yaro na Mubeen kuma this Book for you, gashi ya iso gareki da zafi zafinsa fa💃🤸_
Page 3&4
♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ Tana isa cikin asibitin kai tsaye office na Dr pooja ta wuce, wasu ayyuka ta ɗan bata ita kuma tana yin ɗakin wata me haihuwa da aka kawo, tun cikin dare ta kasa haihuwar da kanta shine ma abinda yasa take tunanin ko C/S ma kawai za'a mata, don tana matakin ƙarshe ne don tana 1/cm haihuwa a koda yaushe, amma gashi abu ɗaya ake fama tin wajajen karfe 7 gashi kuma yanzun har goma na nemar wucewa ma, labcoat nata ta zira da handglov a hannunsa ta sake nufar delivery room ɗin da matar ke ciki, tin kafin ta kai ga ƙarasa shiga room ɗin take jin ihu da salatin matar na tashi, goshinta ta dafe tana ƙarasa shiga da ɗan hanzarin ta, handglov ɗin dake hannunta ta sake gyara zamansa tana kai hannunta ƙasan matar dake kwance saman gadon masu haihuwar nan, ganan dai kan jaririn ya ɗoso sedai daga uwar har yaron ko yarinyar dake cikin cikin kowa fafatuwar tsira da rayuwarsa yake, ita tana son taga tayi duk me iyuwa ta yunƙura koda ta numfashi ne abinda ke cikin cikin nata ya sama damar fitowa, shi kuma dake cikin shima yunƙurin yaga ya fito ɗin yake, wata nurses ta ƙora Damaga kan ta haɗo mata allurar naƙuda kawai tama matar, kanta matar ke jijjigawa gafa ɗaya gumi ya gama jiƙeta sharkaf, da kyar ta iya samun bakin furta. "Karku daura min ruwan naƙuda ina da sugar da hawan jiniiiiii...... San...sa...sa....san...nan...ina da raunin zuciya....." Duk wannan abin da take yi cikin fusgar numfashi take da haki.. gaba ɗaya ta gama saddakarma rayuwar ta gama sallama cewar shikenan ita nata ajalin yazo, don haka ta shiga adda'a 'o'i masu kyau da girma idanunta na ƙoƙarin lumshewa, su kuma gaba ɗaya ma ɗakin sun rasa abinda ya kamata su mata, don haka kawai Dr pooja ta fita babu jimawa se gata hankali a matukar tashe da file na saka hannun mijin matar dake can haraban asibitin yana ta safa da marwa yawa me dawafi. Abinda ze baka ma dariya ƙafansa ɗaya da takalmi ɗayan kuma babu faɗi yake. "Don ALLAH NA'EEMERHTOU karki tafi ki barmu!, ki taimaki rayuwar yaran mu dake dani Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" haka yake ta famar ambata gaba ɗaya shima ya gama jiƙewa se kace shi ne me haihuwar, gefe can kuma dashi wasu mata ne biyu kowannensu ya buga uban tagumi kowa da abinda ke damunsa. A can ɓangaren Meenal shigar Dr pooja office ɗin ta hankali tashe da kuma fitar ta ne itama ya tashi hankalin ta, don haka ta mara mata baya, bayan ta ɗora labcoat da handglov a hannunta koda ALLAH yasa zata iya musu da wani temako ne haka, gaba ɗaya zuwa lokacin kuwa har Dr pooja ta kammala duk wani shiri nata na fara surgical ɗin, harma an nufi surgery room da matar. Lokacin da take kaiwa ainihin room na Surgery room ɗin har pooja ta ɗora Scissors nata saman cikin matar da numfashin da take shaƙa ma na Oxygen ne, don tuni rauninta yayi ƙasa sosai dole se da taimakon oxygen zataci gaba da numfashin. "Wait a minute, ma'ame..." Haka Dr pooja ta tsinkayi muryan Meenal, dakatarwar kuwa tayi tana isowa ita kuma. Cewa tayi pooja ɗin ta taimaka mata da sabuwar rezor, seda ta sake risinar da kanta tana juye baki cikin yaren Ingilishi tace da ita tayi haƙuri ta shiga cikin hurumin da ba nata ba, ba komai tace da ita, don haka kai tsaye ta saka sabuwan rezor ɗin tana ɗan yankar ƙasan matar, da komai bata ji ba sakamakon allurar kashe jikin da aka mata, oxygen ɗin dake hancin matar Meenal ta zare kaɗan tare da ɗan ɗago kan matar kamar zata zaunar da ita ta kuwa takarkare ta saki wani zazzafan numfashin dake kumshe cikin bakinta ya fashe, wanda dama ita Meenal ɗin hakan take son samu daga matar, daga ƙirji zuwa cikinta ta ɗan danna tare da sake mata irin ta ɗazun bayan ta mayar da ita ta sake ɗago ta, aikuwa a wannan karon ma ta sake yin irin na ɗazun, haka har suka yi karo uku, ana huɗun kuwa tayi wani kyakkyawan nishin da kai tsaye ya taho da yaron dake cikin, hannunta ta saka duka biyun tana ƙarasa janyo yaron ya fito kuwa da assalatunsa, wato kuka irin na jarirai sabuwan haihuwa, suluf haka matar taji jikinta ya koma kamar wacce aka sauƙe mata cutar shekara da shekaru, tana meda wasu numfarfashi, kafin ta tafi zuwa duniyar sumewa... Dama tasan za'a yi hakan duk da cewan bata taɓa amsar haihuwa ba amma kuma Alhamdulillah tana da kyawawan da bata mantuwa, don wannan ɗin duk cikin interview ɗin da aka musu ne na irin dabarun haihuwar da tayi gaddama, kuma Alhamdulillah tayi nasara wanda dama se irin kamar ana daf da yima mutum operation ɗin ake son yin hakan, wanda ita da classmate nata sun sha gwada hakan akan kansu da numfashin da suke gumtsa su fesar idan an zame oxygen ɗin, kamar yadda tayi tama matar. Dr pooja ce ta rumgume ta tana furta "Ohhh jesus Today I saw a young lady who was thoughtful and knew her job well.Thank you Jesus.... Thanks u Maanol....." Dake haka tin jiyan take ƙiran ta dashi wato Maanol ɗin. Ko kafin kace mene se gashi tuni har an gama shelanta wa duka sauran Dactor's ɗin dake cikin hospital ɗin cewa ga wata ƴar baiwar likita sun samu me matsakaicin year's. Cikin ƙanƙanin lokaci se gashi sunan Dr Meenerl Shehu Usman na nema yin shura tun a matakin farko, da kansa Dr Bilal ya ziyarci wurin ya kuma zauna da sauran Dactor's tare da Meenal kan fikirar da tazo musu da ita, nan kuwa ta tashi ta ringa musu bayanai daki daki, wanda daga ƙarshe suka gane cewar lallai ashe ba se iyaka private school's bane suke jajircewa wajen koyar da ɗalibansu ba, nan mijin matar ma ya bada wasu kuɗi masu ɗan gwaɓi yace na likitar data ceci rayuwar matarsa ne da kuma abinda ke cikin ta,duk da kuwa kasancewar tana a Cold room ne. Wato ɗakin sanyi amma kuma ai tana ci gaba da shaƙar numfashin daba na oxygen ɗin bane, ga kariyar da aka haifa ɗin tazo cikin ƙoshin lafiya abinta, dake dama tun a lokacin ta gama wa matar ɗinki,don haka yaci gaba da kulawa da marasa lafiya a fannin haihuwa, kowa se kaji yana don ALLAH a ƙirawo masa Dr Meenerl shima tazo ta taimake shi, wanda ita abin ma yake ɗan bata dariya, wato ma ita ne zata temakesu ba ALLAH, ko dan ance me ciwon haihuwa tamkar zautacce haka yake komawa, duk abinda yazo bakinsa faɗa yake. Ba itane ta koma gida ba yau se wajejen ƙarfe 7:30pm, tin kuma 7:15am data fito. Dake dama tayi waya da Ya Ahmad ɗinta cewar yau kar ya biyo da wuri se after magrib ze biyo ya ɗauketa, SO shi kuma lokacin Hajiyarsa ce tayi ƙiransa dole haka ya tafi yace ta biyo napep amma karta yarda ta hau machine... Koda ta dawo ta tarar ya dafa musu farar shinkafa da yaji, ta wani cunkule ƙaramin bakinta kuwa don ita ba Sosai take son farar zallar shinkafa da may da yaji haka ba, har ƙara ya musu couscous ko noodles da egg, haka bayan tayi wanka tana ƙananun ƙunƙunai tana komai ta tuttura abincin... Wayarta ta ɗauka bayan sallarn isha'a ganin be shigo ba ta shiga WhatsaAp nata da duk wunin yau bata hau ba, da test messages na Shareefah ƙanwarta kuma babbar aminiyarta ta fara cin karo, don haka ta shiga, voice note ne don haka ta kunna tare da kaiwa kunnenta ta saurara. Wata ijiyan zuciya ta sauƙe lokacin data kammala sauraran voice note ɗin, kafin itama ta fara mata nata voice ɗin. _Look Shareefah ina son ki kwantar min da hankalinki kinji, ki kuma ci gaba da haƙuri bana son kika sanya wata damuwa daban a cikin ranki, kinsan koda ace da ran Ummanmu ba zata so ganinki cikin damuwar hakan ba, kuma Baffa yana daidai gwargwadonsa a kanmu tsakanin mu da gwaggo Sadiya, kuma ke ba karatun ki ma kike ba, don ta hana ki abinci kuma se yaya ina ce kusan duk bayan 2 weeks nake saka miki kuɗi a account naki?_ daga nan ta tsaida voice
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 14