albarka tare da fatan Allah Ya ninninka masa arziƙinsa ya raya musu ɗansu Abdulwahab.
Bayan sunan Abdulwahab Atine da Malam Musa sun ci gaba da rainon ɗan su cikin kulawa,soyayya da ƙauna irin ta iyaye. Malam Musa sai ya sake dagewa da neman kuɗin da zai ba wa ɗan sa da matarsa ingantacciyar rayuwa. Cikin ikon Allah kuwa sai arziƙinsa ya fara buɗewa har ya fara tara dabbobi yana kiwatawa a gida kamar yanda yake da sha'awa da buri. A hankali Malam Musa ya fara siyan fili yana yadawa. Abdulwahab na kai wa shekara takwas a duniya ya saka kansa a makarantar boko da ya ga yaran garin na zuwa. Sai dai su da sun kammala primary suke tsunduma a harkar noma sai su watsar da karatun. A ɓangaren Abdulwahab kuwa sam bai watsar da karatun bokonsa ba,saboda yana gane duk abinda ake koyar da shi. Bayan an taso daga makarantar boko sai ya wuce ta allo,da yamma ya koma gida ya ci abinci ya yi bitar karatunsa na boko da na arabiyya. Babu jimawa labarin nacin karatu irin na Abdulwahab ya fara karaɗe garin Kura,har wasu daga abokan Malam Musa suka yi ayari su huɗu suka je har gida suka same shi da shawarar;ya kamata ya dakatar da Abdulwahab daga zuwa makarantar boko ya jefa shi a harkar noma kamar sauran yaran garin,gudun kada ya tashi bai iya riƙe fatanya ba. Da jin haka sai Malam Musa ya fashe da dariya ya kalli abokan nasa ya ce.
"Allah mai iko! Ku yanzu akan makarantar da yaron nan yake zuwa kuka yo ayari haka kuke sanar da ni na hana shi zuwa? Ina kuke lokacin da nake cikin gararin talauci da babu? Ina kuke ranar sunansa lokacin da nake neman ragon da zan yanka a sunansa dan na sauke nauyi da kuma kare mutuncin ɗana da ni kaina da iyalina? Ina kuke lokacin da yaron nan ya dinga yawo babu suturar arziƙi a jikinsa ballantana takalmin da zai saka ya shiga cikin tsaransa?"
Idon da ya zuba musu yana neman ƙarin bayani ne ya sanya su sauke kawunansu ƙasa cike da jin nauyi da kunyarsa. Murmushi yayi sannan ya ce.
"Idan baku da amsar bani ku je ku ci gaba da kula da yaranku ta hanyar da kuke ganin ita tafi dacewa da rayuwarku;nima ku barni na kula da nawa yaron ta hanyar da nake ganin tafi dacewa da rayuwar da nake so yarona ya taso a cikinta."
Cike da borin kunya suka kaɗe rigunansu suna faɗin.
"Ai shikenan,dama shi gyara kayanka ba ya zamowa sauke mu raba,shawara ce dai muke baka,dan mu dai bamu ga wanda biro da takarda suka ciyar ba,riƙo da fatanya muka gada kaka da kakanni,ita ce ke bamu abinda muke kai wa bakin salati."
"To ku je ku ci gaba da riƙe fatanyar shi kuma ya riƙe bironsa,Allah Ya bawa kowa sa'a akan abinda ya sa a gaba."
Tin daga wannan ranar abokan Malam Musa suka janye jiki daga gare shi,sannan duk wata harkar noma ta samun ci gaba idan ta shigo garin suke kashe tauraruwarsa su ƙi sanar da shi. A duk lokacin da ɗayansu ya neme shi to ta tiƙe masa ne babu yanda zai yi sai ya nemi shawara ko taimakon Malam Musa. A hankali samun Malam Musa ya fara ja baya,amma duk da haka bai karaya ba,sai ya koma noma filayensa guda uku da ya mallaka da kansa,idan abunda ya noma yayi sai ya je ya siyar. A haka Abdulwahab ya kammala ƙaramar sakandire har ya rubuta jarabawar shiga babbar sakandire. A tsakanin hutun da ya samu ne na rubuta jarabawar shiga senior secondary school ya fara bin mahaifinsa kasuwa yana ganin yanda ake gudanar da kasuwanci. A kuma wannan lokacin ne sha'awar siye da siyarwar kayan abinci ta shiga ransa. Bayan ya koma makaranta sai Malam Musa ya hana shi zuwa kasuwa ya ce ya mayar da hankali akan karatunsa.
Abdulwahab na da shekaru goma sha biyar a duniya Atine ta haifa masa ƙanwarsa mai suna Salma. Sosai Atine ta wahala saboda jimawar da ta yi ba tare da ta haihu ba,jinin da ta zubar sai ya sake rage mata kuzari da karsashi. Wannan dalilin ne ya sa ita kanta yarinyar bata samun cikakkiyar kulawa daga mahaifiyarta yanda ya kamata. Bayan suna da wata ɗaya Atine ta rasu sakamakon rashin jini a jikinta. Malam Musa ya shiga ɗimuwa da zaucewa saboda rashin masoyiyarsa. Ya jima sosai bai koma noma ba ballantana ya girbe amfanin gonarsa ya kai kasuwa. A haka suka ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da kewa tare da maraicin rashin Atine a rayuwarsu. Sosai Malam Musa ya so a bar masa Salma su ci gaba da kula da ita shi da Abdulwahab,amma sai Goggo Kande da sauran ƴan'uwan Atine suka ƙi amincewa da hakan suka ɗauke ta ta koma ƙarƙashin kulawarsu.
Abdulwahab na zana jarabawarsa ta ƙarshe a sakandire mahaifinsa majinginarsa kuma katangarsa ya faɗi ya rasu. Sosai mutuwar Malam Musa ta girgiza mutanen garin Kura da kewaye. Domin kuwa shi ɗin mutumin kirki ne,kuma su na amfana da shi matuƙa gaya a ɓangaren noman rani da damuna. Rasuwar Malam Musa ta sanya Abdulwahab zamowa yaro mara son magana da kuma kaɗaice kansa daga cikin al'umma. Lokuta da dama yafi tafiya cikin gonar mahaifinsa ya kwanta ya sha kukansa,daga ƙarshe bacci ya ɗauke sa,sai idan an aika yara nemansa ne ake samo shi a gona. Sosai Gwaggo Kande take tausayawa rayuwarsa saboda ta fi kowa sanin irin gata da kulawa tare da soyayyar da iyayensa suka bashi. Ganin yana neman ya lalata rayuwarsa ne ya sanya mijin Gwaggo Kande shige masa gaba a lokacin da sakamakon jarabawarsa ya fito; Result ya yi kyau sosai,sai ya biya masa kuɗi ya rubuta JAMB a wannan shekarar. Cikin ikon Allah ya samu makin da ake nema domin shiga jami'a. Malam Bala shi ne yayi tsaye tsayin daka ya saka Abdulwahab a makarantar jami'a ta kano wato Ado Bayero University Kano State. Ranar da Abdulwahab zai tafi makaranta Gwaggo Kande da Salma sai kuka suke yi,shi kuma yana jin wani irin farinciki a ransa zai bar garin Kura ya je wajen da zai yi nesa da inda ya yi rayuwa da iyayensa da ya rasa. Har tasha Malam Musa ya ɗauki Salma suka raka Abdulwahab da kayansa a cikin Ghana most go da leda ViVa.
Bayan tafiyar Abdulwahab makaranta Malam Bala ya ci gaba da kula da shi da buƙatunsa har ya kai level 200. Sai dai zugar abokai da danginsa ce ta sanya shi fara ja da baya tare da cire duk wani tallafi da yake bawa Abdulwahab. Lokacin da Abdulwahab ya samu hutu ya leƙa garin Kura mutanen garin suka gansa fes da shi gwanin sha'awa,sai suka ƙara tinzira Malam Bala suna yi masa nuni da ya zauna yana ta kashe kansa shi da yaransa su na gina yaron da bai san zafin nema ba. Tin suna maganar a ɓoye har magana ta shiga kunnen Abdulwahab. A lokacin da ya ji sai ya ƙi amincewa Malam Bala zai ɗauki zugar masu zuga har ya daina tallafa masa kamar yanda ya saba. Lokacin komawa makaranta na yi ya tinkari Malam Bala da maganar kuɗi,a nan ne fa Malam Bala ya murza wa idonsa toka ya ci wa Abdulwahab mutunci tare da yi masa gori kala-kala. Sosai kalaman Malam Bala suka ƙona wa Abdulwahab zuciya,amma sai ya tuno da alkhairin da ya yi masa a baya. Godiya ya yi masa ya shiga wajen Gwaggo Kande ya sanar da ita zai koma. Sanin halin da ake ciki ne ya sanya ta miƙe wa ta shiga ɗakinta ta ɗakko wata baƙar leda ta dawo ta zauna a gefensa ta ajiye masa a saman cinyarsa ta ce.
"Karɓi wannan,kuɗin awakin mahaifiyarku ne da na sa a siyar tin wancan satin. Kasancewar na fuskanci Malam ya fara ɗaukar zugar mutane ya sa na ce to meye amfaninsu? Shine na ba wa Kawunka Sale na ce a siyar a kawon kuɗin. Ka ƙara haƙuri Audu watarana sai labari. Allah Ya yi maka albarka Ya sa a mori wannan ilimi da kake ta fafutukar nema."
"Amin Ya Allah Gwaggo na gode,Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka in kai ki makka da Madina ke da Baba da Salma."
Guɗa Gwaggo Kande ta zabga tana murna,domin ko Abdulwahab bai kai ta Makka da Madina ba ya biya ta tinda ya sa hakan a niyyarsa. A wannan karon Abdulwahab da kansa ya nemi Salma ta yi masa rakiya tasha ta riƙe masa ƴar ƙaramar jakarsa ta goye suka tafi su na hira tana ta zuba masa surutu irin na yara masu wayo da baki. Da za su rabu ya siya mata kayan kwalama irin na yara a tasha ya tsaya a bakin tashar har ta ɓacewa ganinsa. Gani yayi ana ta loda shinkafa a bayan manyan motoci,gefe ɗaya kuma ga wake,gero,alkama,da maiwa tare da sauran kayan amfanin gona ana ta siyarwa. A hankali Abdulwahab ya matsa kusa da wani shago mafi kusa da shi,sallama ya yi wa mai shagon suka gaisa sannan ya furta masa buƙatarsa na son siyan shinkafa buhu ɗaya. Babu ɓata lokaci suka yi ciniki Abdulwahab ya sa ɗan dako ya ɗaukar masa shinkafar ya kai masa wajen lodi.
Ya na isa garin kano........
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman gidan aure. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️
PAGE 11.
Abdulwahab na shiga garin Kano ya samu abun hawa ya ɗaukar masa buhun shinkafarsa ya kai masa har bakin makaranta,daga nan ya samu machine ya loda masa kayansa ya shigar da shi har ƙofar shiga hostel. Ya na isa bakin gate ɗin hostel ya sauke shinkafa ya sallami mai machine. Abokinsa kuma ɗan ɗakinsu ya kirawo wato Mudassir ya roƙe shi ya taimaka masa suka shigar da shinkafa. Sai da ya yi wanka ya huta ya ci abincin da Mudassir ya gabatar masa sannan ya labarta wa abokin nasa duk abinda ya faru a gida. Ajiyar zuciya Mudassir ya yi kafin ya saki murmushin takaici ya ce.
"Allah Ya kyauta. Ai mutane yanzu suna daga cikin masu hana alkhairi,su basu yi ba sannan basu bar wani ya yi ba. Ni ai tinda na samu dangin Ummanmu na riƙe min Layuzah da amana bayan rasuwar iyayenmu sannan tana zaune cikin gata bani da wani takaici,yanzu haka fa ta na aji uku na ƙaramar sakandire,sannan ƙanin Ummarmu ya biya mata kuɗin bikin saukar ƙur'ani da za a yi musu a ƙarshen watan nan. Shi yasa ka ga ina faɗi tashi ina neman abinda zan rufa wa kai na asiri ba tare da na sake ɗora musu wani nauyin ba,amma fa su ba sa son ina wahala ba tare da na tambaye su taimako ba,ni kuma ina duba halin yau da gobe ne kada azo tin ana yi maka abu ta daɗin rai a gaji da kai,kamar yanda aka yi maka yanzu abokina. Allah dai Ya ƙara shiga lamuranmu. Dama bahaushe ai ya ce babu maraya sai rago,wannan dabarar da ka yi ta yi kyau,bari ma ka ga me ya kamata mu yi tin yanzu."
Da sauri Mudassir ya miƙe ya ɗauki kwanon silver da spoon ya fita tsakiyar saman baranda ya hau kiɗa da kwanon yana kiran mutane. Kafin kowa ya bashi hankalinsa ya rage murya ya tambayi Abdulwahab farashin kwanon shinkafa, Abdulwahab na sanar dashi ya fara tallata wa abokan karatunsa shinkafar akan farashi mafi sauƙi akan yanda suka saba siye a gari. Da yake suna cikin lokacin da wasun su sun dawo da kuɗin shopping daga garuruwansu,wasu kuma sun zo da kayan provision amma basu yi awo ba. Dan haka sai suka dinga rububin zuwa siyen shinkafa. Sai da mutane suka taru Mudassir ya ce.
"To ƴan'uwana ɗalibai ga fa sabuwar sana'ar abokina na siyar da kayan hatsi ko wanne iri mutum yake so,kawai ya faɗa masa in dai da kuɗi hannu ba bashi ba za ku samu akan farashi mai sauƙi. Ni kuma ina nan zan ci gaba da yi muku wanki da aikace-aikacenku kuna biyanaaaa."
Shewa matasan suka ɗauka,wasu na faɗin a basu shinkafa kada ta ƙare. Cikin sauri Abdulwahab ya hau neman kwanon da zai yi awo da shi,da ƙyar suka samu aron kwanon awo a hostel ɗin ya hau auna wa mutane shinkafa Mudassir na karɓar kuɗi ya na ƙirgawa. A haka shinkafa ta ƙare tas wasu na buƙata dan basu samu ba. Cike da murna da farin ciki Mudassir ya yi musu alƙawarin za su samu a cikin satin. Su na koma wa ɗaki ya kwaso kaf kuɗin da aka sayi shinkafa ya damƙa a hannun Abdulwahab yana taya shi murnar siyar da shinkafa da ya yi a ranar farko da ya fara kawo ta. Cike da tsantsar farinciki Abdulwahab ya rungume Mudassir yana yi masa godiya. Daga baya kuma ya yi jimm kafin ya ce.
"Amma na ji ka ce musu za su samu wata shinkafar a cikin satin nan,kada fa ka manta da karatunmu abokina."
"Ai babu abinda zai taɓa mana karatunmu abokina. Da an tashi daga lectures ranar alhamis kawai ka je Kura ka ƙaro shinkafa. Ka ga daga nan ma sai kai ma ka shiga jerin mutanen da za a dinga kawo wa hatsi ba tare da sun je har garin ba,tasha kawai za ka je ka ɗauki saƙon ka kamar yanda na ga wasu ƴan kasuwan na yi."
"Eh kafin na samu wannan damar dole sai na je mun tattauna akan yanayin yanda zan dinga biyansu kuɗinsu,da yanda nima zan dinga samun nawa kayan."
"Kada ka ji komai abokina Allah Yana tare da mu,fatana dai Allah Ya sa ka fara cikin nasara Ya sa hanyar arziƙinka ce."
"Amin abokina. Allah Ya sa hanyar arziƙinmu ne baki ɗaya,domin da alama ba zan iya kasuwancin nan ba idan babu kai a gefe na. Na gode sosai da wannan taimakon da ka yi min,Allah Ya jiƙan Innah da Abbah."
"Amin Ya Allah,kai ma Allah Ya jiƙan Baaba da Baba."
Zama suka yi suka ƙirga kuɗi suka ware riba da jari. Su na kammalawa suka adana kuɗin da kyau sannan suka ci gaba da shawarwarin yanda za su dinga samun kuɗi ta hanyar halal domin biyan kuɗin makarantarsu da kuma buƙatunsu na yau da gobe.
Tin daga wannan ranar kasuwa ta buɗe wa Abdulwahab ya ke samun kuɗaɗen kashe buƙatunsa. A wannan gaɓar ya dinga amfani da ilimin da ya ke koya ta ɓangaren kasuwanci ya dinga bunƙasa kasuwancinsa. Ana haka sai aka samu ƴan gulmar da suka kai gulmar Abdulwahab da Mudassir wajen hukumar makaranta akan sun mayar da hostel wajen sana'ar sayar da hatsi,da fari an yi musu gargaɗi,sai dai hakan bai yi wa duk wanda ya kai gulmar daɗi ba,bai huta ba har sai da aka kore su daga hostel ɗin gaba ɗaya.
Ana korar su suka kama hayar shago a wajen makaranta,a nan suke kwana kuma suke siyar da kayan hatsinsu. Sai ya zamana bayan ƴan makaranta da suka san suna siyar da kayan hatsi akan farashi mai arha har mutanen gari ma suna zuwa siyan kayan hatsi a wajen su Abdulwahab. A hankali kasuwa ta fara buɗe masa sosai tin yana ɗakko buhunan hatsi guda uku,ya koma biyar,daga baya ya koma ya na sauke buhuna goma. Wani lokacin ma mota zuwa take yi har gaban shagon ta sauke kayan ta wuce,ganin kayan na ƙaruwa kuma basu da wajen ajiya;sai Mudassir ya ba wa Abdulwahab shawarar ya kama wani shagon ya zauna a matsayin store,idan ya so wannan da kowa ya san su da shi sai ya zama na siyar da kayan hatsin. Da hidima ta ƙaru akansu sai Abdulwahab ya samu yara guda biyu masu kular masa da shagon,shi kuma da abokinsa sai suka mayar da hankalinsu akan karatunsu.
Da haka Abdulwahab da Mudassir suka samu suka kammala karatunsu,domin daga ƙarshe Abdulwahab shi ya ci gaba da ɗaukan nauyin karatun Mudassir. Sosai Malam Bala ya yi mamakin yanda Allah Ya sanya wa kasuwancin Abdulwahab albarka. Tin daga wannan lokacin sai ya rage matsanta masa da yake yi,domin har kyautar kuɗi Abdulwahab ɗin yake bashi da kuma yi wa iyalansa hidima domin kyautatawa. Ana haka Salma ta isa sawa a makaranta, Abdulwahab da kansa ya ɗauke ta ya kai ta makarantar boko da islamiyya ya yi mata register sannan ya kai ta wajen siyar da yadin uniform ya siya mata wanda zai isa a yi mata har kala uku-uku. Daga nan ya kai ta wajen masu siyar da jaka da takalmi ya zabar mata masu kyau da ƙwari,sai suka wuce shago ya yi mata ƴar siyayyar ƙwalama irin ta yara suka koma gida. Ko da suka koma gida suka sanar da Malam Bala ya so ya turje ya ƙi amincewa da zuwan Salma makaranta. Sai Gwaggo Kande ta murzawa idonta toka ta ce sam bai isa ba. Kan dole ya haƙura ya fita ya bar gidan ya na sababin sisinsa ba zai yi ciwon kai ba a zuwan yarinyar mace mai ƙaranci lokaci a rayuwarta makaranta. Cike da sababi Gwaggo Kande ta ce.
"Shi ma ɗan'uwanta da kansa ya ƙarasa biya wa kansa kuɗin makarantar,tinda kai ka ce ladan ya ishe ka ka biye wa zigar abokan banza ka janye daga biya masa."
Da ƙyar Abdulwahab ya taushe ta ta bar sababi,ya zauna suka hau hirar yaushe gamo. Su na tsaka da hirar ne Gwaggo Kande ta ce.
"To yanzu tinda an gama makaranta sai kuma a zo a yi aure ko? Ka ga shikenan sai ka rushe tsohon gidan iyayenka a siyar da filin Babanku ɗaya ko biyu kai ko dika ukun ma;ka danƙara gininka ku zauna daga kai sai matarka."
Da jin haka ƴar gidan kishiyar Gwaggo Kande mai suna Suwaiba da ke gaban murhu tana iza wutar kalwa da mahaifiyarta ke siyarwa ta tashi ta na wata tafiya ta na karairaya kamar maburgi ta wuce ta gabansu. Kai tsaye ɗakin mahaifiyarta ta shiga ta saka mata kuka tana sake yi mata tuni akan batun soyayyar da ta jima ta na yi wa Abdulwahab. Haƙuri ta bata tare da yi mata alƙawarin a daren nan za ta shawo kan mahaifinta dan ya ƙulla aurenta da Abdulwahab ko yana so ko baya so,tinda ya isa da shi. Da jin haka sai Suwaiba ta hau murna ta fito daga ɗakin ta na yanga ta wuce ta gaban su Abdulwahab ta ci gaba da sauraron hirarsu;wadda ta kasance duk ta samun nasarorin da yake ta yi ne akan kasuwancinsa. Albarka Gwaggo Kande ta dinga saka masa sannan ta tashi Salma da ta fara bacci ta ce ta je ta yi alwala dan an kusan kiran sallar magariba.
Bayan Abdulwahab ya koma gidan iyayensa inda yake kwana ne ya kwanta ya na nazarin maganar da suka tattauna da Gwaggo Kande. Murmushi ya saki mai laushi sannan ya cire rigarsa ya rataye ya fita zuwa makewayi. Ya na fitowa ana kiran magariba,sai kawai ya ɗaura alwala ya koma ɗaki ya saka kaya ya kulle ɗakin ya fita zuwa masallaci. A can masallacin ya dinga haɗuwa da abokan mahaifinsa suna gaisawa,da sun gama gaisawa sai su ce za su masa nasiha akan saka Salma makarantar boko da zai yi. Ina laifin ya ƙyale ta tinda ita mace ce;ta na bin yaran Malam Bala zuwa gona itama ta na taimaka wa da wasu abubuwan,lokacin aurenta na yi Malam Bala ne zai tsaya mata ya samar mata da miji ɗan gaske ya aurar da ita,a cewar su rayuwar ƴa mace bata da tsayi. Da sun gama koro wa Abdulwahab jawabi yake bin su da murmushin nan nasa da suke kira na rainin wayo,ko murmushin ajali. Da takaicin yamaɗiɗin da Malam Bala ya yi masa ya koma gida,domin a ganinsa ko auren Salma ne ya tashi ai suna da dangin uban da za su karɓa mata aure,ko Ƴan'uwan mahaifiyarsu,Malam Bala mijin Goggwan mahaifiyarsu ne shi kawai wanda yake ruƙon ƙanwarsa.
Ya na komawa sai ya tarar da Suwaiba ta kai masa abincinsa ta na jiransa a ƙofar gida ta sha ado da irin kwalliyar ƴan matan ƙauye sai karairaya take yi. Ya na zuwa ta kashe murya ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta miƙa masa kwanon abincin ta na wani sunne kai. Dariya ta bashi sosai,sai ya kawar da kai ya na murmushi,da ganin haka sai Suwaiba ta kwasa da gudu ta yi gida, zuciyarta cike da farincikin Abdulwahab ya kamu da ƙaunarta. Tinda ta koma gida take bawa Innarta labarin irin murmushin da Abdulwahab ya yi mata har Babansu ya dawo daga majalisa ya shige turakarsa.
Da yake Innar Suwaiba ke da girki,sai ta tashi ta nufi ɗakin nasa inda ta ajiye masa duk wani abun buƙata ta zauna. Mafifici ta ɗauka ta hau yi wa Malam Bala firfita. Baki ya kyaɓe ya ce.
"Da dai Kande ce ke yi min firfitar nan da na ce Allah Ya yi mata albarka. Dan ita ba ta yi min biyayyar son zuciya ko ta wata manufa. Dan haka ina jinki, faɗi buƙatarki na ji ki ƙara gaba."
Tura ɗankwali ta yi gaba ta na fari da ido ta ce.
"Ka dai ji da shi Malam,ni ba zan biye maka ba a cikin daren nan da na ƙunso abun alkhairi a baki na mu yi faɗa da kai. Dan haka ka karkaɗe kunnuwanka ka kuma bani hankalinka nan dan jin abinda nake tafe da shi."
Hannu Malam Bala ya siɗe ya na mai ture kwanon tuwon gefe ya kalli Innar Suwaiba ya ce.
"Ikon Allah! Ke kuwa wanne irin abun alkhairi ne haka ya risinar min da ke?"
Sai da ta yi ƙasa da muryarta sannan ta ce.
"Malam bana dai Suwaibar mu an yi miji,irin mijin da kake nema,mai kuɗi wanda zai dinga miƙo wa ba wanda zai siyi akuya ta dawo ta na ci maka danga ba."
Baki Malam Bala ya washe ya kalli matar tasa ya ce.
"Ke ki bari dan manzo? Shi kuwa wannan surukin nawa a ina yake?"
Dariya Innar Suwaiba ta yi cike da jin kunya ta ce.
"Ai abun ƴar gida ce Malam. Tuwona mai na za a yi. Wato dakan ɗaka shiƙar ɗaka tankaɗen bakin gado ba."
"Ke ni ki yi sauri ki sanar da ni ɗan wanne gida ne a kaf ƙauyen nan na ji ko ubansa na da arziƙin da zan iya bawa ɗansa auren ƴa ta."
"Malam ba fa wani bane face Abdulwahabu ɗan gidan marigayiya Atine ta Malam Musa Manomi."......
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 13