shine kawai soyayar da zai iya nuna mata, su Mama kansu haka jikinsu ke rawa cewa suke kennan abin baba ne ya fade shi a nutse babu tashin hankali? Gaba daya rasuwar ta zo masu a ba zata ksmar yadda mutuwa ta iya aikin zuwar ba zata
Yana tuki yana kallon yannayin gari maganar NIHAL ta fado masa
Dan murmushin yake ya yi kawao ya girgiza kansa
Shi fa ba maganar shekarunta dake saman nasa bane damuwa, meye a su yan shekaru hudu dake tsakaninsu shi ko wace ta girme masa da shekara goma zai zauna su kurewa junna man kai, tassssss, dan ko a yanzu dama bai yi ra'ayin zama da yarinya ba, dan baya son kayan haushi da saka ciwon kai da raini, ..........sai dai irin yadda ta kawo zalamarta a bayane ya matukar bashi mamaki, kamar wace take jiran haka ta faru? Ya gaza dora abin a matsaya daya, shin Kwadayi ne ko wauta ce? Ko kuma itace sanadiyar........................................................ Dif ya yi yana dantse lebensa ya juya ya dauki hanyar gidansa dan yana son sake yin wani binciken, a sanninsa a yanzu babu kayan Manal ko daya, dan ya sa sun kwashe, ama kuma ta yiwu ta bar ire iren magungunnan nata na mata
________________________________
Kwonci tashi asarar har Manal ta yi kwana arba'in da rasuwa
A tsakanin kwanakin nan abubuwa da dama sun faru, ciki harda yajin aiki da wasu malamai suka tafi, ama banda wasu daidaiku
A irin wannan ne aka wayi gari yai saura sati hudu a yi saukar su ZAHRAH wace zasu kai hardarta baki daya, gagarumar sauka ce da zata dauki kwanaki ana yi dan har a kafafen yada labaru za'a saketa
Dan sauri take yi da abin amsa amo a kunnenta wanda ta jona da wayarta yar karama tana amsa kiran Ma'awiya tana dan murmushi har ta karaso wajen da zata samu su Furera dan ta sanar masu baba direba fa ya fitar da mota tun dazu su ake jira
Tunda ta karaso gabanta ya yanke ya fadi sakamakon ganninsu da ta yi sunna tare da LARABA sunna hira cikin raha
Sau biyu tana juyawa, sai kuma ta dake ta juyo a sanyaye ta karaso inda suke tsaye ta yi salama cikakiya ta dan dakata tana kallon irin debotan da suke yi sunnaa watsarwa da kallo irin na raini da kaskanci
Sake jan numfashi ta yi a sanyaye ta ce" Asalamu alaikum wa rahamatullah"
"Yau na ga bakin naci da masifa a gidanku Fursy baby, wannan iya yin haka ake maku kennan ba ji ba gani kamar wata tsaftataciya!". Laraba ta fada ba dar, ba kawar da kai, ba jin kunya bare kiyaye batawa dan Adam
Furera da ta fita halin na rashin da'a ta tare maganar tana fadin" Kema kin ga fi'ili irin na makotan masu kudi ko?, Ana abu kamar an san Allah bayan sai a hankali ne kawai!"
ππππππππππ
*DAΖIΖA BIYAR*
ππππππππππ
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin Ζai*
_11_
*Garabasa , garabasa, ππ₯°, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°π₯°π₯°*
Kanta ta sada, zuciyyarta na dokawa da karfin gaske
A hankali ta dan zabura sanadiyar kiran sunnanta da Ma'awiya ke yi da dan karfi dan ya tabata fada ne yan uwanta ke janta da shi dan yana jin komai da suke fadi
A hankali ta ja wani numfashi ta sake dago dubanta tana kallonsu
Aunty Rukaya ce ta juya da nufin tafia , dan ita bata son irin haks, ita bata zagin yarinyar nan, bangarensu daya tare suke kwana sunna tashi, ba ruwanta ne kawai da ita, bayanshi bats zaginta bata wulakantata ko daya
Da sauri Laraba ta kamo hannunta tana karya wuya ta ce" Rukaya ina zaki tafi kuma muna yin managa?"
Rukaya ta ja numfashi tana fuskantarsu ta ce" Aunty Laraba, ni dai kamar yadda na taba fada maki zan maimaita maki, ni kam babu ruwana da wannan rigimar aunty, kin ga yaya Baba tamkar uba yake a wajenmu, ba Sa'an wasanmu bane, babu irin wannan maganar a tsakaninmu da shi, ba zan taba zuwa na nuna masa kina sonsa ba, ko giya nake sha, abu ne dake iya ja min komaima dan haakan raini ne, shi kuma baya so a raina shi, kawai ke ki same shi mana ko ita furerar ta same shi tunda ai itama kanwarsa ce ko?"
Ido Furera ta zarro tana fadin" ke kar ki sakani a halin ha'ula'i bayan ni ba kowa bace, ke idan kika yi duk rintsi yana jin kunyar Mamah "
Rukaya ta tsatsareta da idannuwanta ta ce" Me kike nufi da yana jin kunyar mamah? Ai kin san Baban gida ba futsarare bane, a gidan nan babu uwar wanda ya raina, sai dai shi a ringa neman gannin tabewarsa, wannan kuwa karyar dan Adam tunda Allah ya rika ya kuma iyayensa biyaya"
Itaama fureran sai ta ga ai kamar zaginta Rukaya ke son yi, a hayayake ta budi baki zata rama Laraba ta tare tana shiga tsakaninsu ta ce" Haba yan kanaina menene wannan abin dan Allah? Kunna abu a gaban bare salon ta dauke ku ta kaiku gaba ta watsa? Ku daina irin haka mana ai tataunawa muke yi dan mu samu mafita daya tak wace zata talafa mana mu isar masa da maganar ko?"
Furera ta ja hijabinta da Laraba ta rike tana huci ta kallo wajen da Zahra ke tsaye ta kalli wannan ta kalli wancen ta ce" Ke zaki bar mana nan ko ba zaki bari ba kin tsaya mana a kai kamar aljana kina kwashe mana sirri kamar kin hadu da shegu irinki, ki bace mana a nan tun kafin ranku ya bace !"
Ido ta rintse da karfi tana jin zuciyarta na rinewaa tana yin wani irin baki kamar zata mutu
Rukaya ce ta bude baki, a daken itama, sai dai ba zagi ta ce" Me kike so?"
Da kyar ta iya bude bakinta bayan ta bude idannuwanta da suka yi jajajir tana kallonta a sanyaye ta ce" Dama makaranta ne zamu tafi "
Rukaya ta dauke dubanta, dan hawayen da suka zubo a saman fuskar Zahrah sai ta ji kamar zasu girgiza mata zuciya , ta ce" Baki san kuma kun shigaa hutun bane? Bakwa yi sai an biya malamai!"
"Mtsssss aikin banza aikin wofi bata lokacin banza da wofi, ni da nice ke da zuwa zan yi na kama daki a wajen da za'a ringa biyana ina anfanuwa da dan lokacin da nake da shi tunda uwa bata so uba ba'a san waye ba bale in yi tunanin samun yanci irin na kowa!" Furera ta fada tana jijiga, dukkan bacin rai da tashin hankali na bayana a tare da ita, a duniya ta tsani ta budi ido ta ga wannan yarinyar, bata san me ta mata da zafi ba ama ta tsaneta fiye da komai!
Kaffaafuwanta dake rawa ta kai duke a hankali tana jimke hannayenta duka biyu tana neman hanyar da zata jure ta dauki wannan tashin hankalin dake mata yawo a kwonya
Anya kuwa zata aurun? Gaba daya daidaikun yan matan gidan nan sun tona mata asirin cewa ita shegiya ce
Anya kuwa ba bacin lokacin bane take wani karatu da sauransu zata gama ne ta tashi a tutar babu a banzar bazara
Wani lokaci Saude tace mata ta bi rayuwa a hankali idan aka wayi gari mahaifiyarta ta rasu ko ta bar gidan Docter tata ta kare fa, ta jima tana wannan tunanin daga baya ta watsar, a yanzu kuma sai kawai ya dawo mata a birkice
Kanta ta sake dagowa ta zuba masu ido, bama irin Laraba da Furera, gaba daya baki kirin take kallon gefen da suke tamkar an shafe su an maye su da baki
A zuciyarta suke kwana suke tashi da tsoro da fargabar haduwarta da su a gaban wani bako dan ta san da ta aikata da bata aikata ba sai sun yi sanadiyyar da bakon ya san wacece ita a gidansu cewarsu kar a lalatawa babansu sunna
Da kyar ta iya mikewa tana laluben hanya har ta ji maganar da Ma'awiya ke yi cewar ta bar masu wajen kar ta kula su ya tsinke, hakan na nufin ya katse kiran ne da ya jita shiru
Layi take yi har kamar zata kifa har ta karasa bakin bangaren matar da ta fi kowa jin tsoro a duniya, watau mahaifiyarta
A hankali ta idasa hawa taa shige balbalin dake iya sadata da kofarta ta kama ta murda tana jin hannun wajen murdawar yana da wani irin sanyi, bayan ba sanyi ne da shi ba jikinta ne ya kwashi zafi
Budewar kofar daidai da bugawar zuciyarta da masifafan karfi, ama battaa yi niyar juyawa ba, yau ko me zai faru sai dai yaa faru
A hankali take takawa bata iya yin salama ba tana hangenta a wajen diner tana gyagyara kayan girkinta da ta yi da kanta cikin kwonciyyar hankali sannan cikin shiga ta dogon hijabi har kasa kuma bulememe
" har kun dawo ne?, Kin ga ai har na gama fa ina jejerawa, ajiye min sakon a cen ki dubo min docter ya shigo ne na kai maganinsa" ta fada cikin zazakar muryarta mai fita da sansanyan amo da dan kaza kaza na matar da bata da kiwya
Jin shiru ya sakata juyowa dan ta ji an bude kofar ai da dan sauri dan gannin ko waye, domin mai aikinta ba mace ce mai shiru shiru ba, hasalima shegen surutu ne da ita sosai
Kofin dake hannunta na kwalba ne ya kubuce ya fadi kas, karar fashewarsa da watsuwarsa a ko'ina ya sakata binsa da kallo sannan ta sake dagowa ta zubawa fuskar Zahra ido, sannan ta juya da sauri tana harhade kwanonin du a rikice tama rasa me take yi a hade ta ce" Me ya kawo ki wajena?"
Fatima ta sake zuba mata ido, hawayen saman fuskarta wani na korar wani, a hankali ta budi bakinta dake rawa tana kallonta ta ce" Dan Allah, dan Allah ki taimakeni, ki sanar min wanene mahaifina? Koda mahaukaci ne, koda makaho ne, ko kuturu ne, ko dan daba ne, ko barawo ne, zan so na sanshi, na ganshi, na je inda yake, ta yiwu shi ya yi min uzuri ya yafe min zuwana rayuwarsa matsayin kadarars........."
"Idan baki fitar min a falo ba na juyo na zo inda kike babu abinda ba zai faru ba da ke, ki fitar min a falo tun kafin wani ya zo ya ganki a wajen nan!" Mahaifiyarta ta fada da karfin da ya sakata sake rintse idannuwanta jikinta na kwasar rawa
Da dan karfi Ζadan dan ta samu kwarin gwuiwar korar tsorin dake ruhinta ta ce" Tsintata kika yi? Waye mahaifina ? Dan girman Allah ki sanar min waye mahaifina..................?"
Juyowa ta yi a harzuke har tana taka kwalbar dake zube a hanyarta ta karaso da sauri da abin goge table din cin abinci ta daga shi ta shiga maka mata shi da dayan hannunta kuwa ta shiga hangazata tana turata tana sake turata ita kuma tana tirjewa tana hade hannayenta biyu tana dukawa hadi da fashewa da kuka tana neman riko hijabin mahaifiyar tata har ta karaso da ita wajen kofar shigowar ta saka dukkan karfinta ta hangazata da Hannayenta biyu hakan ya sa ta fito waje kafarta ta gurde wajen matatakala ta yi baya gaba dayanta hijabinta ya kwasheta ya makata da matatakalar nan ta ringa mulmulowa har ta fado kasa sannan ta lumshe idannuwanta tana fatan Allah ya amshi ranta a irin wannan lokacin tana kuma jiyo magangannun ma'aikatan da suka nufota a guje sunna kiran sunnanta cike da tausayawa da taimakawa suka suka kamata suka cicibeta suka nufi bangaren Hajia da ita wasunsu masu rauni na kuka, wasu na alhinin wannan lamari suka shiga suka tarar a lokacin Hajiar na kwasarta na matar Docter wace ta zo takanas tana fada mata cewar tana so a yi zama a cenza tsarin kwana bibiyu a mayar daidaya dan bata so, ba zai yiwu ace sai ta kwana shida kulun ta ga mijinta ha, gashi yanzu Docter ya kai wajen da yake gajiyawa da hidimar iyali dan tsufa ya zo shekaru sun ja sai a hankali ita rabonta da mijinta wata hudu kennan yanzu, shine hajia ke salalami ta rasa ina zata saka ranta dan kunya da tashin hankali har take ce mata ke yanzu me kike nema dama a waje Docter ? Ku ba jaraba ba ku tashi ku aure tsofafi da karfinku da komai su auna maku cikunna su barku da wahalar ya'ya a lokacin da kuka zo ganiyar son sasabawa da su ba? Ki je ku yi maganarku da sauran yadda kuka tsara daidai ne a wajen Zawaira dan yanzu kam ana ta kai wa yake ta kafa............
A irin wannan lokacin ne aka shigo mata da Fatima ZAHRA ranga ranga tamkar a summe
Hannu Hajia ta dora a kanta tana rungumo Fatima jikinta hankali tashe ta dubi wannan ta dubi wancen ta ce" Mota ce ta kadeta? Kai menene ya sameta? Daga makarantar aka dawo da ita ne? Yanzu fa ta tafi makaranta innalilahi ke Zahra, Zahrah "
Hankali tashe aka sanar mata abinda ya faru cewar daga bangaren Aunty amarya ne aka hankadota ta fado daga saman matakala
Kishiyar Mama sai leke take yi tana tabe baki tana son gannin kwaf
Mama kuwa hankalinta ne ya sake tashi, a rikice take ainun ta ce" Dan Allah ku fita, ku fita ku duka ku bani waje, ke salamatu idan kin fita ki saka a fito da mota a kaimu asibiti, Hajia kema ki je na gama magana kawai du yadda kuka yi daidai ne!"
Tana fada tana sake tarro Fatima a jikinta har aka sanar mata an kawi motar, a dole ta yarda aka kama mata suka dauketa suka saka a mota ta aika Ummi sanarwa Aba a wajen masalaci dan ya fita tuni
An amsheta an kuma bata kulawar da ta dace ta farfado aka yi mata allurar barci bayan an gyara mata gocewar da ta yi a kafarta ta yi wani irin sharrr da ita tana barci dogon karan hancinta ya yi zuwat da shi , dan siririn bakinta kuwa ya yi tsuwat da shi ya karra ja , sai ajiyar zuciya da take saukewa lokaci zuwa lokaci a cikin barcinta
Mama na zaune ta zuba mata ido, wani irin tukuki zuciyarta ke yi na balakin dake tafarfasarta
Ta yi kiran numbar Amir da Baban gida su kadai take jira a wajen nan, Amir ya zauna mata da Yarinyar nan babban gida kuwa ya bi bayanta su tarda ubansa da matansa ta ja masu kunne kwonsu da kwarkwatarsu, bata son rashin mutunci, idan aka shiga aikin nan da ita babu wanda zai ji dadinta, tana kiyaye shiga harkar yara dan gudun raini, to fa yara su kiyayeta walahi!
A kalla ta dauki minti talatin bayan an yi sallar magariba an kuma yi ta isha'i sannan sukka karaso
Docter Hajara ce ke yi masu jagora har dakin da marar lafiyar take suka shigo bayan sun nemi izini suka sauke dubansu a kan Mamah da ta mike tana gyara hijabinta daga saman salayar da Direba ya miko mata fuskar nan a hade sosai.
Amir ne ya yi karfin Halin budar bakinsa a hankali ya ce" Subahanalah mama harda karaya ba?, Me ya sameta ne?"
ππππππππππ
*DAΖIΖA BIYAR*
ππππππππππ
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin Ζai*
_12_
*Garabasa , garabasa, ππ₯°, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°π₯°π₯°*
Da kyar Hajia ta iya budar bakinta ta dube shi ta ce" Amir ka zauna min kadan bara na je na dawo, Baban gida mu je gida mu dawo a nan zamu kwana dan bugawar zuciyarta ne likita tace a hatsari"
Sai a lokacin ya kai dubansa inda take kwonce
Kallo daya tak ya mata ya dauke dubansa ya juya ya fara yin gaba har hajia ta sake barawa Amir salahun idan ta farka ya tsoratar da ita ita da shi ne, shi kuma ya yi murmushi kawai ya zauna cen nesa yana chating da wayarsa da amaryarsa jifa jifa yana kallon yar cikin zuciyar Hajia sannan ya maida dubansa kan wayarsa
A cikin motarsa kanshinsa ne ya cike ko'ina, tuki direba ke yi, su kuwa sun yi shiru a bayan motar a zaune
Du a tunaninsa wani abin hajia zata dauko in sun je gidan, shi yasa ya dan yi tsai yana tunanin yadda zai shawo kanta ta yi kwonciyarta a gida idan ya so nurse sa kula da y'ar tata har suka karaso gidan yana nazarin haka...........
Hajia na fitowa ta dube shi ta ce" Ka wuce mu je bangaren ubanka!"
Da sauri ya juyo ya dan zuba mata ido, sai a lokacin ya ga banda halin damuwa na rashin lafiyar y'arta akoy rikici a tatare da Hajiar
A ransa ya ayanna' Ya rab, Docter me kuma ka yiwa Hajia yau ne ?'
A fili kuwa da hannunsa ya yiwa sojawa biyun dake gefe alamar sunna iya tafia sannan ya shiga bin bayan hajiar da har ta kusa shiga bangaren Abah
Salama ta yi kasa kasa tana son yin kiran numbobin matansa da wayar Fatimah dake hannunta , sai ta ja turus tana kallonsu su ukun a zaune kowace na nuna isa irin na mace a gaban mijinta sunna zantawa ama babu Doctern a wajen ta yiwu bai shigo ba ko yana ciki
Bakinta ta bude ta sake yin salama a bayane tana karasawa ta ce" Au ashe kunna nan, masha Allah ya fadi kan kari ba sai na kirayeku ba"
Amsawa suke yi, sannan sunna gaisheta da mutuntawa harda wace bata cika yi mata irin gaisuwar nan mai daraja ba, domin wanda ke bayanta a tsaye ya gaje gaba daya kofar shigowar da shiga irin ta swuit ruwan toka a jikinsa ama farar rigar ta ciki ce kadai babu ta saman a jikinsa, dukkan wata kira da tsarin karfi na jikinsa ana iya ganewa, da dan sanyayan murmushi a saman lebensa mai alamu da jira yake su gama gaisawa da mahaifiyarsa sannan shi ya gaishe su, daya daga cikin halayansa da mahaifinsa ke alfahari da su kennan, girmama matan da ya kawo matsayin kishiyoyin mahaifiyarsa ciki harda wace ya girma ko zasu yi sa'ani da junna
Karar bude kofarsa ya saka du suka waiga hanyar da zai fito
Da dan sauri MarΓ©chal ya karasa inda mahaifinsa yake sannan ya tausasa tafiyarsa ya kuma dan rage tsayinsa ya kama hannunsa daya da bashi da sanda ya rike ta hanyar rike dukkan karfinsa a jikinsa yana sake kallon kaffafuwan mahaifin nasa da suke hayewa kamar baya shan maganinsa suka nufo falon ya kaishi wajen zamansa ya zaunar da shi sannan ya duka yana cire masa slifas dinsa da ya ga sun shiga kumburin kaffafuwan ya mike da su a hannunsa ya nufi dakinsa ya mayar ya dauko safa ya dawo ya duka ya sake kamo kaffafuwan ya dora saman cinyarsa da ya yi zaman rakumi ya saka masa safar sannan ya mike ya ciro wayarsa ya yi gaba da su kadan ya dannawa docter kira, hakan ya saka Aba dan cuno baki yana kallonsu ya ce" Yanzu zai hadani da likita a zo a yi ta jagulata shi dai bai yarda ubansa ya kai wajen da ciwuka sai dai a yi hakuri da su har rai ya yi halinsa ba, karfi da yaji shi sai Ahmadu ya yi lafiya bayan tsufa labari in ji hausawa"
Kusan kowace sai da ta ji ba dadi a ranta, a bayane kuwa suka ringa yi masa addu'a shi kuwa yana amsawa fuskarsa dauke da murmushi mai sanyaya zuciyar dukkan mai kallonsa
A nutse ya ce" Yau dai ga Hajiata da kannenta, Allah ya sa ba laifi na yi aka hadu a zane ni ba?"
Kai Aunty amarya ta sada, ita lamarin nan kunyar da yake bata Allah kadai ya sani, wannan wani irin kayan kunya ne matan Docter suka zo da shi? Kuma su du a tunaninsu idan har bai basu hakin aure ba to fa lalle itace kadai ke amshe daren kowa, ita da zasu rufa mata asiri da sun barta ta tashi ta tafi ta raini ciwon zuciyar da ta wuni da shi ko zata ji sanyi a ranta, basu san cewar tunda ta auri Docter babu wannan maganar a tsakaninsu ba, tunda ya kwatanta ya fuskanci tarin tsoronta a kan lamarin sai yake bin hanyoyi dan ya kwatanta mata cewar abinda take tunani ba haka bane, watau babu firgici ko tashin hankali a lamarin sai tarin ni'ima da kwonciyar hankali da samun nutsuwa wa junna
Hajia dai bata ce komai ba, sai wace ke dauke da ainahin maganar ce ta gyara zamanta da carbin dake hannunta ta dago ta dubi Docter a nutse ta fara magana duda karfin gwuiwarta ya so sacewa da ta ga Baban gida ya dawo ya zauna a saman kafet daf da mahaifinsa , sai dai sun riga sun zo ba zasu yi baya ba, kuma Docter ba wai tsufan shiruftaka ya yi ba, ko yaya ta bashi maganar zai gane tunda shi ba yaro bane
A sanyaye ta ce" Na kai kukana ne kan maganar kwanaki da ake yi bibiyu, cewar ni ina takura da haka ina so a mayar da shi daidaya ko zan gane wasu abubuwan."
Daga haka ta yi shiru ta dauke dubanta ta mayar kan carbin dake hannunta dan dagowar kan Baban gida ya sakata jin kamar zata nutse dan tashin hankali da kunya, daga shi har ubansa sun wani yi mata kuru kuru kamar ta yanka danyan ashar
Hajia ta ja numfashi tana kallon yadda Baban gida ya mike niyarsa zai basu waje kennan dan ta fuskanci maganar nan ba tashi bace
Da hannunta ta masa nuni kan ya dawo ya zauna tana fadin" Asalamu alaikum, Baban gida dawo zauna ni ba maganar da ta kawo ni ba kennan, ina da wata maganar mai mahimmanci da nake son yi a gaban kowa saboda bana so sai an yi gaba ace ban ce ba"
Dan sororo ya yi daga tsayen, sai kuma ya zauna dan Aba ne ya saka hannunsa ya dawo da shi wajen zamansa sannan ya dora hannunsa a saman kafadarsa yana dan bubugawa a hankali , sai kuma ya yi murmushi yana kallonta ya ce" Idan abinda ke kunshe a cikin dalilinki ne ya saka ki kawo maganar shin ke kadai ke dauke da ita ko da sauran baki daya?"
"Ba ni kadai bace docter, harda maman Furera gatanan , dan lamarin ya fara cutar da mu, ba zai yiwu ace walwalarka na tarewa a gaban wannan matar ba, bayan muma ba mutuwa muka yi ba" ta sake fada hankali Kwonce
Murmushinsa bai gushe ba ya kalli Hajia dake kallonsu da mamakinsu, sannan ya dawo da dubansa kansu baki dayansu ya ce" Alhamdulilah, wannan din ba wani damuwa bane, ina gannin cenzawar ya dawo daidaya ko bibiyu duka ba wani matsala bane in har kun samu yardar yayarku gatanan....., Babar matsalar daya ce tak, in dai kan lamarin shinfidar aure ne karma ku bata lokacinku da yawun bakinku a kan haka, domin nan da kuke gannina abinda yake iya samuwa ne kuke ganni idan har ranakunku ne, babu maganar zalunci ko tauye daya dan daya ta fi daya yarinta tunda na san mutuwa zan yi zan kuma gabatar