Share this page
3 / 9
tana kallonya, a sanyaye ta ce" Nafila ne Mamah " Hajia ta gyada kanta ta juya tana sake kallon kofarta ta ce" An fi son nafila idan dare ya tsala, a lokacin da babu hayaniya babu yawan kai kawo, a irin lokacin da wasu bayin ke barci kai ka kokarta ka mike ka gabatar, ka nemi lahira sannan ka nemi duniya, a irin wannan lokacin Allah ya fi amsar addu'ar bayinsa kin ji Zahra?" Kai ta gyada tana sadda kanta Hajia ta dan yi jimmmm ta ci gaba fa fadin" Ba zan taba gajiyawa da tunatar da ku baban abu mafi mahimmanci a rayuwar y'a mace ba, shine mutunci, Zahrah ki kasance cikin bayin da zasu rike mutuncinsu domin Allah, ko me kike ciki ki ringa fadawa Allah sannan kina kokarin kiyaye hakokin adinninki, ke mace ce, kina da daraja sosai, Allah ya yi ki mai rauni sai dai ya dora maki aiki mafi daraja a duniya, shine haihuwa da tarbiyantarda, idan ka tuna zaka haihu wata rana, zaka bada tarbiya sai ka sake kame kanka, ka ci gaba da kare mutuncin kanka, dukkan abinda sauran dunniya zata dubeka kuwa ko menene ka musu uzuri, mafi wawan cikinsu shine wanda ya shagala har ya manta cewa Allah baya kare halitar bawa da daina dora masa jarabawa har sai an saka shi a cikin kabarinsa, FATIMAH na san kina fuskantar abubuwa fiye da tunanin kwakwaluwarki, ki ci gaba fa addu'a ki daina kuka sannan ki rike amanarmu mu iyayenki, ki yi mana adalci, ki yi kokarin saka mana ta hanyar kare mutuncin kanki kin ji?" Wani irin rauni ne ya daskare zuciyarta, da kyar ta iya amsawa Mamah har ta tashi ta fita ta rufo mata dakin tana sake kallon yannayin kofarta da tunanin lalle da wahala idan ba fita ta yi ba, sai dai tunanin ta ina ? Ya dakata kawar da wannan tunanin ta ci gaba da ziyartar sauran dakunan yan matanta, su uku ne dama sai ZAHRA ta hudu, a cikinsu babu wace ta yi barci, wayama suke yi sai Ummi auta dake karatu dan tana fa exam gobe, dukansu kuma da sun ji alamun motsin hajiar sukan boye abinda suke yi ne, sarai tana fahimta, itama cikin nata hikimar take ta yiwa tufkar hanci da kuma tsayuwar dare tana rokon Allah ya kare mata, dan abu ne ya riga ya zama gama duniya, ko baka ba yaron waya ba za'a bashi a waje, Docter dai ne baya son zance, ba'a yi masa zance, idan ka tsaya da saurayi an kusa aurenku ne kawai, shima ba wai da dare ba, no, zaka zo ne da yama ku gaisa ka tafi, sauran maganar kwa yi a waya, shima ba wai masifafiyar wayar nan ba Fatima Zahra kuwa, Mamah na barin dakinta ta samu kanta da fashewa da kuka har ta kasa zama da kyau sai da ta kwonta tana nade jikinta a cikin hijabi Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, shin me yake damun kanta ne? Me yake faruwa da ita ne? Ko dai dan abin ya taba nasabarta ne ya sa yake bibiyarta? Yaya aka yi yai har Ma'awiyah ya ci galabar sakata fitowa a irin wannan lokacin daga gidan shehin malamin da ake koyo da tarbiyar gidansa ta tarda shi? Da ace ya daneta a cikin motar nan ya yi mata wata muguntar kuwa me zata dubi wannan matar mai daraja ta ce mata?, Yaya zata ce da matar da ta rungumeta bayan mahaifiyarta ta tsangwameta ne? Ita ta san idan ta dauko abin kunya Allahn da ya haliceta da kuma Hajia sai Abah sunne wa'inda zata ji tsoron haduwa da su, shin menene wannan masifar dake bibiyarta ne? Ita da kanta ta san tana yiwa Ma'awiyah son da ya dace ta daidaita ko dan rayuwa, shin idan har ya gujeta yaya zata yi kennan? Yanzu haka tana tsintar magangannun da basu yi mata ba sam, idan abu ya sake rikicewa yaya kennan?? Da kyar ta iya samun barci, shima mai wartar nan ne mai wahala bayan ta yiwa kanta alkawarin duk rintsi ba zata kuma fita da dare haka ba, gwarama su rinha haduwar yammarsu kamar yadda suka saba in har ta ci gaba da kulashin wai! _________________________________ A gajiye ya karaso gidansa, hakan ya sa bai leka bangaren matarsa ba, duda ya san sunna da baki yan uwanta da suke nan yau kwana hudu kennan Wanka ya yi, ya saka jalabiya a saman karamin wando sannan ya fito dan zuwa wajen diner, domin shi a rayuwa baya wasa da lamarin cikinsa, sai kuma ya yi Sa'a ya fado kan wace take iya yinta a harkar girki, gaskiya bata da laifi a lamarin sarafa hannu, wannan ya sa yake girmama girkinta sosai Yana zama ya shiga bubudewa hadi da zubawa abincin ido yana nazarin yau kuma wani sabon salon aka girka masa ne? "Barka da zuwa mijin Manal" ta fada a lokacin da ta shigo take karasowa a hankali sakamakon ciwon da mararta ke yi tamkar zata zage gida biyu, kai lalle ta sarawa maganin matan nan na wajen yar uwarta, lahauli da ta sani da bata sha shi da wuri ba walahi, gayanan yana neman fasa mata mararta Dan murmushi ya yi yana zubawa , bai ce komai ba har ta ja kujera ta zauna tana sake kashe idannuwanta da salon kisa irin tamu ta mata ta ce" Yaya gajiya, yaya aiki da fama da mu?" Dan tsai ya yi yana kallonta,....tana acting like mai rikaken wayon nan, ..... Lokuta da yawa takan kwatanta irin halayan nan idan tana cikin bukatar wani abu mai girma ko tana son tafia mai tsayi......., Abin ya kasun masa gida biyu, na farko ya yi tunanin kirsa ce irin ta mata.......sai daga baya ya fahimci idan ta yi haka tana tunanin cin galaba dan ta girme shi da shekara biyu......, Shi kuma yana matukar jin dadin zuba mata ido idan tana irin haka, dan yana son hakan......ba dan komai ba sai dan karra karantar *WOMEN* da yake yi rana zuwa rana daga wajenta "Oga, wai dog din nan bayar da shi zaka yi da gaske? Bayan kana son sa sosai?" Ta sake fada cikin yannayi na tsantsar kisa, da layewa abu dan cinma wani abin irin namu na mata "Yeah" ya bata amsa a takaice yana sake daukan abincin da ya masa dadin dandano a bakinsa ya sake kaiwa bakinsa ya ci..., Wato zai iya cewa zab'insa yana tafe daidai da tsamaninsa, ko yace baban kokarin zabinsa na kayatar da shi daidai misali........, Ta kasance wace ta ci gasar iya sarafa abinci......., Tana daya daga cikin manyan masu yiwa yan mata nasiha.................., Ba laifi tana yin iya kokarinta dan tafiyarsu ta yi karko, kuma yana yaba hakan Sake sauke dan ajiyar zuciya ta yi, ta ce" Gani na yi du cikin karnukan nan babu wanda yake da kishi da iya ba ababen kiwon nan tsaro irinsa, ba'a isa a tunkari wajen kajin cen manya ba fa, sosai yake bada tsaro a wajajen nan, sauran sunna bin bayansa ne......" Ruwa, marrar sanyi ya sha, a hankali ya lumshe idannuwansa yana adu'ar godiya ga Allah, hannunsa daya kuwa a saman shafafen cikinsa , tamkar ba a ciki aka zuba abincin ba, asalima idan kana kallon cikin sai ka dauka baya wani ci, dan gida gidan nan na masu gymn ne da shi, dama su in dai zasu rike shi dole sai da abinci mai gina jiki sosai, in ba haka ba kuwa akoy matsala Manyan idannuwansa ya dauka ya sake dorawa a kanta, yanna kula da ita tunda ta shigo tana yawan dan tsamure fuska, sai kuma ta yi gagawar saki in ta kula zai dubeta A hankali ya ce" Kin sha maganinki kuwa?" Yannayin da ta shigo da shi na tabaci da sannin abinda take yi ne ya so kubuce mata, sakamakon tuna mata da ya yi a yanzu haka a irin zaman da suke zama ne dan an yi da wajewa ya buga ya buga itama ta ja ta ja cewar ta yarda ba maganar haihuwar, ba dan komai ba dai dan a lokacin aurensu basu je suka yi gwaji ba, sai a bayan aurensu aka tabatar da jinninsu irin jinnin nan ne mai dauke da cutar da idan suka haihu tare yaron na iya rayuwa cikin wahala, eh lalle abu ne na gwaje gwajen zamani, sai dai gaskiyar itace hakane!, Yaron na iya zuwa duniya da cutar nan mai karfi watau cutar kashi, ita ke dauke da mai karfin watau SS, shi tasa sunnan yana da ita ne kawai , kasancewarsa mutun mai kokari da sport da komai, sai ya zo masa da sauki, inma ba ya yi niyar tunawa ba akan mance cewar yana dauke da ciwon, damuwar daya ce idan har suka hadu suka haihu zasu samu yaro mai ciwon mai karfi, yawanci za'a zo a yo ta wahalar rayuwa da yaron, astagfrulah lamari ne na ubangiji domin da yawa sun take, wasun kuwa haka za'a yi ta fama yau da gobe, yau da gobe sai hamdallah, wannan abu da aka gani ya saka shi shiga tashin hankali a lokacin da ta taɓa yin wani bari, saima suka tsaya a matsaya guda cewar zasu tafi a haka....watau babu haihuwar, domin ya yi ya yi ya sawake mata ta nuna yanzu ta ga wajen zama, tana daukan magani ne na hanna daukan ciki, wanda ba kulun ba dan wani sa'in saima ta manta da shi kwata kwata, bama irin yanzu da yayarta ke cewa a kan me zasu yi haka? Ta tabata Docter Ahmad bashi da labari, da ya sanar masu ai komai na Allah ne, itana ta san mijinta bashi da wajen gannin rauni irin yara, shi yasa ya zabi kar ya haihun a haka. A sanyaye ta ce" Na sha" Dan tsai ya yi, sai kuma ya kawar da maganar ta hanyar fadin" Auren su Aba karami ya tashi......" Nan take yannayin fuskarta ya so cenzawa, da kyar ta iya kokarin kawar da maganar tana fadin" Oh wauh har auren ya tashi? Masha Allah kace bana akoy aurw aure, yan matan uku ne ko?" Da idannuwansa kawai ya amsata, Ita kuma ta ci gaba da magana ta ce" Masha Allah, bana muna da shagulgula, plz mijina kar ka saka rana daya da na gidan aunty, dan abin zai cakule min , yanzu haka kai kawai take jira da maganar kayan auren ƴaƴan nata ta koma a ci gaba da shirye shirye, ina gannin a cen garin su mahaifinta za'a yi daurin auren" Dan tsai ya sake yi da abinda yake yi ya sake dubanta, .......ita fa haka take, da ake cewa mace na daidaita lokutan tambayar abu daga wajen mijinta, ko ta kasance mai ragewa mijinta wani kashe kashen....., Noh, banda tashi matar, hajiar gidansa bata da wannan tsarin a cikin tsarin rayuwarta, yana gannin irin wannan taruwa ta yan uwanta ya san da walaki, ama bai yi tunanin kayan dakin ƴaƴan yayarta ne zai yi ba, tunda a sanninsa ai da ubansu, ko dan bata gidansa ne za'a yi abu irin na gadarar nan,a nuna masa shine talaka ba'a son nasa?........ Lalle da sun fado babu nauyi, domin ba zai yiwa ƴaƴan kadajen gidan aure ba, domin mahaifinsu da rai, yana da halin haka, ya kuma isa da gidansa, ba zai taba zamowa mai kama masu wajen yada wasu manufofinsu na jin dadi ba "Ba zan yi gadaje ba, ba kuma zaki kayade min abinda ya dace na yi ba" daga wannan ya mike ya sake yin samansa dan hutawa Cikinta sai da ya nemi hautsinewa, idan aka hada da ciwon da yake yi mata, ga kuma wannan magana mai son saka bawa hauka sai ta nemi zubewa a kasa daga saman kujerar bata shirye ba A zabure ta mike tsaye hankalinta na neman dugunzuma ya tashi dan bata yi tunanin haka ba ko kadan Da sasarfa take taka matatakalar, zufa na keto mata, cikinta na sake rikice mata har ta haye ta tura kofar dakinsa a sanyaye dan ba zata taba yarda ta shiga da girgirwar kai ko isa ba, Yana sanye da kayan barci ne riga da dogon wando, yana shirin kwonciya ya juyo ya zuba mata idannuwansa a fuskarta A dan birkice ta so fara magana tana dan dudukewa, sai kuma ta dafe cikinta a rikice ta ce"... *Alhamdulillah.* 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐 *DAƘIƘA BIYAR* 🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐 _MALLAKAR_ *SAJIDA NIGER* *Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai* _5_ *Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰* A dan birkice ta so fara yin magana, tana dan dudukewa, sai kuma ta dafe cikinta a rikice ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, subahanalah, wayo Allahna cikina, marana" Da sauri ya sake kafeta da ido yana dubanta yana mai tabatarwa kansa bata da lafia ne ya sa tun dazu take dudukewa sai kuma ta maze, Da sauri ya tako yana tarota domin kana kalo zaka gane ba wasa take yi ba, ba kuma da gangan bane gaba daya jikinta ne ya ringa wani irin bari tamkar ana girgizata ga wata irin zufa dake neman tsatsafo mata "Hey, hey, hey bb.......menene? Menene?" Yake fada a lokacin da ya riketa sosai a jikinsa yana jin wani irin nauyi da take dauka, jikinta na ci gaba da karkarkar, tamkar yana saki ne , hankalinta na neman gushewa daga gangar jikinta A yan sekwanin da basu zarta biyar ba ta nemi sumewa a jikinsa, lokaci daya ya cicibata ya dauketa ya fito da ita da mugun sauri yana tafe yana sake talabeta har ya fito wawakeken filin gidansa, Sai da ya fito ne ya rasa ina zai nufa dan samun mota a kusa ? a kalla zai iya yin gudu na minti shida kafin ya karasa wajen da ake kilace motocin, Sake riketa ya yi sosai a jikinsa, kasa kasa ya furta" Sorry b, zan maki ihu......" Ya bude muryarsa mai karfin gaske ya ce" SERGENT!, SERGENT!, SERGENT!" SERGENT dake tafe cen nesa kadan yana cikin masu gadin yau ya juyo a rikice jin muryar ogansa a irin yannayin da bai saba ji ba in ba wani tashin hankali yake ciki ba A guje ya karaso yana son gane abinda yake faruwa Da sauri ya juya yana daga wayarsa ya yi kiran wanda ya tabata ya fi shi kusa da wajen motocin gidan ya sanar masa maza maza ya amshi ky yanzu yanzu ya zo bangaren Sir da koma wace mota ce Kafin kace mene yan uwanta dake bangarenta sun fara fitowa da daidaya hankali tashe, domin ihun da ya yi ba na wasa bane du ya amsa gidan, Abinka da mata har sun fara neman rikicewa, da kyar auntynta mai bi mata , maman amare wace bai fi shekara biyu ta bata ba ta dakatar da su ta hanyar daka masu tsawa ta kora su ciki ita kuma ta shige motar gidan gaba tana ta waigowa hankalinta tashe tana gannin jurwayin jinnin da ya bata jikin Maréchal , hankalinta ya sake tashi ta maida dubanta gaba jikinta na rawa, direba ya ja su suka nufi asibiti Baya kwaramniya, tun wannan kira da ya yi da karfi bakinsa ya dinke sai addu'a da yake tofa mata bayan ya rungume fuskarta a kirjinsa hannayenta cikin nasa yana dan massaging A hankali suka silala wajen da za'a amsheta bangaren emergency Sunna tsayawa aka gurguro gado aka dorata cikin gagawa likitoci suka shige da ita a babar asibitinsu ta sojoji Zaune yake, kansa na kallon kasa, Carbin hannun Docter Habunakar ne a yatsarsa yana ja a hankali Dare ya tsala sosai, sai daidaikun masu jinya dake dan kai kawo dan wani uzurinsu, suma daga inda yake zaune a baban office din docter Habubakar yake hangensu, gaba daya jikinsa tamkar babu lakka, wani irin sensation marar dadi yake ji a jikinsa kamar wanda wani abu ke tunkarowa, ........ yakan dafe gaban goshinsa, sai kuma ya saki ya ci gaba da jan carbinsa Basu jima sosai a ciki ba Docter Habubakar ya shigo office din bayan ya dan buga Maréchal ya bashi izinin shigowar Rigarsa ta likitoci ya cire yana dubansa da kula ya ce" Baka dan ringesa ka rintsa ba Sir?" Idannuwansa ya lumshe, da sukai masa luhu luhu da abin barci, da na gajiya, da na tashin hankalin halin da take ciki, a hankali ya ce" Me yake damun MANAL ne Freind?" Zama ya yi sosai a dan daf da shi yana fuskantarsa ya ce" I'm sorry, ta yi miscarriage ne" ................."Bari?" Ya tambaya tamkar bai san yaren da ya yi masa bayani da shi ba Docter ya gyada kansa ya ce" Eh, bari ne ta yi sakamakon wani magani da ta yi matsi da shi mai karfi, a bincikenmu dai inaga irin magungunnan nan nasu na mata ne da kulun muke wayar masu da kai a kansa, ya dace ka dora doka mai tsanani a kan iyalinka ka kuma wayar masu da kai a kan harkar magungunan nan, domin wannan maganin da ta yi anfani da shi ya matukar shigeta da karfi ne, yanzu haka maganar da nake yi maka fama da muka yi dan mu fitar da shi ne ama bamu ganshi a jikinta ba, ga wani irin jinni baki baki fa ya hadasa mata,......" Ya takaita dan so yake yi ya yi masa bayani yadda zai fahimta da kyau harma ya yiwa tufkar hanci a gidansa, watau ya hanna matarsa rarume rarumen magungunnan nan , yanzu kai ya waye, in ba abinda ka sani ba ka kiyaye wawura daga ance maka yana yi ka maka, baka san menene ba, baka san yaya zai amsheka ba!, A nutse ya ci gaba da fadin" Namiji, a wannan zamani mata sun dauki lamarin sex a aure da tsanani tamkar shine kadai zaman auren, ban san me yasa haka ba, ta yiwu laifinmu ne mu maza? Ta yiwu kuma wani ikon Allah ne daban ke tunkaromu,......abinda ke damuna a cikin lamarin shine sanadiyar magungunnan nan babu abinda bama gani, sun ki su fahimci ba komai ne za'a fada masu su tashi su afka kai tsaye ba, sun kasance basa Tiktok, basa whatsup, basa nan basa cen du a cikin binciken magungunnan da wata ta fito tace ta yi ta ji dadi, ko wata kasurgumar mai siyarwa ta basu tabacin nata mai kyau ne, a kan harkar magungunnan nan sunna iya kashe makudan kudi fa, wasunsu sun dauka cewa shine kadai zamantakewar auren....." Ya idasa maganar a tausashe, domin gaskiya yadda take fitar da wani irin bakin jinni sidik ya tsorata , har da nurse din nan sosai, shima abinda ya saka shi saka su shigar da ita wajen bincike a yau yau din nan, dan dole ya san abinda ya hadasa mata abin nan, watau ya san girman hadarinsa ko dan gaba, bari ciwo ne mai tsanani, ama bai kai wajen da zai saka mutun a hali na rashin sannin inda kansa yake har kusan awani ba, bayan an tsayar da risk din, an kuma yi allura Shi kam abin ya girmami tunaninsa, tunda ya yi tsai tunanin abin ne yake yi a cikin zuciyarsa, Bari?, Bata shan maganinta kennan?, Bari? Dan ta yi anfani da wani maganin mai hatsari?, Yanzu shine Manal ta dauka a shashashan namiji ko? Watau ya kai wajen da zai dora mata doka a kan abu dan lafiyar kanta da kuma gudun su haifo dan ya zo ya yi ta fama da rayuwa dan rashin lafiya, a zauna a yi magana a kan abin ta tashi ta yi fatali da kafarta?......shin ta manta baban abinda ya sa ya yarda zamansu zai je daidai dan ta girma ta malaki hankalin kanta ba zata ringa hada masa ciwo biyu bane? ........... Gaban goshinsa ya dafe, a hankali ya mike daga zaunen da yake ya dubi docter ya ce" Man, yaya jikin nata ne ? A magangannunka ban ji ka sanar min da sauki ba," Docter ya ce" Alhamdulilah, in sha Allah komai zai daidaita, da sauki tunda an ga menene matsalar, ana kan shawota ne, an yi mai wuyar tunda an saka abin a kan hanya" Gwauron ajiyar zuciya ya sauke ya sake zama yana jan carbin nan A hankali Docter ya ce" Man kana iya tafia gida ka huta fa, ka san munada masu jinya yanzu haka mutun biyu na bar mata a dakin jinyarta, ana ganninka an san ka gaji....." Dan murmushi ya yi yana tuna gaskiya yau ya gaji, tunda ya fita bai zauna ba, fitar karfe shida na asuba, ya zo zai kwonta din ne jikinta ya kiya Mikewa ya yi ya mika masa hannu suka yi musabaha, sannan ya juya da carbin yana fadin" Zan shigo da safe in sha Allah, kafin nan ina fata zan ringa samunka phone....... thank you man" Daga haka ya fice a office din, ya zagaya ya fice kwata kwata a asibitin ba tare da ya koma dakin da aka ce auntynta ta zauna ba A hankali yake tafe yana duban gari har ya dakatar da wani dan acaba ya haye ya sanar masa anguwar da yake so ya kaishi Shigar dare ya yiwa gidansu, hakan ya saka shi shigewa bangaren mazan gidan ya yi kwonciyarsa saman doguwar kujera yana ci gaba da jan carbinsa har barci barawo ya yi awon gaba da shi bayan ya gama tunanin ko me Amir ke yi yana kai kawo a bangaren cen? Da asuba bayan sun fito daga sallar asubahi shi da ABAH da yan uwansa sunna tafe a tsanake ABAH na fadin" Subahanalah, baban gida bara mu karasa maza a shirya a je asibitin, Allah ya sawaka, ai da ka sanar min tun jiyanma Baban gida sai kawai ka yi shiru abinka sai yanzu?" Dan duban wajen da kanninsa watau Général AMIR ke fige wata zabgegiyar bulala ta dalbejiya da ya karyo ya yi sannan ya amshi hannayen kannensa dake dukawa har kasa sunna gaishe shi da Abansu, zakakun samarin gidansu yan makaranta da zarar sun gaishe su sai bi bayan su, shi da Abansu dake tafe A hankali Docter Ahmad SULAIMANE kasa kasa ya ce" Abahna, ka ga cen dan uwanka ya yi bangaren hajia, Allah ya sa ba cin zalin Y'ayana zai je ya yi ba" Idriss ya yi dariya kasa kasa, dan shi ya san kwanan zancen, shi kuma Maréchal bai bi ta kan wannan maganar ba, so yake yi ya raka mahaifinsu ciki ya dawo ya gaisar da Hajia ya wuce asibitin dan gannin yaya Manal ta tashi Da dan sauri yake nufar bangaren Hajiar, har yanzu kayan barcin ne a jikinsa masu ruwan madara, sannan har yanzu kanshin turarensa na jiya bai bar jikinsa ba, Yana tafe yana amsa gaisuwar ma'aikatan gidan da yan uwansa da yan amsar karatun safe har ya isa ya kama kofar dakin ya bude Saka kafarsa ta dama ya yi daidai da saukar karar marin da Amir ya wanka mata da karfin balaki ya rintse idannuwansa, lokacu daya kuma ya bude ya sake dorawa a kanta yana kallon yadda marin ya ratsata har ya sakata kifawa daga tsugunnin rakumin da ta yi tana firi firi da idannuwanta Gabansa ne ya kwonci kwonci ya fadi, a hankali ya bita da ido a lokacin da ta kifa din sannan ta saki wani irin sansanyan Kuka mai ratsa zuciyar koda makiyinta ne bale masoyinta, uwa ko uba, yaya ko kani........... "Au, ni zaki yiwa tsayaya ko?, Bari ki gani! , Ba zaki sanar min uban waye shi ya fitar da ke tsakiyar dare ba? Ki yi magana dan walahi in baki yi bayani ba sai na kakaryaki yau a gidan nan!" Amir ya fada da karfi har yana mikewa ransa na sake dugunzuma A hankali ya dauke kansa, ya kuma dauke idannuwansa, ya cire kansa kwata kwata daga wajen ya idasa shigowa a nutse yana dan dakatawa dan jin gaba daya sun kwashi miko masa gaisuwa harda

Chapter 3 of 9