Share this page
11 / 13
take jin matsanancin kishin Kande da ƙinta a ranta. Gida-gida Kande ta dinga bi ta na neman Salma amma babu bayani. Cikin kankanin lokaci labari ya baza gari Salma ta gudu,da misalin tara da rabi na safe Malam Rabi'u da Yayansa Malam Jamilu suka zo gidan Malam Bala dan jin karin bayani game da batan Salma. Haƙuri Malam Bala ya dinga basu yana yi musu alƙawarin nemo ta kafin ƙarfe sha biyun rana ya cika. Su na nan suna tattaunawa Baffah Aƙilu ya ƙaraso gidan hannunsa riƙe da na Salma dake ta sharɓar kuka a cikin runtumemen hijabin Gwaggo Kande. Salati Malam Bala ya sanya ya ce. "Dama wajenka ta gudu Alhaji? Ka ganni nan yanzu nake shirin zuwa wajen Malam Mai Jigidar Bala'i ya binciko min inda yarinyar nan take a yi mata kiranye ta dawo gida. Domin kuwa aure dai an riga da an ɗaura shi dole ne ta zauna a ɗakin mijinta babu fashi." Kallon Salma Baffah Aƙilu ya yi ya ce mata. "Maza shiga gida." Sum-sum-sum ta shige cikin gidan kamar mara gaskiya kanta a duƙe ta na satar kallon Malam Rabi'u da ya kafe ta da ido cike da tausayawa. Sosai ya ji tausayin Salma ya danne yanda yake tausaya wa kansa na zama babu aure har na tsawon wannan shekarun,babban abinda ke ƙara ɗaga masa hankali bai wuce yanda duk kyawunsa da abun hannunsa ba mata ke gudunsa. Zuciyarsa ce ta fara gasgata zargin mutane a kansa. Ya na can duniyar tunani ya ji muryoyin Malam Bala da Baffah Aƙilu a sama su na musayar yawu. Babu jimawa Gwaggo Kande ta dawo gidan ita da Kawu Sale. Kai tsaye cikin gidan Kawu Sale ya raka Gwaggo Kande da ke jin numfashinta ya na yi mata wuyar fita. Ta na shiga ta ga Salma a rakuɓe a ƙofar ɗakinta ta na gyangyaɗi Hasiye na ta kaiwa da komowa ta na kwaɓa fanke mai uban yawa a babbar roba,gefe ɗaya kuma tulin kayan miya ne a baho da naman a wata roba,sai rabin buhun shinkafa ƴar gwamnati. Waƙarta take ta yi ta habaici tare da faɗin. "Aure dai ya riga ya ƙullu,kuma dole ne ango ya sha man amarya." Wani kukan kura Kande ta yi sai gata ta dirga a gaban Hasiye,shaƙe mata wuya ta yi ta hau kirɓarta kamar an aiko ta. Cike da azaba Hasiye ta hau ƙoƙarin ƙwatar kanta daga riƙon da Kande ta yi mata ta na faɗin. "Ki sake ni Yaya bana son ƙarasa gawar da ba tawa ba,kada ki hasala ni na yi miki naushin da zaki baje a wajen nan." Jikin Kande ne ya hau rawa saboda gazawa da yake ƙoƙarin yi sakamakon tsufa,yunwa da gajiya da suka haɗu suka yi mata yawa. A daidai wannan lokacin Malam Bala da su Baffah Aƙilu suka shigo gidan. Saura ƙiris Gwaggo Kande ta kai ƙasa Kawu Sale ya taro ta yana faɗin. "Subhanallahi,Gwaggo lafiya? Me yake faruwa ne a gidan?" Hasiye ta na haki tana danne kukan da ke shirin taso mata na azabar da ta sha ta ce. "Me yake faruwa kuwa banda wannan tsohuwar da ta kama ni tana duka kamar za ta kashe. Daɗin abun dai bani na kar zomon ba rataya aka bani." Makullin ɗakin Kande Salma ta lalubo a lalitarta dake jikinta ta buɗe musu ɗakin suka shiga. A gado Kawu Sale ya kwantar da ita ya na yi mata sannu. Cike da tsananin damuwa Kande ta kalli Salma ta ce. "Lokacin da kika gudu kin tuna da ni Salma? Kin yi tunanin halin da zan shiga ko kuma irin zargin da mutane za su ɗora akan ni ce na ce ki gudu?" Da sauri Salma ke girgiza kanta tana kuka. Wani irin tausayinsu ne ya lulluɓe Kawu Sale ba tare da ya shirya wa hakan ba. Cikin ransa yake ayyana. 'Anya na yi wa zumuncin ƴar'uwata adalci kuwa? Nawa ne dubu ashirin har da zan karɓi kuɗi na yi ja gaba wajen kassara rayuwar yarinyar da bai kamata ta shiga irin wannan ƙuncin ba da ƙarancin shekarunta? Salma fa yarinya ce sa'ar Isuhun wajena,yanzu idan ni na tsugunna na haife ta zan so a ƙwace mata ƴancin ta na walwala a doron ƙasa?' Da sauri ya girgiza kai ya miƙe ya bar ɗakin. A tsakar gida ya tarar da Baffa Aƙilu ya na faɗin. "Ai na ji labarin irin kuɗaɗen da Rabi'u ya sakar muku shi yasa kuka amince kuka aura masa ƙaramar yarinya tinda ba ƴarku ba ce. To ku tsaya ku ji da kyau,na aika saƙo wajen Abdulwahabu,dan haka ku tsammaci zuwansa a kowanne lokaci daga yanzu. Kai kuma Sale ka bani mamaki,akan abun duniya ka ci amanar ƴar'uwarka,tir da ɗan'uwa irinka." Baffah Aƙilu na gama magana ya bar gidan,kan dole Kawu Sale ma ya ja guiwarsa da ta yi masa sanyi ƙalau ya tafi nashi gidan. Ɗakin Kande Malam Bala ya nufa ya ɗage labule ya na bin Salma da wani irin mugun kallo ya ce. "Ke kuma daga yanzu kika sake saka ƙafa kika bar ɗakin nan ba da izinin Hasiye ba,sai na lahira ya fiki jin daɗi,munafukar yarinya kawai me fuska biyu,ina ce jiya har da kukan ki kika ce kin ji kin amince za ki yi biyayya ki yi zaman aure? Yau wanne shaiɗanin ne ya ziga ki ki gudu kuma? To ina so ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,idan har ɗan'uwanki ya zo ya ce zai raba auren nan kamar ya raba auren ta da ni ne gata nan kwance gabanki,dan haka sai ki zaɓa zaman aure ki yi ibada ko kuma auren mariƙiyarki ya guntule." Labulen ya saki ya wuce ɗakinsa ya na masifa kamar zai ari baki. Ya na shiga ɗakin Hasiye ta bishi hannunta riƙe da kwanon koko da fanken da suke ta soyawa ita da Mairo da Shamsiyya. Ta na ajiye masa ta zauna a bakin gado ta ce. "Wannan hukuncin da ka ɗauka Malam shi ne daidai,dan idan ba haka ba Abdulwahab na zuwa zai sa a raba auren." Cike da takaici Malam Bala ya ce "To ai abinda zai baki takaici Hasiye shine;da ƙyar fa muka danne Rabi'u ni da Jamilu,da tini ya saki yarinyar nan mu kuma asirinmu ya tonu,dan kuwa a yanzu bani da kuɗin da zan biya shi abinda ya bamu duk na zuba su a noman rani." Haɓa Hasiye ta kama ta na sallami ta ce. "To ai Malam dama fa shi bai baku kuɗi dan rufe muku baki ba,ya bayar ne kawai ba tare da wani sharaɗi ba." Jinjina kai Malam Bala kawai ya yi ya kora kokon da ya kwaso a ludayi. Nan dai Hasiye ta zauna ta ci gaba da zuga Malam Bala tare da bashi mugayen shawarwari. Da azahar mata suka fara cika gidan Malam Bala su na taya Hasiye da Kande murnar auren Salma. Kande dai ta na ɗaki ta na kallon kowa ranta babu daɗi,ruwan farau-farau ta kora ta koma ta kwanta ta na nishin azabar da ƙirjinta ke yi mata. A haka mata suka dinga cin shinkafa dafa duka da zoɓo,su na surutai akan auren Salma kamar a gabansu wasu abubuwan suka wakana. Bayan an yi sallar la'asar Mairo ta shigo gidan ita da ƙawayen Salma da ta gayyato na makaranta,Salma na ganinsu ta ɓuya a bayan ƙofar ɗakin Kande ta na sharɓar kuka. Duk yanda suka so su ja ta a yi party ƙi ta yi,kan dole suka haƙura suka ƙyale ta. Rediyon Hasiye Mairo ta ɗakko ta loda mata sabon batir suka saka kaset suka kunna kiɗa su na ta rawa abunsu cike da nishaɗi da jin daɗin ƙawarsu na aure. ********************* Saƙon da Baffah Aƙilu ya bayar bai iske Abdulwahab da wuri ba. Domin kuwa sai da ya dawo daga aiki ya shiga kasuwa da yamma ake sanar da shi mummunan labarin da ya tayar masa da hankali ƙwarai da gaske. Da yammar ya kira Mudassir ya labarta masa kaf abinda ke faruwa,ko gida basu je ba Malam Sallau ya ja su a ƴar ƙurƙurar motar da suke amfani da ita ta zirga-zirga. Tafe suke su na tattauna lamarin, jinin Mudassir har ya fi na Abdulwahab tafasa,domin shi dama mutum ne mai sanyin halin, Mudassir kuwa ya na da zafi sosai idan aka taɓo shi. Cike da ƙosawa su isa Kura da wuri Mudassir ya ce. "Malam Sallau ba wa motar nan wuta lokaci na ƙurewa." "Tom Malam Mudan a bi komai a sannu,da yardar Allah babu abinda zai samu Salamatu sai alheri." Haka suka ci gaba da tafiya kamar kurame kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa. Gudu suke tsulawa a mota cikin rashin sa'a Malam Sallau ya taka wani abu mai tsinin da ya yi sanadiyyar fashewar tayar motar. Salati Mudassir ya dinga yi ya na jin zuciyarsa na tafasa kamar ta kama da wuta. Gaba ɗayansu fita suka yi suka hau neman taimako ko za su samu wanda zai taimaka musu Malam Sallau ya shiga gari ya samo musu mai gyara. *********************** A can ƙauyen Kura kuwa mata sun ci sun sha sun yi hani'an,hakan sai ya sake tabbatar wa da Kande cewar Hasiye ce ta ƙulla wannan auren dan kawai ta ƙuntata mata. Tabbas kuwa ta yi nasarar sanya ta a cikin baƙin cikin da tinda take a duniya bata taɓa shiga irinsa ba. Ta na daga ɗaki ta na hango yanda Hasiye ta sha shadda ruwan ɗorawa an yi mata jan aiki da jan zare sai shewa take yi ta na taya su Mairo tiƙar rawa kamar wata ƙaramar yarinya. Dare na yi Balaraba da Tafisu da sauran ƙawayen Hasiye ne suka shiga har ɗakin Kande suka ja Salma suka yi waje da ita. Wanka suka saka ta a saman turmi suka yi mata da ruwan lalle da magarya suna ta wanke-wanken amarci irin na ƙauye. Ita kuwa Salma ta gaji da kuka ta tsaya kawai ta na kare ƴan matasan ƙirjinta tare da matse ƙafafuwanta da Balaraba ke buɗawa ta na kwara mata ruwan lalle. Su na gama wanke ta tas suka kaita ɗakin Hasiye suka shirya ta cikin atampar da bata san lokacin da aka ɗinka mata ita ba. Tana juya wa bayanta ta ga akwatina guda uku a ɗakin Malam Bala har da takalmi da jaka a cikinsu. Cike da mamakin lokacin da aka kawo su ta kawar da kanta tana jinjina lamarin da take ɗaukan sa kamar wasa. Turare Balaraba ta fesa mata Tafisu ma ta ƙara mata wani suma suka shafa suna yaba ƙamshin turaren. Anan take jin wannan akwatunan dika nata ne. Mayafi fari ƙal suka yafa mata tare da damƙa mata farar jaka,har ƙasa Tafisu ta duka ta saka mata takalmi fari ƙal sannan suka gyara mata zaman sarƙar dake wuyanta suka kamo hannunta suka fito. A tsakar gida suka tarar da dangin Malam Rabi'u sun zo ɗaukan amarya,ciki har da Samira da ke cike da matsanancin farincikin da ta kasa ɓoyewa. Wajen Hasiye ta je suka tafa a ɓoye su na magana da ido tare da nuni da bakunansu da hannayensu. Har cikin ɗakin Kande su Balaraba suka shigar da Salma suka zaunar da ita a gaban Kande da ke zaune ta zabga tagumi ta na kallon ikon Allah. Guda mata suka kaure da yi da hayaniya kamar ba su kula da halin da Kande da jikarta ke ciki ba. Cike da hayaniya mata suka ce. "To Kande lokacin rabuwa da ƴar gaban goshi ya zo;sai a yi mata nasiha a wuce da ita ɗakin miji dare na yi." Kasa cewa komai Kande ta yi da ya wuce danne hawayen dake ƙoƙarin ƙwace mata;sakamakon jin irin kukan da Salma ke yi. Ganin dare na yi Kande ta ƙi cewa komai sai mata suka ɗauki Salma dake turjewa ta na ihu suka yi waje da ita. A ƙafa suka nufi gidan Malam Rabi'u da Salma suna tafe su na waƙoƙin amare irin na ƙauye. Su na isa gidan Samira ta dawo baya ta ce. "Ai ya kamata ku bar amarya ta fara taka cikin gidanta da ƙafarta kafin kowa ya shiga ko?" Ai kuwa babu musu Balaraba da Tafisu da ke riƙe da Salma suka sauke ta ƙasa su ka tura ta cikin sashen nata wanda aka katange shi da ginin ƙasa aka yi masa filasta tare da shafen koren fenti mai haske. Salma na saka ƙafa a cikin gidan ta ji kanta ya yi wani irin sara mata kamar zai rabe gida biyu,hannu ta sa ta dafe kanta ta ce. "Washhh Allah na kaina." Cikin yi wa Salma tsiya Samira ta ce. "Ai ko bayanki ne ke ciwo amarya yau dole ango ya sha mai,ku shigar da ita ɗakinta ta ga irin dukiyar da mijinta ya kashe mata." Guɗa matan gidan suka kacame da ita kafin su shiga cikin ɗakin da yake shine mallakin Salma. Guɗa Balaraba ta sake rafkawa ta ce. "Ahhh yarinya kin yi goshi barakallah masha Allahu. Inyeee har da sif da dibaida. Allah Ya bada zaman lafiya to,ya kawo ƙazantar ɗaki,amma ba ta ƙin shara ba." Nan fa mata suka dinga yi mata addu'o'i su na lelleƙa sauran wajen su na sam barka. Bayan sun gama ne Mairo da ƙawayen Salma suka zauna mata domin jiran zuwan ango da abokansa dan su basu kuɗin siyan bakin amarya............ MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 19. Da yake ango ba yaro bane shi kaɗai ya zo abunsa;hannunsa riƙe da leda. Ya na shiga ya ji hayaniyar yaran da yake yi wa kallon ƴan kucakucin yaran da ko magana basu gama iyawa ba. Mairo ce zaƙaƙurar da ta isa gabansa ta ci ɗamara ta miƙa masa hannu ta ce. "A cake mana kuɗin siyan baki kafin mu barka ka je wajen amaryarka." Murmushi kawai Malam Rabi'u ya yi ya zira hannunsa a aljihu ya ƙirgo dubu ɗaya ƴan hamsin-hamsin ya miƙa wa Mairo dake wata jijjiga da harare-harare. Ya na bata ya naɗe hannunsa ya na kallon ta yana jiran ya ji kuma me za ta ce. Baki ta washe cike da murna ta ce. "Ku taso mu tafi ango ya yi sallama. Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki sai mun zo da safe cin abincin amarya." Cikin sauri Malam Rabi'u ya haɗe fuska tamau ya ce. "A kul na ga ƙafar wata yarinyar a cikin ku ta sake zuwar min gida." Cike da jin tsoronsa suka ranta a na kare suka bar gidan. Su na tafiya Malam Rabi'u ya samu waje ya raba kazar nan gida biyu,ba tare da ya ce da Salma komai ba ya ajiye mata nata kason a gabanta ya ja gefe da nashi ya hau ci. Jin ɗakin ya yi shiru ne ya sanya Salma durƙusawa ta ce masa. "Ina yini." Murmushi ya saki mai sauti ya ce. "Lafiya ƙalou,ki yi haƙuri na shigo ban yi miki magana ba,a zato na ke ɗin irin yaran nan ne masu rawar kai,ni kuma bana son hayaniya shi yasa na tsuke baki na." Kai Salma ta sake sauke wa ƙasa ta rakuɓe a jikin gadon da take ta mamaki a cikin ranta wai nata ne. Malam Rabi'u kuwa bai sake ce mata komai ba,ya na gama cin kazar sa ya yi gyatsa mai ƙarfi sannan ya ce. "To sai da safe,ina fatan kin san inda bayi yake. Dan bana so ina bacci ki katse ni ki ce za ki zaga,ni da kika ganni idan ina bacci ba a tashi na." Kai kawai Salma ta gyaɗa masa ba dan ta san akan me ta gyaɗa kan ba. Ita dai babban buri da fatan ta bai wuce na ta ganta ta keɓanta ita ɗaya ba ta samu damar yin kukan da ke danƙare a ƙirjinta. Waje Malam Rabi'u ya fita ya nufi wani ɗaki dake kallon na Salma ya buɗe da makulli ya shiga. Fitilar tocilan ya kunna ya ke haska ɗakin da ita, daga nesa Salma ke hango Malam Rabi'u ya na cire babbar rigarsa,gabanta ne ya faɗi sai ta yi saurin kawar da kanta gefe ta sake takure wa a waje ɗaya. Salma bata da ilimi ko na sisin kwabo akan rayuwar aure,a bakin su Mairo da ƙawayenta ne ta ji wasu abubuwan a lokacin da aka barsu tare. Babban buri da fatanta bai wuce Allah Ya sa kada Malam Rabi'u ya zamo daga cikin ƴan isakan mutanen da ke taɓa jikin ƙananan yara ba. Wani irin kuka ne mai cin rai ya turniƙe ta. Nan take ta hau yinsa ta na faɗin. "Gwaggo don Allah ki zo ki taimake ni tsoro nake ji." Haka ta dinga kuka a hankali ta na toshe bakin ta gudun kada wani ya ji ta. Ganin hasken ɗakin Malam Rabi'u ya mutu ne ya sanya ta miƙe wa a hankali ta rufe ƙofar nata ɗakin da sauri. Wani irin tsoro ne ya ke shigarta a hankali. Gado ta haye ta takure a waje ɗaya ta na jin kamar ta ɓace ta ganta a ɗakin Kande. A haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta. ************************* A ɓangaren su Abdulwahab kuwa sai ƙarfe goma na dare suka shiga cikin garin Kura. Su na isa Mudassir ya kafe sai sun je gidan Malam Bala a daren an yi wacca za a yi. Da ƙyar Abdulwahab ya danne shi ya bashi baki kan su bari safiya ta waye a yi komai a ilmance,domin ya kula faɗa da tashin hankali ba zai bashi abinda suka zo nema ba. A daren suka shiga cikin kasuwa suka samarwa kansu abinda za su ci suka koma gida. Abdulwahab wanka ya yi ya gabatar da shafa'i da wutiri kafin ya nemi waje ya kwanta. Malam Sallau kuwa da Mudassir na nan zaune su na hira kamar ba su ne suka sha gajiya tuɓus ba akan gyaran mota Washegari da sassafe bayan sun dawo daga masallaci Abdulwahab ya riga su shiga wanka,ya na fitowa Mudassir ya watsa ruwa ya fito. Malam Sallau kuwa gidan su na gado ya wuce dan ƴan'uwansa basu san ya shigo gari ba a daren jiyan. Ko karya wa ba su tsaya yi ba suka nufi gidan Malam Bala. Su na zuwa suka yi sallama a bakin ƙofa kafin Abdulwahab ya sa kai ya shiga gidan kai tsaye. Hasiye da ke bakin murhu ta na hura wuta ce ta fara arba da fuskar Abdulwahab da ya tamke ta tamau kamar bai taɓa dariya ba. Yaƙe ta fara yi ta hau ƙwala wa mijinta kira da duk wanda sunan sa ya shiga bakinta. Sai take jin ba za ta iya motsa wa ba kada Abdulwahab da ya fusata ya sa ƴan sanda su harbe ta. Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande Abdulwahab ya shiga. Zaune ya tarar da ita akan abun sallah idanuwanta sun koɗe sun yi jawur saboda kuka. Ta na ganinsa ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fashe da wani sabon kukan da yake jinsa a cikin ransa. Durƙusawa ya yi a gabanta ya kamo hannuwanta ya ce. "Gwaggo ki kalle ni,ki dena saukar da kanki ƙasa kamar wadda ta aikata wani laifi." Cikin kuka Gwaggo Kande ta ce. "Na aika babban kuskure Abdulwahab. Na yi nadamar zamowata matar Malam. Ji nake yi kamar na mutu saboda baƙinciki. Ina soyayya da tausayin da Malam ya nuna min a tsawon rayuwarmu? Me ya sa ya zaɓi ya ƙuntata wa zuciya ta a cikin ƙanƙanin lokaci irin wannan? Salma ita ce farinciki na ya kuma san da hakan,sai gashi ya yi amfani da ita wajen rusa wannan farincikin nawa na shekara da shekaru kamar wanda dama can yana jin haushi na. Babbar damuwata yanzu bata wuce zaman Salma da Samira a waje ɗaya ba,Samira bata ƙaunar Salma ko kaɗan,tun su na nan gidan ta saka ta a gaba ban dai taɓa faɗa bane saboda nima bana bari idan ta yi mata abu,to yanzu da suke su kaɗai wa zai rama mata idan Samira ta zalunce ta?" "Allah shi ne zai rama mata Gwaggo,ina so ki dena damuwa dan ba laifinki bane abubuwa suka kasance a haka. Na san laifi na ne ya shafi Salma,ko kin manta ni ne na ƙi auren ƴarsu? Shi ya sa suka biyo ta nan dan su rama abinda na yi musu." A hasale Mudassir dake tsaye yana kallon su ya ce. "To ana so dole ne? Wa ye ya basu dama da ƴancin aurar da yarinya ƙarama babu izinin magabatanta?" Muryar Malam Bala ce ta daki dodon kunnen Mudassir dake tsaye a bakin ƙofa;kamar saukar aradu. "Ni ne nan na ba wa kai na izinin aurar da ita,domin a ƙarƙashi na take,idan tarbiyyarta ta yi kyau ni ne,idan tarbiyyarta ta ɓaci ni ne. Me ya sa lokacin da nake kula da ita cinta,shanta,suturarta da duk wani abu da ya shafi rayuwarta baku ce wa ya bani izinin yin hakan ba,sai yanzu da na ga dacewar na aurar da ita ga mutumin da na san zai kula da ita ko bayan ranmu shi ne na yi laifi?" "Tsohon da ko yau ana iya sanar da mutuwarsa kake maganar zai kula da Salma ko bayan ranmu? Kai Malam ka fa yi son zuciya dole ne kuma a warware wannan auren ko kana so ko baka so." "Kai kuma a wa da kake ta baloƙoƙo kamar wani kwarton ƙadangare?" A hasale Mudassir ya isa gaban Malam Bala yana huci kamar zai kai masa duka,sosai hakan ya tsorata Malam Bala da Hasiye da ke laɓe a jikin labule ta na sauraron duk abinda ke faruwa. Baya Malam Bala ya ja Mudassir ya ƙara binsa ya na zaro ido waje,ji yake yi ba dan tsufan Malam Bala ba da tini ya ɗaga shi sama kamar yanda suke wa buhun shinkafa ya lafta shi da ƙasa. Sai da Abdulwahab ya gama lallashin Gwaggo Kande da bata baki sannan ya fito ya tarar da fusataccen amininsa da Malam Bala a tsaye carko-carko kamar zakarun dake shirin kacame wa da dambe. Tsakiyar su ya shiga ya raba kallon kisan kan da Mudassir ke bin Malam Bala da shi. Sassanyar ajiyar zuciya Malam Bala ya sauke ya yi gyaran murya. Kafin ya ce wani abu Abdulwahab ya ce. "Na ji labarin a gaban sarkin garin nan aka ƙulla auren Salma da Tsohon da ka zaɓa mata ko?" Da sauri Malam Bala ya ce. "To abinda Sarkin ne ma ya wakilci ɗaurin auren tare da sanya masa albarka? Ai kada ka...." Katse masa hanzari Abdulwahab ya yi ya ce. "To ya kamata mu je gaban sarki domin a warware abinda aka ƙulla babu son yarinya da danginta." Ya na gama magana ya yi gaba, Mudassir kuwa sai ya ƙi tafiya ya tasa ƙeyar Malam Bala a gaba suka mara wa Abdulwahab baya. Su na zuwa fada sai suka tarar da mutane ana ta kwasar gaisuwa a wajen sarki ciki har da Malam Rabi'u da Malam Jamilu Yayansa. Su ma zubewa suka yi suka kwashi gaisuwa,daga nan sai Abdulwahab ya gabatar da kansa da kuma ƙorafin da yake tafe da shi. Malam Rabi'u da ke bin su da kallo tin shigowarsu fadar ne ya saki murmushin da yake dabi'arsa ya sunkuyar da kai,kalmar tsoho da ake yawan kiransa da shi tun da ya auri salma ta na yi masa ciwo a rai;ba dan be yarda shi ɗin tsoho bane,amma kafin ya aure ta abokansa kullum yabon kyan jikinsa da yanda jikin nasa baya nuna shekarunsa suke yi,wasu ma sai suka ce ko dan be yi aure bane shi yasa tsufansa ƙin bayyana,wasu kuma suka ce aljanar da ta aure shi ne take son ganinsa da yarinta shi yasa take sabunta masa fatarsa duk shekara,kwatsam sai gashi auren Salma ya jawo masa tuni akan shi ɗin fa tsoho ne da ya yi jika da ita. Kamar daga sama ya ji sarki na gabatar da shi a matsayin mijin Salma. Murmushin dai ya sake sakar musu ya miƙa wa Abdulwahab hannu suka gaisa, Mudassir kuwa kawar da kai ya yi yai kamar be ga hannun Malam Rabi'u ba. Janye hannunsa Malam Rabi'u ya yi yana murmushi ya koma mazauninsa. Bayan sun gaisa Sarki ya ce. "To Alhamdulillahi. Kamar dai yanda kowa ya sani a garin nan kaf Malam Rabi'u ya sha wahala wajen neman matar aure,tausayi da kuma zaman amana tare da ceton rai ne ya sanya Malam Bala baiwa ƙanin amininsa auren Salma. Domin kuwa a ranar da aka fasa aurensa a karo na barkatai suma ya yi anan saboda damuwa,dan haka ina mai roƙon ku da Allah ku kwantar da hankulanku,ku bar wannan aure ya rayu domin bamu san alkhairin da Allah ya jefa a cikinsa ba." Cikin sauri Malam Bala ya tari numfashin Sarki ya ce. "Kuma shi irin wannan auren Allah Ya baka yawan rai,idan mutum ya matsa sai an raba sai

Chapter 11 of 13