Share this page
12 / 13
Allah ya raba shi da rayuwarsa gaba ɗaya." Harara Mudassir ya danƙara wa Malam Bala ya yi ƙwafa. Shi dai har a wannan lokacin ransa bai risina ba,nasiha sosai Sarki ya yi musu wadda daga ƙarshe ta ratsa su ta sanya su yin haƙurin dole ba dan sun so ba. Har gidan Salma Malam Rabi'u ya kai su,su na zuwa suka tarar da ita ta na cin fuffuken kazar daren jiya da bata ci ba,duk da cewa sai da Samira ta shiga ta ɗebi mai yawa ta na faɗin. "Abunka da mai juna,ina zaune jikina ya bani akwai abun motsa baki a nan,to gani na zo a bani kason maƙotaka. Sannan daga yau idan aka kawo miki abun motsa baki ko na kari ki tabbata kin ajiye min na zo na taɓa nima,idan ba haka ba zan yi miki azabar da tunda uwarki ta haife ki baki taɓa ganin an yi wa wani irinta ba." Miƙa mata ledar gaba ɗaya Salma ta yi ta ɗebi son ranta ta bar mata wajen da babu wani nama sosai. Da sauri Salma ta ture ledar dake gabanta ta nufi Yayanta ta rungume shi ta sanya kuka mai taɓa zuciya. Abdulwahab rungume ƙanwarsa ya yi a jikinsa sosai yana jin kamar ya raba jikinsa biyu ya saka ta ciki. Ji yake yi sam be bata rayuwa mai inganci ba kamar yanda ya kamata,sai gashi an datse mata ƙuruciyarta ta hanyar aura mata tsoho. Da sauri Mudassir ya fita ya na sharar ƙwallar tausayawa Salma. A ƙofar shiga sashen Salma ya gamu da Malam Rabi'u ya na ba da kuɗi a siyo wa Salma abun kari. Har ƙasa Mudassir ya durƙusa yana hawaye ya ce. "Baba don girman Allah ka riƙe mana Salma da amana,ka tausaya mata ka ririta maraicinta,ka kuma bata kulawa da gatan da bamu samu damar bata ba,Baba don Allah kada ka bari a cutar da Salma. Mun baka amanar Salma idan ka ci amanar ta amanar Allah za ta ci ka." Jikin Malam Rabi'u ne ya yi sanyi ƙalau,hannu ya miƙa wa Mudassir don ya tashi amma ya girgiza masa kai yana sake haɗe hannayensa biyu yana roƙon Malam Rabi'u akan ya kula musu da amanar Salma. A haka Salma da Abdulwahab suka same shi. Hannu Malam Rabi'u ya miƙa wa Salma ya kira ta gare shi. Sakinta Abdulwahab ya yi ta ƙarasa wajen Malam Rabi'u ta tsaya daga ɗan nesa da shi. Mudassir Malam Rabi'u ya kalla ya dafa kan Salma ya ce. "Gata nan ku tambaye ta daga jiya zuwa yau idan akwai abinda na yi mata wanda ya nuna ni Rabi'u zan yi mugun zama da ita. Kana ji na ko samari? Wannan yarinyar ƙaddarata ce,hukuncin ni zan aure ta ita za ta aure ni a halin da nake ciki ya tabbata babu mai canja hakan. Na yi muku alƙawari da sani na ba zan taba cutar da Salma ba,idan kuma yanzu ta ce bata son aure na a gabanku zan tsinke igiyar da ta ɗaure mu ni da ita." Cikin sauri Abdulwahab da Mudassir suka kalli Salma tare da fatan ta ƙi wannan aure. Ita kanta Salma a zuciyarta tana son furta kalmar saki,amma a zahiri tana jin kamar idan ta bar auren ko ta bar gidan za ta iya mutuwa,wani irin hali ta shiga na firgici da tsoro tare da azabar ciwon kai mai tsanani. Dariyar Samira ce ta sanya su juyawa gaba ɗaya su na kallonta. Takowa ta yi gaban su ta ce. "Ni fa mamaki kuke bani gaba ɗayanku, wai shin akan Salma aka fara aure da ƙarancin shekaru;ko kuwa akanta ƙaramar yarinya ta auri babban mutum? Kun bi kun damu kanku kun ishi mutane da abu ɗaya,aure dai ya riga ya ɗauru,kuma da alama rabo ne ya kira Salma gidan nan, duk wanda ya nemi ya datse igiyar aurenta to da alama tashi rayuwar zai datse." Ta na faɗan haka ta kalli Salma dake jin kamar da ita ta yi maganar ƙarshe,domin kuwa ji take yi idan ta nemi saki za ta mutu. Mudassir ne ya kalli Abdulwahab yana neman ƙarin bayani,da laɓɓansa ya yi masa nuni da ita ce Samira. Girgiza kai ya yi ya na jinjina ƙarfin hali irin nata. Daga ƙarshe dai ɗakin Salma su Abdulwahab suka koma suka zauna suna ta bata haƙuri tare da lallashinta akan ta yi biyayya da yardar Allah za ta ci riba anan gaba. Kuɗi mai yawa Abdulwahab ya bata ya ce. "A duk lokacin da kika ji zaman gidan be yi miki ba,ki je tasha ki hau mota ki zo waje na kin ji ko? Ai zaki gane Ƴankaba ba sai na sake yi miki kwatance ba ko? Sannan duk abinda kike so ki siya da kuɗin nan,idan sun ƙare Malam Sallau zai kawo miki wasu,dan zan dinga aiko miki shi akai-akai." Abdulwahab na gama magana Mudassir ya ce. "Ko kina son wani abu ne Salma? Idan da abinda kike so kuma ki sanar da mu kafin mu tafi." Kai ta girgiza tana murmushi. A hankali ta ce. "Babu abinda nake so Yayah Allah Ya saka da alkhairi,don Allah ku ce wa Gwaggona ta kwantar da hankalinta,wannan Baban ba mugu bane,ta yi min addu'a Allah Ya sa kada ya dake ni ko ya min faɗa. Sannan ku gaishe min da yarana idan Baban nan gidan ya barni zan zo na gansu." Dariya sosai Mudassir ya fashe da ita ya na kallon Malam Rabi'u da ke haɗe fuska a duk sanda Salma ta kira shi da Baba. Cike da shaƙiyanci Mudassir ya ce. "Ai wannan Baban na kula ya na da kirki gaskiya." Da sauri Malam Rabi'u ya kalle shi ya sake tamke fuska. Ganin cewa Mudassir zai fara sakin layi sai Abdulwahab ya miƙe ya ce. "To mu mun tafi sai watarana ko Salma." Idanuwanta ne suka kawo ruwa ta gyaɗa masa kai kawai. Har bakin ƙofa ta raka su ta dawo. Sallama suka yi da Malam Rabi'u suka wuce gidan Gwaggo. Suna tafiya aka kawo abun karyawa Malam Rabi'u ya karɓa ya shige musu da shi sashen su. A zaune ya tarar da Salma tana kuka. Ba tare da ya lallashe ta ko ya hana ta kukan ba ya ajiye mata abun karyawarta a gabanta,wanda yake shayi ne da bread da ƙosai. Nashi ya ja gefe ya ɗauki kofuna biyu a kwandon kwanikan da yake nashi tun yana shi kaɗai ya juye shayinsa itama ya juye mata nata ya tura mata gabanta. Ganin ba za ta dena kukan bane ya sanya shi sassauta murya ya ce. "Ɗauki abincinki ki ci,su yayun naki ai ba za su so su ganki zaune da yunwa ba ko?" Kai ta ɗaga sama ta na jan majina ta ja abun karyarwarta ta fara ci,ta na tsaka da ci ta tuna da gargaɗin da Samira ta yi mata na rage mata duk wani abu da ta ci,da sauri ta ture abincin ta koma gefe ta na zare ido. Malam Rabi'u bai kula da abinda ke faruwa ba,yana gama karyawa ya miƙe ya bar gidan gaba ɗaya. Fitarsa ke da wuya Samira ta afka sashen na Salma,cikin zare mata ido ta ce. "Ina abinda aka bawa Tanimu ya siyo miki?" Da sauri Salma ta ce. "Gashi Yaya Samira." Ɗauka Samira ta yi ta leƙa ledar ta na washe baki ta ce. "Yauwaa yarinyar kirki,idan ki na ajiye min irin wannan lafiya lau za mu zauna a gidan nan ni da ke babu mai jin kammu. Miƙo kofin can na tarfa miki shayin. Ko kuma bari ina zuwa." Ledar ta tattare tai gaba,babu jimawa sai ga Tanimu ɗan mijin Samira wadda mahaifiyarsa ta rasu ta bari ya shiga da wani kwano duk ya yi lamba ya ba wa Salma ya fita. Salma na buɗawa ta ga wani irin tuwo baƙiƙƙirin da koriyar miya fatau. Ture wa ta yi gefe ta zabga tagumi tana tunanin yanda rayuwarta ta koma. A ɓangaren su Mudassir kuwa sai da suka lallaɓa Gwaggo suka kwantar mata da hankali sosai tare da tabbatar mata sun tarar da Salma yanda basu yi zato ba,suna kuma fatan ta tabbata cikin farinciki a gidan nata. Daga ƙarshe suka ajiye mata ƴan kuɗaɗen da za ta yi wa Salma siyayyar duk abinda bata da shi suka tafi. Haka rayuwar Salma ta kasance a gidan Malam Rabi'u cikin ƙuncin da shi kansa bai san ƴar ƙaramar amaryar tasa tana cikinsa ba. Domin kuwa duk wata hanya da Samira ta san za ta goge sawun musguna wa Salma da take yi a gidan ta goge. Dan haka Malam Rabi'u da Malam Jamilu har alfahari suke yi da zaman lafiyan da su Samira ke yi. Lokuta da dama idan ya kawo nama ko kifi Samira yake bawa ya ce ta yi musu dabge saboda Salma ta ci ta ji daɗi. Ba tare da saninsa ba sai dai ta zuba wa Salma romo kaɗan ta bata,ita ta zauna ta cinye naman ko kifin. A hankali Salma ta dinga rama mai muni,Samira kuma na narka ƙiba abunta kamar mijinta shine mai kashe kuɗin domin ta ji daɗi..... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ Mai son ci gaba da karanta littafin MUGUWAR MACE ya saka 1k ta 9031416423 Hamidah Ahmad Sanusi Opay. Sai a tura shaidar biya ta 09031416423. Don tsarkin mulkin Allah kada ki sayi littafi na idan za ki yaɗa shi ba tare da kin bari na kammala ba,idan kika yaɗa kamar kin dakushe min sana'a ne. PAGE 20. LAST FREE PAGE. Dakan kayan yaji da za su yi miyar dare Salma ke yi a ƙaton turmin tsakar gidan nasu wanda marigayiya matar Malam Jamilu ta yi dakan furar sayarwa a ciki. Gaba ɗaya taɓaryar ta yi wa Salma nauyi da tsawo,a haka ta jure ta ke ta faman daka duk ta haɗa zufa;Samira na yi mata faɗan sanyin jiki da take da shi. Salma na gamawa ta duƙa ta kwashe kayan yajin ta nufi madafi da shi ta buɗe tukunyar dake kan wuta ta zuba. A gajiye ta shiga ɗakin Samira dake hango duk abinda take yi a tsakar gidan ta durƙusa har ƙasa ta ce. "Yah Samira na gama,akwai abinda zan yi miki?" Shiru Samira ta yi ta na wani nazari,a cikin ranta ta ce. 'Ya kamata fa na karɓi abinda zan bayar a sunan Hauwa a wajen yarinyar nan,tinda ita ce sabuwar amarya,na tabbata idan na sauka lafiya nima za su rama wa kura aniyarta.' Muryar Salma ce ta katse ta daga tunanin da ta faɗa ta ce. "Yah Samira miyar na kumfa me zan zuba?" "Ki je ki buɗe murfin tukunyar ki saɓa bakin. Yauwa idan kin gama mu je ƙofarki ki buɗe min lefen ki akwai abinda zan ɗauka na kai wa Hauwa na barkatu." "To Yah Samira." Cike da ladabi Salma ta je ta saɓa bakin tukunyar kamar yanda Samira ta umarce ta,daga nan sai ta wuce sashenta ita da Samira,su na shiga Samira ta hau leƙe da dube-dube ko za ta ga wani abun da za ta yi faɗa akai ko ta ɗauke. Har uwar ɗaka suka shiga tare,da ƙyar Salma ta iya sakko da akwatunan ƙasa Samira na kallon ta;amma ta ƙi taimaka mata. Ta na saukewa Samira ta zauna a gaban kayan tana ɗagawa,tsabar son zuciya ji take yi da da hali da ta kwashe kayan dika,domin Malam Jamilu bai kashe mata kuɗi kamar yanda aka kashe wa Salma ba. Hannunta ta ɗora akan wata santaleliyar atampa mai kyau,da dikkan alamu ita ce ma mai babban kuɗi a cikin kayan. Turare da breziya Samira ta sake ɗauka sannan ta miƙe tsaye ta ce. "Maza ki kwashe su ki mayar da su mazaunin su. Ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,ko sama da ƙasa za ta haɗe idan an tambaye ki inda atampa take ki ce baki sani ba,idan kika faɗi suna na sai na sa gabanki gabar na yanke da wuƙa. Shegiya mai ido kamar na mage." Kan Salma ta dangwara sannan ta ɗaga rigarta ta soke atampar da turaren tare da breziya ta fita da sauri. Kai tsaye ɗakinta ta nufa ta cire kayan daga cikinta ta samu leda babba ta saka kayan ta ɓoye. Murna ta dinga yi domin ta samu hanya mafi sauƙi da za ta dinga bada kayan barkatu ba tare da sisinta ya yi ciwo ba. A wannan azaba da uƙubar Salma ta yi wata biyu a gidan Malam Rabi'u. Watarana da daddare Malam Rabi'u da Salma su na zaune yana jefa lomar tuwon da Salma ta tabbatar masa cewa da kanta ta dafa masa. Murmushi ya yi ya kalle ta ya ce. "Inyeee an Salamemen Gwaggo hannu yana ta faɗawa. To ga wannan ki sayi sha ka laɓe ki sha abunki." Hannu ya saka a aljihunsa ya zaro nera ɗari sabuwa kar ya bata. Murna Salma ta dinga yi ta na yi masa godiya. A hankali Malam Rabi'u ya tsaya yana kallon ta shi ma yana murmushi, sai dai bai jima yana murmushi ba fuskarsa ta koma ta jimami,cike da kulawa ya kalli Salma ya ce. "Salma ko dai akwai abinda yake damunki ne a gidan nan da baki sanar da ni ba? Gaba ɗaya kin rame kin yi baƙi kamar ba ke ba,ni kuma na san ina bakin ƙoƙarin na ga na kawo miki duk wani abu na jin daɗin rayuwa,domin a yanzu na yarda na amince bani da wata ko wani da ya dace da ya ci dukiyata da nake ta tarawa da ya wuce ki. Ki na da hankali,natsuwa da tarbiyya,ki na da kawaici da juriya akan halin da kike ciki,shin ko dai har yanzu ba kya so na ne na mayar dake wajen Gwaggo na haƙura da auren? A ƙalla dai duk wanda ya kalle ni zai tuna cewa na taɓa yin aure a rayuwata ko sau ɗaya ne." Tinda Malam Rabi'u ya fara magana jikin Salma ya yi laushi idanuwanta ke zubar da hawaye. Tsabar azabar da Samira ke gana mata ko sunan ta aka kira sai gabanta ya faɗi ta zaci na Samiran aka kira. Ganin hawaye na zarya a kuncinta ne ya sanya Malam Rabi'u kiranta wajensa. Babu musu ta tashi ta isa gare shi ta zauna a saman cinyarsa kamar yanda ya fara sabar mata. Ba dan yana jin wata sha'awa ba haka kawai yake jin daɗi idan Salma ta zauna a jikinsa,ya na ƙaunarta sosai saboda natsuwarta da kamewarta,bata da hayaniya da kwaramniya irin ta yara. Cike da sigar lallashi ya ce. "Sanar da ni abinda kike so Salamatuna. Ko akwai abinda yake damunki?" Kai ta girgiza masa alamar babu komai,sake tambayarta ya yi a karo na babu adadi,da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce. "Ina so na ga Gwaggona. Tinda na zo gidan nan sau ɗaya ta zo ta kawo min kayana,ni kuma ban samu damar zuwa na ganta ba. Kuma ina son ganin Aabid,Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin za ta zo yawon arba'in Kura amma bata zo ba gashi har sun yi wata uku zuwa huɗu." Murmushi Malam Rabi'u ya saki,bai san dalili ba sai zuciyarsa ta ji daɗi da Salma bata ambato matsala a zaman su tare ba,duk damuwarta mai sauƙi ce a wajensa. Kanta ya shafa sannan ya ce. "In dai wannan ne matsalar ki to ki shirya a daren nan zan kai ki wajen Gwaggo ba zan bari ki kwana baku gana ba. Wajen Aabid kuwa ki yi haƙuri ki ƙara ko da wata guda ne sai na kai ki,dan kin san al'adar garin nan amare ba sa yawo idan basu cika shekara ba. To mu dai za mu fara take doka daga yau ko?" Bakinta ta rufe ta na dariya cike da ƙuruciya. Shi ma dariyar ya taya ta,daga ƙarshe ya ƙarasa cin tuwonsa ya na bata a baki har suka cinye. Salma ce ta kwashe kwanukan ta kai waje,ta na fita ta ji kamar an ruga da gudu an bar sashen nata,ta ji tsoro sosai a ranta,amma kuma ta tabbata ko ma wanene ba zai wuce Yah Samira ba,dan ba sau ɗaya ko sau biyu ta kama ta tana yi musu laɓe ba. Hannunta da bakinta ta wanke ta koma ɗakin. Malam Rabi'u kuwa sai da ya zaga bayi sannan ya wanke bakinsa ya kulle ko ina ya miƙa wa Salma sabon hijabi da takalmi ya ce. "To bismillah amaryar Malam Rabi'u mu je ko?" Bakinta ta toshe tana dariya ta yi gaba yana biye da ita. A haka suka isa har gidan Malam Bala. Malam Bala dake ƙoƙarin shiga gida ne ya ga Malam Rabi'u tafe da Salma su na hira a cikin hasken farin watan da ya mamaye ilahirin garin Kura. Sam ransa bai yi masa daɗi ba da ya gan su cikin nishaɗi. Sai ya kawar da kai ya yi kamar be gansu ba zai shige gidan. Cikin sauri Malam Rabi'u ya kira sunansa,washe baki Malam Bala ya yi yana fara'a kamar babu abinda ke damun zuciyarsa. A ɗarare Salma ta durƙusa ta gaishe shi,haɗe fuska ya yi ya ce. "Ince dai Ja'irar yarinyar nan ba wani mugun abun ta gunguma ba ka dawo da ita gida? Ina so ki sani muddin kika kaso auren nan ba dai gida na ba,sai dai ki nemi inda za ki je." Da sauri Malam Rabi'u ya tari numfashin Malam Bala ya ce. "Allah na tuba me wannan halitta mai tsarkin za ta yi min na ɓacin rai? Yarinya kamar ba a cikin shekarun biri take ba. To ka ganta nan da zan ce mata ta haɗiye min ruwa in ji ƙoshi a cikina za ta yi tsabar yanda take yi min biyayya. Gwaggonta na kawo ta ta gani,ka san abun yaro sai ana lallaɓa shi." Ƙwafa Malam Bala ya yi ya saki yaƙe ya ce. "Maza ki tashi ki shiga ciki,kuma kada ki jima,tinda sarai kun sani ai mace bata fita daga gidan miji sai ta shekara,wata ma sai ta haihu idan za ta je wankan gida take zuwa gida ita da abinda ta haifa." Da sauri Salma ta miƙe tsaye ta shige cikin gida cike da murna. Malam Rabi'u kuwa sai ya tuntsire da dariya yace. "Wannan yarinyar kam ai sai dai a yi mata uziri ta yi abinda take so,dan kuwa nan kusa dai ban ga yanda za ta samu juna biyu ba ballantana ta haihu." Kai Malam Bala ya karkace ya ce. "Ban gane nan kusa ba,wai kana nufin har yanzu baka shiga gonar yarinyar nan ba?" A karkace shima Malam Rabi'u ya kalli Malam Bala ya ce. "Habaa Malam! Wannan yarinyar ai ta yi ƙanƙanta da wannan al'amari,kai dai kawai Allah Ya sa mu na da rabon alkhairi a gaba." "Kada ka duba yarintarta fa Rabi'u. Mata nawa aka yi wa aure da shekarunta kuma suka haihu? Ka duba kai iya tsawon shekarun da ka ɗauka a duniya,idan ban ɓata lissafi ba wannan bazarar da za ta zo za ka cika shekara Hamsin da uku a duniya,ka faɗa min wata matar za ka aura nan gaba idan baka tara da wannan ba?" Kyaɓe baki Malam Rabi'u ya yi ya ce. "Ni fa na riga da na yarda da maganar mutane,da dikkan alamu aljana ce ta aure ni,dan bana samun nutsuwa a ko ina sai a cikin bacci na. Na raina wannan yarinyar sosai Malam Bala bata da abinda za ta bani a yanzu dai,ban sani ba ko nan gaba." Cike da takaici Malam Bala ya bar wannan tattaunawar ya ɗakko wa Malam Bala zancen gona. A cikin ransa yana saƙa tsiyar da zai shukawa Malam Rabi'u a nan gaba. A ɓangaren Salma kuwa ta na shiga cikin gidan ta shiga ɗakin Gwaggo ta na murna. Gwaggo ma na ganinta ta saki kaɗin da take yi ta rungume Salma ta na faɗin. "Maraba maraba jikalle na kin fiye min ɗa daɗi." Sai da suka gama murna Kande ta ce. "Ke salma garin ya aka yi kika zo war haka bayan baki cika shekara da aure ba? Ko dai gudowa kika yi bai sani ba? Me yake faruwa a gidan naki na ga kin rame kin yi duhu?" Cikin dariya Salma ta ce. "Gwaggo da shi fa muka zo yana waje yana jiran mu gaisa na je mu koma gida. Kuma ni babu abinda yake faruwa da ni a gidan sai alkhairi. Gwaggo na yi kewar ki sosaiiii." Kai Gwaggo ta jinjina ta na nazari,can sai ta yi ƙasa da muryarta ta ce. "Ko dai kun fara kwana a ɗaki ɗaya da Malam Rabi'u ne Salma?" Da sauri Salma ta kame baki tana zaro ido waje,cike da tsoro ta hau ja da baya,dan bata so Gwaggo ta gane tana sakar masa jiki har ta hau cinyarsa ta zauna. Ganin irin kallon da Gwaggo ke binta da shi ne ya sanya ta fara kuka ta ce. "Ki yi haƙuri Gwaggo zan faɗa miki gaskiya,dama...dama...uhumm shine yake ɗora ni a cinyarsa,ko ya ce na hau,amma Gwaggo ni ban taɓa kwana a ɗakinsa ba,shima kuma bai taɓa kwana a ɗakina ba." Salma ta ƙarasa maganarta cike da yarinta da tsoro. Murmushi Kande ta yi ta ja Salma jikinta,a hankali ta dinga warware mata duk wani tsoro da ta dasa mata a ranta akan maza. Cikin sauƙi take sanar da ita duties ɗin matar aure a wajen mijinta. Lokacin da ta zo kan gaɓar bayani akan kwanciyar aure sai Salma ta hau jin tsoro jikinta ya ɗauki rawa. A haka Gwaggo ta yi mata bayanin komai yanda za ta fahimta. Daga ƙarshe Kande sai ta tashi ta hau haɗa mata kayan cimar da Abdulwahab ke kawowa a kai wa Salma bata samu damar kai mata ba. Hotunan Aabid da aka ɗauka aka wanko Kande ta bata ta ce. "Wannan saƙo ne daga ɗanki. Yana can duk kayansa sun yi masa kaɗan saboda girma." Dariya Salma ta yi kafin ta ce. "Amma Gwaggo me ya sa Yah Audu bai zuwa gani na? Kuma Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin zuwa amma har yau bata je ba." "Hidima ce ta yi wa Layuzah yawa saboda Ammabuwa na ɗauke da juna biyu mai wahalar laulayi,ga yaronta bai yi wani ƙwarin a zo a gani ba,shi kuma Yayanki baya son zuwa gidan ne saboda Samira,ina fatan za ki yi masa uziri." Ɗaga kai Salma ta yi ta buɗe baki za ta yi magana,muryar Hasiye ta katse ta ta yi sauri ta juya tana kallon bakin ƙofa. Washe baki Hasiye ta yi ta ce. "Ah ah! Yau amare ne a gidan namu babu ko sallama ballantana mu ji zuwan baƙi? In ji dai ba wani laifin ta yo ba ya koro ta?" "Sai dai ki ga kora a kan taki ƴar amma ba akan jika ta ba." Guɗa mai ƙarfi Hasiye ta rafsa sannan ta ce. "Yo su waye suka yi silar auren har da za a yi wa mutane firirita? In ce dai ni ce na shiga na fita na haɗa auren? Kuma naga da ai cewa kuka yi ba kwa so,yanzu kuma sauya zani ta yi da zaki ce haka Kande?" Banza Kande ta yi da ita ta gama ƙulle wa Salma kayan da ta haɗa mata kaf. Har Salma za ta ɗauka sai ta tuna yanda Samira ke yi mata iko da ƙwacen kayanta. Cikin sauri ta durƙusa ta kunce ɗaurin kayan ta kwashi hotunan Aabid da abinda ta san za ta iya cinye wa kafin su isa gida ta kwasa da gudu ta yi waje. Duk kiran da Gwaggo ke yi mata bata waiwaya ba ballanta ta amsa ta. A nan ta bar Hasiye na san barka da yanda ta ga rama da duhun fatar da Salma ta yi. A ƙofar gida ta tarar da Malam Rabi'u da Malam Bala,kai tsaye wajen Malam Rabi'u ta je ta ci burki ta ce. "Baba taso mu tafi gida." Harar wasa Malam Rabi'u ya sakar mata ya ce. "Ba na ce ki dena ce min Baba ba? Ni mijinki ne,dan haka kada ki sake kira na da Baba,daga yau ki dinga kira na da Mijin Salma,idan ba za ki faɗi haka ba ki dena kira na da kowanne suna bana so." Dariyar ƙuruciya ta yi ta buɗe ledar biscuit ta fara ci a gabansu ta na rausaya kai cike da jin daɗin abinda take ci ɗin. Tsaki Malam Bala ya ja cike da hassada da baƙin cikin bai samu yanda yake so ba,sallama ya yi musu ya shige cikin gida ya samu Hasiye na ta yi wa Kande rashin kunya. Har a wannan lokacin yana son Kande sosai a ransa,kuma ya na ganin girmanta,shi kansa yana rasa dalilin da ya sa yake rufe ido ya karta mata rashin mutunci. Tsawa ya daka wa Hasiye ya ce. "Ke bana son rashin ta ido,Kanden sa'ar ki ce? Na ce sa'arki ce da zaki

Chapter 12 of 13