Share this page
3 / 13
Mahreen ta farka ta shiga banɗaki,brush ta yi ta ɗaura alwala ta fito ta tada nafila. Tana idarwa Yah Maheer yayi shirin masallaci ya tafi. Bayan ta yi sallar asuba ta shiga kitchen ta fara haɗa musu abun karyawa,tana tsaka da aiki Salimah ta shiga ta hau taya ta,nan da nan suka kammala soya doya da ƙwai tare da dama kunun gyaɗa,sai suka gyara gidan. Ta so ta zuba musu anan su ci dika,sai Salimah ta ce. "Hajiya ta ce na sanar dake,daga yau idan kin yi abinci a dinga kai mana namu can." "Ohhh Hajiya,to Yah Maheer ɗin baƙonta ne?" Murmushi kawai Salimah ta yi wanda ya sanya Mahreen ƙure ta da ido tana murmushi,a hankali ta ce. "Kamanninki da Addah Dijah sai suka bayyana da kika yi murmushin nan." Ƙwalla ce ta taru a idon Salimah ta miƙe da sauri ta bar sashen. Kai Mahreen ta dafe ta na jin babu daɗi a cikin ranta da ta tuna wa Salimah abinda ita kanta yana damun zuciyarta ballantana Salimah da ta fi ta kusanci da Dijah. Jiki a sanyaye ta kwashe abincin da ta zuba ta kai ɗakin Hajiyar. Rashin ganin Salimah a wajen da kuma ƙarar ruwa da ta jiyo a banɗakin ne ya tabbatar mata da wanka take yi,sai kawai ta zauna ta gaishe da Hajiya ta zuba mata abici ta kai mata gabanta. Godiya Hajiya ta yi mata tare da sanya musu albarka sannan ta ja kunun gyaɗar ta hau sha. Yah Maheer na dawowa daga masallaci ɗakinsu ya shige ya hau rama baccin da bai samu ba a daren Jiya. Mahreen kuwa ta so ta zauna su yi hira da Hajiya a haka har ta bigi cikinta ta sanar da ita dalilin dawowarsu nan da zama,amma Hajiya ta kora ta wajen mijinta,kan dole ta tafi ba dan taso ba. ************************* A ɓangaren Aabid kuwa tunda ya siyar da gidansu na gado aka tura wa Aabida kuɗin ta account ɗinta kai tsaye ya samu sauƙin matsin lambar da take yi masa. Wata iriyar soyayya take zuba masa wadda yake jin sa kamar shi kaɗai ne yayi dace da sa'ar macen aure a duniya. A ɓangaren ɗaya kuma kullum da tunanin halin da Hajiyansa take ciki zuciyarsa ke kwana ta tashi,sai dai duk da damuwar da yayi da lamarin baya marmarin zuwa ya ga halin da take ciki ballantana ya san a ina take kuma a wanne hali take. Bayan sati biyu Aabida ta kammala zuba kayan da ta yo order daga ƙasashen waje a sabuwar plazar da ta siya,da kanta ta jagoranci ma'aikatanta suka zuba kayanta da take siyarwa tana ta posting a social media tare da sanar da ƙawayenta Alhajinta ne yayi mata kyautar wajen. Aabid kuwa idan ya ga posting ɗin da ta yi sai ya tsaya yana kallon wajen yana tunani kala-kala a cikin ransa. Yau ma kamar ko da yaushe tun da asuba da Aabid ya farka bai koma bacci ba. Abun karyawa yayi musu sannan ya haɗa wa gimbiyar tashi ruwan wanka mai cike da kayan gyaran jiki kamar yanda take so. Sai da ya tabbatar komai yayi daidai yanda take so sannan ya haura sama ya taso ta. Miƙa ta yi tana hamma tare da yamutsa fuska kamar wadda ta ga kashi. Da kallo Aabid yake binta yana jin wata iriyar soyayyarta zazzafa na ƙara huda kowanne sashe na jikinsa. Kallon Aabid ta yi daga sama har ƙasa ta ɗaure fuska ta ce.......... MUGUWAR MACE. NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 5. "Wai ni don Allah Aabii ban hana ka tashi na kana tsamin dauɗa ba? Ka wuce ka je ka yi wanka bana son ƙazanta." Yawu Aabid ya haɗiya yana kallon kansa a madubin da ya mamaye ɗakin ta ko ina,a hankali ya sunsuna kansa ya kalle ta ya ce. "Sai da fa na yi wanka kuma..." "Don Allah dakata min bana son surutu,idan ka ga dama kada ka yi wankan ka zauna da dauɗa ba abinda ya dame ni bane. Ka haɗa min ruwan wankan?" Da sauri ya gyaɗa kai ya ce. "Na gama komai,sai dai yau ina so na fita da wuri akwai kayan da za a kawo daga Kura,ina so a sauke su akan idona." Taɓe baki ta yi sannan ta ce. "Duk saurin ka dai ka san ba za ka fita ba sai na gama abinda nake yi na fita,dan haka ka je ka jira ni." "Amma ina za ki je da safe? Ko yanzu da safe za ki dinga buɗe plaza ɗin?" "Yaushe muka fara ƴar tinke a tsakanin mu Aabii? Ko kuwa dan zan je na ga Innaji dole sai na faɗa maka inda zan je? Ka ga matsa ni bani da energy ɗin surutu da safen nan." Ya so ya sanar da ita muhimmancin fitarsa da wuri,amma rashin ganin fuska ne ya sanya shi komawa parlour ya zauna yana duba wayarsa. Ba tare da tunanin komai ba ya danna kiran Maheer. Wayar ta jima tana ringing kafin Yah Maheer ya amsa. Cikin yin ƙasa da murya Aabid ya ce. "Don Allah Ɗan'uwa ka je office da wuri a sauke kayan nan akan idonka. Ina da ɗan wani uziri ba zan samu damar fitowa da wuri ba." Takaici ne ya mamaye zuciyar Maheer har bai san sanda ya ce. 'Aabid kana da hankali kuwa?  Wai me yasa kai rayuwar duniya kawai ka saka a gaba kana mantawa da cewa watarana za mu mutu mu je lahira mu girbi abinda muka shuka?' "Me ya faru kake yi min waɗannan maganganun Maheer? Na aikata maka wani kuskuren ne ko saɓon Allah ka kama ni ina aikatawa?" Cike da takaici Maheer ya haɗiye yawu ya ce. 'Shikenan zan je office da wuri,sai anjima. Allah Ya ganar da kai gaskiya.' Jujjuya wayar Aabid yayi a hannunsa yana mamakin kalaman Maheer. Taɓe baki yayi sannan ya shiga ɗakinsa ya sake yin wanka kamar yanda Aabida ta buƙata. Shadda gezna ya sanya ash color ya ɗauki hular da ta dace da kayan ya sanya. Gaban madubi ya tsaya ya hau ɓarin turare tare da buɗe wajen da yake ajiye agogo ya ɗauki wanda ya dace da kayansa ya sanya a tsintsiyar hannunsa. Kallon kansa ya tsaya yi a madubi ya na shafa dogon gemunsa da ke ƙarawa kyakkyawar fuskarsa kyau. Taku ya sake yi zuwa gaban wata ƙofar glass ya buɗe ta,takalma ne kala-kala masu kyau da tsada. Babu ɓata lokaci ya cire na ƙafarsa ya sanya wanda ya dace da adonsa sannan ya rufe wajen ya fita zuwa parlour. Ko da ya isa  dinning room bai ga Aabida ba kamar yanda yayi tsammani. Waje ya samu ya zauna yana jiranta. Ta na fitowa ya hau serving ɗinta abinci ya na kallon kwalliyar da ta yi kamar mai shirin zuwa gasar zaɓen sarauniyar kyau. Ido suka haɗa ya sakar mata murmushi tare da faɗin. "A gaskiya dole na gode wa Allah da ya bani ke a matsayin matar aure na. A koda yaushe kika saka sutura kyau kike yi mata kamar domin ke aka yi ta. Idan kuwa kika saka kwalli sai idanuwanki su dinga fitar da wani haske da sheƙi mai ban sha'awa. Ba dan kar na yi ƙarya ba zan iya cewa duk duniya babu macen da ta kai ki kyau." Wani irin ƙayataccen murmushi ta yi wanda yake nuna tsantsar jin daɗin yabon da ta samu daga wajen mijin nata. Sai da ta ɗebi abinci za ta kai bakinta sannan ta yi fari da idanuwanta ta ce masa. "Ai idan ka yi ƙaryar ma ba laifi bane,domin a soyayya komai ka yi daidai ne kuma ya halatta." Da haka Aabid ya zauna a gaban Aabidah ya na kashe ta da kallon ƙauna har sai da ta kammala cin abincinta sannan ta saɓi jakarta da wayoyinta tare da makullin motarta za ta fita. Gani yayi yau ko arziƙin yafa siririn mayafin da take yi a saman kanta bata yi ba sai ta saƙala shi a hannunta irin yanda ƴammata ke yi,kamar zai ƙyale ta sai ya ji ya kasa,wani irin matsanancin kishinta yake ji kamar ya ɓoye ta daga idanun duniya. Gyaran murya yayi ya na kallonta kamar mai jin tsoron yin magana ya ce. "Amma Baby a haka za ki fita yau ko abun tatar kokon ba za ki yafa a saman kanki ba sai a hannu za ki riƙe?" Da wani irin mugun kallo ɗauke a idanuwanta ta juya ta na dubansa,nan take Aabid ya sauke ƙwayar idanuwansa ƙasa. Ganin yanda ya shiga taitayinsa ba tare da ta ce masa komai ba ne ya sanya ta sakin murmushi tare da yin ƙwafa ta sa kai ta fice daga gidan. Aabid ne ya tsaya ya kashe kayan lantarkin gidan tare da rufe ko ina sannan ya shiga motarsa mai gadi ya buɗe masa gate ya bar gidan. Tsaki yayi saboda ganin ya makara fiye da yanda ya tsara. A haka ya isa Kamfaninsa na siyar da kayan abinci. Ko da ya isa ya tarar da an gama sauke kayan har an fara loda wa a store Maheer na tsaye shi da sakatarensa suna rubuta yawan kayan da wanda aka yi asararsu a yayin saukewa ko shigarwa cikin store. Murmushi ya sakar wa Maheer wanda Maheer ɗin na ganinsa amma ya ɗauke kansa ya ci gaba da abinda yake yi. Cikin ransa yayi alƙawarin idan har Aabid bai kawo masa maganar siyar da gidan da yayi ba,da barin Hajiya ba tare da mataimaki ba shi ma har abada ba zai yi masa zancen ba. Bayan Aabid ya fito daga motarsa sai ya wuce office ɗinsa ya zauna yana duba lissafin da aka tura masa na tsawon kwanaki biyar da bai duba ba;sakamakon sauke gajiyar da ya kwaso a gida da yake yi a office. Ya na nan zaune yana danne danne a laptop tare da zabga hamma sakataren Maheer ya ƙwanƙwasa masa ƙofa,sai da ya bashi izinin shiga sannan ya buɗe ƙofar bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Takardun hannunsa ya miƙa masa sannan ya tafi. Ajiye su a gefe Aabid yayi ya ci gaba da duba abinda yake yi a ƙasan ransa yana mamakin sauya masan da Maheer yayi. A can office ɗin Maheer kuwa ya so matuƙa ya bi bayan Aabid ɗin ya kai masa takardun da kansa,amma takaicinsa da yake ji ba zai bashi dama ya yarda su haɗu ba a daidai wannan lokacin. Dan haka Allah Allah ya dinga yi ya gama abubuwan da zai yi ya wuce gida. Tin daga wannan ranar Aabid da Maheer suka koma kamar baƙin juna. Domin kuwa a ɓangaren Aabid yana ganin bai aikata komai ba da Maheer zai ɗora masa karan tsana,hasali ma tausaya masa ya kamata Maheer yayi akan halin da yake ciki na rashin hutu,daga ya gama aikin gida ya dawo office sai kace inji,shi kuma Maheer yana ganin laifinsa akan abubuwan dake faruwa a cikin rayuwarsu gaba ɗaya. **************************** A zaune Aabida ta tarar da mahaifiyarta yafe da mayafi ta na kurɓar fura ta na yi wa mai aikinta masifa kamar za ta cinye ta. Cike da ladabi matashiyar budurwa ke bata haƙuri tare da goge wajen da Innaji ta zubar da fura bisa kuskure. Ba tare da sallama ko gaisuwa ba Aabida ta zauna daɓar a kujera ta na lumshe ido. Goshinta ta shafa ta ce. "Kai Innaji kin fiya masifa,don Allah ki yi shiru ki huta wa ranki. Idan kin gama shan furar ki taso mu tafi." "Ni dai da za ki yi haƙuri a bar yaron nan haka Aabidah da ya fi. Me kike so ne ki mallaka daga gare shi wanda baki gama mallaka ba? Baki da kishiya a yanzu,kin raba shi da iyayensa da danginsa,ma'aikatansa ma sai wanda kika so yake hulɗa da su,kin raba shi da abokansa,ke mai aiki wannan baki da ita a gidanki shi yake yi miki komai,tsabar ƙulumboto da neman asiri babu inda bamu je ba,daga nan ƙasar hausa har ta yarabawa sai da muka taka da ta fulani. Ka da fa ki manta har Akwa'ibom garin inyamurai sai da muka ratsa aka yi masa mugun ɗauri da gawa mai kimanin shekaru ɗari a duniya saboda auren ku ya zamo mutu ka raba. Ki na da tabbacin za ki kai shekara tamanin ne a duniyar nan ma ballantana ɗari Aabidah?" A sheƙe Aabidah ke kallon mahaifiyarta da ke roƙarwa Aabid salama a wajen matarsa da yake masifar so kamar ransa. Cike da gatsali da isgili ta ce. "Innaji kin dai san ko da ke ko babu ke zan nausa duniya na ci gaba da neman asirin da zai kafe min Aabid ya zamo nawa ni kaɗai;ta yanda ko mutuwa na yi ba zai taɓa kallon wata ƴa mace a matsayin mace ba ballantana har ya aure ta ko? Innaji zan shiga ruwa na faɗa wuta sannan na yi ninƙaya a teku na dawwamar da fatalwata a cikin kabarin Aabid domin ko a kushewa bana so mu rabu,ina so mu kasance a tare har a aljannah. Bayan haka kina tunanin duk wannan mugun abun da nake yi a wajen wa na gado su? Ko har kin manta ke wacece? Kishiyoyi goma sha uku cif kika kora a gidan naki mijin,wasu ma fa kashe su kika sa ayi,wasu kin haukata su,wasu sun ɓace ba a san inda suke ba har yau,to shikenan ni daga farawa ta sai a ce na dakata? Sam ba zai yu ba,idan zaki tashi mu je ki tashi kawai." Waro ido mai aikin Innaji ta yi kafin cikin sauri ta kwashe kayan da take mopping ta bar wajen. Ta na zuwa kitchen ta ajiye bokitin mopping ɗin ta dafe ƙirji ta ce. "Kai ku ji min ja'irar mata,ta na irin wannan shirkar da manyan arna ke yi amma take tunanin wai a haka za ta shiga aljannah. Hummm maji ma gani ai idan tusa za ta hura wuta." Aikinta ta ci gaba da yi ta na mamakin yanda su Innaji da ƴaƴanta suke rayuwa kamar basu san kalmar la'ilaha'illallah ba. Ta na tsaka da aikinta ta jiyo Innaji na ƙwala mata kira,da sauri ta saki soson wanke-wanken ta nufi parlourn ta durƙusa har ƙasa. Ta gabanta Aabidah ta shige ta na rausaya ƙugunta da ke a cike da manyan mazaunai da cinyoyi. Muryar Innaji ce ta katse mata hanzari ta ce. "Sannu sa'idawa masu bacci da ido ɗaya,ana ruwa kuna ƙirgawa,idan kun ga hayaƙi kun san me ake dafawa a maƙota. To ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki jini, za mu fita yanzu ki kula da gidan,idan na ji kin shiga maƙota yawon gulma a bakin aikinki,dan ba a kan ki na fara sallamar masu aiki ba,kuma ba a kan ki zan gama ba. Idan waccan gantalalliyar ta dawo ki sa ido kada ta shigar min ɗaki ta yi min sata.shi kuwa wancan shashashan ki ce masa ya jira ni na dawo kada ya sake ya sake sa ƙafa ya bar gidan nan ba da izinina na balle ya sake jawo min magana. Sai na dawo." Gyaɗa kai kawai Laure ke yi tana amsawa da "To Hajiya,a dawo lafiya." Su na fita Laure ta samu waje ta kame a kujera ta na ƙarasa shanye sauran furar da Hajiya ta bari. Cike da jinjina kafurci irin na su Innaji ta jinjina kai ta ce. "Wato a ƙiyama ba dan kowa ta kansa yake yi ba,da na roƙi Allah Ya nuna min yanda za a yi wa waɗannan bayi hisabi. Ni yanzu ina ni ina tinkarar wannan da'un na ce masa kada ya sake fita? Ai ni ya fitar min da kaina daga gangar jikina idan ban yi wasa ba,ita kuwa wannan kinfi karuwar taɓargaza ta zo ta yi duk abinda taso babu ruwan Laure,ita da gidan ubanta meye nawa a ciki? Ke kanki Hajiya ba jin maganarki suke yi ba balle wata Laure ƴar aiki. Mtswww." A ɓangaren su Aabida kuwa suna fita kai tsaye hanyar barin cikin garin Kano suka ɗauka. Kasancewar ta kwana biyu bata je wajen bokan nata da ke yi mata aiki ba,gashi a kwana biyun tana yawan fama da mafarkan da bata gane kansu,shi yasa take so su koma ya bincika mata goben ta ya ga me yake shirin tunkaro rayuwarta...... MUGUWAR MACE. NA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 6. A bakin ƙofar gidan boka Aabidah ta tsayar da motarta sannan ta sake fesa turare a jikinta,dariya sosai Innaji ta hau yi dan ta san dalilin da ya sa Aabidah ke fesa turare. Harara Aabidah ta banka mata,sai ta saka hannu ta zuge bakinta ta yafa mayafinta ta fice daga motar tana ci gaba da dariya. Itan ma dariyar ta yi sannan ta yafa mayafinta a kafaɗa ta ɗauki jakarta da wayoyinta ta fita. Kulle motarta ta yi sannan suka shiga gidan bokan ba tare da sallama ba. Zaune suka tarar da shi ya na ta yin wasu abubuwa kamar mai ciwon farfaɗiya. Ya jima a haka kafin ya dawo hayyacinsa yana sharce zufa. Wani ɗaki ya shige su Innaji suka bishi ba tare da kowa ya tanka wa ɗan'uwansa ba.  Su na shiga suka tarar da bokan ya tanƙwashe ƙafa jan ƙallen dake jikinsa ya rufe masa iya gabansa,jikinsa ya rabu da ƙasa kamar wanda yake zaune a saman iska. Jajayen idanuwansa da ke a kulle ya buɗe ya zuba wa Aabidah su kamar zai fasa jikinta ya hango zuciyarta. Ba tare da jin tsoro ba Innaji da Aabidah suka fara yi wa bokan nasu da suka yi matuƙar imanin in dai yana raye babu su babu jin kunya kirari. Sun jima suna jinjina masa akan mugayen ayyukan da yake yi musu kafin ya ɗaga musu jelar damisar dake hannunsa yayi musu nuni da wasu ƙwarya guda biyu. Da baya da baya suka isa wajen ƙwaryar suka zauna kamar yanda suka saba. Ido ya kulle ya hau yin surkulle kafin daga baya yayi shiru. Su na jin yayi shiru suka miƙe tsaye daga saman ƙwaryar kowaccensu ta kafe ƙwaryar da ta zauna akai da ido. A gaban idanuwansu ƙwaryar farko wato wadda Innaji ta zauna ta buɗe kanta ta isa gaban boka ta tsaya a saman iska kamar yanda yayi. Kallon ƙwaryar yayi sosai sannan ƙwaryar ta juya kanta tana fuskantar Innaji. Cikin wata iriyar murya mara daɗin sauraro boka ya kalli Innaji ya ce. "Da alama yaranki bana sun yi nisan kiwo,saƙon da kika bayar a basu zai jima bai isa kunnuwansu ba." Tagumi ta zabga tana jin wani irin zafi a cikin ranta. Sosai take son ƴaƴanta bata son abinda zai taɓa rayuwarsu, shi yasa a koda yaushe take ta faɗi tashi dan ganin ta inganta musu rayuwarsu ko ta halin ƙaƙa,sai gashi rayuwar Aabidah ce kawai ta inganta a cikinsu har suka raɓu da ita suke yin walwala, Junaid da Jauhara a kullum cikin ɗakko mata magana suke. Hannu ta sanya a jakarta ta lalubo kuɗi ta jefa a cikin ƙwaryar ta koma gefe tana matsar ƙwalla. Kafin ta gama daidaita tsayuwarta ƙwaryar da Aabidah ta zauna ta buɗe kanta ta isa gaban Boka ta tsaya,ya jima sosai yana kallon ƙwaryar kafin ƙwaryar ta koma gaban Aabidah ta tsaya,shiru ta yi tana kallon ƙwaryar cike da rashin fahimta. Kai Boka ya jinjina mata sannan ya ce. "Ƙwarai da gaske. Ni ma abinda ke damu na kenan a cikin ƴan kwanakin nan game da aikin ki Aabidah. Na rasa gane dalilin da ya sa idan dai wannan mutumin ya shiga cikin aikinmu bama ganin komai sai wannan hasken mai kashe idanu. A yau ina so na baki shawara ba wai dan na gaza a aiki na ba;sai dan kawai ina so kema ki yi wani yunƙurin da zai taimaka mana ta ɓangaren ki,ina so ku sani ba koda yaushe ne ake dogara da sihiri ba. Ina so daga yau ki jawo wannan mutumin jikinki ba da tirsasawa ba ya amince ya dinga zuwa gidanki da kansa,sauran bayanin zan yi miki shi daga baya. Ke dai abinda zaki yi kawai shine ki tabbata kin gama naki ɓangaren." "Ya kai babban Boka...." "Kada ki ce komai,domin wannan na daga cikin fassarar mafarkanki. Ki je ki yi naki ɓangaren ni ma zan ci gaba da yin nawa ɓangaren kamar yanda na saba." Jinjina kai Aabidah ta yi cike da sarewar guiwa ta zira hannu a jakarta ta zaro kuɗi ta ajiye a cikin ƙwaryarta. Ɓacewar Bokan daga wajen da yake ne ya basu damar fitowa daga ɗakin da baya da baya suka bar gidan. Su na shiga mota Aabidah ta ja dogon numfashi ta shaƙi iskar cikin motar mai cike da oil perfumes da take sakawa da kuma turaren mota. Ganin Innaji na ta sharar hawaye ne ya sanya ta juya ido sama ta kunna motarta suka bar wajen. Kai tsaye gidanta suka nufa domin a ƙa'ida idan suka fita sai sun biya ta gidan Aabidah Innaji ta ci ta sha sannan ta yi guziri da duk abinda yayi mata. A bakin gate Aabidah ta tsayar da motarta tana ta danna horn kamar za ta tashi sama. A guje Laminu mai gadi ya isa ya buɗe mata gate ɗin wandonsa a hannu,da alama zagayawa yayi kuma bai gama uzirinsa ba ya taso gudun kada uwar ɗakin nasa ta balbale shi da masifa. Kamar za ta bi ta kansa da motar haka ta shige gidan da tana cin magani,juya baya Laminu yayi yana jin wani irin tsoronta na sake huda shi. A haka ya kulle gate ɗin ya tsaya yana jiran ya ji saukar ruwan masifa daga bakin Uwar ɗakin nasa. Sai dai shirun da ya ji ne ya tabbatar masa da bata da lokacinsa. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya koma banɗaki yana tsine wa talauci da yayi sanadiyyar kawo shi gidan MUGUWAR MACE kamar Aabidah. A ɓangaren su Innaji kuwa suna shiga cikin gidan ta ware ta na kalle-kalle kamar wata baƙuwa,kallon sauye-sauyen da ta gani a parlour ta hau yi tana tambayar Aabida lokacin da suka sauya wasu abubuwan tare da ƙara wasu abubuwan. Guntun tsaki Aabidah ta ja saboda yanda take jin ranta babu daɗi game da abinda boka yace mata,rai a ɓace ta ce. "Wai ke Innaji yau kika fara zuwa gidan nan ki ga sabon abu ne? Ke komai kika gani sai kin yi magana akai haba ! Idan akwai abinda kike so kawai ki yi magana na siya maki irinsa. Ni bari na shiga ciki na huta idan kin gama ki wa Laminu magana ya mayar dake gida,in kuma za ki jira ni sai yamma mu tafi plaza tare to ki jira." "To me nake yi a gidan idan na koma banda mugun tunanin halin da yaran can suka jefa kansu a ciki? Shiga ciki kawai ki yi hutawarki ƴar albarka da yamman kin ajiye ni a gida." Ɗaki Aabidah ta shige tare da bugo ƙofa ta rufe. Kai tsaye kayan jikinta ta hau cirewa sannan ta faɗa wanka,ta jima tana dirzar jikinta kafin ta fito sanye da bathrobe a jikinta kalar  purple mai haske. Kanta ɗaure da ƙaramin towel kalar bathrobe ɗin jikinta ta samu waje ta zauna a kujerar dake gaban madubinta tana shafa mai tana tunanin ta inda za ta fara hilato Maheer zuwa gidanta. Ta sani idan umarnin kawo Maheer ta bawa Aabid cikin awa ɗaya zai kawo mata shi gidan ko yana so ko baya so,to amma ta ya za ta sa Maheer zuwa gidan da kansa kuma da son ransa ba tare da ta samu matsala ba? Sanin kanta ne ita da Maheer sun tsani junansu,rayuwa suke yi kamar

Chapter 3 of 13