na gidan sai dangin marigayiyar
Yau kwana takwas da rasuwar, ra fito daga wanka tana ciro kayan wankinta da take so idan an rage ta kai ta zuba a machine Γ laver ta ji an bude kofar an shigo da salama
Da sauri ta juyo tana amsawa sai kuma ta yi saurin sada kanta sakamakon wanda ta gani.............
ππππππππππ
*DAΖIΖA BIYAR*
ππππππππππ
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin Ζai*
_9_
*Garabasa , garabasa, ππ₯°, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°π₯°π₯°*
Da sauri ta juyo tana amsawa, sai kuma ta sada kanta sakamakon wadda ta gani atsaye tana yi mata kallon tuhuma
Mamah kuwa dake kallonta tawasali take sake yi ga ubangijin talikai, Allah da ya halici bawa, ya yi baki ya yi fari sannan ya kawata halittar su
Tabas Fatima Zahra tana cikin bayi masu kyakyawar hakita da nutsatsen zanen halita, tun daga yannayin tsarin halitarta har zuwa gashin kanta masha Allah ta keru , a dole zata sake dage mata da addu'a domin wani lokacin kyauma yakan janyo wata masifar idan ya yi yawa kuma aka ringa wasa da shi ba kula da kiyaye bakin duniya
Ita babu abinda ya dameta da wani nasabarta, yarinya fa bata da laifin komai, haihuwarta aka yi, idan ta fito ta wannan hanyar a hanyar zuwam duniyarma ta hanya rikitaciya watau a zamantowartama shegiyar ta rikitacen hanya ba yanna nufin an shawarceta ba bale har a tsangwameta, burinta Allah ya wanke miji ya bata na gani na fada mai adini da tsoron Allah ko masu kyamatarta sa ji kunya da tsoron lamarin ubangiji, sam bata so a cikin kadarar yarinyar wani mugun abu ya sake fitowa a tare da ita komai kankantarsa kuwa, shi yasa take kafa kafa sannan take yin addu'a da dukkanin karfinta dan ta san bata isa ta kare ba sai dai Allah ya kare mata
"Bana son gaisuwar, shin Auta bata sanar da ke nace ku ringa saukowa cikin mutane ba? Ke kennan kin fi kaunar kauracewa mutane ko? Ba zaki daina wannan banzan sabin ba ko? Meye kike yi a dakin sati guda? In na hayo da dare har kin yi barci, gashi da sasafe nake sauka a lokacin na tabata kina azkar, meye wannan sabuwar akidar ne? Bana so fa"
Kanta a sade take ba Maman hakuri tana sheda mata tarin karatun dake gabanta ga sauka da ta yi ita kadai a dakinta, wannan ya sanyaya zuciyar Maman har ta umarceta kan ta sauko yau maza ta shiga kicin ta dama waina ta yi sadaka, ai ba'a yin sauka ba'a raka da sadaka ba
Da wannan Maman ta sauka, ta barta da zulumin sauka cike da tsoron kar aje ta sake hadewa da mahaifiyarta, duda ta san da wuya yau kwana takwas fa kennan da yin rasuwar
A kalla ta dauki awa sannan ta fito sanye da hija mai doguwar riga, irin hijaban nan na Turquie masu fadi da kyan gaske, ruwan kasa ya kama fuskarta dasss ya bude hananyenta a cikin hannun hijaban mai roba mai tsayi, ya dai amsheta sosai hijabin, kafarta kuwa dauke da safa fara kalll irin mai velours din nan mai kyau, sai dan sansanyan kanshin turaran da take yi ta idasa saukowa tana tafiya a hankali ta nemi nufar hanyar kicin din, sai dai bata kai ga nufar ba idannuwanta suk sauka a kan mutanen dake falon a zaune aka tataunawa, wace ta so juyawa ta koma, sai dai Mamah dake kallin hanyar saukowar ta ce" FATIMA wuce mana ki yi abinda ya sauko ki kina jan jiki ashe baki sauko ba sai yanzu?"
Dagowar mata ukun dake zaune suka zuba mata ido ya sake neman sakata faduwa, nan da nan kuma tsoron wanda ke zaune hankalinsa ba a kansu ba ya darsu a zuciyarta tana tunanin Allah ya sa ba shi bane a wajen
Da kyar ta iya aro jarumta ta karaso inda mutanen ke zaune ta duka kar kasa daf da Mamah muryarta a sanyaye ta ce" Barka da warhaka, yaya karin hakuri?"
Amsawa suke yi su dukansu, Mamah ta ce" Alhamdulilah Zahrah, kin ga mahaifiyar narigayiyar nan, ga yayarta ga kuma kanwarta........"
Sannan ta dube su ta ce" Hajia y'ata ce, sunnnata Zahrah"
Da kula suke sake gaisawa, a sanyaye take amsawa sannan a dari dari
Dan murmushi wace aka kira da yayar marigayiyar ta yi tana duban Hajia ta ce" Mamah na zata su Maryam ne kawai yan kannan nawa....................?"
Mamah ta yi murmushi ta ce" Baki santa bane, itama yata ce"
Sai kuma mama ta kalleta ta ce" Tashi ki je ki fitar da dukkan kayan bukatarki ki je kicin din filin gida ki ba baba ta gyara maki komai sai ki toya da kanki, nima ina jira kwanona maza yar albarka"
Kai ta gyada ta mike da dan sauri, domin dama kamar an wani daureta haka take ji ko dan mutanen wajen bakinta ne da kuma wanda yake dodo a wajensu baki daya?
Da sauri ta shige kicin din, sai kuma ta ja turus tana kallon ikon Allahn da ake yi a babar kofar kicin din ta baya, watau kofarsu ta aikata munafurcinsu daga boye, itane ake rufewa da gini bama da kofar ba bale su yi tunanin wata rana a bude
Dan gwauron numfashi ta sauke sannan ta shiga harhada kayan bukatarta gaba daya ta fito da su ta wuce tana mamakin hali irin na yayansu,
Yanzu zaman makokinma ba zai yi da manyan suturu irin ka su ABAH ba? Kuma a gaban sarakuwarsa ne yake zaune haka kirji a aune yana binsu da kallo ido cikin ido,......uhum Allah shi kyauta
Mama dake kallon iyayen marigayiya da mahaukacin mamaki irin mai neman kashe bawan nan da kyar ta iya jan gwauron numfashi tana dauke dubanta ta maida kan Baban gida, sai dai yadda ta ga ya saka idannuwansa cikin na matar da aka gama magana a kanta tamkar yan giya yana kare mata kallo daga sama har kasa ya sakata jan dan numfashi hadi da yin alamun da shi take , kafin ya juyo dubansa ya daj zuba mata ido sai kuma ya dauke duban nasa ya mike tsaye ba tare da ya basu amsa daya ba ya dan sada kansa a hankali ya ce" Zan je office yau, sai na sauko"
Gaba dayansu sai wani katon shakunsa ya nemi kama su, banda Mama dake kallonsa a ranta tana tunanin hala tafia zai yi ya barta da basu amsa bayan ita bata san me yake tunani da wannan magana ta shirme ba?
Da kula ta ce" Baban gida ama ai magana ake yi ko?"
Fuskar mahaifiyarsa mai tarin ni'ima irin haske na fuskar uwa ya zubawa ido, sai kuma ya lumshe luhu luhun idannuwansa masu shige da na mashaya a nutsensa ya ce" Ku gama maganar Mamah"
Daga haka ya sake juyawa
Har ya kusan ficewa ya kuma jin muryar mahaifiyarsa a daf da shi, watau biyo shi ta yi a sanyaye ta ce" Kai, yaya zaka mike ka barni da mutanen dake zaune dominka kace wai na yanke hukuncin da ya dace bayan ka san ana iya yankewar bai maka ba?, Ni abinma ya girmami tunanina, su da suke da macen yau dududu kwana takwas da rasuwa su fito da wannan maganar? Kuma yayarta bama wata kanwarta ba? Ama ka fadi abinda ke ranka zai fi ka ji tunda kai zaka zauna da ita ba kowa ba"
Shi kam bai ga menene na jan maganar ba, ba yace a yanke hukuncin ba? A yanke kawai menene a ciki kuma?,
Dan murmushi ya yiwa Mama a hankali ya ce" Du abinda kika yanke zan yi biyaya, kuma a nan zan ci abincin rana, na tafi Mamah "
Ya wuce ba tare da ya sake jiran jin wata maganar ba
Mamah rasa me zata fasarta wannan lamari ta yi, jiki ba karfi ta dawo ta zauna a sanyaye ta ce" Hajia, ku yi hakuri dan Allah......"
Hajia bata tsaya ta ji karashen maganar Mama ba murya na rawa ta fashe da kula tana sada kanta irin abu na sukartan nan ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Hajia dan girman Allah kar ku ce mana aa, mun zauna mun yi shawara ya fi a irga, kin ga dai yarinyar nan shekararta tara tana zawarci, run yana da shekara ashirin da shida shida take gida , yayanta biyu yan mata daga su bata sake wani auren ba bale ta haihu, ta kama mutuncin kanta tana sana'arta, a kulun kulanta shine ba zata sake aure ba dan tana tsoron lamarin mazan zamani, tana tsoron ta tashi ta ba wani namiji yarda ya wulakanta ta, a yau da yar uwarta ta rasu na kawo mata maganar nan ta sha kuka, daga karshe ta gane lalle inafa gaskiya babu dan mutuncin da zai riketa irin MARΓCHAL, HAJIA ku taimaka ku mana rai ku amshi tayin nan yar uwarta ta maye gurbinta su yi zamansu lafiya...."
Gaba daya ji Mama ta yi gwuiwarta ta sake sacewa, sosai lamarin take jin shi wani iri
A nutse ta ce" Ba nufina ku yi hakuri hakan ba zai yiwu ba fa Hajia, nufina ku yi hakuri har a raraka, gani na yi yaushema Allah ya amshi Manal? , Bayan wannan kin sani sarai a hausa ba mace take da iko da Ζ΄aΖ΄anta ba, yaron nan da mahaifinsa mai tsaye a kan ra'ayin kansa, inaga ku bani lokaci na same shi, abinda yace in sha Allah sai na sanar maku ta waya"...........
A gaskiya ba haka suka so ba, so suka yi Mama na jin haka ta hhaye ta zauna kan maganar harma ta fi su nuna farin cikinta, ama a yanzu sai suke jin wata shaka shaka ta afkawa abin kai tsayen da suka yi, da sun sani da sai sun fara samun kansa sannan su kawo maganar
Kuma Allah yana gani maganar bama ta Maman su manal din bace ta yayar tata ce, ta nuna mata cewar idan fa ya kubuce masu shikenan, dukkan wani jin dadi da farin ciki da gata da isa da suke da shi a da zai zama babu tunda wadda ta hada ta mutu
Wannan dalilin ya sa ta zabura ta nemi ganawa da Maman da kuma MarΓ©chal din, sai gashi ta gani gannin idannuwanta cewa Mama ba kanwar lasa bace kamar yadda y'arta ke ce mata bata so su shigi junna da Mama dan walahi d'anta na yi mata biyaya fiye da tunanin mai karatu, babu wanda ya isa ya saka shi abu kai tsaye komai wahalarsa ya aikata irin iyayensa, baya wasa da su baya hadasu da komai, kimkim dinsa kuwa halita ce ta dan Adam
Jiki a sanyaye suka fito suka nufi bangaren Docter dan yi masa salama domin tafia zasu yi sai kuma sun juyo
A cen suka samu Aunty amarya tana zaune tana karatun Alkur'ani shi kuma yana jan carbi yana kuma sauraronta, dan bashi da abin yi yau, ita kuma girkinta ne
Sosai ya sake yi masu gaisuwa da fatan alkhairi, shima ya karra masu wata kyauta sannan ya masu addu'a suka mike suka fice
Tunda suka fita take son dauko maganar ama ta gaza dan Auntu amarya dake zaune, har dai ta gaji ta ce" Magana nake da ita fa docter"
Murmushi kawai Abah ya yi ya ki ce mata komai, har dai Aunty Amarya ta kilace alku'aninta ta shiga taka matatakala ta haye sama Hajua kuwa na binta da kallo har ta bacewa ganninta sannan ta ja tsaki kasa kasa ta ce" Sai shegiyar dakakiyar zuciya kin sako yarinya a gaba kamar ita ta aikata laifin ko kunya bakya ji kai kamar na saliha ama na tantiriya ne!"
Ido Docter ya dan kankance yana dan saurarawa dan ya ji abinda take fadi,
Ido ya dan wara ya ce" Laifin me ta maki ita kuma?"
Dubanta ta maido kansa da yannayin sunna iya fashewa idan ta kama ta ce" Na taba yar gwal ko Docter?"
Murmushi ya yi bayanane kasa kasa ya ce" Eh gaskiya kusan haka..."
Baki ta tabe tana cire kai hadi da girgiza kafafuwanta, kana dubanta zaka fahimci tsabar rigima ke cinta take kuma nema su yi da wanda ke kusanta a irin wannan lokacin
Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye dan ya kawar da fadan nasu ya ce"
ππππππππππ
*DAΖIΖA BIYAR*
ππππππππππ
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin Ζai*
_10_
*Garabasa , garabasa, ππ₯°, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°π₯°π₯°*
Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye dan ya kawar da fadan nasu ya ce" Allah ya rahamshe da Manal Maman Baban gida"
Da sauri ta kalle shi, sai kuma ta sada kanta, shi kam ya iya saka mutun jin kunya, tsakani da Allah tana matukar jin kunyar cirat a ambaceta da maman Baban gida, Allah ya taimaketa daga ita sai shi da yau ya raba mata abin kunya walahi
Murmushi ya yi yana dan jan kafarsa a hankali da ta masa nauyi ya ce" Kin gani ko Zuwaira? Idan kika kawo min kukan kina damuwa da lamarin halayarta ya dace ace ta rungumi dangi a matsayinta na matar baban wansu....... nakan ce maki ki yi hakuri mu yi ta sanarwa Allah, Baban gida ba zai taba tabewa ba domin d'a ne mai biyayar iyaye, albarkarmu na biye da shi du inda ya yi, babu abinda zai ci karfinsa da ikon Allah sai dai idan Allah ya riga ya hukunta kadararsa ce matakin ci gaban rayuwarsa ko samun aljarnarsa ne hakan, sannan mu bai taba kawo mana karar matarsa ta masa wani abin ba, kin ga gaba dayama ashe zaman nasu ba zai jima ba shekara biyar cikin ta shida da aure Allah ya amsheta, Allah ya sa mu cika da kyau da imani"
A sanyaye Mama ta ce" Amen ya Allah "
Sai kuma ta dago, fuskarta ta nuna ainahin alhinin dake cikin zuciyarta
A sanyaye ta ce" yanzunma cikin wata damuwar nake Docter, na rasa a wani gurbi zan ajiye haka, abin kamar an saka son zuciya, rashin sannin ciwon tasu da ta rasu ya mik tsauri ni kam, zuciyata sai take nuna min harda wata manufa a kasa, ko kawai hasashena ne?........gaba dayama ni na rasa me zan kirayi lamarin, ya girmami tunanina, Yaushema yarinyar nan ta rasu? Y'arsu ce fa kuma, kanwarta ce ita kuma y'arta ce, ama wai suka kawo min maganar yayar tata ta maye gurbin kanwar, yau fa kwana takwas kadai da rasuwar nan, kuma ka san cewa itama Manal din nan ta girmeshi bale yayarta? Bayan wannan ka sani sarai Baban gida baya magana, koda an kaishi ana cutar da shi ba zai taba sanar mana ba, bawan Allah salihi da shi baya cewa komai, abin tausayi da shi kana gani fa baya cewa komai Docter, kuma shikenan sai mu tashi mu sake daukan wata gyatumar mu maka masa kennan shi a haka zai gama rayuwarsa ne da auren yayunsa?, Gaba daya lamarin nan bai kwonta min ba a raina Docter "
A gaskiya abin shima ya bashi mamaki, idan aka yi duba da rasuwar kanta yaushe aka yi? Menene na gagawar nan? Ba maganar gagawa dan kuwa idan haka dinma suke so ai sai su yi hakuri a kalla a yi arba'in din mamaciyar ko? In wasu nema har sa bari a yi shekara domin a hausa muna daukan rasuwa da mahimmanci sosai, idan muka rasa wani namu abin na taba mu, munna jimawa kafin mu saku sosai, su kuwa gashi tashi daya har sun dubi haka, duda abu ne mai mahinmanci sosai, shi din kansa a yanzu ai zai shiga hali ne na takura na rashin mace a gefensa dan kuwa wanda ya saba da kulawa irin ta mace yakan shiga hali na matsi idan ya wayi gari babu kulawar nan, ko a baka abinci a kan lokaci ai alkhairi ne, bale sauran bukatu nantau da gobe, sai kuma maganar salihi da shi din ya so bashi dariya, wai bawan Allah baya cewa komai wai mu kaishi a ringa cuta masaπ....... uhum lalle Zuwaira bata san aljanin danta a zuciyar mararsa jin cikin gari ba, rashin kawo kukan iyalinsa sun masa wani abu kuwa yana jin dadin haka dan hakan zai kawar da wasu rashin jituwa a tsakanin iyayen miji da matarsa
Da kula ya ce" Yaushe suka yi maki maganar?"
Mama ta ce" dazun nan kafin na rako su nan, kuma wai Baban gida ya tashi ya tafi ya barni da su wai abinda muka yanke ya yi daidai"
Da mamaki ya ce" Shi Baban?"
Hajia ta tabatar masa kwarai kuwa
Aba ya sake yin dan tsai , sannan ya ce" Kin gane, in sha Allah lamarin nan zamu tsaya mu fuskance shi yadda za'a ji dadinsa, kin ga idan adini muka yi duba, wanda a cikinsa muke, dokokinsa muke bi dan son samun rabauta, haka din ba laifi bane, domin mace aka ce ta yi takaba ba namiji ba, namiji ko yau iyalinsa ta rasu ana iya aura masa wata yana iya tarewa da ita, sannan amsar da ya baki cewar ko yayane kika yanke dan ke kika haife shi, kai tsaye ba zai aminta ko ya ki aminta da abun bayan gaki a zaune ba, wannan ladabi ne irin na Ιan docter baban Ahmadu jikan Sulaimana, zamu fara basu lokaci, mu yi bincike a tsanake, mu fadawa Allah, ko yayane muke son mu ganshi da mace ba zamu dauki ko wace kala mu hada su aure ba dan mun haife shi ko dan mun isa da shi, yana da haki a kanmu na yin binciken macen da ya dace ya aura, in har alkhairi ce a gareshi ki kwontar da hankalinki Allah ya tabatar mana, idan kuwa ba alkhairi bace Allah ya hanna"
Da dan damuwar ta ce" Docter yayar matarsa ce fa, itama matar tasa ta girmeshi fa, shekaru kusan biyar tsakani kennan?"
Da mamaki yake kallonta, sai kuma ya ce" Na san dai ba addini kike son ce min ya hanna ko ya yi nuni da yin hakan ana wahala ba, ko so kike ki ce min ta fi karfin yaronki ?"
Kasa kasa ta kalle shi tana soke kai dan yadda ya yi tambayar harda ta neman magana da son sakata fadin abinda bata yi niya ba!
Gwauron numfashi ta ja sannan ta sauke, kwarai kuwa maganar Docter haka ce, Allah shi kadai ya san yaya gobe take, ko menene ka fara kai kukanka gareshi shi zai saka ka a hanyar da ta dace da kai
Zata je ta dukufa ta yi ta fadawa Allah, Adu'ar mahaifiya ba zata taba faduwa kasa ba, gaba daya sai lamarin duniya ya sake fice mata a rai, watau dai wanda ya mutu shi da mutuwarsa ko? Allah ka rufa mana asiri.
Mikewa ta yi ta masa salama domin ta saka matarsa ta tashi tun dazu babu dadi, in sha Allah gobe idan ta zo zasu karra tataunawa a kan lamarin Baban gidan
A daidai lokacin da suke wannan tataunawa, a irin lokacin ne shi kuma yake zaune a office din abokinsa Docter Habubakar
Hoton cikinta da aka dauka ne a gabansa yana kallo da kuma bayanin da docter ya yi masa
Ajiyar zuciya ya sauke hannunsa daya a jimke a saman takardar hoton ya dago dubansa ya ce" ka san a zamana da ita, ta matukar dauki magungunnan matan nan da mahinmanci, yawancin lokuta kuma yayarta ke aiko mata da su, wasu kuwa ta siya da kanta........., Koma menene ya hadasa mata wannan zubar jinnin har ya yi sanadiyar mutuwarta sai na nemo shi, kuma ko waye ya kawo shi kasar nanma sai na daure shi!"
DOCTER Habubakar cike da jin ba dadi a zuciyarsa na halin da MarΓ©chal ke ciki ya ce" a gaskiya ko menene idan ba poison bane, toh wani mugun abu ne da aka hada dan ya zubar mata da jinnin !,ko menene yana iya kisa a sha ko a matsawa, irin yadda ya ringa sakata zubar da gudajin jinnin nan baki ba karamin guba ne ba"
Kai ya girgiza yana dafe gabain goshinsa, a nutse ya ce" Na gode docter, Please ka hada min duka kaf takardun gwaje gwaje da magungunnan da kuka yi mata anfani da su da dukkan hasashenku da abinda bincikenku ya baku, zan gabatar da bincike a tsanake bi'izinillah"
Da wannan suka yi salama ya tafi domin sai ya harhada komai zai kawo masa da kansa
Koda ya karasa office ya kasance ne hankalinsa a matukar rabe gida biyu, daya na tunanin lamarin nan, dayan kuwa a kan rigimar da ake yi da shi kan sai ya saka hannu a kan daga yau yan mata sunna da yancin yawo da pant ma idan sunna so , domin yancinsu ne, du wanda ya zage su ko ya nemi shiga hakkinsu sai iko ya kama shi an ja shi an yi shara'a da shi
Takardar ya dauka ya ja waje ya sakata ya rufe sannan ya ci gaba da aikinsa dan yana son abinda zai dan dauke masa kewa da tunanin iyalinsa,
A saman lebensa ya furta" Allah ya maki rahama Manal, Allah ya sa aljanna ta zamto makomarki, ni dai baki yi mun komai ba,koda kin min na yafe maki, ina fatan nima baki tafi da fushina ba Manal" ( Ya Allah ka azurta mu da samun yafiyar abokanan rayuwarmu a kowani Hali )
Bai samu komawa gidan ba, sai kusan karfe hudu Amir ya nemi izinin shiga office dinsa yana dauke da kayan abincin da Mamah ta yi kiransa ta saka ya kawo masa dan ta ji shiru bai zo ba kuma tana kiransa bai daga ba
Abincin yake kallo, Waina ce ta yi hulu hulu ta yi jajir ta yi kyau a ido, ga kanshi dai ya cika wajen, sai miyar taushe ta samu wadatacen naman rago itama sai daukan ido take sannan babu mai a kwonce a cikinta kamar dai yadda baya son abinci da mai din nan
Dan kallon Amir ya yi yana son tambayarsa wa ya girka? Sai dai yan nauyin bakin suka rufun masa har ya zuba masa a plate ya ajiye ya bude frij dinsa ya dauko jus dinsa da ruwa ya ajiye cikin girmamawa ya sanar masa zai koma office idan an jima kadan zai dawo ya kwashe kayan
Idannuwansa ya lumshe masa alamun godiya yana kallonsa har ya fice sannan ya matso abincin ya yi Bismillah ya fara ci a hankali da tunanin ba zai taba samun dandano irin na hannun Manal ba, yana fara ci ya ji test din wainar ya yi masa sosai a saman harshensa, ko dan yana tare da yinwa ne ko yayane? Shi dai ya ji ba laifi wainar ta birge shi dan haka ya ci iya cinsa ya koshi ya yi hamdallah sannan ya mayar gefe ya mike dan fita zai yi zagayen cikin gari, dukkan abinda zai dauke masa kewa yake nema ido rufe dan baya son damuwa a rayuwa, rasuwar iyali kuwa babu abinda ya kaishi damuwa, da aka sanar masa babu ita sai da ya ji kamar zai summa a tsaye, kallon gawarta kawai yake yi ya rasa abin fada har sai da Abansu ya zo ya tunasar da shi abu mafi mahimmanci watau ya gafarta mata sannan ya yi mata addu'a