Share this page
7 / 13
min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 12. Ganin irin kallon da Malam Bala ke yi mata ne ya sanya ta muskutawa kusa da shi ta yi ƙasa da muryarta ta ce. "Malam kada ka ce komai game da wannan maganar,kai dai kawai ka saka wa lamarin nan albarka. Ko ka manta yanda haihuwar yaron nan ta zamo silar arziƙin ubansa kafin ya bar duniya? Sannan ka duba ka ga yanda arziƙi ke shigo masa ko ta ina daga fara sana'ar saye da siyarwar hatsi. Na tabbata nan gaba sai ya fi haka arziƙi domin da dikkan alamu ya na da ƙashin arziƙi. Idan aka ce wannan yarinyar kuwa ta aure shi ai ba ita da take a matsayin matarsa ba;mu kammu iyayenta sai mun huta." Fuskarsa da ya ɗaure ya saki ya hau washe baki. Kwanon abincinsa ya ja gabansa ya yanko loma sannan ya ce. "Ki je ki fara shirya yarinya lokacin aurenta ya yi." Guɗa Innar Suwaiba ta kama hanci za ta zabga, Malam Bala ya riƙe mata hannun cikin sauri ya ce. "Matsalata da ke hauka. Yanzu idan wani ya ji ki na guɗa ai sai a zo jin bahasi,daga nan shikenan kuma kin rusa mana duk wani tanadi. Dan na tabbata yaron nan sai an yi masa ƴan dabaru zai yi mana biyayya,mugun taurin kai ne da shi kamar dutsen wuta." Baki Innar Suwaiba ta kama ta na dariya ta fita daga ɗakin ta koma nata ɗakin. Zaune ta tarar da ƴar tata da ta gama yi musu laɓe ta ji komai,amma sai ta nuna sam bata san me yake faruwa ba. Ta na ganin mahaifiyarta sai ta miƙe tsaye cike da damuwar ƙarya ta na tambayarta yanda suka yi da Babanta. Nan Innah ta zauna ta sanar da ita komai cike da murna. Ihun murna Suwaiba ta sanya ta na ta tsalle tare da zayyano wa mahaifiyarta irin jin daɗin da za su samu idan har ta auri Abdulwahab. A wannan daren da ƙyar Suwaiba ta samu bacci ya ɗauke ta tsabar murna. Washegari da sassafe sai ga Suwaiba an yi ciki tsami waje fes-fes an sha kwalliya kamar mai zuwa gidan biki. Ta na gamawa ta samu waje ta yi zamanta a ɗaki kunnuwanta na baje a tsakar gida ta na jin mai shiga da kuma mai fita. Da misalin takwas da rabi na safiya Abdulwahab ya shigo gidan cikin adonsa irin na ƴan birnin wancan lokaci. Kai tsaye ƙofar ɗakin Malam Bala ya nufa ya samu waje ya zauna a saman tabarmar da yake shimfiɗawa ya zauna da safe ya karya;tare da karɓar gaisuwar yaransa. Cike da ladabi Abdulwahab ya gaishe da Malam Bala. Malam Bala ma washe baki ya yi tare da jimƙe hannun Abdulwahab a nasa ya na amsa gaisuwar kamar zai kwanta a ƙasa. Su na cikin gaisawa. Suwaiba ta fito cikin kwalliyar da ke ba wa Abdulwahab dariya ta na karairaya ta zo gabansa ta dire kwanon sha. Cike da jin kunyarsa ta kashe murya ta gaida shi. Amsa wa ya yi yana binta da kallo ya na dariyar gayunta. Ita da Malam Bala sai suka ɗauki hakan a matsayin ƙyasawar Abdulwahabu. Ko buɗe kwanon be yi ba ya nufi ɗakin Gwaggo Kande inda yake jiyo kukan Salma ta na faɗin ita dai ba za ta je makaranta ba Baba ya hana. Ya na shiga ɗakin Salma ta nufe shi ta na shassheƙar kuka. Zaunar da ita ya yi a saman cinyarsa ya na shafa kitsonta da ya kwanta a kafaɗunta ya ce. "Ai tun jiya mu ka yi magana da Baba ya amince ki je,ashe bai sanar da ku ba Gwaggo?" "Humm ka san Salma yarinya ce mai biyayya kamar mahaifiyarku. Tinda ta ji ya ce baya so ta tsiri wannan iya shegen. Amma tinda ta ce ba za ta je ba a bada kayan nata a amshe jakar duk a bayar. Wannan kayan ƙwalamar da ka siyo mata ma sadaka zan yi da su,dan babu amfanin ajiye wa." Salma na jin haka ta wuce ta hau saka uniform ta rataya jaka ta fice ta bar ɗakin ba tare da ta ce musu komai ba. Dariya Abdulwahab ya yi ya ce. "Ke ce maganin ƴar gidan naki Gwaggo." "Ahaf ai maganin biri karen maguzawa Abdulwahab." Gaisawa suka yi ta jawo masa abincinsa sannan ta fita daga ɗakin dan zuwa yin wasu ayyukan. Ta na fita Malam Bala ya kira ta ya ce ita da Innar Suwaiba su je ya na son yin magana da su. Babu ɓata lokaci ta ajiye ƙwaryar dusar awaki ta wuce ɗakin Malam ta zauna ta na jiransa. Ba ta jima da zama ba Innar Suwaiba da Malam Bala suka shiga ɗakin. Su na zama Malam ya yi gyaran murya ya ce. "Ba wani abu bane ya sa na ce ku zo turakata dikan ku face ina so na sanar da ku wani abun farinciki da ya same mu. Kande dama ke ce baki san me yake faruwa ba,dan ita Babar su Suwaiba ta san komai. Ina so ki taya mu murna bana dai Allah Ya yanke wa Suwaiba zaman gida za ta yi aure." Murmushi Kande ta yi ta ce. "Barka barka Hasiye Allah Ya sanya alkhairi da albarka ya nuna mana lokacin da rai da lafiya." Ta na faɗin haka ta ja bakinta ta yi shiru. A ƙufule Innar Suwaiba ta ce. "Shikenan abinda za ki ce Yaya? Wai ni sai yaushe za ki rage wannan zafin kishin naki akai na ne? Ai a ƙalla kin taya ni murna Allah Ya yanke wa ƴata wahalar zaman gida ko?" Cike da mamaki Kande ta ce. "Ah ah ni Kandala ɗiyar Mamman yau na ga abinda ya fi zare tsayi? To in banda abinki ai ta Malam bata wuce amin ko? Me kuma kike so na yi bayan addu'ar da na yi ta sanya albarka?" Ƙwafa kawai Innar Suwaiba ta yi domin bata so su yi faɗa ta hasala Kande ta ƙi haɗin auren. Malam Bala kuwa ya na ganin haka sai ya ce. "To in banda abunki Kande ya za ki tsaya sa-in-sa da surukarki?" Kallon sa Kande ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Surukata kuma Malam? Ta ina Hasiye ta zama surkar tawa?" Washe baki suka yi a tare shi da Innar Suwaiba kafin ya ce. "To ai Abdulwahabu shi ne angon. Kin ga kuwa idan da kara ai ke kakar amarya ce." Miƙewa Kande ta yi ta na tafa hannayenta tare da yin salati,sai da ta gama tsaf sannan ta kalle su ta ce. "Lallai ma Hasiye baki da kunya. Kin manta irin wulaƙanci da cin kashin da kike yi min a gidan nan saboda ni ban haihu ba? Wanne irin gori da tozarci ne baki min ba akan Suwaiba da ƙannenta? Har ta kai ta kawo gaba ɗaya yaran nan sun raina ni. Shi ne yanzu dan kun ga yaro ya yi ƙumbar susa kuke so ku bashi ƴarku ya aura,to ni dai babu ruwana a wannan zance,idan yana so a yi aure,idan baya so babu wanda ya isa ya yi masa auren dole." Da sauri Malam ya kashe ta ya na faɗin. "Haram ba bashi ita za mu yi ba,ni da kai na na fuskanci saƙon soyayyar da yake aika mata ta idanuwansa. Shi yasa na yanke shawarar haɗa su aure tinda itama ta na son sa." "Au haka abun yake? To Allah Ya bada sa'a Ya sanya albarka." Kande na fita daga ɗakin sai ta ƙwala wa Abdulwahab kira ta ce ya je Malam na neman sa,dan ta san halin mutanen nata muddin bata yi haka da wuri ba suka zauna waje ɗaya da Abdulwahab tsaf za su ce ita ta hana auren. Gaban Hasiye ne ya yanke ya faɗi domin ba ta haka ta so ya san da maganar ba. Dake wa ta yi ta gyara zama a turakar Malam Bala har Abdulwahab ya je ya zauna a tabarmar ƙofar ɗakin. Wani irin kwarjini Abdulwahab ya yi musu,sai dai son abun duniya ya rufe musu ido. Dan haka Malam Bala ne ya fara gabatarwa da Abdulwahab buƙatarsu na auren Suwaiba. Da sauri kuma ba tare da jin nauyi ko kunya ba Abdulwahab ya ce. "Baba ai ni ina da wadda nake so da aure har mun tattauna da Gwaggo ma akan hakan jiya. Dama ina jiran ka gama kari ne na zo maka da maganar dan har na sanar da Kawunaina da Baffanina,sun kuma amince za su zo su ɗauke ka ku je nema min auren Layuzah ƙanwar abokina da muke kasuwanci tare wato Mudassir." A guje Suwaiba ta fito daga ɗaki ta na gursheƙen kuka duk hodar ta ta caɓe domin maka ta ta yi da kyau,ga baƙin kwalli duk ya dame mata fuska. Kallonta Abdulwahab ya yi ya ji dariya ta zo masa. Malam Bala da ya ɗaga labule ya ce. "To idan baka son Suwaibar murmushin uban me kake yi mata ɗazu da ta kawo maka kunu? Sannan yanzu ma dariyar me kake yi mata?" Ƙunshe dariyarsa Abdulwahab ya yi ya ce. "Baba wannan kwalliyar ta fuskarta kaɗai ta isa ta firgita duk wani wanda ya zo neman aurenta ai." Baki Hasiye da Malam Bala suka buɗe suna kallon Abdulwahab da ke ci gaba da dariyar kukan Suwaiba. Dawowar Kande daka wajen awakinta kenan ta ga yanda Suwaiba ke mulmula a ƙasa ta na kurma ihu tare da faɗin ta shiga uku ta lalace. Da sauri ta nufe ta za ta ɗaga ta Hasiye ta riga ta ta ɗaga ƴarta ta na sharar kwalla ta ce. "Ni dama na jima da sanin ai ba kya ƙaunata ni da ƴaƴana a gidan nan,shi yasa kika hana Abdulwahab auren Suwaiba. To ki je ke da Allah,kuma muna nan zaune Suwaiba za ta auri wanda ya dame Abdulwahab arziƙi da kyau da nasaba." "Ba na yi mata baƙin cikin samun nagari,domin ni ma ina bin dare na yi mata addu'ar samun miji na gari inda za ta huta wani nata ma ya huta;wanda bana jin a matsayinki na uwarta kin taɓa bin dare kin yi sallah kin roƙar mata miji na gari. Tinda ku dai a kullum baku da buri sai auren mai kuɗi." Cike da takaicin wulaƙancin da Abdulwahab ya yi musu Malam Bala ya ce. "Ke ɗin ma ai auren kuɗin ki kai da ni. Amma dai komai ya wuce,tinda ya ce baya son jinina ya je can ya auri duk wadda ta yi masa,amma ba da yawu na ba." Haƙuri Abdulwahab ya dinga ba wa Malam Bala amma sam ya ƙi haƙura ya riƙe shi a ransa. Daga ƙarshe sai ya shuri takalmansa ya bar gidan. Ya na fita ya hau yayata cewa duk alkhairin da ya yi wa Abdulwahab da ƙanwarsa amma ya ce zai haɗa shi aure da Suwaiba ya baɗa masa kasa a ido. Nan take mutane ƴan bani na iya suka hau zagin Abdulwahab su na tsine wa dukiyar da ya fara tarawa albarka. A ɓangaren Abdulwahab kuwa bai koma Kano ba sai da Baffansa Habu da Kawunsa Sale. Kai tsaye gidan su Mudassir suka je suka nemar masa auren Layuzah. Babu ɓata lokaci Iyayensu Mudassir suka amince da auren nasu,domin kuwa sun jima da sanin aiken da Abdulwahab ɗin yake yi wa Layuzah ta wajen Mudassir. Sannan kuma sun yaba da tarbiyyarsa da riƙonsa da addini. Sosai iyayen Abdulwahab suka ji daɗin tarbar da aka yi musu. Tin daga wannan ranar Abdulwahab ya riƙe wuta wajen zuwa zance da kafa gwamnatinsa a wajen Layuzah. Ita kuwa dama ta jima da yaba wa da abokin Yayan nata ba ta dai nuna alama ba ne kawai saboda kunya irin ta ƴa mace. Bayan wata ɗaya da zuwan iyayen Abdulwahab,ya shirya ya je ƙauye ya siyar da filayensu gaba ɗayansu da duk wata kadara da kiwon iyayensu aka raba musu gado shi da Salma. Kasonsa ya ɗauka ya gyara gidan iyayensa aka yi musu ginin zamani,a ciki ya yi lefe ya kuma aje na sadaki. A wannan lokacin ne ya haɗu da Malam Sallau. Malam Sallau mutum ne mai riƙon amana,ya ƙware a harkar gini da dillancin gidaje da filaye. Tin daga wannan lokacin suka fara ƙulla alaƙar kasuwanci,domin kuwa Malam Sallau Abdulwahab ya ba wa kuɗin Salma aka siya mata fili ma daidaici,sai ya bada hayarsa wa manoma,duk shekara idan sun yi noma su na ba da kuɗin hayar gona. Ya na zuwa Kano sai ya buɗe mata account a bankin da yake ajiyar tasa dukiyar. Bayan watanni uku aka ɗaura auren Layuzah da Abdulwahab. Aure ne da ya samu halartar dangin iyayensu Abdulwahab ɗin baki ɗaya. Sai dai abun mamaki ta ɓangaren Malam Bala bai je ba,haka ma Hasiye ta ƙi zuwa kuma ta hana yaranta ko ɗaya zuwa. Kande kuwa abun bai dame ta ba,sai ta shiga cikin danginta ta dinga farinciki da murna har aka yi taro aka tashi lafiya,amarya ta tare a ɗakinta cike da gara mai tarin yawan da ba a taɓa irinta a ƙauyen Kura ba. Nan fa mutane suka dinga zuzuta arziƙin iyayen Layuzah wasu ma sai suka dinga yi mata ladabi da biyayya saboda ita ɗin mace ce mai yawan kyauta da ihsani. Layuzah na yin wata biyu a gidan aure Abdulwahab ya ɗauke ta ya mayar da ita Kano,gidan da suka kama haya ya mayar da ita ta ci gaba da zuwa makarantar bokonta. Da gari ya waye suke raba aikin gidan saboda su gama da wuri. Su na gamawa sai su yi wanka su shirya ya ɗauke ta a babur ɗinsa ya kai ta makaranta ya wuce shagonsa da ya bunƙasa ƙwarai da gaske. Sosai Mudassir ya riƙe amana,haka sauran ma'aikatan wajen ma suna son ubangidansu dan baya yi musu mugunta,shi yasa su ma suke kyautata masa suke yin aiki tuƙuru da ransu da lafiyarsu. Cikin ikon Allah duk yanda mutane suka dinga surutun Layuzah bata haihu ba bai dami Abdulwahab ba. Hasali ma gode wa Allah ya dinga yi da bata samu ciki ya katse mata karatu ba. Saboda yanda mutane ke damun Layuzah da zancen haihuwa a Kura sai Abdulwahab ya dena zuwa da ita. Idan ya tashi sai ya je ya yi musu hutun ƙarshen mako ya koma. Duk wanda ya yi masa zancen haihuwa sai ya ce. "Allah bai kawo ba har yanzu tinda tasa ce shi ke bayarwa wanda ya so ya hana wanda ya so. Wanda ya ba wa kuma muna taya su murna da fatan su samu damar yi wa kyautar da Allah ya basu kyakkyawan riƙo." Halin ko in kular da yake nunawa na damun dangin mahaifansa,har meeting suka haɗa akansa amma ya je ya faɗa musu komai lokaci gare shi ya tashi ya yi tafiyarsa. Ana haka Mudassir ya ɗora idanuwansa akan wata Buzuwa da ke zuwa wajen su ta na siyan gero. Tinda Mudassir ya ɗora idonsa akanta ya ji ya kamu da ƙaunarta amma yana jin tsoron ko matar aure ce saboda yanayin yanda take shiga cikin mutunci. Ganin yanda ita ma idan ta je shagon bata gansa ba take tambayarsa ne ya sanya shi binta har gidansu a ɓoye dan ganin inda take, Sai da ya bari ta shiga sannan ya aika yaro gidan dan ya kira masa Buzuwar. Lokacin da ta fito ta ga Mudassir sai ta ce. "Wataƙila rabo ne yake kiranka. Domin kuwa daf mahaifina yake da bada ni." Ƙirji Mudassir ya dafe ya ce. "Ki ce da na yi jinkiri da an yi babu ni?" Murmushi kawai ta yi ta rufe fuskarta. Shi ɗin ma mayar mata da martanin murmushin ya yi ya ce mata. "To ya sunan masoyiyar tawa?" "Ammabuwa." "In Sha Allahu ke mallaki na ce,ke ce za ki zamo uwar yarana. Ni suna na..." "Mudassir. Kada ka yi mamakin yanda aka yi na san sunan ka." "Lallai kuwa ba zan yi mamaki ba,tinda yanzu sunan shagon namu ma na neman ya koma shagon Mudassir." Gyaɗa kai ta yi tana murmushi. A haka mahaifinta ya dawo ya tarar da su. Cike da girmamawa Mudassir ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi,shi ma cikin mutuntawa ya amsa ya shige gida. Ya na shiga Ammabuwa ta bi bayan mahaifinta ta shige gida ta na ɗaga wa Mudassir hannu. A wannan ranar Mudassir ya tunkari Abdulwahab da zancen Ammabuwa,shi kuwa babu ɓata lokaci ya sanya musu albarka,sannan ya yi masa alƙawarin kashe masa duk wani kuɗi da zai buƙata domin aurensa. Cikin lokaci ƙanƙani aka yi auren Ammabuwa da Mudassir,inda suke zaune a gida ɗaya da shi da amininsa da ya zamo masa tamkar Ɗan'uwa. Matansu sai suka zamo kamar Hassana da Hussaina,sosai Ammabuwa ke girmama Layuzah,saboda Layuzah ta girme ta da shekara ɗaya,kuma bayan haka mijin Layuzah shi ne mai arziƙin da suke raɓe suke ci ta kowacce siga ita da mijinta. Bayan watanni uku da auren Ammabuwa da Mudassir.... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 13. Bayan watanni uku da auren Ammabuwa da Mudassir ta fara laulayi mai matuƙar wahala,har sai da ya zamto ba ta iya yi wa kanta komai sai an taimaka mata. Da safe kafin Mudassir ya fita kasuwa shi yake taya ta wanka ya sauya mata kaya. Su na tafiya Layuzah za ta shiga ta kwashe kayan wankin Ammabuwa da na Yayanta ta wanke musu,ita ke dafa mata duk wani abu da take son ci sannan ta zauna ta yi mata hira. Sosai take farinciki da samun cikin da Ammabuwa ta yi,ita kuwa Ammabuwa tsoron kada ta haihu jikinta ya lalace Mudassir ya ƙara aure shi ne ya janyo mata tsanar cikin jikinta. A kullum idan Layuzah na murna ta na faɗin irin gatan da za ta bawa yaro ko yarinyar da Ammabuwa za ta haifa sai Ammabuwa ta ce. "Ni da ma ke ce kika samu cikin nan ba ni ba,domin gaskiya ba zan iya da ɗawainiyar yara ba. Ko a gidanmu ni kaɗai ce bani da wa bani da ƙani,bana son hayaniyar yara ballantana hidimarsu." Cike da sanyin murya Layuzah ta ce. "Ki gode wa Allah,domin shi kaɗai ne ke bada kyautar ɗan mutum ga wanda ya so,wannan maganganun naki sam basu dace ba." A haka suka ci gaba da zama cikin aminci da mutunta juna har cikin Ammabuwa ya cika watanni biyar a duniya. Daga nan ne maƙota masu gulma suka fara shige da fice suna ƙoƙarin raba kan Layuzah da Ammabuwa saboda ganin yanda suke zaune lafiya,Layuzah na bawa Ammabuwa girmanta a matsayinta na matar Yayanta,ita kuwa Ammabuwa na ba wa Layuzah girma a matsayinta na wadda mijinta ke kula da su da duk wata ɗawainiyarsu. Sai dai cikin hukuncin Allah babu wadda ta yi nasarar dasa musu tsanar junansu. Daga ƙarshe da Layuzah ta fuskanci masu shige da fice a gidan na neman yi musu yawa,kuma ba da alkhairi suke zuwar musu ba,sai suka fara zama a waje ɗaya a duk sanda ɗayarsu ta yi baƙuwa. Ganin haka sai mutanen unguwar suma suka fara ja da baya suka rage zuwa,ko sun zo sai dai a gaisa a tsakar gida babu mai kai su ɗakinta su tashi su tafi,sosai su Ammabuwa suka toshe duk wata kafa da za a raba kansu. Wannan abun da suka yi ya faranta ran mazajen su ƙwarai da gaske. Lokacin da cikin Ammabuwa ya kai wata takwas Abdulwahab ya sauya musu gida suka koma Ƴankaba da zama. Komawarsu Ƴankaba ya sake zuwar musu da sabon arziƙi;har sai da ta kai ta kawo Abdulwahab ya fara fitar da kayan hatsinsa zuwa ƙasashen Nijer,Ghana,da Chadi. Sosai arziƙinsa yake ta bunƙasa har ya sayi ƙaton fili a cikin garin Kanon. Har sun manta da sun miƙa takardunsu wajen neman aiki,sai gashi Abdulwahab ya samu aikin da yake buri da fata. Murna sosai Mudassir ya taya shi ya ce. "Ka ga shikenan ni sai na ci gaba da kula da ɓangaren kasuwancinmu na nan kai kuma kana zuwa aikinka na gwamnati." "Ai kuma sai abubuwan su yi maka yawa abokina,tinda aikin gwamnatin da na samu duk ya shafi harkar noma wannan kasuwancin namu ma ba zai gagare ni ba. Wataƙila idan na tura kayanmu ma sai ka ga sun samu shiga a wajen gwamnati." Haka su Abdulwahab suka dinga tattaunawa suna samawa kansu mafita akan ci gaban rayuwarsu. Watarana Abdulwahab ya samu Mudassir da shawarar yana so ya biya wa Gwaggo Kande kujerar Makka kamar yanda ya yi mata alƙawari,domin kuwa ita yake gani a matsayin iyayensa a yanzu,dan kuwa ita ce macen da ta yi masa riƙo na gaskiya da amana. Sosai Mudassir ya ƙara ba shi ƙwarin guiwar yin hakan. A tare suka je Kura suka sanar da Malam Bala ƙudirin Abdulwahab na kai Gwaggo Kande Makka,wani irin kishi,hassada da ƙyashi ne ya taso ya lulluɓe zuciyar Hasiye,ji take yi kamar ta zuga Malam Bala ya hana Kande zuwa Makka,sai dai tana ji ta na gani Malam Ya amince su Abdulwahab suka ɗakko Gwaggo Kande da Salma suka kawo su Kano. A cikin satin suka kai ta aka yi mata international passport da duk wani abu da ya dace. Su na dawowa suka tarar da Ammabuwa na naƙuɗa Layuzah na ta kuka saboda bata san da me za ta taimaka mata ba,gashi zamanin babu waya ballantana ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki. Ko ajiye hijabi Gwaggo Kande bata yi ba ta kori su Mudassir da suka rikice su na faɗin ta fito a tafi asibiti. Su na fita Gwaggo Kande ta taimaka wa Ammabuwa har ta haifi sankacecen ɗanta kyakkyawa fari tas mai kama da ita. Kukan jaririn ne ya sanar da su Mudassir Ammabuwa ta sauka ƙalau. Murna sosai suka dinga yi shi da Abdulwahab. Layuzah kuwa hamdala ta dinga yi tana maimaitawa bakinta ya ƙi rufuwa. Da yammar Gwaggo Kande ta hura wuta a murhu, nan da nan ta ɗora ruwan wanka ta wanke jariri da mahaifiyarsa. Kafin su gama shiri Abdulwahab ya je wajen mai gashin nama ya siyo nama mai yawa da madarar shanu da dabino ya kawo. Yanda ya dinga hidima da Ammabuwa da jaririnta sai ka rantse Layuzah ce ta haihu. Mudassir har kuka ya dinga yi yana ji a ransa zai iya bada rayuwarsa saboda Abdulwahab. Washegari ya je gidansu Ammabuwa ya sanar da haihuwarta, mahaifiyarta ta so ƙanwarta ta je ta kula da Ammabuwa,amma sai ya ce ai akwai mai kula da ita,domin Ammabuwa da kanta ta sanar da shi bata son kowa ya zo saboda gudun gutsiri tsoma na mutane har a yi abinda zai taɓa zumuncinta da Layuzah. Abdulwahab shi ne ya sayi ragunan suna manya guda biyu. Dan haka ranar suna Mudassir ya ce yaro ya ci sunan Abdulwahab. Sosai hakan ya yi wa Abdulwahab daɗi sai Layuzah ta ce za su dinga kiransa da Maheer. Ita dai Ammabuwa har a wannan lokacin yaron bai wani shiga ranta ba,shi yasa ko kuka yake idan Layuzah ta kawo mata shi dan ta shayar da shi,sai ta dinga kuka ta na faɗin zai mayar da ita tsohuwa. Sai da Gwaggo Kande ta yi mata wankin babban bargo sannan ta ce za ta je har gidan iyayenta ta faɗi iyashegen da take yi,sannan ta rungumi yaronta ta na bashi kulawar da ta dace duk wata uwa ta ba wa ɗanta. Bayan suna da sati biyu Gwaggo Kande ta tafi Makka,sosai Salma take taya Ammabuwa rainon Maheer. Idan aka goya mata shi bata sauke shi har sai ya yi kukan yunwa,ya na shan mama za ta ce a goya mata shi,sam bata gajiya da ɗawainiyarsa. Layuzah na matuƙar jin daɗin zama da Salma,domin yarinya ce ita mai matuƙar natsuwa da hankali tare da sanin ya kamata. Satin Gwaggo Kande biyu a Makka ta dawo cike da tsaraba mai tarin yawa. Domin kuwa duk wasu ƴan kuɗaɗen da za ta ci abinci da Abdulwahab ya bata bata saki jiki ta kashe su ba,Salma kanta sai da ta samu riguna da takalma bakwai.

Chapter 7 of 13