nata, kawai yana dauke kai ne sabo da yaransu, to amma tun da ta nuna masa iyakarsa da cewar shi be isa ba to ya rantse a yau ba sai gobe ba seta bar masa gidansa. Ahmad ɗin idanunsa sunyi jajir ya nufa Abban nasa yana bashi hakuri shima ya buga masa wata tsawa yace ya fice ya bar masa gida. Fatima kuwa wani irin kuka take na nadamar halayen momin nasu marasa kyau. Ta buɗe baki da niyar sake bashi wani hakurin ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba, tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta ko sauran mafaka,
Jiki a sanyaye Ahmad ɗin ya fice a parlourn nasu itama Fatima ta wuce nata ɗakin. Ita kuma Umman nasu da jikinta ke rawa ne ta wuce ɗakinta babu jimawa se gata ta fito da hijjab ɗin bata fiye yawan da shiba. Ganin daga se himar nata ne ya saka shi sake buga mata tsawa yana cewa maza ta haɗo kayanta a akwatu don ba nan kusa zai nemeta ba, har se lokacin data dawo da Meenal ɗakinta. Sosai ta sake razana da lamarin wata muguwar nadama na sake kamata, tana jin tsanar mugwayen halayenta da har yay sanadiyyar rabata da bugun numfashinta wato Abban, don ba ƙaramin mahaukacin SO take masa ba. Shi yasa ma take taka tsantsan da duk wani abinda ya shafe sa, amma se gashi yau saboda wata watsatstsiya can daban har yana mata barazana da nata auren, sosai ta sake jin tsanar Meenal ɗin a cikin rai da ruhinta. Babu jimawa se gata ta fito da akwatun ta taf da kaya ta fice tana jan majina, ido yayi fulin fulin tsabar kuka... Kai tsaye daga nan gidan su Meenal ɗin tama tsinke, taje ta sake yayyaɓa maganganunta san ranta, har da cewa yo dama ita yar malamai ba dole ubanta ya shiga tsakanin zaman lafiyarta da mijinta ba, daidai kuma Baffa ya kawo kansa lokacin da take faɗar kalaman nata, don haka ya ƙaraso yace da ita. Ta sani ita data koma gidan ɗan nata har abada, domin ta gama zaman aure dashi, tana nan zaune In sha ALLAHU se taga mijin Meenal ɗin zata aura ko ba jima ko ba daɗe, kuma taje duk abinda tayi kanta, se da Baffa ya mata tasss kana ya komar da Meenal ɗakinta da idanunta suka sake rinewa sosai, Runtse idanunta a karo na biyu tai tana ƙoƙarin kwatar numfashin ta dake barazana wa gangar jikinta. danne dukkan abinda ke yunƙuro mata tayi, tun da ga aurenta da Ahmad da irin baƙar tsanar da ummansa ke nuna mata haka kawai, har zuwa loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani, amma duk da haka baiwar ALLAH'r nan ba zata barta ta huta haka nan ba, se tayi ƙoƙarin mantawa da abu kana se wasu mutane su sake tado mata da danyen raunin da ya dauka hanyar warkewa.Lallai ta sake yarda duk inda Kalmar KADDARA take, lallai kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu yawan gaske a cikinta, domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwa juna. haka kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar ita ta amshi nata da hannu bibbiyu In sha ALLAHU, kamar yanda Baffan ta yasha ce mata Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin rayuwarsa game da duk abinda ALLAH ya riga tsara masa, to kuwa lallai kayi hakuri da duk abinda ALLAH ya tsara maka domin kuwa shi ne mafi alkhayri agareka. Sake Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake jujjaya mata. Maganganun Umman Ahmad ɗin na son haifar mata da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar hakan faruwa. Domin kuwa ita ɗin mutumce me tsananin ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama dama yay crossed nata mind ba, duk yadda maganganun suka so haukata kanta amma ƙin bama hakan dama tayi. Lumshe idonta tayi ta taji hawayen da suka tara nemar zubo mata, amma ta sake shanye hakan har tana jin yadda jinin jikinta ke wani irin harmutsawa tamkar ana aza wuta a jinin jikintan haka take ji, shigowar Shareefah ne ya sakata ɗago rinannun idanunta ta zuba mata, zuwa loƙacin kuma jikinta har rawa yake a mugun wahalce ta nufi jikin Shareefah'n , dama tasan ita ɗince ta biyo ta lallashi bayanta. Rungumeta kawai Shareefah ɗin tayi tana bata baki da haƙuri. Ganin duk yacce Shareefah'n tabi ta ruɗe ne ya sanya Meenal ɗin ɗan janye jikinta ana Shareefah 'n tare da ƙaƙaro murmushin dole wai duk don ta kwantar mata da hankali. Saidai zubowar ruwan wahayen dake yankar zuciyarta da bala'i bala'in zafi da ƙunar da suka kusa haifar mata attack take ne ya saka Shareefah fashewa da nata kukan itama, jin yadda jikin yayar nata ke jijjiga......
_The comments are dropping. 😔 ko dai baya muku daɗi ne? Naga ba comments ba reactions naku._
_Please don't be a silent reader. Comment, vote and share. Thank you 👏👏👏_
_Love you all my mutanena Amanana😘🫂_
_Put a smile on my face please. Vote, comment, and share My lovely friend's ana tare_
# Voice of the innocence
# Team AMEENEERH SHEHU USMAN where Are You???
_Team Meenal wai kuna ina ne haka? meke meke shirin faruwa daku haka?_
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
Unexpected and Surprising 🔥💥
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏....
Page 19&20
♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ ƙarar data fasa ne ya saka Ya Sadeeq da Baffa da Bilkisu har dama gwaggo rige rigen shigowa dakin nasu. A sanƙame suka ganta jikin Shareefah ɗin gaba ɗaya jijiyar kanta sun gama fitowa sun yi ruɗu ruɗu. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Ya Sadeeq ya ambata shikenan abinda suke ta gudu ɗin ya faru, mutanen kan Meenal ɗin sun motsa, wani kalan tashi hankali muraratan kake kalla daga cikin idanun kowannensu, don kuwa jinya ce ta sau da tari ma sukan mance da cewar Meenal ɗin na ɗauke da ita, wanda suke kamar gadon mahaiyar tane tayo, idan tsanani yay tsanani suka tashi to sukan shafe tazarar kwanaki da suke ganin ace akai akai ɗin ne suke tashi, a wannan sanƙamen da take takan iya kaiwa har gobe uwar haka bata ko motsa ba, duk kuwa kalan ƙarfin adda'an da ake mata, idan suka tashi gaba ɗaya se hankalin kowa ya tashi, wannan shi ne karonta na uku kenan a tashin nasu, bata motsi bata numfashi babu alamar me rai tattare da ita. Se jijiyar babbar yatsarta kawai da take harbawa wanda shine zai baka tabbacin cewa tana da rai, a gabanta Ya Sadeeq ya zube yana amsar ta daga hannun Shareefah Baffa shima yakai tsugunne suna fara tofa mata adda'o'i masu kyau, har zuwa wani lokaci can cikin dare kana suka fita kowa ransa babu daɗi aka bar Shareefah da Bilkisu wacce da cewa yay gwaggo Sadiya ta kwana da ita tace wllh ba da ita ba, ita dai Bilkisun da taga zata iya bismilla to ga wuri na ta tsallake ta fita, su biyu kwana da ita a tsakiyar suna ci gaba da mata adda'a ɗin har bacci ya ɗauke su suma, bayan sun yi kukan sunyi har sun gode ALLAH. Ko washe gari haka yaran Malam suka ringa shigowa suna ma su Shareefah sannu dame jiki, ido duk yay jeme na alamar fita a hayyaci, Malam kuwa kusan kwana yayi zaune akan binciken ire iren matsalolin aljannu masu shige da nata, don haka da kyar ya samo wata hanya me ɗan tsauri. Da sassaucin abin ya tashi bayan Sallah a masallaci ya aiki Sadeeq Jigawa amso masa magungunan wurin hasalin tsohon malamin da ya koyar dashi. A asuba ɗin ya tafi sha biyu kuwa bata kai ba se gashi ya dawo da magungunan dana shaƙawa dana hayaƙi, wanda mafi ƙarfin cikinsu da saurin dawo da sinadaran ƙwaƙwalwa shi ne ɗan tumfafiyar da aka busar dashi a inuwa, tare da lafar ganyensa ɗaya da ɗan ɗaya se a rubuta _WALA YA HUDU HU HIFZU HUMA WA HUWAL ALIYUN ALIM, HASBINALLU LA I LA HA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHEEM AZEEM..._ SO za'a rubatasu ne a jimlamce matsayin kafa bakwai bakwai, idan ya bushe ya dake ya zama gari a shaƙama wanda yake fama da irin makamanciyar jinyar aljannu irin haka, ko me cutar farfaɗiya, to bi'izinillahi za'a sama waraka, se wasu manyan turarukan jinnul-Aashiq. Su zamfar su zauzau manyan turarukan jinnul-Aashiq ne, Shareefah fa ne ta shafe gaba ɗaya jikinta dashi wajen kala uku, kana ta kama hancinta tana cusa mata ciki, a take wata gigitacciyar hatshawa ta taho mata tana wani ƙoƙarin miƙewa a gigice, Ya Sadeeq da ya shigo yay hanzarin ɗamkar ta, wani ihun da kusan seda ya saka Baffa dake waje wurin almajirai kifawa, yayo gidan wasu maganganun da basu da kan gado ta shiga yi, tana wani jijjiga tana ƙoƙarin kwatar kanta daga mummunar riƙon da Ya Sadeeq ɗin ya mata, ahankali ahankali kuma jikinta ya shiga saki numfashinta na daidai ta koma yarab bayan a kan idonsu wani abu me kama da hayaƙi ya fita ta cikin goshinta. Wata ijiyar zuciyar data saka kowa sakin tashi shima ta saki tana laluben hannun Shareefah...
Umman Ahmad kuwa a lokacin da ta kai gidan ƙanwar mahaifiyarta Hajja ta zayyane mata komai, dake Hajja ɗin ba kanwar lasa bace itama tayi kanta tana faɗan ina ruwanta da rayuwar auren yaron nata?, wannan abu shi sake tuƙe zuciyarta har munanan kalaman Mijin nata suka shiga dawo mata daki daki........ "Bana son kicemin komai Yahanasu domin kuwa komai ɗin ya isa haka nan!, Na riga da na gaji da munanan halayenki Yahanasu, wallahi kinji na rantsema awannan karon kam babu makawa se kin tafi, tin har kika saka ɗan ki ya saki matarsa alhalin yana sonta, yanzu ki dubi halin da yaron naki yake ciki ko tausaya masa ba zakiyiba, ke kuwa wacce iriyar uwa ce data fiye son kanta da yawa uyhmmmm?, Karfa ki manta kema kina da yara matan nan har biyu, akwai Amina ga kuma Fatima kuma ke kin ma yima kanki adalci kuwa har dan ita uwar mijin Aminan tana takurata itama ki ringa tsine mata?, kin ga ashe babu daɗi ma kenan, baki isa ƙuntatama ƴar wasu kuma ke kice naki Ƴaƴan su zauna ƙalau a nasu gidajen ba, ƙarya ma kenan never wllh. Don haka kema dole kiji irin raɗaɗi da baƙin cikin dake cikin tozarcin aure........." Haka kalaman Mijin nata ya katse ta a lokacin suna yin dinner da yaranta ta hanyar faɗan haka cikin wani irin mugun ɓacin ran da bata taɓa ganinsa a ciki ba.... A lokacin jajayen idanunta ta ɗago tana kallarsa cike da wani kalan mamakinsa. Wani irin tsannin baƙin cikin ne taji ya mugun turnuƙeta, babban abun takaicin ma shima shine a gaban yaranta ya mata hakan, ji tayi kanta na nemar zare mata don tsananin sarawan da yake mata kamar zai rabe gida biyu, a lokacin da take tunawa da maganganun nasa, tashi tayi ta bar parlourn wacce take madadin uwa a gare ta ko iya kallon gabanta batayi sabo da tsantsanr ɓacin ran dake cunkushe da ita, har tana fidda wani numfashi mai zafi. Haka ta wuce uwar ɗakan Mamar tata tana sharce hawaye, se gashi abu kamar wasa ko Fatima Abban ya hana zuwa inda uwar take, bare me dungurin uwar du ɗin Ahmad, wasa wasa har ta cinye satin farko ta shiga na biyu, idan ta ƙira wayarsa baya taɓa amsawa, tin da ya taɓa bata amsar cewa sai idan buɗar ido kawai yay yaga Meenerl ta dawo ɗakinta, kuma har gida ya sake zuwa shida Ahmad ɗin suka sake bama Baffa hakuri yace wllh babu komai, amma zancen kome kam babu shi, haka ma sun gode ALLAH ya amfana zaman da aka yi baya, Umman bata tashi aune ba se ganin katin ɗaurin auren Abban tayi ita da wata tsohuwar aminiyarta ta ƙut da ƙut, da duk wani tafarkin rashin kirki ita ke ɗorata akai ta aure mata mijin, aikuwa tayi kukan kura irin na mahaukatan nan ta buzanta taje har gidan ƙawar nata me suna Lubna suka kwashe tsiran karen mahaukaciya da ita, ta ce ita ai bata faɗa da mahaukata jahilai sedai da masu hankali. Aure ne kuma ta kwantar da hankalinta kamar anyi an gama ne ita da masoyinta IBRAHIM SHAREEF, tace mata babu boka babu malam kamar yadda ta sani a tsarin shedules nata, amma kuma tsantsanr makirci da kisiisina za suyi aikinsu da kyau, kuma ta zuba ido tayi kallon ikon ALLAH. Anan sema ta rasa bakin magana taje gida kuma zata ma Maman nata rashin m ta dakatar da ita ta hanyar mata tass,tace ai da lokacin da take bata shawarwari akan ƙawayen banza bata ji, gani take ma lokacin da ba ita ta haife ta bane take mata hassada, har takai ta kawo seda ta ɗauke ƙafarta cakk daga gidan Maman da itace ta reneta tin daga haihuwa, wacce uwarta na haihuwar ta ta mutu, wacce kuma a lokacin uban ita yahanasun da take aure yace ba zai riƙe taba shima rashin sa'a da baƙin halin jaririyar ya shafe sa ko ya kashe saba, ita ta rene ta shayar da ita amma daga ƙarshe sakamakon data bata kenan na tsameta daga cikin rayuwarta gaba ɗaya, se da iftila'in rayuwar data gama koya mata hankali ya sameta kana ta tuna da ita, bayan auren da sati biyu sega takardar sakinta har biyu daga mijin nata ya aiko mata har gida, yace tun da ta gaza dawo da Meenal ɗin dakin nata, afujajan ta isa gidan su Meenal gaba ɗaya ta fita a hayyacinta babu alamar kowacce iriyar nutsuwa tattare da ita, haka ta din gama Baffa kuka da magiyar ya taimaka ya ceci AURENTA Meenal ta koma ɗakin ta, wanda ita kuwa zuwa lokacin ma har ta gama zubar da komai taci gaba da gudanar da rayuwar ta yacce ta zaɓa mata. Ca yay da ita Meenerl da gidan Ahmad kan babu kome amma maganar aurenta da tayi yacce wannan zai taimaka mata da ƙarfin adda'a har mijinta ya dawo gareta, yace kuma ta gane tabbas su malamai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ta inda wani malamin yana kallar ana cutata diyarsa a gidan auren ta amma ko jarkar rubutu daya ba zai taɓa bata ba da sunan mallake wani, kuma itama yace babu rubutun da zai mata amma taje za taga ikon ALLAH In sha ALLAHU....
Duk se jikinta yayi sanyi ta ringa rokar tafiyar Meenal ɗin tace babu komai ita dama bata taɓa riƙe taba, don kowa yayi na fari kai nasa. Cikin kwanaki uku kuwa Malam ɗin ya ƙira Alhaji Ibrahim Shareef ɗin har ƙofar gidansa ya masa nasiha,yace kuma ya sani auren Meenal dama ALLAH yayi bame tsayi bane, kawai dai ita ta zama sila ne, wanda dama komai da yake faruwa a cikin duniyar yana da sila ko sanadi, yace indai don akan auren Meenal ɗin ne ba niyar juyama matarsa baya yayi ba to yayi hakuri ya maida ta,nan jikin Abban Ahmad ɗin yayi sanyi ya sake godema Baffan ya nufi gidansu Maman kai tsaye, anan gaban Maman ya sake ƙare mata tanadi ya kuma warware mata duk maganganun da uban wacce tafi tsana ɗin fiye da komai ya sanya shi amincewa ya dawo da ita ɗakinta, kuka ta dinga yi tana cewa sharrin zuciyane dana shaidan amma In sha ALLAHU bata sakewa ta tuba,tuba kuma na har gaban abada wllh. ALLAH sarki akace uwa uwace duk kuma inda ɗan uwa yake daɗi ne, haka kafin ta koma Maman ta sake bata wasu sirrika irin nasu na tsofin da da su suke kame zuciyar mazajensu, ta kuma sake mata faɗa da nasiha sosai kana ta koma gidanta. Sannu a hankali ta ringa sace zuciyar mijin nata duk da dama can ita ɗin ce a ciki, sedai rashin kirkin ta yasa ta fita a kan nasa, Gyaran kwanakin da kawai tasha a wurin Maman nata da adda'a 'oin data ɗorata akai suka fara tasiri, tuni ta sake janyo zuciyar mijinta gare ta, adda'o'i kala kala Maman ta bata, har da wani sirri data bata ganin yadda Ibrahim ɗin ya ɗan wazana Yar nata, tace ta nemi tsamiya cikin tafin hannunta biyu, wacce ba'a bare ɗin nan ba se da kanta ita ta ɓareta ta jika a cikin ɗan kofi haka, daga safe zuwa dare zata barta ta jika, idan dare yayi se ta ɗauko kofin data jiƙa tsamaiyar nan nata se ta karanta YA WADUDU, ƙafa bakwai, kowacce ƙafa ɗaya ta tofa a cikin ruwan, bayan ta kammala seta shanye ruwan ta ce da yadda ta bare wannan tsamiyar ta shanye ruwan ta haka ta ɓare zuciyar mijinta ta shanye, ta ce ta bata wannan sirrin ne kuma ba dan ta yi cuta ko tun kaho ba, ta bata ne kawai don ta kwato ƴan cinta daga wurin mijin nata da ƙawa ta mata kwace.... Kwarai ta bata sirrika da yawa masu kyau irin na gargajiya....
★..
Ahankali jirgin ɗaya taso daga ƙasar Istanbul ya fara landing a babban filin jirgin Aminu Kano, ahankali fasinja suka fara fitowa zuwa lokacin daya sanyi kansa shima a natse cikin layin passingee's ɗin dake fitowa a natse. Wata iska ya shaƙa ta ƙasarsa da kusan 3 months kenan da baya cikinta, sakamakon damuwar data kusa haifar masa da ciwon zuciya ya saka Daddy'n tattarasa ya komar wurin Yayansa ABDOUL-MAJEED, da dama sunansa ne Majeed ɗin yaci, Kansa a ƙasa ya fara tafiya yanajin kamar wacce aka yi safarar zuciyarsa daga wata ƙasa zuwa ƙasar ne, Taku yake yi cikin natsuwa wanda kallo ɗaya zaka masa kasan cewar ehhhh lallai MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ba ƙaramin jarumin namiji bane, yanda yaje kan matakin girmansa daya ɗara samartajarsa, se dai kyaun jikinsa ke ɓoye hasalin shekarunsa. duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai sedai yanayin murjewan fata dana jiki kawai wanda hasalin Luxury da Luxury suka gama ratsawa, se dai Yanayinsa kaɗai zaka kalla ka tabbatar da cewan lallai ba lafiyansa lau yaje ba .Amma darajar addininsa hadi karamci da kuma tsananin kwarjinin sa suka shanye yanayin san na kowanne irin halin da yake a ciki, Toyota Camry TRD ɗin da tazo ɗaukarsa ya nufa, sedai ga mamakinsa Bilal ne tare da Ikleemerh dama Ayla. Rumgume Ayla a jikinsa yayi yana sakin wata wahaltacciyar ijiyar zuciyar kewarta da kawai yayi. Hannu Bilal ɗin ya basa suka gaisa, Ikleemerh ma ta gaidasa ya amsa cikin kulawa kai tsaye suka lula zuwa gida...
Meenerl....
Alhamdulillah abubuwa sunci gaba da gudana cikin rayuwarta, inda dama bata da wata idda akan ta sakamakon barin cikin da tayi, sosai Baffa da yan uwanta sune ƙoƙari akanta,kafin kace me har masoya sun yi ca a kanta ciki kuwa harda samari don sunce ai sauta ga wawa ce, tin da ko shakera ba tayi da auren ba kuma ta fito, gashi ko haihuwa ba tayi na, sedai bata taɓa kula kowa har se da Baffanta ya mata magana, yace ta ɗauki dangana kuma ai dole zata yi auren ba wai ta ƙare shi bane da wannan ƙananun shekarun nata, kuka ta saka masa a lokacin tace ita Allah tsoron mazanma take, tsoron tayi zaɓen tumun dare take yi, nan su Yaya Sadeeq suka yi ta bata baki, ga nan ma wani nan cikin anguwarsu daya nuna yana son nata amma taƙi, don matarsa bata da mutumci suna na gaba gaba wajen aibantata a lokacin da wannan ƙaddarar ta sameta, don haka tace bata son shi, ita ta ma rasa ta yadda aka yi mutane suka san da maganar sakin nata, ita da tin da abun ya faru zata iya irga fitanta dududu be fi uku zuwa huɗu ba ƙarewa maza suka mata Caaaa aka. Se dai ana tsaka da wannan danbarwa se ga bayyanuwar Alƙalin daya mata Shari'a, wato ALƘALI YAHAYA SHEHU ƊAN BATTA shima ya faso cikin maneman nata, wanda tsananin tausayinta a karon farko ne ya addabi rayuwarsa, bayan ya bibiya lamarinta har ya gano mijinta ya rabu da ita, sedai beyi gaggawa don se wajen wata na biyar kana ya bayyana, wanda kai tsaye kuma ta hannun Baffa ya biyo ganin shi ba yaro bane, kawai ra'ayinta za'a tambaya masa ita in tana yin sa shikenan, wannan karamci da Baffan ya masa ne yasa har yake jin har abada ba zai taɓa mantawa da shi ba,a lokacin da Baffanta yake tinkararta da maganar se taji ta ɗan fi samun nutsuwa akan sauran mane man nata, don haka Baffan ya bashi umarnin fitowa yace ba da gaggawa haka ba, don yana son su fahimci juna kafin komai, don shi rayuwar soyayya yake son suyi bata alfarma ko ta girmama juna ba, don yana son soyayya sosai gaskiya, ɗan dudu du ba zai wuce 40 year's ba. Kuma jikinsa a gine yake daidai misali don haka ya fara zuwa zance, Maganar aikinta da ada har zata koma ta koma baya, ɗaukarta yake yana kaita wuraren shaƙatawa yadda zata sake sakewa dashi, ta kuma manta da giɓin dake cikin rayuwarta cikin sauƙi. ALHAMDULILLAH kuma sun fara fahimtar juna har tana jin sa cikin zuciyarta, Dake anan cikin Kanon yake anguwar SHARAƊA PHASE 0, kuma matansa biyu ata uku zata je, sedai ba gida ɗaya zasu zauna ba amma Baffanta yace inda hali ya haɗesu a gida ɗayan, sama yana da wadataccen gidan kawai dai dan kar ya zama kamar ya tauyi haƙkin tane ya saka shi ware mata gidan, amma se da ya sake tambayarta tace ba komai ALLAH ya basu zaman lafiya. 3 months ya saka bikin domin akwai buƙatan yayi wasu ƴan gyare gayre, ana saura 2 weeks bikin aka kawo lefen da ya bama koma mamaki don kowa be sha har wani laife ze mata ba, amma ga mamakin kowa se ga akwatu har guda biyar da kaya na kece raini a ciki, dede da wayar hannunta ya jima da sake mata ya sai iphone 13 pro max. Kuma gata hannunta Pop 9 Tecno, se ta barma Shareefah Pop ɗin nata ita kuma ta bama Bilkisu nata da itama babbace babu laifi, gwaggo Sadiya dai kada ran kada han haka take tsakanin nasu. Se ta ga dama take shiga lamarinsu in bata so bata shiga, amma su basa taɓa renata, ko kayan lefen ma a dakin gwaggo Sadiyan yake.... Kuma sunci gaba da mutumcinsu da Dr pooja har takan zo mata ma.
A lokacin da ya dawo Risach nata ya fara yi amma yaga bata dawo wurin aikin ta ba, don haka se ya cire duk wani abu daya danganceta yaci gaba da rayuwarsa kamar baya, Sedai yafi bama aikin company'nsa ƙarfi fiye da hospital ɗin, gashi ma shirye shiryen bikin Ikleemerh suke suma nan da 3 weeks.......
Kwanci tashi aka ce asarar me rai se gashi har ranar tazo, sosai Meenerl ta sake yin kyau na musamman wanda farin cikin wannan aure babu ya Shareefah don tana kallar kamar wahalar yayar nata ne ya yanke yazo ƙarshe se dai aka ce kashh?..... Cikin nutsuwa da aminci aka gabatar da komai cikin kwanciyar hankali,sedan tin da ake abun babu mahaifiyar Alƙali ko kaɗan. Ranar da aka ɗaura mata Aure da Alƙalin ranar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 14