Share this page
9 / 9
a kotu a kan yarinyar nan! Kun ji na fada maku!" Hankalinsa ne ya tashi, ya kure Aunty Amarya da kallon tuhuma, wace nan da nan hawaye suka bale mata kanta a sade sunna diga a jikin hijabinta Dubansa ya maido kan Hajia ya ce" Me ya faru? Auta ke ce min kun je asibiti na zata ko ciwon nan nata na mara ne dake kaiku lokaci zuwa lokaci?" Rai bace Hajia ta ce" Babu ciwon mara, abinda ya ainahin faru na san ba zamu taba sani ba sai a lahira, dan ita ba zata fada min takamaiman me aka yi mata ba, abinda na sani shine ta je wajenta ita kuma ta hankadota daga kofa wajen matatakala ta mulmulo ta fado a summe, yanzu haka maganar da nake yi maka likita yace sai mun kwana zuwa gobe dan bugawar zuciyarta ya ki daidaita, a cikin barcima haka take sauke ajiyar zuciya, wannan wani irin masifa ne, a kanki aka fara samun y'a haka ne? Menene laifinta ita? Ko menene matsalar ne? Idan bakya son ganninta ba sai kin wulakantata ba, danma d'a da uwa ne har take duban inda kike, da wata ce ba mahaifiyarta ba na rantse maki ko gawarki ba zata bi ba , haba dan Allah haba jama'a, ku kuma da kuke sakin jiki kunna wasa da kishi saboda uwarta kunna wulakantata ku sani Allah ba ruwansa da kai wanene ko ga dalilinka ita din da ta haifeta sai Allah ya saka mata irin cin zalinta da take yi bale ku, wanda aka zalinta zai sakawa ko ba dade ko ba jima!, Kuma mata ne, kuma kun haifi mata da cikunnanku, ku kiyayi yiwa lamarin ubangiji shishigi, dan Allah ya haliceta a haka ba dan ya tsaneta ba, dan ta kasance haka ba dan ta aikata laifi ba, haka yake son ganninta, tata salon jarabawar kennan, Kasancewarta a tsakaninku kuma wata jarabawarku ce, idan kun dage ku sake dagewa zaku gani a kwaryarku!, Yarinya dai babu inda zata je Docter da ya kawota ya kireta yarsa a gidan ubanta take in kuma akoy wace ke bata kwondala ta daina daga yau na yafe, walahi walahi kun ji na rantse idan har matar nan ta fada a gabanku ta kuma fada a gaban docter a yau cewar eh ta bar min yarinyar cen ni kuma zan sake kilaceta zan kuma sake rungumarta, ko ya'yan da na haifa suka zageta sai na yafe su duniya bale ku kishiyoyi! A nan zaku san ainahin wacece Zuwaira, shiruna ba tsoro bane ba kuma gabana aka shiga ba!" Lahaula wala kuwata ila bilah, ai fadanta mai sauki ne a kan wanda ABAH ya dauka Hankali tashe yake masifantarsu yana karawa, tambaya yake yi haka suke zaune ba tausayi ba jin tsoron Allah? Tambayarsu yake yi me ta masu? Tambayarsu yake yi cikinsu akoy wace ta isa ta zagaye idan Allah ya hukunta haka a gareta? Fadi yake yi bara su ji kar su ga sun dauki shekaru sunna gidan miji, ko haihuwarsu ta tsaya babu ruwan wanda ya halice su in suka kawo lamarin wulakanci a hukuncinsa lalle zai nuna masu shi ya halicesu shine da iko da gaban jikinsu ya dora masu abinda suke zagin halitarsa dominsa ya ga yaya zasu yi? A hankali ya rike hannun BABAN GIDA da ya mike ya rike nasa yana kallonsa a tausashe da aika masa duban ya rufa masa asiri ya daina magana da karfi kar ya jiwa kansa rauni A hankali ya ringa sanyayar da muryarsa har ya juyo kan Aunty amarya dake kuka bilhaki Muryarsa a tausashe ya ce" Ashe zan iya neman alfarma ki kasa yi min? Kafin na sanki yarinyar nan na sani a masalacin juma'a tana zuwa bara, hankalina ya tashi da aka kawo min maganarta aka nunan cewa samari sun fara shiga sabgarta , a lokacin na saka aka bita aka gano inda kuke na nemi ganninki da karin haske a kan abinda aka fada, a lokacin yaya muka yi da ke?" Sosai take hawaye, tana sharewa muryarta a sarke sosai ta sake sada kanta ta ce" Dan Allah ka yi hakuri" "Ba hakuri nake so ba Nana , so nake yi ki sanar min yay muka yi da ke?" "Ka min nasiha, ka min fada, ka kuma nunan ilar barinta tana yawo, ka nunan ilar hantararta da korarta da hannata kwana a inda nake, ka kuma nunan zaka talafa mana da taimakon muhali da abinci in riketa in bata tarbiya,......." Ta dakatar da maganarta tana zuba masa ido, kukanta na daukan wani irin yannayi mai zafi da kunna tana kallonsa ta ce" YAYA ZAN IYA RAYUWA DA ITA TANA WACE YAYAN MAHAIFINA YA YI MIN FYADE NA SAMETA?" A haukace kishiyoyinta gaba daya suka zuba mata ido sunna zarro idannuwansu, su dai sun san y'a bata da uba ama basu san haka zancen yake ba Baban gida kansa sai da ya zuba mata ido na dakikun da suka zarce yadda yake kallon mutumen da ba muharaminsa zuciyarsa na bugawa a tsayen da yake ya juyar da dubansa yana kallon baya gaba dayansa ya lumshe idannuwansa A sanyaye ta dora da fadin" a lokacin na nuna maka nima abin a rike a bani tarbiyar ce domin nima nawa nake? Inada shekara tara na haifeta a lokacin da muka hadu da kai bata wuce shekara takwas ba ni kuma sha bakwai a duniya, ka juya ka tafi dab sama mana salama da mafaka, ni shaida ce irin yadda ka ringa nema min mijin da ya dace ya zauna da ni da zuciya daya, ama a lokacin kowa sai ya kiya dan ya san ni din dati ce ga kuma wani datin, .................................................. Aban baban gida Sanadiyar cikinta da na samu ta hanyar wayo da akai min, yayan mahaifiyata ya hadani da shi , yayan mahaifiyata fa Docter, yayan mahaifiyata................" Sai kawai ta sarke, ta fashe da wani irin kuka ta ringa fitar da numfashi sama sama kamar zata summa Hajiar ce kuma ta mike ta amshi ruwan da Baban gida ya dauko ya bude ya miko sannan ya juya ya basu baya hannunsa daya a jimke a bayansa dayan kuwa a cikin aljihunsa yana kallon garu har sai da tarin da take yi ya dan tsagaita, cikin muryar kukan ta ce" Sanadiyar fitowar maganar nan fili Mahaifiyata ta fadi ta mutu da ciwon zuciyar da bamu santa da shi ba, dama mahaifina baya raye, dangi suka kore mu dan kar abu ya fito a shiga uku, shi kuma ya karyata ya zauna a garinmu mirsisi aka yarda da fadarsa ba tawa ba........ A dole na baro garinmu na gudo ama abu ya biyoni an san wace ni wa nake riko ama an dauka a matsayin ta yiwuma karya nake ubanta ba daya bane da yawansu dan ai dai sunnanta shegiya ba yar halal ba............., Sai da ya kai aikatau ya gagareni samu dan na ci abincin bakina, saima lalatatun maza dake bibiyata burinsu mu lalace tunda sun ganni rungume da y'a sun gama gannin karuwa............., Ba zan taba yafe masa ba,, ita kuma wace ka ba sunnan nan ba zan iya dubanta a yanzu ba, na koreta na sanar mata ta barni na samu nutsuwa zan sanar mata abinda take son sani ta ki ta fahimta , shin idan na sanar mata cewa Yayan mahaifina ne ya yi min fyade har ta zo duniya ita zata iya daukan wannan maganar a zuciyarta ne ko tana tunanin zata yi darajar da zai dubeta ya watsa mata kwata ne?, na fada a tsaye na fada a zaune ina bukatar lokaci ban shirya fuskantar lamarin nan yanzu ba ama an ki a fahimta?, .................." "Wannan din ba shine hujarki na wulakantata ba!" Baban gida ya katseta da karfi, ya fada a karro na farko tun wanzuwarsa a wajen , murya a dake, rai a bace, kirjinsa na yin sama yana yin kasa, yana kallonta da idannuwansa rinanu masu dauke da ruwan bacin ran da ya zarta misali Idannuwansa da suka yi ja ya sake dorawa a kansu baki dayansu ya ce" Maganar nan ta dawo hannuna sannan ta zamo sirri a tsakaninmu, domin idan ta fita ta shiga kunnenta cewar waye mahaifinta a tsakaninmu ne ta fita, idan na san wanda ya fitar da ita sai inda karfina ya kare, zan ja da shi a hanyar kotun musulunci, hanyar iko, hanyar dabanci har sai na yarda cewar dukkan wani burbushin abinda zai iya zamtowa farin ciki a duniyarsa ya kare kaf sannan na barshi koda zamu yi mutuwar kasko ne ni da shi!!" Ya idasa da dan karfin da ya saka gaba dayansu hankalinsu tashi suka ringa kallonsa a tsorace banda Hajia da Aba dake dubansa tsigar jikinsu na tashi, hajia kuwa tana mamakin dama ya iya fada da karfi haka? Ita kuma Aunty amarya da sauri ta sake shigewa jikin hajiar tana hade jikinta da yake neman sake kwasar rawa Gefe ya maida dubansa dan kallon da mahaifinsa ke yi masa na son sanyayar da gabansa, a hankali kamar yadda ya saba masu magana a da ya ci gaba da fadin" Ya dace mu iya rike dukkan wani sensation da émotion dinmu a gaban yaran nan, ku sani ko me zaku ringa aikatawa tarbiyantar da su kuke yi a haka, irin halayan nan kuwa ba kowa zai jure zama da mace a haka ba mu kuma ba kwadasu zamu yi mu cinye ba! Daga Aunty karama har zuwa aunty j ku zauna da ita da zuciya daya, kar ku daura fitina a kanta ku rayu hankali yadda kuke so, itama ku barta rayu hankali kwonce kamr sauran ya'ya a gidan nan, yadda zan kare hakin Rukaya haka zan kare nata, idan ta samu miji a aurar da ita ta yi tafiyarta dakinta, bana son a kan maganar nan a sake saka ABAHNA a gaba ko mu sake irin zaman nan da ku, ko ba komau ai iyayena ne ku ba zamu yi haka ba, sai dai ku fahinta bana son na sake tsayuwa a kan lamarin nan da ku daga babarku har karama...................... *ITAMA Y'A CE, KUMA MAI YANCI CE* baku san wa zai talafeku gobe ba, baku san wacece ita Allah ya baku ba.......so ku mutunta ko ku zuba mata ido shi nake umarta!" Daga haka ya juya wajen Abansa da ya zuba masa ido yana sauke ajiyar zuciya yana kallonsa nutsuwa na ratsa shi da kwonciyar hankali, ya riga ya sani ne ko yau ya fadi ya mutu yana da tsayaye a cikin ahalinsa A sanyaye ya furta" A huta lafiya, in sha Allah satin gaba zamu fita harkar ƙafafuwan nan, a fara shiryawa" Nanma bai tsaya ya ji jayayar Abah a kan maganar ba ya fice a falon gaba daya ya nufi wajen motarsa ya shige domin tuni an bude masa ya yi tsai yana kallon hannunsa dake jimke yana jiran fitowar Mamah Tsuru tsuru suka yi a falon, kowa na kallon kowa har sai da Hajia ta gama yarda Baban gida wanke su ne ya yi tasss ya yi tafiyarsa, ta ja numfashi ta mike ta nufi wajen wayar Fatima ta dauka ta kalli Docter ta ce" Allah ya tashe mu lafia Aban Baba" Murmushi ya yi yana sauke ajiyar zuciya, ya zata zata ce kana kallo ya mana tasss kaa kyale shi? Sai ya ga bata yi mitar haka ba, hasalima murmushi ke boye a ni'imtaciyar fuskarta tana kallonsa A sanyaye ya ce" To uman Sulaimana sai da safe in sha Allah zamu yi safiya mu zo mu ga Baiwar Allah, Allah ya bata lafiya yar gidan Ahmadu" Da amen ta amsa ta yi gaba ta barsu a nan, Da mamaki matarsa ta ce" Yanzu docter kana kallo Baban gida ya ja mana warning ya mana ihu a kai baka ce komai ba?" Ido ya dan zarro ya ce" In ba abinki ba nima baki ga cewa ya yi maza a shirya ya kaini gannin likita ba?, Idan kuwa da magana Nana ta daukon wayata na kira maku shi ku zanta....." Kumburo baki ta yi ta cire kanta bata bashi amsa ba, shi kuma ya yi murnushi ya dora da yi masu nasiha da sake jaddada masu a yanzu ba ruwansa idan sunna so su ci gaba ko su daina su da Baban gida, kuma walahi kar su yarda su ga fuskarsa dake boye, wace basu sanshi da ita ba, hakan ba zai masu da dadi ba Su din kansu wani irin shaku da tsoro da tunanin me zai same su idan sun aikata ya ji labari suke Ai kam kowace ta dauri niyar koda zata muzgunawa yarinyar to fa a boye ba dai a bayane ba, ita din kanta mahaifiyarta ta yi niyar ba zata kuma yi mata abu mai zafin haka ba, zata kiyaye dan irrin yadda yake gannin mutincinsu ba zata so su dawo yar tsama ba, da wannan dai du suka mike suka barshi da wace ke kwana a bangarensa yau ___________₦₦₦₦ Shiru, shi ya fi yawa a cikin motar har suka karaso asibitin A hankali Mamah ta fito daga motar bayan an bude mata ta yi tsaye ta ga ya fito shima sannan ya tsaya yana magana da wani mutun dan Kasuwa da ya zo yana gaisar da su harda Maman Gaba ta fara yi ta karasa kofar dakin da Fatima ke kwonce A hankali ta dakata da bude kofar da take son yi tana sauraron muryar Amir dake magana a nutse ya ce" Fatimah, dan ba lafiya sai ki ringa hawaye?, Ki daina kuka mana ki yi addu'a sai ki ji sanyi na ciwon kin ji ko yar gidan mamanta?" Dan murmushi Mama ta saki ta murda zata shiga ta ji muryar Fatima tana hawaye, da kyar ta iya budar bakinta ta ce" Cewa suka yi wai idan aunty amarya ta bar gidan ABAH ko ta rasu ko Aban ya rasu shikenan tawa ta kare sai dai na koma na kama daki wai, kuma da na je auntyn ta sanar min inda mahaifina yake sai ta koroni tace bata son sake ganina a ind.... A inda take wai" Amir a hankali ya dakatar da maganar da yake yi ta whatsup ya dubeta da duba irin na tsanaki, A lokacin da zai yi magana, magana irin ta sanyayar nata da zuciya, da sanar mata cewa kar ta saki ta dauki haka a matsayin damuwa da sauransu Marechal ya karaso yana fadin" Mama baki shiga ba?" A dole Mama ta bude dakin ta shiga da salama muryarta na fita a sanyaye tana kokarin kawar da damuwarta ta dubi wajen da Amir ke zaune nesa da gadon Fatima sosai, sannan ta kalli Fatiman tana karkaro murmushi ta ce" Zahra kin farka?" Amir muryarsa a sanyaye ya ce" Ta farka mama, da saukina ko Zahran mamanta?" Fatima ta lumshe idannuwanta ta kasa cewa komai dan dodonsu ya shigo dakin ya yi wani kikam yana kallonta bai kuma ce komai ba Baki ya tabe ya ce" Ta tashi mu je gida, ba zaki kwana a nan ba Mamah" Da mamaki Mama dake ciro mata madara mai sanyi daga frij ta dago ta dube shi ta ce" *ALHAMDULILAH, DAGA NAN NA TSAYAR DA FEEE BOOK, NEMI NAKI HAJIATA KI SIYA MU PANTAMA MU MORE TARE......., AKOY CAKWAKIYA A TAFIYAR NAN MAI ZAFIN GASKE...., TO WAI ABINDA ZAI FARU A DAKIKA BIYAR DIN YA FARU KO A GABA? MENENE SHI? MEYE MA'ANAR HAKAN? ME DAKIKA BIYAR KE IYA HAIFARWA?, MUN SANI NE ƊAKIKA BIYAR NA IYA TARWATSA BAUTA TA SHEKARA DARI, KAMAR YADDA TAKE IYA SAKA BAUTA , TABA IYA LALATAWA KO DAIDAITAWA, TANA IYA WANZAR DA ZAZAFAR SOYAYA KO TA KASHETA.......A ƊAKIKA BIYAR KOMAI NA IYA FARUWA, .......KU ZO MU JE MU JI LABARIN NAN DA SOYAYARSA A ZUCIYARMU DA SHAUKI🥰😁, taku ce yar mutan NIJAR SAJIDA* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9