sa ta a gaba kina yi mata rashin ta ido? Wuce ki tafi ɗakinki."
Ko shiga ɗakin Kande bai yi ba ya wuce nashi ɗakin ya hau rage kayan jikinsa yana ƙulla mugunta a cikin ransa. A haka Hasiye ta shiga ɗakin ta na kumbura baki ita a dole fushi take yi da Malam Bala yayi mata tsawa a gaban kishiya. Zama ta yi ta na ɓata rai,sai ta ba wa Malam Bala dariya,nan ya zauna ya bata labarin gidan Malam Rabi'u. Ranta ne ya ɓaci ta ce.
"Yo me aka yi kenan Malam? Ai ni so nake ace ya yi mata fata-fata ya yayyaga ta ta yanda sai an ɗinke ta kamar ƙwarya. Gaskiya da sakel,ai ni ban yi wannan gamin dan Salma ta zauna lafiya a gidan miji ba."
Shiru suka yi na wani lokaci kowannensu na tunanin irin gadar zaren da zai haɗa wa Salma domin daƙile farincikin da take samu a gidan aurenta.
Bayan wata ɗaya Salma ta saki jiki sosai a gidan miji,Malam Rabi'u ya fara dawowa cin abincin rana a gida,wannan dalilin ne ya sa dole Samira ta rage musguna wa Salma gudun kada mijinta da Malam Rabi'u su gani. A hankali Salma ta fara cika haskenta na dawowa. Watarana har ƴar bireziyar da Samira ta rage mata guda ɗaya take ɗauka ta dinga gwadawa ta na dariya ita kaɗai a ɗaki. Fatanta bai wuce watarana itama ta shiga cikin sawun matan da ke sanya bireziya ba.
A ɓangaren girki kuwa ta ƙware sosai,domin Samira sakar mata komai take yi,sai dai ta dinga nuna mata abinda za ta yi,ita ke share sashenta ta share na Samira,wankin banɗaki da wanke-wanke dik aikinta ne. Ɗiban ruwa a rijiya ta cika randuna na daga cikin aikinta. Idan Malam Jamilu ya ga aikin ya yi wa Salma yawa ya yi magana sai Samira ta dafe ciki ta hau karairaya ta na cewa.
"Yanzu Malam me tsohon juna me za ta iya yi? Ai idan aikin ya min yawa sai na haihu lokaci bai yi ba."
Kan dole yake ƙyale ta ba dan ya so ba,tinda ai lokacin da tsohuwar matarsa na raye da cikin Tanimu babu abinda bata yi.
***********************
Yau ma kamar kowacce rana tun safe Salma ta tashi take aikin gida. Wanke-wanke ta fara yi,sannan ta yi shara,daga nan ta wanke banɗaki. Ta na gamawa ta kwashe ɗumamen tuwon da ta aza ta ɗora ruwan kunu. Lokacin da ta gama komai Malam Rabi'u har ya yi wanka yana zaune yana jiran a kai masa kayan karyawarsa. Babu jimawa Salma ta shiga ɗakinsa da babban faranti mai ɗauke da kwanon tuwo,kofin kunu da kwanon sha cike da ruwan randar sanyi. Ajiye wa ta yi ta miƙa masa butar ƙarfensa,daga nan inda yake zaune ya wanke bakinsa ya watsa ruwan waje,sannan ya miƙa hannunsa waje ya wanke ya ajiye butar. Zama ya yi ya fara cin tuwon yana santi Salma na yi masa dariya. Bayan ya kammala ya yi mata sallama tare da bata nera ɗari biyu ko da za ta sayi wani abun. Godiya ta yi masa ta karɓa ta ajiye a inda ta saba ajiye wa. Wani irin sauyi ya ke ji a jikinsa wanda bai taɓa jin irinsa ba a kaf rayuwarsa. A haka ya daure ya fita waje yana jiran Yayansa. Ko da Malam Jamilu ya riski ɗan'uwansa a zaure sai ya ce.
"Lafiya kake kuwa yau Rabi'u?"
Murmushi ya yi kawai ya gyaɗa kai alamar lafiya yake. Ba tare da sun sake yin magana ba suka hau samam babur ɗaya Malam Rabi'u na tuƙawa suka wuce kasuwa.
Tinda suka tafi kasuwa Mairo ta zo gidan suka ƙule da Samira a ɗaki,sun jima sosai a ciki kafin Samira ta fito cikin shirin fita. Ko sallama basu yi wa Salma ba dake ta shaƙar ɓaccin gajiya a zaune. Bayan awa biyu da fitar Samira Malam Rabi'u wanda ya kasa zama a kasuwa ya dawo gida. Hankalinsa a tashe ya nufi ɗakin Salma. A kishingiɗe ya ganta tana baccin gajiya. Bai ɓata lokaci ba ya tura ƙofar ɗakin ya saka sakata sannan ya nufi Salma gadan-gadan...........
*Wacece Aabida da Innaji?*
*Ta yaya Aabida ke shiga rayuwar Aabid har su zamo ma'aurata?*
*Wacece Dijahn Aabid?*
*A tsakanin Aabida,Innaji,Hasiye da Samira wacece asalin MUGUWAR MACE?*
*Ya ƙarshen waɗannan mutane zai kare?*
*A cikin MUGUWAR MACE PART 2 ne kawai za ku samu amsar tambayoyinku.*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 13