Share this page
saura ƙiris Ahmad yabar duniya, amma kuma yana nan yana Adda'ar ALLAH ya fito da ita in yaso komar da ita, tin da dama haramta auren ai yayi, kuma zuwa yanzun Ummansa ta sake musulunta dan har wurin bikin ma tazo, tana sake kuka tana cewa ALLAH yasa Meenerl ɗin rabon ɗan tace, su a nufin su kamar tayi Auren kisan wuta kenan ta fito se ya sake aurenta, a ranta take jin batayi wannan auren don ta fito ba, kuma ko babu komai hankalinta ya sake kwanciya da Alƙali Yahaya Shehu ɗin tin da ya ɗan manyanta yasan darajar sosai, ita kuma dama can ba son ƴan bama bakwai ɗin nan tayi ba, sedai idan ta tuna cewar cikin mata uku zata shiga gabanta kan faduwa time to time, amma data gayama Yaya Sadeeq shi kuma ya faɗa ma Baffa se ya saka wani ɗalibi mata rubutu na tsawon sati guda, kuma Alhamdulillah ta rage jin hakan, har sauƙa Baffa ya mata tun da yaga wani shirun baya isar wa, kuɗinta da Ahmad ya turo mata lokacin daya mata sakin nan dubu ɗari biyar ta bama Baffa ya sake mata kaya masu kyau, duk da be so amsa ba amma haka ta matsa masa. Ankai ta gidanta lafiya bayan da akayi sallar isha'a, wasu daga cikin dangi suka mikata bayan sun shan koke koke ita da da Shareefah, dan haka Baffa ya hana rakiyan da ita yace daga baya taje. Dake da wata ƴar uwar ummansu dake ƙauye aka mata rakiyan, seda suka miƙata wurin kishiyoyinta inda ɗaya ta amshesu a mutumce ɗayar kuma ko zama bata bari sun yi ba ta ce ALLAH basu alkhairi ala kuma kade fitina, daga haka suka wuce nata bangaren da ita, nasiha suka mata sosai har da gwaggo Sadiya kana suka tafi suka barta cikin kewarsu da zata yi. Zuwa can wajajen tara da rabi sega Malam ango ya shigo ɓangaren amaryar tasa, jikinsa se fidda daddaɗan ƙamshi yake me cike da nutsuwa, tanajin shigowarsa gabanta ya yanke ya faɗi, amma tayi saurin ambatar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un cikin ranta, zame babbar rigarsa dake saman kayansa yayi yana ajjewa kan madubinta ruwan zuma, zama yayi daga gefenta yana sake saɓunta mata sallar da yayi, a ɗan tsorace ta amsa tana gaida shi cikin sanyin murya, jikinsa ya ɗan jawo ta yana ƙoƙarin zame mayafin dake kanta ta ɗan riƙe jikinta na ɗan rawa, a kunnenta ya raɗa masa wai da kar zafi ya miki illa ne, ga solar gidan naku ta kallace ta laso min kuɗi masu ɗan nauyi, dariya tayi ƙasa ƙasa ya miƙe yana shiga toilet, ya ɗan jima be fito ba don da dukkan alamu lodi ya rage ga amarya kuma se ɗan doddone hanci take, don fufu ɗin nashi akwai ɗan wari ba laifi... Yana fitowa ta dena doddone hancin cewa yay tayo alwala itama, shi ga tayi se famar zuƙe numfashi take dan har lokacin da wari warin fufu ɗin da yayi. Akan darduma ta tarar dashi yajasu sallarn raka'a biyu adda'a sosai ya musu ta zaman lafiya, kafin ya janyo lafiyayyun ledojin kajin daya shigo da su, plat ta sama a cikin locer ɗin madubinta kana ta ɗaurayo a ban daki ya zuba musu me ɗan dama, ita dai se kallonsa take don ba zata iya ci da yawa ba, kaɗan kuwa taci ta koshi shi kuwa ya buɗe ciki kamar ba'a gaban amarya yake ba yaci yay ƙat yay gatsa kana ya wanko bakinsa ya haye gado, jikinsa ya janyo ta gabanta nata faɗuwa, a kunne ya raɗa mata. "Da dukkan alamu wannan amaryar raguwace matsoraciya ce kuma me rowa, don haka ango yau ya ɗaga mata ƙafa amma ban da gobe...." Daga haka ya shigar da ita jikinsa bayan ya rage mata kayan jikinta suka kwanta. Washegari daya fita sallan asuba be dawo ba, ashe ɗakinsa ya wuce ya kwanta ƙarfe bakwai kuma ya fita wurin aiki lokacin daya leƙo tana bacci, tana zaune wata dattijuwa ta shigo da kayan kari tace itace me aikin gidan, duk abinda take buƙata zata iya mata magana, godiya ta mata kana ta saƙƙo tayi karin, a ɗarare ta ce matar ta rakata ɓangaren matayen, ta farkon dai a wani yankwane ta amsa gaisuwar data mata, ta biyun kuma da fara'anta , har tana tsokanarta ashe ma ƙanwar tasu ƴar shila, a dole mijin su ya nemi daya zauce musu. Anan da ɗan jima kafin rana ta tasa ta koma ɓangarenta, kafin dare har ta ware tayi wankanta cikin doguwan riga ta bacci me kyau, kwanciya yayi sedai babu jimawa yace ya shigo kissing ɗin goshinta yayi ta biyo sa, dogon hijjab har ƙasa ta saka bayan ta sake feshe jikinta da turare da humra kana ta fito, yana parlour a zaune yana jiranta kana ya kama hannunta suka nufi ɓangarensa daya kasance shima daban, Suna zuwa ya zare himar ɗin yana tsokanarta yau babu ɗaga kafa fa, murmushi tayi duk yacce gabanta ke faɗuwa amma haka ta daure, kwanciya a saman gadonsa yayi da yake ɗan cif da cif yana janyowata, hannunsa ya saka ya kashe wutan dakin yabar dum light me haske kaɗan, ahankalin ya soma mata wasu abubuwan, tin yana binta a hankali har se da kansa ya kwace ya bita a yadda yake so, sosai ya wahal da ita a daren, ɗan wajen 3 round ya mata, inda tayi da masa kuka da magiyar ya kyaleta,wanda dama a ka'ida bazawara kwana uku ake mata, da safe sosai ya sake bata kulawa sedai be sake yunƙurin mata komai ba, sedai kin fita ko ina yayi yana tare da jikinsa don shi kaɗai yasan kalan abinda yaji, don haka ya sharirince wajen bata duk wata kulawarsa, se da ya fita sallar zuhr kana ta gudu ɗakinta, ALLAH ma ya so ta bata haɗu da kowa ba har ta shige ɓangarenta duk tana jin kunyar kanta, idan ta tuno yadda ya ta mata wasu surutai kamar wani yaro ba babba ba, anan tayi har isha'a duk da se da ya biyota amma taƙi yarda ta bisa, ko da dare kafin ya shigo harta kwanta tayi baccin ƙarya, don wllh ita kunyar binsa take ƙara shi yazo hakan se yafi, tana kwance taji turo kofarsa da ƴar ƙaramar sallama, yana sanye da jallabiya fara ya isa har inda take kwance, zama yayi yana ɗagowa kanta ya ɗora akan cinyarsa yana sauƙe mata wani numfashi me ɗumi, cewa yay mata yau ma anan zasu kwana kenan kamar ranar farkon ta, ai kuwa ya mike yana zare jallabiyar jikinsa, saurin rumtse idonta tayi ganin ashe daga shi se jallabiyar yake, cikin bargon da take ciki ya shige yana ƙanƙame ta a jikinsa, wutar abinda yaji jiya na sake taɓa kansa da motsa duk wani yanayinsa, kwanaki ukun daya mata sosai ya darzi amarcinsa babu ƙarya, yo ya sama ƴar shila, wacce da suna biyu yake kiranta koya ce mata Ƴar shila ko jaririyata. Zuwa lokacin har ta fara wayewa da kowa na gidan yaransa bakwai, manya hudu ƴan madaidai biyu se ƙaramar da tsakiyarunsa ke goyo,uwar gidan hudu ne nata kuma suna manyan, daga su kuma bata sake haihuwar ba, kasancewar shi da kansa yake baka tsari, in kana son haihuwar da yawa fine yace se yayi ta maka cikin, idan kuma baka so se kaje asibiti a sa ma planning ko allura, babban ɗan sa namiji ne yana Abuja da karatu, ita kuma wacce ke bi masa Nusaimah yar shekara sha shida se maza biyu, ba laifi suna da tarbiyya bakin gwargwado don Nusaimah ɗin ma shigowarta biyu ɓangaren nata..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 0810449315 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏.... Page 21&22 *End of Last free Page's end🤗* # SingleAndThriving ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci riga da wando masu laushi. Kafin ta shiga fesa turare mai sanyi, bayan ta shafe jikinta da humra, tana cikin saka hula ya shigo yana sanye da pyjamasa blue colour sunyi matuƙar masa kyau, kallonsa tayi ta tarar da shima ɗin ita ya zuba ma ido. Sosai ya tsare ta da ido yana wani haɗiye yawun da yake neman sarƙe maƙoshinsa, ita kuwa gabanta se faɗuwa yake, don dama tunanin zuwa tirakarsa take don abin da kunya, wata numfashi ya ajje yana isa gabanta ya kamo hannunta ya tsotsi yatsarta ƙaramar, kafin ya rungumeta yana sakin ajiyan zuciyan kewanta da yayi. Wayarsa da yay ring ne ya saka shi rabata da jikinsa yana hanyar fita da hannu ya nuna mata ta biyo shi. Hijab kawai ta ɗora dogo akan kayan baccin dake jikinta ta nufi part ɗin nasa, baya palourn nasa hakan yasa direct ta nufi bedroom nasa, a zaune ta same sa a gefen gado yana danna waya. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta gabanta yana tsanan ta bugawa, a farkon gadon taja ta tsaya kanta a ƙasa tana wasa da hijab ɗin ta, sam bataji tahowar saba kawai sai hucin numfashinsa taji a fuskanta, hakan yasa da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa. Wani murmushi me kyau yai yana lasar lips ɗinsa, kafin yakai hannu ya zare mata himar ɗin dake jikinta, Ajiyar zuciya ya sauƙe yana kanainayeta gaba ɗaya a jikinsa. Sosai ya wani sake lafewa a jikinta wani daddaɗan ƙamshi na bugar masa hanci, ga wani kalan laushin da fatar jikin nata ke da, haba ai dole ne yake neman zaucewa akan wannan ƴar shila ɗin. Kai tsaye a gadonsa ya mata masauƙi shima ya kwanta bayan ya kashe musu fitila...... Washe gari ya rigata tashi sai da yai alwala sannan ya tashe ta, Hijab ɗin ta kawai ta ɗauka ganin ya fita don haka ta nufi hanyar fita, sai dai har takai ƙofa ta dawo a gurguje ta gyara masa gadon dakin ta fita. Sallah tai ta shige kitchen ta musu breakfast don yace kowa ta ringa girkinta kuma duk wacce take dashi itane zata ka abinci dashi, lokacin daya haɗe su ya musu nasiha...Breakfast ɗin ta ɗiba takai masa parlourn sa, sedai tana shiga ta tarar da Matarsa ta biyu me suna Raƙabiya ta wani hakimce a parlourn ita da yaranta uku, da ɗan murmushin yaƙen data ƙaƙaro ta iso tsakiyar parlourn tana ajje breakfast ta gaida ta a mutumce, wani tsuka tayi tace ta riƙe aunty'nta bata so zata iya ƙiranta da Raƙabiyanta ma fine, bata ce komai ba ta shige bedroom nasa don masa magana, a gaggauce ta gansa yana shiryawa tace lafiya ko wani wurin zashi?, yace mata wllh Mima ce bata da lafiya ze miƙa su hospital. ALLAH ya bata lafiya tace masa suna fitowa a tare se dai abinda ta tarar ne ya bata mamaki, da uwar da ƴaƴan ne gaba ɗayansu suke biki akan breakfast ɗin data kawo masa, shi ma sai da ya ɗan yi turus kana ya isa gabanta yana tambayarta ko miyeye dalilinta na cinye musu abinci, tana wani kwarkwasa tace... "Kasan jiya nace maka kwana mukai bamuyi bacci ba, shi yasa ko abincin na kasa tsayawa na mana..." A ɗan tsawace yace da ita kuma duk masu aikin gidan basu mata ba har se tazo ta nemi fitina?, wani ƙututun baƙin ciki ne taji ya ƙume don haka ta miƙe a fusace fuuuu taja hannun yaranta tana cewa tama fasa zuwa asibitin... Kwanci tashi aka ce hasarar me rai se gashi har sunyi wata huɗu da aure suna daf da shiga na biyar ma, kuma Alhamdulillah zuwa yanzun sosai take sakin jiki da Alƙali Yahaya,sedai har zuwa yanzu tsakaninta da tsaki yarunsa Indai sun haɗu su gaisa sama sama ta wuce itama ta wuce. Don ba ƙaramin kishi ne da ita da sam bata iya sarrafa shi, tsakanin ta kuwa da Uwar gidansa Hajiya Asma'u se son barka. Don tamkar ƙanwa haka ta ɗauke ta, duk da dai itama tana kishi da Meenal ɗin, ko dan sabo da yadda Mijin nasu hankalinsa yafi karkata akan Meenal ɗin, komai yace ita duk randa zai koma ɗakin ta uban kowa se yaga kalar rawan ƙafan da yake, amma duk sanda ze bar ɗakin nata kuwa kusan kowa se yasan yadda baya son ya baro ɗakin nata, in me girkin ma batai wasa ba ranar ko kallo bata ishe shi ba, amma fa idan ta tanka masa, don duk da hakan yana ƙoƙari sosai don abinda yake zasu daga yarinyar shi kadai yasan kayansa. To amma sedai takan danne hakan itama ta kuma yi adda'a, amma banda shugaba Raƙabiya da ake kwasar yan kallo da ita... Tin wajen ƙarfe tara saura yake zamar jiran shigowarta har gashi yanzun wajajen goma saura, don haka ya miƙe ya nufi Part ɗinta ya shiga ba kowa palourn kuma palourn a share yake sai dai ba wani ƙamshin da kullum baka raba parlourn dashi, bedroom nata ya nufa kai tsaye kwance ya same ta ta dugungune a cikin bargo, da sauri ya isa gaban gadon yana kaiwa zaune, hannunsa ya ɗaura a gefen wuyanta Jin zafi rau ne yasa shi faɗin "Baki da lafiya Meenal amma shi ne baki fada min ba?" Rintse idonta tai hawaye suka silalo tace "Daddy na ƙira ka ai amma bai shiga ba kuma wayar tawa ta mutu ban sa a charge ba" takai ƙarshen maganar a mugun wahalce. Ɗan shiru yayi na wani lokaci kafin ya miƙe yace "Bara na dauko mukullin mota muje hospital, ai zama da jinya babu daɗi...." Yay maganar yana fita, babu ɓata lokaci kuma se gashi ya dawo hannunsa riƙe da car key, da kansa ya taimaka mata ta saka kaya ya tallafota suka fice zuwa compound na gidan, da ko ina hasken solar da bata jima ba aka gyara, suna gaf da isa gaban motar se ga Raƙabiya kamar wacce aka cillo daga sama, kallo ɗaya ya mata don haukarta tayi yawan da ko tanka ta baya son yi, gaba ɗaya yanzun kaff gidan itace me basa ciwon kai. Be kula ta ba sema kwantar da Meenal da yayi akan kujerar motar, kana ya zaga ɓangaren me zaman banza yaja motar suka fita, kai tsaye wani private Hospital ɗin dake nan kusa da su ya kaita, sai da ya buɗe mata file sannan suka shiga gurin doctor ɗin. Ƴan tambayoyi tai mata dake Dr ɗin macece kafin ta kira nurse tace suje ayi mata test, nan suka je aka mata shi dai Alƙali Yahaya yana ta adda'ar ALLAH yasa ciki ne da ita, sedai saɓanin hakan ya samu don cewa sukai maleria ne ya mata yawa. Magunguna aka basu suka koma gida, anan ɓangaren nata ya kwana yana kulawa da ita, washe gari bayan ya dawo daga sallar subhi ya dawo se ya ɗan janwota jikinsa bayan ta gaida shi yace.... "Wai yaushe zaki bani baby?, ina son inga kin haifa min baby kyakkyawa me kama dake..." Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsun hannunta tace "ALLAH ne be kawo ba amma nima ina so ai..." "ALLAH ya kawo mana masu albarka" yace yana fita kai tsaye don shiryawa ya tafi wurin aikinsa. Sannu a hankali ababuwa suka fara cakuɗema ma Meenal a gidan, ga yara da kamar ma turo su ake takanas su mata rashin kunya, in abu ya sayo irin duk gidan nan se an ga dama za'a raba da ita, gashi yanzun kamar sun haɗe mata kai ne, bata da wata kyakkyawar sukuni a gidan, tin bata kai masa kara har ta fara don ababuwan sun fara fin ƙarfin, ga wata shegiyar rama da tayi ita ba wacce tasan jinyar laulayi take ba, tin a wasu ababuwan yana bin bayanta yana bata kariya harta kai ta kawo yanzun se dai ma ya hauta da faɗa da masifar cewa da shi duk be san wasu ababuwan nan ba se da auro ta, shifa yanzun wani bin har dana sanin aurenta yake, gaba ɗaya ta gama ficewa a hayyacinta gashi tin da aka yi auren zuwanta gida befi uku ba, don matsin lamba ce dashi wajen fita, kuma baya taɓa barin ta wuni sedai taje da magribar fadi isha'a yaje ya ɗauko ta, wai a hakan ma ada ɗin kenan yanzun wani bin ma girkinta yakan shiga har ya fita bata saka Alƙali a idon taba, kafin taje ya rufe ɓangarensa wanda tin abun baya mata ciwo har shi ma ya shiga sahun daya sake figar da ita, idan kaga yadda ta tsige ta rame zaka ɗauka DEEPIKA PUDAKUNE ce farkon shigarta BOLLYWWOD dan rama, ko ina se ƙasusuwa da ƴan hakwara likely dai tamkar deepika ɗin ga duk wanda ya mata farin sani farkon fara film nata lolz🤩. A lokacin da Shareefah ta mata zuwan ƙarshe da kuka suka rabu ita kuka itama kuka, amma tace karta faɗama Baffansu ko yaya Sadeeq su tashi hankalinsu, gashi shirye shiryen bikin Shareefah ɗin da Bilkisu ake lokacin, dan dama kusan fikon turakane tsakaninsu. Ko da ta koma gida adda'a ta dukufa yima Sister ɗin nata kan ALLAH ya yaye mata dukkan abinda ke damunta, in kuma rabuwar su ce alkhairi Ubangiji ya bama kowa hakuri don idan wata ukubar tayi yawa rabuwan shi yafi alkhairi... Ita kuma Meenal a nata ɓangaren ba taji zata sare ba, za taci gaba da juriya da hakuri In Sha ALLAH, don bata son aurenta ya sama matsala se adda'ar itama data riƙe da nafilfilu kuma har lokacin ko ɓatan wata bata taɓa yi ba a gidan. Komai take cikin ƙarfin hali da ƙarfin zuciya take, wanda hakan har bama Shareefah mamaki take, don ta sha tambayarta ita kuwa wanne kalan ƙarfin hali ke gare ta, takan yi murmushi a lokacin tace mata. _Wani lokacin muna murmushi ne domin kar duniya tasan ciwon dake cikin zukatanmu.._ Akwai mutanen dake kewaye dani amma babu wanda ke fahimtar irin kaɗaicin dake cikin zuciyata, ina murmushi ne kawai don kar a tambayeni amma har cikin zuciya hawayene ke kwarara ba tare da tsayawa ba. Na koyi zama ni kaɗai na kuma sake yarda da wasu ke cewa, wasu mutanen daga nesa suke burgeka saika haɗa hulɗa dasu zaka yi nadama. Wasa wasa se gashi har gashi har mun shiga wata na huɗu cikin wannan matsalar, wanda ya kama watanmu tara da aure kenan, tuni kuwa har wasu ƙananun maganganu sun fara fita waje har zuwa can cikin anguwarmu, wai Miji da kishiyoyi nacin ubana suna soya min aya a hannu, duk lokacin da zanji makamantan zantukan kalan hakan nakan yi murmushi ne kawai kamar yadda na saba, murmushin na lulluɓe duk wani miƙin dake cikin zuciyar tawa... Yau dake girkin tane da wuri ta kammala shirinta, don yau itama ta tanaji kalaman fara dawo dashi kan daidai ɗinsa, da huri ta isa lokacin ɓangaren nasa tin kafin ya shigo, amma se da ta tabbatar me girkin ta fita kuma Maman Abeed ce wato Raƙabiya. Ɗakinsa ta fara gyara masa tsaf kana ta fito parlour ta kunna kallo, tana zaune sega Maman Abeed ɗin ta shigo kamar wacce tayi mantuwa, bata ko kalla inda take ba har ta gama juye juye da aune aunenta ta kama hanya ta fice bayan ta mata tsaki, amma in ta tankatama ai ta sama arziƙi... Babu jimawa kuwa se gashi ya shigo ɓangaren nasa, sedai turus yaja ya tsaya yana kallarta da take cikin shigar kayan bacci masu kyau. Zaune ta tashi fuskarta ba yabo ba fallasa, sannu da zuwa ta masa lokacin da yake kaiwa zaune saman kujera. Gaidasa tayi a natse ya amsa yana jin duk babu daɗi da abinda yake mata, Se dai babu yacce ya iya ne dole ne saboda ya na son bata kariya.... Se dai be san da wanne bakin ze mata magana ba, be kuma san da wanne idon ze dube taba, wata ajiyar zuciya ya sauƙe yana kamo tafin hannunta cikin nasa, lumshe idonsa yayi yana jin kamar zuciyarsa zata fashe da tsananin ƙaunarta da tausayinta. Ahankali ta zame hannunta daga cikin nashi tana kaiwa ƙasa cikin rawan murya tace... "Daddy'n Nusaimah don ALLAH ka yi hakuri idan na baka wani abu ne ba tare da sani naba,kasan duk inda ɗan Adam yake azijine wllh ban san kome na maka ba, na kuma duk iyaka yi na amma ban gano daga inda matsalar take ba... Daddy'n Nusaimah Me ya sa kake ƙoƙarin sanjawa daga yadda na sanka?, Me ya sa kake ƙoƙarin daina bani kulawanka?, Me ya sa ka daina jin tausayina?, Me ya sa a yanzu bana gabanka?, ka dena lallashina. Me ya sa ka sanja min cikin ƙanƙanin lokaci haka?, Me ya sa?, Me na maka?....." Tayi maganar muryanta na rawa sosai... Hannunta ya kamo tare da ɗago ga yana share mata hawayen fuskarta cikin taushin murya yace. "Baki min komai ba Ameenatou!,babu abinda kika min wllh, kawai ina jin kamar ba daidai nake ba, ina kuma jin kamar ban chanchanta inci gaba da zama dake irin haka ba, sedai na rasa akan me akan kuma wane ne..... Wani kuka ta fashe dashi tana me furta. "Tabbas na fara zargin kaina da cewar ko ababuwan dana aikata ne ALLAH be gama yafe min, amma nima a cikin raina inajin kamar cewa tabbas wata rana zaka rasani, sannan zakai kewata ba don nafi kowa ba, ba kuma don na zarta sauran matan kaba, A ahhh se dan kawai na san ranar zata zo maka wata rana, kuma idan wannan ranar tazo, kada ka kira shi da ƙaddara, ka ƙira shi da sakamakon abinda ka aikata!!!, tun da na tambayeka laifi na kace ban maka komai ba, haka kawai zuciyarka ta tsara maka fara tsanata sabo da binciko tsoffin laifukana na baya shi ne ka fara ɗora alamar tambaya akai na ka kuma dena SO da TAUSAYINA, wanda dama nasan su suka huce maka gaba wajen auren na...." Daga nan ta kwace jikinta a nashi ta fice daga ɗakin a guje tana riƙe bakinta da kuka ke son kwace mata...Ahankali kuma taɗan buɗe idanunta wanda cikinsu ya cika da ruwan hawaye, ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, tare da ƙoƙarin shanye ruwan hawayen nata, dan batajin zata iya barinsu sukai ga sauƙa akan fuskar _MAJEED DAWOUD_ zaune yake saman sofar dake gaban gadonsa, system na shi ajiye saman desk se wasu ƙananun glass cup yana opreting wasu files na asibitin daya ziyarta na Young pharmacy and private clinic...tshirt ce mai gajeran hannu a jikinsa sai dogon wandon ta masu taushi. Idanunshi a sakaye cikin farin glass ya zuba su akan system ɗin da yake ta famar aikinshi akai. Daga gefen sa kuwa Ayla ce kwance ta dora kanta saman jikinsa,kanta babu scaf anyi saima space buns ɗin da aka mata irin na Babyn nan, wanda suka mata kyau sosai gwanin birgewa... Duk da kasancewar aikinsa yake gudanarwa amma kuma ƙasan zuciyarsa mamakin abinda ya gani yake, amma duk da haka cikin ƙarfin halin danne abu a zuciya da kuma yanayin sa na rashin bama abu mahimmanci da basarwa ya ture tunaninta a ransa, se kuma yayi saurin istighfari a ƙasan zuciyarsa yana sakin wata ajiyan zuciya, abinda ya danne ƙirjin nasa na ɗan lafa masa yana jin ɗan sassaucin ba kamar ɗazun ba. Shiru kawai yay yana lumshe idonsa tare da jingina bayansa da jikin gadon, kafin ya sauƙe idonsa ahankali akan Ayla dake lafe a jikinsa tana bacci hankalinta kwance, sake lumshe lumsassun fararen idanuwansa yayi yana ɗan tafiya wata duniya... Wani gauron numfashi ya kawo kuma jin numfashinsa na shirin fiffizgewa , alaman tunanin daya tafi me ɗan zurfi ne. Da Ayla ya tashi a jikinsa kai tsaye Part na Ummiensa ya nufa, kai tsaye ya kwantar da ita a gadon ummie bata ɗakin, peck ya bata a goshi kana ya fice yana komawa room nashi. Zaune yake dafe da kansa ya ɗan jima a hakan kafin yayi kundin

Chapter 13 of 14