Share this page
kafin komai ya dawo mana dai-dai gwargwado iyaka abinda naga naga zan iya, ba zan rabu dake ba INA SONKI ina ƘAUNARKI Meenal........" Sosai ta buɗe ido da baki da hanci tana kallarsa da wani kalan yanayi, kafin bakinta na rawa ta ce... "Har yanzun kana jin zaka iya ci gaba da zaman aure dani Ya Ahmad?, bayan na gama take aurenka dake kaina, wasu kuma sun gama wulaƙanta martaba da yardar dake cikin auren namu amma har yanzun kake jin zaka iya zaman auren dani?...." Kansa yake ɗan jujjuya mata kafin Yace... "Kifar taso da abinda ya riga da ya gama faruwa, ki ɗauka hakan a wani issue ne na daban daya shafi interest nawa da kuma naki kawai, ki dena sako ko danganto wani a ciki domin zuciyata ba zata ci gaba da jure hakan ba...." Wani kuka ta saka tana ɗamke hannunsa dake cikin nata take furta. "Na gode!, na gode ALLAH, Alhamdulillah ko yanzun ALLAH ya ɗauki raina na gode masa...." Rumgumeta kawai yayi domin bazai iya ci gaba da saurarar kukan taba, daga nan Dr pooja ta shigo ta sake dudduba jikinta ta haɗa mata magani ta basu sallamar da ita ce da kanta tace a basu, Sosai Baffa da Ya Sadeeq suka ta yima Ahmad ɗin godiya don duk dama zullumin hukuncin da zai yanke a kanta suke da tsoron kar ace ya rabu da ita, Se da suka musu rakiya har gida kana Baffa ya sake jaddada godiyarsa ga Ahmad kana suka bar gidan.... Bayan tafiyar su Baffan sun jima zaune a wurin zaman kurame kafin tayi kundin balar sake nemar yafiyarsa gare ta, Komai bai ce mata sema tashi da yayi ya bar mata parlour ya shige bedroom nashi, don kansa wani bala'in ciwo yake masa, koda ta bishi taji ya rufe ɗakin kanta kawai ta jinginar da jikin ƙofar tayi kukanta me isarta a wurin, kafin taja ƙafafunta ta nufi bedroom nata, kwanciya tayi zuciyarta na wani kalan mata bugu da tafasa, ƙarfe biyu bayan tayi Sallah ta fito tayi girkin rana, ɗakinsa ta leƙa daga a rufe ta woje alamar ya fita kenan, kaɗan ta ɗan cakali abincin itama ta ture ta koma tayi wanka ta ɗauki Alqur'ani tayi karatu, har kusan yamma sosai tana nan zaunen kafin ta tashi taje ta meda na dare, bayan ta kammala tayi sallar magrib, ta sake karatun Alqur'ani tsakanin magrib da isha'a, wajajen tara taji alamun shihowansa gidan, tayi hanzarin fitowa jikinta da himar har ƙasa, daidai lokacin yake ƙarasa bayyana a cikin parlourn, sannu da zuwa ta masa ya amsata da hannunsa yana ƙoƙarin wucewa, cewa ta mishi ga abincinsa yace ya gode amma ya koshi, bata ji daɗi ba amma haka ta danne ta kyale shi, kana ta mara masa baya zuwa ɗakinsa, Sedai ya dakatar da ita ta hanyar ce da ita tayi haƙuri yana bukatar balance ne sosai, don haka ta dawo parlourn jikinta a matuƙar sanyaye, seda dare ya tsala sosai kana tabar parlourn, koda ta shige bedroom nata bata kwanta ba Alwala tayi ta fuskanta alƙibla, ta fara jero sallolin da bata san iyakar su ba, har aka ƙira asuba, A hankali ya turo ɗakin nata don tada ta tayi sallar subhi ɗin, Sedai ganinta a zaunen da yayi ne ya saka shi fita be ƙaraso ba, wajan shida ta fita ta ɗora musu brekfast. Lafiyayyar Doya da kyau ta musu, da lemun kwakwa, a gurguje taje tayo wanka kana tazo ta zauna cikin parlourn tana jirar fitowar sa, babu jimawa kuwa se gashi ya fito da brifcase nashi a hannunsa ta fita aiki, saurin miƙewa tayi tana isa gare shi yay hanzarin janyewa ya koma gefe guda, kanta ta sunkuyar ƙasa ta gaida sa, amsata yayi sama ² tace dashi ga breakfast yace da ita ya gode zeci a woje. Kusan a wannan karon kam daskarewa a tsaye tayi, shin me yake nufi ne wai, ko dama shi ne haƙurin da ya ce se tayi? In sha ALLAHU zata yi za kuma ta jure da Ikon ALLAH... Tin tana kallar kamar zata iya jurema yanayin, har hakan ya fara fin ƙarfin tunani da kuma kanta, don takai ta kawo ko zama ya dena yi inda ta zaune, tayi kukan tayi adda'ar amma duk a banza, abinci kuwa dama tuni ta dena yi dashi, don ko tayi Sedai ta tayin asara tana bama getman ya rabama almajirai, abinda ya sake bata mamaki kuma shi ne da sati ɗaya da faruwan abun ya zo mata da zancen zata iya ci gaba da aikinta tace ta dena ta haƙura har gaban abada, komai daga haka be sake ce mata yaci gaba da rayuwarsa, har takai ta kawo gidan ma yanzun kafin ta tashi ya fita, lokacin da zai dawo kuma tayi bacci, inda sosai hakan ke damunta, har take jin ƙara kawai ya rabu da ita idan har hakan shi ne mafi alkhairinta, saboda da wannan matsalar nasu har Shareefah seda ta tuntuɓa da lamarin, kai tsaye kuma tace da ita ta ƙara hakuri akan wanda take yi, In sha ALLAHU komai zai wuce, gama hucewar ne be yiba. Tin Dr pooja na ƙirar ta har ta haƙura, inda daga ƙarshe take jin kyakkyawan labarin musluntar Dr pooja ɗin, wacce ta musulunta a hannun Baffansu a masallacin ƙofar gidansu, a yanzun haka tana amsa sunan AYSHA ne, tayi murna sosai da jin lamarin na musuluntar da tayi, Ta inda take sake godema ALLAH ma shi ne da bata da komai, idan kuma ta tsaya ta tsai da ranta rashin samun cikin da batayi ba a tin farkon Aurensu har zuwa yanzun kan damunta, se dai shima ta barma ALLAH lamarinta, haka sukaci gaba da gudanar da rayuwar Aurensu, ba tare data sake fuskantar kowa da matsalar ta ba, har kimanin 2 Months, gashi ma har suna kokarin shiga na uku... Masu iya magana sukan ce a duk lokacin da wani abu ya tunkaro ɗan Adam yana yi masa barazana da rayuwarsa, sai yaga kamar duk duniya babu wanda ya kai shi shiga tsananin rayuwa. Har takan kai wasu ƙarancin imanin fara fafutar nemarwa kansu mafita ta kowacce siga ce kuwa domin kawar da ita wannan matsalar da yake fuskanta. Kamar yadda ya kasance a cikin rayuwar Meenal a ƴan tsakan kanin lokutan da suke wucewa a cikin rayuwar aurenta da Ahmad. Lallai ta sake yarda da wannan maganar da ake yawan cewa. Ciwon da ya addabi hannu idanu yake hanawa bacci. Idan ido bai yi bacci ba to lallai dukkan jiki ba zai huta ba. Jikin da rashin hutu ya yiwa sarƙa kuwa yana tattare da ƙarantar kuzarin kare kansa daga bullowar wasu cututtukan ne, Kamar yacce sannu a sannu wani irin ciwon da bata san ko ainihin na minene ba ke famar wajiga rayuwarta, Ta kuma sake yarda da ake cewa idan bamu magance ciwon hannun ba, da sannu sannu shi dai wannan ciwon zai iya kama ragowar sassan jiki ko kuma ya bayar da ƙofar samuwar cutar da tafi ta hannu. Sannu a sannu rayuwarta ke ci gaba da gudana cikin kunci a gidan Ahmad, ga ciwon dake ƙoƙarin kaita ƙasa amma tana gwada jarumtarta akan hakan, har tana daukar hanyar wata guda kenan da wannan jinyar, wanda a zahiri na gaskiya ba haka hasalin lissafin yake ba, wannan jinyar alamu ne bayyanuwar cikin haihuwa a jikinta, sedai tsananin kunci da damuwar da take ciki be saka ta fuskanta hakan ba, ko daga yanayin sanje sanjen da take samuwa daga wasu sassa na halittar jikinta, se dai idan aka ce tashin hankali to anan nufin gaba da komai kenan, don babu cikakkiyar nutsuwar da ya kamaci ace ta tsaya duba ko tantance yanayin da take a ciki ba... Ranar da ba zata taɓa mancewa da ita ba a cikin rayuwarta itace ranar wata LAHADI, ranar ta tashi ne kamar ba ta kai labari ba, gaba ɗaya tin daga kamo daren ranar har kamo la'asar ɗin ranar haka ta wuni a kwance ko ruwa kasa zama a bakinta yayi, tana daga kwancen a yadda take ta fara ƙoƙari da yunƙurin miƙewa, da shigowar Ahmad sassan nata da rabon daya shigo shi har ta manta, gaba ɗaya ya gama fitar da ita daga cikin rayuwarsa tun faruwar wancan lamarin, ko zama kusa dashi be sake bari tayi ba. Kin kallar inda take kamar ko da yaushe, kamar yaga dogon zunubin da ze iya kifewa koya halakar dashi, haka ya dubeta yace tayi maza ya shirya ta fito yana jiranta a mota, tambayarsa tayi lafiya ina kuma zai kaita, wayarta yace ta duba Dr pooja (AISHA) tayi ta ƙiranta amma ta gaza taƙi amsawa, ƙoƙarin komawa kwancen data yunƙura ta tashi take, tana ce dashi..... "Babu inda zani Ahmad!, ai na faɗa mata bana jin daɗi ne, ko kuwa duk Dactor's ɗin dake cikin asibitin basu isa ba se lallai dole ni naje???, Haba Ahmad da wanne kake son inji, na baka hakuri kaki ka haƙura ka fita a cikin rayuwata, ka dena sakewa dani ka dena kusantata, komai daɗa lalacewa yake, memakon ace samun sassauci nake, Bayan kuma na baka hakuri na baka hakuri, don girman kayi hakuri mana..." Tsaiwarsa ya gyara yana fuskantar da kyau yace. "Wanene ya gaya miki ban haƙuraba?, Idan da ban haƙura ba da tin tuni kin jima da tafiya gida!, kinga yanzun dai wannan a matsayin umarni da kuma temakon rai zakiya, kasancewar weekend na babu yawaitar manyan Dactor's duk se ƙananu shi yasa suka biyo ta hannu nama, Dr Bilal ne yamin waya don shi ashe ma baya 9j ɗin ne......... Da kyar ta yunƙura tana shigewa bathroom, babu jimawa ta fito babu laifi kuwa taji ƙarfin jikinta sosai, don haka ta zira doguwar hijjabarta har ƙasa ta fito ta same shi cikin motarsa. Karatun Afid muhd taj ya saka musu, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa asibitin, tin daga yanayin tsaron da aka bama hospital ɗin ta gane cewar lallai wani babban ne ko ɗan gidan wani kusar ne me jinyar, tana isa ta shiga wani room ta sanja kayanta zuwa na surgery, hannunta da handglovs idanunta da glasses fari ta nufi ICU inda nan ne me jinyar yake, Dactor's biyu ne suka mara mata baya ta shiga, tana isa Dr Aysha dake kan majinyancin ta bata hanya, isa tayi gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta ta saka hannu kenan da niyar amsar tiyatar idanunta ya sauƙa akan................... _To fa shin akan mene ko waye idanun Dr Meenerl ya sauƙa?..._ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. Page 9&10 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Wannan fuskar da ba zata taɓa mancewa da ita ba, ita dai wannan fuskar data mata fyaiɗe ta kuma wargaza rayuwar aurenta. Ta raba da da daraja da kuma kimarta, don haka bata san lokacin data saki Scissors ɗin dake hannunta tana zare glass ɗin ta jefar a ƙasa, tare da handglovs da hannunta ke ciki, bakinta ta toshe da duka wannuwanta tana fitowa daga ICU ɗin, idanunta na ƙoƙarin rufewa ko ganin gabanta bata yi, saboda dishi dishin da take kalla, kanta na mata wani kalan masifa da bala'in bugu na ƙafar ya zazzago ƙasa, ganin yadda ta koma lokaci guda ne ya saka nurses biyun dake tare da ita saurin mara mata baya suna tambayar lafiyanta kuwa?, Komai ƙin ce musu tayi har seda ta danga da lafiyayyun kujerun dake center na asibitin, irin na zaman jiran marasa lafiyar nan, babu jimawa sega Dr pooja (Aysha) ta bayyana a wurin tana cewa "Lafiya kuwa Maanol, meke shirin faruwa haka?, naga ma har kin cire uniform ɗin tiyatar?" Idanunta da take suka sanja launi ta ɗago tana kallar pooja ɗin tace, "Sabo da bazan taɓa iyama wannan mugun mutumin tiyatar bane...." Ɗan ja baya Dr pooja ɗin tayi ta ce. "Sabo dame Maanol?" A matuƙar tsawace ta ce. "Sabo da shi ne mugun mutumin daya min fyaiɗ....... Bama ta ƙarasa ba sabo da tsabar yadda ta sarƙe har numfashinta na kamar zebar gangar jikinta... Ga idanunta daya fara ja baya yana lumshewa kamar zata sume... "Subhanallahi Dr Meenerl!!!........... Ɗaya daga cikin Dactor's ɗin ta faɗa don babu wanda ya lura da yanayin sanjawa yanayin nata, don haka Dr pooja tayi saurin tallafota amma tana zamewa ta ma mike ta shige wani daki ta bugo wani kalan masifar kuka na taso mata, akan wani gadon marasa lafiya ta faɗa kukan na kufce mata da tari wanda tarin na fitowa sega jini ya faɗi gudul, zuciyarta ta danne gefenta da hannunta tana ambatar. "Hasbinallu wani'imal wakeen ³" babu jimawa sega Dr pooja ɗin ta sake biyota riƙe da wayarta a hannunta, miƙa mata wayar tayi tana saka ta a handsfree, kamar sauƙar aradu haka taji saukar muryan Ahmad yana bata umarnin Lallai lallai tayi aikin nan, "Wallahi bazan yi ba Ahmad, ba zan iya ba...." Daga ta ɗauka wayar nata tana dokata da ƙasa ta tarwatse kuwa take, zama Dr pooja ɗin tayi tana tallafota ta ce. "Haba Dr Maanol!, kiyi hakuri mana ki fara ceton lafiyarsa, ya kike abu kamar wacce baki san dokokin asibitin nan ba?...". "Wllh babu wanda ya isa ya saka ni yin wannan tiyatar da dai nayi masa ya sama lafiya yaci gaba lalata auren mutane ƙara ya mutu ko babu komai an rage mugun iri." Takai ƙarshen maganar nata zata miƙe, saurin dawo da ita zaune Dr pooja tayi tana sake furta. "Haba mana Maanol yanzun idan ya mutumin nan ya mutu kuma fa?, kin san iyayen yaron nan zasu iya kaimu ƙara kotu fa...." A ɗan zuciya tace "To bazan yi ba, na gaya miki bazan mai aikin nan ba, SO duk ku rabu dani sabo da ba'a dole...." Suna cikin haka sega shigowar wata Matashiyar mata a ɗan burkice, kallo ɗaya zaka mata ka gane cewar bata a hayyaci da nutsuwarta sosai. Har ta zarta su ta dawo tana me furta, "Ina ne inda ɗana yake?...daga yanayin yadda hankalinta yake a tashe ne ya saka su gane cewar uwar yaron ce, don haka kai tsaye nurses ɗin dake gefe da ita tace "Nan ne...." Tana mata nuni da ɗayan ɗakin dake ta bayansu ta glasses,don ɗakin da suke ta fado kai tsaye. Babu jimawa kuma se gata ta dawo tana balbala masifa da bala'in... "Where Are You The Dactor's?, kina ina?, tana ina?, me kike nufi ne?, so kike ki kashe min ɗa ne?, shin dama ba biyanki ake ba?, ko kuwa ba aikin ki bane?, to maza ki tashi yanzun ki duba min yaro!!!, Dan wllh² idan ya mutu sena nuna miki irin ƙarfin ikon da muke dashi a ƙasar nan, kin ji ko maza ki tashi kije ki duba min yaro....." Gaba ɗaya tin da ta fara maganar nata da hargowa take, gaba ɗaya bata cikin hankalinta....... Tsaye Meenal ɗin ta miƙe ta saka idonta cikin tsaƙiyar na matar bayan ta nuna ta da yatsa tace, "Bari kiji in gaya miki indai akan wannan dabbar ɗan naki ne!, to ba zan masa aikin ba!, in kuma anayi doke to bismilla ki sani inyi mu gani?... Wani ihun daya kusan cika harabar wurin tayi tane me furta. "Ƙarya ne!, Ɗan kwara ɗaya ya mutu? Wllh ƙarya ne kuna ina.....ina....ina...ina me asibitin yake?, yana ina Wllh sena sa an ɗaureku idan ɗana ya mutu baku duba shi ba...." Tafiya zata yi tayi hanzarin shan gabanta kamar za tayi kuka kuma ta ce. "Dan ALLAH kiyi hakuri ki duba min shi, shi ɗaya tal ne dani...." Wasu hawayene suka zubo mata tace bazan taɓa iya duba ɗan ki domin shi ne ya ruguza yardar dake cikin aurena, ya lalata min gobe na!, ya kuma illata rayuwata,illar da bata da ƙarshe har gaban abada..... Hannun Meenal ɗin matar ta kama tana shirin kaiwa tsugunne amma Meenal ɗin tayi hanzarin fizge jikinta daga gare ta, cikin ɗaga murya matar tace. "Don ALLAH baiwar ALLAH ki fara duba min yaron nawa!, in yaso in warware ko....ko...kome kike so se...se....se.... Ayi Don ALLAH kiyi hakuri......" Takai ƙarshen maganar nata ta na zubewa ƙasa tana ci gaba da kuka, se ga fitowar wani Dactor nan yana share zufar dake zubo masa, kansa matar tayi da gudu tana me furta, "Ya farfaɗo?, kun duba min shi?..." Kansa yake girgiza mata kafin ya furta. "IS GONE MA'AM, Sedai muce ALLAH ya masa raham..... Ai tin kafin ya ƙarasa maganar nashi ta wani fasa uban ihun da kaff asibitin seda ta ɗauka, ta zube ƙasa tana kururuwar sun kashe mata ɗan ta, kafin kuma kamar wacce aka zabura ta lalubo wayarta kai tsaye ta saka ƙiran numbern mijinta, wanda ƙasar ma, sedai dirarsa ƙasar kenan dake dama yau ɗin ze dawo. Ya a daga wayar ta fasa masa wani uban kuka tace... "Asi....asi....asibitin....4&4 sun kashe mana shi!!!!, sun kashe mana Sameer ɗin mu, sun rabamu dashi, sun ki masa aiki, sunki kulawa dashi har ya mutu Alhaji...." Ɗif ɗif ɗif Haka ƙarar datse ƙirar da aka yi daga ta can ɓangaren me wayar, cikin abinda be gaza 30 minutes ba sega jiniyar ƴan sanda da sojoji sun gama karaɗe ilahirin asibitin, gaba ɗaya jami'ai suka ma hospital ɗin ƙawanya kamar irin za'a kama mutum dubu ɗin nan masu laifi, Cikin mugu mugun tashin Dr Aysha ta ƙira Bilal take sanar masa halin da suke ciki, cikin mugun tashin hankalin da yake jin kaf rayuwarsa be taɓa shiga bane yaji ya shiga a lokacin, gashi baya ƙasar baki ɗaya, ga MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ma da yake da tabbacin shima baya ƙasar, don haka ƙirar Daddyn MAJEED ɗin kai tsaye ya saka yana sanar masa abinda ke faruwa, wanda daidai lokacin da Dr Majeed ke ƙoƙarin cire sau cikin dake ƙafarsa da sauƙarsa kenan a ƙasar, shigowarsa kuma ƙasar kenan, don haka ya dakata cak shi be cire ba shi kuma be saka ba, wani Gwauron numfashi mahaifinsa ya sauƙe yana ce dashi shi kawai ya huta bara yaje yaji da matsalan, kansa ya girgiza masa yana zira sawu cikin nasa, kai tsaye ya sake fita cikin wata lafiyayyar motarsa ta *LAMBORGHINI* wacce ba'a fiye samar kalarta a Nigeria ba, sabo da kuɗin masu nauyin da motar ke lasa, gata wata a wani shafe, wacce ni kuwa AMMEY LAYLERH nace ehhhh lallai yaci a ƙira ta da sunan Lamborghini ɗin,domin kuwa a lamgwamen take, kalarta ma daka kalla kasan ta daban ce ba irin sauran motocin daka saba gani bane, irin su jeef, marcadez benz, toyota highlander, dadai sauransu to wannan ba kalarsu bace.... Tin daga kan yadda yaga an zagaye asibitin nashi ransa ya sake masifan ɓaci na ƙarshen ƙarshe, dan haka da wani mugun gudu ya danna kansa cikin ainihin compound na asibitin, jami'an dake tsare asibitin duk suka yo kansa, sedai bayyanuwarsa akan diga digan sane ya saka su ja baya da alamun mamakinsa me girmar, Me kuma ya kawo *BILLIONAIRE MAJEED DAWOUD ISHAQ?* Wannnan asibitin a cikin irin wannan lokacin?, kallo ɗaya ya musu kai tsaye yana kutsa kansa cikin ainihin ginin asibitin. Dr pooja kai tsaye ya ƙira ya tambayeta tana wanne room ne, cikin rawan jiki ta sanar masa room ɗin da suke, don dama rufe su ne tayi don gaba ɗaya jami'ai sun gama kewaye wurin, don ma sa'ar su ɗaya ƙofar bluetfroof ce, shi ne taimakon da ALLAH ya musu, amma in ba dan haka ba da tuni an gama bandarsu nama ɗanye, gaba ɗaya kusan Dactor's ɗin a ɗakin, don haka ya nufo room ɗin drectly... Bayyanuwarsa ya ankarar da jami'an dake zagaye da wurin, da da farko har sun nufo shi sedai suma ganin nasa ne ya saka su jan birki daga inda suke, shi kuwa Alhaji Kabeee mahaifi ga yaron daya rasu suna can shi da Matarsa Hajiya Madinah suna aikin kuka, sun saka shi a tsaƙiyarsu babu abinda suke se kuka. Da wani spire key yayi using ya buɗe ƙofar, kuma ya barta buɗe in yaso me shigar ma ya shiga. Dr pooja ce ta gama koro masa duk abinda ya faru, har kan case na fyaiɗen da mutumin ya ma Meenal ɗin bata ɓoye ba, don baya da wata mafita kuma a yanzun daya wuce fadar gaskiya. Tana gama bashi jawaban ya wuni juyo ga Meenal ɗin yana zuba mata shegun idanunsa masu kama dana mayu,lolz inji Meenal ba inji LAYLERH..... ★.. "WHO IS SHE'S??" Shine kawai abinda ya fara tambaya kafin komai.... "You..." Wata daga cikin nurse da jikinta ke rawa ta sake nuna masa Meenal ɗin a karo na biyu bayan bayanin da Dr pooja ta masa... .....Fin sama da 5 minutes kenan da suka zuba juna idanu, suna kallon tsaƙiyar idanun junansu babu ko ƙyaftawa, yayinda sauran Dactor's ɗin kowa ke sake shan jinin jikinsa daga yanayin kallon tsana da ƙamar da yake jifarta dashi, da wani kalan ɗan iskan salo ya wani juya mayan oily ayes ɗinsa dake kanta masu matuƙar haske da kyau, kafin ya wani kauda fuskarsa gefe yana mai furzar da wani irin hucin ɗumin da zuciyarsa ta ɗauka, Sai kuma ya sake dawo da idanun nasa a kanta cike da barazana da isa da basarwa ya furta, "WHO ARE YOU?" Yi tayi kamar bama tasan ALLAH yayi ruwansa a wurin ba, sakamakon tsohon miƙin da aka famo mata na daga cikin rayuwarta. Cikin ihu ya wani buga mata tsawa yana sake furta... "Who are you? Tell me who you are, answer me who you are?..." Haka yake ta famar nanatawa don ganin kalan renin hankalin da take son zuwar masa dashi. Ita kuwa a nata ɓangaren duk da yacce yake maganar nashi cikin tsawa be sa ta ɗago ba, bare yasa ran zata tanka mishi. Sema sake riƙe kanta da tashi tana jin duk wasu hargagi da kalamansa ɗaya bayan ɗaya suna mata wani irin amsa kuwwa da tartsatsi a cikin kunnenta, har kan nata na kamar ze rabe gida biyu ko ya fashe mata haka take ji, domin gaba ɗaya komai da take gudun ya dawo mata sabon ne ya dawo mata. Ga wani irin zafin lokaci gudan daya game ilahirin gwaɓɓan jikinta, yana narkar nata da duka wasu gwaɓoɓin dake jikinta da ƙasusuwanta tamkar zasu narke.... "You won't answer me?..." Ya sake faɗa cikin gizago da tsawataccen sauti mai cike da fusatuwa, har yana bugar desk ɗin dake gabansa. Wanda ya sakata miƙewa tsaye tana sauƙema fuskarsa zazzafen marin da yazo masa a matuƙar bazatar da ya saka kowa rufe bakinsa dake wurin, musamman ma Dr pooja da tafi kowa dake wurin sanin irin ƙarfn iko da matsayin da yake da. Jikinta wani irin rawar zafin dake cigaba da ratsata tun daga saman kai har yatsun ƙafafunta, duk da yanayin da take ciki da kuma yadda jikinta ke fitar da wani kalan hucin masifar zafi seda ta bude lips nata, cikin wata irin dakiya da jarumtar da ta aro ma kanta ta shiga nuna shi da hannu tace.... "Idan baka san daraja da martabar mace ba to lallai kayi gaggawar zuwa ka koyo!, Kai waye da akan wannan dabbar mutumin har kaka cira min sauti?, Ba mace ba ce ta haife ka?, ko kuwa baka da ƴan uwa Matan ne?, yanzun idan da ƙanwar kace a cikin irin wannan halin da nake ciki zaka mata haka? Uyhmmmm zaka tambaye ta akan me yasa taƙi duba mutumin daya wulaƙanta mata rayuwa, Ni nasan daraja da kuma mutumcin kaina, wannan ma na baka warning ne don gaba ka kiyaye...." Tin da ta fara maganar a karo na farko kenan daya wani kauda kansa gefe guda. Kafin kuma ya wani ɗan yamutse

Chapter 6 of 14