Share this page
2 / 9
gaskiya yana siyan tsada, da wannan ya fice, Mahaifinsa ya bi shi da kallon tausayi da kuma addu'a, cikin ikon Allah sai da ya ringa haihuwar ya'ya har bakwai da matansa biyu sunna komawa ga ubangijinsa , shine na farko da ya zauna, daga shi kuma har yanzu babu wanda ya rasu, bai wani dauki shekaru ba, dan bai fi talatin da biyar ba, ama a haka Allah ya saka masa albarka, bayan dogon karatu ya fito ya damki aiki mai daraja har ya zamo kafada mahutar dangi da jama'ar gari A muntuce ya ringa bi daki daki, tun daga kan aunty Amarya, har zuwa dakin mahaifiyarsa wato uwar gidan Docter Hajia ZUWAIRIYA , Kowance idan ya shiga bangarenta ya gaisheta, yakan saurara ya saurari bukatunta, da kawo kararta da sauransu dai, abinda ba za'a rasa ba , ba zai bar wajen ba har sai ya biya mata dukkaan bukatunta da yake iyawa, wa'inda baya iyawa kuwa yakan yi addu'a ne ya tashi A dakin Aunty amarya kawai ya shiga ya fito bata ce tana bukatar kudi ba, ko ta kawo karar yar uwarta ba, har ya gama dan zama ya mike ya bar bangarenta ta bishi da addu'a kanta a sade dan fushin mijin bai saketa ba, watau da ya fadi sunnan da bata so, bata kauna ba kuma zata tana so ba! Irin zaman da ya yi a saman kujera yana dan cakalar dankalin turawan da Hajia ta zuba masa da kanta irin zama ne da akan yi idan an zo gaban mahaifiya, wato ba d'ar ba dari d'ari. Abincin yake ci, bata yi masa magana har sai da ya gama ta yi kiran daya daga cikin yarenta ta umarceta kan ta kwashe , ta kwashe ta mayar kicin ta kimtsa wajen sannan ta dawo sumui sumui ta haye sama numfashinta a makogwaro har ta shige sannan ta ja numfashi tana shigewa dakinta hadi da adu'ar Allah ya sa kar Hajia ta sanar masa cewar yau bata yi wanke wanke ba, wancen bara gurbin ta saka ta yi mata ya ci kakanin babaninta! Hajia ta sake zubawa fuskarsa ido, sai kuma ta tabe baki tana cire kanta kasa kasa ta ce" wannan ja na lebenka kamar dai ba na lafiya ba......" Kasancewar yana kallon fuskarta ne, kuma yana jin dukkan abunda take fada, sai ya yi murmushi bai ce komai ba, bai san me yasa kalar lebensa yake saka mahaifiyarsa koda yaushe mita a kai ba, shi dai ko goro baya taunawa bale a kai ga sigari ko giya, hasalima kamaninsa da na mahaifinsa tamkar kaki ya yi ya tofar, itace baka sannan a kaf ya'yan mahaifinsa su uku ne suka yi farinsa, ama Hajia sai tace shi nashi jan ya yi yawa anya na lafiya ne? "Baban gida, na san abanka ya maka maganar kayan lefen yaren nan ko?" Hajia ta fada tana dubansa A nutse ya amsata yana sake dubanta Hajia ta hade fuska sosai ta ce" To bari ka ji abinda zan fada maka, ban lamunce maka kwasar kudi ka je ka kwashi kaya na makudan kudade ka zubawa ya'yan da kwanan duniya iyayensu ke koya masu tsanarka da kiyayarka ba, ka sani ni na haifeka babu wanda zai fi ni sonka ko sannin zafinka a duniya, ka kula Baban gida, idan nace bana so kar ka saki ka yi!" A hankali ya dago kansa dake sade, shin yaya zai yi da iyayensa ne? Idan wannan ya ce ga abinda yake so a yi, sai wancen ya ce kar a saki a yi, ya kuma yi aiki da karfinsa da ikonsa a kansa Bai san me yasa Hajia take yin wasu abubuwan ba wani lokacin, bayan shi ya sani mahaifiyarsa mutun ce mai matukar kyauta da son mutane "Yaya zaka tsareni da ido kana min wani kallo kamsr sa' arka Baban gida?, So nake ka fada min abinda abanka yace kaf ina saurare" ta sake fada harda harde ƙafafuwanta, irin jira take ta ji abinda bai yi mata ba a yi wada za'a yi Ajiyar zuciya ya sauke a tausashe ya ce" ABAH bai ce min komai ba, nine nake so mu yi maganar da ke, sai na ga abinda ya dace a yi, MAMAH kar ki manta nine baba a gidan nan, ko me za'a yi ya zama wajibi na shanye na kuma nuna masu halin girma, da haka ne zasu yi koyi da ni idan kowa ya malaki hankalin kansa ya rike zumunci duk rintsi, Mamah, dukkan abinda suke yi ko giya suka sha babu wanda zai tunkarenk, tun daga kan AMIR har zuwa kan ummi Auta..., Ko a haka aka tsaya da sauki a irin tab'arb'arewar zamani da zumunci..." Zama ta gyara da kyau tana kallonsa ta katse maganarsa a harzuke ta ce" Ba zai yiwu ba fa, ba zai yiwu ba, su rike zumunci ko kar su rike wannan damuwarsu ne, ba zai yiwu a taru a kashe min ɗa ba, na tabata abanku ba wani tausayinka yake ji ba, bari ka ji, idan ya ce sai ka yiwa ya'ya mata kayan daki da komai ba laifi ka yi, bayansu idan ka yarda ka yiwa matansa ko maza kayan aure ban yafe ba! Nace ban yafe ba baban gida, bama irin matar nan da yake sakawa a gaba tsofai tsofai da shi yana ikirarin soyaya, wace soyaya kuma Allah na tuba gayar yawun tsufa, na yanke magana Baban gida ba zai yiwu ba!" Idannuwansa kawai ya mayar ya rintse, lokuta da dama yakan rasa ina mahaifiyarsa ta dosa, A lokacin da Aba ya auri matar nan baki dayansu sun nuna mata kiyaya, uwa uba y'ar da Abah ya kawo matsayin tata ya kuma nuna ta zama tasa, yarinyar na fuskantar tsangwama da kyara a wajen dangi dan ta zamto wace aka haifa ba da aure ba, wulakanci kala kala na rayuwa tale gani, mahaifiyarta da ta haifeta da cikinta ta fi kowa tsanarta dan ko kofi ta taba ba zata taba ba, rana tsaka MAMAH ta ba kowa mamaki ta dauko yarinyar nan ta hada da ƴaƴanta ta kuma jajirce a kan yarinyar ta sakata makaranta take kuma tsaye a kan tarbiyarta, har yau an kasa gane me hakan yake nufi, domin a bangarenta yarinyar ke rayuwa, a wajen mama ba zata taba fuskantar kyara ko tsangwama ba, hasalima tana rike da ita da zuciya daya kamar yadda zata taro ƴaƴanta ko ta gyara haka zata yi mata, takan ce yarinya tata ce, ama bata son uwarta, hakan na ba kowa mamaki, sai dai a duniya ita Mama bata iya rayuwa ta munafurci ba, idan tana yinka tana yinka ne, idan bata yinka bata iya boye boye ko yi da gangan ba, FATIMA ZAHRAH tana samun hutu ne da kwonciyyar hankali idan tana gaban Mamah, du fada irin na Mamah tana jin du duniya bata da wajen mafaka sai a saman kafadunta, zaka ga Mamah ta wanke ƴaƴan kaf da fada kowa ya gudu ama ita sai ta karaso ta duka ta dora kanta a saman cinyiyinta ta yi ta sauke ajiyar zuciya..........wannan tsakani nasu na ba kowa mamaki ciki harda Docter Ahmad SULAIMANE Wannan babin Mamah ta rufe ta sake dauko na iyalinsa, Hirar da sam bata wani so, ba kuma ya farin cikin sauraro, sai dai wace ke yi din nan itace Allah ba zai saka shi aljannah ba idan har bata daga kafarta ba, du duniya itace take kallon idannuwansa tace zan fa ci ubanka babana, kuma a saurara a yi murmushi dan ta isa, bayanta ko mahaifinsa a yanzu sun zo bigiri din da yake lalaba shi, yake kuma yi masa komai a hankali du zafi irin na AHMAD SULAIMANE. *A bayan Layi* A tsaye take tana bin motar mai kirar Corolla da ido sannan tana jin muryarsa yana sake kiran sunnanta a karro na uku A hankali ta dauko idannuwanta masu kama da na mashayiya, uwa uba tsarin halitarsu tanaa da girma daidai misali, sannan fattar saman mai bugun ido ce,, irin kana kallon su zaka so fara kawar da dubanka, dan ba irin idannuwan da ake tsatsarewa da kallo bane, ga wani ruwa ruwa mai nuni da daf ake da iya fara kuka, koma sama da haka, bayan babu maganar kuka a kusa kusa a cikin tsarinta, ba dan ta kasance mai tsaurin ido ko mai taurin kai bane, ko daya, hasalima ana iya kiranta da farar kura dan tsabar tsoronta, dan tana da saurin jin tsoro, ama kuma halitarta mai bayar da tsoro ce Farar fuskarta dake dauke da kwontacen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hanna su bayana ba ne ke daukan jajaja, kumatunta na neman kumbura lokaci d'aya. *Alhamdulillah.* 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐 *DAƘIƘA BIYAR* 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐 _MALLAKAR_ *SAJIDA NIGER* *Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai* _3_ *Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰* Farar fuskarta dake d'auke da kwontacen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hana su bayyana ba ne ke d'aukan jajaja, kumatunta na neman kumbura lokaci daya ta sake duban fuskarsa, a sanyaye ainun ta ce" Motar wa ka samu yau kuma?" Goshinsa ya dafe da hannunsa yana furta" Oh shiiit, flowrs wai ba zaki shigo din bane sai na yi fushi na yi tafiyata? Why kike min irin haka ne, sai kace wani bakonki ko wanda zai maki lahani? Ke kin san ni ba mugunki bane, in kuma yanzu tsorona kike yi fine, bara na tafi kawai." Zuciyarta ce ta ji ta buga, zata iya irga mutanen da bata had'a b'acin ransu da kowa a duniya, idan har ta ga alamun b'acin rai a fuskarsu sai inda k'arfinta ya k'are, bale ace itace silar b'acin ran?, Ko kusa ba zata iya yarda da hakan ba. A hankali ta daka hannunta mai d'auke da awarwaraye na roba irin masu kyalin nan kwaya biyu bak'ak'e sidik ta bud'e motar ta shiga ta zauna ta rufo ta juyo zata sake tambayarsa a inda ya samo mota, bayan ta san bashi da ita ta ganshi daf da ita, idan nace daf da ita ina nufin kusancin da take iya shakar numfashinsa ya kuma shaki nata. Da sauri ta ja baya, tana doka bayanta da jikin madubin motar, hannunta daya kuwa tana kokarin ture shi ta hanyar dorawa a saman fuskarsa ta tura muryarta a dan dage ta ce" Subahanalah meye haka kuma?" Fuskarsa dake dauke da walwala ce ta yi kici kicin , ya saka hannunsa ya rike nata yana kallonta ya ce" Me kike yi haka ne Flowers, ban gane menene haka ba, wani abu zan maku ne kamar kin ga dodo daga matsowa daf da ke dan na ji wannan turaran mai kanshi kuma yaya sunnansa shikenan sai ki wani zabura kammar kin ga dodo? Haba dan Allah, idan kina min irin haka sai na ji hankalina na tashi, sai na yi tunanin sam baki yarda da ni ba, sai na ringa hasaso kamar tsorona kike yi, ko kina min kallon dan iska, bayan kin san ni da zuciya daya nake sonki, a kan sonki ina iya rasa raina, burina aurenki, yau koda jikinki na taba nawa ne, kowa ya sani mutane ne kawai ba'a tara suka sheda ba, wanda nake tunanin soon zamu kai ga ci, da zarar na gama shafe bangarena na gidanmu, ke kin san a kanki na bar yan mata, bana kula kowace, kin san akoy yan matan dake kawo min kansu na so su, ama na ja na tirje ni sai ke, ama sai ki ringa wani abu baya baya kamar wani wanda zan maki Fyade?" Cikin dabara ta janye hannunta, tana mayar da shi cikin hijabinta gaba daya, fuskarta a matukar raunane ta ce" Ba haka bane Khalb, kai ka san nima ina sonka, ka san ba zan taba duban waninka ba, ama kuma a kulun ina fada maka, ka daina nuna zalamarka a kan jikina, bana so, Abanmu na fadi cewa bai halata namijin da ba huruminki ba ya ringa taba kofa hannunki ne, haramun ne khalb, kuma fa ka san lamari na shedan." Nan da nan ya yi takwaf takwaf da fuskarsa, ya cire dubansa ya maida bakin layi, a kausashe ya ce" shikenan, tunda ba zaki taba yarda da ni ba shikenan, ama ki sani so fa ba kiyaya bane, ke kin san irin dogon wajen da na ratso na zo, kin kuma san in ba so ba, babu abinda zai kawo ni da wannan tsohon daren anguwar nan, na zo zaki saka min da haka dan kawai na ji kanshi mai dadi a jikinki na so matsowa dan na ji shi da kyau, ki yi hakuri, ki sauka ki koma gida, nina san ni kadai nake wahala a sonki, tunda na ganki ya wadatar, Allah ya bamu alkhairi." Gaba daya sai ta ji kamar yana neman dakatar da numfashinta ne, a hankali ta fitar da hannayenta tana murzasu hankalinta a tashe ta ce" Dan Allah, ka yi hakuri, ka yi hakuri, ni fa ba nufina kennan ba, haba wani maganar zaka cuceni kuma, da kana cutana ai da ka yi ba yau ba..." "To me kike nufi dan kawai na nufo fuskarki zaki wani zabura kina ture ni? Ko sun maki wani abu a gidan cen naku da basa kaunarki?" Ya fada a wani zazafan shi a dole ga wanda ya isa da ita. Da sauri ta girgiza kanta, tana auna maganarsa wai wani akai mata a gidansu da ba'a sonta, a saninta sandiyar haduwarta da shi ta fito daga gidansu wani lokaci da mahaifiyarta ta wulakantata, tana kuka suka hade, hi kuma zai je anguwa da yama, tana kuka ta rasa inda zata nufa ya ringa binta yana yi mata magana har sai da ta dakata daga saurin da take, tana kallonsa ta fashe da kuka, domin inda zata fadi damuwarta take nema a lokacin, a ranar ne ya ringa nuna damuwarsa har sai da ta sanar masa daga gidansu ne, irin rudanin zuciya ya sakata cewa ba'a sonta a gidansu, dan shine kadai amsar da ta zo bakinta, domin ba zata iya dubansa ta sanar masa mahaifiyarta ce bata sonta ba. A hankali ta sake girgiza kai, muryarya na rawa ainun ta budi baki zata yi magana wayarsa ta dauki ringa. Kamar yadfa ya saba sai ya kawar da screen din daga fuskarta ko zai dauki kira haka ne yauma, sai da ya kawar da wayar sosai ya duba mai kiran nasa sannan ya daga kiran, sai dai ya yi mantuwa da Bluetooth din ya yi connectng da motar yana shan kidan Davido , hakan na nufin abinda zai fito daga wayar zai shiga kunnen kowa ne ba iya shi ba "Hello?, Hello abokina ina ji salama alaikum" ya fada yana kai wayar kunnensa. "Wa'alaika salam, kai wai yayane tun dazu muke jiranka mu wuce ka wani shanya mu a nan, kar ka ce min ka je wajen wannan banzar yarinyar ne mana!" Abokin nasa ya fada hadi da dan jan tsaki, hakan ya saka shi dan zabura yana waigowa wajenta dan sai a lokacin ya shiga neman wajen da zai datse hakan, ama bai sani ba, hasalima hadawarma sai da aka hada masa, tukin motarma ya iya mota ne irin iyawar nan ta garari , domin a hannun abokansa ya'yan masu da shi yake warta yana dannawa har aka dace. A dan hargitse ya bude motar ya fice, sai dai bai yi nisa da motar ba kasa kasa sosai ya ce" Kai me yasa baka da hankali ne, amsa amon motar fa a bayane yake kake magana tana jinka meye haka?" Abokin nasa ya ja tsaki, wanda maganar tasa ne kawai take iya ji, bata iya jin me ma'awiyan yake fada, dan ya rufo motar ama yana daf da motar Da yannayi na rashin kunya ya ce" Ka katse mana ai laifinka ne malan zaka wani shanya manyan babs ka je wajen da ko lebe ba za'a barka ka darza ba kamar wani an fika tsatson kirki bayan mun san..................." A lokacin ne kuma maganar ta dauke, dan ba shiri ya yi gaba da sauri yana amsa kiran. A hankali Ta bude nanauyun idannuwanta da suka cenza launi suka yi wani irin ja ta sake zubawa a kan hanyar da ya mika yana amsa wayar Wani irin nauyi jikinta ya dauka, nauyi mai zafin gaske, tamkar yau kunnayenta suka fara jiyo mata magana irin ta wulakanci da zagin nasabarta.....ko dan wannan ya fito daga bangaren wanda ta riga ta aminta cewa mutuwa ce kawai zata iya rabata da shi, sannan babu ɗa namijin da zai iya sonta ya kare hakinta irinsa? Da kyar ta iya bude motar, bayan ta kasheta ta bar masa makulin a jiki, dan kar wani ya zo ya gane ba kowa ya yi gaba da ita, ta rufe ta shiga tafia jiki a sanyaye tamkar zata kifa kasa dan ciwon da zuciyarta ke yi Tana karasowa kusa fa gidan abokin hadin bakin nata yana tsaye jikinsa sai bari yake, adu'arsa daya kar Oga ya fito a lokacin da zata dawo, fatansa daya ta dawo ta shige gidan nan tun kafin a san bata cikinsa, Magana yake yi mata jikinsa na rawa yana nuna mata maza ta shige, Oga fa na nan, hakan ya sa gabanta sake yankewa ya fadi, duda bata gane wane a cikin ogannin nasu ba, abinda ta sani shine su dukka ogannin nasu babu daya da yake wasa da su, daga wansa zai iya saka bulala ya zane masu jiki tas, sai wanda kallonsa ke fasara idan ka yarda ya damkeka sai dai wani ba kai ba Hakan ya sa ta dan daga kafa, sannan ta shanye abinda ke ranta ta shige gidan a darare ta bi ta cikin shukoki har ta samu ta isa wajen babar bishiyar da take zama lokuta da dama , a lokacin ta ja ta tsaya tana jin tamkar fitsari zai zubo mata sakamakon jin an ce WAYE? Jikinta ne ya dauki rawa, zufa na neman karyo mata, lokaci daya kuma ta juyo wajen da aka daleta da hasken fitila dan koma waye ya gane wacece din da yake son sani. A hankali ya sake zuba mata ido, tun daga yannayin tsayuwarta, gumin da take tsatsafawa, idannuwanta dake ta kasa sunna sama, fuskarta da ta d'auki ka, har zuwa hannayenta da ta damk'e hijabinta take wani abu kamar mai jin kashi. Sake daleta ya yi da hasken nan yana kallonta , muryarsa a dake ya ce" Fitsari kike ji ne?" Tambayar tasa ta yanzu ta sakata gane wanene a wajen Shikenan, ashe ogan da ake nufi yana gidan kennan? Ai su sun zatama an tada shi daga garin an maida shi wani garin har sunna murna da samun yanci a cikin duniyarsu, sai gashi yai ta yi gamo da muryarsa a irin wannan lokacin da ta kwaso tarin tashin hankalinta. Kai ta sada, hawaye ya shiga bin kumatunta, hawayen da ita kanta bata san tana iya zubat da su ba, batama san a kan me zata zubar da su a nan a gaban wannan mutumen da ta san yana cikin masu kyankyaminta.....to wannan tambaya tashi batama san ta mecece ba sam. A hankali ta sake sada kanta sosai, ta kasa bashi amsa. Baki ya tabe ya kashe fitilar ya mayar aljihunsa sannan ya yi gaba wajen motarsa ya shige ya tayar ya shiga juyar da ita dan barin gidan. Da sauri ta dage hijabinta ta kalkala da gudu ta bi ta cen baya , hakan ya saka shi take birki ya zubawa hanyar ido, sannan ya sake dawo da yannayinta a cikin idannuwansa. A hankali ya ji kansa ya sarra masa, sanadiyar wani tunani da ya shigo cikin kwakwaluwarsa. Take motar ya yi ya fice a gidan da gudun gaske dan tuni aka bude masa get. Cikin sand'a ta lek'a falo, gabanta ne ya sake kwonci kwonci ya fad'i sakamakon hangi Hajia na falo bata hau sama ba, duda baban fargabarta ace hajiar ta hau saman ta bi dakunnansu ita bata sameta a nata ba, gaskiya ba zata kuma yarda ta fita a irin wannan lokacin ba, haka kawai salon ya sakata a uku , bama zata kuma fita inda yake ba, domin ba zata zauna rayuwarta a gida a tsangwameta a tare da shi a tsangwameta ba. Ta jima a tsaye a wajen nan tana addu'a tana zufa, har dai Hajia ta mike ta kakashe fitilu da sauransu sannan ta sahiga hawa sama da carbinta a hannunta da gilashinta na karrin karfin gani. Da sanda take dan bin bayanta har ta shige dakin farko, ita kuma da sauri ta kama kofarta ta bude ta shige cikin hanzari ta rufo ta cire hijabinta ta yi wurgi da shi cen san bed, tana kiciniyar cire rigar dake jikinta ta ji an bud'e k'ofar an shigo lokaci daya ta idasa sakarwa ta nemi samin fitsarin mararta har abinda ke d'aure da gashin kanta wato Ribom ya fad'o k'as ya daki k'afafuwanta. K'afafuwan nata Hajia ta bi da kallo, sannan ta sake d'auko kallon ta dawo da shi har zuwa wajen fuskarta. Tsare fuskarta ta yi da kallo, hakan ya sa ta sake d'aukan yanayi irin na wanda ta d'auka a d'azu da take gaban wancen mutunen. "Ke zo nan!" Hajia ta fad'a da d'an k'arfi tana nuna mata gabanta bayan ta nunata. *Alhamdulillah.* 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐 *DAƘIƘA BIYAR* 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐 _MALLAKAR_ *SAJIDA NIGER* *Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai* _4_ *Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰* "Ke! Zo nan." Hajia ta fad'a a dake da d'an k'arfi, sannan tana nuna gabanta, zabure ta duka ta d'auko ribom d'inta da ya fadi ta shiga daura shi jikinta na bari tamkar zata kifa ta nufo wajen hajiar ta nemi dan dukawa dan ba zata tsaya mata k'erere ba, hajia bata d'aukan wannan rainin. Damkar hannunta hajia ta yi ta janyota sosai ta shiga dube dube a jikinta har zuwa sket dinta da ya saketa sosai bai rike jikinta ba Sake zuba mata ido ta yi sannan ta saki b'oyayyar yar ajiyar zuciya a hankali ta ce" Kuka kika yi ne? Me kike yi har karfe goma sha daya na dare ke neman yi baki kwonta kin yi barci ba?" Bakinta dake bari kad'an ta bud'e a hankali ta ce" Mamah,dama, sallah zan yi ne." Fuskarta ta sake kurewa da ido, sai kuma ta ja numfashi ta shigo da kyau dakin ta zauna bakin gado ta ce" Je ki yi alwallar ki fito." Da sauri ta juya ta shige tana zarro ido had'i da dafe gaban kirjinta, da kyar ta iya dauro alwallar ta fito ta nufi salayar da Hajia ta nuna mata still tana binta da kallo. Hijabinta ta saka ta haye salayar ta tayar da sallah , a hankali a hankali jikinta dake bari ya daina har ta zurfafa ta yi raka'a biyu kadai ta salame ta shiga danna yan yatsunta kanta a kasa. Hajia ta bud'e baki a nutse bayan ta ga ta gama sallar ta ce" Shafa'i da wuturi ne kika yi, ko nafila ne tun yanzu?" A hankali ta juyo

Chapter 2 of 9