Share this page
9 / 13
ta yi mata wanka tsaf suka fito. Sosai Ammabuwa ta dinga mamakin yanda Layuzah ta jure ruwan zafi bata yi raki ba kamar yanda ita ta yi a lokacinta. Gari na wayewa Abdulwahab ya aika Sallau can Kura ya taho da Gwaggo Kande. Da zuwanta ta karɓi aikin kula da wankan yaro da kuma Layuzah'n kanta. Bayan suna Salma ta gama jarabawarta Malam Sallau ya je ya ɗakkota ya kawo ta gidan. Sosai ta dinga murnar ganin yaron. Bacci,wanka,sallah da cin abinci ne kawai ke raba ta da Aabid idan ta ɗauke shi. Lokacin da Gwaggo Kande ta zo komawa sai Salma ta kafe ba za ta bi ta ba har sai sakamakon jarabawarsu ya fito sannan za ta koma. Kan dole Gwaggo Kande ta koma ba tare da Salma ba. Ta na isa gidan bayan ta huta Malam Bala ya same ta har ɗaki riƙe da kwalin chewing gum,minti da goro yana washe baki. Cikin rashin fahimta Gwaggo Kande da ke ƙarasa ninke zanin kayan da ta cire a jikinta ta ce. "Ah ah! Malam wannan kuma fa? Ko dai Mairo aka yi wa baiko da bana nan?" Washe baki Malam Bala ya sake yi sannan ya ce. "In banda abinki Kande nawa Mairon take? Ai yayarta aka ɗaurawa aure ɗazu a masallacin Juma'a. Liman har ma da manyan garin nan duk sun shaida kuma sun saka wa abun albarka." Mamakin kalaman Malam Bala ne suka sanya Kande zama a bakin gadonta ta karɓi abubuwan da yake miƙa mata ta ajiye a gefenta sannan ta ce. "Malam ka na ta yi min magana a duƙunƙune,dan Allah ka fito fili ka yi min bayani,domin ni dai a iya sani na Samira ce kawai ta girmi Mairo a gidan nan;kuma an yi mata aure. To wacece kuma Yayar Mairo da aka aurar babu baiko balle saka rana?" "Ke dai ba kya cin ribar zance Kande. To auren Salma ta wajenki aka ɗaura yau a masallacin Juma'a da Rabi'u ƙanin mijin Samira." Wani irin faɗuwar gaba da tashin hankali ne ya dirarwa Gwaggo Kande wanda ya sanya ta jin jiri na ɗibanta daga wajen da take zaune. Cike da tashin hankali ta kalli Malam Bala ta ce.......... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 15. Cikin tsananin ɓacin rai Gwaggo Kande ta kalli Malam Bala ta ce. "Lallai kuwa za ka je duk masallaci ko ƙofar gidan da aka ɗaura wannan ƙaddararran auren a kunce shi;dan ba zan taɓa amincewa a cuci yarinya ƙarama a aura mata tsoho kamar Malam Rabi'u ba." Tsayuwa Malam Bala ya gyara ya ce. "Kayya! Kande wai dika-dika Malam Rabi'un nawa yake? Ƙanin ƙanin bayana ne fa." A hasale Kande ta ce. "Mutumin da ko za ka girme shi bai wuce ka bashi shekara uku zuwa huɗu ba shi ne yaron? Kada fa ka manta Salma bata wuce shekara sha biyu zuwa sha uku ba." Cikin sauri Malam Bala ya ɗaga wa Kande hannu ya ce. "To kin ga kenan ta yi gadon ki. Ai idan ban manta ba kema da waɗannan ƙananan shekarun aka aura min ke." "Malam wancan zamanin da wannan da muke ciki akwai banbanci,sannan kuma lokacin da muka yi auren ina da ƙananan shekaru ai kai ma ba wani babba bane." "Banbancin na menene Kande? Tuwon hatsin aka dena ci ko kuwa shinkafar? Ko kuma kwanciyar sunnar aka canja? Matan ne suka koma na gwal ko me? Bayan haka Kande indai da kara ba karaya ba ni ai uba nake a wajen Salma,a zato na zan iya zartar da komai a kanta. Dama Hasiye ta faɗa min idan kika dawo sai kin yi tijara na karyata ta saboda na sanki da biyayya. Ashe ta sauya zani ban sani ba." "Malam babu zanin da ta sauya,har gobe da jibi ina nan a Kanden da ka sani mai yi maka biyayya akan dikkan umarninka matsawar bai saɓawa Allah ba. Amma wannan abinda ka yi ba zan taɓa yi maka biyayya akansa ba ballantana kara,yanda ka je aka ɗaura aren nan babu sanin dangin uwa da uban yarinya dole ka je a warware." A hasale Malam Bala ya tsaya a gaban Kande ya na zazzaro mata ido waje ya ce. "Ke ba na son shashanci fa. Wa ya faɗa miki dangin uwa da uba basu sani ba. A gaban kawunanta, Sarkin garin nan liman da duk wani mai faɗa a ji na ƙauyen nan aka ɗaura,kada ki so ki ga yanda akai ta saka miki albarka da ita kanta yarinya,ko babu komai kun yi taimakon musulunci " "Ka ce haka mana Malam tinda an ɗaura wa yarinya aure da tuzuru. Ina son ka sani duk wani mummunan abinda ya sami Salma ba zan zauna da kai ba na gama auren ka kenan Malam. Habaa ta ya za a yi wa yarinya aure sai kace wata ƴar tsana? Idan gaskiya ne abun naka ai ka na da wata ƴar ka bashi mana,sai a haɗa ta da ƴar'uwarta gida ɗaya su yi zaman aure,amma ba wai a ɗauki marainiya a kai ta gidan da na san da biyu ka ƙulla auren dan kawai a cutar min da ita ne." Ta na gama maganarta ta fito waje fuuuu cike da fushi. Karo ta yi da Hasiye da ke yi musu laɓe ta na jin duk abinda suka yi magana akai. Cike da borin kunya Hasiye ta tsugunna tana ɗaukan duk abinda hannuwanta suka hau kai. Murmushin takaici Kande ta yi ta ce mata. "Na dawo na ga tuggu da munafurcin da kika ƙulla Hasiye,dan kuwa na sani sarai ke ce za ki zuga Malam ya yanke wannan mummunan matakin akan Salma. Ina so ki sani da yardar Allah Salma za ta ba ki mamaki. Sai kin yi nadamar wannan haɗin auren da kika yi ko ba jima,ko ba dade." Harara Hasiye ta banka wa Kande ta tsirtar da yawu sannan ta ce. "Eh ɗin ni ce nan matar da ta isa da miji da gida,uwar magada mai mulkin gidan Malam Bala. Har ke kin isa Ƴata ta nuna tana son auren jikanki ki hana ta? To bari ki ji Samira ba ta yi auren tsoho a banza ba,kema dole ne taki jikar ta je can ta ɗanɗani zama da sa'an ubanta. " "Ba kanta farau ba Hasiye,kuma na tabbata ba za a gama akanta ba,dan ta auri tsoho ba shi ne yake nufin ƙarewar numfashinta ba. Kuma ina so ki dinga tinawa da mugunta dai fitsarin fako ce,kuma idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere." Haka su Kande su ka dinga musayar yawu ita da Hasiye har ta ga rashin dacewar biye mata su yi ta hayaniya. Ɗaki ta shiga ta killace tsarabar da ta zo da ita ta zari mayafinta ta saka ta kulle ƙofarta ta nufi gidan Kawu sale. Ta na zuwa ta dinga doka sallama a tsakar gida domin ko ɗaki bata jin za ta iya shiga. Yanda suka haɗa kai da Malam Bala aka aurar da Salma ba da saninta ba dole ne su je duk inda za su je a warware wannan auren. Ta na nan tsaye Kawu Sale ya fito ya na suɗe hannu tare da haɗe su waje ɗaya ya murtsuke. Washe baki ya yi yana kallon Kande ya ce. "Ah ah Gwaggo yau ke ce a gidan namu war haka?" Harara ta banka masa sannan ta ce. "Da abinda ya fi war haka ma za ka ganni Sale,tinda baku ƙulla gaskiya ba da kai da wancan azzalumin. Yanzu Sale amanar da aka bar mana ita kuka wulaƙanta? Ina laifin ku aura wa Salma matashi wanda ƙarfinsu zai yi ɗaya, kurum sai ku aura mata sa'an ubanta?" Tsayuwa Kawu Sale ya gyara sannan ya tsotse haƙorinsa ya ce. "Don Allah Gwaggo Kande ki yi haƙuri da abinda ya faru. Matsala aka samu gagaruma . Wato auren Malam Rabi'u aka fasa saboda yarinyar da zai aura iyayenta sun ji labarin Yayansa dika yara mata yake haifa,kuma yaran ne ke zuwa masa gona su yi duk abinda yaro namiji zai yi,watarana ma har marigayiyar matarsa yake ɗauka ya kai ta gona su yi aiki su dawo. A taƙaice dai sun ji ƙishin-ƙishin ɗin aikin gona da na gida ne ya yi ajalin matar wansa. To shi ne fa Malam Rabi'u da be taɓa aure ba hankalinsa ya tashi da jin wannan mummunan labari sai ya yanke jiki ya faɗi. Da ƙyar aka zuba masa ruwa ya farfaɗo aka kai shi can asibiti aka saka mas ruwa. Ni dai ban san ya aka yi ba bayan kwana biyu an tashi sallar Juma'a sai ga Malam Bala ya zo muna tare da Sarki a idar da sallah ya ce wa Malam Rabi'u ya bashi ƴarsa Salma ya aura idan yana so." "Shine kuka amince ba tare da yin tunanin zaluntar yarinya marainiya da ake son a yi ba ko?" Kai Kawu Sale ya sosa ya na faɗin. "A yi haƙuri Gwaggo ƙaddara dai ta riga fata yanzu." "Humm Allah Ya kyauta,gobe da sassafe zan koma Kano na sanar da ɗan'uwanta duk abinda kuka ƙulla." Gaban Kawu Sale ne ya faɗi,nan take nadamar ƙin hana auren Salma da Malam Rabi'u ta kama shi. Sai dai ya baro gini tin ran zane. Kande gida ta koma ta na matsar hawaye tare da hango irin tarin kalubalen da Salma za ta fuskanta a cikin wannan auren. A haka ta kwana da zullumi da fargaba. Washegari da safe ta shirya tsaf da nufin tafiya Kano ta sanar da Abdulwahab abinda yake faruwa. Sai dai lokacin da ta je ta sanar da Malam tana neman izininsa na zuwa Kano sai ya ce. "Babu inda za ki je ki hure wa yarinya kunne ta bijire wa mijinta. Nan da jibi Hasiye da matar Sale za su je su yi barka sannan su taho da ita." Hawayen da Kande ke ta riƙewa kada su zuba a gaban maƙiyinta Malam Bala ne suka zubo mata. A daren jiya ta raɗa masa sunan maƙiyi,domin kuwa babu wanda zai aitaka abinda Malam Bala ya aikata a kira shi da masoyi. Ba dan ta so ba dole ta haƙura ta bar ɗakin nasa ta koma ɗakinta ta na sharar hawayen takaici. A kan idonta Hasiye ta dinga rawar kan zuwa Kano. Tin da safe ta tsefe kanta ta je aka rangaɗa mata sabon kitso,sai kuma ta ɗaura jan lalle a ƙafarta da dare. Gari na wayewa Hasiye ta sheƙa wanka ta saka atamparta sabuwa da suka ci bikin Suwaiba da ita ta fito ta na kallon kanta a ƙaramin madubin hannu ta na gyara zaman mayafinta a kafaɗarta. Washe baki Malam Bala ya yi ya ce. "Har an fito kenan?" "Allah Ya yarda Malam. Tinda a yau za mu je mu dawo a yau,ai gwanda mu gaggauta mu yi abinda ya kamata." "Haka ne Hasiyatu matar fir'auna,waii matar Malam Bala. Kin ga kyan da kika yi har ya ruɗa ni zan sauya miki sunan miji. To ga wannan a yi na mota ko?" Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin mota ya bata yana dariyar samun nasara. Har cikin ransa yake jin daɗin rama wulaƙancin da Abdulwahab ya yi masa na ƙin auren Samira. Sosai ya yaba da shawarar da Hasiye ta bashi na aura wa Malam Rabi'u Salma dan yin ramuwar gayya. Ɗaki ya koma kai tsaye ya zauna ya fara karya wa. A tasha su Hasiye suka haɗu da matar kawu Sale. Gaisawa suka yi da juna suka samu mota suka shige. A mota banda zuzuta gidan da su Abdulwahab suke a Kanon babu abinda Hasiye take yi,ita a dole ta san kan waje Matar Kawu Sale bata sani ba. Haka suka dinga hira har suka isa garin Kano. Su na isa suka sauka daga mota suka samu taxi suka shiga. Da kwatance motar ta kai su har gidan Abdulwahab. Su na zuwa suka hau buga ƙofa suna faɗin. "Ohh mutanen birni,su fa yanzu bacci suke yi ko?" Hannu Hasiye ta sa ta sake buga gidan da ƙarfi. Su na nan tsaye wani ƙaton mutum ya buɗe gidan jikinsa ko riga babu ya kalle su ya na muzurai ya ce. "Kai ku su wanene kuke damun mutane?" Yawu Hasiye ta haɗiya a tsorace ta ce. "Wajen Jikana Abdulwahabu muka zo." "Waye me wannan sunan kuma? Malama ku ware daga nan nan gidana ne ni ban san wani Abdulwahab ba." Ƙirji Hasiye ta dafe ta ce. "Kai ɗannan don Allah kada ka yi mana wasa..." A hasale mutumin ya zabura ya ce. "Na yi miki kama da abokin wasanki ne?" Kai Hasiye ta girgiza ta ja hannun Balaraba Matar Kawu Sale suka fara tafiya. Cike da tsananin damuwa Balaraba ta ce. "To ke da Hasiye kin san baki san gida ba kika rakito mu muka taho ?" Kai Hasiye ta karkace ta ce. "Aradun Allah wannan ne gidan. Bayan Abdulwahab ya kama haya a Kano sun dawo shi da matarsa na biyo Kande da za ta kawo musu ziyara. Tin daga nan ko shigowa na yi siyayya sai na biyo na ci na sha na yi warkajami na da abun duniya nake wucewa gida." "To da dikkan alamu sun canja gida,ko kuma wani abu ya sami Abdulwahab ɗin amma Gwaggo Kande bata sanar da kowa ba." "Idan ina faɗa muku muguwa ce sai ku dinga ganin laifina,to ai gashi yanzu ta baku misali." Haka suka ɗauki laifi suka ɗora akan Gwaggo Kande gaba ɗaya. Daga ƙarshe sai suka dinga bi gida-gida suna tambayar inda za su samu gidan Abdulwahab amma basu samu ba. Ganin lokaci ya tafi bar an yi azahar basu dace ba,sai kawai suka yanke shawarar komawa Kura idan Kande ta sanar da su sabon gidan Abdulwahab ɗin sun dawo.... *Ku yi haƙuri bani da caji ne shi yasa kuka ji ni shiru.* MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 16. A matuƙar gajiye su Hasiye suka isa gidan Malam Bala da ke ta zarya a tsakanin cikin gidan da ƙofar gidan Malam Rabi'u dan ganin dawowarsu. Bai jima da fita ba ya dawo ya tarar da Hasiye zube a tsakar gida ita da Balaraba wadda ta kasa ƙarasawa gidanta ta ce sai ta huta ko zuwa dare ne; tinda ba ita ke da girki ba yara sun raka ta. Fuskar Malam Bala ɗauke da mamaki ya hau leƙen ƙofar ɗakin Kande ko zai hango takalman Salma amma ya ga wayam. Kallon Hasiye ya yi ya ce. "Mutanen Kano an shawo rana,ke Mairo je ki kawo musu farau-farau mana,da dikkan alamu sun yi aswaki da kaji a birni." Tsaki Hasiye ta ja tana zabga wa Malam Bala harara. Bakinta da ya bushe ta lashe da harshenta da ya ƙafe babu ɗigon yawu a jiki ta ce. "Ai idan bamu ci kaji ba mun ci uwar wahala. A gaskiya Malam Baƙin halin Kande ya munana babu na biyun ta a mugun hali a kaf cikin ƙauyen nan namu da kewaye." Waje Malam Bala ya samu ya rakuɓe a jikin gini ya na kallon Hasiye da ta amshe kwanon shan ruwa a hannun Shamsiyya ƙaramar ƴarta ta kwankwaɗe ko kurɓa daya bata rage ba. Tana sauke numfarfashi ta ce. "Wai ka san kuwa yaron nan Abdulwahabu ba ya gidansa da na sani amma bata damu ta sanar da mu ba;duk da cewa ta san can za mu je mu taho da matar mutane?" Ido Malam Bala ya zaro waje ya dafe ƙirji sannan ya ce. "Ki bari dan manzo Hasiye! Wai ki na nufin Abdulwahabu ya sauya muhalli daga wanda muka sani? Ki ce arziƙi ya ci uban na da. Ohhh yanzu fa da shikenan Samira ce a gidan take ta dandalar arziƙi." "Hummm ai Kande ba macen da za a raɓa a dandali arziƙi bace Malam,ta nuna maka iyakar ka. Yau in da ka ga azabar tafiyar da muka ci da ƙafafuwan nan namu sai ka tausaya mana. Wani ƙato ma ce wa ya yi idan bamu bar ƙofar gidan ba zai lakaɗa mana na jaki,kan dole mu kai ta zagaya unguwar har maƙotan unguwannin da basu da nisa muna tambayar gidan Abdulwahab mai siyar da hatsi,amma bamu samu ba. Yanzu don Allah Malam dubi yanda ƙafar Balaraba ta yi haushi kamar ta me tsohon ciki." Sannu suka dinga jera wa Balaraba da ke ta kurɓar farau-farau. Kande kuwa ta na ɗaki ta na jin su bata tanka musu ba har aka kira sallar magariba ta fito dan yin alwala. Ko kallon inda suke bata yi ba ta ɗauki butar ta ta zaga. Ta na fitowa ta hau yin alwala ba tare da ta kalli inda suke ba,Malam Bala ne ya isa wajenta a hasale kamar zai kifa. Cike da matsanancin fushi ya warce butar ya yi wurgi da ita ya ce. "Wato ma kin mayar da mutane mahaukata ko? Ki na fa kallo da jin abinda ke faruwa a gidan nan,amma ko sannu ba za ki iya buɗe baki ki yi wa bayin Allah'n nan ba da suka tafi ɗakko Salma dan a kaita gidan miji ta raya sunnar ma'aiki." Shiru Kande ta yi bata tanka masa ba ta miƙe daga tsugunnon da ta yi ta ɗakko butarta ta wanke ta sake zuba wani ruwan ta hau yin alwala. Ƙwafa Malam Bala ya yi ya ce. "To ki buɗe kunnen ki da kyau ki jini. Zan je wajen yaransa da ke kai masa kaya Kanon da kaina mu je har shagonsa,ni da kai na zan je na taho da Salma idan zuciya za ki haɗiya sai ki yi magana a baki ruwa ki kora." Murmushin takaici kawai Kande ta saki ta miƙe tsaye ta wuce ɗakinta. Ta na shiga hawaye ya zubo mata,nan da nan ta hau tuna irin rayuwar da suka yi da mijinta a baya. Rayuwa ce mai cike da so,ƙauna,tattali,kulawa da mutunta juna. Duk wani abu da zai ɓata mata rai baya son sa. Da yardarta da amincewarta ya auri Hasiye saboda ita bata taɓa haihuwa ba. Sai gashi tinda aka auro ta bata huta ba daidai da rana ɗaya. Gashi yanzu tsufa ya cimmata har ta dena al'ada ballantana ta sanya ran haihuwa. Zama ta yi a bakin gadonta ta rushe da kuka mai cin rai saboda ta tabbatar da cewa wani makircin da muguntar Hasiye ke ƙullawa ƙaramar yarinya kuma marainiya Salma. Gani ta yi kukan ba zai kai ta ko ina ba lokacin sallah na wuce wa. Sai kawai ta miƙe ta nufi saman abun sallarta ta gabatar da sallar magariba ta zauna tana ta addu'o'inta. A can tsakar gida kuwa Balaraba da ta gama cin tuwon dare sai ta miƙe ta na ɗingisa ƙafa ta ce. "Bari na je na gaida Gwaggo Kande tinda na huta." A bakin ƙofa ta coge ta ɗage labule ta ce. "Barka da war haka Gwaggo,mun same ku lafiya?" Ba tare da Gwaggo ta nuna mata halin da take ciki ba ta saki ranta ta amsa mata,su na gama gaisawa Balaraba ta ce. "To ni na tafi sai da safe. Allah Ya sanya alheri ya ba su zaman lafiya. Idan amarya ta iso mun zo da su Tsahare da yaran." "Uhumm Allah Ya kaimu to." Gwaggo Kande ta faɗa ta na tunanin shin ita ce ƴar'uwarsu Kawu Sale ko kuma Hasiye da Malam Bala ne ƴan'uwansu? Ta na wannan tunanin ta ji yaran Hasiye sun tafi raka Balaraba da kwanon tuwo a hannunsu, wanda Mairo ce ta dafa ta zuba wa kowa nasa. Kallon inda aka ajiye mata nata ta yi sai ta ji ko sha'awar ci bata yi,tin safe farau-farau kawai take kurɓa saboda ɓacin rai. A haka Gwaggo Kande ta kwana cike da damuwa har safiya bata rintsa ba. Da sassafe ta ji Malam Bala na yi wa Hasiye sallama ko ta ƙofar ɗakinta bai bi ba ballantana ya san ya ta kwana ya fice ya bar gidan. Kai tsaye babbar kasuwar Kura ya nufa inda ake ta hada-hadar loda hatsi a manyan motoci. Yaran Abdulwahab ya nema suka gaisa ya ce shi ma can wajen nasa ai ya nufa shi ne ya ce bari ya zo a rage masa hanya. Sanin matsayinsa a wajen Gwaggo Kande ne ya sanya su amincewa bayan sun gama lodi suka ɗauke shi a saman mota suka tafi da shi. Su na isa Kano suka nufi Ƴankaba domin sauke wa Abdulwahab kayansa. Su na zuwa suka tarar da yaran shago na ta shara tare da ba da space domin kayan da za a kawo. Da taimakon matasan wajen Malam Bala ya diro daga saman motar ya ƙarasa gaban shagon Abdulwahab yana gaisawa da mutanen wajen. Malam Sallau ne ya sanar da shi cewa ai Abdulwahab bai iso ba sai rana ko yamma yake shigowa kasuwa. Malam Mudan ne kawai ke zuwa da safe amma kuma shi ɗin ma bai iso ba. Da sauri Malam Bala ya ce. "Ni da da yanda za a yi a kai ni can gidan nasa ma ai da kun kyauta. Dama rashin sanin muhallin da ya koma ne ya sa na biyo ta nan." "Ah bari to na jawo babur na kai ka gidan yanzun nan.' Albarka Malam Bala ya dinga sanya wa Malam Sallau. Malam Sallau na jawo babur ya buga shi ya ce wa Malam Bala. "Bismillah Baba mu je." Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidan Abdulwahab wanda ke tsaka da shirin fita office. Sallama Malam Sallau ya rafka sau uku,a na huɗun Mudassir ya fito ya na faɗin. "Man Sallau kai ne a gidan namu war haka?" Hannu Malam Sallau ya miƙa masa suka hau gaisawa,sannan Mudassir ya durƙusa ya gaida Malam Bala. Cike da fara'a ya ce. "Shigo ciki mana Baba,ka tsaya daga waje? Aboki na ciki ya na shirin tafiya aiki,bari na sanar da shi zuwanka." Sallama Malam Sallau ya yi musu ya koma kasuwa. Su na shiga ciki ya nufi parlourn da suke ajiye baƙi zai buɗe masa kenan Salma ta fito daga ɗakin Layuzah bayanta goye da Aabid. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa har bata san sanda ta furta kalmar. "Wayyo Allah na shiga uku." Ba. Washe baki Malam Bala ya yi kamar bai ji ta ba ya ce. "Lallai ne Salma zaman birni ya karɓe ki ƙwarai da gaske. Kin ga yanda kika murje kika ƙara kyau da girma kuwa? Kwanto min yaron na gansa." Jiki a mace Salma ta isa gaban Malam Bala ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi. Amsa wa ya yi cikin sakin fuska ya karɓi Aabid da ya fara kuka,sama Malam Bala ya wurga shi yana masa tawai kafin ya miƙa wa Salma yaron ya shige parlourn da aka buɗe dominsa. Ya na shiga ya kama baki ya na faɗin. "Inyeee! wato bayan wancan gidan da suka shaƙe da kayan alatu suka barwa aljanu suna dabdalarsu a ciki a can ƙauye,nan ɗin ma sai da suka cika shi da dukiya. Lallai yaron nan ba ƙaramin baƙinciki ya yi mana ba. Yanzu da Samira ce a gidan nan ai mu da talauci sai dai mu hango shi a maƙota." Zama ya yi a kujera ya ji ya lotsa saboda laushi,sai ya sake miƙe wa tsaye ya zauna da ɗan ƙarfi kamar wani ƙaramin yaro. Ya na nan yana zancen zuci da na fili Abdulwahab ya shigo parlourn cikin shirin fita office. Gaisawa suka yi cike da girmamawa sannan Abdulwahab ya ƙwala wa Salma kira ya ce a kawo musu abun karyawa shi da Malam Bala. Layuzah ce ta yi sallama riƙe da babban faranti ta shiga ta ajiye a tsakiyarsu sannan ta koma gefe ta tsugunna. Gaida Malam Bala ta yi tare da tambayar mutanen gida. Nan ya dinga shirga ƙarya ya na faɗa musu yanda Kande ta yi kewarsu har ta tashi da zazzaɓi ta na ta cewa a kawo mata Salma amanarta,shi yasa ya yi mata alƙawarin zuwa ya tafi da Salmar. Cike da tausayawa Layuzah ta tambayi jikin Gwaggo Kanden,Malam Ya ce da sauƙi,ya dai kula kawai kewar Salma ke damunta,da an kai mata Salma za ta ware,fatan samun sauƙi Layuzah da Abdulwahab suka yi mata ta miƙe ta fita ta basu waje. Abdulwahab da kansa ya buɗe food flask ɗin masa ya zuba wa Malam Bala,sannan ya ɗauki kwanon miya ya zuba masa miyar gyaɗa da ta ji naman rago. Kunun gyaɗa Abdulwahab ya zuba masa a babban mazubi sannan ya saka madara da sugar mai yawa ya juya masa ya ajiye masa a gabansa. Yawun Malam Bala kamar zai zubo haka ya dinga magana yawun na tsartuwa. Babu ko bismillah ya danna hannu ya hau ci yana zuba surutu, a cikin surutun nasa ne yake sanar da Abdulwahab zai wuce da Salma gida idan ya bada izini. Ba tare da Abdulwahab ya kawo komai a ransa ba ya ce. "Babu damuwa Baba,ai dama ko randa za ta tafi ta so ƙwarai

Chapter 9 of 13