tana kallonta, muryarta a kasa kasa ta ce" Kin kuwa gane me nace? Ina nufin fa ABAH Docter?"
Fatima ta sauke ajiyar zuciya tana kallon hanyar da Furera ta bi, sannan ta sake duban Aisha a hankali ta dage nikaf din fuskarta ta mayar da shi baya sosai ta yadda fuskarta ta bayana sosai
Dan murmushi ta yi kasa kasa ta ce" duda duskana a haye ga kuma magani da aka shafa min, ama inaga ai ke din kin min farin sannin da kumburin fuskana ba zai saka na bace maki ba......., Shin a fuskar nan kin ga kamani irin na gidan ABAH? Inace kema da bakinki kikan ce kin rasa da wa nake kama a gidanmu, wani lokacin sai ki ga kamar ina yannayi da Maréchal sai ki ga aa ba wani yannayi dan kawai yana fari ne nima ina fara, daga baya saima kika ce gaba daya bana kama da kowa a gidanmu ko bama irin maganar nan da ke?"
Amsa ce dake bayane a saman lebenta, amsar da take yawan fada mata, ama a yau sai jikinta ya ringa yin rawa ta kasa zaunawa tana tsaye tana kallon Fatima
Farima ta saka hannunta ta zarro wayarta , hakan ya da Aisha zabura a tsorace tana waige waige, dan ba'a barinsu zuwa da waya makaranta
Datse kiran ta yi tana dubanta, a sanyaye ta ce" Aisha, bana tare da abinda ya dace ace na cika iya yi da hobara da takama!, Asalima ina yawan yin shiru dan bana so bakina ya ja a san usulina!, Tabas bani da wata kalma da zan furta dan kare kaina, duda ban san lokacin da aka aikata laifina ba, banma san yaya aka aikata shi ba, dan soyaya ne ko dan kadara ce ta yan dakikun da basu zarce biyar ba?, Abinda na sani ni fai gani nak, mutun ras ina raye, mace mai raunin gaske, a tsakiyar wa'inda suka kasa amsata, ita daya tak ke zabga min mari idan na nuna ni bare ce a cikin ƴaƴanta, kuma ita suke yiwa kallon marar kirki, itace tak ke janyoni ta min nasiha har tace na rufa masu asiri kar na tona masu asiri, sai manyan ƴaƴanta maza d anake rasa shin neman hanyar da zasu kasarani suke yi ko gyara ne irin nasu haka?, Aisha ban sani ba, wasu lokutan shagala kan sakani neman yin abu tamkar nima y'a ce kamar kowa, sai an wayi gari masu laushin cikinsu sun ware su uku sun barni ni kadai a gefe, na fi kaunar in labe idan sunna sabga ta fito na fito dan ina tsoron na fito mahaifiyata da kanta ta mayar da ni dan magana ake ta mutunci ba tawa ba!, Aisha shin nice datin bayan ido na bude na ganni nima a cikin bayin da ubangiji ya halita dan mu yi masa ibada?, Nakan ji kamar nice na yi sanadiyar zuwana duniya ba wai kawoni aka yi ba, Aisha a haka kike so na shagalta wai har ni Zahrah na dubeta na mayar mata martani a kan maganar da karfi fa yaji suka saka na yarda cewa eh haka take kuma haka zata dawama har na mutu wato *NI SHEGIYA CE KUMA BA'A SAN WAYE UBAN NAWA BA?!*, na yarda, na amince, bani da ja, in sha Allah kuma ba zan taba yarda na yi zaman aure da mai uba ba, dan kuwa zan fi so na zauna da irina komai rintsi ba zai min gorin nasaba ba!,....." A hankali ta saka hannunta ta share hawayen dake zuba a saman fuskarta ta dora da fadin" Aisha ai sun min kokari, sunna kan yi min, ki tuna waye ABAH a kasar nan, suka yarda nake cikinsu, duda ba shawararsu aka tambaya ba, a haka na yi bake bake da dukkan abinda suke da iko nima mai ikon ce, nake rayuwa a tare da su ba dare ba rana, sun min kokari da suka rufa min asiri basu bi ta kowace hanya suka koreni titi nake bin kwararo kwararo dan samun wajen kwanciya ba, sun rufan asiri da suke bani abinci, sutura, tsafta , uwa uba tarbiyya, babu fa abinda na nema na rasa sai UBA da kuma MAHAIFIYA..............." ta idasa wannan karron lebenta na balewa da wani irin bari hawaye wani na korar wani a saman fuskarta
Kiran dake ta shigowa ya sakat dauke idannuwanta daga kan Aisha dake kuka ksmar zata summa dan bigawar zuciya da jin wannan bakon labari kamar almara na tashin hankali
Muryarta a shake ta daga ta ce" Dan Allah baka san idan ka yi kira daya biyu uku hudu ba'a daga ba ka daga kafa ne?"
"Dan girman Allah kar ki yi fushi da ni a kan laifin da ban san na yi maki ba, Fatina ina kofar makarantarku daga baya dan Allah ki zo na sanar maki, kin san Allah tun daga jiya har zuwa yau ban rintsa da idannuwana ba, hankalina a tashe yake, na fita ina waya da abokina yana fada min magangannun banza na matsa ina masa masifa dan ba zan so ace kin ji abinda nake fada masa ba na dawo na tarar da bakya nan, na bi ta kofar gidanku ya fi a irga karshe na tafi dan saina ga kamar yayanku dayan nan soja a kofar a tsaye kuma motar tawa yake kallo, Yanzu dama zaki iya yin fushi da ni mai tsanani haka a kan laifin da ba nawa ba? Ki tuna fa ba ni na fada ba koma meye ya bata maki rai, tun jiya har zuwa yanzu ban ci komai ba, ban sha komai ba, ban samu nutsuwa ba kwata kwata, haba dan Allah matatah, ki yima Allah ki leko na duka har kasa na baki hakuri, in ba haka ba yau ina iya shiga gidanku sai dai a harbe ni!"
Yaya kuke so na kamanta maku girman shiga zuciya da karfin iko irin na samari masu irin halayar nan? Yaya kuke so na yi maku kwatance abu mafi karfi a duniyar yan matanmu? Garari mai girman gaske wanda ko wuka a wuya bai isa ya datse ba, kalaman ire iren wadinnan nada karfin da sai lokaci ke bambance masu me yake boye, idan ido ya rufe akan makance wani lokacin sai mai aukuwa ta auku, tashin hankalin da baka gani bale ka rike ka jijiga ka maka da kasa!
Du irin ruri , turiri, tashin hankalin da take ciki sai ta ringa jin lalle kamar ta yi gagawar yanke hukunci cikin fushi bayan yana da gaskiya bama shi ya yi mata wani laifi ba
Duda haka sai ta yi iya yinta murya a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri, tarayars da kai ba zata taba iya yin nisa ba, a jiya yayanmu ya ga shigowata ya kuma yankan kashedi a kanka, ka yi hakuri dan lafiyarka da tawa baki daya, Allah ya ba ko.......
"Aunty FATIMA, tun dazu ina nemanki ashe a nan kike? Ki taso ga mota cen daga wajen aikin ABAH an zo daukarmu, innalilahi wa inna ilaihi raj'une ni kam hankalina ya tashi, ance gaba dayanmu a daukomu!" Ummi ke fada sai yawo take hankalinta a tashe
A zabure ta mike, ko kashe wayar bata yi ba ta bi bayanta da gudu suka nufi waje inda katuwar Bus din Masalacin Docter Ahmad ke parker du sun shige itane ba'a gani ba dama, shi kuwa direban ya ki tafia dan ba zai taba tafia babu daya a cikin motar ba
Yadda take gumi jikintama rawa yake yi, saima da ta ji Baba lawal ya daga waya a sanyaye yana amsawa yana fadin" Amen ya Allah, aa in sha Allah da yama za'a yi sutura a nan dai gidan DOCTER, eh in sha Allah, to sai kun zo...." Sai kawai motar ta nemi rikicewa da kuka gaba daya kowa tambaya yake yi wa ya rasu? Baba lawal Docter ne ya rasu? Mamana ne? Yayana ne? A dakinmu ne? Hajia ce? Tambayoyi dai a harhade a dole ya taka birki dan kar su saka shi ya maku da wani wajen a sanyaye yaa dube su ya ce"
Ya ALLAH......, Wa ya rasu?😭😭😭😭
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
*DAƘIƘA BIYAR*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_8_
*Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰*
A dole baba direba ya ja birki a sanyaye ya ce" Rukaya kece baba ama harda ke a rikicewa bayan a nan babu wanda bai san Kullu nafsin za'ikatul maut ba?, Ku rage ihu mana ku yi addu'a, matar Baban gida ce Allah ya yiwa rasuwa"
Lalle mutuwa babar aya ce dake girgiza bawan da Allah ya nufa zata saka ya ji darr sanadiyar zuwanta waje, ita ko yaya ta kawo ziyara ko makiyi ta dauka zaka ji zuciyarka ta girgiza, koda baka yi hawaye na soyayar wanda ka rasa ba zaka yi hawayen ganninsa kwonce bashi da ikon yin komai sai yadda aka yi da shi, hakan na nufin abinda ya tardoshi na nan yana jiranka ko ba jima ko ba dade......, Hakan ne ya faru da iyalan DOCTER AHMAD SULAIMANE,
A maganar gaskiya babu wata shakuwa a tsakaninsu da matar Baban gida, hasalima harta ƴaƴan dakinsu ba zasu ce ga wani abu da yake hadasu da ita ba, ita dai mace ce mai matukar kula da kanta da kuma lamarin mijinta kawai, a lamarin mijin natama babu tarikitan danginsa, nata dai ana kula, ama nasa sai yadda hali ya bada ne, ama a haka motar ta dauki shiru sai kukan daidaikun da suke da matukar rauni, sai ko umartarsu da Rukaya ta yi kan su yi mata addu'a, Allah ya kyautata makwoncinta, su da suka rage Allah ya sa su yi kyakyawan karshe........, Da wannan suka dauki hanya dab karasawa gida
Tunda suka tunkaro gidan tarin jama'ar dake kofar ya sake tsintsinka masu zuciya
Taron masu kaki ya fi yawa a cikin tafiyar, sai datawan malamai da manya manyan yan kasuwa da sauransu, tuni an nemi dinke anguwar da al'umma tamkar yanzu yanzu za'a rakata makwoncinta, bayan tana asibiti saima an kimtsata za'a zo da ita a salaceta sannan a kaita makwoncinta na gaskiya
Sai da ya shige da motar har cikin gida, sannan ya tsaya a cen hanyar da mutane basu fiya kai kawo ba
Yana gama parking suka ringa saukowa bayan ya bude Bus din, kowace na nufar bangarensu rikw da hannun y'ar uwarta ko sun jejera kusan tare
Hakane ya kasance da su, su hudu suka nufi bangaren Hajia , su ukun sun fita sauri sosai, ita tana cen baya jiki a mace tana jefa kafafuwanta ne kawai har ta shiga itama tana sauke idannuwanta a wajen da kuka ke tashi irin mai tsuma zuciyar nsn mai saka bawa fashewa da kuka koda bai so ba
Idannuwanta ta mayar wajen yan uwanta, ko tace yan uwan mijin mamaciyar, sun karasa jikin hajia sun tsuguna sunna masu nuna alhininsu da kuka mai tsuma zuciya
A hankali idannuwanta suka sauka a kan Bugun zuciyarta, mamalalin numfashinta, jini da bargonta, sanye da zumbulelen hijabinta kamar yadda ta saba a koda yaushe, tana rike da carbi da kuma tissu a hannunta , da kula ta kama yan matan nan biyu ta ja su tana yi masu maganar rarashi da ban baki ta nufi hanyar sama da su tana umartarsu kan maza su je dakunnansu su kimtsa kansu su dauko Alkur'aninsu su dawo kasa su hade da masu karatu a yiwa mamaciyar gatan da ya fi komai dadi, watau a rakata da addu'a da fatan alkhairi
A sanyaye itama ta karaso ta duka tana dage nikaf dinta, muryarta a sanyaye bayan ta kalli Mamah ta ce" Mamah, yaya hakuri? Allah ya jikanta da rahama, Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareta..............".".".."."."."."
"Ke tashi!" Ta ji muryar wace zata rantse nan da wata biyuma bata yi mata koda kallon banza bane bale har a kai ga magana
Kasa kasa ta yi maganar, sai dai wa'inda ke zaune daf da Mamar dole su ci, ciki harda maman su Furera, da maman Azima
Sai a lokacin ta ga irin kallon da suke yi mata su biyun nan, wani irin kallo da ta saba ganni a idannuwansu, tamkar masu jifanta da kallon tsana, ko tace na kyankyami, yanzu kuwa harda harara harara haka..................
Da sauri ta mike, tana gannin kallon da Mamah ta bisu da shi, kallo ne mai dauke da wani irin ruwan tausayi a cikin idannuwanta, sai dai halin da ake ciki ba zata tashi ta amsheta ko ta yi fada dan ana daf da yi mata abinda ya dace da ita
Ky din dakin take ta murdawa hannunta na rawa, gabanta na dokawa,
Da kyar ta iya budewa ta saka kafarta a hankali da nufin shiga ta yi taga taga da karfi ta je ta fadi a daf da abin fitilar tsakiyar daki
A tsorace ya dago dubanta ta sauke a fuskar Matar da ta haifeta, kallo ne mai tafe da tsoro da tashin hankali
Itama rai bace ta dubeta a kausashe ta ce" Kar na kuma gannin kafarki a cikin gidan nan da sunnan yawo ko zaman makoki , ba a falo cikin mutane ba, harta a tsakar gida bana son ganninki har sai an yi taron nan an gama, domin ba zaki ringa zuwa waje kina wanzuwa ana yi maki kallon san karrin bayani har a hada da ni ba!, Ki barmu mu ji da damuwarmu bana sin ganninki bana son jinki kin ji abinda na fada?"
Jikinta na rawa take gyada kanta, har mahaifiyarya ta juya ta fita ta mako mata kofar nan da karfin da ya sakata sake jin tamkar zata summa dan tashin hankali
Kuka ta ci mai ratsa zuciya, tun bata fuba lokaci har ta dawo duba lokaci da aunawa a kwakwaluwarta cewar a yanzu ko menene an riga an yi, watau an yi sutura................
Lamari na bawa, sai ta ringa tunanin inama inama ace itace? Da ace ta san me abinda zata tarar a karkashin kasa ya fi sakawa zuciya salama da nutsuwa da ta yi fatan zuwa da wuri wuri ba sai ta karra shakar iskar duniya ba
Sai da ta gama wannan, sannan ta sake dawowa tunanin shikenan kennan babu fita tamkar y'ar kaso? Dan ta kasance abin kunya ba zata fita ba ko dan ta sha iska?, Dan ta aikata laifi ba zata leka nan da kofa ba?, Laifin zuwanta duniya a matsayin shegiya? Wai menene baban aibun da wace ta kawotan nan take kyankyaminta har haka? , Kennan zata zauna ne ba abinci bale mu'amala da jama'a koda ba zata shiga sabgar kowa ba ka ringa gannin wulgin dan Adam ma ai arziki ne......
A hankali ta ringa sauke hucin wahala ta mike ta daura alwallah ta haye salayarta , dan ta gabatar da sallah , a cen kasan zuciyarta kuwa ta riga ta karra yarda Mahaifiyarta ba zata taba dubanta ba a duniya!
A wannan rana ta ga rayuwa, har sai ta tuna lokacin baya kafin ta je bara wajen DOCTER AHMAD SULAIMANE, a lokacin da take wuni a boye da yinwa
Sosai abin ya so rikitata har ta manta cewa a dakunnansu babu wanda zai rasa dan abin tabawa kama daga madara da biscuit da ake ajiye masu bayan na kicin, dan dukkan kokarin iyayensu dan su ji dadin zama a gefensu sunna yi, har sai da dare ya raba tsaka , shiru ya wanzu a kowani lungu da sako sannan ta tino, a galabaice ta karasa wajen ta wawuro ta nufi bayi ta cika kofi da ruwa ta kada ta kafa kai sai da ta yi nak ta ajiye ta dawo gefen gadonta ta zauna tana ambaton Allah da zikiri har barci ya yi awon gaba da ita cikin salamar zuciya, dan kuwa babu damuwa ko tashin hankalin da zai ziyarci bawa ya kasa samun sauki idan ya sanarwa ubangijinsa
Washe gari, har kusan karfe goma, yan gaisuwa na ta shigowa, yayan gidan du sun zo sun gaishe da masu zaman makoki , harda mahaifiyarta dake nan da yayarta, da yan uwanta du sunna nan, ana ta shige da fice ana ta sadaka da karatu ba ji ba gani gata irin na malamai tana samu ta ko'ina hankula du sun karkata a nan, har sai da sha biyu ta yi sannan Mamah ta kula cewar rabonta da Fatima tun jiya, yau yayan gidan sun yi ta sunturi bara ganta ba, nan hankalinta ya dan so tashi ta yi kiran auta ta aikata dubo mata ita
Kwonkwasawa Ummi ta yi, sannan ta yi salama ta dakata tana jira
Jim kadan ta ji karar bude dakin da ky, dan haka ta tura ta shiga da salama a bakinta tana sauke dubanta a kan FATIMA
Tsaye take da doguwar riga mai siririn hannu, kanta sanye da hula irin ta kulun zare kore mai haske ya rufe gashin kanta ruf, dogon karan hancinta ya yi zuwat da shi sai kyali yake yi, fuskarta sai fitar da annuri take yi duda kumburinta da kuma kumburin wajen idannuwanta ama annurin bai bace ba, ta kalli litafin dake hannunta litafin hadisi ne mai larabci ziryan sannan ta idasa shiga dakin tana jin kanshin da yake fitarwa da kuma sanyin da yake dauke da shi
"Ummi lafiya?" Fatimah ta tambaya da muryarta fake kurya, hakan ya sa Ummi sake juyowa tana kallonta, a hankali ta ce" Lafiya kalau, dama Mamah ce tace bata ganki ba tun jiya na nemo mata ke ko lafiya?"
Idannuwanta ta lumshe, tana karyata zuciyarta dake ce mata koda zata shekare a dakin babu mai nemanta , da ace itace ta rasu babu mai yi mata addu'a har ta samu wani sansanyan murmushi ya subuce mata a hankali ta ce" Aya, ki ce ina daki ina so na yi sauka ne kafin sati, ga kuma karatun harda da zamu bada ta bagara a makaranta".........
Ummi ta kureta da ido, haka kawai sai ta ji ta kasa yarda da maganar,
Ita dai ba wata yarinya karama bace gaskiya dan yanzu haka shekarunta goma sha biyar......., Takan gane wani abun da aka so bata shi a baibai , bale lamarin FATIMAH zata ce ta fi sauran fahimtar wacece ita
Wajen gadonta ta duba, ta hangi dan kayan kwalam da makulashe da masara da kofi.......
Ta san mahaifiyarta na wajen nan kwonciya kawai ke mayar da ita bangarenta, itace a tsaye a kan komai, sauran matan na Aba kowace a nade take tana mus mus da baki sai utace ke kai kawo da bada umarni a dukkan abinda ya dace, ta kuma san babu halitar da take tsoro irinta, itama babu halitar da ta ki jinnin waigowaa ta gani irinta, ita da kanta ta sha sheda marin da ta dauka na mahaifiyarta dan kawai ta gaisheta, har sai da ta daina gaishetan idan ta ganta har sai ta bar waje take dago kai, ta tabata da wani abin, hakan ya sa ta ce" Aya Allah ya taimaka Aunty, ama ki ringa leka Mamah kin san fa ba zata karbi uzurinki ba, bata son irin hakan, ko ba wannan bama kema ai bai dace ki shige ciki ki labe ba bayan rasuwar matar Baban gida ne, ya dace ace kina cikinmu ana sauka ko?"
Tsareta kawai Fatima ta yi da ido tana sauraronta da mamakin furucinta, uhum ita? Idan ta je ai zata tsinci rashin hankalinta a hannunta dan ta tabata sai sun gwada mata bata da wayo walahi, wannan lamarinma gata ne tana gannin akai mata gwara ta zauna inda Allah ya ajiyeta
Haka fai Auta ta gama ta fice ita kuma ta rufe dakinta ta koma bakin abinda take yi, jiya zuwa yau ta yi kuka ya fi a irga, idan ta yi kuka sai ta yi karatu, in ta gaji sai ta yi ta rawatawa a cikin dakin tana ciro kayanta ninkaku tana sake ninkewa dan dai kar zaman ya zame mata damuwa ne
Ci gaba ta yi da karatunta har rana ta yi
Tana kallon madarar nan tana jin ta gundureta , ta shiga tunanin me zata ci? Yaya zata yi ta samu? Aka buga mata kofa a karro na biyu da salamr muryar Ummi
A gajiye ta mike ta karasa ta bude kofar ta dan ja baya tana kallon Ummin da ta shigi da plate mai dan girma dauke da flask na abinci da kuma wani dauke da miya, sai cokali da goran ruwa manya biyu ta kai t ajiye mata nan kusan kwalin madarar bata ce nata komai ba ta dawo zata fita, a nan ne ta iya budar baki muryarta na rawa a hankali ta ce" Ummi, na gode, Allah ya saka da alkhairi"
Ja Ummi ta yi tana jin zuciyarta na neman karyewa, ai kuwa ga tabacin abinda take tunanin, ta yiwu mahaifiyarta ce ta hannata fitowa
Subahanalah, shi yasa take gannin beken da yawan mutanen gidan nan da suka tsangwameta, da ace zasu fuskanceta su barta da zafi mai zafin gaske tsana irin ta uwama da sun tausaya mata sun taya ta da addu'ar samun sauki, ama du sun saka mata ido ba tare da ta yi masu komai ba, bata zaune a kansu, bata tsare samunsu ko lafiyarsu ba, sunna manta kadara idan har abinda ya kawota duniya ya same su yaya zasu yi? Ita bama ita ta aikata ba ama tana kwasar tashin hankalin duniya da mutanen cikinta, to da itane ta aikatan yaya kennan? An fi tsangwamarta fiye da mahaifiyarta ko dan mahaifiyar tata bama zaka ganta ba sai in ta kama ne ita kuma dole zata fito ta cudu da kowa ko dan zuwa makaranta?, Tana matukar tausayawa wannan baiwar Allahn, gaba daya rayuwarta abin tausayi ce, gata da wuyar sabo da wuyar sakin jiki, kusan tsoron kowa take ji a gidan dan an tsangwameta
Dubanta take yi har dai ta dan yi alamar zata rufe sannan ta sauke ajiyar zuciya a nutse ta ce" Mamanki ne tace a kawo maki, kuma tace saura ki rike byro har ciwon kanki ya tashi ta gamu da ke...." Ta karashe tana dan sakar mata murmushi, ta kirayi Mamah da mamanta dan ta ga réaction dinta, so take ta taimaka mata ko yayane
Ai kam ta ga ta saki dan murmushi tana sada kanta, a hankali ta ce" In sha Allah Ummi, na gode"
Itama murmushin ta sake yi ta juya ta tafi da katon hijabinta kamar zai taketa ta fadi
Har sauri take yi wajen bude abincin
Da dan sauri ta zuba ta tankwashw kaffafuwanta ta yi Bismillah ta ringa ci tana sauke ajiyar zuciya har sai da ta ji cikinta ya cika daidia misali sannan ta kwashe ta kilace sauran da niyar shi zata loda da dare domin girkin tai mata dadi a bakinta ko dan tana jin yinwa ne?
Dana wannan lokacin sai matsalarta ta dan rage, harma ta amsa wayar saurayinta tana amsar gaisuwar da yake yi mata da neman izinin sake kiranta da dare, a nan ta amince suka yi salama ta yi zurru tana tunanin rayuwa....kai gwarama ta yi hakuri da fushin nan da take yi da Ma'awiya ko zai maida hankali ya nemi aurenta ta karra gaba, domin idan har ta biya fadan yaya Amir haka za'a zo a wanke yan matan dakin nan kaf tana gantali har a zo kan Auta, a lokacin ne kuma abinda ake mata ikirari zai tabata, watau Y'AR ISKA
Magariba na yi Auta ta sake zuwa ta kawo wanu abincin, sannan ta dauke kwanukan na ranar da sauran wanda ta rage dan ci da dare, daga nan ta sake sakin ranta ta fuskanci karatu kala kala dan samun nutsuwar zuciyarta, takan bude window ta zubawa masu kai kawo ido tana kallo, idan ta gaji ta koma ta yi kwonciyarta har aka yi kwana uku , aka yi Adu'ar sati, sannan gidan ya fara ragewar jama'a har ya zamto sai su ya su